0% found this document useful (0 votes)
70 views119 pages

FADEELAH by Fadila Sani Bakori - TXT by Hausanovels - Com.ng

The document is a narrative centered around a character named Fadeelah, who faces familial pressure regarding her job at Rahama TV. Her father disapproves of her work, leading to a conflict between her aspirations and family expectations. The story also touches on themes of societal judgment and personal choice within the context of Hausa culture.

Uploaded by

4ytghtdfkt
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as TXT, PDF, TXT or read online on Scribd
0% found this document useful (0 votes)
70 views119 pages

FADEELAH by Fadila Sani Bakori - TXT by Hausanovels - Com.ng

The document is a narrative centered around a character named Fadeelah, who faces familial pressure regarding her job at Rahama TV. Her father disapproves of her work, leading to a conflict between her aspirations and family expectations. The story also touches on themes of societal judgment and personal choice within the context of Hausa culture.

Uploaded by

4ytghtdfkt
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as TXT, PDF, TXT or read online on Scribd
You are on page 1/ 119

📚 FADEELAH 📚

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare
da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻

Daga
Fadila Sani Bakori

Marubuciyar 👇🏻

1) Oga Habib
2) Abdurrahim matukin jirgin ruwa ne
3) Meenalyn daddy
4) In da rai
5) Rayuwar Haidar
6) So ne sila
7) Daga Allah ko d'orawa kai And now Fadeelah

GARGAD'I: Ban laminta ayi min amfani ko a juyamin littafi ba tare da izinina ba,
dan haka a kiyaye.
08063
830828

SANARWA" Masu tambayata akan gyaran jiki ,akwai hanyoyi daban-daban da zan kawo
muku na gyaran jiki acikin wannan littafi mai suna Fadeela.

GODIYA: Ina godiya da Allah Ubangijin talikai da ya ba ni lafiyar rubuta wannan


littafi.Yadda na fara lafiya Allah ka sa in gama lafiya cike da nasarori.
SADAUKARWA" Wannan shafin sadaukarwa ne ga jaruman marubuta masu aiki da jarumta
wajan fadakarwa, ilimantarwa ,tare da nishad'antar da jama'a abisa harshen
Hausa,wato Jarumai writers association 👍🏻

Littafin Fadeela na kud'i ne Auntyna, za ki same shi akan farashi mai sauki #300
kacal .

Page 1

Bismillahir rahmanir rahim.

KADUNA GARIN GWAMNA


Tafiya take yi ahankali da alama dai kamar agajiye take.Sanye take da jalbab Hijab
brown har kasa sai madai-daiciyar hand bag da ta rataya a kafad'arta. Yanayin
tafiyarta kawai zaka kalla kasan ma'abociyar hankali da tunani ce,dan duk da
tafiyar da sauri take yinta,hakan be hana fitowar natsuwarta ba, akwai isassar
natsuwa a tare da ita.Wani madai-daicin gida ta shiga wanda daga ganin gidan kasan
mutanan cikinsa suna rayuwa a takura ne acikinsa,dan gidan k'arami ne kwarai, kuma
gaba d'aya d'akuna biyu ne acikinsa,sai bayi da d'an k'aramin dak'in girkinsu
(kitchen).

Da sallama ciki-ciki ta shiga gidan.


Wata dattijuwar matace ta fito daga kicin d'in , wadda ba zata haura shekaru
arba'in ba, da gani girki take dan idonta sun cika da hayak'i ,jin sallamar
Fadeelah ne ta fito.Kallan mai sallamar ta yi ta ce"Fadeela,yauma sai yanzu kika
samu damar dawowa? " Wadda aka Kira da Fadeela cikin sanyi alamun dakyar ma take
maganar ta ce"Yi hakuri Mama ,da fatan dai Baba bai dawo ba ?" Matar banza ta yi da
Fadeelah ta koma kicin d'in ta ci ga da girkinta.

Fadila ko guri ta samu ta zauna tana mai yaye Hijab din jikinta,tana nan zaune wata
yarinya daga gani dai k'anwarta ce ta zo ta ce"Aunty kin dawo?"Fadila kai ta d'aga
ma yarinyar,yarinyar kuma ta ci gaba da cewa"Aunty ,Baba d'azu da ya dawo gida sai
fad'a ya ke wai har yanzu biki dawo ba,kuma ya ce daga yau kin gama zuwa
aiki"Fadeelah cikin furgici da jin abin da k'anwar tata ta ce ta d'ago manya-manyan
idanunta tana kallan k'anwar tata da su ,tama kasa cewa komai,sannan dai zuwa can
ta ce"Husna, an
b'ata ma Baba rai ne ? Inda ko da zan fita aiki mun gaisa da shi" Husna da yake
irin yaran nan ne masu gulma da shaigen surutu, ta ce"Wallahi Aunty, ji na yi yana
cewa wai daga y...."Bige bakin Husna da mahaifiyarsu ta yi ne ya sa ta yi shiru.
Fadeelah cikin damuwa ta kalli mahaifiyarta ta ce"Mama,abin da Husna ta ce da gaske
ne ko?"Ban sani ba,idan Baban naku ya zo kin ji daga bakin shi,"

Fadila da a Duniya in dai kana so ka ga furgicinta tom ayi mata maganar dakatar da
ita daga aikin da take yi a Rahama TV.

Ji tayi gaba daya ma yunwar da take ji ta koma,hakan ya sa ta shiga d'akinsu ta


kwanta ,tana tunanin me za ta yi ko tace ma mahaifinta idan ya tunkareta da
maganar,dan shekararta d'aya kenan da fara aikin amma kusan koda yaushe haka suke
da mahaifinta,kusan kullum dai maganar kenan,har ta fara tunanin aje musu aikin su
ta huta.

Fadila na nan kwance ta ji shigowar mahaifinta.Ya shigo ba jimawa aka kira sallar
magriba,ana Kira ya tashi ya fita,hakan ya ba Fadeela damar fitowa tsakar gidan ta
yi alwallah da sauri ta koma d'aki dan tana gudin had'uwarta da mahaifin nata.

Fadeelah bacin ta idar da sallar magriba ne ta aiki k'anwarta Husna ta zubo mata
tuwo ta ci
Tana nan zaune tana jiran Kiran mahaifin nata amma shiru har barci ya kwasheta.

Washegari dama kullum k'arfe bakwai ( 7:00 AM) Fadeelah ke fita aiki, bayan ta idar
da Sallah ta yi azakar kamar yadda ta saba duk safiya, ta yi wanka ta shirya ta
d'akko Jakarta ta lallab'a tana tafiya,so take ta fita a hankali gudin kar
mahaifinta ya ji motsinta,ta kama k'ofar gidan zata bude kenan sai jin muryar
mahaifin nata ta yi yana cewa"Fadeelah, zo nan"gabanta na faduwa alamun tsorata da
ganinta da mahaifin nata ya yi ta k'arasa inda yake.

Tana zuwa ta zuk'unna kanta k'asa,cikin rawar baki ta ce"Ina kwana Baba"Maimakon ya
amsa gaisuwarta sai cewa ya yi"Ina za ki kike sand'o haka?"Cikin rawar baki
Fadeelah ta ce"Aiki"Lafiya kike sand'o?" To nan fa ba amsa,shiru ne ya biyo baya.
Mahaifin Fadila cikin d'aga murya alamun ya fusata ya ce"Na ce lafiya kike sand'o?
Hakan ya tabbatar min da kin ji sak'ona kenan ?"Fadila dai kanta kasa ta kasa cewa
komai.Mahaifin Fadila ko ya ci gaba da cewa"Fadila,daga yau na hanaki wannan aiki
dan bashi da amfanin komai gareki illah zagi da kike jawo min wajan jama'a, sannan
zan baki zabi guda biyu zaki iya daukar duk wanda ya yi miki ko dai ki kawo min
wanda kike so ko kuma ni in zab'a miki ,dan in Allah ya yarda ba zaki k'ara min
wata uku agida ba,dan naga abin naki bana k'are ba ne!"Mahaifin Fadila na gama
fadin abin da yake fada ya bar Fadila nan zuk'unne ya shige dak'in shi.

Fadila dakyar ta samu ta lallab'a ta tashi ,sannan ta Kira abokin aikinta. Bacin
sun gaisa ne ta ce"Jamilu,Baba fa ya yi yadda ya saba,yau ma ya hanani zuwa
aiki,ko kuma in ce maka ma yau ya fi na koyaushe, dan bana jin zai kuma barina
k'ara zuwa aiki ,ina ganin Jamilu zan hak'ura in aje aiki kawai "
Wanda Fadila ta Kira da Jamila ya ce"A'a,Fadila kar ki yi haka, ni shawarar da zan
baki ki yi auran mana, idan kina son aikin Wanda za ki aura in ya amince sai ki ci
gaba da aikinki"Jamilu,kasan dai bana maka boye-boye ko? ko kuma ince kasan komai
dan gane dani,wa zan aura in kace haka?" Daga can b'angaran Jamilu ya ce"Ina, M'd
fa?, Allah Fadila da gaske yake son ki,ko aiki kina ganin sai ki kwana nawa biki zo
ba amma ba zai ce miki komai ba,hakan kad'ai ya isa ya sa ki yarda yana sonki so na
aur.."Fadila dakatar da Jamilu ta yi ta hanyar cewa"Dan Allah mu yi magana mai
amfani kabar wannan maganar ina zan kai tunbin mutumin nan Allah bana son
shi"Dariya Jamilu ya yi ya ce"Tom ,shi kenan zan tayaki addu'a, zan zo gidan in na
tashi aiki in yi magana da Mama"

Sallama su ka yi ta kashe wayarta ta tashi ta koma d'akin su.Cire hijb din dake
jikinta ta yi ta share dan madaidaicin gidan nasu,ta yi wanke-wanke, bacin ta gama
ne ta samu mahaifiyarta ad'akin mahaifinta shi kuma lokacin ya fita.
Bacin sun gaisa ne Fadila ta kalli mahaifiyar tasu ta ce"Mama,dama nace inda yanzu
Baba kasuwar sai a hankaki ,dan Allah kisa baki ya barni na ci gaba da aikina,
albashin zai taimakamana"Mahaifiyar Fadila ta dade tana kallan Fadila bata tanka
mata ba ,sannan zuwa can cikin sanyi ta ce"Fadila,mahaifinki fa shi ya biya miki
kud'in da kika yi karatu har kika kai haka,kuma da amincewar shi da taimakonshi
kika fara aikin nan,sai dai Fadila, tunda kika fara aikin nan k'ananun maganganu
suka yi yawa akanki wa mutane,kowa da abin da yake cewa ,tom mahaifinki ya kasa
jure maganar mutane dan acewarshi duk abin da aka ciki yawan magana akan shi baya
albarka, saboda wasu bakinsu ba mai kyau bane, ni da mahaifinki munsan wacece
ke ,tom amma futane sun sa ma aikin nan naki ido ana ganin kamar mun dogara da
aikinne kina yawace-yawacanki kina cida mu in da yanzu kowa yasan mahaifinki ba
kamar da ba ,dan haka ni yanzu shawarar da zan baki ki yi hakuri da aikin nan idan
akwai wanda kuka yi wata magana ki fito da shi ki yi auranki, alabashi idan mijinki
ya amince sai ki ci gaba da aikinki a d'akinki"Shiru Fadila ta yi,sannan zuwa can
bacin ta ja doguwar ajiyar zuciya ta ce"Tom, Mama na ji na yarda, amma abin da nake
so ki fahimta koda da fa na aje aiki a yanzu bani da wanda mu ka yi maganar aure"

Atakaice dai Fadila babu yadda ba ta yi ba ganin ta shawo kan mahaifiyarta akan
mahaifinta ya janye kudirinsa akanta ,amma taki fahimta,dole ta hakura ta tashi.

Abu kamar wasa yau satin Fadila biyu kenan da daina zuwa aiki har ma ta hakura.

ADAMAWA STATE

Koda na shiga garin Adamawa ban tsaya ko ina ba sai gidan wani mai da na tsaya shan
mai dan in kara gudu.Saidai sosai na mamaki ya isheni ganin an zuba min man ance in
tafi ba tare da an amshi kud'ina ba.Mamaki ya sa na ja na tsaya na kasa tafiya.Abin
mamaki motar da ke bayana ma hakan take itama ba'a anshi kud'in ta ba,haka akai ta
zuba ma duk motar da ta shigo shan mai mai kyauta ba tare da an amshi kud'i ba.Ni
ko kasa tafiya na yi dan ina son in ji dalin hakan,hakan ya sa na samu d'aya daga
cikin ma'aikatan na tambayeshi dalilin da ya sa suke bada mai kyuta.Cikin washe
baki ya nuna min wani bangare daga jikin gidan man ya ce min"Me aka rubuta a can?"
Ni ko na bashi amsa da "Alhaji Sagir mai shadda" ya ce min "Tom yau ne ake auran
yaronshi d'aya tilo,wato Muhammad Sagir,ai shi ne dalilin da ya sa kaga ana bada
mai kyauta, murnar auran ne kasan yana ji da yaron sosai"Kai na jinjina sannan na
kama hanya zan tafi,wanda na tambaya tareni ya yi da cewa"Amma dai Malam ba anan
garin kake ba?"Eh,ni ba d'an garin nan ba ne,amma me ya sa ka tambayan?"Yau ai duk
wanda yake Adamawa ya san alhaji Sagir mai shadda ,kai kuma naga bisa alama baka
san shi ba shi ne dalilin tambayar" Kad'a kai na yi na tafi ba tare da na amsa mai
ba.Ina fita ban tsaya ko ina ba sai Gidan Alhaji Sagir mai shadda,dan in je in
inga wainar da za'a toya agidan ,dan nasan za ayi kallo,hakan ya sa na lalibi
gidan.

Tun kafin in isa layin gidan nake jiyo ganguna maroka kala-kala natashi,tafiya nake
ina kalle-kalle ganin tsaruwa layin gidan kawai,sai dai mai ina zuwa get d'in
farko na shiga gidan akatareni alamun ina get past dina,hakan ya sa dole na ja na
tsaya ,ina nan tsaye sai ga wasu maroka sun zo in bude musu get din za su shiga na
yi b'adda kama na shige cikinsu muka shege tare.

Koda ganin yawan zama'ar taron bikin kadai ya isa ya shaidamaka bikin d'angata ake
yi. Shagullula ake kala-kala na wasannin gargajiya da na zamani, nama rasa ina zan
kallah,ga masu gidan gwarya nan da mabiyansu ,da masu kid'an shantu abin dai gunin
burgewa.Barin wajan na yi dan naga jama'a sun fi ra'ja'a awani Shashi can da nake
hangowa wanda adon wajan yafi na ko ina,sai dai tun kafin in isa wajan daddad'ar
sanyayyar muyar Auta MG boy ce ke tashi a wajan,da sauri na isa wajan dan tabbas
taron na manya ne.Cikin daddar muryar nan tasa yake rero ma amarya da ango
wak'a ,Baitoci ne masu tsada ke tashi awajan Wanda sukasa na kasa matsawa ko
ina.Ana cikin haka ne Amarya da ango suka iso wajan,sosai na shakala da kallan
Muhammad Sagir,kyakkawan matashi ne dan kwalisa ,kallo daya za ka yi mai kasan
bashi da wata damuwa , fuskar nan tashi cike take da annuri ,ga jajan lip's din shi
da suka k'ara ma fuskarshi kyau.
Muhammad Sagir mai shadda kyakkyawa ne na bugawa a Jarida.Amayartashi ma ma sha
Allah.Komai da komai ya ji dan itama zan iya kiranta kyakkyawa ta bugawa a Jarida.
A haka dai Auta MG Boy ya wakesu da wakar da ya yi ta dominsu.

Haka aka gama shagalgula aka d'auki Amarya aka nufi da ita gidanta da ke Nasarawa
road.

Muhammad zaune agaban mahaifinshi da wadda take mazaunin uwa agaresa wato Hajiya
baturiya.Mahaifin Sagir kallan hajiya baturiya ya yi ya ce"Ga shi nan ki yi mai
nasiha kafin abokanshi su karaso"Murmushi hajiya baturiya ta yi ta ce"Abokanshi ai
tuni na yi musu magana nace gobe sun je suga amarya, amma ni da kai za mu raka
Muhammad gidan shi, dama kuma ba shi da abokan da suka wuce mu, dan haka ni da kai
za mu raka shi"Alhaji Sagir murmushi ya yi ya ce"To fa,wannan kuma wana irin sabon
salo ne? ace mu zamu raka shi d'akin shi ga abokanshi ga komai dan Allah ki bari su
tafi da abokanshi"
Muhammad da sauri ya kalli mahaifinsa ya ce"Daddy,ka yi yadda mommy ta ce plz"Tom
shi kenan Muhammad,amma fa sai dai ka Kira abokanka su je su sallami friends din
amarya sannan ,idan ba haka ba, ba za ni ba"Muhammad waya ya ciro ya Kira Usman ya
sanar da shi su je su sallami k'awayan amarya, daddynshi da mommynshi za su raka
shi d'aki.

Usman da sauran abokan Muhammad suka je suka sallami kawayan amarya.


Can b'angaran Muhammad kuma mahaifinshi ya kallai ya ce"Muhammad,Hafsat dai
k'anwarkace kaida ita duk kallo daya nake muku,kuma nasan Hafsat tana da hankali
sosai dan Allah Muhammad ku zauna lafiya"Muhammad jinjin kai ya yi ya ce"In sha
Allah Daddy"
Hajiya baturiya ma haka ta yi mai nasiha sosai,sannan ta kalli Alhaji Sagir ta
ce"Alhaji,mu je anbar amarya ita kadai"

Amotar Alhaji Sagir suka tafi,shi ya ja motar, babu yadda Muhammad baiyi ba amma
yaki yace shi angone ya huta.

Suna zuwa mai gadin ya bud'e musu get suka shiga.

Muhammad daidai kukannan hajiya baturiya ya ce"Mommy, ban fa so tafiyar nan da


daddy ba, idan fa amarya ta rigo za ta yi min oyoyo ya zan yi da Daddy da muka tawo
da shi?"Hajiya baturiya cikin tonan Muhammad ta kalli Alhaji Sagir ta
ce"Alhaji,yanzu idan amaryata zo zata yi hugg..."Muhammad cikin zaro ido alamun
tsoro da sauri ya rufe bakin hajiya baturi yana raurau da fuska alamun karta
fad'a.Alhaji Sagir ko da ya gane inda maganar tasu ta dosa sharewa kawai ya yi
yana murmushi.

Bakunansu d'auke da sallama suka shiga tankameman falon amaryar.


Saidai amaryar ba ta falon.
Hajiya Baturiya kallan Muhammad ta yi ta ce"Tom, ka shiga ciki ka fito mana da ita"

Muhammad kallan mahaifinshi ya yi ya ce "Daddy,Wallahi gabana fad'uwa ya ke yi tun


da muka shigo gidan nan"Murmushi alhaji Sagir ya yi ya ce"To fa! kin ji kuma wani
sabon salo,wai gabanshi fad'uwa ya ke?"Kai hajiya baturiya ta jinjina ta ce"Nima
tun safe abin da ke damuna kenan fad'uwar gaba ,addu'a kawai na dage na keta ta yi"

Shiru alhaji Sagir ya yi ,dan shi tun jiya yake fama da fad'uwar gaban nan.Cikin
jarumta ya ce"Muhammad,babu komai ku yi ta nanata innalillahi wa inna ilaihir
raj'un.Shiga ka fito mana da a maryar lokaci ya ja"

Muhammad kallan daddynshi ya yi ya yi murmushi ,sannan ya nufi b'angaran amaryar.

Saidai mai tun kafin ya isa ya fara cikin karo da d'ige-d'igen jini,hakan ya sa ya
✍🏻
karasa shiga d'akin da sauri cikin matsanancin tsoro

📚 FADEELA 📚

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare
da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻

Daga
Fadila Sani Bakori

SANARWA: Masu tambaya akan gyaran jiki akwai hanyoyi kala-kala daban-daban da zan
kawo muku na gyaran jiki acikin wannan littafi mai suna FADEELAH.

Page 2

Muhammad kallan daddynshi ya yi ya yi murmushi sannan ya nufi bedroom d'in amaryar.

Saidai mai tun kafin Muhammad ya idasa ya fara cikin karo da d'ige-d'igen
jini ,hakan ya sa ya k'arasa shiga d'akin da sauri cikin matsanancin tsoro,take
jikin shi ko ina ya fara rawa lokaci guda numfashin shi ya tsaya cak ya yanke jiki
ya fad'i.

Can Falon ko alhaji Sagir jin shiru-shiru Muhammad bai fito ba ya sa ya kalli
hajiya baturiya ya ce"Kin ji yaran nan shiru , anya ba tafiya za mu yi ba dan ina
jin ya ma manta da mu"ka kira wayarsa mana dan shirun ya yi yawa"Cewar hajiya
baturiya.
Alhaji Sagir wayar Muhammad ya kira har sau uku bai d'auka ba,hakan ya sa ya kalli
hajiya baturiya ya ce"Yaron nan fa ya manta da mu ,kuma tsabar iskanci na kira
wayarshi bai dauka ba"Shiru hajiya baturiya ta yi sannan ta ce"Bari in yi mai
magana"

Hajiya baturiya cikin tsoro da mamaki ta bi d'ige-di'gen jinin da ta gani da


kallo.Hakan ya sa cikin tsoro ba tare da ko sallama ta iya yi ba ta shiga cikin
d'akin.
Saidai abin da hajiya baturiya ta gani ya sa ta fasa ihu ta fita d'akin da gudu.

Alhaji Sagir ya na nan zaune ya ji ihun hajiya baturi,ko kafin ya yi yinkurin


tashi har ta fito da gudu cikin tsananin tsoro da furgici,dan idanunta gaba d'aya
sunyo waje.
Alhaji Sagir da sauri ya riko hajiya baturiya ya na tambayarta" lafiya ?"Cikin jin
tsoran yanayin da ya ganta.
Hajiya baturiya ko babu bakin magana dan idonta gaba d'aya ya fiffito tsabar tsoro,
bakinta har kunfa ya ke ta na nuni da hannunta kuma ta na son kwacewa daga rik'on
da ya yi mata.Alhaji Sagir ganin hajiya baturi kamar ma ba cikin hayyacinta ta ke
ba ,hakan ya sa ya rik'e hajiya baturiya da k'arfi ahaka ya na janta ya nufi steps
din da zai sada shi da bedroom d'in da suke.
Hajiya baturiya ko ganin inda za su shiga kaita fara girgiza ma alhaji Sagir alamun
ba zata shiga ba.Haka dai alhaji Sagir ya na rik'e da ita ya idasa shiga cikin
d'akin.

Alhaji Sagir cikin rud'ewa ya k'arasa kan Hafsat ganinta kwance cikin jini anmata
yankar rago.Hajiya baturiya ko suna shiga ta yanke jiki ta fad'i.

Alhaji Sagir cikin gigita yake cewa"Hafsat! Hafsat !! Hafsat!!! Ki tashi mana dan
Allah! Ki tashi ki fad'imin wanda ya yi miki haka"Alhaji Sagir ya dad'e cikin
wannan gigitar kafin ya lalibo wayarshi ya yi kira ba tare da yama san wanda ya
kira ba.Ya na kira tun kafin ya ji an d'aga yake cewa"Dan Allah ku tafo da folisawa
an kashe min Hafsat"

Usman da mamaki ya kuma bin wayar da kallo ,cewa ya ke "Daddy,lafiya? Me ya faru ?


Daddy ka na inane?" Alhaji Sagir ko ya rud'e cewa kawai yake ataho mai da folisawa
an kashe mai Hafsat.
KADUNA GARIN GWAMNA

Fadeela yanzu har ta dangana da maganar wani aiki ,haka take zama gida tana taya
mahaifiyarta aikin gida,saidai acikin zuciyarta sosai rashin aikin nata ke damunta.

Mahaifin Fadila da mahaifiyarta zaune suna fira,mahaifin Fadeela ya kalli


mahaifiyarta ya ce"Ina yaran nan?, dan gidan Sale mai kifi?"Mahaifiyar Fadeela ta
jinjina kai alamun ta tuna shi,ya ci gaba da cewa"Tom yau ina kasuwa mahaifin yaron
ya zo ya saman akan yaron yana son abashi izinin zuwa wajan Fadila"Tom,ai shi kenan
,yaran yana da hankali ba laifi"Cewar mahaifiyar Fadila.Nan dai suka ci gaba da
zantawa akan maganar.

Fadeela na zaune da wani littafi anhunta tana dubawa mahaifiyarta ta shigo d'akin.
Mahaifiyar Fadila zama ta yi gefan Fadilar.
Fadila ko ganin haka tasan magana ce mahaifiyar tata ke tafe da ita,hakan ya sa ta
aje littafin hannunta.

Mahaifiyar Fadila shiru ta yi kamar mai tunani ,sannan ta ce"Fadila ,akwai wanda
kuke tare ne? Ma'ana wanda kuka yi wata magana da ta shafi aure?" Kai Fadila ta
girgiza.
Manaifiyarta kuma ta ci gaba da cewa"Dama Babanku ne ya ce in sanar da ke koda yau
she zaki ga bak'o,dan haka ni abin da zan ce miki nasan yaran da mahaifinki ya yi
magana akanshi dan haka in ya zo ki amsheshi hannu biyu,dan abisa alama da na gani
mahaifinki sun yi magana mai k'arfi da mahaifin yaron,kuma nasan yaran yana da
hankaki sosai da natsuwa sannan yana da abun yi"
Fadila shiru ta yi ta rasa abin cewa,sannan dai gudin kar ta yi laifi ta ce"Tom,
Mama"

Fadila na zaune mahaifinta ya aiko kiranta ta je waje ta yi bak'o.


Fadila tashi ta yi ta sa Hijab dinta ta fita.

Zaune ta sameshi kan mashin din shi ,ba yabo ba fallasa Fadila ta gaida shi.

Bayan sun gaisa ne,ya fara jero bayanai kamar haka" Malama Fadila,na dade ina
ganinki kina wuce ni kullum da safe in za ki wajan aiki,tuntuni na so bayyana miki
hak'ik'anin gaskiyar abin da ke raina,amma Allah bai yarda ba sai yanzu, ina fatan
za ki amshi tayin soyayyata hannu bibbiyu?"

Ya idasa maganar ya na mai kallan Fadila.

Jin shuru bata tankamai ba,kamar ma ba zata tanka ba ya ce cikin fargaba "Malama
Fadila,kin yi shiru?"

Nan ma dai shirun ta yi kamar ba zata tanka ba, sai zuwa can ta ce"Ka yi hak'uri
dan Allah ina da wanda nake so zan aura,ina mai baka hak'uri"

Fadila na fad'in haka bata saurari amsarshi ba ta tafi ta bar shi nan tsaye.

Tun daga ranar kullum sai ya zo wajan Fadila fira,inda har ya yi maganarshi ya gama
bata tanka mai,dan fitowar ma sai in mahaifiyarta ta yi mata dole take fita.

Ana cikin haka kuma mahaifin Fadila ya sanar da Kabiru in dai ya shirya to ya aiko
kawai a tsaida ranar auransu.
Kabiru bai yi k'asa agwiwaba ana sanar da shi ya sanar da mahaifinshi,inda
washegari iyayan Kabiru suka zo .Atakaice dai a ranar aka tsaida auran Fadila da
Kabiru.
Fadila ta ga dai mahaifinta ya yi bak'i amma bata san wainar da ake toyawa ba.
Zaune take suna waya da abokin aikinta yana mata magana akan MD fa ya matsa mai
akan maganarta dan Allah ta ba shi dama,shigowar mahaifiyarta ne ya sa ta ce mai
"Ina zuwa "ta kashe wayar.

Mahaifiyar Fadila bayan ta zauna ne ta wurgoma Fadila tambaya kamar haka,ta ce"da
wa kike waya?" Jamilu ne abokin aikina"Shiru mahaifiyar Fadila ta yi,sannan zuwa
can ta ce"Fadila, mahaifinki ya amshi kud'in auranki,dan har sun tsada ranar aure
wata uku"
Fadila cikin alamun mamaki da tsaro ta ce"Mama ,kud'in aurena kuma? Da wa to?" Da
Kabiru mana"Mahaifiyar Fadila ta bata amsa kai tsaye.
Fadila da sauri ta tashi ta zuk'unna kusa da mahaifiyarta ta kamo hannunta ta
ce"Mama,dan Allah ku yi hak'uri ku k'ara min lokaci ,Wallahi ba na son wanda kuke
k'ok'arin had'ani da shi,ki yi ma Baba magana ya ya janye dan ..."Aure babu
fashi,kuma babu mai sawa in janye koda ko kin kawo min wanda kiki so,inda na riga
na fita hak'inki sai da na baki zab'i"Cewar Manaifin Fadila kenan da ya na bakin
k'ofa ya na jin maganar da Fadila ke yi.

Fadila da ta rasa abin cewa fashewa da kuka ta yi.

Haka Mahaifin Fadeela ya ci gaba da shiye-shiryan auran Fadila,inda ta b'angaran


Fadila kuma har yanzu tana nan akan bakarta na ba zata aure Kabiru ba.
Dan yanzu ko wajanta ya zo ko gaisuwa bata had'asu,abin da ya fara ba Kabiru tsoro
kenan,amma da ya sa mu mahaifin Fadila akan zai hak'ura ya ce "Kabiru,ka yi hak'uri
ina sane da abin da Fadila kema,kuma daga zarar kun yi aure in sha Allah zata
bari,hakan duk ta na yi ne dan ka ce ka fasa"Wannan maganganun da Mahaifin Fadila
ya yi sai suka k'ara ma Kabiru kwarin gwiwa sosai.

