0% found this document useful (0 votes)
393 views185 pages

IN KUNNE YA Ji PART 1 SODANGI

The document is a dedication and acknowledgment section of a book by Hajiya Hafsat C. Sodangi, expressing gratitude to various individuals and groups for their support. It includes a description of the cultural significance of the town of Adanta, particularly during the rainy season, and highlights local traditions and agricultural practices. The author emphasizes the importance of community and cultural events in fostering relationships among neighboring towns.
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as DOCX, PDF, TXT or read online on Scribd
0% found this document useful (0 votes)
393 views185 pages

IN KUNNE YA Ji PART 1 SODANGI

The document is a dedication and acknowledgment section of a book by Hajiya Hafsat C. Sodangi, expressing gratitude to various individuals and groups for their support. It includes a description of the cultural significance of the town of Adanta, particularly during the rainy season, and highlights local traditions and agricultural practices. The author emphasizes the importance of community and cultural events in fostering relationships among neighboring towns.
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as DOCX, PDF, TXT or read online on Scribd
You are on page 1/ 185

Idan kunne yaji…….

1
Sodangi

IN KUNNE YA
JI…

NA

HAJ. HAFSAT C. SODANGI

Haqqin Mallaka (M)


1
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Mallakar littafin na marubiyaciyar shi
ne.
Hajiya Hafsat Yunus Abdullahi Dabai.

GODIYA
Godiyata kullum ga Allah take
masanin yau da gobe, mai kowa
mai komai wanda ya halicci
mutum da aljan don su bauta
mishi.
Tsira da amincin Allah su
tabbata ga cikamakin Annabawa
shugaban manzanni Annabin
qarshe Muhammad (S.A.W) da
alayensa da sahabbansa da
waxanda suka bima tafarkinsa na
gaskiya har zuwa ranar qarshe,
wato ranar rarrbuwa tsakanin
qarya da gaskiya, “Alqiyama’
Ubangiji yasa mu dace.
Godiya mai xumbin yawa har
yanzu gareku makaranta littafina
na kusa da na nesa, na gode da
kulawarku, na gode saqonnin ku
da basa yankewa, na gode
2
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Ubangiji ya saka muku da alheri,
amin.
Hafsat C. Sodangi
07035586299

SADAUKARWA
Har kullum sadaukarwar
littafina za ta ci gaba da
kasancewa ta iyaye na, Malam
CHINDO Muhammad Sodangi, da
mahaifiyata Hajiya Fatima Musa
Sodangi, saboda xawainiyarsu,
tarbiyyarsu da kuma kulawarsu a
gare ni. Ubangiji ya saka musu da
alheri, ya qara musu yawan rai da
imani, ya qara musu lafiya da son
Annabin rahama Muhammad
(S.A.W).

TUKUICI
Tukuicin littafin na mijina
ubansu Maryam, Aisha, Yunus da
3
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Abdulmajeed. Alhaji Yunusa
Abdullahi Daban.
Allah ya saka maka da alheri,
amin.

JINJINA
Ga qanwata Hajiya Hadiza C.
Sodangi (Mrs. Nasir Idris Kiru)
Maman Idris da Aminu.

GORO
Ga qanina xan autan Hajiya.
Muh’d Kabir C. Sodangi
(ATBU Bauchi)

FATAN ALHERI GA
Hajiya Shafa’atu Argungu
Hajiya Saudatu Buhari
Hajiya Saratu Sada
Hajiya Mariya Ibrahim
Hajiya Dije Muskawa
Hajiya Umma Muhammad
Panisau

4
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Ubangiji ya saka da alheri na
gode.

KUNA RAINA
Hajiya Sadiya Jabbar
Hajiya Mami Xan Hassan
Hajiya Jamila Bature
Hajiya Aisha Balarabe (JAZAN)
Hajiya Mariya Sada Katsina
Hajiya Jummai Muh’d Kazaure
Hajiya Zainab Barau Potiskum
Hajiya Fatima Muh’d (NDA)
Hajiya Rakiya Abida Yazid
Na gode Ubangiji ya bar
zumunci, amin.

NA GODE
Hajiya Jamila Zokka ta gidan
redion Yola, Adamawa State.

GAISUWAR SADA ZUMUNCI


Sadia Muhammad Kankia
Zakiyya Abdullahi Katsina
5
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Samira Isyaku Zangon Dakata
Kano
Falila Kankia (Maman Abdul)
Hassana Abubakar Birnin
Kebbi
Halima Adam
Hafsat Muhammad rivers
Na gode.

INA GAISHEKI
Maryam Muh’d Keffi, Ubangiji
Allah ya baki lafiya, tare da sauran
musulmi baki xaya, amin.

YABO
Yabon naki ne, Hajiya
Rabi’atu Sani Madakin Gini.

GAISUWAR BANGIRMA
Uwargida sarautar mata
Rakiya Aliyu Xanjuma
Samira Abubakar Rambuwal
6
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Karimatu Gamawa

GAISUWA GAREKU
Balaraba Abubakar
Baraka Sani Zaira
Bilkisun Sokoto
Hadiza Umar Ahmad
Adamawa
Binta Xanjuma Unguwa Uku
Maryam Abubakar Adamawa
Nafisatu Abdulkarim Yola
Fadilatu Ibrahim Gumel
Ruqayya Usaini Zuru
Aina’u Nasir Getso
Fatima Adam Minna
Sai’ida Slisu Maikanti
Maryam Muhammad Zaria
Hauwa Idris
Suwaiba Hoza Birnin Kebbi
Zuwaira Xanbatta
Zainab Mani
Samira Tal’udu
Sa’adatu Jega
Nafisa Birnin Gwari
Maryam Yola
7
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Maryam Kabir Azare
Maryam Abdullahi Manga
Zainab Muhammad
Zainab Kabir Azare
Na gode da kulawarku.

Jinjina ta Musammn ga
Maxaba’ar
Ip & Computer services Kano
Saboda tsayawar su tsayin
daka wajen futo min da littafaina
Allah ya qaro cigaba Amin

LITATTAFAN SODANGI
UWAR MIJI
NA GA TA KAINA
RABON KWAXO
CIKAR ALQAWARI
WAYYO DUNIYA
ABU NAKA
YIWA WANI
TABBATACCEN AL'AMARI
KIFI NA GANINKA..
GANI GAREKA

8
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
ME ZAMU CE DA MAZA
MATA MASU DUNIYA
BIYAN BUQATAR RAI
HATTARA!
DAGA QIN GASKIYA
DA KAMAR WUYA
SHAMAKI
MAI UWA
DUK XAYA
MATA DA KICIN XINSU
WACE CE NI?
GARIN BANZA
AYI DAI MU GANI
WATA FUSKAR...
MATA DA KICIN XINSU
MIJIN TA CE

Har kullum littafan basu nufin


habaici ko yi da wani, abin nufi da
rubuta su kawai faxakarwa ne da
nishaxantarwa, don haka ina
neman afuwa ga duk wanda ya ga
wani abin da ya yi daidai da shi ba
da shi ake ba. Na gode.

9
Idan kunne yaji…….1
Sodangi

BABI NA XAYA

T sululun damina ne ko kuma in ce


lokaci ne na marka-marka kamar
yanda muka san ana kiran irin
wannan lokacin a wasu wurare.
Lokaci ne na tsakiyar damina,
saboda tansanin zuban ruwan sama
da ake yi mafi yawancin lokaci a irin
wannan lokacin za ka samu mutane a
takure suke, musamman ma dai ‘yan
kasuwa waxanda tsananin ruwan
sama kan takura musu ya hana su
gudanar da al’amuran kasuwarsu
cikin walwala ko annashuwa, saboda
qarancin mutanen dake samun
ziyartar kasuwanni don gudanar da
sayayya irin ta buqatun yau da
kullum.
Sai dai wannan bayani da ya
gabata savani ne da abin da yake
gudana a garin ‘ADANTA’
Adanta gari ne da mutane suke
zaune a cikin shi suka saba rayuwa a
cikin ruwa rani da damina, duka
wurinsu lokacin ruwan sama ne, don
kuwa su daminarsu kan xauke su har
10
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
tsawon watanni goma ne, wannan
kashi tamanin cikin xari na
rayuwarsu suna yin shi ne cikin
ruwa, ko in ce cikin damina.
Bisa wannan dalili sai suka zamo
sunyi matuqar sabawa da ruwa,
zubar ruwan sama bai hana su
gudanar da harkokin su, inda ba
ruwan saman ya yi matuqar yin yawa
bane.
Garin Adanta gari ne mai
matuqar kyau, yanayin shi mai ban
sha’awa ne saboda yawan bishiyoyin
shi da korran ciyayi sharr! A
kowanne likaci gari ne na ni’ima
qwarai, saboda gari ne dake samun
ruwan sama ba tare da anyi wani
hadari mai tsanani ba, ko kuma iska
mai tayar da hankali, gashi kuma
wani lokaci sai a wuni a kwana ana
zubar da ruwan.
Ga wanda ya san kudancin
Nigeria, ya san wannan bayani da
aka yi kan garin Adanta bai zamo
wani abin mamaki ba, ko mutum bai
san kudun ba kuwa, to ya san ba zai
kasa karanta bambancin yanayin
11
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
dake tsakanin kudu da arewa ba a
makaranta inda su suke da daminar
da tsawonta kan kai watanni goma,
wani lokacin ma har sha xaya.
Wannan shine dalilin da ya sa su
‘yan kudu basa iya noma irin kayan
amfanin da muke nomawa a arewa,
irin su wake, gero, masara, dawa,
shinkafa, alkama, gyaxa, auduga da
kuma kayan lambu irin su tumatur,
attarugu, tattasai, albasa, kabeji da
abubuwa da yawa da ba za su iya
lissafuwa ba.
Wannan dalili ne ya qara haifar
da qarin bambancin dake tsakanin
kudun da arewa ba ta hanyar xabi’a
ko al’ada ba kawai har damina, don
kuwa yayin da mu a arewa cimarmu
ta fi raja’a kan masara, shinkafa,
gero, acca, dawa, alkama, wake da
makamantansu.
Su a can su kan ta’allaqa ne kan
rogo wanda suke sarrafa shi ta
hanyoyi da yawa, irin su garin kwaki,
da loi-loi wanda suke yin shi tamkar
tuwo, sai kuma sakwara, rogon da
kuma na doya. Ita ma kuma doyar
12
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
tasu tana da bambanci da irin tamu
ta arewa.
Sai kuma abin da suke samu a
jikin kwakwa, plaintain waxanda
suke wata hanzarce kuma ta samun
kuxaxen su tsakaninsu da arewa.
A xabi’a ta halayya kuwa zan iya
cewa mafi yawancinsu ba masu jurar
wahala ko xawainiya bane da yawa,
don kuwa kusan kowa kan noma
gonar shi ne ta gadon iyaye da
kakanni, don ci a gida ba don
sayarwa ba.
Garin Adanta gari ne ba mai faxin
qasa ba sosai, saboda ruwan da ke
zagaye da shi ya yi mishi zobe ya mai
da shi tamkar tsibiri, ko kuma ya yi
kama da tsibirin wato ya zagaye shi
ta kusurwowi guda uku.
Sai dai kuma sun yi sa’a rashin
faxin qasar su bai zamo musu wata
matsalar ba, saboda kasancewar
garin nasu gari mai yawan ni’ima, an
kuma albarkace shi da ‘ya’yan itace
irin su lemo, abarba, ayaba, da kuma
dabbobin ruwa iri daban-daban.

13
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Wayewar gari yau an tashi ne
cikin wani irin yanayi na hadaran-
kadahan, wato babu tsananin rana
babu kuma tsananin sanyi, yanayin
mai matuqar daxi ne da kuma ba da
sha’awa.
Daga inda duk kuke kuna iya
ganin zirga-zirgar jama’a cikin
walwala da farin ciki, saboda
kasancewar ranar yau xin nan ce
muhimmiya ta ko’ina mutane sai
fitowa suke yi suna harkokinsu da
kuma shirye-shiryen zuwan yau don
karvar baquncin jama’ar garin dake
maqwabtaka dasu wato garin
ALIMINI Tawon.
A duk lokacin da shekara ta
zagayo a kuma irin wannan lokacin
na tsululun damuna, gaba xaya
garuruwan dake maqwabtaka dasu
guda takwas waxanda tarihi ya nuna
asalinsu da amutum xaya ne, wato
uba xaya, yana shirya qasaitacciyar
wasa da kan yi dalilin haxuwar su
wuri xaya don sada zumunci da qara
qarfafa shi a tsakanin su.

