Isa ga babban shafi

Shugaban Kamaru Biya ya koma gida bayan raɗe-raɗin mutuwarsa da aka yi

Shugaban ƙasar Kamaru Paul Biya ya sauka a filin jirgin sama na babban birnin ƙasar Younde yau litinin bayan raɗe-raɗin mutuwarsa.

Shugaban ƙasar Kamaru Paul Biya ya koma gida bayan raɗe-raɗin mutuwarsa
Shugaban ƙasar Kamaru Paul Biya ya koma gida bayan raɗe-raɗin mutuwarsa via REUTERS - WU HAO
Talla

Shugaban ya kwashe makwanni da yawa baya ƙasar abinda ya haddasa cece-kuce mai zafi da nuna damuwa kan rashin snain inda ya shiga.

Shugaban mai shekara 91 a duniya ya bayyana a talabijin bayan saukar jirginsa a Younde, an kuma hangi yadda yake gaisawa da manyan jami'an gwamnati yayin da matarsa Chantal Biya ke kusa da shi.

Bayan kammala gaisawar ne jerin gwanon motocin shugaban ƙasar suka ɗauke shi inda aka hangoshi yana ɗagawa magoya baya hannu

Murna ta kaure da kiɗe-kiɗe bayan da shugaban ya sauka a filin jirgin, inda nan take ya zarce fadar shugaban ƙasa kamar yaddda gidan talabijin na CR ya nuna dawowar shugaban.

An hangi yadda magoya bayansa suka sanya riga ɗauke da hoton Paul Biya suna murnar dawowars aƙasar..

A baya bayannan ƴan ƙasar sun ta nuna damuwa da tambayar halin da shugaban ke ciki da ma halin lafiyarsa bayan nemansa da aka yi sama ko ƙasa aka rasa tun bayan da aka ganshi a watan Satumba lokacin da ya je ƙasar China da ƙasashen Afirka.

Shugaban ya sauka a jirgi mai lamba CMR001, kuma ya taso daga birnin Geneva inda ya kwashe makwanni yana zaune kamar yadda jami’an gwamnatin ƙasar suka tabbatar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.