ADAMAWA STATE
Usman jin alhaji Sagir kamar ba ya cikin hayyacinshi hakan ya sa ya kastse kiran ya
kira Muhammad amma bai d'aga ba,ganin haka ya sa ya tashi ya d'auki mota ya yi
gidan Muhammad d'in in da ya san alhaji Sagir na can in da ance shi da iyalinshi za
su raka Muhammad d'akin amarya.

Yana tafiya a mota ya yi tunanin kiran 'yan sanda ya sanar da su dan gaskiya
yanayin yadda ya ji muryar alhaji Sagir ba lafiya ba .

Usman bai yadda ya shiga gidan ba har saida 'yan sanda da ya Kira suka k'araso
sannan suka shiga tare. Suna shiga gidan shiru ,dan lokacin alhaji Sagir har ya
sume shi ma. Tun kafin su k'arasa cikin d'akin su ka ci karo da d'ige-d'igen
jini ,cikin tsallake jinin suka k'arasa cikin d'akin.Inda suka iske su duk
asume ,sai alhaji Sagir da ya suma kan gawar Hafsat da ke kwance cikin jini an
mata yankar rago.

Haka suka kama alhaji Sagir da Muhammad da hajiya baturiya su ka yi asibiti da su.
Gawar amarya kuma suka d'auki hotunan da za su d'auka sannan itama su ka yi asibiti
da gawar.

Alhaji Sagir da iyalanshi ana kaisu asibiti aka basu taimakon da ya dace,inda cikin
lokaci aka samu kansu duk kansu.
Alhaji Sagir na farkawa ya fara kiran Muhammad, ahakan ya sa dole aka kai shi wajan
Muhammad d'in wanda shi ma farkawarshi kenan.
Alhaji Sagir cikin danne yadda ya ke ji ya karasa wajan Muhammad wanda ke kwance
yana fusge-fusgen shi sai an barshi ya je ya ga Hafsat ,wato amaryar shi kenan.
Ana cikin haka ne aka shigo da alhaji Sagir d'akin. Alhaji Sagir da sauri ya
k'arasa inda Muhammad d'in ya ke. Cikin danne yarda ya ke ji game da abin da ya
samesu ya fara magana kamar haka"Muhammad, ka yi hak'uri mu je gida Hafsat na gida
ka ji"
Muhammad kallan mahaifinshi ya yi ya na girgiza kai ya ce"A'a Daddy ,Sun kashe min
Hafsat? Su waye daddy?"Alhaji Sagir so ya ke ya yi ma Muhammad magana amma ya
kasa ,saboda kukan da ke son kwace mai,hakan ya sa ya fita d'akin da sauri ya koma
motar Usman ya na kuka.

Ya dad'e ya na kuka sannan ya samu ya lallashi kan shi ya yi shiru.Hafsat ta


kasance ita kad'aice ta rage mai wadda zai kalla ya tuna da kanwarsa, ga shi itama
ta tafi ta bar su ko kuma an rabasu da ita lokaci guda.

Alhaji Sagir sai da ya yi kuka mai isarsa sannan ya fita shima sakamakon Kiran da
Usaman abokin Muhammad ya yi mai ne.

Usman cikin sanyi ya kalli alhaji Sagir ya ce"Daddy,dole abin akwai tashin hankali
da tsantsar damuwa amma za mu iya barin haka a matsayin lokacin Hafsat ne ya
yi,saboda wani bai isa ya kashe wani ba sai in kwananshi ne ya k'are. Yanzu kaga
11:49 PM, bari in kira Muhammad mu je gida"
Alhaji Sagir kallan Usman ya yi da jajayan idonshi sannan ya ce"Ina hajiya baturiya
fa?" Ita da Muhammad ga shi nan za a fito da su mu tafi"

Alhaji Sagir da Usman suna nan tsaye aka fito da Muhammad da hajiya baturiya,hajiya
baturiya hannunta rik'e da na likitar da ta dubata,inda Muhammad hannun shi ya ke
rik'e da na d'aya daga cikin police d'in da Usman ya kira da ya ke abokinsu
ne.Shiga su ka yi su ka tafi.
Hajiya baturiya na kuka kad'an-kad'an,in da kukan nata ke kuma d'aga hankakin
Muhammad da alhaji Sagir.
Lura da hakan da Usman ya yi ne ya sa ya ce"Mommy,dan Allah ki yi hak'uri duk mai
rai dama mamaci ne Hafsat lokacinta ne ya yi ,yanzu addu'a ya kamata mu bita da
ita"Haka Usman ya yi ta lallashin hajiya baturi da kyar ya samu ta yi shiru.Shi ko
uban gayyar Muhammad ajiyar zuciya kawai ya ke ja ,kallo daya za ke mai za ka hango
tsantsar tashin hankalin da damuwar da ya ke ciki.Ahaka dai suka isa gidan alhaji
Sagir mai shadda.Suna fitowa daga cikin motar dukansu suka nufi part din alhaji
Sagir.Suna shiga idonsu ya yi tozali da photon Muhammad da Hafsat da ya ke manne
jikin kusurwar d'akin,wannan photon da Muhammad ya gani sosai ya k'ara d'aga mai
hankali hakan ya sa lokaci guda jikin shi ko ina ya fara rawa ,ko kafin Usman ya
taro shi har ya yanke jiki ya fad'i awajan a sume.

Muhammad har gari ya waye bai farfad'o ba,hakan ya sa daddyn shi ya sa aka yi da
shi wata private hospital dake kusa da su.

Gawar Hafsat ko anyi duk wani aune-aune da gwaje-gwaje da za ai an bada gawar dan a
yi mata sutura .
Ko kafin a iso da gawar Hafsat gida gidan ya kuma cika da mutane dama kuma da akwai
sauran mutane da ba su watse ba na biki.Isowa da gawar Hafsat sosai ya d'aga
hankalin mutane,hakan ya sa gaba d'aya gidan ya rud'e da koke-koke.
Hajiya baturiya ko ta na ganin an shigo da gawar Hafsat ta yanke jiki ta fad'i.
Haka dai jama'a akaita koke-koke dan Hafsat kowa na tane bata da damuwa.

Cikin lokaci aka yi zana'idar Hafsar aka kaita gidanta na gaskiya ,in da aka bar
folisawa da bincike.

Muhammad ko sai da ya yi sati biyu a asibiti kafin ya fara dawowa daidai.Yaune aka
dawo da shi gida dan alhamdulillah jikin nashi,saidai rashin k'arfin jiki wanda
hakan ya farune a dalilin rashin cin abinci da kuma rashin kuzari da ke faruwa da
duk Wanda akai mai rashi irin haka.

Muhammad na zaune hajiya baturiya ta tasa shi kamar za ta yi kuka tana lallab'arshi
akan ya daure ya ci abinci,ana cikin haka ne mahaifinshi alhaji Sagir da abokin shi
suka shigo falon.

Alhaji Bala abokin Alhaji Sagir ,zama ya yi gefan Muhammad ya na dafa shi cikin
alamun tausayawa ya ce"Muhammad, ka yi hak'uri ka ji ka saki ranka ka dawo rayuwa
kamar da,Hafsat lokacin ta ne ya yi In ba haka ba babu wanda ya isa ya d'auki
rayuwarta.
Haka alhaji Bala da mahaifin Muhammad suka ta sa Muhammad sai na siha da lallashi
suke mai,amma har suka yi su ka gama Muhammad bai d'auki abinciccikin da aka aje
mai a gaban shi ba ko d'aya.Haka suka gaji suka tashi suka barshi.

Falon Alhaji Sagir suka koma suka zauna,bacin sun zauna ne alhaji Bala ya kalli
alhaji Sagir ya ce"Alhaji, ni fa ina ganin aima Muhammad wani auran cikin satin
nan,kila a samu kwanciyar hankalinsa,dan gaskiya yanda na ga Muhammad abin ya ta da
min hankali"
Shiru alhaji Sagir ya yi sannan zuwa can ya ce "Ni ma na yi tunanin haka? Amma wa
zan aura wa Muhammad shi ne abun tunanin? " Maryam yarinyar wajena ita za a aura
✍🏻
mai

📚 FADEELAH 📚

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare
da fad'akarwa da jama'a bisa harshen Hausa
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻

Na
Fadila Sani Bakori

SANARWA: Masu tambaya akan gyaran jiki akwai hanyoyi kala daban-daban da zan kawo
muku na gyaran jiki a cikin wannan littafi mai suna FADEELAH.

Page 3

Falon alhaji Sagir Suka koma suka zauna ,bacin sun zauna ne alhaji Bala ya kalli
alhaji Sagir ya ce"Alhaji,ni fa ina ganin a yi ma Muhammad wani auran cikin satin
nan ,kila a samu kwanciyar hankalinsa,dan gaskiya yanda na ga Muhammad abin ya
tadamin hankali sosai"
Shiru alhaji Sagir ya yi sannan zuwa can ya ce"Ni ma na yi tunanin haka ,amma wa
zan aura wa Muhammad ?Shi ne abun tunanin"
Maryam,yarinyar wajena ita za a aura mai cikin satin nan kuwa in sha Allah"
Mahaifin Muhammad hanun alhaji Bala ya kamo ya na cewa"Na gode sos...."Dakatar da
shi alhaji Bala ya yi ta hanyar cewa"Haba ai yi ma kaine,babu godiya tsakaninmu dan
na yi ma Muhammad wani abu"
KADUNA GARIN GWAMNA

Bikin Fadila yanzu saura sati shida inda har yanzu ta na kan bakarta na ba za ta
auri Jamilu ba.Mahaifin Fadila ko ya ce babu gudu babu ja da baya aure kamar ma an
yi sa ne.Haka aka ci gaba da shirye-shiryan biki.

Yau kwananan Jamilu goma kenan rabanshi da zuwa wajan Fadila,inda ko ya je shi ke
kid'ansa shi ke rawar shi,Fadila ba ta tankamai.

Fadila na zaune ta yi shiru kamar kullum,k'anwarta ta zo ta sanar da ita Jamilu na


d'akin Babansu wai ta zo. Tun da aka tsaida ranar auransu Mahaifin Fadila ya ce su
rika shiga d'akinshi suna fira.

Fadila tashi ta yi ta sa hijab dinta ta nufi d'akin mahaifinta.


Fadila zama ta yi ba tare da ta tankamai ba.
Jamilu kallanta ya yi ya ce"Barka da zuwa malama Fadila,da fatan kina lafiya? Ina
Kiran wayarki amma baki d'agawa,hankakina ya tashi na ce bari in zo in ji
lafiya,daga nan inga kyakkyawar fuskarki"Ba na kusa ne"Fadila ta ba shi amsa a
tak'aice,sannan ta d'ora da cewa"Jamilu,ina son in fallasamaka abin da ke cikin
zuciyata,saidai babu lallai ba dole ka aminta da abin da zan ce,amma kuma duk abin
da ya biyo baya ban yaudareka ba,kuma ban d'auki alhakinka ba.Magana guda d'aya ta
gaskiya ita ce,Zuciyata ta kasa aminta da taka zuciyar,na yi iya k'ok'arin ganin na
tursasata amma abin ya ci tura,atakaice har rauni na yi mata wajan jajircewa da
bujire mata akan aminta da kai amma ta k'i,ina had'aka da girman Allah ka yi
hak'uri ka hak'ura da zuciyar da ta kasa aminta da kai ka janye maganar da ke
tsakaninmu,saboda ko ka aure ni zai zamana gangar jikina kadai zaka aura"

Jamilu shiru ya yi zufa na keto mai kota ina,daga k'arshe ma ba tare da ya tanka ba
ya tashi ya tafi.
Yau sati d'aya kenan da Fadila ta sanar da Jamilu akan ya janye maganar
auranta,saidai har yanzu ba ta ji wata magana ba mai kama da an janye
,saidai tun daga ranar Jamilu bai kuma kiranta a waya ba,saidai akwai abu d'aya da
ta lura da shi mahaifinta kwana uku kenan baya amsa gaisuwarta,yau ne kuma ta
k'udirci tuntub'ar mahaifiyarta dan jin ko ta yi ma mahaifinta wani laifi ne.

Mahaifiyar Fadila da daddare bayan ta idar da sallar magriba ta na zaune kan


sallaya Fadila ta zo ta zauna gefan mahaifiyar tata,shiru-shiru kamar mai tunanin
ta in da za ta fara,sannan ta ce"Mama,kwana biyu idan na gaida baba baya amsawa dan
Allah ko na yi mai wani laifi ne Wanda ni ban sani ba?"
Mahaifiyar Fadila d'ago kai ta yi tana kallan Fadila,sannan ta girgiza kai ta
ce"Tom,Fadila ni in kin yi mai wani abu ma ban sani ba,dan bai fad'amin ba,saidai
in ya dawo ki je ki tambaye shi ki ji"
Fadila cikin marairaicewa ta kalli mahaifiyarta ta ce"Mama,dan Allah ki mai magana
da kanki kin ga ni ba zan iya yi mai ba"Tom,shi kenan sai ki hak'ura ,dan nima ba
zan iya yi mai ba."

Fadila haka ta hak'ura ta tashi.

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya,in da ya rage har saura sati d'aya d'aurin auran
Fadila kamar yadda mahaifinta ya sa.

Fadila ko yanzu abin da ke damunta bai wuce na gaisuwarta da mahaifinta ya bar


amsamata ba.
Jamilu ko har yanzu tun da ta yi mai maganar nan bai kuma kiranta a waya ba.

Fadila har ya kama saura kwana uku biki bata ga ana wani shirye-shirye shirye na
biki ba,haka ya tabbatar mata da babu bakin kenan,kuma dama ta dad'e tana zargin
hakan.
Yau ne ya kama ranar da za'a daura auran Fadila kamar yadda mahaifinta ya
tsaida,amma kuma shiru ka ke ji.

Fadila sosai ta yi murna da hakan,amma b'angare d'aya na zuciyarta cikin fargabar


mahaifinta ta ke.

Da daddare Fadila na kwance mahaifinta ya aiko kiranta.

Fadila koda ta je ta dad'e a tsuk'unne ba tare da ya tanka mata ba,kamar ba zai


tanka mata ba sai zuwa can ya ce"Fadila, kin maida ni karamin mutum, mutumin banza
mai k'aramar magana,dama mutane na namin kallan wanda baisan abin da ya ke ba na je
kamar ki a gida ba aure,idan an ce rashin mijine yanzu gashi mijin ya zo kin
korai.Yanzu fad'amin me ye nufinki in ji?"
Fadila shiru ba amsa.Mahaifinta ko ya ci gaba da cewa"Fadila,Allah ya sa ni na fita
hak'inki,na baki ilimin na addini da na zamani,na had'aki da mijin aure har uku duk
kin k'i kin nuna min ke wayayyiyace ba aure ba ne a gabanki,dan haka ga
mahaifiyarki nan ta zama shaida"Mahaifin Fadila dakatawa ya yi ya na kallan
mahaifiyar Fadila,sannan ya ci gaba da cewa"Watan uku muke ko?"Kai mahaifiyar
Fadila ta d'aga alamun haka ne. Ya ce "Kafin nan da k'arshan shekarar nan in dai
Fadila ba ta kawo wanda take jin zata iya aura ba,Wallahi Allah d'aya na gama zama
da ita acikin gidan nan,saidai ta san in da zata zauna amma ta gama zamam min a
gida in dai wannan wa'adin ya cika"

Fadila shuru ta yi kanta a k'asa.Mahaifin Fadila kallanta ya yi ya ce"Idan har muka


kai watan sha biyu ba tare da kin kawo daidai da ke din da kike jin za ki aura
ba,karki kuskura in zo in iskeki a gidana ,ba dai gidana ba Wallahi saidai ki naimi
wajan zama"

Mahaifin Fadila sai da ya kuma nanata ma Fadila akan karka kuskura ta k'are
shekarar nan ba tare da wata magana ba,sannan ya ce ta tashi ta bashi waje.

ADAMAWA STATE
Alhaji Bala yana komawa gida ya sanar da matarsa hajiya Halima maganar ba da Maryam
da ya yi ga Muhammad.
Hajiya Halima sosai ta ji dad'in maganar ,dan Alhaji Sagir mai shadda abin alfahari
ne ka had'a iri da shi.

B'angaran Maryam ma ko da mahaifiyarta ta tareta da maganar take ta amince babu ja.

Mahaifin Muhammad ko da ya sanar da hajiya baturiya ta ji dad'in hakan,dan acewarta


k'ila hakan ya kwantar ma Muhammad da hankali.

Da daddare alhaji Sagir ya samu Muhammed da maganar.Amma har ya yi maganar shi ya


gama Muhammad bai tankamai ba.Hajiya baturiya ta ce"Muhammad,ba ka ji abin da
daddynka ya ce bane,sun yanke shawarar had'aka da Maryam yarinyar alhaji Bala
aure,saboda tunanin hakan ko zai sa ka kwantar da hankalinka"

Muhammad da ya rasa abin cewa,kuma baya son gwalishe mahaifinsa hakan ya sa ya


ce"Tom,mommy"

Hajiya baturiya za ta sake magana alhaji Sagir ya d'aga mata hannu alamun ta yi
shiru.

Kwana goma suka tsaida auran,hakan ya sa b'angaran amaryar suka ci gaba da shirye-
shiryan biki,inda b'angaran alhaji Sagir babu wani shiri da su ke yi.Maganar lefe
ma alhaji Sagir kud'i ya ba su ya ce su yi komai.
B'angaran Muhammad ko yama manta da maganar wani aure da za a yi mai.

Ranar da ta kama d'aurin aure ba wani taro a ka yi ba,garama gidan su Maryam d'in
sosai su ke shirin auran.

Ranar Juma'a da safe aka d'aura auran Maryam da Muhammad,in da ba wani taro a ka yi
ba na ku zo ku gani.

Lokacin da labarin d'aurin auran ya isa kunnan Muhammad,sosai abin ya d'aga mai
hankali ,dan sai da a ka Kira alhaji Sagir aka sanar da shi halin da Muhammad d'in
ya ke ciki.

Alhaji Sagir sosai hankalinshi ya tashi ganin yarda Muhammad ya ke kuka.Babu irin
lallashin da alhaji Sagir bai yi mai ba,amma kamar ma ba da shi ya ke ba.

Alhaji Sagir ganin yadda Muhammad ya ke kuka ko ranar da Hafsat ta rasu ma bai yi
kuka haka ba,hakan ya sa cikin tashin hankali da damuwa ya ce"Muhammad, ko auran ne
ba ka so?"
Muhammad cikin kuka ya d'aga ma mahaifinshi kai ya ce"Daddy ,bana son auran nan dan
Allah,mu yi alk'awari da Hafsat ba zan tab'a auran wata in ba ita b..." Muhammad ya
karashe maganar cikin tsantsar kuka da bayyanar tsantsar ta shin hankali a tare da
shi.

Mahaifin Muhammad cikin damuwa ya ce"Muhammad, ka yi hak'uri ,Hafsat ta mutu ta je


in da dukkan mu za mu je,dan haka dan ka auri wata ba laifi bane"

Haka alhaji Sagir da hajiya baturiya su ka yi ta yi ma Muhammad nasiha da lallashi


a haka suka sa mu ya yi shiru .

D'aya daga cikin gidajan alhaji Sagir ya ba Muhammad in da za su zauna,dan acewar


shi ba za'akai Maryam in da akakai Hafsat ba,itama gidanta sabo za a kaita.

Usman abokin Muhammad shi ya jagoranci komai game da d'aukar amarya aka kaita
gidanta.

Usman da sauran abokan Muhammad babu yarda ba su yi ba bayan sun kai amarya sun
dawo akan Muhammad ya shirya a kaishi gidan amaryar amma ya k'i.Daga k'arshe sai da
su ka fad'ama alhaji Sagir.
Alhaji Sagir babu yarda bai yi da Muhammad ba akan ya tashi abokanshi su raka
shi,amma ya k'i.Da suka damai ma kuka ya sa musu,hakan ya sa dole suka rabu da
shi.
Usman da d'aya daga cikin abokan Muhammad d'in suka koma gidan amaryar.Lokacin ko
sun samu kawayan duk sun watse sun barta ita kad'ai.

Ita ko Maryam ta yi sunanin angon ne ma ya shigo,amma sai ji ta yi Usman na


cewa"Amarya,ki yi hak'uri za ki kwana ke kad'ai, Muhammad ba shi da lafiya saidai
zuwa gobe in sha Allah za ki ganshi.Amma idan kina jin tsoro sai in kai ki gidansu
ki kwana "Maryam murmushi ta yi ta ce"Ya jikin na shi?" Alhamdulillah, da
sauk'i"Shi kenan,karka damu kanka zan iya kwana ni ka dai babu wata damuwa"

Alhaji Sagir cikin fargaba ya yi barci,duk da ya sa ma'aikatan tsaro sosai a gidan


gani ya ke kamar itama Maryam din za a iya yi mata abin da a ka yi ma Hafsat.

Cikin dare alhaji Sagir ya farka a furgice sakamakon mummunan mafarkin da ya yi.
Hajiya baturiya jin tarin alhaji Sagir ne ta farka tana tambayar shi "Alhaji,lafiya
kuwa? yanayinka kamar a furgice kake?"Alhaji Sagir jan numfashi ya yi,sannan ya ce
kamar zai yi kuka"An kashe Maryam kamar yadda a ka yi ma Hafsa.."Hajiya baturiya
katse shi ta yi da cewa"Haba,alhaji mafarki fa ba gaskiya ba ne,na san mafarki ka
yi,ka kwanta da tunanin haka ne a ranka shi ne hakan ya zo maka a mafarki, amma in
sha Allahhhu babu abin da zai samu Maryam."

Shiru alhaji Sagir ya yi gaba d'aya ya k'osa gari ya waye dan ya je ya dubo 'yar
mutane.

Alhaji Sagir na nan zaune har a ka kira sallar asuba.Ana Kira ko ya tashi ya
d'auki key d'in motar shi zai fita.
Hajiya Baturiya cikin damuwa ta ce"Alhaji,in sha Allah babu abin da ya samu
Maryam,ka daure mu yi sallah sai in raka ka mu je"
Da kyar hajiya baturiya ta shawo kan alhaji Sagir ya yarda su ka yi Sallah.Suna yin
Sallah suka fita gidan zuwa D'an maliki road in da aka kai Maryam.

Suna zuwa ma su gadin suka bud'e alhaji Sagir ya shige cike da tarin fargabar abin
da idonshi zai gani.

Sun dad'e suna bubbugawa,amma shiru.Hakan sosai ya d'aga hankalin alhaji Sagir da
hajiya baturiya. Hajiya baturiya cikin fashewa da kuka ta ce"Mun shiga uku,alhaji
kar mafarkinka ya zama gaskiya!"

Alhaji Sagir ya na son ya Kira mahaifin Maryam ya ce ya ba shi numberta ya Kira ya


ji,amma kuma yana ganin kamar zai d'aga mai hankali.

Alhaji Sagir ci gaba da bugun k'ofar ya yi,inda kamar daga sama sai ji ya yi an
ce"Waye?"Alhaji Sagir cikin jin sanyi aranshin jin muryar Maryam d'in ya ce"My
daughter daddynki ne bud'e ko"

Maryam bud'ewa ta yi tana mamakin dalilin zuwan alhaji Sagir da asuba haka.
Alhaji Sagir da hajiya baturiya haka su ka bi Maryam da kalo.

Maryam wadda cikin barci ta ji yo bugun kofar falon,cikin sanyi ta ce"Daddy Allah
ya sa dai lafiya na ganku da asuba ko jin Muhammad d'in ne?" Dan ita ta d'auka ko
Muhammad ne ma ba lafiya.

Alhaji Sagir cikin sauke bayyanannar ajiyar zuciya ya ce"Maryam, Wallahi wani mugun
mafarki na yi hankalina ya k'i kwanciya shi ne dalilin zuwanmu muga lafiyarki"

Murmushin jin dadi Maryam ta yi ganin yarda surukan nata suka nuna kulawa sosai
akanta, ta ce"Ayyah,babu komai Daddy,in sha Allah babu abin da zai faru da
ni,wancan ma wani rubutaccan al'amari ne"

Alhaji Sagir kai ya jinjina ya ce"Haka ne Maryam.Shi kenan bari mu tafi"

Hajiya baturi cikin marairaicewa ta ce"Ni dai alhaji duk da Maryam ba ita kad'ai
bace a gidan hankalina ya fi karka ta akan mu tafi da ita,Allah bashi sai su dawo
da Muhammad tare"

Alhaji Sagir cikin gamsuwa ya ce"Haka ne,Maryam d'akko mayafinki mu tafi ,kun dawo
anjima da Muhammad tare"
Haka alhaji Sagir suka tasa Maryam su ka tafi da ita.

KADUNA GARIN GWAMNA

A yau jama'ar gasuwar magani ta Kaduna suka tashi cikin tashin hankali saboda rusan
kasuwa da a ka yi musu,wanda abin ya had'a harda shagon mahaifin Fadila da ke saida
kayan gwari.

Sosai rayuwa ta fara sauya wa su Fadila,inda dama kullum sai an fita kasuwa an nemo
suke samun abin da su yi cefane.

Yanzu rayuwa ta fara tsananta wa su Fadila,Yanzu haka yau sun tashi babu abin da za
su ci,ga shi kasuwar da aka dogara da ita wadda kullum sai an fita ake samo kudin
cefanan abin da za su ci, gashi an rushe kasuwar.

Mahaifin Fadila kwance yana tunanin abin da za su ci,kallan mahaifiyar Fadila ya yi


ya ce"Maman Fadila,na ce ko shinkafan nan za a auna a saida a samu kud'in cefanan
abin da za mu ci?"
Shiru mahaifiyar Fadila ta yi,sannan ta ce "To,shinkafar ita kasan ta kare saura
mudu uku ta rage mana,idan an saida mudu d'aya kaga saura mudu biyu kenan?" Tom,Ya
za a yi haka nan za a saida in da za a zauna da yunwa ne?"
Mahaifiyar Fadila ba dan ta so ba haka nan taba yaro ya je ya saida mata mudu daya
daga cikin shinkafar da ta yi ragowa,bayan yaron ya dawo ne su ka yi cefanan kayan
mahad'in girkin shinkafar.

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya,inda ya kasance komai nasu Fadila ya kare,duk wata
dabara ta kare.

Yanzu haka tun safe har dare ba su ci komai ba.Mahaifiyar Fadila cikin taushin
murya ta fara yi ma mahaifin Fadila magana kamar haka"Baban Fadila,dama cewa na yi
inda dai ka ga in rushe maka hanyar da muka dogara da ita,wadda muke ci da sha a
cikinta,me zai hana ka yi hak'uri Fadila ta koma aikinta kodan mu samu abin da za
mu rik'a ci"

Shiru mahaifin Fadila ya yi kamar ba zai tanka ba sannan ya ce"Shi kenan zan yi
✍🏻
tunani akan hakan

📚 FADEELAH 📚
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare
da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻

Na
Fadila Sani Bakori
SANARWA: Masu tambaya akan gyaran jiki akwai hanyoyi kala daban-daban da zan kawo
muku na gyaran jiki a cikin wannan littafi mai suna FADEELAH .

Page 4

Yau sati d'aya kenan da maganar komawar aiki da mahaifiyar Fadila ta yi ma mahaifin
Fadila , ya ce zai yi shawara amma har yanzu shiru kuma har yanzu da kyar suke
samin abin da suke ci.

Mahaifiyar Fadila bayan ta idar da sallah, fadila ta zo ta same ta ta ce"Mama, dama


nace ko za ki ma Baba magana in koma aiki Kafin Allah ya kawo mai wata hanyar "

Mahaifiyar Fadila d'ago kai ta yi tana kallan Fadila ta ce"Nima tunanina kenan har
magana na yi mai amma ya ce min in saurare shi zai yi tunani, yau sati d'aya kenan
amma kin ji shiru sai ka ce baya ganin halin da muke ciki, amma ki bari anjima zan
kuma yi mai magana "

Da daddare mahaifin Fadila na zaune yana lazimi ,har lokacin tun kokan da suka sha
na safe ne ke cikinsu , Mahaifiyar Fadila ta zo ta zauna gefan abun sallar tashi ,
sannan zuwa can ganin lazimin nashi ba na kare bane ta ce "Baban Fadila, dan Allah
ka bar Fadila ta koma aikinta mana ko dan mu samu abin da za mu rik'a ci, idan kace
zaka biye ma maganar mutane Allah mutum ba zai yi abun kirki ba , shi ya sa ka yi
abun da ke gabanka kawai , yanzu su mutanan da ke kawo ma maganganin k'arya
akanta halinnan da muke ciki cikinsu waya taimaka maka? kuma babu wanda bai san an
rushe kasuwarku ba.Wallahi ka toshe kunanka daga maganganun mutane ka barta ta
koma ta ci gaba da aikinta mu kuma mu dage mu rakata da addu'a "
Mahaifin Fadila d'ago kai ya yi yana kallan mahaifiyar Fadila kamar ba zai tanka ba
sai zuwa can ya ce"Shi kenan ta koma aikin"
Daga jin yarda ya yi maganar kasan dole ce ta sashi furta hakan.

Mahaifiyar Fadia zuwa ta yi ta sanar da Fadila mahaifinta ya amince ta koma bakin


aikinta.

Allah sarki Fadila take ta Kira Jamilu abokin aikinta ta sanar da shi gobe zata
dawo aiki ,ta k'ara da cewa"Amma Jamilu kana ganin wannan Karan MD zai yarda kuwa?
Dan ya kikkira wayata ban d'auka ba, kuma kaga ban tab'a dad'ewa irin na wannan
Karan ba ? "

Jamilu dariya ya yi ya ce"Fadila , kema dai kina tonona ne , amma kinsan ko shekara
za ki yi biki zo aiki ba kema dai kinsan MD hannu bibbiyu zai amshek ba tare da
wani k'orafi ba "

Haka dai su ka yi sallama bacin Fadila ta sanar da shi dawowarta aiki gobe .