14
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Ga al’ada kuma in anyi wasan a
wannan garin yau, to a washegari
kuma sai ayi shi a wani garin, a haka
a haka har sai ayi ta zagayawa, a duk
lokacin da qarshen wasu ya zo to a
kan baiwa gari ko mutanen garin da
suka fi jarumtaka kyauta ta
musamman don girmama
jarumtakarsu ta hannun babban
sarkinsu.
Wannan wasa kuma ba komai
bane face damben kokawa.
Wasan kan zamo wata hanya ta
nuna bajinta tsakanin garuruwan,
kowa yana qoqarin burgewa don ya fi
suna da fice, don haka ne ma za ka
samu inda duk aka je wasan za su yi
matuqar qoqarinsu wajen ganin sun
burge bikin da nau’o’in abinci iri-iri.
Masu hali daga cikin jama’ar garin
ma za ka samu har akuyoyi suke
yankawa.
Ba ta hanyar ciyarwa kaxai
bajintarsu ta tsaya ba, su kan nuna
bajinta har ta hanyar hana ruwa,
wati hana ruwan sama ya sauka.
Saboda su kan xauka saukar ruwan
15
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
sama a daidai lokacin da ake
gudanar da wasan abin kunya ne
babba ga gari mai masaukin baqi.
Kan haka kullum daddawa
gwanayen riqe ruwan sama su hana
shi sau kan yi aiki tuquru wajen
ganin sun riqe ruwan har ayi wasan a
gama ba tare da sun bari xigon shi
ya sauko ba, don su samu su fidda
garinsu daga jin kunya ko kunyata a
gaba ‘yan adawa.
Lokacin agogo ya nuna qarfe
huxu daidai, samari da ‘yanmatan
garin da wasu daga cikin daddatawa
sai zirga-zirga suke yi, kusan kowa
ka gani a cikin sauri yake don gudun
kar a fara wasan bai samu isa filin da
ake gudanar da wasan ba.
Maazi Nleem Counpound, wato
harabar gidan na Maazi Nleem shine
harabar da ta fi kowanne girma a
garin, don haka a duk sanda aka
tashi gudanar da irin wannan wasan
ko wata gasa a qofar gidan ake
gudanar da shi.

16
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Duk inda ka waiwaya jama’a ne
bila adadin sun zagaye wani babban
fili da aka kewaye don yin dambe.
Samari da ‘yanmata kowa ya sha
ado ana tsaye, yayin da can gefe
kuma ‘yan wasa ne suke ta faman
mummotsa jikinsu don shiryawa
damben, ya yin da wasu kuma ke
tsattsaye mafi yawancinsu sanye da
gajejjerun wandona iya gwiwa, wasu
kuwa bante wanda aka yi shi da
ganyen kwakwa.
Wasan duk wani wanda ya
kamata ya halarci gasar yana wurin,
ciki kuwa har da Salim Sulaiman Jalo
xan asalin Jihar Adamawa, wanda ya
je garin Adanta a dalilin hukumar
yiwa qasa hidima ta qasa ta tura shi
garin don yi hidimarta, hakan kuma
ya zama sanadin da ya zama tamkar
xan garin saboda zamowar shi
ma’aikaci da haziqancin shi ya yi
dalili da ya samu aiki a bankin da ya
yiwa hidimar.
Kyakkyawan saurayi dogo fari sol
ma’abocin kwarjini a dalilin cikar
halillatar shi, kyakkyawan saurayin
17
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
da ya laqanci kwalliya da jurar kashe
kuxi don yin kwalliyar, ga tsafta ga
qamshin shi na musamman a kowane
lokaci, kallo xaya za ka yi mishi ka
gane xan arewa ne, asalin wanda ya
fito daga qabilar Hausa/Fulani.
Salim yaro ne da ya taso cikin
gida na tarbiyya, addini da kuma
sanin qima da darajar xan Adam.
Mahaifinsa Malam Manu ba wani
mai wadata bane, sai dai yana da
matuqar qoqari a kan harkar riqe
iyalinshi. Xan koli ne dake sai da
kayan kolinshi a cikin kasuwar
Jimeta, mutum ne mai iyali don ko da
yawa, da mace guda xaya Inna.
Ubangiji ya albarkaci auren nasu
da ‘ya’ya xai-xai har goma sha xaya,
waxanda suka yi musu tarbiyya suke
kuma rayuwa qarqashin kulawa
sosai, don babu wanda ba ya zuwa
makarantar Islamiyya, Allo da kuma
ta boko.
Iyaka dai su matan karatunsu kan
tsaya ne daga primary sai ya yi musu
aure, saboda a wurinshi ita mace

18
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
tsaida ita yin karatun boko wani vata
lokaci ne kawai sai dai ‘ya’ya maza.
Tsayuwar hakan da ya yi ne ya yi
dalilin da Salim ya samu damar yin
karatun boko, kasaancewar shi
babban xa a jerin ‘ya’ya maza uku da
suke gidan, amma na uku a gurin
haihuwar gidan mai ‘ya’ya goma sha
xaya uku maza takwas kuma mata.
Duk da kasancewar iyayen Salim
ba masu wadata bane sun nuna mishi
gatan da ya sanya shi zamowa cikin
xalibai masu rufin asiri, in ba ka san
gidansu ba to baka sanin iyayen shi
talakawa ne, saboda qwalisar shi,
gashi kuma duk wani abin da aka
nema a makarantar yana cikin
xaliban farko da suke gabatar da shi.
Inna Wuro tana matuqar son
Salim, shima Salim xin ya san hakan,
kowa ma ya san haka, komai ya
nema tana ba shi, shima kuma yana
matuqar sonta.
Sai dai duk da wannan da Inna
Wuro ke yiwa xanta na komai ya
nema za ta yi mishi saboda
kasancewar ta mai kiwo ce, tun daga
19
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
tumaki, awaki, talo-talo har kaji,
kiwon kuma ya karve ta, Malm Manu
a tsaye yake qwarai wajen tarbiyyar
xan nashi, ya bashi ingantaccen ilimi
na Arabiyya da boko, ya kuma
tarbiyantar da shi kan al’amura masu
yawa kamar dai yanda aka san uba
na qwarai yana yi.
Gatan da uwa ke yiwa Salim bai
hana shi tsayuwa ya yi karatun shi
ba, an kuma yi sa’a fasihi ne, don
kuwa ya kammala karatun shi na
Jami’a ne da takardarshi ta first
class. Wanda hakan ne ya qara zama
sanadin da lokacin da ya gama
bautar qasa a bankin da ya tura shi
na Guarantee Trust Bank, suka nemi
ya tsaya a matsayin cikakken
ma’aikacin su, tare da yi mishi tayi
na albashi da alawus mai yawa, ban
da kuma dama yana da wani tayin da
jami’arshi ta ba shi na yaje ya yi aiki
tare da ita kamar dai yanda aka san
manyan makarantu suna yiwa
haziqan xalibansu.
Tayin da aka yiwa Salim na
komawa kudu yin aiki bai yiwa
20
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
mahaifiyar Salim daxi ba, saboda ita
kam ta fi sha’awar ya zauna a gida
ya yi aikin shi, a kuma yi mishi aure.
Don haka ta gabatar da maganar
ga mijinta don ya hana shi tafiyar
bisa hujjar da ta bayar na nisa da
kuma zama cikin mutanen da ba
naka bane.
Shi kuwa Malam Manu bai xauki
hakan a matsayin wani dalili da zai
sa a hana Salim yin aiki da yake so
ba, don haka sai ya ce mata.
“Ai namiji ne, duk inda ya kamata
ya tafi kan aikin shi zai iya tafiya,
tunda ai ci gaba yake nema. Karatun
boko kuwa dama dalilin yin shi kenan
neman ci gaba a rayuwar duniya”.
Game da xaukan xabi’un da ba
nashi ba kuwa gaba xaya Malam
Manu share maganar ya yi, saboda a
ganin shi a irin tarbiyyar da aka yiwa
Salim xin bai kamata a ce an ji tsoron
wani abu mummuna game da shi ba,
musamman da yake ko a sanda ya yi
hidimar qasar shi ya iya tattala kuxin
alawus xin shi ya zo gida ganin
iyayen shi har sau biyu.
21
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
A farkon zaman Salim a garin a
lokacin zuwan shi bautar qasar shi
xin, wani irin mutum ne mai qoqarin
ganin ya tsare mutuncin tarbiyyar da
aka yi mishi ta addini da kuma
al’adarshi ta xan arewa. Bai yarda ya
saki jiki da kowa ba balle ya shiga
wani abin da bai kamace shi ba.
A wancan lokacin burinshi guda
xaya ne wanda yake kwana da shi
yake tashi da shi, shine na ya
kammala bautar qasar shi ya koma
gida ya je ya kama aikin da jami’ar
shi ta yi mishi ta yi, ya samu ya rinqa
kula da taimakon iyayen shi uwa da
uba, da yake ya san babu xawainiyar
da basu yi ba kan karatun nashi.
Yadda ya san Inna Wuro ta yi
hidima da xawainiya da shi, haka
kumaa ya san baban shi Malam Manu
ya yi, don a kan idon shi ne Malam
Manu ya tava sai da gonar shi ta
gado ya karvi kuxin ya damqa mishi
su a hannun shi yaje ya yi hidimar
karatun su.
Burin Salim bai wuce samun
dama na ya kyautatawa iyayen nashi
22
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
ba da kuma duk wani wanda yake da
alaqa a kanshi, sannan aikin da zai yi
a cikin jami’ar tasu zai ba shi dama
da zai ci gaba da qara ilimin shi.
Sai dai yana jin tayin albashi da
alawus xin da bankin Guarantee suka
ba shi sai gaba xaya hankalinshi ya
tashi daga komai, ya ga babu abin da
yake so irin zuwa kudu ya zauna ya
yi wannan aikin, yana son kuxin da
suka yi tayin albashin, in yaso duk
wata ya rinqa yiwa iyayen nashi aike
tunda ai hakan ma wata dama ce da
zai kula dasu sosai da sosai.
A farkon kama aikin Salim a can
wanda ya yi dalilin da Guarantee
suka tura shi branch xinsu na garin
Adanta, yana nan a yanda yake
aikinshi kaxai ya sanya a gaba, bai
da wata harka in ba ta aikin shi ba, a
kowane lokaci in baya gun aiki, to
yana gidanshi.
In har zai fita daga gida kuwa, to
mafi wurin hirar nashi bai wuce na
Jinjiri mai tsire ba, xan arewa ne
dake garin yana sana’ar tsire.

23
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
A wannan lokacin Salim yana
karvar albashinshi yake xaukan abin
da zai iya isar shi zuwa wani watan,
ya dunqule sauran ya turawa
mahaifin nashi, hakan kuma bai hana
shi in ya samu hutun shi ya kama
hanya ya tafi gida don yin hutun
nashi tare da iyaye, ‘yan’uwa da
kuma abokan arziki.
Wannan duka ya faru ne shekara
ta farko da kuma ta biyu, har ma ta
uku da fara aikin nashi. Amma da
al’amura suka ci gaba harkoki suka
qara buxewa, kuxi masu nauyi suka
fara shiga hannu, duniya ta fara
samuwa, sai al’amura suka fara
sauyawa.
Hausawa suka ce wai, ‘yau da
gobe, mai sawa a mari amarya, ko
zama da maxaukin kanwa mai kawo
farin kai”.
Sannu a hankali Salim sai ya
soma yin abokai ‘yan gayu, ko in ce
‘yan gataa masu iyayen da suka
tsaya musu. Sannu a hankali kuma
sai al’amura suka soma sauyawa,
sannu a hankali kuma sai shim aya
24
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
miqe qafa ya warware ya shiga
gudanar da al’amuranshi kamar
yanda suke yi, tamkar dai ya mance
shi waye? Ko kuma daga ina ya yake?
Shi mai qyamar barasa sai gashi
shima yana kwankwaxar ta,
‘yanmata kuwa ba a maganarsu, sai
ya zamo babu wata mahaxa wato
joint ko hotel-hotel xda bai sani ba
ko baya zuwa.
Kasancewar shi kyakkyawan
saurayi ma’abocin farar fata da kyan
kwalliya, ga kuma matan wurin da
son farin mutum, sai ya zamo nan
kusa duka babu inda ba a san shi ba,
garuruwa irin su Umueche, Erume,
Ogbodo da sauransu, saboda su xin
garuruwa ne da suka yi fice da
kyawawan ‘yanmata.
Qarfe huxu da minti goma sha
biyar alqalin wasa ya buga qararrawa
don fara gudanar da wasan, jaruman
guda biyu suka bayyana a fili, kana
ganinsu ka san majiya qarfi ne
dukkansu da suka shiryawa gasar, za
kuma a fara wasan ne tsakanin
Chibenhem na garin Adanta masu
25
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
masaukin baqi, da kuma Olubube xan
asalin garin Alimini.
Bayan an buga qararrawar
farawa ne maza suka haxu aka fara
gwabzawa, su kuma makaxa da
mawaqa suka kama aikinsu na kowa
ya zuga gwanin shi don ya qara
himmar da zai yi nasara kan abokin
karawar shi.
Ana cikin haka jaruman suna ta
tsima suna kaiwa juna cafka ta
ko’ina, ana hakan ne kawai sai sa’a
ta juya wajen Chibuenhem, Ubangiji
ya taimake shi ya danfara shi da
qasa.
Wuri ya xauki sowa da tafi,
‘yanmata da samari sai ihu suke yi
suna rungumar juna su da suke
saukar baqi jaruminsu ya yi kaye.
Wata mace ta yi ihu ta yi tsalle ta
faxa fili ta shiga yage kayan jikinta
ta yi fatali dasu, ta kama yin rawar
tasu tunvur don murna. Su kuwa
makaxa suka yi maza suka dafa mata
abin da ya yi matuqar burge samari
suka shiga tsima.