Washegari da wuri Fadila ta yi shirin tafiya aiki , bayan ta gama shiryawa ne ta


shiga d'akin mahaifinta, bayan sun gaisa ne ta ce"Baba, na shirya zan tafi" Za ki
tafi ina ? " Cewar mahaifin Fadila .
Fadila cikin sanyi ta ce "Zan koma wajan aiki , jiya mama ta ke sanar da ni ka
amince in koma"
Mahaifin Fadila shiru ya yi yana kallanta kamar ba zai bata amsa ba dan har ta cire
rai ma sannan ya Kira sunanta ya ce"Fadila "
Fadila cikin sanyi ta amsa da "Na'am ,Baba"
Ya ci gaba da cewa"Fadila , dan Allah ki ci gaba da tafiya kamar yadda na sanki ,
kwanakin baya surutun mutane da kuma tsoron bakin mutane akanki ya sa na dakatar da
ke aiki ba wai dan na yarda da abin da su ke cewa ba" Shiru mahaifin Fadila ya yi
sannan ya ci gaba da cewa"Fadila , ki sani duk abin da za ki yi Allah na kallanki ,
tashi ki tafi Allah ya tsare "
Fadila cikin sanyi ta tashi tana mai amsawa da "Ameen ,Baba"

Misalin k'arfe takwas (8:00AM) Fadila ta shiga Rahama TV tana zuwa office din MD ta
shiga.

Kamar a mafarki haka ya ga Fadila.Seat d'in da ke facing d'in shi ya nuna mata
alamun ta zauna.

Bayan Fadila ta zauna ne ya ce"Fadila , me na yi miki kike son fasa zuciyata? Tun
da kika bar zuwa aiki ban tab'a kiranki kika d'aga ba? "

Fadila ji ta yi kunya ta gamata, saboda kodan alfarmar da ya ke yi mata be cancanci


ta yi mai haka ba , saidai ba daga ita bane daga zuciyarta ne ,zuciyarta ta ka sa
aminta da shi bare kuma har ta yi waya da shi.
Fadila cikin alamun ban hak'uri ta had'a hannuwanta ta ce"Afuwa rankashi dad'e ,
kana kirana duk bana kusa da Wayar ne , kuma babu kati a wayar bare in biyoka "

Shiru ya yi sannan ya ce" Shi kenan Fadila za ki iya zuwa ki ci gaba da aikinki ,
saboda ganinki na sa zuciyata cikin damuwa "

Fadila ta shi ta yi ta ce"Shi kenan bari in tafi ba zan so in zama silar damuwarka
ba,in da ganina damuwa ya ke saka"
Da sauri ya tashi ya sha gabanta ya ce"Tsaya mana, ba haka nake nufi ba, ke d'in ce
kin kasance wani abu mai girma gaske a zuciyata ,da zaki yarda da sai in ce miki
ban tab'a so wani abu kamar ki ba, dan Allah ki ban dama mana Fadila?"

Fadila tafe kai ta yi, dan dama tunaninta kenan na dawowa aiki daga ta dawo MD zai
fara ta kura mata da maganganun shi da baya gajiya.
Fadila cikin k'osawa tabar Office d'in shi ta ce"Shi kenan, zan yi tunani"
Kai MD ya girgiza ya ce " A'a , Kullum haka kike ce min , ki ban amsa ta kawai ko
zuciyata zata samu sukuni dan Allah "

Fadila tana tsoran ta furta mai kalmar k'i ta zo ta samu matsala a wajan aiki ga
shi a halin yanzu tana buk'ar aikin sosai, hakan ya sa cikin sanyi ta ce"Shi kenan,
zan ba Jamilu sak'o ya baka "

Tana fad'in haka ta fita office d'in da sauri kafin ya k'ara wata magana.

ADAMAWA STATE

Alhaji Sagir bayan sun dawo da Maryam Kiran mahaifinta ya yi ya sanar da shi masu
zuwa ganin gidan amarya sai dai su bari in ta koma zuwa an jima yanzu tana gidan
shi .

Mahaifin Muhammad yana gama wayar mai da kallan shi ga Muhammad ya yi ya ce "
Muhammad, saboda masu zuwa ganin gidan amarya ka shirya yanzu ku tafi, kudin kar a
zo bata nan "

Muhammad shiru ya yi baice komai ba .


Alhaji Sagir ya kuma cewa " Muhammad ba ka ji abin da na ce ba ne, ka tashi ka
shirya kafin a fara zuwa ba kowa gidan "

Muhammad ba dan ya so ba sai danne zuciyarshi da ya yi gudin kar ya watsa ma


mahaifinsa k'asa a ido ganin duk yana yin hakan ne dan farincikinsa , hakan ya sa
cikin sanyi ya ce"Tom, Daddy "
Alhaji Sagir wayar shi ya ciro ya kira Usman abokin Muhammad ya sanar da shi ya zo
yanzu.

Alhaji Sagir kallan Muhammad ya yi ya ce"Idan akwai abin da za ka yi na kira Usman


ya zo ya kaiku ka yi kafin ya k'araso "

Muhammad kamar zai yi kuka ya ce"Babu abin da zan yi Daddy"

Sunanan zaune Usman ya yi sallama ya shigo.Bayan sun gaggaisa ne alhaji Sagir ya


ce" Muhammad ka tashi ku tafi"

Muhammad d'ago kai ya yi yana mai zubar da hawaye ya ce"Daddy , da bakinka kake
cewa in tashi in tafi in zauna da wata ba Hafsat ba , Daddy me ya sa ka yi saurin
mantawa Hafsat ? Da ace Hafsat zata dawo duniya za ta yi mamakin hakan Daddy"
Kuka ne ya kwace ma Muhammad ,cikin kukan ya ci gaba da cewa "Daddy, ka yi hak'uri
ba zan iya zama da kowa ba in ba Hafsat ba, ita kadai idaniyata ke gani,ita kad'ai
zuciyata ta yarda ta so,haka ruhina da gangar jikina da ita kad'ai ta aminta za ta
yi rayuwa.Haba Daddy me ya sa kuka dage sai kun tursasa ruhina zama da wata ba
Hafsat ba? Bacin na yi mata alk'awarin ruhina ba zai taba rayuwa da ruhin wata ba
in ba ita ba.Daddy dan Allah ka bar ni in yi rayuwa da Hafsat ita kad'ai"

Daga Hajiya Baturiya har Usman kallan Muhammad kawai suke, Alhaji Sagir ko ya ma
rasa abin da zai ce masa.Inda Maryam ta fita d'akin da sauri tana kuka jin zantikan
da Muhammad d'in ya ke yi.

Alhaji Sagir dafa Muhammad ya yi cikin damuwa ya ce " Muhammad , ka yi hak'uri


Hafsat ta tafi, ta tafi har'abada ba za mu sake ganinta ba sai a mafarki, ka yi
hak'uri ka amshi Maryam wadda mahaifinta ya baka ita dan samun kwanciyar hankalinka
kaga baikamata mu zuba masa k'asa a ido ba, da Maryam da Hafsat duk kusan d'aya ne
awajanja, yadda Hafsat take k'anwarka Maryam ma k'anwarka ce ahankali watarana za
ka sota itama "

Haka dai suka taru suka yi ta ba Muhammad ba ki a haka suka samu ya tashi.Saidai
ana dubawa kuma ba Maryam.

Alhaji Sagir kallan Hajiya Baturiya ya yi ya ce " Ina Maryam d'in fa? "
Hajiya Baturiya cikin mamaki ta ce"Muna nan tare da ita fa bari in dubata muga "

Hajiya Baturiya a falonta ta iske Maryam ta kifa kai a kan caution sai kuka take.

Hajiya Baturiya da sauri ta k'arasa wajan Maryam tana d'agota tana cewa "Haba
Maryam ki yi hak'uri kin ji ki yi ma Muhammad uziri , har yanzu yana cikin damuwar
rad'ad'in mutuwar Hafsat, kuma yadda abin ya yi kusa babu nisa tsakani dole sai kin
yi hak'uri har ya fara mantawa, kin ji 'yata ? "

Maryam d'aga kai ta yi.


Hajiya Baturiya ta ce"Yauwa, ko ke fa , share hawayanki "

Hajiya Baturiya tana rik'e da hannun Maryam suka k'arasa har in da Usaman ya yi
parking suna jiran Maryam.

Suna zuwa Maryam ta shiga suka yi musu sallama su ka tafi.

Suna zuwa k'ofar gidan masu gadin suka bud'e musu suka shiga tank'ameman falon
amaryar wanda ya ji kayan alatu da abubuwan more rayuwa.

Maryam ko har yanzu ta kasa na tsuwa ta saki jikinta, dan ta gama furgita da jin
kalaman angon nata akan marigayiyar amaryarshi .
Usman lura da hakan da ya yi ne, ya kalli Muhammad da ke kwance kan three seater
kanshi a sama kamar wani sabon maraya ya ce"Muhammad, da farko dai ina son in ce
maka ka ji tsoran Allah ka rik'e Maryam amana, Hafsat kuma a halin yanzu tana
buk'atar addu'arka ne ta haka ne zaka nuna mata soyayyar da kake mata, amma kukan
da kake yi mata azaba ne a gareta,Manza Alllah (S.A.W) Ya ce ana ma mamaci a zaba
da kukan wanda yake da rai"
Shiru Usman ya yi sannan ya maida kallanshi gun Maryam ya ce" Maryam, na dawo
gareki, da farko dai abun da nake son in ce miki , sai kin daure kinsa hak'uri da
juriya kafin ki samu komai ya wuce, ki daure kar ki sa gajiyawa dan Allah. Ina mai
yi miki albishir d'in za ki ji dad'in zama da abokina , Muhammad ba shi da wata
matsala ga shi da tausayi da son fita hak'in duk wanda wata hurd'a ta had'a shi da
shi, hakan ne ya sa nake mai kyakkyawan zaton adalci agareki , sboda shi d'in
adaline mai tausan na k'asa da shi "

Usman sosai ya yi musu nasiha da jan hankali akan zaman aure sannan ya tafi.

KADUNA GARIN GWAMNA

Fadila cikin sanyi ta k'arasa office d'insu, kasan cewar Jamilu ya sanar da dawowar
Fadila aiki babu wani mamaki da abokan aikinta su ka yi.

Bayan sun gaggaisa ne, Jamilu ya fara nuna ma Fadila shirin da za su tattauna yau
akan shi.

Fadila na zama babu dad'ewa ,Jamilu ya kalleta ya ce"Lokaci fa ya yi mu je "

Kamar yadda kuka sani kuke kallo haka Fadila ta fara gabatar da Shirin da take
aiki akai.

Zaune take ad'akin gabatar da Shirin nasu ga masu aikin d'aukar shirin, komai dai
an shirya kamar dai yadda kuke kallo a TV.
Fadila ta fara magana kamar haka"Assalamu alaikum barkamu da sake saduwa da ku
acikin shirinmu mai suna DARAJAR 'YA MACE, wanda ni Fadila Sani nake gabatar muku
tare da Jamilu Hassan.DARAJAR 'Ya mace,in ji Hausawa suka ce aure "

Yau za mu yi bayanine akan ta yarda ake gane fiffofin mace mai daraja.

Fadila mai da kallanta ga Jamilu ta yi ta ci gaba da magana kamar haka, "Malam


Jamilu, shin taya ake gane siffofin mace mai daraja? "

Jamilu mai da kallan shi ya yi ga camera ya fara bayani kamar haka "Da akwai alamu
da dama da ake gane wannan ita ce mace mai daraja, ana gane mace me daraja ne ta
hanyoyi da daban-daban, amma zan kawo kad'an daga ci:
Ana gane mace mai jaraja ta yanayin maganarta, ko ta d'abi'unta, yanayin maganarta
da mutane da kuma mu'amalarta da mutane, da kuma yanayin suturar da take sawa , da
kuma yanayin abokan hurd'arta "

Jamilu kallan Fadila ya yi ya ce " Wannan suna daga cikin siffofin mace mai daraja
"

Fadila cikin gamsuwa ta ce" Wasu hanyoyi zan bi dan in kasance d'aya daga cikin
mata masu daraja ? "

"Duka-duka dai anan muka kawo k'arshen shirinmu mai suna DARAJAR 'YA MACE.
Ku kasance da mu acikin mako na gaba dan jin yadda za ki kasan ce mace mai daraja"

Bayan su Fadila sun gama gabatar da Shirin DARAJAR 'YA MACE ne, ta kalli Jamilu ta
ce"Jamilu, MD fa ya matsamin, d'azu hanani fitowa office din shi ya yi wai sai na
fad'a mai matsayin shi a guna, da narasa yadda zan ce mai shi me nace zan baka
sak'o ka ba shi, yanzu mi kake ganin zan ce mai? Allah ya sani bana son shi "
Jamilu shiru ya yi sannan ya ce"Ni kuma da zan baki shawara sai in ce ki hak'ura da
shi , kin ga kin fada min yarda kuka yi da iyayanki, ki amshi tayin soyayyar MD
kodan ki rik'a aikin ki cikin dad'in rai, K'in amsa tayin nashi ina tsoran kar ya
jawo mik wata matsala anan, dan haka zance masa kin amince "

Shiru Fadila ta yi tana kallan Jamilu sannan ta ce "Amma kasan Ina sonsa ba wai
yana nufin zan aureshi ba ne ?" Eh, na sani , kuma shi ma ya san hakan" Cewar
Jamilu.

Haka dai Jamilu ya yi taba Fadila shawara akan Ogan nasu.

ADAMAWA STATE

Bayan Usman ya tafi Falon ya yi shiru sai kukan Maryam da ke tashi kad'an-kad'an.
Muhammad tashi ya yi ya barta a wajan ba tare da ko in da take ya kalla ba.Hakan
sai ya kuma in giza Maryam ta ci gaba da kuka, haka dai ta ci kukanta ta gaji babu
mai lallashi, karshe da ta gaji ta yi shiru.

Yau satin Maryam d'aya kenan a gidan ,amma kusan har yanzu ban da gaisuwa babu wata
kwakkwarar maganar da ke shiga tsakaninta da Muhammad.Saidai yanzu ya fara sakin
ranshi ba kamar daba,in da yana fita sosai kuma takan ji suna fira da Usman in ya
Kira shi a waya, haka Alhaji Sagir ma da Hajiya Baturiya duk ya fara sakin rashin
su yi fira in sun zo.

Maryam a yarda ta lura kusan da ita kad'aice baya sakin jikinshi da ita .
Tun da Maryam ta zo gidan daga gidan Alhaji Sagir mahaifin Muhammad ake kawo musu
abinci kullum, amma yau ta k'udiri a niyar da kanta zata shiga kitchen ta yi musu
girki.

Koda ta shiga kitchen d'in kusan a kwai komai na buk'ata ,so take ta yi abin da
zata burge Muhammad wanda zai ci kuma ya ji dad'in shi, saidai bata san wana kalar
abinci ya fi so ba.

Wayarta ta d'akko ta kira Hajiya Baturiya, bayan sun gaisa ne ta ce"Mommy, ina son
in shiga kitchen ne yau in mana girki, tom ina son in yi wanda Muhammad zai ji
dad'in shi ne sosai shi ne na kira in fambayeki best food d'in shi"Hajiya Baturiya
dariya ta yi sannan ta ce"Taliya da miyan kwai shi ne girkin da Muhammad ya fi so"

Atak'aice Maryam ta shiga kitchen ta dafa mai taliyan ta soya mai miyan k'wan.

K'arfe shida Muhammad ya dawo, saidai yana dawowa ya yi alwallah ya fita.

Bashi ya dawo ba sai da ya yi sallar issha'i acan,dan Muhammad akwai ibada.

Maryam zaune take a falon tana jiran shigowar Muhammad.Sanye take da abaya jikin
abayar baki d'aya ya sha ado da stones.

Maryam na nan Zaune Muhammad ya shigo, hanyar steps d'in bedroom d'in shi ya yi
Maryam ta yi saurin cewa"Ga abinci na girka maka" Bana buk'ata na koshi" Muhammad
ya ce atak'aice ya yi tafiyar shi ya bar Maryam nan tsaye.
Maryam d'akko kulan abincin ta yi ta bi Muhammad da shi.

Yana zaune ta yi sallama shiru ya yi mata baice ta shiga ba, da ta gaji da tsayuwa
shiga ta yi.

Muhammad da ido ya bita da kallo,alamin lafiya.

Maryam aje kulan abincin ta yi, ta fita ta d'akko plate d'in da zata samai aciki.

Bayan ta dawo ta bud'e kulan ta zuba mai taliyan da miyan kwan,sannan ta kallai
ta ce"Na zab'i in yi abin da ka fi so ne dan ka ci , dan Allah karka ce ka k'oshi
ko d'iba daya ka yi ka ci zan ji dadin hakan, sannan in samu ladar ciyar da mai
gida" Maryam ta idasa maganar a hankali tana murmushi.

Muhammad kallanta ya yi ya ce"Waya ce miki ina son taliya?" Mommy na tambaya"

Kasan cewar Muhammad nasan taliya sosai kuma dama kusan bai ci kimai ba, hakan ya
sa ya fara cin taliyar.

Yana tsak'ar cin ne Kira ya shigo wayar shi, yana ganin mahaifin shi ne ya tuna da
kiran da yake mai, kafin ya d'aga Kiran ya katse.Muhammad kallan Maryam ya yi ya ce
"Zani gida zan dawo yanzu "

Muhammad na fad'in haka ya aje abincin ya tafi.

Allah sarki Maryam sai ta ji dad'in sanar da ita din da Muhammad ya yi,dama in bata
manta ba abokinshi ya ce mata yana da sauk'in kai ba shi da damuwa tabi a hankali
zata samu kanshi.
Muhammad koda yaje mahaifinshi ya yi mai magana ne akan tafiyar da zaiyi Lagos gobe
zai yi kwana biyu ya dawo.Haka dai suka d'an zanzanta sannan ya tafi, tare da mai
alk'awarin zai zo ya kai shi airport.

Misalin k'arfe Tara Muhammad ya shigo, yana shiga direct bedroom d'in shi ya yi.

Muhammad cikin tsananin furgici da tashin hankali ya ke kallan Maryam da ke kwance


✍🏻
male-male cikin jini

📚 FADEELAH 📚
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare
da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻

Daga
Fadila Sani BaBakori

*🤝 SDEEND MTN DATA SERVICES🤝*


*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦250
2GB = ₦700. 1GB ₦500
3GB = ₦1050. 2GB ₦1000
4GB = ₦1400. 3GB ₦1500
5GB = ₦1750. 4GB ₦2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

SANARWA : Masu tambaya akan gyaran jiki akwai hanyoyi kala daban-daban da zan kawo
muku na gyaran jiki acikin wannan littafi mai suna FADEELAH .

Page 5

Muhammad cikin tsananin furgici da tashin hankali ya ke kallan Maryam wadda ke


kwance cikin jini an mata yankar rago.

Tsananin tashin hankali da furgici ya sa Muhammad ko kukan ma ya kasa yi.Zuwa ya yi


yana ta girgiza gawar Maryam da ke kwance cikin jini.

Zuwa can kuma ya fad'i gefanta a sume.


Washegari alhaji Sagir ya yi ta sauraran zuwan Muhammad ya kai shi airport kamar
yadda su ka yi zai zo ya kai shi amma shiru .Hakan ya sa ya kira Muhammad d'in a
waya.

Alhaji Sagir sai da ya yi ma Muhammad kira hud'u amma bai d'auka ba, take hankalin
Alhaji Sagir ya tashi.Kallan Hajiya Baturiya ya yi ya ce" Anya ko Muhammad lafiya
na kira shi bai d'auka ba?" Tom, ka kira matarshi Mana" Cewar Hajiya Baturiya .
Alhaji Sagir Maryam ya Kira, itama dai ta b'angaranta haka ya yi ta Kira ba ta
d'auka ba.Take jikin alhaji Sagir ya fara rawa ya ce "Ina ji ajikina babu lafiya na
kira Muhammad bai d'aga ba haka Maryam ma "

Alhaji Sagir ya na maganar ya na tafiya da sunan za shi gidan Muhammad d'in.Hajiya


Baturiya da sauri ta taro shi tana cewa "Alhaji, ka kwantar da hankakinka babu abin
da zai samu Muhammad in sha Allah, bari in zo in yi driving d'inmu yadda ka rud'e
haka ai ba zaka iya tuk'i ba"

Hajiya Baturiya ita ta tuk'asu duk da itama hankakin nata a tashe yake dan ta kusa
yaddasu .

Suna tafiya a mota Alhaji Sagir ya na kuma Kiran numbobinsu amma shiru.

Suna zuwa Alhaji Sagir ya tambayi masu gadin cewar jiya ko sun ga dawowar
Muhammad.Suka amsa mai da "Eh"

Ya ci gaba da cewa "Lafiya dai ko babu wani abu da ya faru?" Nan ma suka amsa mai
da"Eh,ranka shi dade babu abin da ya faru wani ne ya ce maka wani abu ya faru ne ?"
Alhaji Sagir bai amsa musu ba ya nufi in da zai sadashi da k'ofar falon Muhammad
d'in.

Saidai babu kalar bugun da ba su yi ba amma shiru.

Hajiya Baturiya na ganin haka tasa kuka cikin kuka take cewa "Na shiga uku sun
kashe mana Muhammad" kukan Hajiya Baturiya ne ya sa d'aya daga cikin masu gadin ya
k'araso yana tambayar " lafiya? "

Alhaji Sagir goge zufar da ke feso mai ya yi ya na nuna mai k'ofar falon alamun ya
bud'e mai ita.

Babu kalar jijjigawar da bai yi ma kofar ba amma tak'i bud'uwa, saida ya Kira wani
daga cikin su suka taru suka bud'e k'ofar da kyar.

Alhaji Sagir da Hajiya Baturiya atare suka shiga cikin hanzari.

Koda suka shiga bedroom d'in Muhammad lokaci d'aya tsoro,ranaza,tashin hankali ya
mamaye zukatansu...

Hajiya Baturiya da gudu ta yi kan Muhammad da ke kwance babu alamun rai a jikin shi
tana jijjigashi .

Alhaji Sagir gun Muhammad ya yi da niyyar amsarshi daga hannun Hajiya Baturiya jiri
ya dibai ya yanke jiki ya fad'i, dan a tunanin shi Muhammad d'in ya mutu ne.
Mutum biyu daga cikin masu gadin gidan jin alamun kuka suka biyo bayan su Hajiya
Baturiya suka shigo .Sosai suka rud'e ganin gawar Maryam kwance ak'asa an mata
yankar rago.

D'aya daga cikin su ne ya yi ta maza ya kira office d'in su ya sanar da su.

Cikin lokaci motar folisawa ta iso gidan.

Atak'aice dai nan 'yan sanda su ka yi bincike- binciken su sannan suka d'auki gawar
su ka yi asibiti da ita.

Duk wani bincike an gudanar akan gawar Maryam sannan aka yo gida da ita.

Haka aka yi zana'idar Maryama aka kaita gidanta na gaskiya. Har aka yi aka gama
daga Alhaji Sagir har Muhammad basu san abin da ake ba saboda allurar barcin da
likita ya yi musu.

Iyayan Maryam lokacin da idonsu ya yi tozali da gawar Maryam sun yi kuka sosai da
danasanin had'a auran Maryam da Muhammad da su ka yi.

Muhammad ba shi ya farkaba sai gaf magriba, inda Alhaji Sagir har lokacin baisan
wanda ke kanshi ba sai can cikin dare ya farka.

A wannan lokacin abin ya fi tab'a Alhaji Sagir dan har ya farka baya magana, saidai
ya kalli mutane.
Muhammad na kwance kan shi a sama, yana tunanin me ke faruwa da rayuwar shi haka
ne. Yana a wannan yanayin ne Hajiya Baturiya ta shigo. Kallan Muhammad ta yi tana
shafa kan shi ta ce "Muhammad, kar ka sa kanka cikin tunani wani mugun ciwan ya zo
ya kamaka, sannan ni kaina idan ina ganinka haka hankalina ba zai kwanta ba"

Muhammad tashi ya yi ya zauna yana kallan


Hajiya Baturiya ya ce "Mommyna, soda dama ba zafin ciwo ake ma kuka ba, tunanin
halin da ake ciki ne .Sannan, mommy duk jarumtar Jarumu ba kowana rad'adi yake iya
juremawa ba" Hajiya Baturiya kai ta d'aga ma Muhammad alamun haka ne, ya ci gaba da
cewa "Mommyna, na rasa yadda zan lallashi kaina in yi hak'uri da rashin Hafsat a
rayuwata. Amma da na yi wani nazari sai naga ko ba wannan lokacin ba Hafsat zata
mutu watarana,sai na yi tunanin fara ba kaina hak'uri in amshi Maryam a matsayin
mata, saidai ina cikin tunanin hakan ne zuciyata na gaf da amince min da ita suka
kasheta suka rabani da ita itama" Muhammad shiru ya yi kamar mai tunani ko mai son
tuna wani abu, sannan ya ce"Mommy! Su waye ne? Waye ya kashe su? Me su kai musu ?
Shi nake son san..." Hajiya Baturiya rufe bakin Muhammad ta yi tana kuka, ta ce "Ka
yi shiru Muhammad, karka sa kanka cikin wata damuwar, koda ace abin da mahaifinka
ya mallaka zai kare ne sai an binciko wa inda suka aika haka, ni na san haka. Ka
tashi mu je ka ga mahaifinka abun nashi ya fara bani tsoro, baya magana tun da ya
farka na yi na yi ya k'i yin magana"

Muhammad cikin daure yadda yake ji da tsoran karya rasa mahaifin shi ya nufi bayan
Hajiya Baturiya suka yi falon Daddynshi.

Kwance ya samu mahaifin nasa kansa a sama kamar mai k'okarin tuno wani abun da ya
shege mai .

Muhammad cikin k'arfin hali ya kalli mahaifinshi ya ce"Daddy, ka tashi ka ci abinci


plz"Alhaji Sagir da sauri ya mai da kallan shi kan Muhammad .
Ya dad'e yana kallan Muhammad d'in sannan ya ce "Muhammad, ka ci abinci kai ?" Kai
Muhammad ya d'aga mai.

Muhammed Hajiya Baturiya ya sa ta kawo mai tea ya ba Alhaji Sagir. Kad'an dai su ka
samu ya sha.

BAYAN SATI D'AYA DA RASUWAR MARYAM .

Ma sha Allah. Yanzu Alhaji Sagir da Muhammad sun fara kwantar da hankalinsu.

Bincike ko har masu gadin gidan an kama amma babu wata hujja ko d'aya da aka samu
daga kan rasuwar Hafsat har ta Maryam.

KADUNA GARIN GWAMNA.

Yau Sati d'aya da kenan da komawar Fadila aiki.Saidai kullum cikin takurar Oganta
ta ke.Dan tunda Jamilu ya sanar da shi ta amince da soyayyarshi tun daga nan ya
fara ta kurata. Haka dai Fadila ke daurewa ta na biye mai suna fira badan tana jin
dad'in firar da shi ba.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya Fadila kullum sai ta je aiki.Mahaifinta kuma babu
tasa dole ya kauda kai da surutan mutane.

Babu laifi yanzu suna rayuwarsu da sauk'i .Dan kullum Fadila ta tashi aiki sai
gogannata ya bata kud'in mashin din zuwa gida, tom da sune take kaiwa su yi
cefane.

WATA UKU KENAN DA KOMAWAR FADILA AIKI.


Yanzu Fadila ta saki jikinta sosai da Ogan nata duk da bata wani son shi ta fara
tunanin auranshi, dan wa'adin da mahaifinta ya bata yana gaf da cika.Kuma har yanzu
mahaifinta kullum cikin k'ara tunatar da ita yake akan yana nan fa akan bakarshi
daga wa'adin da ya sa mata ya cika ko ta yi aure ko kuma ta bar mai gida.Wannan ya
sa ta fara sakar ma ogan nata fuska, idan ta ga ba hali ta yi hak'uri ta aure shi.

Yanzu har gidan su Fadila sun san soyayyarta da ogan nata.

Yau Fadila bayan ta dawo aiki, mahaifinta ya kirata .Ya dad'e ya na kallan Fadila
kamar mai neman wani abu a jikinta, sai zuwa can ya ce"Fadila, yau saura wata biyu
wa'adin da na baki ya cika, amma har yanzu bikice min komai ba?"
Fadila shiru ta yi gabanta na fad'uwa.Haka dai ta daure ta ce"Eh, Baba ban manta
ba"Ya yi kyau"Mahaifin Fadila ya ce.

Fadila ranar haka ta kusan kwana tana tunanin mafita, abu d'aya da ta sani shi ne
bata son Ogan nata, saidai za ta yi hak'uri haka nan ta aure shi in da bata da wata
mafita.Haka Fadila ta yanke ma kanta auran ogan nata ba wai dan tana son shi ba sai
dan mahaifinta da ya hura mata wuta.

Washegari Fadila ko da taje aiki zama ta yi shiru, kallo d'aya za ka yi mata ka


gane tana cikin damuwa.
Jamilu abokin aikin Fadila, da zuwan shi kenan cikin tsokanar Fadila ganin ta yi
nisa a tunani ya ce"Alamar tambaya ta na ga mai yawaita tunani, musaman in ya shiga
halin soyayyar zamani , ya...." Kallan da Fadila ta yi ma Jamilu ne ya sa ya yi
shiru yana dariya ya ce"Ko za ki cemin wannan shurun naki ba soyayya ba ce sila?"
Ba ita bace hasali ma k'i ne sila"

Jamilu zama ya yi ya ce"To fa, ba ni in Sha?"Fadila cikin sanyi kamar za ta yi kuka


ta ce"Jamilu zan auri MD ba dan ina son sa ba saidan banda wata madafa"Jamilu ko da
har kullum bai ga wani aibun MD d'in ba ya ce"Fadila, ki kwantar da hankalinki MD
ba shi da wata matsala, sannan shi d'in masoyi ne gareki na hak'ik'a"

Haka dai Jamilu ya yi taba Fadila kwarin gwiwar auran MD d'in.


Fadila bacin ta tashi aiki kamar kullum sai sun tab'a hira da Ogan nata sannan take
tafita gida.Tom yau acikin firar ne take sanar da shi ta bashi dama koda yaushe zai
iya aikowa gidansu.

Murnar da MD ya yi kad'ai ta k'ara tabbatar ma Fadila da son da yake mata.

Cikin tsantsar farincikin da ya kasa b'oyewa ya kalli Fadila ya ce"Zan iya aikowa
gobe kenan?" Kai Fadila girgiza mai ta ce "Gobe Baba zai yi tafiya saidai in ya
dawo "

Haka Fadila suka rabo da MD d'in akan daga mahaifinta ya dawo daga tafiyar da zai
yi za su aiko.

Washegari mahaifin Fadila da wuri ya shirya tafiyar da zai yi zuwa Gombe.

Fadila da mahaifiyarta su ka yi mai rakiya har tasha. Sai da motarsu ta tashi


sannan suka dawo, in da Fadila ta nufi wajan aiki mahaifiyarta kuma ta yo gida.

Satin mahaifin Fadila d'aya ya dawo.

Yau Fadila bayan ta tashi daga aiki ne MD ya rakota kamar yadda ya saba ya kalleta
ya ce"My Fadila, har yanzu Baba bai dawo ba?" Fadila ji tai bata buk'atar sanar da
shi yanzu in da tasan maganar aikawa zai mata, hakan ya sa ta ce " Bai dawo ba "
Kallanta ya yi ya ce "Sai yaushe kenan?" Duk lokacin da ya dawo zan sanar da kai"
Fadila ta ce atak'aice.

Sai da Fadila ta samu keke-napep ta hau sannan MD ya juya ya tafi.

ADAMAWA STATE

BAYAN WATA UKU DA RASUWAR MARYAM.

Ki manin wata uku kenan da rasuwar Maryam. Yanzu Muhammad ya dangana har ya koma
bakin aikin shi.

Alhaji Sagir zaune yana danna waya Hajiya Baturiya ta kallai ta ce "Alhaji, ban ji
dadi ba da ka hana Jibirin dawowa, yanzu ace Muhammad ya yi aure har biyu duk ba
matan amma ace be zo ba" Alhaji Sagir murmushi ya yi ya ce"Tom ba gashi ba yanzu ya
gama karatunshi lafiya lau, ko da ya zo me zai mai? "Alhaji Sagir suna cikin haka
ne Muhammad da ya je airport d'akko Jibirin suka shigo tare bakunansu d'auke da
sallama.

Alhaji Sagir cikin washe baki ya ke cewa"Ka ga mutanan Turai, jibirin ka ganka ko
har ka fara komawa kalarsu"Gaba d'ayansu dariya su ka yi sanna Jibirin ya zauna
suka gaggaisa da iyayan nasa.

Alhaji Sagir kallan Jibirin ya yi ya ce"Jibirin ku je ka ci abinci ka ga isowarka


kenan.

Jibirin tare da Muhammad suka ci abincin, dama kuma komai nasu tare su ke yi.
Dawowar Jibirin tasa Muhammad ya kuma sakin ranshi sosai ya fara mantawa da duk
wata damuwarshi.

Alhaji Sagir zaune da su Muhammad suna fira, kamar yadda suka saba kusan duk dare
in Alhaji Sagir na gari.Alhaji Sagir ya kalli Muhammad ya ce"Muhammad ina so in
baku shawara kai da Jibirin, duk kanku ya kamata ace duk kun yi aure, duk da dai
kai Muhammad ka yi amma Allah da ikon shi ga abun da ya faru, amma duk da haka
hakan ba zai zama hujjar da zaka rik'e kace wai ba za kai aure ba, gara ma Jibirin
k'aninka ne "

Muhammad kamar zai yi kuka ya d'ago yana kallan mahaifin nashi ya ce"Daddy, dama za
ka kuma iya yi min maganar aure? ,Daddy, na za ci kai kanka ka hak'ura da wannan
batun, wa kake gani yanzu zai iya ban auran 'yarsa ma? " Muhammad ya idasa maganar
kamar zai fasa ihu.

Jibirin cikin tausaya ma Muhammad ya dafa kafad'ar shi ya ce"Ni na yi imanin babu
wadda za ka je naiman auranta ta k'i Muhammad, kuma ta bakin Daddy haka ba hujja ba
ce ka jaraba naima ka gani mana"

Muhammad shiru ya yi baitanka musu ba.


Alhaji Sagir ya ce "Muhammad, ka yi shiru?" Muhammad cikin gatse dan ya san babu ma
wanda za su k'ara ba shi aure ya ce"Daddy, idan an samu wadda zata iya aure na shi
kenan babu damuwa na amince"

Jibirin kallan Muhammad ya yi ya ce"Amma kasan Laila na sonka? "

Muhammad da ya tabbatar ma kanshi babu wata wadda zata aure shi ya ce"Idan ta
amince babu damuwa Jibirin"

Alhaji Sagir kallan Jibirin ya yi ya ce"Wacece ita yarinyar? " Yarinyar Mansur
Inuwa ce" Shiru mahaifin Muhammad ya yi sannan ya ce"Shi kenan ka yi min magana da
yarinyar tukun idan ta amince"
Da daddre Jibirin ya je wajan Laila ya sanar da ita abin da ke tafe da shi.Bud'ar
bakinta sai cewa ta yi "Allah ya tsareni, wato in je nima a tsotse jinina kamar
yadda aka yi ma wa in can" Haka dai ta yayyab'a ma Jibirin magana ta tafi ta bar
shi anan.

Jibirin cikin damuwa ya sanar da Alhaji Sagir yadda su ka yi da Lailar.

Muhammad ko ko da ya ji basu k'ara tada mai maganar ba ya san sun je ba a dace ba.

Tun daga ranar mahaifin Muhammad bai kuma yi ma Muhammad zancan aure ba.

KADUNA GARIN GWAMNA

Fadila kullum tana so ta sanar da MD akan ya aiko gidansu kafin mahaifinta ya kuma
yi mata maganar, amma zuciyarta ta k'i aminta da shi a matsayin miji a gareta.

Yau dai Fadila ta yi alk'awarin sanar da MD d'in ganin saura sati biyu wa'adin da
mahaifinta ya bata ya cika, duk da yanzu taga gaba d'aya MD d'in ya fara jan baya
da ita ba kamar da ba.

Yau ne ranar da Fadila ta yi k'udirin sanar da MD ya aiko gidansu.Saidai ko da taje


aiki yau da ta gaida shi sama-sama ya amsa gaisuwarta daga nan bai kuma saurarta ba
ya ci gaba da abin da yake.Hakan sosai ya ba Fadila mamaki, amma saita bar hakan
akan k'ila jamai ran da take yi ne kullum tace mai yau tace gobe.

Fadila cikin sanyi da yanayin yarda ya yi mata ta ce"Na san ni mai laifice a
wajanka, amma ya wuce, ina mai yi maka albishir d'in duk lokacin da ka shirya koda
ko yaune ka aiko wajan mahaifina"
MD ya dad'e yana kallan Fadila bayan ta kai bayananta, sannan ya kauda kan shi ya
ce"Fadila, ina miki fatan Alkairi Allah ya baki miji na gari, babu maganar aure
yanzu tsakanina da ke sai zumuminci"

Fadila cikin tsananin mamakin take kallan shi, so take ta yi magana ma amma ta
kasa. Sai da ya furta mata haka fargaba ta ci kata idan mahaifinta ya b'ullo mata
wuta ya za ta yi.

Fadila cikin murmushin yak'e ta ce"Sir, ko na yi maka wani laifin ne?" Kallanta ta
ya yi ya ce"A'a, biki min komai ba, son ne kawai ya fita araina, amma zumincinmu
na..."

Fadila bata saurareshi ba ta yi tafiyarta.

Fadila cikin sanyi ta shiga Office dinsu. Jamilu da kallo d'aya ya yi ma Fadila ya
fahimci tana cikin damuwa, dan ita Allah ya halicce ta cikin wa inda ba sa iya
b'oye damuwarsu.

Jamilu cikin tsokanar Fadila, ya ce"Kowattab'aki zo ki gaya min, in dai a kanki ne


ba a iya min, nasha aradu kanki nasha Yasin, akanki zana aika mutum yanzu ko da ko
MD ne" Fadila murmushi ta yi ta ce"MD ne ya tab'a ni Jamilu, bana son MD amma abun
mamaki wai dan MD yace ya fasa aurena ka ji yarda na ji kuwa?" Jamilu cike da
mamaki da al'ajabi ya ke bin Fadila da kallo ya ce"Fadila, ban fahimta ba? Na ji
kin zo min da wata sabuwar tatsuniya ne"

Shiru Fadila ta yi tana kallan Jamilu ,sannan ta ce"Na yi mamaki sosai da jin
furicin MD dama kuma kwana biyu ya fara sauya min" Jamilu shiru ya yi sannan ya ce
" Tabbas wannan abun mamaki ne, da ace bansan halinki ba da sai in ce k'ila ya samu
abin da yake so ne, to amma ni d'in nasan wacece Fadila" Cewar Jamilu da al'ajabi
ya isai.
Atak'aice dai Fadila haka ta koma gida tana jinta duk babu dad'i. Abu d'aya yake
damunta shi ne mahaifinta yana gaf da ya yi mata magana ga shi ta gama sakin jiki
da MD d'in akan shi zata aura duk da ba wai dan tana son shi ba.

BAYAN SATI D'AYA

Fadila ta tashi yau bata jin dad'in jikinta haka nan dai taje aiki.Koda ta je bayan
sun gama gabatar da Shirin da take ne ta kalli Jamilu ta ce"Jamilu, bari in yi ma
MD magana gida zani bani da lafiya" Fadila tana fad'in maganar ta tashi da sunan
✍🏻
tafiya, saidai sakamakon jirrin da take gani tana tashi ta yanke jiki ta fad'i

📚 FADEELAH 📚
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare
da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻

Naga
Fadila Sani Bakori.

SANARWA : Masu tambaya akan gyaran jiki akwai hanyoyi kala daban-daban da zan kawo
muku na gyaran jiki acikin wannan littafi mai suna FADEELAH .

Page 6
Fadila ta tashi yau bata jin dadin jikinta, hakan nan dai ta je aiki, koda ta je
bayan sun gama gabatar da Shirin da suke yi ne ta kalli Jamilu ta ce"Jamilu, zan yi
ma MD magana gida zani ba ni da lafiya. " Fadila tana fad'in haka ta tashi da sunan
tafiya , saidai sakamakon jirin da take gani tana tashi ta yanke jiki ta fad'i"

Jamilu da sauran abokan aikinsu cikin rud'ewa su ka yi kan Fadila da ke kwance a


k'asa a sume.

Jamilu fita ya yi ya je ya yi ma MD magana ya sanar da shi halin da Fadila take


ciki.
MD Cikin mamaki ya kalli Jamilu ya ce"Jamilu, bata da lafiya ne dama?" Tom, ni dai
ban sani ba, sai yau bayan mun gama aiki take sanar da ni bata jin dad'in jikinta
za tafi gida, tom ta tashi ne ma da niyyar zuwa ta sanar da kai ta yanke jiki ta
fad'i " MD cikin damuwa da halin da aka fad'a mai Fadila na ciki ya ce " Mu je
akaita Asibiti a duba lafiyarta"

Da taimakon Firdausi da Ummi aka Fadila a mota, wa inda suma ma'aikata ne a gidan
TV , suka tafi Asibitin.

Suna tafiya kafin su isa Asibitin Fadila ta farka , kallan Ummi ta yi wadda take
kwance ajikinta, cikin k'asa da murya irin ta marasa lafiya Fadila ta ce" Ummi ,
Lafiya ? Ina Zamu? " Ummi cikin kwantar ma Fadila da hankali ta ce " Ba ki da
lafiya ne shi ne za mu kaiki Asibiti a duba lafiyarki " Fadila shiru ta yi tana
mamakin yadda akai haka , Sannan ta ce " Na ji sauk'i MD mu juya "

Ba tare da ya juyo ya kalleta ba ya ce" Ki bari mu je a duba lafiyarki hakan na da


kyau"

Koda suka shiga cikin Asibitin Fadila saida ta dafa Ummi saboda tsananin jirin da
take ji . MD Ummi ya ba kud'i ta sayi katin Asibitin sannan suka shiga wani Office.
Likitar kallo d'aya ta yi ma Fadila ta gano abun da ke damunta, amma sai cewa ta
yi" Me ke damunki ? " Jirine kawai sai rashin k'arfin jiki da ke damuna " Cewar
Fadila. Kai likitar da jinjina sannan ta ce" Tun yaushe kike jin hakan ? " Tsakanin
jiya da yau ne na fara jin hakan " Likitar laboratory Lab ta tura su Fadila blood
test.

Cikin kankanin lokaci aka yi ma Fadila awon ta kawo ma likitar sakamakon .

Likitar na dubawa murmushi ta yi ta kalli Fadila ta ce " Kira min mai gidanki shi
zan fad'ima ma wannan sakamakon " Fadila murmushi ta yi ta ce" Ba mujina bane Ogana
ne , ki fad'in kawai "

Shiru likitar ta yi tana kallan Fadila, Sannan ta ce" Kina d'auke da cikin wata
d'aya da kwana kai " Fadila zaro mayan-manyan idanunta ta yi tana kallan likitar
ta ce" Likita ciki kuma ? , Kuma ni ? Kai ! ki sake bincikata dai ki gani , budurwa
ce ni fa ba ni da aure ! " Likitar kara kallan Fadila ta yi da kyau sannan ta ce "
'Yan mata kina zuwa kallo d'aya na yi miki na gano abun da ke damunki "

Fadila tashi ta yi ta ce" Ina ban yarda ba Wallahi , ciki fa ? Kuma ni ?, to ,ta ya
ya?"

MD jin alamun kamar hayaniya tsakanin Fadila da likitar , ya shigo office d'in yana
tambayar Fadila Lafiya.

Fadila tsabar takaici kasa ba MD amsa ta yi , sai likitar ce ta ce " Ciki take
d'auke da shi, shi ne ta tsaya tana gaddama wai in sake bincike , bacin tunda ta
shigo kallo d'aya na yi mata na fahimci abun da ke damunta "

MD rasa abun cewa ya yi ya tsaya yana kallan Fadila kamar wani sakarai , Fadila
kuma tsabar takaici kawai sai ta fashe da kuka ba wai dan ta yarda da maganar
kikitar ba ne , tana kukan shairin da ta yi mata ne.
Likitar ko ganin haka kallan Fadila ta yi ta ce" Yi hak'uri 'yan mata share
hawayanki idan biki yarda ba ko kina ganin shairi na yi miki za ki iya zuwa wani
Asibitin a dubaki" Tana fadin haka ta kalli MD ta ce za ku iya tafiya "

Haka suka fito ba wanda ya tanka ma kowa. Ummi ko wadda ta ji duk abun da ke
faruwa ita kanta ba k'aramin mamaki ta yi ba.

Fadila da har yanzu jiri take gani rik'e Ummi ta yi da sauri . MD kuma ganin haka
ya ce " Kinga ma ko magani ba mu tsaya amsa ba , mu je wani Asibitin a dubaki a
baki magani "

Innalillahi wa inna ilaihir raj'un , hankalin Fadila ba k'aramin tashi ya yi ba ,


lokacin da aka maimaita mata tana d'auke da ciki kamar yadda waccan likitar ta
fad'a mata. Abun ka da mai ganin jiri Fadila yanje jiki ta yi ta fad'i wajan asume.

Take aka ba Fadila gado , in da MD kuma ya kalli Ummi ya ce" Ki kula da ita ina
zuwa "

Ummi ko da dama ba wani shiri suke da Fadila ba ,ai abun yad'awa ya samu agareta ,
gefe guda ta koma , Jamilu ta fara kira ta sanar da shi Fadila na d'auke da ciki.
Jamilu jin maganar ya yi wata iri ,sannan cikin b'ata fuska ya ce " Ummi , wannan
kuma wata irin magana ce haka ? Idan ma wasa ne wannan ai ba wasa ba ne , haba ki
rasa kan wadda za ki fad'i wannan muguwar fatar taki sai kan Fadila "Ummi da abun
da ake so ya samu ta ce" Jamilu , Wallahi kar ka ji batun wasa Fadila ciki gareta
ta , da aka fad'i ita kanta nunawa ta yi bata yarda ba irin borin kunyar nan , to
shi ne MD ya ce mu je wani Asibitin a bata magani saboda wancan borin kunya ya sa
ta k'i bari a bata maganin ma , aiko muna zuwa nan aka maimaita mata kamar yadda
aka fad'i a d'ayan Asibitin"
Jamilu Allahhuma ajirni filmusibati kawai ya ke maimaitawa sannan ya ce" Ummi ,
kuna wana Asibin ne idan na tashi aiki in zo? " Muna nan Wisdom Hospital "

Ummi na nan zaune Jamilu na tashi aiki ya zo cikin k'osawa da ya ga halin da Fadila
take ciki . Allah ya sa tana farkawa ya shigo. drip d'in da aka samata saura kiris
ya kare .
Jamilu cikin sanyi ya ce" Sannu Fadila , ya jikin naki ? " Fadila fashewa da kuka
ta yi ta na cewa " Jamilu , ka ji shairin da su ka yi min ko ?" Fadila ta idasa
maganar cikin tsantsar tashin hankali da damuwa.

Jamilu shiru ya yi yana kallan Fadila ya ma rasa abin cewa.

Fadila tashi ta yi tana kallan Jamilu ta ce" Jamilu , dare ya yi za a naimeni a


gida , gida zan tafi " A'a , Fadila ki yi hak'uri jikin ki ya yi sauk'i , Sai in je
gidanku yanzu in sanar halin da kike ciki " Fadila kallan Jamilu ta yi ta ce " Me
za ka ce musu yana damuna ? " Zan sanar da su ne cewa baki jin dadin jikinki" Kai
Fadila ta girgiza ta ce " Karka fad'a musu komai , bari na ji sauk'i zan iya kowa"

Babu yarda Jamilu bai yi da Fadila akan ta kwana Asibitin zuwa gobe a bata sallama
in da ance jikin nata da saura, amma tak'i .

An sallami Fadila suna bakin titi za su tari Keke-Napep motar MD ta tsaya .Bud'e ma
Fadila ya yi ya ce " Shigo in k'arasa da ke gida " Fadila ji ta yi bata da wani
zab'i wanda ya wuce ta shiga , in da dakyar take tsayuwar dan gaba d'aya bata jin
k'arfin jikinta ,hakan ya sa ta shiga motar.

MD sai da ya kai Fadila har k'ofar gidansu sannan ya mik'a mata ledar
maganungunanta ya juya ya tafi ba tare da ya ce mata komai ba.

Mahaifin Fadila ya fito kenan za shi masallaci sallar Issha'i aka sauke Fadila a
mota akan idon shi, Mahaifin Fadila bin bayan Fadila ya yi da kallo ganin yadda
take tafiya kamar wata 'yar maye.

Fadila ahankali cikin raunanniyar murya ta yi sallama ta shiga gidansu.


Mahaifiyar Fadila da kallo tabi Fadila ganin yadda ta shigo kamar wadda tasha ta
bugu .Fadila na zuwa ta kwanta kan d'an madaidaicin gadonsu.

Mahaifiyar Fadila tashi ta yi tana cewa" Fadila , lafiyarki kuwa ? " Ban da lafiya
" Fadila ta bata amsa a takaice.
Mahaifiyar Fadila shiru ta yi sannan ta ce " Shi ne dalilin dad'ewar taki kenan ? "
A'a mun je Asibiti ne " Me ke damunki ? " Mahaifiyar Fadila ta tambayi Fadila.
Fadila cikin rashin sanin amsar da zata bata ta ce" Ban sani ba nima" Ta fad'i
maganar tana goge hawayan da ke zubar mata.

Mahaifiyar Fadila ko da bata kawo komai aranta ba dan ita ta yi tunani ma kodan
lokacin da mahaifinta ya bata yana gaf ya cika ne ya sa kila take son sa kanta
cikin damuwa, hakan ya sa ta zauna bakin gadon da Fadilar ta ke, ta ce " Fadila ,
me ke damunki ne ? Lokaci guda haka kika rikice, In dan ma maganar mahaifinki ce ki
kwantar da hankalinki shi aure ai lokaci ne , dan haka karma ma ki sama kanki
damuw..."
Sallamar mahaifin Fadila ce ta sa Mahaifiyar Fadila ta yi shiru. Mahaifin Fadila ya
ce " Fadila , wa ya kawo ki k'ofar gidan nan a mota ? " Fadila tana goge hawayan da
ke zubar mata ta ce " Ba ni da lafiya ne ba na jin k'arfin jikina shi ne MD ya
kawoni a motarsa " Shiru mahaifin Fadila ya yi dan sosai ya ke yabawa da hankalin
ogan nata .
Ya san tabbas in ba rashin lafiya ba kodan munafukan layin nasu ya san Fadila ba
zata yarda ta hau motar kowa ba ya kawoka har k'ofar gida , kuma a cikin wannan
lokaci haka ba rana ba .

"Shi kenan, Fadila dan Allah a k'ara kulawa da kai , duk in da kike kisan in ba ma
ganinki mahaliccinki na ganinki " Fadila dakyar ta iya bud'e baki tana mai
k'ok'arin danne kukan da ke taso mata ta ce " In sha Allah, Baba "

Mahaifiyar Fadila da kanta ta sawo ma Fadila tuwon da ta yi ta kawo mata .

Fadila ko ba dan tana son cin tuwan ba sai dan kar a fahimci halin da take ciki ta
daure taci kad'an , Sannan ta lallab'a ta yi sallah ta koma ta kwanta.

Kasancewar har washegari Fadila bata jin k'arfin jikinta hakan ya sa bata yi wani
yunk'urin zuwa aiki ba.
Mahaifiyar Fadila na kitchen tana dama musu koka k'anwar Fadila wadda ke bi mata
Aisha kenan wadda satin d'aya kenan da dawowa hutu da yake bording School take
yi .Bayan ta gaida mahaifiyar tasu ne ta ce " Mama , anya kuwa ba akwai abin da ke
damun Aunty Fadila ba ? Jiya fa kwana kuka ta yi ? Ko yanzu haka idan kika shiga
d'akin za ki ganta tana kuka kad'an-kad'an " Mahaifiyar Fadila barin abun da take
yi ta yi tana kallan Aisha ,sannan ta ce" Biki tambayeta me ke damunta ba ? " Jiya
da daddare dai bayan kin fita na tambayeta ta ce min babu komai , daga nan ni kuma
ban kuma tambayarta ba " Shiru mahaifiyar Fadila ta yi , sannan ta tashi ta nufi
d'akinsu Fadilar.

Kwance mahaifiyar Fadila ta samu Fadila tana kuka k'asa-k'asa sosai , sai uban
ajiyar zuciya da take ja .Mahaifiyar Fadila zama bakin gadon ta yi tana bubbuga
k'afar Fadila , ta ce " Fadila , tashi ki zauna"
Fadila da sai yanzu ta ji alamun da mutun ad'akin goge hawayanta ta yi da sauri ta
tashi ta zauna.

Mahaifiyar Fadila ganin yadda idon Fadila ya kumbura ya yi jajir tsabar kuka ,
cikin damuwa ta ce " Fadila , lafiya me ke damunki Wanda ya sa kika kwana kina kuka
tun jiya har yau ?" Fadila k'asa ta yi da kanta tana mai goge hawayan da ke zubar
mata.

Mahaifiyar Fadila ta kuma cewa " Fadila, me ya faru dake ne haka wanda ba zaki iya
fad'imin ba? Idan ni biki fad'a min ba sai ki sanar da Aisha , kalli fa yadda
idonki ya kumbura "

Fadila ci gaba da kukan ta yi kuma tak'i yin magana .Mahaifiyar Fadila kamar ta yi
zuciya ta rabu da ita ,amma kuma ta kasa , hakan ya sa cikin damuwa ta kuma cewa "
Ko wajan aikin naku ne akai miki wani abun ? " Kai Fadila ta girgiza. " Me a kai
miki to? " Nan ma dai Fadila shiru babu amsa.

Atak'aice Mahaifiyar Fadila babu irin tambayar da ba ta yi ma Fadila ba akan abun


da ke damunta amma shiru tak'i magana sai kuka. Suna cikin haka ne Aisha k'anwar
Fadila ta shigo .Aisha cikin damuwa da halin da taga Fadilar ta kalli mahaifiyarsu
ta ce " Mama, me ke damunta ne ? " Aisha ban sani ba , tak'i fad'a min , kira min
Jamilu awaya mu yi magana da shi in ji ko wani abun ne ya faru jiya acan wajan
aikin nasu "

Mahaifiyar Fadila Jamilu ta sa aka kira mata, bacin sun gaisa ne ta ce " Jamilu ,
lafiya ? Tun jiya Fadila da ta shigo gidan nan take kuka na yi na yi ta k'i fada
min abun da take ma kuka , shi ne na ce bari in tambayeka ko ka sani ? "

Jamilu shiru ya yi dan baisan amsar da zaiba mahaifiyar Fadila ba , hakan ya sa ya


ce "Mama, idan na tashi aiki zan biyo ta nan "

Mahaifiyar Fadila da Aisha tashi su ka yi suka bar Fadila anan tana mai ci gaba da
kukanta.

Har Jamilu ya tashi aiki ya zo gidan idanun Fadila ba su bar zubar hawaye ba.
Mahaifiyar Fadila bayan sun gaisa da Jamilu ta ce " Jamilu, tun jiya Fadila ke
kukan nan har yau , mun yi mun yi ni da 'Yar'uwarta ta k'i fad'amana abun da ke
damunta , shi ne dalilin kiranka na ga taku ta zo d'aya ko kai ta fadi maka ? "
Jamilu shiru ya yi ,ya ma rasa ta ina zai fara . Tabbas zuciyarshi ta kasa aminta
mai da wai Fadila na da ciki .
Jamilu kallan Fadila ya yi ya ce " Fadila, ko dai ki fad'a mana damuwarki ko kuma
ki yi hak'uri da kukan nan da kike yi , kina sa 'Yan'uwanki da mahaifiyarki cikin
damuwa, dan Allah ki daure ki sanar damu gaskiyar lamarin abun da ke damunki ? ".

Fadila kai ta d'aga tana kallan Jamilu da idanunta wa inda har sun fara kankancewa
tsabar kuka .Sannan cikin kuka ta fara magana kamar haka " Jamilu, nima bansan
abin da ke damuna ba. Saidai ina jin rayuwata ta zo k'arsh..." Aisha k'anwar Fadila
rufe mata baki ta yi ta ce kamar za ta yi kuka ,dan tabbas kome yake damun Aunynta
mai girma ne, wanda har ta kasa fad'a musu.
Aisha da hawaye har ya fara zubo mata ganin yarda Fadila ke kuka ta ce " Haba,
Aunty Fadila, dan Allah kar ki sa zuciyarmu cikin waswasi mana, kisa mu yi ta
canke-canke abun da ba shi kenan ba , dan Allah ki fad'amana damuwarki ? Idan kuma
kink'i zan je in kira Baba in sanar da shi abun da ke faruwa na san shi zaki fad'i
mai " Aisha na fad'in haka jin Fadila bata ce komai ba ta tashi zata fita alamun
zata kira mahaifin nasu.
Fadila da sauri ta kamo hanun Aisha tana mai k'ara tsananta kukanta ta ce " Mama ,
ku yi hak'uri zan sanar da ku ? Amma dan Allah ina rok'onku ku ban nan da sati
✍🏻
d'aya sannan

*🤝 SDEEND MTN DATA SERVICES🤝*


*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦250
2GB = ₦700. 1GB ₦500
3GB = ₦1050. 2GB ₦1000
4GB = ₦1400. 3GB ₦1500
5GB = ₦1750. 4GB ₦2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For

📚 FADEELAH 📚

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare
da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻

Na
Fadila Sani Bakori.
SANARWA: Masu tambaya akan gyaran jiki akwai hanyoyi kala daban-daban da zan kawo
muku na gyaran jiki acikin wannan littafi mai suna FADEELAH.

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*


*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦250
2GB = ₦700. 1GB ₦500
3GB = ₦1050. 2GB ₦1000
4GB = ₦1400. 3GB ₦1500
5GB = ₦1750. 4GB ₦2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

Page 7

Fadila da sauri ta komo hannun Aisha tana mai k'ara tsananta kukanta ta ce " Mama,
dan Allah ku yi hak'uri zan sanar da ku abin da ke damuna amma ba yanzu ba , ku ban
nan da sati d'aya sannan " Shiru Mahaifiyar Fadila ta yi sannan ta ce " Fadila ,na
yarda zan baki nan da sati amma saidai da sharad'in ba za ki zauna kina mana koke-
koke ba " Fadila kai ta d'aga ta ce " Eh, na yarda "

Haka mahaifiyar Fadila ta tashi jiki babu kwari ta fita , dan tana ji ajikinta abu
mai girma ke damun Fadila .
Bayan mahaifiyar Fadila ta fita ne Aisha ma ta ta tashi ta fita, ya rage daga Jamiu
sai Fadila .