26
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Ana cikin hakan ne kawai babu
zato babu tsammani sai kawai aka ji
saukar ruwan sama kamar da bakin
qwarya shaaaa!
Abin da ya tarwatsa taron ba tare
da an tsaya an ga qarshen wasan ba,
aka yi ta arawa a cikin na kare ba
tare da an gama kallon gasar ba, aka
nufi gidajen abokanan arziki.
Nan take kuma aka kama
gudanar da girke-girken alfarma
cikin farin ciki da annashuwa saboda
nasarar dasuka gani duk kuwa da
sun ce turo musu ruwan aka yi don a
vata musu wasan daga garin
Umueche don ganin da suka yi za su
yi nasara saboda sune abokan
adawarsu.

27
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
BABI NA BIYU

B
a kasafai yake sha ya bugu ba
a cikin kwanakin aikin shi,
saboda sanin irin yanayin aikin
shi dake buqatar sammako. Sai dai a
daren jiya hakan bai yiwu ba saboda
irin abokan harkar shi da suka raba
dare tare dasu ana holewa, wanda
hakan ya zama sanadin makarar shi
a yau talata.
Cikin faxuwar gaba mai yawa ya
farka daga barcin nashi ganin hasken
da ya bayyana a xakin nashi, da suari
ya ture Oluchi dake kwance a fiye da
rabin jikinshi tare da balbale ta da
faxa saboda rashin tashin shi da ba
ta yi ba.
Ya faxa toilet cikin gaggawa ya yi
wanka ya fito, ya yi sallah wacce ita
kaxai ce abin da ya saura mishi
wanda bai daina ba, sai ko azumin
watan Ramadan.
Yana idarwa ya jawo brush xinshi
ya matsa man wanke baki na
sensodyne a jiki, ya yi wanka ya fito
yana xaure da tawul a jikinshi, ya yin

28
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
da yake riqe da wani a hannunshi
yana goge kanshi da jikinshi.
Bai wani vata lokaci ba kayanshi
kawai ya sanya, baqaqen suit da
longlleve mai ruwan bula da necktie
xinshi.
Oluchi ta buxe ido za ta yi mishi
magana cikin magagi yasa qafa ya
tokare ta, wanda hakan ya yi dalilin
wattsakewar ta garau.
“Ai kin san dokar kwana a gidana
shine za a yi sammakon tashina daga
barci a kuma yi mini abincin karyawa
da kuma na rana kafin in dawo”.
Bai saurari amsarta ba ya suri
robar ruwan swan guda xaya ya
kwankwaxe ya jefar ya fita.
Ba qaramin sa’a ya yi ba, don
kuwa yana yin parking xin motar shi
aa wurin da ya saba ajiye ta ya
hango ta M.D xinsu yana shigowa,
don ma shima a yau xin makarar ya
yi.
Da suari ya shige cikin office
xinsu inda ya smau Nonso abokiyar
aikinshi tana fama da customers, ya

29
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
yin da wasu suke tsaye a gefe alamar
shi suke jira.
Nonso ta xago kai ta kalle shi a
lokaci guda kuma tana cike wani cek
xin dake gabanta, suna gaisawa ta ce
mishi.
“Amma dai ka yi sa’a, don yanzun
nan aka turo daga head office cewar,
report xin da ka bayar na wancan
watan kan account xin Alor local
governmenta akwai kuskure a ciki, suna
buqatar sabon bayani da bincike
cikin gaggawa”.
Salim ya zaro ido yana kallon
Ninsa dake yi mishi bayani tare da
dafe kai, idan aka ce ya yi kuskure a
kan wannan riport xin ba wani abin
mamaki bane, don kuwa idan bai
manta ba ya bayar da report a
safiyar litinin xin da ta wuce, bayan
ya yi kwana biyu a hotel xin
Delacruise shi da sabuwar
budurwarshi Lawrenta, wanda hakan
ne ya yi dalilin da ya yi aikin a
gaggauce ba tare da yaa tsaya sake
dubawa ba ya je ya miqa, gashi kuma
idan bai yi sa’a ba zai zamo mishi
30
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
matsala a kan aikin nashi, duk da shi
xin ya yi fice qwarai wajen fitar da
irin waxannan report xin.
Ya xago kai ya dubi Nonso bayan
ya gama tunanin shi ya ce, “To me
kika ce musu Nonso?”
Ta xan xaga kafaxa tare da tave
baki ta ce, “Na ce ka fita city branch
don gudanar da wani aiki, idan ka
dawo za ka kira ka yi musu bayani.
Don haka sai ka bari zuwa 12:pm xin
nan sai ka kira ka yi musu bayani”.
A hankali ya yi ajiyar zuciya ya ce
mata, “Na gode Nonso”.
Ilai kuwa ba a yi mintuna talatin
ba wayaarshi dake ajiye a gefen
tebur xin shi ta faara ruri, ya xauka,
kira ne daga ofishin M.D.
Cikin hanzari ya ajiye takardar da
ke riqe a hannunsa ya zari kot xinshi
dake rataye a bayan kujerar da yake
zaune yana sakawa tare da baiwa
mutane biyu dake zaune kan kujeru
na jiran shi uzuri, ya fita zuciyarshi
tana mai tunanin abin da zai tarar a
wurin M.D nasu.

31
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Bai samu sakatariyar shugaban a
wurin zaman ta ba, don haka
qwanqwasa qofar kawai ya yi aka ba
shi izinin ya shiga.
Dogo ne baqiqqirin kakkauwara
mai zane kwaya-kwaya a fuskarshi,
wanda yeke bayyanar da asalin shi.
A.A Adedigha, abin da yake rubuce
kenan jikin wani abu mai kyau dake
ajiye kan teburin nashi.
Yana tsaye jikin wata kabinet
riqe da takardu a hannun shi lokacin
da Salim xin ya shiga ofishin. Ya
gaishe shi ba tare da ya zauna ba ya
waiwayo yana kallon shi tare da ba
shi izinin zama.
Sannan ya jawo kujerarshi shima
ya zauna, ya kai mintuna uku da
zama yana haxe da hannayen shi
guda biyu a kan tebur xin kafin ya
buxe baki ya ce.
“Mr. Salim”.
Yanayin da ya kira sunan Salim
xin ne ya sashi kasa xagowa daga
sunkuyon da ya yi.
“A farkon zuwan ka wurin nan kai
xin wani irin haziqin ma’aikaci ne mai
32
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
matuqar qoqari da sadaukar da kai a
kan aikin ka, in ban manta ba
wannan watan da ya wuce ka cika
shekaru huxu ne da fara aiki a nan,
wanda a cikin shekaru ukun ka na
farko duk kana cikin haziqan
ma’aikatanmu guda uku da ake
fitarwa daga main branch xinmu ayi
musu kyauta ta musamman da ake
yiwa haziqan ma’aikatan shekara,
saboda qwazunsu da kuma qwarewar
su.
Amma a bana baka samu ba,
baka cikin haziqan ma’aikatanmu na
wannan shekarar, ban ga kuma
alamar hakan ya dame ka ba, saboda
na lura kana canzawa kana da wani
abin da ka sanya a gabanka, ko da
ban san shi ba kuma zuciyata tana
gaya min cewar ba alheri bane.
Ina yi maka wannan maganar ne
saboda kishin da nake da shi a
kanka, ni ba mutumin arewa bane
amma na zauna a arewa, na san
xabi’un mutanenta, irin tarbiyyarsu,
na kuma san da a can kake a gaban
iyayenka ba za ka yi waxannan
33
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
abubuwan ba na wasa da aiki ka
canza halinka.
Ko da ba wani mu’amala ne a
tsakanina da kai wacce ta wuce
mu’amalar aiki, ni xin na fahimci ka
canza daga asalin halinka da ka zo
da shi garin nan, don haka nake yi
maka magana tare da qara jaddada
maka cewar, shi aikin banki wani irin
aiki ne da bai xaukar kuskure balle
ya yarda da yin gyara, don haka ka
kula”.
Duk da cewar Mr. Adedighba bai
fito fili ya cewa Salim komai game da
report xin nashi ba ya fahimci cewa
shi xin ya yi mishi hannunka mai
sanda ne, ya kuma gane cewa yana
sane da abin da yake yi, tunda ya
fara canza halayen nashi.
Kuma bai tava sanin cewar akwai
wani wanda ya gane abin da yake
ciki ba sai ko yau. Haka nan duk
zaman shi da Mr. Adedigba bai tava
sanin ya san kalmar “zo” ba sai yau
da ya rattabo mishi wannan dogon
bayanin cikin harshen Hausa.

34
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Jikinshi ya yi matuqar yin sanyi,
ya zauna kan kujerar shi tare da dafe
kai saboda tsananin sarawan da yake
yi, babu kowa a office xin alamar
Nonso ta sallami masu jiran nashi, ita
kuma ta tafi break.
Duk da rashin karyawar da bai yi
ba babu alamar yunwa a tare da shi,
illa tunane-tunanen abubuwa. Ya
juyo da fuskantar desktop computer
xin dake gabanshi wacce take kan
tebur xin shi ya kunnata tare da buxe
sukutum xin fayel xin da yake
mallaki na Akor Local Government.
Sake sabon report ya yi, sa’ar shi
guda xaya akwai fahimta mai yawa
tsakaninshi da Nonso, dan haka sai
ta taimaka mishi ta haxa customers
xinshi da nata duk ta sallame su.
Da ta gama kuma ba ta wuce ta
tafi ba, sai ta sake tsayawa ta
taimake shi aikin da yake yi, sai
wajen qarfe shida sannan ta yi mishi
sallama ta tafi, aka barshi nan daga
shi sai masu gadi duk da Nonso ta yi
qoqarin su tafi tare gobe in yaso sai
ya qarasa bai yarda ba, saboda
35
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
jikinshi ya riga ya yi sanyi da abin da
ya faru da shi, wanda hakan ba
komai bane illa alama na shi xin ya
fara wasa da aikin shi.
Sai wajen qarfe goma ya rufe
computer tashi tare da niyyar gobe
ya qara yin wani binciken kafin ya yi
printin xin takardun ya aike dasu.

BABI NA UKU

Y
a buxe bayan motarshi tare da
jawo kot xinshi, sannan ya rufe
ko’ina ya nufi barandar flat
xinshi wacce sai ka buxe ta kafin ka
isa asalin qofar xakin nashi.
Wani irin mummunan faxuwar
gaba ne ya same shi, saboda ganin
abin da bai yi zato ba kuma bai yi
tsammani ba, na duk gilasan gidan
na qofofi da winduna a farfarshe.
Ya tsaya yana qarewa wajen kallo
tare da tunanin abin da ya kawo
hakan.
Ya waiwayo jiki a sanyaye tare da
amsa kiran da ya ji anyi mishi daga
bayanshi, Baban Amedi ne.

36
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
“Mun yi ta jiranka tun xazu baka
dawo ba shiru-shiru, yanzu ma
motsin tsayuwar motar ka na ji na
fito”.
Salim ya kalle shi ba tare da ya
jira ya yi mishi bayani ba ya tambaye
shi.
“Me ya faru ne Baban Amedi na
ga haka?”
Ya ce, “To, ni dai na dawo ne
daga aiki na zo na samu suna yi ban
san abin da ya haxa su ba”.
Takaicinshi ya kama Salim ya na
ja mishi bayanin da yake yi, cikin
qosawa ya tambaye shi.
“Su waye kuma me suka yi Baban
Amedi?”
Gaba xaya hankalinshi a tashe
yake, ya qosa ya ji abin da ya faru da
gidan nashi.
Ya gyara tsayuwar shi ya ce, “Ka
yi min bayani kawai kai nake
sauraro”.
Ya ce, “To na dawo ne na same
su waxannan ‘yanmatan naka guda
biyu ne suna dambe a xakin, har ita

37
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
wannan ‘yar farar da na ga ta kwana
jiya ta yanki xaya da kwalbar giya”.
Wani irin abu ne ya taso ya
tokarewa Salim qirjinshi, take kuma
ya ji gumi yana keto mishi duk da
xan yayyafin da ake yi saboda
tsananin vacin rai.
“To wace xayar?” Cikin qarfin
hali ya yi tambayar.
Baban Amedi ya ce, “Ban santa
ba, amma dia na ji kamar tana cewa
‘yan sandan da suka zo tafiya dasu
wai sunanta Lawrenta”.
“Yan sanda ka ce Baban Amedi?”
Ya ce, “Eh, ai ma sa’a aka yi
Chisa ya yi maza ya je ya kira ‘yan
sandan, don da a ba san abin da zai
faru ba tunda babu yanda ba a yi ba
a raba su abin ya gagara, damben
nasu ai ba qarami bane. Kai dai
tunda ka dawo a makare, to ka je
kawai ka huta gobe da safe sai ka je
can police station, don sun ce suna
son ganin ka a wurin su ka je ka yi
report”.
Salim ya juya jiki a sanyaye ya
zaro mukulli da nufin buxe qofar
38
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
dake rufe, yana tava ta ta yiwo
kanshi da sauri ya kauce mata ta nufi
qasa ji kake duuum! Ta faxi alamar
dama jinginata aka yi.
Yana shiga xakin ya qara hsiga
cikin wani irin yanayi na qunci da
baqin ciki.
A hankali ya kai mazaunan shi
kan kujerar dake xakin yana qarewa
falon kallo cikin qunan rai. Babu wani
abu mai amfani da ya saura in dai
mai fashewa ne, komai ya yi raga-
raga an fasa shi.
T.V Plasma, home thearter, glass center table,
komai ma babu saura. Zaman wurin
ya ishe shi ya miqe ya nufi can cikin
kicin xin don ya girka abin da zai ci.
Nan ma a tarwatse yake an
farfasa komai, kayan abincin dake
kicin xin ma an hargitsa komai wuri
xaya, manja da mangyaxa da omo
tare da sugar da gishiri duk sun
gauraya wuri xaya.
Wani sabon baqin ciki ya sake
kama shi, ya ga babu wani abin da
zai dace da shi irin hanzarta barin
gidan, don haka cikin sauri ya nufi
39
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
xakin kwanan shi ya buxe wardrope
xin dake xakin ya jawo suit guda
xaya brwon da longslive xaya da kuma
brown takalmi sau ciki, ya jawo qofar
ya fita ba tare da ya tsaya kulle qofar
falon ba ya shiga motar shi ya yi
tafiyar shi.
Tafiya yake yi a cikin motar tare
da tunanin ko ya tava shiga cikin irin
wannan matsanancin vacin ran?
Ya ja wani mummunan tsaki tare
da tunanin ko wacce irin rayuwa ce
wannan? Oho!
Mintuna goma sha biyar ne daidai
suka kawo shi qofar shiga hotel xin
Dela Cruise, ya fito ya rufe qofar
motar shi ya shiga TAKE BAR xin su
wato mashaya.
Yarinyar tana hangoshi ta taho
da saurinta ta tsaya a gaban shi.
“Sir. how many Bottles?”
Ya xaga hannu ya ware mata ‘yan
yatsunshi ta gai gida biyu, sannan ta
juya ta tafi da sauri don cika umarni
da ya ba ta.
Ba yau ya saba zuwa ba, don
haka ta san wacce yake ta’ammali da
40
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
ita, tana tsaye gabanshi tana qoqarin
buxe xaya daga cikin kwalaben biyu
da ta dire a gabanshi, shima yana
qara ba ta wani umarnin.
“Hot meat pepper soup I plate and I plate of
oleporollo mixed”.
Take ta sake juyawa don
hanzarta biyawa costoman nata
buqatar shi.
Yana zaune wurin tare da
abubuwan da service ta kawo mishi
amma ya kasa tava komai balle ya
gwada kai wa bakinshi, saboda kai
kawon da zuciyarshi ke yi.
Ya xaga ido ya kalli danqareren
agogon bangon dake sagale a jikin
bango, sha xaya da rabi da minti
biyar, wato dai sha biyu kenan saura
minti ashirin da biyar.
Ya qara kallon tebur xin dake
gaban nashi, babu ko shakka idan ya
ce zai sha barasa a yanzu, to zai
makara zuwa office, don in har ya
yarda ya fara sha to bai san adadin
kwalaben da zai sha tuttula ba.
Yana zaune a wurin ya yin da
zuciyarshi take ta faman saqe-saqe
41
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
kan abubuwan da suka faru da shi a
office yau, bai kai yankewa ranshi
irin matakin da zai xauka ba, sai
kawai ya hango Prisca tana shigowa
wurin.
A da ko in ce a baya Prisca tana
daga cikin ‘yanmatan shi da yake
matuqar ji dasu, kyakkyawa ce
qwarai ta kuma iya tafiya haxaxxiya
ce, gata gwanar iya kwalliya.
A yau ma kuma tana sanye ne da
wata irin riga doguwa baqa, tsawon
ta ya tsaya mata ne iyakacin rabin
cinyarta, ilahirin bayanta a buxe
yake har zuwa kan kwankwasonta,
gaban rigar kuma daga qasan
qirjinta an tsaga shi anyi mishi wani
ado da wata irin igiya mai ruwan
gwal, duk da rigar mai dogon hannu
ce ta saka wani irin warwaro qato
shima kuma mai ruwan gwal. Haka
nan kuma ‘yan kunnen ta da
takalmin qafarta da ya fi kama da ta
hau dutu dukansu masu ruwan gwal
xin ne.
Bai san dalili ba, a yau yana qare
mata kallo sai kawai ya ji bai da
42
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
buqatar ta, saboda sai yake jin
tamkar duk wata mace ma a yanzu
kamata kawai ya yi ya fita harkarta
tunda dai ya gane su, su xin matane
da basu san ciwon kansu ba, basu
san ya ya ake yiwa wanda ake so ba
don a faranta mishi rai, mu’amala
dasu ba komai bane face neman wa
kai sanadi na haxuwa da baqin ciki,
ba cin nan da kuma sanadi na asarar
dukiya, don haka ya qudurarwa
ranshi fita harkarsu daga yanzu yana
ganin babu wani abin da zai sake
haxa shi dasu.
Ta jawo kujerar dake kusa da shi
ta zauna, bayan ta xan sumbace shi a
gefen kuncin shi guda biyu duka.
“Oh! Derling me ya same ka haka
na ga tamkar baka jin daxi? Ina fata
dia komai lafiya”.
Bai amsa mata ba, bai kuma
canza yanayin fuskarshi ba, haka ita
ma bai dame ta ba don ba yau ta fara
sanin miskilancin shi ba.
Ta jawo xaya daga cikin kwalaben
giyar dake ajiye a gabanshi ta buxe
ta fara tuttulawa a cikin kofin glass
43
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
xin dake ajiye kan teburin ta kuma
yafito service da hannunta ya iso.
Ta ce mishi, “Kwalba huxu”.
Ya juya da sauri don kawowa. Ya
yin da ita kuma ta juyo wajen Salim
don yin magana da shi.
“Kai kam ka fara lalacewa, ko
kuma son kuxi ne yake qara yi maka
yawa oho, in ba haka ba kamar kai
da kake odar kwalba goma sha biyu
ka kwankwaxe ta zauna lafiya a cikin
ka daram shine yau kake odar
kwalba biyu, in ba kafirin son kuxi da
lalacewar da ta fara smaun ka ba
mene ne wannan?”
Kafin Prisca ta gama tuttula
ruwan barasan cikin kofin a karo na
biyu, tuni har Salim ya xan fara yin
nisa.
Cikin mamaki ta xaga ido ta bishi
da kallo baki a buxe cikin tsananin
mamaki da kaxuiwa, sai dai kuma
yanda duk kaxuwar tata ta kai da
tsananta ba zai yiwu ta miqe ta bishi
ba, saboda hakan zai zamo mata
tamkar wulaqanta kan a gaban kuma
ximbin samarin da idonsu yake kanta
44
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
suke fata ta basu dama ta ga abin
mamaki a kan soyayyar da suke yi
mata tunda ita xin mai kyau ce.
Ko shi a wurin shima kuma Salim
xin bin nashi ba komai bane illa qara
wulaqanta kai da kai da ba shi damar
da zai ci gaba da disgata a kowane
lokaci.
Tsunduma ta yi cikin nazari na
tunanin mene ne dalilin da ya sa
kullum ta yi tattaki ta kawo kanta ga
Salim sai ya san abin da ya yi ya
tozarta ta ya yi sanadin da vacin rai
zai same ta? Ina dalilin da kullum bai
da wata xabi’a illa ta son nuna mata
cewar ita xin ba komai ba ce a wurin
shi? Bai sonta ne yasa yake yi mata
hakan ko kuwa dai ita ce ta yi
sakacin da ta bari ya gane son da
take yi mishi ya fi wanda yake yi
mata yawa?
Surar kofin dake gabanta ta yi
wanda ta riga ta cika da barasa ta yi
maza ta kwankwaxe shi sannan ta
buga shi kan teburin dake gaban
nata ya yi maza ya tarwatse.

45
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Ilahirin mutanen dake zazzaune
kan kujeru dake wurin suka juyo da
kallon su gare ta, cikin sauri service ta
taho da wani sabon kofin a hannunta
ta ajiye mata ta kuma tattara duk
wani abin da yake wurin ta gyara.
Wani saurayi dake zaune shi
kaxai can gefe yana kallon abin da ke
faruwa ya miqe tsaye tare da gyara
kwalar rigar shi ya tako cikin qasaita
ya iso teburin nata da Prisca take
zaune a kai ya ja wata kujerar ya
zauna, kafin ya kalle ta cikin ido tare
da murmushi mai gamsarwa ya ce.
“Hey beatifull just chill up, ai kune ma
da abin haushin tsiya, ku kuke
jawowa kanku wulaqanci a wurin
waxannan gidadawan mutanen,
amma in ba haka ba a irin kyan nan
naki har yaushe ne za a ce wani xan
qauye da fatara da talauci ya koro
shi daga yankinsu ya zo mana nan ya
zo roron duddugar man fetur xinmu
zai iya wulaqantaki.
Dube ki fa ki qara duban kan naki
ki qara gani, to kun basu kanku suna
wulaqanta ku bayan cin arzikin mu
46
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
suka zo yi, mu kuma da muke tare
daku kun raina mu kuna wulaqanta
mu saboda rainin hankali, kuna
baiwa wasu matsiyata fatararru
kanku suna cin mutuncinku”.
Prisca ba ta kalle shi ba, ba ta
kuma tanka mishi ba, ta ba da
nutsuwarta da hankalinta kawai
wajen kwankwaxar barasarta.
Mutumin nan ya qara
ranqwafawa gare ta tare da faxin.
“Kin gane ko? Na kama xaki a
sama ina ganin mu haura kawai muje
can mu huta sai ayi odar wasu sabbi
a can. Nawa ake biyanki dare xaya?”
Ya gama maganar tashi daidai
lokacin da ya xora hannunshi kan
cinyoyin nata da suke bubbuxe yana
shafawa a hankali, abin ya yi
matuqar qonawa Prisca rai.
Ta yi maza ta warware hannu
cikin zafin nama ta yanke shi da wani
irin lafiyayyen mari a kumatunshi na
hagu tau...
Cikin tsananin kaxuwa a dalilin
bai zata ba yasa hannu ya rungume
kumatun nashi duka biyu, zuba mata
47
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
ido ya yi cikin tsananin kaxuwar dake
bayyanar da vacin ranshi a sarari.
Cabkar da ya yi mata ne ya
zaburar da mutanen dake zazzaune
suna kallon diramar dake afkuwa a
tsakanin su a table no 11. suka
mimmiqe suka kawo xauki suka
rirriqe mutumin nan ana qoqarin ba
shi haquri, masu son ganin abin ya
lalace kuma suna faxin.
“Kai haba wane irin wulaqanci ne
wannan? Wani ya yi mata wulaqanci
ta rama a kan wani? Kai ku qyale shi
ya daki banza kun ji. Haba, iya
shegen ai ya yi yawa”.
Daga can nesa kuwa wasu da
abin ya zarce magana a wurin su faxi
suke yi cikin zukatansu.
“Kai lallai babu mai rainin hankali
da rainin wayo irin mace, in ba haka
ba ina dalilin wannan irin mari na
wulaqanci?”
Masu hankalinsu kuwa haquri
suke ta faman bayarwa suna faxin
haquri kawai zai yi kar ya ce zai hau
dokin zuciya ya biye mata, sai abin
ya lalace don ba a san abin da zai
48
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
biyo bayan dukan da zai matan ba in
an barshi tunda ya riga ya tunzura da
yawa.
Duk abin da ke faruwa a kan idon
Salim yake, saboda tsayuwar da ya yi
a wurin reception yana kallo tare da
qoqarin biyan kuxin xakin da zai
kwana a ciki.
Ya buxe qofar xakin ya shiga ya
nufi toilet xin bayan ya yi jifa da kot
xin dake riqe a hannun shi kan
kujera, shower kawai ya buxewa
kanshi.
Da ya gama sai ya xauro alwala
ya zo ya yi sallar shi ta magariba da
isha’i, sannan ya buga intercom don
yin odar abin da zai ci, don ya san ba
zai yiwu ya ce zai kwana a haka ba,
saboda rabon shi da sa wani abu a
bakinshi yau tun ruwan swan xin da
ya kwankwaxa da safe.
Service ta shigo riqe da babban tire
a hannunta ta ajiye tana sauke kayan
dake kai, coconut fried rice ce da
rabin kaza, sai kwalbar coke guda
xaya da robar ruwan swan guda
xaya.
49
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Tsawon lokaci yana qoqarin
xurawa cikinshi abincin nan hakan
bai yiwu ba, saboda ya riga ya
cunkushe mishi ban da haka kuma
al’amuran da ya wuni a cikin nasu
duka ba masu daxi bane.
Ya dafe goshinshi da tafin
hannunshi saboda sarawan da kan
nashi ke yi, don haka ya qara danna
intercom, service ta sake shigowa ya
ba ta umarnin kawo mishi kofin shayi
da kuma paracetamol, kafin mintina
biyar ha ta kawo ta sake fita.
To shayin kam ya sha, shine
kuma ya samu har ya ci rabin kazar
ya watsa qwayoyin maganin guda
biyu ya hau gado ya mimmiqe, a
cikin zuciyar shi kuma tunanin hauka
irin ta matan kudu yake yi waxanda
bsu mai da marin xa namiji a bakin
komai ba.
Ya sake jinjina al’amarin marin
cikin zuciyarshi saboda girman abin a
wurin shi, bai san yanda aka yi ba sai
kawai ya ji hannunshi yana shafa
kuncin shi wanda ya dace da
saurayin da Prisca ta sharawa maari.
50
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Kai wannan rainin hankali da
yawa yake, ko sau nawa ya tava
ganin wata mace ta sharawa xa
namiji mari irin wanda Prisca ta
sharawa wannan a zaman rayuwar
shi ta arewa?
Kai ba zai iya tunawa ba, bai tava
gani ba bai tava ganin irnda ‘ya mace
ta warware hannu ta mari xa namiji
ba a arewa.
Matan arewa mata ne masu
kunya da kamala, suna kuma da
xabi’a ta girmama xa namiji.
Ya xan gyara kwanciya cikin
lumshewar ido tare da tunanin in da
shi Prisca ta yiwa wannan marin irin
fici-ficin da zai yi da ita, ko ya
vavvallata.
Nan da nan ma ya yi maza ya
kawar da wannan tunanin tunda shi
kam ma ai ya san babu wata mace da
za ta yi gigin xora hannunta a
fuskarshi, tunda ai ba yau ya soma
mu’amala dasu ba, ba kuma yau ya
soma samun savanin dasu ba,
wataqila dai suma sun san waxanda
suke yiwa irin wannan iya shegen.
51
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Tunda Hausawa ma ai suna da
karin maganar da suke cewa wai
‘WATA FUSKAR TA FI GABAN MARI’,
ko kuma ‘TUNKU YA SAN SHURIN DA
YAKE YIWA KASHI”.
Wani tunanin ya sake zuwarwa
Salim cikin zuciyarshi, to amma da
abin da suka yiwa gidanka da mari
wanne zafi?
Nan take ya ji zuciyarshi tana
raya mishi ai gara da marin suka yi
mishi da ya fiye mishi, tunda a halin
da yake ciki a yanzu ba zai iya
qiyastawa kanshi irin asarar da suka
ja mishi ba.
To amma kuma mari a cikin
ximbin jama’a? Kai duka biyun dai
yana ganin babu wani na daxi, ko a
ce shine gwanda.
A haka barci ya xauke shi. Bayan
ya saka alarm a wayarshi don gudun
makara.