Jamilu kallan Fadila ya yi cikin tausayawa ya ce " Fadila, wai da gaske ne maganar
da Ummi ta fad'amin kina da ciki? " Fadila d'ago idanunta ta yi dake zubar da
hawaye ta ce " Ban sani ba nima Jamilu, amma haka likitoci har biyu suka ce "
Jamilu shiru ya yi , sannan ya ce " Fadila , amma babu wani wanda kika tab'a ba
dama ? " Fadila kallan Jamilu ta yi ta ce " Kamar ya kenan ? " Nufina ko kin ba
wani dama ya kusanceki kamar MD da naga kuna tare ?" Fadila fashewa da kuka ta yi ,
cikin kukan ne take cewa " Jamilu, na zaci kana cikin mutanan da za su bada shaida
akaina, saidai kash jibi tambayar da kake jifa da ita , hakan ya tabbatar min in
wasu sunmin irin tambayarka ba zan ji haushi ba, MD kuma saninkane bana son shi,ko
wanda nake so ba zan bashi damar haka ba bare MD, dama Jamilu ba zaka iya bada
shaida akaina ba? "

Shiru Jamilu ya yi sannan ya ce " Fadila, kina da ciki fa aka ce , kuma kina fadin
ni kike tunanin zan shaideki ? to taya ? In ce ma mutane me ? " Fadila kamar za ta
yi kuka ta ce " Ka fada musu abin da ka sani akaina " Jamilu tashi ta yi tsaye
alamun zai tafi sannann ya ce " Fadila, shawarar da zan baki ki sanar da
mahaifiyarki abun da ke damunki " Ba zan iya ba Jamilu " Tom shi kenan ni na
tafi"

Jamilu sallama ya yi ma Fadila ya tafi.

Bayan Jamilu ya fita Aisha d'akin ta shiga. Zama ta yi kusa da Fadila ta ce cikin
sanyi "Aunty Fadila , nasan Jamilu ya san abun da ke damunki ya b'oye mana ne kawai
, Aunty Fadila , ko ni ce in dai kin yarda zan iya rufa miki asiri dan Allah ki
sanar da ni abun da ke damunki? "

Fadila hanun Aisha ta rik'e ta ce "Aisha zan sanar da ke zuwa gobe "
Aisha ta shi ta yi ta je ta kawo ma Fadila tuwan dare sa su ka yi, amma da kyar ta
samu ta ci.

Duk abun nan dake faruwa na koke-kok'en nan da Fadila ke yi Mahaifinta be sani ba.

Yauma dai kamar jiya Aisha tana jin kukan Fadila kad'an-kad'an a haka barci
yakwasheta ta bar ji.

Washegari bayan sun karya ne Aisha ta kalli Fadila da ta yi tagumi ta yi shiru,


daga gani ta yi nisa a duniyar tunani " Aisha cikin damuwa da damuwar Auntynta ta
ce "Aunty Fadila , yau ne kika yi min alk'awarin za ki sanar dani damuwarki ? "
Fadila shiru ta yi , sannan ta ce " ki kai min ruwa a bayi in yi wanka ki shirya ki
rakani wani waje " Aisha tashi ta je ta kaima Fadila ruwan , sannan ta dawo ta
sanar da ita.

Bayan Fadila ta fito wankan ne ta ce ma Aisha ta sanar da mahaifiyarta zata raka


wani waje yanzu za su dawo.

Mahaifiyar Fadila da kallo tafi su lokacin da za su fita.

Bakin titi suka je Fadila ta tarar musu Keke-Napep suka hau . Fadila ta ce ma me
keken ya kai su 44 Hospital.

Aisha da mamaki ta kalli Fadila ta ce " Aunty Fadila , Asibiti kuma ? Me za mu je


mu yi acan ?" Fadila cikin sanyi ta ce " Aisha, ina son mu je canne dan sanin
ainihin abun da ke damuna , ance suna da kwararrun likitoci "Aisha dai kai ta
jinjina bata ce komai ba.
Koda suka je Asibitin Fadila bayanin duk yadda take ji ta yi ma likitar. Wata roba
likitar ta ba Fadila ta ce ta kawo mata fitsarinta.

Kasan cewar 44 babban Asibiti ne hakan ya sa a ka yi ma Fadila duk wani aune-aune


da ya kamata.

Bayan an gama ne likitar ta kalli Fadila ta ce " Kina dauke da cikin wata d'aya da
kwanakai "

Aisha k'anwar Fadila zunbur ta mik'e tana kallan likitar cikin rud'ewa ta ce "
Likita ciki kuma ? Auntyna fa ba matar aure ba ce budurwa ce! ? " Abin da ke damun
Auntyki nasanar da ita k'anwata "

Fadila tana kuka ta rik'e k'afar likitar tana cewa " Dama mutum zai iya samun ciki
ba tare ya d'aya namiji ya kusance shi ba likita? " Kai likitar ta girgiza ta ce "
Haka ba zai tab'a faruwa ba k'anwata mace d'aya ce a duniya haka ya faru da ita ita
ce Maryama Mahaifiyar Annabi Isa "

Fadila cikin kuka ta ce " Nima Wallahi irin nata ya faru dani ,dan Allahi ki
taimaka min ki rufa min asiri ki cire min shi " Dokar Asibitin nan ko maganin da
zaizubar miki da shi bamabadawa bare kuma acire miki , za ku iya tafiya " Likitar
ta fad'i maganar tana nuna ma Fadila hanyar fita .

Fadila fita ta yi tana goge hawayan da ke zubar mata ita da k'anwarta Aisha.

Aisha tsayawa ta yi ta goge hawayan dake zubar mata tana yi ma Aunty nata wani irin
kallo na kyama ta ce " Aunty Fadila , dama fuska biyu gareki? kullum maganarki akan
mutunci hasalima aikin da kike yi duk dai magana d'aya ce nan ma maganarki kullum
DARAJAR 'YA MACE ashe ke ba ki da DARAJAR da kike yawan b'ab'atu akanta, da haka
kika yi amfani kika yaudari Iyayanmu " Shiru Aisha ta yi tana goge hawayanta,
sannan ta ci gaba da cewa " Amma basu kika yaudara ba kanki kika yaudara "Kuka
Fadila take yi sosai , da kyar ta bud'e baki za ta yi magana , Aisha ta d'aga mata
hannu ta ce " Aunty Fadila, babu wata magana da zaki yi min , dan ko me za ki ce
babu wanda zai kuma yarda da mayaudaran kala manki " Aisha na kaiwa haka ta tafi da
sauri ta bar Fadila nan tsaye tana kuka.

Aisha da sallama ciki-ciki ta shiga gida. Mahaifiyarsu da kallo ta bita ganin Aisha
ta zama wata iri ga fuskarta ta nuna alamun ta ci kuka.

Cikin Sanyi Mahaifiyar su Fadila ta kalli Aisha ta ce " Aisha, Ina Auntyn taki
fa ?" Aisha ta bud'e baki zata yi magana ne ta fashe da kuka.

Mahaifiyar Fadila cikin alamun rud'ewa ganin yadda Aishar ke kuka ta ce " Wani abu
ya samu Fadilar ne ? "
Mahaifin Fadila dake d'aki fitowa ya yi yana tambayar mahaifiyar Fadila lafiya .
Mahaifiyar Fadila cikin sanyi na alamun damuwa ta ce " Nima ban sani ba, haka ta
shigomin tana kuka "

Mahaifin Fadila kallan Aisha ya yi " Ya ce ina Fadil..." Shigowar Fadila ya sa ya


yi shiru . Saidai abun mamaki Fadila ma da kuka ta shigo tana zazzare manyan-
manayan idanunta , dan ita a tunaninta Aisha ta sanar da su tana da ciki.

Mahaifiyarsu Fadila cikin fad'a-fad'a ta ce " Wai lafiyarku za ku zo ku tasa mutane


kuna musu kuka ba za ku fad'i abun da akai muku ba? " Dukkansu shiru ba magana sai
kuka.

Mahaifin Fadila da shi sai yanzu ma ya san abun da ke faruwa cikin fad'a da yake
irin mutanan nan ne masu fad'an, hakan ya sa cikin d'aya murya da hargagi ya ce "
Aisha!, bada ku mahaifiyarku ke magana ba ? "

Aisha da ko Karan haka ya cijeta ba zata tab'a iya furtama ma Iyayan nata abun da
ke faruwa ba bare kuma ita kanta Fadila. Aisha cikin rashin sanin abun cewa, ga
iyayan nasu sun tsaresu da ido ta ce " Baba , wa'adin da kaba Aunty Fadila saura
sati d'aya ya cika , shi ne abun da ke damunmu "
Mahaifinsu Fadila ajiyar zuciya ya sauke , in da mahaifiyar Fadila bata yarda da
abun da Aisha tace ba .

Mahaifin Fadila ba tare da ya tanka ba ya girgiza kai ya fita.

Aisha da Fadila ko haka suka dawo kamar wasu marayu, ranar dai gaba d'aya gidan sai
ya zamana kamar anyi mutuwa .

Da daddare Mahaifiyar Fadila ta shiga d'akin yaran nata . Zama ta yi tana fuskantar
su Fadila da ko wacce idonta ya kunbura tsabar kuka.

Mahaifiyar Fadila cikin sanyi ta fara magana kamar haka " Fadila , yanzu idan kuna
da damuwa akwai wanda zaku fad'amawa wanda ya wuce ni ? Haba Fadila , haka d'in da
kuke yi bakwa tunanin sani cikin wani halin ? Tom in dai kun d'aukeni Uwa
mahaifiya agareku ina son yanzun nan ba sai gobe ba ku fad'a min damuwarku ? "

Aisha tashi ta yi ta kifa kanta a cinyar mahaifiyarsu tana kuka, cikin kukan ne
take cewa "Mama , Aunty Fadila ta b'ata mana suna , ta jawo mana abun gori a gari ,
ta aje mana tabon da ba zai taba gogewa ba "

Mahaifiyar Fadila gabanta dukan uku-uku ya fara , cikin sanyi a hankali dan jikinta
har yau d'auki rawa ta ce " Aisha, me ya faru ? Ki min bayani da sauri ? "
Aisha cikin kuka ta ce " Mama, Aunty Fadila na da ciki " Ciki ! Wana irin ciki
kuma ? " Mahaifiyar Fadila ta fad'a arud'e cikin rawar baki.

Aisha kai ta d'agama Mahaifiyarsu ta ce "Haka likita ta fad'a a gabana "

Mahaifiyar Fadila tashi ta yi ta yi kan Fadila ta niyyar bugu , saidai tana zuwa ta
b'ungire ta sume awajan tsabar razana da jin abun da Aisha ta ce.

Aisha da gudu cikin fasa kuka ta d'ebo ruwa tana yayyafa ma mahaifiyarsu, sannan ta
farfad'o .

Mahaifiyar su Aisha kuka take sosai ta ma kasa magana. Fadila ko ganin yadda
mahaifiyarta ke kuka tana jan numfashi kamar wadda numfashinta zai d'auke ,sosai
abun ya furgitata.

Mahaifiyar Fadila tana a wannan halin ne mahaifin su Fadila ya shigo gidan da sauri
cikin tashin hankali dan Husna k'anwar su Fadila ta samai a kofar gida ta sanar da
shi da Mama da su Aunty Fadila sun had'u sai kuka suke . Hakan ya sa ya shigo gidan
a rud'e , tun kan ko ya k'araso ya jiyo sautin kukan mahaifiyarsu Fadila , hakan ya
sa ya'idasa cikin d'akin su Fadilar a rud'e yana cewa " Maman Fadila , Lafiya za
ki zo ki tasa yara ku taru kuna kuka sai kace bani gidan da ba za ku fad'imin abun
da ke damunku ba, In kuma maganar da na fad'a ce kan Fadila ni na janye tuni ina
mata addu'a Allah ya kawo mata miji na gari "

Mahaifiyar Fadila , ido ta d'aga tana kallan mahaifin Fadila ta kasa magana sai
kuka.

Mahaifin Fadila tsugunnawa ya yi kusa da Fadila da idonta gaba d'aya sun k'ank'ance
tsabar kuka ya ce " Fadila, yi shiru kin ji ki natsu ki yi min bayanin abun da ke
faruwa ? " Fadila da ido ta bi mahaifin nata da kallo dan ba zata tab'a iya
fad'amai abun da ke faruwa da ita.
Mahaifin Fadila da sosai suka d'aga mai hankali, zama ya yi yana fad'a yana cewa "
Wai me kuka maidani ne zan zo in tambayarku abun da ke faruwa babu wanda ya
saurareni? " Mahaifin Fadila k'asa ya yi da murya cikin sanyi kamar zai yi kuka ya
ce " Ko dan kun d'aukeni talaka ne ba zan iya yi muku maganin damuwarku ba ya sa ba
za ku fad'a min ba? , Tom indai kun d'aukeni uba wanda kuke kallan zai iya
sharemuku kukanku ku fad'a min damuwarku dan Alllah ? " Mahaifin Fadila ya idasa
maganar kamar zai yi kuka . Dan sosai hankalinshi ya tashi ganin yadda yaranshi da
mahaifiyarsu suka had'u sai kuka suke , daga gani dai wani babban al'amarin ne ya
faru.

Mahaifiyar Fadila d'ago jajayan idanunta ta yi ta duresu a fuskar mahaifin


Fadila.Da katawa da kukan da take yi ta yi tana tunanin ta inda zata fara sanar da
mahaifin Fadila Fadila na d'auke da ciki.
Mahaifiyar Fadila da ta rasa ta inda zata fara sai cewa ta yi " Ka tambayi
Fadila , ita ta fi cancanta ta sanar da kai abun da ke faruwa da bakinta "

Mahaifin Fadila mai da kallan shi ga Fadila ya yi ya ce " Fadila, sanar da ni abun
da ke damunku kin ji?" Fadila k'ara tsananta kukanta ta yi.
Mahaifin Fadila ganin haka sai ya koma kan Aisha ya ce " Aisha, inda su sun k'i
sanar dani , ke fad'a min abun da ke faruwa koma me ye zan muku uziri zan fahimta
" Aisha cikin kuka ta fara magana kamar haka " Baba, zan sanar da kai duk da
zuciyata ta kasa yarda a abun da kunnuwana suka ji min, saidai kukan da Aunty
Fadila kad'ai take yi ya isa ya sa in yarda da abun da kunnuwana suka ji min ,
sannan dan in tabbatar da kanta ta d'aukeni ta kaini Asibitin 44, da farko na zaci
bata da kafiya ne amma sai na ji akasin haka , ashe bata son ta sanar da nine da
bakinta cewar tana da ciki " Aisha ta idasa maganar tana kuma rushewa da kuka .

Mahaifin Fadila cikin tsananin furgici da razana da jin abun da Aisha ta ce, ya ce
" Ciki ! ? Wa ke da cikin ?" Aisha cikin kuka ta ce " Aunty Fadila ke da ciki Baba
" Mahaifin Fadila baki ya bud'e zai yi magana take k'in-k'ina ta shigai ,da hannu
ya ke nuna Fadila jikinshi ko ina yana rawa.Magana ya ke son yi amma ya ka sa,
jikinshi ko ina rawa yake. Ya d'urk'ushe a wajan ya yi yana dafe da k'arji yana
nuna Fadila .Tari ya ke sosai wanda hakan har ya ba su Aisha tsoro, lokaci guda
kuma numfashinshi ya tsaya cak ya fad'i a wajan.

Mahaifiyar Fadila da sauri su ka yo kan mahaifinsu suna girgizashi suna kuka.Ana


cikin haka ne Ahmad mai bi ma Aisha ya shigo gidan, mahaifiyarsu Fadila cikin
rud'ewa ta ce " Ahmad jeka taho da keke-Napep a kai mahaifinku Asibiti " Ahamad
matashin yaro ne d'an kimanin shekara goma sha biyar.Ahamad juyawa ya yi da gudu ya
fita ya je ya zo da mai keke-Napep d'in.

Da taimakon mai Napep d'in su ka sa mahaifinsu Fadila a cikin Napep d'in su ka yi


da shi Asibiti.

Suna zuwa ko da aka duba gawa suka kawo.

Daya daga cikin likitocin ne ya zo ya samu mahaifiyarsu Fadila da su Fadila da ke


zaune jugum-jugum ya ce " Saidai ku yi hak'uri fa gawa kuka kawo mana , Zuciyarshi
ta riga ta buga" Mahaifiyar Fadila a razane ta kalli likitan ta ce " Likita, kana
so ka ce min ya rasu kenan !?" ta fad'i maganar cikin kuka.

Kai likitan ya d'aga mata ya ce " Saidai ku yi hak'uri ya rasu, ku yi hanzarin zuwa
d'aukar gawar kafin su kaita mutuwari "

Da taimakon wani mak'ocin su Fadila da Ahmad ya sanar da shi aka d'akko gawar
mahaifin Fadila daga asibiti.

✍🏻
Haka aka yi zana'idarshi cikin lokaci aka kai shi gidanshi na gaskiya

📚 FADEELAH 📚
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare
da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
💪🏻J.A.W 💪🏻

Daga
Fadila Sani Bakori

SANARWA : Masu tambaya akan gyaran jiki akwai hanyoyi kala dabn-daban da zan kawo
muku na gyaran jiki acikin wannan littafi mai suna FADEELAH .

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*


*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦250
2GB = ₦700. 1GB ₦500
3GB = ₦1050. 2GB ₦1000
4GB = ₦1400. 3GB ₦1500
5GB = ₦1750. 4GB ₦2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

Page 8

Haka aka yi zaman zana'idar mahaifin Fadila, Inda mahaifiyar Fadila da su Aisha
sosai mutuwar mahaifin nasu ta tab'asu, dan gaba d'ayansu sun fita yayyacinsu ba
kamar Fadila ba da take ganin kamar ita ta ce silar mutuwar mahaifin nasu , inda
silarta ne zuciyarshi ta buga.
Haka suka kasance cikin jimamin mutuwar har aka yi addu'ar bakwai. Bayan an yi
addu'a ne 'Yan'uwansu Fadila da suka zo gaisuwa da sauran mutane duk su ka watse,
ya rage daga mahaifiyarsu Fadila sai su Fadila.

Daga Aisha har mahaifiyar Fadila babu wanda ke mata magana abinci ma babu mai ce
mata ta ci ko karta ci. Abunka da mara lafiya hakan sai ya k'ara ma Fadila ciwo
sosai.

Yau Aisha jin Fadila shiru ko sallar Asuba bata tashi ba hakan ya sa bayan ta je ta
dama musu koko ta zo ta zauna bakin gadon da Fadila take tana Kiran sunanta, amma
shiru . koda Aisha ta duba sai taga ashe Fadila asume take. Hakan ya sa Aisha cikin
tashin hankali ta yi d'akin mahaifiyarsu da gudu ta sanar da ita halin da Fadila
take ci.

Allah sarki mahaifiyar Fadila dake zaune tana kurbar kokan da Aisha ta dama musu
cikin rud'ewa ta tashi har tana zubar da kokan bata sani ba.

Mahaifiyar Fadila koda ta je taga halin da Fadilar ke ciki, cikin tsananin damuwa
ta ce " Aisha, Kira Napep mu kaita Asibiti "

Kacan cewar babu nisa tsakanin su Aisha da bakin titi hakan ya sa Aisha na fita ta
zo da mai Napep. Da taimakon Aisha da mahaifiyarta suka sa Fadila acikin Napep
d'in.

Wata k'aramar Asibiti da ke kusa da su suka kaita.

Suna zuwa ko aka fara ba Fadila duk wani taimako da ya dace.


Saida aka sama Fadila ruwa leda uku sannan ta fara dawowa hayyacinta. Likitar
kallan mahaifiyar Fadila ta yi ta ce "Mama, gaskiya indai kina son yarinyarki da
abun da ke cikinta to ku yi ma mijinta magana , tana buk'atar kulawa sosai idan ba
haka ba zaku iya rasa abun da ke cikinta, sannan ta rik'a rage ma kanta damuwa ,
dan yanayinta duk ya bayyana ha...." Maganar da Fadila ke yi ce ta sa likitar ta yi
shiru ,dukansu suka kai dubansu gareta.

Fadila cikin sanyi dan muryar tata ta yi k'asa sosai, ta ce " Mama, dan Allah ku
yafe min kubar fushi da ni akan abin da nima bansan yadda ake ba. Mama dan Allah ku
yadda dani Wallahi mama bansan ya akai nake da ciki ba, dan Allah ku yadda da n.."
Marin da mahaifiyar Fadila ta yi mata ne ya sa ta yi shiru .

Mahaifiyar Fadila ta d'aga hannu zata k'ara ma Fadila wani Marin ne likitar take
rik'e hannunta tana cewa " Ki yi hak'uri Hajiya k'addara ce , haka Allah ya
k'addara miki " Likitar ta fad'i maganar tana rik'e da hannun mahaifiyar Fadila dan
ta fahimci Fadila bata da aure.

Mahaifiyar Fadila ko cikin tsantsar takaici ta ce " Wallahi, indai kika kuskura
kika k'ara yi min irin wannan maganar zaki ga abun da zan miki , wato har yanzu
kina nufin ke ta kirkice kina da bakin kare kanki ko ? " Fadila dai ba magana sai
kuka

Likitar nasiha ta yi ma mahaifiyar Fadila sosai ta ce " Hajiya mai faruwa ta riga
ta faru saidai ki yi mata addu'ar Allah ya raba su Lafiya "

Mahaifiyar Fadila kasa jure zaman Asibitin ta yi ta koma gida, dan idan tana kallan
Fadila ji take kamar ta shak'eta ta mutu ta huta, hakan ya sa ta dawo gida tabar
Aisha. Kwanansu biyu Fadila ta warware baki d'aya.

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya , yanzu haka an yi arba'in d'in mahaifin


Fadila.Saidai ta b'angaran Fadila ta fara dangana da k'addarar ta ta farka ta
tsinci kanta acikinta. Yanzu abu d'aya ke damunta fushin da mahaifiyarta take yi da
ita dan ko gaisuwarta bata amsawa .Aisha ma sai taita yi mata magana ta yi banza da
ita.
BAYAN WATA UKU

Yanzu kimanin wata uku kenan da rasuwar mahaifin Fadila , kuma har yanzu Fadila na
gida bata koma aiki ba, haka 'yan wajan aikin nasu ma babu wanda ya k'ara
tuntub'arta ya ji ya jikinta, garama Jamilu yakan kirata su gaisa .

Yanzu rayuwa ta fara sauya ma su Fadila, dan komai nasu kusan ya k'are, yanzu haka
yau sun tashi basu da abin da za su ci.

Fadila yanzu cikinta watanshi hud'u kenan, saidai da yake ba mai girman ciki ba ce
in ka ganta ba lallene gane tana da ciki ba, sannan kuma dama yanzu kullum da hijab
take zama a jikinta.
Yanzu abu d'aya ke damun Fadila shi ne saurin jin yunwa gashi abun da za su ci yana
naiman gagararsu . Hakan ya sa Fadila ta yanke ma kanta shawarar komawa ta ci gaba
da aikinta .Fadila tashi ta yi ta je ta samu mahaifiyarta a d'aki zaune kan sallaya
tana lazimi , dan tun da mahaifin Fadila ya rasu ta maye gurbinshi,dan shi mutum ne
da kusan koda yaushe zaka ganshi da carbi a hannu yana lazimi.

Fadila cikin fargaba ta fara yi ma mahaifiyarta magana, dan ita kanta yanzu kusan
bata son abin da zai had'asu magana da mahaifiyar tata. Fadila cikin sanyi ta ce "
Mama, idan kin amince zuwa gobe ina so zan koma wajan aiki ? " Mahaifiyar Fadila
kallan Fadila ta yi tana tab'e baki ta ce " Abun da ake gudu har ake hanaki ada ya
riga ya faru , tom me ya rage ? , duk inda kika ga dama ki je ba aiki ba tashi ki
bani waje " Fadila tashi ta yi a sanyaye dama tasan haka zata faru.

Fadila d'aki ta koma tasha kukanta ta gaji ta ba kanta hak'uri.


Bayan Fadila ta gama kukan ne Aisha ta shigo d'akin ,Fadila da sauri ta ce " Aisha,
dan Allah ki tsaya mu yi magana " Aisha tsayawa ta yi ba tare da ta juyo ba ta ce
"Ina jinki " Aisha, dama aiki na ke son in kama gobe dan Allah ki yi ma mama magana
ko zata fahimce ni "

Aisha batare da ta tanka ma Fadila ba ta juya ta yi tafiyarta.


Fadila ganin yunwa zata kashesu dan yau kwana biyu kenan ba su yi girki ba sai 'yan
dabe-bare da suke yi, hakan ya sa yau ta shirya ta nufi d'akin mahaifiyarta.

Duk da bata amsa gaisuwarta haka Fadila ta gaidata ,amma bata amsa ba, Fadila ta ci
gaba da cewa " Mama, zani aiki? " Fadila ta fad'i maganar a tak'aice a hankali
saboda yunwar da take ji. Mahaifiyar Fadila bata tanka mata ba haka ta gaji da
tsugunno k'arshe ta tashi ta tafi dan bata da wata mafita wadda ta wuce hakan dan
yunwa nagaf da illatata.

Fadila na zuwa office d'in MD ta fara shiga dan gani take ma kamar zai dakatar da
ita , inda tun da suka rabu ma ko ya kirata ya ji ya jikinta.

MD da kallo ya bi Fadila ganin yadda ta rame ta yi bak'i , cikin tausayamata ya ce


" Ya jikin naki ? " Na ji sauk'i na dawo bakin aiki ne? " Kai MD ya jinjina ma
Fadila batare da ya tanka mata ba, sannan ya ce " Shi kenan , kima Jamilu magana "

Fadila ko yadda ta ga abokan aikin nata na kallanta tasan duk sun ji abin da ke
damunta. Haka dai ta daure batare da nuna ta damu da kallan da aike mata ba suka
gaggaisa, sannan ta nufi office d'insu.

Kasan cewar Fadila ta sanar da Jamilu dawowarta aiki ya sa bai yi mamakin zuwanta
ba, saidai ya yi ta binta da kallan mamakin ganin ramar da bak'in da ta yi.

Fadila bayan ta zauna haka ta kwashe kaf matsalar gidansu da halin da take da
mahaifiyarta ta sanar da Jamilu.

Jamilu sosai ya tausaya ma Fadila , kud'i ya bata ya ce ta je restaurant d'in kusa


da su ta ci abinci.

Abin da ya ba Fadila mamaki lokacin da ta tashi aiki MD ya aiko mata da dubu daya
(1000) kamar yadda ya sa bata ya ce ta hau Napep, sosai hakan ya ba Fadila mamaki.
Yanzu Fadila ta koma aiki, aikinta take kamar da , inda a hankaki-ahankali cikin
jikinta sai k'ara girma yake. Sannan yanzu rayuwar tasu da sauki tana yin amfani
da dubu d'ayan da MD ke bata suna yin cefane .

Saidai tsakaninta da mahaifiyarta har yanzu babu wani sauk'i. Dan har yanzu bata
amsa gaisuwarta kuma so da dama sai taita yi mata magana ta yi banza da ita.

Haka rayuwa ta yi ta tafiya har cikin Fadila ya tsufa , yanzu kam duk wanda ya san
ciki kallo d'aya zai yi mata ya gane tana da ciki, duk da ta kasance ba mai girman
ciki ba.

Rahama TV yanzu hankalin su gaba d'aya ya koma akan taron da za su yi na murnar


cikar gidan TV shekara goma da fara aiki. Sosai suke shirin taron wanda za su yi
Ranar Asabar kamar yadda suka tsara.

ADAMAWA STATE

Muhammad yanzu rayuwarshi ya ke lafiya lau ya cire duk wata damuwa a ranshi . Yau
Muhammad bayan ya dawo aiki ne yana zaune falon mahaifinshi suna fira, mahaifin
Mahammad ya ce " Mahammad, yakamata dai wannan Karan ace ka k'ok'arta ka je murnar
cikar shekara goma da Rahama TV za ta yi , kodan kasan cewarsa mallaki ga
mahaifiyarka, Allah sarki lokacin ta yi k'ok'ari sosai ganin gidan TV ya fara aiki
sai dai bai fara aiki ba har sai bayan ranta , dan idan ba zan manta ba sai ta ya
yi shekara kusan koma cir da bud'eshi amma ba'a fara amfani da shi ba sai bayan
kusan shekara koma, tun da kadawo karatu kullum nake maka magana akan kaje ka
ganshi amma kak'i "Muhammad kai ya jinnina ya ce " Daddy, in sha Allah wannan Karan
dai zan je, yaushe za'ai taron ? " This coming Saturday" Shi kenan zan yi k'ok'ari
inga na je" Tom zan yi magana da Murtala Isa shi ne shugaban gidan TV "
KADUNA GARIN GWAMNA

Yaune ya kama za ai taron Rahama TV , inda Fadila ta shirya ta tafi da wuri duk da
bata jin dad'in jikinta sosai , tun jiya take fama da ciwan mara haka dai ta daure
ta tafi.

Taro ya yi taro inda taron ya samu halarta manya mutane da dama , daga ciki hadda
Muhammad Sagir mai shadda da ya yi tattaki shima tun da ga Adamawa ya zo.

An yi taro angama inda sosai abun ya k'ayatar da Muhammad ,sai dai yadda ya ji ana
bada tarihin yadda mahaifiyarshi ta shiga ta fita dan ganin ta bud'e gidan TV , sai
dai Allah da ikonshi gidan TV bai fara aiki ba har sai bayan ranta, hakan ya sa
Muhammad ya k'udirci taimaka ma gidan TV ganin ya d'aukaka yafi da haka.

Bayan an gama taron ne aka gabatar da Muhammad amatsayin wanda zai ba ma'aikatan
gidan TV Frame na shaidar karramawa. Haka aka fara Kiran d'aya bayan d'aya ana basu
har aka zo kan Fadila, wadda ta tashi duk a d'arare dalilin cikinta da ya fito.