BABI NA HUXU

Q
arfe bakwai dai-dai yana qofar
bankinsu ya shiga qoqarin
haxa report, Ubangiji kuma ya
52
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
taimake shi kafin qarfe tara na safe
yana office xin Mr. A.A Adedigba
manaja don bayarwa.
Mr. Adedigba ya qara kallonshi
ya ce, “Mr. Salim ina ganin kamar ya
kamata ka qara dubawa kafin a miqa
musu ko kuwa?”
Cikin ladabi ya ce, “Ai na yi duba
mai kyau yallavai, a kanshi jiya na
wuni na kwana”.
Ya ce, “To babu laifi”.
Bai samu matsala a office ba
ranar, don haka yana fita kawai
wucewa ya yi ya je ya ci abinci
sannan ya qarasa wurin kafintan da
suka saba dashi ya kai shi gidanshi
don fara gyaran ta’adin da aka yi
mishi.
Suka daidaita a kan gyaran da
sauran abubuwan, sannan ya sallame
shi ya tafi.
Ya shiga xakinshi ya kwave kayan
aikin shi sannan ya fito sanye da
farar singileti da wando three quarter, ya
fara kikkintsa xakin.
T.V home theater da sauran abubuwa
duk ya tattara su ya fitar ya ajiye a
53
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
garejin motarshi, sannan ya tattara
duk wasu kwalabe ya gyara ko ina
tsaf kamar ba a yi komai a xakin ba.
Ya shiga toilet ya yi wanka
sannan ya samu ya sarara, ya shiga
kicin don shirya abin da zai ci. Yana
cikin aikin abincin mahaifiyarshi ta
faxo mishi.
Nan take kewarta ta lulluve shi,
mace gwanar kirki da shirya abinci
mai sauqin kashe kuxi, ga kuma
xanxanonshi mai matuqar gamsarwa.
Shi kam a tsawon rayuwarshi bai
tava cin abincin da ya fiye mishi na
Innarshi xanxano ba, tun cikin
quruciyarshi har kawo yau xin nan.
Sai dai a fi Inna girka mai kyan
gani a ido, amma ba xanxano a baki
ba. Hakan kuma zai faru ne a dalilin
wancan xin ya fi nata tsadar
sarrafawa.
Gwanar shirya.....ya yi maza ya
hana zuciyarshi abin da yake nufin
cewa gwanar ce, ya koma tambayar
kanshi, to mene ne ma ba ta iya ba
ne? Gata da haquri, ga girmama miji,
ga haquri ga na qasa da ita.
54
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Ya koma tuna shekarunshi na
haihuwa shekarun da ya yi su a
manne da ita a wancan lokacin da
wannan lokacin bai tava zaton zai iya
rayuwa a inda ba ta nan ba.
Gabanshi ya yanke ya faxi da ya
gwada yin lissafin rabon shi da ita,
kai anya ya kai haka? Shi da kanshi
ya yiwa kanshi tambayar.
Shiru ya yi cikin wani tunanin da
ya xauke shi da nazarin tunani mai
zurfi. Zuwa can ya ce, tabbas haka
abin yake, shekaru biyu ne cif har da
watanni shida rabon shi da Innarshi
da mahaifinshi, dama sauran
danginshi gaba xaya.
Baya ko kiransu a waya balle ya
yi musu wani aiki ko kuma su san da
lafiyar juna, hakan kuwa ya faru ne a
dalilin gajiya da qaryar gashi nan
zuwa da yake ta yi musu, ya ga bari
ma kawai ya dena neman nasu gaba
xaya, randa ya samu zuwa kawai sa
ganshi.
Kai amma ya kyautawa kanshi
kuwa da ya yiwa iyayenshi irin
wannan abin da ya yi kuwa? Anya ya
55
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
yiwa kanshi adalci kuwa? In shi ya
san inda suke bai je bane kawai anya
su inda sun san inda yake da basu
fito neman shi ba?
Nan da nan ya ji tausayin
iyayenshi da ‘yan’uwanshi ya kama
shi, to ko zai kirasu ne don su ji
labarin juna da kuma lafiyarshi don
hankalinsu ya kwanta?
Kai ba zai yi hakan ba tunda in ya
kira su wacce hujjar zai bayar kan
daxewar da ya yi bai kira ba? Kan
haka ya yi tunanin yin aike.
Nan ma dai ya gane ba zai yiwu
ba, saboda sanin halin baban shi
Malam Manu, don haka ya yanke
shawarar haqura kawai har sai
lokacin da hutunshi ya zo ya tafi ya
yi hutun shi a can kamar yanda dama
ya saba yi a shekarun farkon aikin
shi, in yaso in ya je sai ya gaya musu
cewar ayyuka ne suka tsare shi.
Gabanshi ya yi mummunan
faxuwa da ya tuna kenan bayan laifin
da ya yi na rashin kaiwa iyayenshi
ziyara tsawon lokaci zai qara da yin

56
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
qarya wacce zunubinta ya fi komai
tsanani.
Tsayawa ya yi cak yana kallon
girkin nashi, sai dia idanuwan ne
kawai a kan girkin amma hankalinshi
baya nan.
Tambayar kanshi yake yi, anya na
yi daidai da wannan abin da na yi?
Iyaye? Iyayena ne masu alheri masu
sadaukarwa, masu kulawa, babu abin
da basu yi ba wajen ganin sun ba shi
ilimin addini da na zamani mai
inganci.
Ya xan ja tsaki kaxan kafin ya
cewa kanshi, bari wannan hutun
nawa gaba xaya a Yola zan yi shi,
don ya samu lokacin basu haquri kan
kuskuren da ya aikata musu.
Matsalar ita ce, ko watanni uku
bai yi ba da ya kammala hutun shi na
shekara, sai wasu watannin kamar
tara ne zai yi hakan, tunda shi da
kanshi ya san neman hutu haka
siddan a wurin aikin nashi ba
qaramin al’amari bane ko da kuwa na
kwanaki biyu ne, saboda yanayin
aikin nashi.
57
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Amma anya bai tsoma kanshi
cikin wani al’amari ba? Ya yi maza ya
kawar da wannan zancen cikin
zuciyarshi saboda bai son sanya
kanshi cikin damuwar da za ta hana
shi jin daxin rayuwarshi.
A hankali ya ja xan qanqanin
tsaki, cikin zuciyarshi kuwa cewa ya
yi, “In na yi haqurima babu komai,
tunda in dai ana raye ai shekara
kwana ne!”

** **

58
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
BABI NA BIYAR
ADAMAWA

“B
aba! Baba!!” Hamza ne
yake ta faman kiran
Malam Manu dake
qoqarin tsaftace gidan nashi ta
hanyar cire yanar gizo-gizon dake
manne a rufin tsohon gidan nashi.
Ya juyo ya kalli Hamza ya ce,
“Uhm! Ina jinka Hamza, mene ne
ya faru na ji kana qwala min kira
haka?”
“Baba ina so ne ka je ka baiwa
Inna Wuro haquri ta daina kukan
da take yi, tun jiya nake ta ba ta
haquri taqi ta haqura ta bar
kukan, tunda wannan malamin da
muka je wurinshi ni da ita ya
tabbatar mana da cewar yana nan
a raye ina ce sai ta kwantar da
hankalinta”.
Malam Manu ya gyara
tsayuwar shi tare da gyara riqon
da ya yiwa doguwar tsintsiyar
dake hannun shi, kafin ya ce
59
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Hamza, Hamza ya sake duban
mahaifin nashi cikin nutsuwa ya
ce.
“Ka yi haquri ba zan sake zama
in vata lokacina wajen baiwa
mahaifiyarku baki ba kan
al’amarin yayanku, tunda dai na
rarrashe ta na rarrashe ta na ba ta
haquri, na yi mata duk bayanin da
zan yi mata tun muna biyu a xaki
babu ma wanda ya san me muke
ciki, tun zancen nan bai fito ba har
kowa ya gane ma mene ne ba ta
haqura ba.
Ba sau xaya ba sau biyu ba, na
gaya mata yaron nan fa yana nan
a raye lafiyar shi kuma qalau, abin
da ya ga ya fiye mishi kenan ya
rabu damu ya fita harkarmu,
wataqila ya yi nazari ne ya gane
bamu dace da zama iyayenshi ba,
to muma mu yi haquri kawai, mu
kuma yiwa Ubangiji godiya da ba
shi kaxai ya bamu ba.

60
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Mu kam ai mun rabu da
iyayenmu lafiya bamu kuma yi
musu abin da ya yi mana ba, mun
rabu dasu ne suna sanya mana
albarka, to mene ne damuwar
mu?”
Ya zubawa Hamza ido yana
kallon shi cikin natsuwa kafin ya
ce, “Shine ya saura, shine bai san
komai game da wannan duniyar
ba, shi ya sa take yi mishi daxi har
yana shagala da ita bai sani ba
cike take da abubuwan ban tsoro
iri-iri”.
Ana cikin haka Babba Idi ya
iso, “Wurin ka fa na zo Malam
Manu”. Maganar da ya fara yi
kenan bayan ya yi mishi sallama
ya amsa.
Malam Manu ya kalli qanin
nashi wanda cikin zuciyarshi yake
zaton ya san abin da ya kawo shi,
ya ce, “To ni da ka same ni ina
wannan aiki Idi ka ce min wurina
ka zo”.
61
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Baffa Idi ya kalli aikin da wan
nashi yake yi ya ce, “Wannan aiki
ai na yara ne Malam, kai Hamza
karvi ka yi”.
Da sauri Hamza ya karvi
doguwar tsintsiyar daga hannun
Malam Manu, saboda sanin Baffa
Idi ba mai wasa bane yanzun nan
ne zai iya kai mishi maka.
A tsakar gida suna zaune kan
tabarma bayan sun gama gaisawa.
“Malam shekara biyu da rabi
ne fa yaron nan bai zo gida ba, tun
abin nan kuma bai kai haka ba
nake yi maka magana ko zan bi
bayanshi ne don aje a san halin da
yake ciki, kana faxin wai ai lafiya
ce take vuya da bai da ita da tuni
ya neme ni, in kuma da baya raye
da tuni na ji labari, don ita
mutuwa ba ta vuya.
To gashi abin sai qara nisa
yake yi, shi yasa na zo in gaya
maka ni kam a cikin makon nan
zan bi bayanshi, na ma riga na yi
62
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
magana da maqwabcina Malam
Dauda dake kai kayan gwari can
wajejen nasu”.
Malam Manu ya yi murmushi
kafin ya kalli xan’uwan nashi cikin
natsuwa ya ce mishi.
“A kan Salim ne za ka tafi kudu
don ka nemo shi? Shi fa Salim ya
san kudun nan ba kuma tun zuwan
shi na farko ne bai tava zuwa ba,
a’a, ya zo ya koma ya zo ya koma,
yanzu ne kawai ya daina zuwa, ba
kuma denawa kwata-kwata ya ce
muku ya yi ba, a’a, ya xan kwana
biyu ne kawai bai zo ba.
Ku dole kullum sai an zo inda
kuke? Ba’a shekara goma ba aje
anga iyaye ba ko kuwa........?”
Baffa Idi ya tari numfashinshi
cikin yanayin girmamawa ya ce,
“A’a, Malam mu bar irin waxannan
maganganun, Salim baya cikin irin
waxannan maganganun, ba kuma
zai zamo daga cikinsu ba, don

63
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
haka zan tafi in dubo halin da yake
ciki”.
Malam Manu ya ce, “To ban
yarda ba, Salim dai in ka cire shi,
shi kaxai a cikin ‘yan’uwanshi to
daga nan gidan zuwa naka kana
da sauran guda ashirin koma har
da xaya, in har waxannan ashirin
xin basu gamsar da kai ka yiwa
Ubangiji godiya ka haqura da shi
shi kaxai ba, to ni da bani da kowa
sai kai ba zan haqura da kai in
barka ka tafi neman shi wurin da
baka sani ba balle tava zuwa ba,
baka tava ganin mutanen dake
rayuwa a can ba, in ka tafi kaima
baka dawo ba ta ina zan fara
neman ka?
Tunda ni kam ai tafiyata da tafi
nisa a nan haka iyakacina Gombe,
ta baza nan ne nake nisa in wuce
Mambila in shiga har qasar
Cameroun saboda ana zuwa wurin
‘yan’uwa”.

64
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Baffa Idi ya yi ta ‘yan bayanan
da zai yi Malam Manu yana jinshi,
zuwa can sai ya ce mishi, “Ni fa
duk wani wanda na san kafin
zuwan shi cikin duniyar nan na
rayu a lokacin da shi baya cikinta,
wataqila rayuwar da na yi a
wancan lokacin ta fi mini wacce
nake yi a tare da shi daxi, to baya
xaga min hankali matuqar na san
shi xin da nufi ko da sanin shi
yake yin abin da yake yi.
Shi yasa ma ni da na ce yaran
gaba xaya a fidda su daga
makarantar bokon mu da bamu yi
bokon ba mun yiwa iyayenmu iya
shege ne?”
Baffa Idi ya ce, “A’a, Malam a
barsu suyi bokon su ba laifin boko
bane, to in bokon ne ma shi xan
gidan Malam Sadau ba tare da
Salim xin suka yi ba, ba kai ne
kake gaya min bana ya zo ya
biyawa Malam Sadau xin zai tafi
ya sauke faralin shi ba?”
65
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Malam Manu ya ce, “Haka ne”.
“Ni har yanzu na fi ganin
kamar ka barni in je, ai shi Malam
Daudan ya san wurin ya saba
zuwa yana dawowa, don na fi
zaton Salim ba zai bar gida haka
kawaia ba”.
Malam Manu ya qi amsa
maganar ya kauce ta ta hanyar
qwalawa matar shi kira, “Ni ina
Inna Wuro take ne ko har yanzu
xumamen bai yi bane?”
Inna Wuro ta fito suna gaisawa
da Baffa Idi, ta wuce ta shiga
xakin dahuwarta shi kuma yana
binta da kallo.
Ta fito tana ajiye musu abincin
a gabansu ya zuba mata ido yana
yi mata wani irin kallo, kukan me
Inna Wuro ke yi haka?
Ba ta kula shi ba ta wuce ta
koma xakinta, ya bar cin abincin
ya miqe ya bi bayanta.

66
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
“Inna Wuro ba dai
Muhammadu Salim kike yiwa
wannan kukan ba ko?”
Shiru ta yi ba ta amsa mishi
ba.
“Kina so ne ki jawa yaro wata
fitina kike irin wannan zubar da
hawayen a kanshi? To in dai don
na roqe ki ki rinqa yi mishi addu’a
ne yaasa har kika samu damar da
za ki rinqa yi mishi kuka ki je ki ja
mishi wata fitina, to na fasa roqon
naki ki bari kawai ko ni kaxai zan
rinqa yi”. Ya wuce ya fita ya bar
gidan.
Malam Manu ya ce, “Uh! Taku
ake ji wai mahaukaci ya faxa rijiya
ya ce ni in aka barni ma wanka
nake yi”.
Inna Wuro wacce kullum take
tuna hirarrakin da suka sha yi tare
da xan nata, daxin daxawa
kalaman da ya kan yi mata a
lokutan da suke hirarsu alqawura

67
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
masu daxi da ya kan yi mata yana
faxin;
Bari dai in kama aiki Inna Wuro
za ku huta, gaba xaya zan hutar
daku daga nan gidan har gidan
Baffa Idi, ban sake barin wani
cikin matsala. Bari ma dai ke Inna
Wuro da zan samu yanda nake
fata, to da komai ma yi miki za a
rinqa yi in dai ga kin huta, in hutar
dake in jiyar dake daxi, ki daxi ki ji
daxi ki zama baki da wani aiki in
ban da na yi mana addu’a ni da
‘yan’uwana.
Ta kasa haqura ta yarda da
maganar da mijinta ke yawan faxa
mata ita da xan’uwanshi cewar
Salim lafiyar shi qalau bai ga
damar zuwa gida bane kawai, ya
samu duniya ne ya gane su xin
basu dace da zama iyayenshi ba.
Wasu sabbin hawayen suka
sake zubo mata, ya ya ma za a yi a
ce Salim mancewa kawai ya yi da
gida, ko kuma ya gane iyayenshi
68
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
basu dace da haihuwar babban xa
kamar shi ba. To sai su wa? Shi
kuwa ai mai son iyayen shi ne da
kuma ganin girmansu.
Sai da Malam Manu ya gama
shirinshi zai fita sannan ya leqa
xakin Inna Wuro, tana zaune kan
sallayarta tunda ta idar da sallarta
ta walaha ba ta miqe ba.
Gyaran muryar da ya yi ne ya
sanyata saurin shafa fatiha ta
kalle shi cikin nutsuwa da
girmamawa.
“Har za ka fita ne Malam?”
“Eh”. Inna Wuro zan fita, kafin
in fitan ne nake so in tuna miki
cewar, take haqqin mutanen dake
da haqqi a kanka, ko kuma
quntata musu yana daga cikin
abubuwan da suke hana addu’o’in
bawa karvuwa”.
Gabanta ya yi matuqar faxuwa,
ta xaga ido ta kalle shi cikin
nutsuwa ta ce, “Me ya faru
Malam?”
69
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Ya zuba mata ido yana kallon
ta, “Jiya da shekaran jiya duk baki
yi abincin rana ba a gidan wuni
kike yi a kwance baki da aiki sai
na kuka, kina tsammanin su
qannen shi basu da haqqi ne a
kanki sai shi kaxai?”
Yana fita Inna Wuro ta yi maza
ta miqe ta kama aikace-aikacen ta
na gida kamar yanda ta saba, in
har akwai wani abin da yake faxar
mata da gaba, to bai wuce a ce
mata ta yi wani abin da zai iya
hana addu’o’inta samun karvuwa
ba.
Nan da nan ta kira Hamza da
Yakubu waxanda dama sune suke
bin Malam Manu kasuwa bayan
sun dawo daga makaranta, xaya
ya zauna ya taimaki Malam Manu
da wasu ayyuka, xaya kuma ya
xauko cefane ya kawo gida.
“Inna Wuro yauma garin rogon
zamu jiqa mua sha?”

70
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Ta yi maza ta ce, “A’a, Yakubu
cefane za ka kawo in yi muku
abincinku mai daxi, don haka ana
baka kar ka tsaya wasa ka
hanzarta ka kawo”.
Ya ce, “To Inna Wuro”.
Tana zaune a tsakar gida ita
kaxai bayan ta sallami duk
mutanen gidan, na makaranta ya
tafi, mai tafiya kasuwa ma haka.
Al’amarin Salim take tunawa,
mafarkin da ta yi da shi a daren
jiya ba wani mai daxi bane. Ko da
yake dai ta yi addu’o’i bayan
farkawar ta daga baccin da ta yi
mafarkin kamar yadda sunnar
manzon rahama (S.A.W) ta nuna.
Amma kuma duk da haka
mafarkin ya qi wuce mata, ta yi
shiru na xan wani lokaci bayan ta
yi qwafa.
Malam Manu ta tuna mutumin
da ya yi ko in kula da al’amarin
Salim, tamkar dai ba shine
ubanshi ba har ta kaima ita kam ta
71
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
daina furta sunan Salim a
gabanshi, don tana ambaton
sunan nashi maimakon ya taya ta
jajanta al’amarin suma samu su
xan tattauna kan abin da suke ciki
na rashin zuwan shi, sai kawai ka
ji ya ce wai.
“DUNIYA ce tayi daxi ne yasa
aka jishi shiru, waxanda suka fishi
daxewa da barin gidan ma da ta
kacame musu sun dawo sun nemi
dangi.
Hausawa ma ai suna da karin
maganar da suke cewa, ‘RAN daxi
sai bare, ran wuya kuwa sai
NAKA”.
Wasu sabbin hawayen suka
sake zubo mata, ko me Salim ya
yiwa Malam har yake iya furta irin
waxannan kalaman a kanshi oho?
Cikin zuciyarta ta sake ci gaba
da add’o’inta na roqon Ubangiji ya
maido mata da Salim xinta gida
lafiya, ya kuma kare mata shi
daga dukkan sharri.
72
Idan kunne yaji…….1
Sodangi

** **

73
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
BABI NA SHIDA

G
arin Ogbodo gari ne mai
ximbin tarihi da kuma
albarkatai masu yawa
saboda kasancewar shi a bakin
ruwa, babban gari ne qwarai gashi
kuma a cike da baqin mutane dake
zuwa daga wurare daban-daban.
Wani irin gari ne mai kyan
fasali da tsari, ruwan da ya zagaye
shi xin ba qaramin ruwa bane, don
ta kan ruwan mutum zai iya isa
garuruwa daban-daban ta cikin
kwale-kwale ko qaramin jirgin
ruwa.
Garuruwa irin su Warri, Lagos
da Bayelsa da kuma
makamantansu, bisa wannan dalili
sai ya zamo mutane suna halartar
cin kasuwar Ogbodo da ke ci wata-
wata daga garuruwa daban-daban
na nesa da kuma na kusa.
Babbar kasuwa ce take ci a
bakin ruwa, mafi akasarin
mutanen dake cin kasuwar ma ta
74
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
cikin kwale-kwale suke zuwa,
kaxan ne kawai suke zuwa a mota
ko kuma a qafa, daga cikinsu
akwai irin su Salim waxanda su
suke zuw aodn sayan abin da za
su ci ne kawai saboda sanin
kayayyakin da ake samu a
kasuwar masu matuqar kyan
yanayi ne da aka xebo su a ranar
daga gona, ko daga bishiya, ko
ruwa, irin su Agade plantain, kifi,
kwakwar manja da dai sauransu
na dangin ‘ya’yan itatuwa.
Yana tafe cikin motar Toyota
Corolla L.E wacce ba ta rabo da
tsabta da kuma qamshi, tafiyar
yake yi cikin natsuwa da nishaxi
tare da bin sansanyar waqar dake
tashi sama-sama a hankali cikin
motar tashi, wacce ta “Beyonce”
ce mai taken “Irrepraceabel”.
Yana tafiyar tare da qara
kallon hanyoyin nasu, yanayin
wurin yana burge Salim, yana
sha’awar yanayi irn na garin, inda
75
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
kullum za ka ganshi lulluve da
ni’imar da babu tsananin rana
babu tsananin sanyi, ga bishiyoyin
kwakwa, ayaba, agade, lemo,
gwanda, abarba ba zai yiwu ma ya
tsaya qirga su ba, gasu nan iri-iri
birjik.
Sai dai abin mamakin da ya fi
komai baiwa Salim mamaki bai
wuce kowacce bishiya ka gani in
ka tambaya sai a ce maka ga mai
ita ba, ga ciyayi masu tsabta sun
yiwa qasa shimfixa lif-lif kamar
yanda bishiyoyi suka haxu suka
yiwa garin rumfa mai ban
sha’awa.
Yawan sha’awar da Salim ke
yiwa garin sai ya yiwa kanshi
sha’awar zaman cikin shi.
Ya yi parking a daidai qofar
gidan da ya zamanto shine nashi,
ya buxe but tare da fara sauke
kayayyakin da ya sayo daga
kasuwar Ogbodo da ya je ci.