Muhammad cikin fara'arshi ya mik'ama Fadila Frame d'inta inda aka d'aukesu photo
dai dai zai mik'a mata.

Haka aka yi taro aka tashi, bayan taro ya tashi ne Muhammad ya yi ma MD magana akan
yana so ganin lungu da sak'o na gidan TV. MD Fadila ya Kira a waya ya ce ta samai a
office d'inshi, bayan ta zo ne ya ce " Fadila, ki zagaya da shi ko ina na gidan
nan " Fadila cikin daurewa da ciwan marar da take ji ta tafi.

Muhammad tashi ya yi ya bi Fadila , duk in da suka je Fadila za ta yi mai bayanin


wajan. Inda Muhammad ke jinjina kai kawai ba tare da ya tanka ba.
Fadila d'akin da suke gabatar da shirye-shiryensu ta kai Muhammad ta ce " Nan ne
muke gabatar duk wani shiri da muke yi " Muhammad kallan Fadila ya yi yana mamakin
yadda ba sai ya tambayeta ba take mai bayanin duk in da suka je kuma takan yi mai
gamsassan bayani da ba sai ya naimi k'arin bayani ba.

Muhammad kallan Fadila ya yi ya ce " Ke awana b'angaran kike ?" Fadila shiru ta
yi ,dan yanzu takan ji ma kunyar fad'in b'angaran da take aiki akai,haka dai ta
daure cikin sanyi ta ce " Ni ce shubatar Shirin DARAJAR 'YA MACE " Wonderful "
Muhammad ya ce , sannan ya ci gaba da cewa "Wata matsala ce kuke fuskanta ? Sannan
me ye kike ganin zai k'ara d'aga darajar gidan TV nan dan na yi sha'awar bada
gudinmuwata? " Fadila da mamaki ta d'aga kai tana kallan Muhammad , take kuma ta
kauda mamakinta dan shi d'in ya yi kama da wanda zai iya hakan"
Fadila magana zata yi ta kasa jin yadda mararta gaba d'aya ta murd'a , dama kuma
dauriya kawai take dan tun jiya take jin hakan. Fadila da sauri ta duk'e a wajan
tana mai dafe mararta tana cije baki.

Muhammad da mamaki ya kalleta ya na tambayarta " Lafiya ? "Fadila da kyar ta iya


bud'e baki ta ce " Cikina " Subhannallah baki da lafiya ne ? " Fadila zuwa yanzu ba
ta iya magana , durk'ushewa ta yi awajan ta rik'e marar katakam.

Muhammad juyawa ya yi da niyyar ya yi ma MD magana, sai dai kafin ya d'aga k'afar


Fadila tsabar azaba da ta ji ta rik'e mai k'afa d'aya katakam, tana jijjiya kai dan
na kud'ace gadan-gadan ta taho ma Fadila.

Muhammad rasa yadda zai yi ya yi yana son zuwa ya Kira MD amma Fadila ta rik'eshi
bada wasa ba. Muhammad Kiran MD ya yi awaya ya sanar da shi halin da Fadilar take.

MD da sauri ya nufo inda suke , yana zuwa ya kalli Muhammad ya ce " Da'alama na
k'uda take aihuwa zata yi " Haihuwa kuma ? Shi ne ta zo aiki kuma ? "

Jamilu da yaga lokacin da Fadila da Muhammad suka wuce yanzu kuma ga tahowar MD da
sauri tashi ya yi ya nufi inda suke dan shi gaba d'aya ya fara zargin MD akan cikin
Fadila .
Jamilu koda ya je ya ga halin da Fadila ta ke ciki cikin rud'ewa ya yi kanta.
Tsawar da MD ya yi masa ce ya sa ya fasa kamata d'in da ya yi niyya.

Muhammad kuma kallan MD ya yi ya ce " Ku kira mijinta mana ku sanar da shi halin da
take ciki ? " MD shiru ya yi baitanka ba, sai zuwa can ya ce " Da akwai wata
asibiti nan kusa bari in je in taho da d'aya daga cikin likitocin su dubata.

Muhammad da Jamilu nanan kan Fadila da ke ta cije-cije a wajan , kuma har yanzu
rik'e take da k'afar Muhammad.

Muhammad da mutum ne mai tausayi sosai kallan Jamilu ya yi ya ce " Ku kira mijinta
mana " Jamilu shiru ya yi dan bai san amsar da zai ba Muhammad ba, kuma hakanan ya
ji baya buk'ar sanar da shi Fadila bata da miji.

Muhammad sunan tsaye MD ya zo da likitoci biyu mata.

MD da ya fara rud'ewa da yadda ya ga Fadilar ya ce " Ku kamata mu tafi asibitin


mana " D'aya daga cikin likitocin ta ce " Nak'udarta ta riga ta kankama zata iya
✍🏻
haihuwa a mota muna tafiya sai dai mu bari ta haihu a nan

SANARWA : Ba zan yi posting weekend ba , sai ranar Monday za ku jini in sha Allah.

📚 FADEELAH 📚

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare
da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻
Na
Fadila Sani Bakori

SANARWA : Masu tambaya akan gyaran jiki akwai hanyoyi kala daban-daban da zan kawo
musu na gyaran jiki acikin wannan littafi mai suna FADEELAH.

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*


*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦250
2GB = ₦700. 1GB ₦500
3GB = ₦1050. 2GB ₦1000
4GB = ₦1400. 3GB ₦1500
5GB = ₦1750. 4GB ₦2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

Page 9

MD da ya fara rud'ewa da yadda ya ga Fadila ya ce , "Ku kamata mu tafi Asibiti


mana? " D'aya daga cikin likitocin ta ce " Nak'udarta ta riga ta kankama zata iya
haihuwa a mota muna tafiya sai dai mu bari ta haihu a nan " Tana fadin haka ta
kalli MD ta ce " Ku d'an bamu waje "
MD da Muhammad da Jamilu duk a tare suka fita.

Duk wani taimako da ya kamata sun ba Fadila anma bata haihu ba, hakan ya sa d'aya
daga ciki ta fito ta zo ta samu MD ta ce" Ina jin fa sai dai mu tafi da ita
Asibiti, saboda kan yaron bai gama yowa k'asa ba "

Muhammad da takaici ya cikasa ga haihuwa nan kusa amma tsabar rashin sanin aiki wai
sai sun je da ita Asibiti. Muhammad kallan MD ya yi ya ce " Ku sanar da mijinta
idan ya amince ni zan amshi haihuwarta " MD shiru ya yi yana kallan Jamilu , kamar
mai son tuna wani abu sannan ya ce " babu damuwa ai taimako zakai zaka iya dubata "

Muhammad kallan likitocin ya yi ya ce " Ku muje in gwada muku wani abu "

Tare da Muhammad suka koma wajan Fadilar.

Muhammad koda ya duba ya ga halin da Fadila ke ciki bai tab'a taba fita ya yi ya
ce ma MD " Bata da k'arfin da zata iya haihuwa da kanta sai dai ayi mata aiki
( theater) yanzu bari mu k'arasa Asibitin sai ka sanar da mai gidanta kafin nan "

Da taimakon Muhammad da na likitocin mata su ka sa Fadila a motar MD suka tafi.

Suna isa Asibitin aka shigar da Fadila theater room.

Muhammad suna kaita ya juya zai tafi MD ya kamo hannunshi da sauri ya ce " Kasan
cewar muna saurine ya sa na kawota Asibitin nan , gaskiya daga gani kamar ma basu
da kwararrun likitoci da kayan aiki , idan babu damuwa ka dubata mana, zan yi
magana da d'aya daga cikin likitocin Asibitin"

Muhammad da gaba d'aya shima ya raina Asibitin dan daga gani ma kamar basu da wasu
kayan aiki , hakan ya sa ya amince saboda hakan nan sai ya ji tausayin mai haihuwar
ya ke.

Muhammad da kanshi ya shiga theater room nasu . Cikin kwarewarshi ya yi ma Fadila


aiki ya zaro mata baby boy d'inta.

Sannan ita kuma ya yi mata al'lurai masu k'ara kuzarin jiki , sannan aka maidata
d'akin hutu.

Lokacin da Muhammad ya fito da yaron da sunan ya ba MD shi sai ya ga baya nan sai
Jamilu kad'ai . Muhammad da alamun mamaki ya kalli Jamilu ya ce " Har yanzu wani
nata bai zo ba ? "

Jamilu ganin kokarin da Muhammad d'in ya yi akan Fadila , hakan ya sa ya ce " Ranka
shi dad'e, bata da aure shi ne dalilin da kaga har yanzu babu wanda ya zo wajanta
" Muhammad da mamaki ya kalli Jamilu jin furicinsa amma sai ya share ya ce, " Shi
kenan, ni zan tafi " Jamilu da sauri ya ce " Ranka shi dad'e , tabbas Fadila zata
so yi maka godiya, idan babu damuwa ka tsaya ta farka ko ka ban numberka in bata
dan ta isar da sakon godiyarta gareka " Muhammad kai ya girgiza ya ce " Karka damu
na yi mata dan Allah bana buk'atar godiyarta " Muhammad na fad'in haka ya juya zai
tafi .

Jamilu da sauri ya kuma cewa " Ranka shi dade, nasan Fadila tana daga cikin
halittun Allah musu godiya da son saka ma duk wanda ya taimaketa koda ko kad'anne
tom bare kuma kai , tabbas nasan zata shi ga damuwa idan har akace ta rasa hanyar
da zata isar da sak'on godiyarta a wajanka " Muhammad kai ya jinjina sannan ya ce "
MD na da number ta" Ya na sanar da shi haka ya tafi.

Jamilu ko ganin Fadila zata farka ba kowa kusa da ita hakan ya sa ya yi tunanin
zuwa ya sanar a gidansu.
Mahaifiyar Fadila suna zaune da Aisha suna fira da Jamilu ya yi sallama ya shigo.
Bayan sun gaisa ne Jamilu ya ce " Mama , Fadila ce ta haihu bayan an yi mata
theater an ciro yaron , yanzu haka tana nan Asibitin sawa , shi ne na zo in sanar
ko Aisha ta je gudin karta farka ba kowa kusa da ita " Mahaifiyar Fadila wadda tun
da Jamilu ya fara bayani kirjinta ke dukan uku-uku . Hannuta ta d'aga sama tana
godiya ga Allah tana cewa a cikin rawar murya mai son fidda kuka " Alhamdulillah !
Allah na gode maka da ka amsa rok'ona kasa Fadila bata zubar min da wannan bak'in
jinin anan ba " Mahaifiyar Fadila mai da kallanta ga Jamilu ta yi ta ce " Allah ya
raya abun da ta haifa ya kuma bata lafiya , amma babu wanda zai je acikinmu "
Mahaifiyar Fadila ta fad'i maganar tana goge hawayan da ke zubar mata.

Jamilu shiru ya yi dan ya rasa abun cewa ,sai zuwa can ya ce " Mama , dan Allah ki
y....." ? Mahaifiyar Fadila d'aga ma Jamilu hannu ta yi ta ce " Jamilu , sai an
jima ka sanar da ni haihu tom na yi mata addu'a da ita da abun da ta haifa , tom
sai me ye kuma ya rage ? " Ta fad'i maganar da alamun ranta a b'ace yake.

Jamilu tashi ya yi bai kuma cewa komai ba.

Har ya tafi mahaifiyar Fadila ta ce " Ka sanar da ita katta dawo min nan bana
buk'atar kara zama da ita "

Jamilu ganin idon mahaifiyar Fadila ya rufe ya sa bai k'ara cewa komai ba ya tashi
ya tafi.

Aisha k'anwar Fadila goge hawayanta ta yi ta ce " Mama , ki yi hak'uri ki bar Aunty
Fadila ta dawo nan ta zauna , idan kin koreta ina zata ? "

Mahaifiyar Fadila cikin kuka ta ce " Aisha , zuciyata ba zata iya jurewa ba inga
Fadila da yaron shege tana raino , ina ba zan iya daure haka ba , ku yi hak'uri
karku sake rok'ona wata alfarma akan Fadila ta zauna , idan kuma kun matsa sai dai
ni in bar muku gidan "

Aisha shiru ta yi bata k'ara cewa komai ba.

B'angaran Fadila ko lokacin da ta farka ba kowa kusa da ita . D'akin ta bi da


kallo, daga gani dai Asibiti ne hakan ya sa ta shafa cikinta da sauri sai jin shi
ta yi wayan ba komai. Fadila cikin jin dad'i ta ce " Alhamdulillah . Allah kai ne
abun godiya Allah na gode maka " Fadila ta fad'i maganar tana goge hawayan da ke
zubar mata dan ita ta yi tunanin cikin da ke jikinta ya zube ne .
Fadila na a wannan halin ne d'aya daga cikin likitocin da suka dubata ta shigo
ringume da jaririn yana kuka.

Fadila d'aga kai ta yi tana kallan Jaririn da ke a cikin tsunma a hannun likitar.
Fadila cikin rud'ewa da ganin jaririn ta ce " Jaririn waye ? " Murmushi likitar ta
yi ta ce " Jaririn da kika haifa kenan, amsarshi ki shayar da shi" Ta fad'i maganar
tana d'ora ma Fadila jaririn akan k'afarta.

Fadila duk'ar da kai ta yi tana kuka sosai ta kasa magana. Likitar ko dama ta riga
ta gama fahimtar Fadila babu aure ta haihu , hakan ya sa ta ce " Kukan me kuma kike
yi bacin mai faruwa ta faru? Yanzu saidai ki rungumi yaronki gaba kuma kin kiyaye,
dama abun da ake hangar muku kenan ake muku fad'a kuke ganin kamar takura muku ake
yi "

Suna cikin haka ne Jamilu ya shigo . Jamilu zama ya yana yi ma Fadila ya jiki .

Fadila bata samu damar amsa mai ba saboda kukan da ta ke yi.

Haka Fadila ta yi ta kuka Wanda Jamiku ya kasa ce mata komai yana zaune yana
sauraranta .

Jamilu d'akko jaririn ya yi jin yana kuka . Babu kalar jijjigar da bai yi ma
jaririn ba amma ya dage sai kuka ya ke gaba d'aya ya cika Asibitin . Inda kukan
jaririn ke k'ara tun jira Fadila tana k'ara nata kukan itama .

Jamilu gyaran murya ya yi sannan ya ce " Fadila , yanzu fa maganar kuka ta riga ta
k'are , kukan nan babu wani magani da zai miki , ni shawarar da zan baki ki yi
hak'uri ki bar sa ma kanki damuwa saboda tsoran wani ciwo.." Jamilu shiru ya yi
saboda sugowar likita, likitar kallan Fadila ta yi ta ce " Bi ki ji baby na kuka ba
? Ki d'auke shi ki shayar da shi mana " Fadila ci gaba da kukanta ta yi ta kasa
d'aukar jaririn.
Ana cikin haka ne MD ya shigo da flask babba a hannun shi da kuma ledar kayan tea.

MD da kan shi ya had'a ma Fadila tea ya mik'a mata. Kacan cewar Fadila na jin yunwa
bata musa ba ta amsa ta sha.

MD d'aukar jaririn ya yi ya yi masa hud'u ba sannan ya kalli Jamilu ya ce " Nasa


ma baby boy d'inmu Ahmad " Allah ya raya shi" Jamilu ya ce.

Fadila na gama shan tea d'in MD ya kalleta ya ce " Mu je in kaiki gida " Jamilu
Kallan MD ya yi ya ce " MD , idan babu damuwa akwai maganar da nake son mu yi " MD
tashi ya yi suka fita.

Bacin sun fita ne Jamilu ya kalli MD ya ce " MD , Fadila fa ba zaiyuwu ta koma gida
da zama ba , saboda a halin yanzu mahaifiyarta tana cike da jin zugun zafin
haihuwarta , gani nake idan zaiyuwu ka sama mata wani wajan ta zauna kafin nan da
ta sakko "

Shiru MD ya yi baitanka ba sannan ya koma d'akin da Fadila ta ke ya ce ta shirya


yanzu zai zo "

Shiru-shiru MD bai dawo ba , Jamilu kasa jurewa ya yi ya tafi gida ya ce mata yana
zuwa.

D'aya daga cikin likitocin ko jin kukan jaririn ya yi yawa ya sa suka tursasa
Fadila ta shayar da yaron.
MD ba shi ya dawo ba sai 10:40 PM dan Fadila ma har ta cire ran dawowar shi.

D'aya daga cikin likitocin ce ta rungume jaririn ta rakasu har motar MD sanna ta
juy.

Fadila da mamaki ta bi MD da kallo ganin ya d'auke wata hanya daban maimakon hanyar
gidansu. Hakan ya sa ta ce " MD ina zaka kai ni kuma? " MD bai tankama Fadila ba.

Daidai wani babban gida MD ya yi parking , Fadila dai kallan shi kawai take batace
komai ba . MD kuma fita ya yi daga cikin motar ya bud'e get d'in gidan sannan ya
dawo ya shiga da motar.

MD kallan Fadila ya yi ya ce " A nan gidan za ki ci gaba da zama har zuwa lokacin
da Mama zata yi miki afuwa ki koma ku ci gaba da zama tare "

Fadila kallan MD ta yi wanda ke rungume da jaririn ta ce " Mama, ta hana in ci gaba


da zama da ita ko ? " Ki yi hak'uri komai zai wuce watarana m...." Barka da zuwa
ranka shi dad'e, har kun iso ? " Cewar wata karfaffar dattijuwar mata da ta fito
daga cikin gidan ta katse maganar da MD ke yi.

MD jaririn hannun shi ya mik'a mata sannan ya ce " Ga mejegon nan ki bata duk
watakulawa da ta kamata " In sha Allah , ranka shi dad'e "

MD mik'a matar nan jaririn ya yi ya kalli Fadila ya ce " Ni zan tafi Allah ya
sawake " Fadila kai kawai ta iya d'ama mai ya juya ya tafi , ita kuma ta bi bayan
matar nan suka shiga cikin gidan.
Three bedroom plate , ma sha Allah gidan ya yi kyau. Fadila zama za ta yi
dattijuwar matar nan ta ce " A'a jikata, kar ki zauna mu je ki gasa jikinki " Matar
nan goya jaririn ta yi sannan suka shiga bayin ta gaggasa Fadila suna fitowa ta
kai Fadila har d'akin da yake mazaunin nata .

Fadila da mamaki ta bi dak'in da kallo dan komai sabo ne na d'akin , bud'e manyan
jakunkunan da ta gani ta yi , d'aya cike take da kayan sawa kamar nata , d'aya kuma
da kuma kayan jariri ne cike . Fadila na nan tsaye tana mamakin kayan, matar nan ta
shigo da jug cike da kukun gyad'a ta kawo ma Fadila ta ce " Ga kunun gyad'a nan na
yi miki ance sai zuwa gobe za'a fara baki abinci shima ba mai k'arfi ba in da an yi
miki theater ne"

Fadila cikin sanyi ta ce " Tom, na gode "

Matar nan fita ta yi shima jaririn ta wankoshi tas kamar dai yadda ake ma jarirai
sannan ta yi mai gashin cibi ta kawo ma Fadila shi ta fita.

Fadila tagumi ta yi ta tasa yaron gaba tana kallo tana kuka . Sai da ta yi kukanta
ta gaji sannan ta kwantar da shi ta zuba kunun gyadan tasha ita ma ta kwanta , take
barci b'arawo ya saceta.

Cikin dare jaririn ya tashi yana ta kuka amma kasancewar barci mai nauyi ya d'auki
Fadila bata ji ba, sai Baba Lami ce ta ji ta shigo d'akin Fadilar .
Bubbugata ta yi ta tashi ta mik'a mata yaron sannan ta fita.

Fadila aduk lokacin da zata kallin yaron sai ta ji hawaye na zubar mata . Goge
hawayan ta yi tana kallan yaron ta ce " Ina tausayinka sosai araina, ina tausaya
maka yadda zaka tashi ka rayu babu uba , ina ji maka gorin da zaka rik'a fuskanta
wajan jama'a , saidai ba zan gajiya ba wajan rok'a maka Allah ya nisantamu ni da
kai ya kaimu duniyar da za mu rayu babu gorin zama'a acikinta " Fadila ta idasa
maganar tana kuka sannan ta kwantar da yaron ta kwanta gefan shi , har aka kira
Sallah barci ya gagari idon Fadila.
Washegari Baba Lami da wuri ta tashi ta yi ma su abin Kari , ta taimaka ma Fadila
ta yi wanka ta wanke jaririn .

Fadila na zaune tana shan kunun gyadan da Baba Lami ta dama mata Kiran Jamilu ya
shigo wayarta , bayan sun gaisa ne Fadila ta ce " Jamilu, MD ya taimakeni alokacin
da nake tsananin naiman taimako Allah ya saka masa da alkairi " Jamilu "Ameen "ya
ce ya k'ara da cewa " Ba MD kad'ai za ki gode mawa ba har da wanda ya yi miki
theater , Fadila, Muhammad Sagir mai shadda kamar sunansa kenan ? Wanda ya halarci
taron anniversary namu shi ya amshi haihuwarki , bawan Allah nan ya yi k'okari
sosai haka muka tafi muka barshi , gaskiya ya yi miki k'ok'ari sosai " Fadila sai
yanzu ta tuna da shi ta ce " Allah sarki har ya tafi ko ? " Eh , ya wuce " Jamilu
ya bata amsa. Fadila cikin sanyi ta ce " Amma naso in yi masa godiya Allah ya saka
masa da alkairi " Nima na rokeshi akan ko numbersa ya baki ki yi masa godiya amma
ya k'i, da na dameshi ya ce ki amsa wajan MD "
Fadila ta ce " Aiko zan amsa gaskiya in yi masa godiya "

Bayan Fadila sun gama waya da Jamilu MD ta Kira ta rok'eshi ya bata number Wanda
ya yi mata theater zata yi mai godiya .

Take MD ya tura mata number Muhammad.

Number na shigowa Fadila ta Kira shi har kira uku bai dauka ba, hakan ya sa ta tura
✍🏻
mai text message kamar hak....

📚 FADEELAH 📚
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare
da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻

Na
Fadila Sani Bakori

SANARWA : Masu tambaya akan gyaran jiki akwai hanyoyi kala daban-daban da zan kawo
musu na gyaran jiki a cikin wannan littafi mai suna FADEELAH .

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*


*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦250
2GB = ₦700. 1GB ₦500
3GB = ₦1050. 2GB ₦1000
4GB = ₦1400. 3GB ₦1500
5GB = ₦1750. 4GB ₦2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

Page 10
Number Muhammad na shigowa Fadila ta Kira shi har kira uku bai d'aga ba, hakan ya
sa Fadila ta mai text massage kamar haka : Assalamu alaikum. Da fatan ka je gida
lafiya ? Na gode da sadaukar da lokacinka da ka yi agareni ka bani taimako har na
haihu . Na gode sosai Allah ya sa ka maka sa mafificin alkairi "

B'angaran Muhammad ko lokacin da Fadila ta kira shi baya kusa , yana zuwa sakon
text massage d'in ta na shigowa. Muhammad koda ya duba murmushi ya yi a zuciyarshi
ya ce " Allah sarki tabbas ta cika mara manta halacci inda ga shi har ta amshi
number ta ta kirani ta yi min godiya " Kasan cewar Muhammad mutum ne mai saukin kai
hakan ya sa ya yi replying d'inta da " Ameen , ya jikin naki ? "

Fadila sosai ta kara ya bawa da kirkinshi da rashin kirman kanshi hakan ya sa cikin
jin dadi ta mai da mai amsa da " Alhamdulillah. Na ji sauki "

B'angaran gidan su Fadila


Aisha sosai ta shiga damuwar rashin dawowar Fadila da bata yi gida ba.Hakan ya sa
Aisha yau ta shirya da niyyar zuwa ta nemo in da Fadila take . Aisha koda ta gama
shiryawa b'oye ma mahaifiyarsu ta yi inda zata, ta fita da sunan tafiya Islamiya.

Aisha bayan ta fito Kiran Jamilu ta yi a wayar mahaifiyarta da ta fito da ita bata
sani ba. Jamilu na d'agawa bayan sun gaisa ne Aisha ta ce "Jamilu, zuciyata ta kasa
jurewa da rashin ganin Aunty Fadila , dan Allah tana ina ina son ganinta ? " Jamilu
shiru ya yi , sannan ya ce " Aisha, Wallahi nima takamaimai bansan inda Fadila take
ba, ki kira numberta mana "A'a bana son ta san da zuwan nawa na fi son kawai ta
ganni" Cewar Aisha.

Jamilu shiru ya yi sannan ya ce " Bari in turo miki number MD sai ki tambayeshi "
Aisha ta ce "Ka tambayar min shi mana? " A'a Aisha ,da alama MD baya son in je in
da Fadila take dan haka ki kirashi da kanki ki tambayeshi "

Aisha katse Kiran ta yi ta kira MD , bayan sun gaisa ne take sanar da shi tana son
zata je wajan Fadila ne.
Shiru MD ya yi sannan ya ce " Shi kenan ki samu keke-napep sai ki had'ani da shi in
ba shi Address d'in gidan "

Aisha mai Napep ta samu ta had'a shi da MD ya sanar da shi unguwar da zai kaita da
number gidan .

Mai Napep d'in na aje Aisha ta fara nocking get d'in . Aisha na nan tsaye Baba Lami
ta zo ta bud'e kasan cewar MD ya sanar da ita zuwan Aishar.

Baba Lami cikin fara'a ta ce " Sannu da zuwa , mu shiga tana ciki "

Aisha bin bayan Baba Lami ta yi har cikin d'an madai-daicin falonsu.

D'akin da Fadila take Baba Lami ta nuna ma Aisha ta ce " Ki shiga tana can "

Aisha da sallama ta shiga d'akin.

Fadila da ke zaune ta yi tagumi ta yi shiru ga yaron kwance kan katifar kusa da


ita. Fadila da sauri ta kai dubanta ga k'ofar d'akin jin muryar Aisha.

Fadila tashi ta yi da sauri ta nufi wajan Aisha da niyyar rungumeta , sai dai da
sauri ta tsuk'unna dan ta fama aikin da akai mata a ciki. Aisha da sauri ta k'arasa
wajan Fadila ganin ta tsugunne tana dafe saman mararta .

Aisha cikin sanyi ta ce " Sannu ya jikin naki ? " Fadila ahankali ta matsa ta koma
kan katifar ta zauna tana kallan Aisha, magana take son yi mata amma sakamakon
kukan da ya zo mata ta kasa.
Aisha ko cikin sanyi ta ce " Aunty Fadila , sauri nake dan Mama bata san da zuwana
ba , ki yi hak'uri ki bar kukan mu yi maganar da ta kawo ni " Fadila goge hawayan
ta yi tana kallan Aisha alamun ina jinki.

Aisha kamar ba zata yi magana ba , sannan ta tashi ta d'akko jaririn da ke kwance


kan makekiyar katifar d'akin irin gado huta d'in nan.

Aisha rungume jaririn ta yi tana kallo wanda ya sha tsadaddun kayan sanyinsa .Sosai
Aisha ta yaba da kyawun yaron a zuciyarta .

Aisha kallan Fadila ta yi cikin sanyi ta ce "Aunty Fadila , wa ye mahaifin yaron


nan ? " Fadila kallan Aisha ta yi da raunannun idanunta da yanzu ba su da wuyar
fidda ruwa ta ce " Aisha, biki yadda dani ba ko ? " Aisha cikin alamun fad'a da
kuma gajiya da rainun wayan da Auntyn tata ke yi musu ta ce " Aunty Fadila , me
kike so ki ce min ne ? Haba Aunty Fadila, ki yi hak'uri ki bar yaudarar zuciyoyinmu
haka nan mana, haihuwa fa kika yi ! Amma kike tambayata ban yadda da ke ba ? "
Aisha ta fad'i maganar kamar ta rufe Auntyn tata da duka. Sannan ta ci gaba da cewa
" Aunty Fadila , dan Allah ki bar yaudarar kanki damu kuma ki sanar damu mahaifin
yaron nan ? "

Fadila kallan Aisha ta yi tana tashi da kyar dan ta fama ciwan ta inda aka yi mata
theater . Fadila ta ce " Aisha , ina zuwa dan Allah "

Fadila toilet ta shiga ta yi alwallah ta fito, Aisha dai duk tana kallanta . Fita
ta yi ta je d'akin Baba Lami sai gata ta dawo da Al'Qur'ani a hannunta .

Fadila kallan Aisha ta yi sannan ta ce " Aisha, zan miki rantsuwa da Qur'anin nan
ba dan komai ba sai don bana son kina had'ani da abin da ban tab'a kusanta ba, na
rantse da Allah da wanna Al'qur'anin idan har na tab'a kusantar zina Allah ya sa
wannan al'wur'anin ya cine ,Allah ya nisanta ni da duk wasu rahamomin sa idan
ha.... " Aisha da sauri ta rufe bakin Fadila tana kuka ta ce " Kin aika kuskure
mafi muni Aunty Fadila, koda gaskiyarka baka rantsuwa da al'qur'ani, tabbas na
yadda dake Auntyna ,hakan na nuni da cewa kenan Fyad'e akai miki ? " Fadila tana
kuka ta ce " Ban sani ba Aisha , ni dai abu d'aya na sani ban tab'a aikata zina ba
" Aisha kai ta jinjina, sannan ta ce " Aunty Fadila, idan haka ne ya tabbata
jaririn nan MD ne ubansa , dan ni Wallahi shi nake kyautata zargina akan shi "
Fadila shiru ta yi dan ita kanta lokuta da dama tana zargin MD d'in , saidai in ta
tino ko sau d'aya maganar banza bata tab'a shiga tsakaninsu ba sai ta kauda
tunaninta .