76
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Amedi ya garzayo aguje don
taimakon shi xiban kayan.
Salim ya kalli yaron ya ce
mishi, “Yau baka je shago bane?”
Ya ce, “Eh, na roqi baba ne ya
barni a gida yau don in je in gai da
kakata”.
Salim ya ce, “Ka yi qoqari
Amedi”.
Ya gama shigarwa da Salim
kayan da ya sayo ya shirya mishi
su a store, sannan ya fito ya samu
Salim xin a tsaye jikin motarshi.
Ya zo zai wuce shi.
“Zo nan Amedi”. Salim ya kira
shi. “Ungo wannan”. Takardar xari
biyar ce ya miqa mishi.
Ya yi maza ya girgiza kai tare
da nuna alamar rashin karva,
“A’a, na gode Sir, idan na karva
babana zai buge ni”.
“Ba zai buge ka ba Amedi, ai
na riga na yi mishi magana kan
dukan da ya yi maka wancan
karon saboda karvan abin da na
77
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
baka da ka yi, ba zai sake ba
karvi”.
Amedi ya kai gwiwowinshi qasa
ya sa hannu biyu ya karva tare da
faxin, “Thank you sire”. Ya wuce
ya tafi.
Salim ya xan bishi da kallo
cikin zuciyarshi ya ce, “Ko ina dai
akwai nagari, suma wasun su kan
tsaya su ga su yi tarbiyyar
‘ya’yansu”.
Yana tsaye a kicin xinshi yana
gyara xanyen kifin tarwaxa da ya
zo da shi daga Ogbodo, cikin
zuciyarshi zance yake yi shi kaxai,
in banda ma dai shi mene ne na
wani tara ‘yanmata a gida suje
suna ja mai asara, tunda in ma
girkin da suke yi mishi ne ai ba kai
shi iya girki mai daxi suka yi ba.
Ya yi tsarki a bayyane sanda
ya jawu kayan miyan da zai yi
amfani da shi, su attarugu, albasa,
tumatur. Ya jawo ya fara

78
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
markaxawa a sabuwar blander da
ya saya.
Ya gama haxa miyar sannan ya
jawo sabuwar agada tsinkar ranar
wace ba ta gama nuna ba ya
wanke ta ya xan vavvare ta ba
tare da ya tsaya vare ta ba ya
sakata a tukunya ya zuba ruwa ya
rufe ya xora ta a kan coker ya
soma dafata, yana fitowa daga
kicin xin wanka ya shiga ya haxo
tare da alwalar sallar azhar.
Ya tsaya a cikin xan
madaidaicin xakin nashi mai xauke
da madaidaicin gadon da ya sha
shimfixa mai ban sha’awa saboda
dacewar da ya yi da kyakkyawar
katifa, planbed sheet ne a
shimfixe sai madaidaicin wardrop
da kuma dogon madubi a tsaye, in
ka xebe waxannan abubuwan
babu komai cikin xakin.
Ya tsaya gaban madubin yana
kallon kanshi a ciki, bayan ya
gama gyara jikinshi sanye yake da
79
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
wando three quater ruwan qasa da
riga jersey mara hannu.
Ya kalli fuskarshi, shi kanshi ya
san shi xin mai kyau ne ba farar
fatar shi ce ta fi komai daukar
hankalin mutane ba a tare dashi,
har da irin surar da ke gare shi ta
cikar halitta.
Shi ba mai jiki bane, ba kuma
siriri bane, ga tsawon shi dake
yawan sanya shi nishaxi a duk
sanda ya tsaya ya ga ya kere wasu
masu yawa.
Ya fito daga bed room ya nufi
kicin don sauke girkin nashi, ya
vace dafaffiyar plantain xin,
sannan ya sanya ‘yar wuqa mai
tsabta ya yanyanka ta kuci-kuci
daidai yadda za a ji daxin kaiwa
baki, sannan ya xuako kwanon
tangaran ya zuba miyar a ciki ya
fito falo ya ajiye kan center tebur
xin da ke wurin, ya buxe fridge ya
ciro robar ruwan da coke guda
xaya, ya je ya xauko tambulan ya
80
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
haxa ya ajiye, ya juya ya sake
komawa cikin xakin shi.
Bai ji qwanqwasa qofar ta ba
iyaka dai ganinta kawai ya yi a
tsaye a tsakiyar xakin, ya qara
kallon ta cikin mamaki amma
gaskiya Oluchi ta raina shi, abin
da kawai ya fara zuwa cikin
zuciyarshi kenan.
Wato har ma za ta iya dawowa
gidanshi bayan iya shegen da
suka yi mishi. Ya ajiye abin da ke
riqe a hannun shi tare da karkaxe
hannun tamkar dai wanda ya ajiye
wani abu mai qura.
Oluchi ta raina shi, zuciyarshi
ta sake raya mishi hakan. Me ya
kawo ki gidana? Tambayar da ya
fara yi mata kenan bayan ya xaga
ido ya kalle ta.
Ta zuba mishi ido tana kallon
shi, kallo irin na mamaki.
“Abin da ma za ka ce tambaye
ni kenan?”

81
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Ta xan motsa kafaxarta tare da
tave baki.
“Ban ga laifinka ba ni na kawo
ma kaina, xan iska kawai mara
mutunci, karuwarka ta biyoni har
gidan ka tana neman ta kashe ni
shine za ka kwashe borin kunya da
hauka.
To ka ji kunya, tunda gashi ka
sake ganina bayan an ce maka ina
police station baka je ka fito dani
ba to na fito. Na kuma zo ne don
ka ganni in kuma gaya maka ka
gayawa wannan ‘yar iskar karuwar
taka ta yi hankali dani, don ina
tabbatar maka da cewar randa ta
yarda muka sake yin ido biyu da
ita a gidan nan ina tabbatar maka
da cewar sai na kashe ta har
lahira”.
Rainin hankalin ya yi yawa,
rainin ya kai inda ya kai. Abin da
zuciyarshi ke ta faman gaya mishi
kenan. Ya zame mishi dole ya
xuaki mataki.
82
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Cikin hanzari ya nufi can cikin
xakin nashi ya fito riqe da
tafkeken belt a hannunshi, bai
ganta a falon ba, nan take ya
shiga waiwaye-waiwayen duba
inda ta shiga.
Sai kawai ya ganta ta fito daga
kicin xinshi riqe da plate xin da ta
shaqo da abincin da ya girka,
ranshi ya qara vaci, nan take ya
shiga zuba mata belt ya shiga
tafkarta da duka tamkar aiko shi
aka yi.
Ita kuma tana ihu tana kuma
kurma mishi ashar mai tsanani,
abin da ya yi daluilin da dukan ya
xauki lokaci mai tsawo.
Sai da ya ga ya yi mata lilis
sannan ya tura ta waje yana faxin
“Yar iska kawai mara mutunci, ki
sake zuwa min gida ki ga yanda
zamu qare dake”.
Har wannan uban wahala da
Oluchi ta sha bakinta bai mutu ba,

83
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
tana daga wajen tana aiko mishi
da ashar.
Ya dawo ya zauna yana kallon
tashar C.C.T.V inda ake magana a
kan qaruwar farashin hannun jarin
kasuwar duniya.
Bai sake fita daga gidanshi ba
sai da ya idar da sallar isha’i, yana
tafiya a hankali cikin motar shi
cikin kwalliya ta ban sha’awa, ga
qamshin shi mai daxi.
Wurin Jiniri mai tsire ya nufa,
can yake nufin cin abincin shi na
dare daga nan su xan yi hira.
Wurin Jinjiri mai tsire
matattara ce ta ‘yan arewa dake
wannan garin, don haka ne ma ya
sa babu wani juyi da za a yi ka ga
wurin babu mutane, tun daga kan
ma’aikatanmu da aiki ya kai su
can, har zuwa ‘yan cirani.
Ko shi Salim a farkon zuwan
shi Adanta ba qaramin taimako
dandalin na Jinjiri mai tsire ya yi
mishi ba, hasalima ko gidan da
84
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Salim yake ciki Jinjiri ne ya nemar
mishi.
Haka nan cikowar da ake samu
a wurin ya sanya mutane da yawa
suna zuwa wurin don kawo abin
sayarwar su, hakan ne kuma yasa
ba kalar mutanen da babu a
wurin, ga masu gasa kaji ga kayan
marmari nan iri-iri, ga kayan
masarufi, ga kuma abin sha da ya
danganci ruwa, sai dia ban da
barasa.
Daga nesa kaxan ya samu wuri
ya yi parking don ya samu ya xan
gaggaisa da jama’a, hr ya iso
wurin Jinjiri ya miqa mishi hannu
suka gaisa.
“Kai oga Salim ka yi wuyar
gani”.
Salim ya xan yi tsaki kafin ya
ce, “Bari kawai Jinjiri, aikin namu
ne sai a hankali, bai barin mutum
ya samu wani lokaci mai yawa don
kanshi”.

85
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Jinjiri ya ce, “Eh, akwai wannan
kam, amma kuma ai akwai kuxi a
aikin, kai ka ga irin canzawar da
ka yi kuwa? Ka wani murje ka cika
ka yi gwanin sha’awa, haskenka
ya qaru, kwarjininka ya qara
bayyana sia wani annuri ke fita
daga jikinka”.
Salim ya yi murmushi ya ce,
“Kai dai Jinjiri baka rabo da
zolaya, yi min haxi irin na kullum.
Amma na rantse in ka yi min mix ba
zan biya ba”.
Jinjiri ya tuntsure da dariya
tare da faxin “Oga Salim kenan
baka da dama, ni ban ma jin na
tava yi maka wani mix, kai dai
kawai a kawo mai zafi”.
Salim ya ce, “Oho! Wannan
kuma ruwanka”.
Yana tashe da tsiren nashi,
yana ci cikin nishaxi da
annashuwa suna kuma hirarsu,
daga nesa kaxan suka hango
hayaniya tan xan tashi, kan ka ce
86
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
meye wannan suka hango wata
yarinyar mace ta cakume wani
mutum ta shaqe mishi kwalar riga,
tuni kuma har ‘yan gaza gani sun
fara zagaye su don ganin qwal
uwar daka.
Salim ya kalli Jinjiri dake ta
faman yankawa kostomominshi
tsire ya ce, “Kai ana wani al’amari
a garin nan, wai mace ta sa hannu
ta cakume namiji ko kuma ta
warware hannu ta yanke shi da
mari bai zame mata komai ba”.
Jinjiri ya ce, “To wane abin
mamaki kake gani tunda kana iya
kwana bakwai har fiye da haka
baka zo nan wurin ba”.
Salim ya ce, “Kai Jinjiri, wane
abin mamaki ne ya wuce mace ta
mari namiji ya tsaya sonqoqon
yana kallon ta?”
Jinjiri ya ce, “A’a, to oga Salim
in bai yi sonqoqon ba me zai yi?
Ramawa zai yi?”