Aisha kallan Fadila ta yi da ta tsunduma duniyar tunani ta ce " Ki k'ara nazari


sosai ki tuna ki yi tunani ki tuna abubuwan da suka faru a baya tsakaninki da
shi ?, Ki yi dogon tunanin Aunty Fadila, na san za ki tuna " Fadila kai ta
jinjina ta ce " Shi kenan Aisha zan yi"

Aisha kallan Fadila ta yi ta ce " Zan tafi " Fadila cikin sanyi ta ce " Aisha, dan
Allah ki yi ma Mama magana indawo gida in zauna tare daku bana jin dadin zama nan
da nake yi " Aisha kallan Fadila ta yi ta ce " Tom , ki yi tunanin abin da na ce
miki ni na wuce " Aisha na fad'in haka ta juya ta tafi.

Aisha ko da ta koma gida bata sanar da mahaifiyarta ta je wajan Fadila ba.

BAYAN WATA UKU

Yanzu Fadila ta yi arba'in , inda Baba Lami ma tuni ta tafi tunda Fadila ta yi
arba'in. Yanzu ya zamana Fadila ita kad'ai ce a gidan .

MD ko tunda Fadila ta zo gidan sau biyu ya tab'a zuwa shima duk abu ya kawo musu,
ko d'akin Fadila bai shiga ba.

Yanzu Fadila ta gaji da zaman gidan dan kusan wata biyu kenan ita kad'aice a gidan
sai yaronta da ya yi girma sosai tubarkallah .
Fadila so take ta koma gidansu da zama amma tana tsoran mahaifiyarta, haka dai ta
k'udiri aniyar komawa dan tana ganin hakan ya fi mata mutunci . Ta kira MD ta sanar
da shi k'udirinta amma ya ce ta jira tukun.

Yau sati d'aya kenan da Fadila suka yi magana da MD zai zo amma har yanzu bai zo ba
. Fadila na zaune ta yi ma Ahmad wanka ta kwantar da shi saboda ya yi barci, ta ji
shigowar MD bakin shi dauke da Sallama .

Fadila kai ta d'aga tana kallan MD sannan cikin jin dad'in zuwan MD d'in dan yau ta
k'uduri barin zaman gidan ta ce " Barka da zuwa " MD kai ya jinjina ma Fadila
sannan ya ce " Kin kirani akan zaki koma gida ? Kina ganin babu matsala ?, Mama ta
hak'ura ne ? " Zan gwada in gani ne " Kai MD ya jinjina nan ma , sannan ya mik'a
mata hollondia Yoghurt d'in da ya zo da shi ya ce " Ga shi ki sha wannan sai mu
wuce " Fadila amsa ta yi ta sha dama yau ta kasa yin girki tsabar tasa ranta a
tafiya gida .

Fadila na gama shan hollondia d'in take ganinta ya fara d'aukewa ta fara ganin
duhu-duhu . Fadila cikin rud'ewa da yadda ta ji take ta sauya ga ganinta ya d'auke
dishi-dishi take gani ta ce " MD, ba fa na gani duhu-duhu nake gani ? " Fadila ta
fad'i maganar a rud'e

MD baitanka ma Fadila ba.

Fadila tashi ta yi ta fara laliban hanya sai ji ta yi an rungomata baki d'aya,


daga nan jinta da ganinta ya d'auke bata k'ara sanin abin da ake ba.

ADAMAWA STATE
Yau ya kama Weekend Muhammad na gida, dama shi an fi samun shi a falon Hajiya
Baturiya in dai yana gida. Muhammad zaune ya ke suna fira da Hajiya Baturiya Alhaji
Sagir ya shigo falon wanda dawowarshi kenan daga maiduguri. Zama ya yi yana cewa "
Tom , Alhamdulillahi. Yanzu dai muna sa ran komai ya kusa zuwa k'arshe ko ince ya
zo k'arshe , Muhammad, wannan tafiyar tawa da na yi baki d'ayanta taka ce, wato
wani abokina ne mu ka yi magana da shi akan mutuwar matanka, shi ne yake sanar da
ni wai yawanci idan ana samun irin haka kuma har mun yi bincike babu wani
information da muka samu to shairin iska ne , ya ce yawanci Al'jana ce ke aurar
mutum haka ke faruwa, daga ya yi aure ta kashe matar , dan kamar yadda ya sanar da
ni yarinyar abokinshi haka ta faru da ita , itama duk wanda ya aureta washegari za
a farka a ga gawarshi, intakaice muku zance yanzu haka ya kaini har wajan shehin
malamin da ya yi ma 'yarinyar addu'a yanzu haka ta yi aure har ta haifafa ma , tom
sai dai malamin ya mutu amma akwai yaronshi babba wanda shi ya gadai , dan baka ga
mutanan da ke zuwa wajan shi d'aukar karatu ba, Muhammad , yanzu haka a maganar da
nake maka an sauke al'qur'ani har so uku , kuma gashi nan an rubuce shi ya ce a
baka kasha , sannan duk gidan da zaka zauna a tabbatar an sauke al'qur'ani a
gidan . Kai in tak'aice muku gaba d'aya yanzu haka shi wannan abokin nawa da nace
muku ya kaini inda aka yi addu'ar nan yanzu haka ya ba Muhammad auran 'yarsa
Kadija, dan haka duk lokacin da ka samu lokaci cikin Week din nan ka je ka ganta "

Muhammad da gaba d'aya yanzu babu maganar aure a gabansa sai be ji dad'in hakan
ba , amma sai ya boye ma nahaifinsa ya ce " Daddy, duk da zuciyata har yanzu cikin
fargabar abun da ya faru nake ba zan k'i na'am da duk abin da kuka yanke akaina
ba , a koda yaushe uwarninku kawai nake jira , dan haka ba sai na ganta ba na
aminta " Muhammad ya fad'i haka dan faranta ran mahaifinshi kamar yadda yaga shi ma
akoda yaushe yana k'okarin ganin nashi farin cikin .

Alhaji Sagir kallan Hajiya Baturiya ya yi ya ce " Mommyn Muhammad , biki ce komai
ba?" Hajiya Baturiya murmushi ta yi ta ce " Indai Muhammad ya amince nima a shirye
nake da amsa tayin " Alhaji Sagir murmushi ya yi ya ce " Tom , alhamdulillah ,
yanzu zan samu mahaifin yarinyar mu tsaida magana inda ka yi na'am. Saidai kamar
yadda nace maka ka shirya ka je ku ga juna , dan muna son yi abun cikin lokaci "

Bayan kwana biyu da maganar Muhammad ya shirya inda Jibirin d'an'uwansa ya yi masa
rakiya suka je suka ga Kadija . Kadija ba wani yi ma Muhammad ta yi ba amma
kasancewar ita d'in zab'in mahaifinshi ce sai ya hak'ura .

B'angaran Kadija ko take ta amince saboda Muhammad babu macan da zata gan shi ta
k'i shi ,dan ya ji komai kota ina mutum ne .
Haka babu b'ata lokaci aka fara shirye-shiryen biki.

Ana gobe biki Malamin nan da aka had'a Alhaji Sagir da shi suka kwana karatun
al'qur'ani a gidan da za a kai Kadija shi da d'alibanshi.

Washegari aka d'aura auran Muhammad da kadija.

Usman da sauran abokan Muhammad su suka kai amarya da k'awayanta har gidanta ,
wanda ya kasan ce shima sabo ne .

Bayan an akai amarya ba jimawa Muhammad bai tafi ba , Usman jin Muhammad shiru-
shiru bai zo ba Alhaji Sagir ya Kira ya sanar da shi suna can suna jiran Muhammad
ya zo kafin su wuce.

Alhaji Sagir d'akin Muhammad ya shiga zaune ya iske Muhammad da photon Hafsat yana
kallo yana kuka. Alhaji Sagir fusge photon ya yi ya ce " Muhammad har yanzu ka
kasa yadda wanda yafi ka son Hafsat ne ya d'auke abarshi , idan har ba kana son
samun damuwa bane ko kasa ma kanka ka tashi ga su Usman can suna jiranka sai ka je
su tafi " Muhammad goge hawan idonshi ya yi ya ce " Daddy, bana d'akko photon
Hafsat ba dan in sa ma kaina damuwa na yi haka ne dan innuna ma Hafsat har yanzu
tana raina ban manta da ita ba kuma ba zan tab'a mantawa da ita ba har ranar da
numfashina zai bar gangar jikina " Alhaji Sagir goge hawayan Muhammad ya yi ya ce "
Addu'a zaka yawaita yi mata ta haka ne kawai yanzu zaka nuna soyayyarka a gareta ,
jeka su Usman na jiranka "

KADUNA GARIN GWAMNA

Fadila tun safe ba ita ta farka ba sai a azahar


Fadila kwance ta ganta kan katifar d'akinta, jin jikinta take yi ya yi sanyi sosai
kamar dai irin wanda ya tashi jinya .
Shiru ta yi tana tunani take duk abin da ya faru da ita ya dawo mata na zuwan MD
gidan da kuma hollondia yoghurt d'in da ya bata ta sha daga nan ganinta ya d'aushe,
shi ne fa bata sake sanin abun da take ba sai yanzu da ta farka ta ganka kwance.

Fadila da sauri ta tashi tana bin sassan jikinta da kallo, tashi ta yi da sauri
tana duba kanta saidai ita bata ga wata alama ba a jikinta wanda zata shaida ko MD
ya kusanceta , saidai tana jin gaba d'aya jikinta babu dad'i. Da sauri Fadila ta
kai duba ga Ahmad amma bata gan shi ba.

Fadila tashi ta yi da sauri ta nufi falon nan ma babu Ahmad. D'akunan ta fara
diddubawa nan ma babu shi . Ji ta yi hankalinta ya tashi sosai dan take jikinta ya
fara rawa .

Fadila Kiran MD ta yi a waya sai jin wayarshi ta yi a kashe. Take ta rud'e


hankalinta ya tashi , dan tunaninta ya bata MD ya bata abun da zai b'atar mata da
hankali ne dan ya gudu mata da Ahmad , hakan ya sa Fadila jikinta na rawa ta d'auki
✍🏻
hijab d'inta ta fit.

Ku bar gaggawa za ku fahimta, ku dai ku biyoni a hankali , ku bar sani ina gudu kar
in ji ciwo mana 😰

📚 FADEELAH 📚
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare
da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻

Na
Fadila Sani Bakori.
SANARWA : Masu tambaya akan gyaran jiki akwai hanyoyi kala daban- daban da zan kawo
na gyaran jiki acin wannan littafi mai suna FADEELAH .

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*


*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦250
2GB = ₦700. 1GB ₦500
3GB = ₦1050. 2GB ₦1000
4GB = ₦1400. 3GB ₦1500
5GB = ₦1750. 4GB ₦2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

Page 11

Fadila Kiran MD ta yi a waya amma wayarshi akashe, take ta rud'e hankalinta ya


tashi dan tunaninta ya bata MD ya bata abun da zai b'atar mata da hankali ne dan ya
gudu mata da Ahmad, hakan ya sa Fadila jikinta ko ina ya kama rawa , hijab dinta ta
d'auka ta fita. Fadila da sauri - Sauri take tafiya ahaka ta samu keke-Napep ta
hau. Fadila na cikin Napep din tana kuma Kiran number MD amma akashe.
Fadila ak'ofar gidansu tasa mai napep din ya tsaya. Tsabar a rud'e take kai tsaye
ta shiga cikin gidansu ta bar mai napep d'in nan tsaye bata bashi kudi ba, mai
napep din ko jinta shiru kuma ganin hankalinta kamar a tashe ya ke ya sa ya juya
ya tafi.

Fadila a d'akinsu ta iske mahaifiyarta da Aisha da sauran k'annanta suna zaune


jigun - jigun kamar masu zaman makoki.

Mahaifiyar Fadila da sauran k'annanta da dukkansu da kallo suka bi Fadila. Fadila


ko koda taga bata ga Ahmad a gidan ba tunaninta ya bata tabbas MD ya gudu da Ahmad,
hakan ya sa Fadila ta d'ad'e da kuka .

Aisha da sauri ta nufi inda Fadila take tana tambayarta lafiya , inda mahaifiyarsu
ta bi ta da ido .

Aisha cikin sanyi jin Fadila bata tanka mata ba kuma ta ci gaba da kuka ta kuma
cewa " Aunty Fadila , lafiya ? Ina yaron fa ? " Sai sannan Fadila ta bud'e baki ta
ce cikin kuka " MD ya gudu da shi " Aisha a zuciyarta ta ce " Alhamdulillah " Amma
a fili sai cewa ta yi " Lafiya ya gudu da shi ? " Nima ban sani ba " Fadila ta bata
amsa.

Suna a haka ne Kira ya shigo wayar Fadila , koda ta duba ta ga number MD da sauri
ta d'aga kiran .

MD sanar da Fadila ya yi yana k'ofar gidansu .

Fadila fita ta yi da sauri. MD na ganinta ya fito cikin motar rungume da Ahmad a


hannun shi ya mik'a ma Fadila shi . Fadila amsar Ahmad ta yi tana sauke sanyayyar
ajiyar zuciya , Sannan ta kalli MD ta ce " Me ka sa min a yoghurt d'in da ka kawo
min ? " Fadila ta fad'i maganar tana kure MD da ido .

MD cikin mamaki ya ce " Me na sa miki kuma ? Ni dai na kawo miki yoghurt ina jiran
ki sha mu tafi in kawo ki gidanku amma abun mamaki kina sha ko da ma barci kike ji
ne ban sani ba ,daga kina zuwa kika je kika kwanta kika kama barci , nima ganin
haka sai ban tasheki ba na d'auki Ahmad muka fita " Fadila shiru ta yi sannan kamar
za ta yi kuka ta ce " MD , dan Allah ka ji tausayina ka sanar da ni abun da ban
sani ba , dan Allah ka cireni a kokonto ka sanar dani ? " Wata magana kike yi ne
haka Fadila ? , Me ye biki sani ba ? Me ye ya shige miki duhu wanda biki sani ba
kike son sani ? , Yi min bayani yadda zan gane ? " Cewar MD ya k'ure Fadila da ido.

Fadila cikin sanyi ta ce " MD me kasa min a cikin yoghurt d'in da ka ban ? " Oh !
Ya Allah , Fadila me zansa miki ? Wata magana ce kike yi haka ? " Fadila kallan MD
ta yi da raunannun idanunta ta ce " Baka samin komai ba kace ? , Tom na ji baka
samin komai ba , amma ka sani kafin ganina da jina ya d'auke naji lokacin da ka
rungume ni , sannan na farka na ji jikina ba yadda nake ba " Fadila ta idasa
maganar cikin kuka ta ce " Ta ya hakan ta faru ? " Shiru MD ya yi , sannan cikin
sanyi ya ce " Fadila , atakaice dai idan na fahimceki kina zargina na yi miki wani
abun ne . Haba Fadila ki tuna fa ko gidan nan bana zuwa in ba yauba da shima ke
kika bukaci in zo in kawo ki gidanku na zo shi ne daga k'arshe abun da zaki
sakamin dashi kenan , sannan Fadila ki tuna fa ko kafin Baba Lami ta tafi idan na
zo ko dakinki bana shiga hasalima bana dadewa nake tafiya . Amma ki yi hak'uri sai
yanzu na gano dalilin da ya sa kike zargina, yoghurt din da na baki kika sha a
daidai lokacin kina jin barci kika sha, kika yi barci acikin barcin kika yi
mafarkin an rungumeki kina ganin duhu - duhu kamar yadda kika ce , amma kuma yanzu
kika dawo da mafarkinki gaba d'aya akaina " Fadila kallan MD ta yi yadda ya ke ta
kawo mata hujjojin kare kai ta ce " Shi kenan , na yadda duhun da na gani da
rungumata da aka yi duk a mafarki ne , tom amma da na tashi na ji jikina babu dadi
bacin lafiya lau nake jin jikina kafin in sha yoghurt din da ka ban shi kuma fa? "
Fadila kenan , to so nawa mutum zai kwanta barci ya tashi da zazzab'i ko ciwan kai
? "

Fadila da taga duk inda ta bulloma MD yana k'ok'arin kare kan shi hakan ya sa ta ce
" Shi kenan MD Allah ya na tare da mai gaskiya idan har ka zalinceni na barka da
Allah " Fadila na fadin haka ta shige gida da sauri ta bar MD nan tsaye.

MD na kiranta amma bata saurare shi ba. Yara ya samu ya basu kayan Fadila da na
Ahmad da ya kwaso musu ya ce a shigar mata da su cikin gidan , sai kayan abinci
Taliya , makaroni , cous -cous sai buhun shinkafa . Siyayya ce sosai ya yi musu .

Mahaifiyar Fadila ita kanta da mamaki take bin kayan da kallo , sai da aka gama
shigo da su tas sannan ta kalli Fadila ta ce " Kin je kin sake saida mutunci naki
ne ? Baku da abinci shi ne aka kawo mana ? Tom ki tattara da ke da duk kayan nan
ki koma inda kika fito ! "

Mahaifiyar Fadila ta fara cilli da kayan da aka kawo ma Fadilar tana ta fitar mata
gida ba zata zauna da karuwa ba , kuma ba zata ci abincin da aka samai ta hanyar
sab'on Allah ba .
Mahaifiyar Fadila bayan ta gama cilli da duk kayan da zata iya d'agawa ta koma tura
Fadila dake rungume da Ahmad cikin hijab tana cewa " Fita ! ba zan zauna da karuwa
ba "

Aisha ganin mahaifiyarsu na niyyar tara musu jama'a rik'eta ta yi tana kuka ta ce "
Mama, dan Allah ki bar furta mata kalmar karuwa , Aunty Fadila ta sanar da ni
ainihin abun da ke faruwa da ita . Mama , naje wajan Aunty Fadila , kuma ta yi min
rantsuwa da al'qur'ani mai girma akan bata tab'a kusantar abun da muke zarginta da
aikatawa ba , mama , ke kika haifemu na tabbata ke kanki har yanzu zuciyarki ta
kasa amince miki da abun da idanunki ke ganin hak'ik'anin gaskiyarshi , Mama ,
kinsan Aunty Fadila ba za tab'a rantse min da al'qur'ani ba akan k'arya dan kawai
a yadda da ita , sannan ke da kanki kina shaidar fad'in gaskiyarta komai
d'acinta . Me ya sa yanzu ba zaki yi mata uziri ba ki zauna ki tattauna da ita
kamar yadda kika saba yi abaya , haba Mama, ke Uwace fa me ya sa ba zaki rungumi
'yarki ba zaki watsi da ita taje ta idasa lallacewa kenan ? Haba Mama kar yi abun
da zaki zo kina danasani "

Allah Sarki mahaifiyarsu Fadila sakin Fadila ta yi tana kuka .Aisha kuma zuwa ta yi
duk ta gyara kayan da mahaifiyarta ta yi watsi da su.

Mahaifiyar Fadila kuma take jikinta ya yi sanyi ta kuma tuna wacece 'yartata
abaya , tabbas ta yadda da maganar Aisha cikin Fadila k'addararsu ce inda ida kanta
duk da yaron da take gani zuciyarta ta k'i aminta mata da Fadila zata aikata zina .

Fadila da ta kasa jure kukan mahaifiyar tata zuwa ta yi ta tsugunna kusa da ita ta
ce " Mama , dan Allah ki bar kukan nan ina tsoran fushin Allah ya sauka akaina ,
dan ni ce silar kukan naki " Mahaifiyar Fadila kai ta d'aga da jajayan idanunta
tana kallan Fadila ta ce " Fadila, abu d'aya nake so ki sanar da ni yanzu waye
mahaifin yaron nan ? " Mama , Wallahi tallahi ! Ban sani ba nima , dan Allah ki
yafe min ki bar fushi dani ko zan samu sununin zuciya " Cewar Fadila tana kuka.

Mahaifiyar Fadila tashi ta yi tana tada Fadila ta ce " Na yafe miki Fadila , ni
kuma Allah ya sa mun dangana "

ADAMAWA STATE
Muhammad da kan shi ya tuk'a kan shi har zuwa sabon gidan shi . Bai shiga ba sai da
ya yi addu'o'i sannan .

Ango d'an kwalisa kad'an ya rage da ka zo kaga wayam , dan da amarya za mu tafi .
Muhammad murmushin yak'e ya yi ya ce " Haba , kun isa ma "

Nan dai suka yi ta tsokanar Muhammad sannan su ka yi musu fatan alkairi suka tafi .

Muhammad bacin abokanshi sun tafi kallan Kadija ya yi wanda har ga zuciyarshi yake
jin bata yi mai ba , amma dai ya yi alk'awarin zama da ita saboda mahaifinsa .

Muhammad ledar da ya shigo da ita ya mik'a ma Kadija ya ce " Bismillah " Na yi


fushi gaskiya , tun dazu baka zo baka barni da abokanka suka ci kani da surutu "
Muhammad bai k'ara jin baya son Kadija ba sai da ta yi magana ya ji baki d'aya ma
ba ta yi mai ba , dan shi yana d'aya daga cikin abuwan da yake son mace dasu , yana
son mace mai murya , amma wannan baki d'ayanta ba ta yi mai ba , ga shi da alama ma
tana da surutu .

Kadija ko jin Muhammad ya yi shiru ta ce " Baka ji abin da nace ba ne ? Ba zan ci


ba na yi fushi idan kana so in ci to ka kallasheni "

Muhammad kallan Kadija ya yi ya ce " Saina lallasheki zaki ci ? " Wayyo Kadija
muryar Muhammad ta tafi da ita , kasa bud'e baki ta yi ta yi magana sai d'aga ma
Muhammad kai ta yi .

Muhammad kallanta ya yi ya ce " Ki yi hak'uri ki ci kin ji amarya kwana da yunwa


babu dadi " Muhammad na fad'in haka ya yi shigewarsa ciki ya barta anan zaune .

Kadija bin bayan Muhammad ta yi da kallo ta ce " Wayyo dace kan dace gaskiya na
shigo duniya a sa'a , kyakkyawa ne mai daddadar murya , dole ma in bisa yadda yake
so kodan in samu damar mallake zuciyarsa "

Kadija ta dad'e tana sambatunta akan Muhammad sannan ta d'akko ledar da Muhammad ya
aje mata . Tana gama lashe -lashenta barci ya kwasheta a wajan.

Muhammad cikin barci ya jiyo gurnanin mutum , tashi ya yi yana fitowa falon da
sauri .

Kadija ya gani kwance sai haure - haure take .

Muhammad da sauri ya idasa inda take saidai take ya zazzaro idanunsa ganin Kadija
kwance cikin jini an mata yankar rago amma har yanzu ran bai gama fita ba .

Muhammad cikin furgita ya ke nanata " Innalillahi wa inna ilaihirraj'un ! "

Muhammad na nan tsaye kan Kadija har ranta ya fita ya bar gangar jikinta . Muhammad
da gaba d'aya tsoro ya fita ranshi da sauri ya bud'e k'ofar falon ya fita , wajan
masu gadin gidan ya je hankali tashi , ya na tambayar su waye suka shigomai gida .
Sai dai Muhammad a lurar da ya yi gaba d'aya masu gadin basa cikin hayyacinsu ,
hakan ya sa bai bi takansu ba ya bud'e get d'in ya fita.

Saidai unguwar shiru bai ga komai ba bai ga kowa ba. Ahaka tsabar rud'ewa
Muhammad ya kama hanya cikin daran ya isa gidansu a k'afa , Muhammad na zuwa ya yi
ta bubbuga get d'in gidan amma shiru sai da ya dade yana yi sannan aka ce " Waye ?
" Muhammad ne ku bud'e " Jin muryar Muhammad da sauri suka bud'e get d'in ya shiga.

Da mamaki suka bi Muhammad da kallo dan daga gani ma kamar ba a hayyacinsa ya ke ba


. Hakan ya sa kafin Muhammad ya idasa shiga gidan d'aya daga cikin masu gadin da
yake na hannun damar Alhaji Sagir ne ya kirashi awaya ya sanar shi ga Muhammad ya
zo kuma da alama a furgice ya ke .

Alhaji Sagir cikin tsoro da jin Muhammad ya zo cikin tsakiyar daran nan ya tashi ya
fita ya biyoshi . Gaf k'ofar da zata sada Muhammad da falon Alhaji Sagir suka had'e
.
Muhammad na ganin mahaifinshi ya ce " Daddy , ka ga ni ko abun da nake tsoro kenan
itama sun kasheta , Daddy , an mata yankar rago kamar wa incan "

Iya furgita alhaji Sagir ya furgita da kalaman Muhammad , kama Muhammad d'in ya yi
ya zaunar da shi dan ganin kamar ba ya cikin hayyacinsa .

Atakaice dai cikin daran Alhaji Sagir suka je da motar 'yan sanda suka taho da
gawar Kadija . Haka dai aka yi duk wasu binciken da za ai akan gawar .

Sosai mahaifin Kadija ya furgita lokacin da sakon mutuwar Kadija ya isarmai . Haka
dai ita ma Kadija aka sallaci gawarta aka kaita gidanta na gaskiya .

KADUNA GARIN GWAMNA

Mahaifiyar Fadila haka ta sama kanta hak'uri da dangana dan yanzu har daukar Ahmad
take . Yanzu dai atakaice kusan duk sun saki ransu sun dawo rayuwarsu kamar da .
Abu d'aya ke damun mahaifiyar Fadila shi ne surutun 'yan unguwa , dan haka nan tana
zaune sai taga an shigo gidan wai an zo gaidata da wayan aga dan da Fadila ta haifa
.

BAYAN WATA D'AYA

Yanzu watan Fadila d'aya kenan da dawowa gida . Yau Fadila ta samu mahaifiyarta da
maganar zata koma aiki.
Maifiyar Fadila shiru ta yi sannan ta ce " Tom , Fadila Allah ya tsareki dan Allah
ki kula sosai " Fadila cikin kwantar ma mahaifiyarta da hankali ta ce " Karki damu
Mama , babu abin da zai faru dani in sha Allah "

Yau Fadila ta koma aiki , in da MD ya amsheta babu yabo ba fallasa , dan abun da ya
ba Fadila mamaki gaisuwarta ma ciki - ciki ya amsa , ta zaci ma zai dakatar da ita
aikin ne amma sai ta ji ya ce " Ta je ta samu Jamilu su yi magana " Fadila ta juya
zata tafi ne , MD ya ce " Ahmad fa ? " Fadila kamar karta bashi amsa amma sai cewa
ta yi " Ahmad yana gida " Kina nufin acan zaki barshi ? In yana kukan abinci fa ?,
Gaskiya ba zai yuwu ba sai dai ko ki rik'a zuwa da shi ko kuma ki bar aikin "

Fadila kallan MD kawai ta yi bata tanka mai ba ta fita.

Koda taje ta samu Jamilu take ya sanar da ita akwai aikin da za su yi yanzu haka .
Haka Jamilu ya yi ta nuna ma Fadila tsare - tsaran da suka canza . Bayan ya gama
nuna mata ne suka gabatar da Shirin da suke gabatarwa tare in da rashin Fadila ya
sa suke yi da Ummi .

Bayan sun gama kabatar da shirin ne suka bada damar aiko da sak'onni ta waya ko ta
Gmail address nasu . Bayan sun dawo hutun takaitaccan lokaci da suka je ne Fadila
ta fara karanto sak'onin kamar haka , ta ce " Mai sakon farko Hassana Sani ta ce "
Shin macan da ta haihu agida za'a iya kiranta da sunan mace mai daraja itama ? "
Fadila ta gama fad'in sak'on tana kallan Jamilu wanda tasan duk wanda ya yi
tambayar nan da ita yake kuma dan ita aka yi .

Jamilu ma ya gane hakan , hakan ya sa ya bada amsa kamar haka " Eh , sosai ma kuwa
za'a iya kiranta mace mai daraja itama idan har ya kasance ta hanyar tsautsayine ta
same shi "

Abun mamaki tambaya ta biyu ma suna kamancece niya da ta faro , haka dai ita ma
Jamilu ya bada amsa a ilimance .

Haka dai suka gama shirin Fadila ranta yana mata duk ba dad'i .
Fadila ta tashi aiki zata tafi gida MD ya tareta ya ce " Fadila, kamar yadda nace
miki kodai ki rik'a zuwa da Ahmad aiki dan bai isa barshi a gida ba ko kuma ki
✍🏻
dakata da zuwa aikin har ya yi kwari

📚 FADEELAH 📚

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare
da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻

Na
Fadila Sani Bakori

SANARWA : Masu tambaya akan gyaran jiki akwai hanyoyi kala daban - daban da zan
kawo muku na gyaran jiki acikin wannan littafi mai suna FADEELAH .

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*


*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦250
2GB = ₦700. 1GB ₦500
3GB = ₦1050. 2GB ₦1000
4GB = ₦1400. 3GB ₦1500
5GB = ₦1750. 4GB ₦2000
*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

Page 12

Fadila ta tashi aiki zata tafi gida , MD ya tare ta ya ce " Fadila , Kamar yadda
kika ji na ce miki kodai ki rik'a zuwa da Ahmad aiki ko kuma ki dakata da zuwa aiki
har ya yi k'wari "

Fadila juyawa ta yi ta fita ba tare da ta tanka ma MD ba .

Fadila koda ta koma gida bata b'oye ma mahaifiyarta yadda su ka yi da MD ba .


Mahaifiyar Fadila shiru ta yi Sannan ta ce " Fadila , kodai MD shi ne mahaifin
Ahmad ?" Tom , mama ni ma ban sani ba , amma ni ma ina zargin hakan " Cewar
Fadila .

Aisha da ke zaune kusa da su ta ce " Nifa mama da za ku bi ta tawa Wallahi d'aukar


yaran nan za'ai akai mai abinsa , dan babu ma makawa d'ansa ne Wallahi " A'a Aisha
har yanzu ba mu da wata k'wak'k'warar hujjar da za mu yi haka , amma idan mu ka yi
hak'uri Allah zai kawo mana hujjar da za mu kamashi da ita "

Da daddare Fadila tana hau Facebook, anan ta ci karo da posting d'in Usman abokin
Muhammad yana cewa " Assalamu alaikum. Jama'a dan Allah ku taya mu addu'a Allah ya
kawo ma abokin Muhammad Sagir mai shadda mafita akan halin rayuwar da ya tsinci
kansa . Muhammad Sagir auranshi uku kenan , amma daga ankai matan gidansa washegari
zai farka aga anyi musu yankar rago , gashi duk wani bincike da kuka sani babu
wanda ba mu yi ba , amma har yanzu dai Allah bai bayyana mana wanda suke haka ba .
Dan Allah kusa Muhammad Sagir a addu'a Allah ya toni asirin duk mai akatamai haka,
idan kuma iskace Allah ya yi mai maganinta "

Fadila haka taita bin comments din jama'a , inda mutane da dama sukan ce " K'ilama
al'jana ce ta aurai take ta mai ta'asan nan " Haka dai jama'a kowa da abin da yake
cewa .

Fadila shiru ta yi , dan tabbas idan bata manta sunan wanda aka ce ya yi mata aiki
ya ciro mata Ahmad ba shi ne , dan tabbas haka ya gabatar da sunan shi ga jama'a
ranar taron bikin cikar shekara goma da RAHAMA TV ya yi . " Muhammad Sagir mai
Shadda tabbas haka sunan ya ke"

Fadila dan ta cire ma kanta kokwanto Jamilu ta kira , bayan sun gaisa ta ce "
Jamilu , dan Allah ko zaka iya tuna min sunan wanda ya yi min theater ya ciro min
Ahmad ? " Eh , sunansa Muhammad Sagir mai shadda " Fadila shiru ta yi sanan ta ce "
Shi kenan, na gode sai anjima "

Fadila bayan ta kashe wayarta number Muhammad ta kira acewarta ya cancanci ta yi


mai gaisuwa . Abun mamaki kira d'aya Muhammad ya d'aga .

Fadila da bata yi tunanin ma zai d'aga ba take ta rikice , haka dai ta daidaita
natsuwarta ta fara magana kamar haka " Assalamu alaikum . Ina wuni " Muhammad
adak'ike ya amsa da " Lafiya , bangane wake magana ba ? " Sunana Fadila daga nan
Kaduna , ni ce wadda ranar da ka zo taron anniversary namu na haihu ka yi min
theater , tom yanzu nan na cikaro da wani posting da abokinka ya yi akan mutuwar
matanka , Allah sarki Allah ya yi musu rahama Allah ya sa maka juriya na rashinsu ,
Allah ya kuma tona ma wanda yake aikata maka haka asiri "

Muhammad sosai ya ji dad'in addu'ar Fadila , cikin jin dadi addu'ar tata ya ce "
Ameen ya Allah . Ina yaronki fa ? " Ahmad yana nan ya fara wayo watan shi hudu
kenan " Ok ki tura min photonsa ingansa " Fadila cikin jin dad'i ta ce " Tom "

Daga haka Muhammad ya kashe wayarshi.

Fadila kuma take tahau WhatsApp ta tura ma Muhammad pics din Ahmad kala uku .

Muhammad koda ya hau online ya ga pics din Ahmad da Fadila ta tura mai sosai ya
yaba mata kyan yaran , dan har yana tonanta da cewe " Za ki ban shi ko ? " Fadila
da hawanta Online kenan ta ci karo da sak'on Muhammad, dariya ta yi ta ce " Eh ,
zan baka , amma kuma ai baka da matar da zata rik'e maka shi " Amma kuma ai ina da
mama kinga mamana zata rik'emin saidai in kina min wasa ne ba bani zaki ba " Cewar
Muhammad da ya biye ma Fadila .
Fadila ta maida mai amsa da cewa " Kai ma wasa kake ba amsa za kai ba "

"Hmmm, ki bani ki gani " Daga nan Muhammad ya sauka .

BAYAN WATA D'AYA

Fadila watanta d'aya kenan da daina zuwa aiki , inda MD ya dakatar da ita ya ce sai
Ahmad ya yi kwari . Saidai kullum sai ya aiko ma Fadila dubu d'ayar da yake bata ,
yanzu kuma acewarshi ta saima Ahmad Pampers .

Ahmad yanzu watan shi biyar kenan .

Fadila 'yan kwana kan nan jiri take fama da shi da yawan ciwan kai . Dan ma
sauk'inta mahaifiyarta da Aisha suke rainon Ahmad .

Fadila yau gaba d'aya kwance ta wuni kuma kusan bata ci komai ba .Mahaifiyar Fadila
da shigowarta d'akin kenan ta ce " Fadila , kinga yaron nan kuka yake d nono bai
isheshi ba , gashi kin k'i tashi ko wani abun ma ki ci " Fadila cikin murya irin ta
mara lafiya ta ce " Mama, jiri nake gani ga ciwan kai dake damuna Allah ji nake ko
zama bana iya yi " Tom ki tashi ko chamise d'in kusa damu din nan ku je Aisha ta
rakaki a baki magani mana " Tom bari Aishar ta dawo "

Bayan Aisha ta dawo ne ta raka Fadila chamise .

Lokacin da suka je za su shiga chamise din kenan Aisha ta had'u da wata k'awarta
hakan ya sa Fadila kad'ai ta shiga . Fadila ba yani ta yi ma mai chamise d'in na
yadda take ji . Kallanta ya yi ya ce " Madan anya ko ba ciki gareki ba ? " Fadila
a furgice ta d'ago dara-daran idanunta tana kallan shi a furgice ta ce " Ciki kuma
! ? " Tabbas , amma zaki iya zuwa Asibiti dan tabbatarw..." Tom shi kenan na gode
sai anjima " Fadila ta ce haka sakamakon Aisha da ta shigo.

Aisha kallan Fadila ta yi yadda ta fita da sauri kuma yanayinta gaba d'aya a
furgice take . Aisha da mamaki ta k'ara sauri ta iddo Fadila tana cewa " Aunty
Fadila , Wai lafiya ? " Eh ce min ya yi ciwan kaine da jiri ke damuna " Aisha da
mamaki ta ce " Dama ai akan abun da muka je kenan yana damunki ina ? " Eh ,haka
suka ce " Aisha da mamaki ta bi Fadila da kallo dan gaba d'aya ta rud'e maganar ma
kamar bata san me take cewa ba .

Aisha da bata kawo komai a ranta ba , haka suka tafi ba tare da ta k'ara magana
ba .

Koda suka shiga gida mahaifiyar Fadila tambayar Fadila ta yi ta ce " Me ke damunki
ne ? " Jiri ne da ciwan kai kawai " Fadila ta fad'i maganar a furgice dan ta rud'e
sosai da jin cewa tana da ciki.

Mahaifiyar Fadila ta ce " Sun baki magani ko ? " Eh, cewa sukai jiri ne da ciwan
kai " Mahaifiyar Fadila da mamaki ta bi Fadila da kallo jin tambayar da ta yi mata
daban da amsar da ta bata , haka dai ta kuma cewa " Fadila ! Cewa na yi sun baki
magana ni ? " Mama , Allah ciwan kai ne " Fadila ta fad'i maganar tana goge
hawayan da ya fara zubar mata .

Mahaifiyar Fadila da mamaki ta kalli Aisha ta ce " Ikon Allah , Aisha wai me ke
damun Fadila ne ? "

Fadila da sauri ta amshe zance ta kuma cewa " mama , Allah ciwan kai ne da jiri "
Daga Mahaifiyar Fadila har Aisha da kallo suka bi Fadila . Sai zuwa can mahaifiyar
Fadila ta ce cikin sanyi " Aisha , lafiya wai ? " Aisha kallan mahaifiyarta ta yi
ta ce " Mama tunda muka fito chamise din gaba d'aya Aunty Fadika ta rud'e " Tom ,
ko wani abun ya ce mata ne ? " Mahaifiyar Fadila ta tambaya .

" Da yake ba tare muka shiga ba , na gamu da Aunty zee muna gaisawa ita kad'ai ta
shiga "

Mahaifiyar Fadila batare da ta kuma cewa komai ba ta d'akko hijab dinta a daki ta
fita . Daga Fadila har Aisha da kallo suka bi ta .

Mahaifiyar Fadila chamise din da su Fadila suka je ta je . Bayan sun gaisa da mai
chamise din ne ta tambayeshi abun da ke damun Fadila . Ya bata amsa kamar haka "
Mama , gaskiya abisa alamomin yadda ta sanar da ni ciki ne , amma na sanar da ita
ta je Asibiti a dubata ta gani "

Mahaifiyar Fadila a rud'e ta dawo gida dan tabbas idan bata manta ba cikin Ahmad ma
haka Fadila ta yi , sannan yana yin laulayin nata yana kama da na mai cikin .

Mahaifiyar Fadila lokacin da ta isa gida jikinta ko ina rawa yake . Su Aisha na
zaune ita da Fadila da itama har yanzu a rud'e take , ba kamar da mahaifiyarta ta
fita ba dake ta k'ara rud'ewa dan tasan chamise din da suka je mahaifiyarta zata .

Mahaifiyar Fadila nuna Fadila ta yi tana cewa " Fadila , gwanne za ki a haihuwar
shegen ? Ciki fa aka ce kina da shi , dan babu wata tantama alamun ki gaba d'aya ya
nuna na masu ciki , nima so kike ki kasheni kamar yadda kika kashe mahaifinki ?
Fadila , mu zaki tozarta a idan duniya ? Tom Ina rok'on Allah ya tsaida wannan
tozarcin da kike kok'arin yi mana akan ki ke kad... " Aisha da sauri ta rufe bakin
mahaifiyarsu tana kuka ta ce " Mama , dan Allah duk abin da zaki mata ki yi mata
amma karki mata baki dan Allah "

Mahaifiyar Fadila kallan Aisha ta yi tana kuka ta ce " Aisha , shi kenan ba zan yi
mata baki ba , amma Wallahi idan duniya zata taru akaina bazan zauna da Fadila ba ,
kodai tabar gidan nan ko kuma ni in bar muku gidan . Aisha , tun yanzu shiga mutane
yana naiman gagarata duk in da na yi nunani ake , naga alamar so take ta maida mu
abun kwatance a idon duniya gwanne fa Aisha ! Watan Ahmad nawa Aduniya ? "

Usaini wanda ke bima Aisha ma kuka ya sa cikin kukan yana cewa " Wallahi Mama
rannan da mu kai fad'a da abokina gori ya yi min wai su gidansu ba a aje abun kunya
ba , gaskiya Aunty Fadila , gara ki tafi kawai da ki maida mu abin kwatance a
unguwa "

Fadila ko badan kuka ta kasa cewa komai .

Mahaifiyar Fadila ko da yake irin iyayannan ce masu zafi ta ce cikin hargagi "
Fadila , ki fita nace ke ba mai son shiryuwa ba ce gwanne acikin shege ? Wallahi
ba zan zauna da ke ba ki zo ki fita in bar ganinki ! "
Fadila tashi ta yi jikinta na rawa kota ina ta ce " Mama , ki yi hak'uri ba da
sanina ba ne amma zan sanar da ke iya abun da na sani " Bana buk'ar jin komai daga
gareki ki ! ki fita kafin in miki illah "

Mahaifiyar Fadila da yake bata iya bacin rai ba ganin Fadila har yanzu bata fita ba
, da sauri ta fita sai gata da wata sanda ta shigo , tana shigowa kuma ta yi kan
Fadila da ita .

Aisha cikin tsoro da gigita ta rik'e sandar katakam tana kuka ta ce " Mama , dan
Allah ki daure ki saurareta ki ji abun da zata ce " Aisha ki sakar min sandata
kafin ranki ya b'ace " Fadila ko ta d'are can k'arshen gadonsu tana kuka jikinta
ko'ina kakkarwa yake kamar mai jin sanyi .

Aisha cikin kuka ta kuma cewa " Mama , dan Allah ki yi hak'uri kar ki buga mata za
ki mata illah fa "

"Shi kenan , na hak'ura amma ta d'auki Ahmad su fita bana son ganinsu duka " Cewar
mahaifiyarsu Fadila .

Aisha cikin sanyi ta ce " Mama , dare ne fa idan kika koreta ina zata ? "

Mahaifiyar Fadila cikin b'acin rai ta wanka ma Aisha mari ta ce " Dan ubanki ba
zaki sakeni ba , Duk in da zata ta je, ana tattalin abun da bai riga ya
lallace bane , wanda kuma ya riga lallace me ye amfanin ? me ye abun tsoro dan ta
fita cikin daran ? "

Aisha tsabar jin zafin Marin da mahaifiyarsu ta yi mata ya sa ta saki sandar bata
sani ba . Tana ko sakin sandar mahaifiyarsu ta yi kan Fadila da ita ta ta buga
mata wanda ya sa Fadila ta fasa ihu jin zafin saukar sandar a goshinta .

Mahaifiyarsu Fadila ta d'aga zata k'ara buga mata ne , Usaini da Aisha suka rik'e
sandar suna kuka .
Duk yadda mahaifiyar Fadila ta yi akan su saketa sun k'i dan sosai suka rud'e yadda
suka ga ta fasa ma Fadila goshi.

Wata mak'ociyarsu Fadila jin hayaniya ta yi yawa a gidansu Fadila shigowa ta yi


tana tambayar lafiya .

Bud'ar bakin mahaifiyarsu Fadila sai cewa ta yi " Gwanne za ta yi min ! " Ciki ! ?
to fa " Matar na fadin haka ta lallab'a ta bar gidan .

Aisha kuma cikin takaici ta ce " Haba , mama wannan wana kalar b'acin raine wanda
zaisa ki tona mana asiri " Tonan asiri kuma na nawa ? Asiri ya gama tonuwa ai "

Aisha kallan mahaifiyarta ta yi ta ce " Mama , dan soyayyarki da annibi Muhammadu (


S . A . W ) ki yi hak'uri mu saurari abun da Aunty Fadila zata ce ? "

Mahaifiyar Fadila shiru ta yi bata kuma magana ba sai ajiyar zuciya da take saukewa
.

Aisha kuma ta ce " Aunty Fadila , muna jinki "

Fadila da kyar ta iya bud'e baki ta ce " Aranar da zan dawo gidan nan da zama
tabbas na yi zargin MD ya aika wani abu dani dan ya bani Yoghurt na sha kuma tunda
na sha Yoghurt din bankara sanin kaina ba sai bayan dogon lokaci "

Fadila ta idasa maganar da kyar .

" In dai ko haka ne ya zama dole mu yi karar MD " Cewar Aisha .

Mahaifiyar Fadila dai bata tanka ba ta tashi ta fita ta koma d'akin ta .


Bayan mahaifiyar Fadila ta fita ne Aisha ta d'auki Ahmad da ke kuka ta goya shi .

Atakaice dai ranar gidan babu wanda ya yi barcin dadi .

Washegari Aisha da wuri ta shirya bayan ta shirya ne ta kalli Fadila ta ce " Aunty
Fadila , nifa na shirya ki zo mu je sharia court mu kai karar MD can, za su kwatar
miki hak'inki "

Fadila tashi ta yi ta zumbula hijab dinta suka tafi .

Su Aisha na zuwa wani lawyer ya buk'aci su bada kud'in shigar da k'ara , dama Aisha
ta taho da kudi a hannunta ta mik'a musu . Nan Fadila ta bada address d'in MD .

✍🏻
Aranar aka kaima MD takaddar sammaci

SANARWA : Saura page d'aya in gama free page , idan biki biya ba ki hanzarta .

# 300 ne kacal 👌🏻

My Number 08063830828

📚 FADEELAH 📚

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare
da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻

Na
Fadila Sani Bakori

SANARWA : Masu tambaya akan gyaran jiki akwai hanyoyi kala daban - daban da zan
kawo muku na gyaran jiki acikin wannan littafin mai suna FADEELAH .

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*


*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦250
2GB = ₦700. 1GB ₦500
3GB = ₦1050. 2GB ₦1000
4GB = ₦1400. 3GB ₦1500
5GB = ₦1750. 4GB ₦2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

Last free page 13


Aranar aka kai ma MD takaddar sammaci.

MD koda ya gama duba takaddar sammaci ya ji dalilin k'arartasa , waya ya ciro ya


Kira Fadila .

Fadila lokacin sun koma gida babu dad'ewa Kiran MD ya shigo wayarta , nuna ma Aisha
ta yi , Aisha ta ce " Ki d'auka ki ji abun da zai ce miki " Fadila d'agawa ta yi .
MD cikin lallashi ya fara magana kamar haka " Haba , Fadila tsakanina da ke kuma me
ya yi zafi wanda har sai an had'a da kotu ? Indai maganar Ahmad ce ni na ji ki
janye k'arar zan mai komai na rayuwa , kuma ai ba gazawa na yi da hidimominsa ba
bare kice . Ni dai yanzu rak'on da nake miki ki janye karar nan zan zo mu sasanta
aji yadda za a yi " Ba ni na kai ba iyayena ne " Cewar Fadila.

MD shiru ya yi sannan ya ce " Amma hakan ba kya ganin karar tonuwar asirinki ne ? ,
ki yanje karar nan ni kuma na yi miki alk'awarin zamema Ahmad Uba harda wanda zaki
haifa ma , kuma duk abin da uba ke yi ni zan musu , na yi miki alk'awain ba za su
tab'a kukan rashin uba ba " Ba ni na kai kara ba ba ni da ikon janyewa " Ok , shi
kenan , inda na biki ta lallama kin k'i mu je kotun sai me " MD na fad'in haka ya
kashe wayarsa .

Fadila bin wayar ta yi da kallo .

Aisha kallan Fadila ta yi ta ce " Aunty Fadila , ina tsoran kar mu je kotin ma ya
kadamu dan naga alamar yana da baki " Hmm, Aisha Allah ya fishi " Cewar Fadila .

Washegari ya kama za a gabatar da k'ararsu Fadila .

Fadila sammakon tashi su ka yi suka je Asibiti kamar yadda lawyer da suka samu ya
ce su zo da takardar shaidan ciikin jikinta . Bayan sun dawo asibitin ne Aisha ta
kalli mahaifiyarsu ta ce " Mama , kin ga ko ba aje kotu ba gaskiya fa ta bayyana ,
Ahmad da cikin jikin Aunty Fadila duk na MD ne , saboda kin ga cikin wata biyu suka
ce , kuma wata biyu kenan da dawowar Aunty Fadila gidan nan " Mahaifiyarsu Fadila
kamar ba zata tanka ba sai zuwa can ta ce " Aisha , ni dai abun da nake so indai
gaskiya ta bayyana to dan Allah karku dawo da Ahmad ku bashi d'an shi , cikin
jikinta ma daga ta haihu zata bashi abun shi " Tom, mama ki mana addu'a mun tafi "
Cewar Aisha .
Kutu ta cika duk wani wanda ake buk'a ya halarta har MD ma ya zo .

Kasan cewar kotun kotun musulinci ce ya sa aka fara gabatar da k'ararsu babu wani
bata lokaci . Inda aka sanar da MD dalilin da ya sa Fadila take k'ararsa. Inda MD
ya fara kare kanshi kamar haka " Eh , tabbas ni na san Fadila na zargina da cewa
Ahmad da kuma cikin jikinta na yanzu duk naune , amma kuma a hak'ik'agin gaskiya ba
haka bane , ina tausayin Fadila ne shi ne silar yimata komai da nake yi wanda ya
janyo min zargi a wajanta , ni kuma da harda yaran da zata haifa ashirye nake da
in taimaka mata akan shi , saboda kasan cewarta marainiya , hakan da nake mata dan
tausayi shi ne ya jawomin zargi a wajanta , amma a hak'ik'agin gaskiya bani jib'i
da Ahmad da kuma cikin dake jikinta yanzu haka "

Alk'akin kai ya jinjina sannan ya ce " Aranar da Fadila zata bar gidan da ka bata
ta zauna ka kawo mata wani yoghurt wanda tana shansha jinta da ganinta ya d'auke ,
inda take zargin ka yi anfani da haka ne dan ka cika burinka akanta, me za ka ce
akan hakan ? " Eh , haka nima tace min , kuma tabbas na kawo mata yoghurt , amma
maganar gaskiya ni ban mata komai ba kamar yadda take zargi "Cewar MD.

" Amma kuma tana shan yoghurt d'in barci ya kwasheta kuma kafin haka ta ji lokacin
da ka riketa kamar yadda ta ce , shi fa me za ka ce akan haka ? " Cewar alk'alin .

Nan ma dai MD ya fara kawo hujjojinshi kamar haka " Eh , nima tace min haka wai ta
ji lokacin da na rungumeta amma a hak'ik'anin gaskiya ni ban rungumeta ba , nafi
tunanin hakan ya zo mata a mafarki ne "

Alk'akin kotun kai ya jinjina sannan ya ce kamar yadda kuka sani dai ana yi a kotun
musulinci ga duk shari'a da ta gagara sanin ainihin gaskiya . Alk'akin ya kalli MD
ya ce " Yanzu zaka iya rantse mana kenan da al'qur'ani akan Ahmad da kuma abin da
ke cikin Fadila ba kai bane mahaifinsu ? " Shiru MD ya yi ya fara waige - waige
kamar mai neman wani . Alk'alin jin ya yi shiru ya kuma cewa " Shin zaka iya
rantsuwa da al'qur'ani ba kai bane mahaifin Ahmad da cikin dake jikin Fadila kamar
yadda take zargi ? " Nan ma dai MD shiru ya yi kamar mai nazarin wani abu , sannan
ya ce " Eh , zan iya rantsuwa " Zaka iya rantsewa da alqur'ani mai girma ? " Eh ,
z..a..n.. iya " MD ya fad'i maganar yana rawar baki .

Alwalla aka raka MD ya je ya yi , bayan ya dawo ne aka bashi Al'qur'ani mai girma .
In da MD ya amshi Al'qur'anin jikinshi ko ina ya na rawa .

Inda aka Umarci MD da duk abin da aka ce ya maimaita . Nan mai gabatar da rantsuwar
ya fara jero mai kamar haka " Ka ce Ka rantse da wannan Al'qur'anin da ke hannunka
baka tab'a kusantar Fadila ba , sannan ba kai bane mahaifin Ahmad da cikin
jikinta , idan kuma kai ne ka b'oye Allah ya sa wannan Al'qur'anin ya cika , Allah
ya hanaka abun da kake nema duniya da lahira , Allah ya nisanta ka da duk
rahamominsa " Haka MD ya nanata kamar yadda mai karanto mai ya karanto , inda MD ya
idasa maganar jikinshi ko ina yana rawa ga zufa da ke keto mai kota ina, wadda
hakan ya ba kowa mamaki .

MD na kai rantsuwar Alk'alin ya kalli Fadila wadda ke kuka ya ce " Fadila , babu
zargi yanzu kan MD saboda ya yi rantsuwa da Al'qur'ani mai girma , dan haka ya
wanke kanshi daga zargi "

Alk'alin na fad'in haka ya tashi .

Fadila kuka take sosai , inda Aisha ma kukan take , sannan ita ta lafa da nata ta
kamo hanun Fadila ta ce " Ki tashi mu tafi " Fadila tashi ta yi , sun zo k'ofar da
za su fita ne su ka ci karo da MD , MD kallan Fadila ya yi ranshi b'ace ya ce "
Fadila , da ace kin ji maganata biki kawoni nan ba da na rufamiki asiri , amma
yanzu ki sani natsame hannuna akan duk abin da ya shafeki dake da Ahmad har da ma
wanda zaki haifa " Fadila kai ta d'aga tana kallan MD sannan ta ce " Ka ji tsoran
Allah MD , ka amshi cikin jikina ko ba zaka amshi Ahmad ba , ni nasan cikin jikina
naka ne koda ko zaka had'iyi Al'qur'ani ne , saidai da ya ke ka kasance cikin
marasa tsoran Allah masu rantsuwa akan k'arya ka ji tsoran Allah" MD kallan Fadila
ya yi cikin tausasa zancesa dan sai kuma ya ji tausayinta ya ce " Fadila , bani da
jib'i akan cikin jikinki shi ne gaskiyar lamari , na so in ci gaba da taimakonki
saidai gudin zargin zama'a akaina ba zan iya ba , ina miki fatan alkairi sai
watarana duk da nasan akwai ranar da zaki sake naimana " MD na fad'in haka ya yi
tafiyarshi da sauri "

Aisha hannun Fadila ta ja suka tafi .

Mahaifiyar Fadila a gida ko ta k'osa su Fadila su dawo ta ji yadda suka k'arke .


Tana nan zaune su Fadila suka shigo . Mahaifiyarsu Fadila tashi ta yi da sauri tana
kallan Aisha ta ce " Aisha , ku tsaya daga nan kusanar dani yadda ake ciki ? "
Aisha cikin kuka ta zayyana ma mahaifiyarsu duk yadda aka yi.

Mahaifiyar Fadila kallan Fadila ta yi ta ce " Fadila , zan miki wata alfarma guda
d'aya, zan ci gaba da zama dake badan ina so ba dan kin fira raina , amma ba zan
zauna dake da Ahmad ba da kuma cikin jikinki ki je duk inda zaki idan kika haihu
sai ki dawo amma da su ba ki naimi ubansu ki ba shi su , ba zan zauna da yaran
shegu har biyu ba, ki fita kije ki naimi ubansu dan wallahi ba zaki kwana gidan
nan ba yau "
Aisha cikin marairaicewa ta ce " Mama , dan Allah ki yi hak'uri idan kika koresu
ina za su ? " Mahaifiyarsu Aisha cikin d'aga murya ta ce "Aisha , Wallahi in duniya
zata taru akaina ba zan zauna ina kallan Fadila da shegeba tana raino ga kuma wani
aciki yana shirin zuwa duniya , amma ta je duk inda zata ta haihu , k'ila in ta
haihu ta dawo min ba da su ba in yafe mata "

Aisha zata k'ara magana mahaifiyar Fadila ta ce " Wallahi , indai Fadila bata bar
gidan nan ba na bar ganinta zan mata baki "

Fadila sanin halin mahaifiyarta da ta yi na indai ta yi zuciya babu mai iya


lankwasata ya sa ta shiga d'akinsu ta d'akko wasu daga cikin kayanta da na Ahmad ,
tana rungume da Ahmad ta je wajan mahaifiyarta tana kuka ta ce " Mama , zan tafi in
sha Allah kuma ba zan dawo da Ahmad da abin da ke cikina ba , amma dan Allah mamana
ki bar fushi dani ki samin albarka ko zan samu sukunun zuciya dan Allah kar ki yi
fushi dani "

Allah sarki mahaifiyar Fadila ma kuka take cikin kunan ne ta ce " Fadila , ki tabi
zuciyata ta kasa jure ganin Ahmad da abin da ke cikinki dan Allah ki tafi bana son
ganinku baki d'aya ! "

Fadila tana kuka ta juya ta fita gidan har tana sake juyowa .

Fadila na fita Aisha ta durkushe awajan tana kuka sosai .

Fadila ko koda da ta fita rasa inda za tabi ma ta yi , hakan ya sa ta mik'e hanya


tana tafiya tana kuka ga Ahmad rik'e ahannunta . Fadila sai da ta yi tafiya sosai
tabar unguwarsu baki d'aya sannan ta samu wani waje ta zauna tana tunanin inda zata
. Tunanin Kiran Jamilu ta yi sai kuma taga shi ma yanzu d'auke mata kai yake hakan
ya sa ta fasa .

Fadila na nan zaune , Muhammad Sagir mai shadda ya fad'o mata arai , charting
d'insu ta tino da yake ce mata zata bar mai Ahmad ,ta ce shi da bai da mata wa zai
rik'e mai , ya ce ga mommynshi nan .

Fadila shiru ta yi tana tunani ta ce " Tom kodai da gaske yake , kai koma bada
gaske yake ba yana da kirkin da zai iya taimakamin "

Fadila da keneman ceto da kuma tunanin kamar zaitaimaka mata ya sa ta Kira number
shi .

Sai dai ta Kira bai d'aga ba, sai da ta yi mai kira uku amma bai d'auka ba .

Fadila ganin bai tauka ba ta fara tunanin ko gidan marayu zata ta kai Ahmad ita ma
ta zauna in ta haifu ta bar abin da ta haifa acan ta dawo gida , in da mahaifiyarta
ta ce zata amsheta in dai babu su Ahmad .

Fadila tashi ta yi ta samu Napep ta ce ya kaita gidan maru dan Allah da ke nan kusa
.

Fadila koda suka isa gidan marun ce mata akai sai ta zo da wani nata sannan a
amshi Ahmad .

Fadila bacin ta biya mai Keke - Napep d'in , tafiya ta fara yi ak'asa batare da ta
san inda zata ba. Fadila jin ta gaji ta fara ganin jiri ga Ahmad har ya fara kuka ,
hakan ya sa ta samu waje ta zauna , ta na zama ta sake tunanin k'ara kiran Muhammad
, nan ma sai da ta yi kira uku amma bai d'aga ba .

Wani tunani ne ya zo ma Fadila a zuciyarta ta ce " Tabbas , Muhammad Sagir ya na


da kirki kuma ina ji ajikina zaitaimakamin dan haka Adamawa zani kafin in isa zanta
kiran numbersa har Allah ya taimakeni ya d'aga "

Fadila na gama wannan tunanin ta tashi ta hau Napep ta nufi tasha , tana zuwa ko ta
✍🏻
samu motar Adamawa ta cika saura mutum d'aya ta hau suka tafi
FADEELAH free page ya k'are ga mai muk'ata # 300 kacal 👌🏻

Kud'in littafin FADEELAH d'ari uku ne dan Allah idan ba siya zaki ba karmu b'ata ma
juna lokaci 🙏🏻

My Number 08063830828

You might also like