87
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Salim ya ce, “A’a, ni kam mace
ta warware hannu ta mare ni ai
kuwa jikinta ne zai gaya mata,
tunda mu dai a wurinmu ai bamu
taso mun ga haka ba, to don muna
nan kuwa ai ba zamu koya ba”.
Jinjiri ya yi dariya ya ce, “Oga
Salim kenan, har yanzu da sauran
ka quruciya tana xiban ka, in ba
haka ba ita mace a ba a dukan
ta”.
Salim ya kalli Jinjiri da gefen
ido ya ja tsaki ya ci gaba da cin
naman shi, a zuciyarshi kuwa qara
yabon naman Jinjiri yake yi.
Xaya daga cikin ‘yan aikin
Jinjiri da ya tafi kallo ya dawo
wurin shi ya zauna, ya kama aikin
shi tare da baiwa Jinjiri labarin
abin da aka yi.
“Maigida ai xan iskan mutumin
nan ne da ya karvi xanin xakinka
rannan ya qi biyanka xari biyun
ka, ashe ita ma yarinyar sa kai
kawai ya yi yayi tafiyar shi ya
88
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
barta ko na abinci bai ba ta ba,
shine ita kuma yanzu da ta hango
shi cikin jama’a ta lallavo ta zo ta
cakume shi tana faxin ya biyata
kuxinta ko kuma suyi wacce za su
yi, don kuwa ai jikin nata ba jikin
banza bane”.
Jinjiri ya yi tsaki ya ce, “Ai
matsiyaci ne yaron, dama qyale
shi kawai ta yi”.
Tasi ya ce, “Haba maigida, ta
qyale shi kuma? Gobe ma ais ai ya
sake yiwa wata haka, sannan ka ji
irin bayanin da take yi ne a
kanshi? Ta ce da kamar qaramin
zango ne da shi ma to da sai ta
haqura, amma a irin dogon zangon
da yake da shi ya ba ta kuxinta
kawai”.
Jinjiri ya qyalqyale da dariya
yana faxin, “Ja’iri, da ganin shi ai
ka san wannan za a tava dashi”.
Salim wanda taxin nasu ya zo
mishi a wani dunqulallen
cukurkwaxaccen qazamin taxin da
89
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
bai fahimci ainihin me suke nufi
ba, bai san sanda ya tambayi
Jinjiri, “Kana da xakin haya ne a
garin nan naka na kanka?”
Jinjiri ya xan ranqwafo da
kanshi kusa da Salim ya ce, “Oh-
oh! Wata ‘yar hikima dai kawai na
samo oga Salim, wannan xan
xakin nawa ne daka sani, tattara
iyalina na yi na mai da ita gida na
ce ta je can ta zauna kawai a
qauye ita da manyan udka na
rinqa samun lokaci ina zuwa ya fi
min ta zo nan ta zauna min tana ta
sani a gaba da fitina, a can ban
huta ba a nan ma haka, ka san su
xin sai haquri kawai, amma ai ba
wani zaman lafiya ake yi dasu ba”.
Salim da bai ma san iyalin ba
balle ya san ana zaman lafiyar
dasu ko ba a yi, ya ce, “Haka ne”.
Tare da ci gaba da sauraron
bayanin da ake yi mishi.
Jinjiri ya sake kallon Salim ya
sake rage murya sosai ya ce,
90
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
“Yauwa, to mu nan dukanmu ba
nema ne ya kawo mu garin nan
ba?”
Salim ya gyaxa kai tare da
faxin, “Qwarai kuwa”.
Jinjiri ya qara jin daxin
fahimtar zancenshi da Salim ke yi,
ya sake faxin “Yauwa, to shine
xakin nawa maimakon in barshi ya
yi ta zaman banza haka kawai sai
nake ba da xanin shi ga waxannan
qananan ‘yan iska masu yi a
ko’ina saboda basu da kuxin kama
xakunan Hotel awa xaya xari biyu,
awa biyu xari huxu.
A haka in gaya maka oga Salim
ba qaramin alheri nake samu ba,
da ka ji an ce su biya xari uku ka
riqe canjin, to sauran xari biyun ta
xakin ne. A wuni sai in samu dubu
biyu, dubu uku ka gane?”
Salim wanda vacin ranshi kan
bayanin na Jinjiri ya kasa voyuwa
gare shi ya ce, “Zan dai gane, da
fa nan haka suka yi in sun
91
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
matsu.....” Bai jira qarin bayanin
na Jinjiri ba ya kama hanyar shi ya
tafi.
A cikin mota yana tafiyarshi a
hankali yana tunanin kai wanda ke
zaune a arewa bai yi kallon komai
ba, shi kam a iya zuwan da ya yi
garin nan ya ga abubuwan ban
tsoro da ban mamaki iri-iri, amma
kuma a iya duk abin da ya gani ko
ya ji, to bai tava gani ko jin abin
da ya vata mishi rai ya ba shi
qyama irin na Jinjiri ba.
Yana kwance a kan gadonshi,
shirin yin bacci yake yi, hirarshi da
Jinjiri ta sake faxo mishi cikin
zuciyarshi, kai wacce irin
kwamacala ce wannan? Wane irin
iya shege ne haka? Wane irin
qazanta ake yi a garin nan?
Wannan wace irin rayuwa ce?
Magidanci mai iyali ya kora
matarshi gida don kawai tana yi
mishi fitina ya mai da xakin da
suke kwana a ciki shi da ita na
92
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
haya ga mazinata, sannan in an
gama shima ya shiga ciki ya je ya
kwanta.
Wannan wace irin qazanta ce?
Kai bai tava jin qyamar wani
mutum irin qyamar da yake yiwa
Jinjiri ba a halin yanzu.
Kai tir! Me Jinjiri zai yi da kuxin
da yake karva? Wai me mutane ma
suka xauki kuxi ne? Kai daga yau
ba zai sake zuwa wurin Jinjiri mai
tsire ba, ba ma zai sake cin tsiren
nashi ba.
Yana cikin haka sai kuma ya
tuna an ce, addini nasiha ne. Nan
take ya tsaida ranshi a kan kafin
ya xauki mataki a kan jinjiri, to
bari ya samu lokaci ya yi mishi
nasiha tukunna, in yaso in ya qi ji
sai ya fita hanyar shi, in kuwa ya ji
to sai ma ya samo wasu kuxin ya
ba shi kyauta don ya qara jarin
shi.
In ma yana da matsalar jari ne,
tunda ai yana da sana’a mai kyau,
93
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
kuma shima Jinjiri yaa yi mishi
alheri mai yawa a farkon zuwan
shi garin nan, to bai kamata kawai
ya guje shi ba tare da ya jarraba
gaya mishi gaskiya ba.

94
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
BABI NA BAKWAI
ADAMAWA

F
irgigit! Ta farga daga baccin
nata saboda mummunan
mafarkin da ta yi da Salim,
yauma kenan ba za ta yi baccin
ba, gashi a satin nan gaba fama ta
yi ta yi da wani irin matsanancin
ciwon kai.
Ta zauna kan gadon nata tana
ta faman tunane-tunane, yanzu a
haka za ta zauna babu halin ta
xora kanta a filo da sunan bacci
sai ta yi mafarkin yaron nan?
Mafarki kuma mara daxi, kusan
kullum ganin shi take yi cikin daji
yana gudu yana neman taimako
saboda mugayen mutanen da suke
biye da shi.
Amma babu halin ta gayawa
Malam Manu sai ka ji ya faxi wata
maganar da za ta gwammace da
jan bakinta kawai ta yi ta yi shiru
da ya fi mata sauqi.

95
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Tabbas Salim bai cikin
hayyacinshi yana cikin wani hali,
abin da zuciyarta ta ja ta tsaya a
kai kenan.
Inda yana cikin hayyacinshi da
babu yanda za a yi ya yi wannan
daxewar bai zo ba, kuma ai da
yanayin mafarkin nata ma zai xan
canza amma ba kullum ta rinqa
ganin shi a cikin buqatar taimako
ba, daga ta ganshi yana gudu a
daji ana biye da shi da wuqaqe da
adduna sai ta ganshi a xaxxaure
anyi mishi xauri irin na huhun
goro.
Ta yi kamar ta je ta tashi
mijinta ta gaya mishi irin mafarkin
da yauma ta sake yi, sai kuma ta
ga in ta gaya mishi to me zai yi
mata in ban da baqar magana, da
ita yake yiwa ma to da da sauqi,
to xan nata yake yiwa.
Ta xaga ido ta kalli agogon
dake saqale a xakin nata wanda

96
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
shima Salim xin ne ya kafa mata
shi a nan wurin.
Qarfe biyu ne da minti arba’in
da biyar, ta gyara ta kwanta ta
sake jan abin rufuwarta ta rufu,
sai dai ta san ba don ta yi bacci ta
yi hakan ba, don kuwa ita ma ta
san bai smauwa gare ta.
Washegari tana idar da sallarta
ta yi maza ta hanzarta baiwa
iyalinta abin karyawa don kar
Malam Manu ya ce haqqoqin
mutane da take dannewa a kan
Salim yana cikin dalilin da suke
sawa matsalolin da take cewa
Salim xin yana ciki.
Ta gama abin da take yi ta je
ta samu mijin nata cikin nutsuwa
da ladabi ta nemi izinin shi na
zuwa barkar haihuwa gidan su
Ladin Liman.
Ya ce, “Sai kin dawo”.
Karva na mutunci Ladi ta yi
mata saboda tsohuwar sanayyar

97
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
dake tsakanin su da kuma
mutunci.
Bayan sun gama gaisawa ta yi
mata barka kan haihuwar da
surukar tata ta yi, ‘yar hirar ‘yar
qanqanuwa suka yi Ladin Liman ta
kalle ta ta ce, “Ni bana Inna Wuro
ciwo kike yi a tsaitsaye ko kuwa
Malam ne ya tasan ma qaro mata?
Tunda ai kin san su maza basu
girma da yin aure”.
Inna Wuro ta kalle ta a sakarce
ta ce, “In Malam zai yi aure sai ayi
me?”
Ladi ta yi dariya ta ce, “Uh-uh!
Inna Wuro”.
Kan ta yi wata magana Inna
Wuro ta ce mata, “Ke ni qyale ni
da maganar wata kishiya, ai an
riga an ci dubu sai ceto, in da
Malam kishiyar ya yi min ai da ya
fi min sauqi kan halin da nake
ciki”.

98
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Da sauri Ladi ta kalle ta ta ce
mata, “Me ya yi zafi haka Inna
Wuro? Wani ciwo ke gare ki?”
Inna Wuro ta gyara zama cikin
bayani mai cike da kara irin ta
mutanen mu ta ce mata, “Xanki”.
Ladi ta yi maza ta dafe qirji ta
ce, “Kar dai ki ce min shine yake
cikin matsalar?”
Inna Wuro ta ce, “Yau shekaru
kusan uku kenan rabon shi da
gida, babu shi kuma babu wani
bayani game da shi”.
Nan take Ladi ta kama salati
har tana share fuska da gefen
zani, alamar wani hawaye ne yake
zuwa mata.
“Haba ni fa na kwaana biyu
ban ji Liman yana faxin ga wani
alheri an kawo mishi daga gidan
nan naku an ce daga wurin shi ne,
to amma shine kike zaune shiru
haka babu wani motsi?”
Inna Wuro ta ce, “To me zan
yi? Ya ya zan yi? A gida ma fa bani
99
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
da halin yin wata magana sai
Malam ya hau faxa”.
Ladi ta ce, “Kya biye mishi, ai
ba zai yiwu ba kin san su maza
jarumtakarsu kan al’amarin ‘ya’ya
daban ne, mu kuma tamu daban.
Su suna iya fushi da xa tun kafin
su ganshi, mu kuwa ko zamu yi
fushin to mu kam mu kam bari sai
mun ga xa ya zo gabanmu mun ga
lafiyarshi sannan duk abin da
zamu yi sai mu yi”.
Inna Wuro ta ce, “Haka ne
Ladi”.
Ladi ta ce, “A’a, to ana ma
magana wannan wuri da in kana
jin labarin shi sai ka ga tamkar in
ban da dole babu abin da zai sa
naka ya tafi, wata da take bani
labari fa cewa ta yi, mu a nan ne
muka xauki cin mutum wani
mummunan al’amari, su a can har
da irin allon nan na kan hanya mai
nuna alamar wuri, to su can har da
mai nuna inda za a samu idon
100
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
mutum ko harshe ko hannu, ko
kunne. Ke abin dai gashi nan sai
su da suka je suka san yanda
lamarin yake.
Inna Wuro dake zaune a gefen
Ladi cikinta ya ba da sautin qululu
har sai da Ladi ta jiwo ta.
“Ai ba za ki biye mishi a zauna
haka ba, addu’a za ki yi ta yi ko in
ce zamu yi ta yi”.
Inna Wuro ta ce, “Ina kam”.
“Ai ba ke kaxai ba, za kuma
kisa ayi ta yi”.
Inna Wuro ta ce, “To kamar wa
kenan za a sa?”
Ta yi murmushi ta ce, “Ka ji
kuma Inna Wuro, a iya shekarun ki
baki da wani Malami da kike
mu’amala da shi?”
Inna Wuro ta ce, “Uh-uh! Ladi
ni da kike ganina tamkar kifin
rijiya nake, ban san komai ba, ‘yan
matsalolina tashi kawai nake yi
cikin dare in yi ‘yan addu’o’ina
daidai gwargwado”.
101
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Ladi ta ce, “Uh! To haka ne, ai
da yake mijin naki ba mai yawan
kwaramniya bane, amma mu da
yake kullum a cikin maganar
kishiya muke ai bai yiwuwa mu
zauna haka sai a nemi a sabauta
ka, in kin tashi na raka ki wajen
wani nan ta baya”.
Inna Wuro ta ce, “Sai dai ban
gayawa Malam cewar bayan nan
xin zan sake shiga wani wurin ba”.
Ladi ta yi murmushi ta ce,
“Inna Wuro wannan da gangan ma
dai kike rama, don kuwa na gane
abin bai wani dame ki ba”.
Inna Wuro ta ce, “Ba haka
bane Ladi, amma dai to muje in na
koma gida na yi mishi bayani”.
Suna zazzaune gaban Malam,
bayan Ladi ta yi mishi bayanin
komai, shi kuma ya shiga bincike
yana duddubawa a qasa.
Ita kuwa Inna Wuro gabanta
sai faman harbawa yake yi, ta kai
matuqa wajen tsoro saboda sanin
102
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
irin bayanin da mijinta ke yi mata
kan mata masu zuwa wajen
bokaye.
To shi wannan dai ba qasa
yake zanawa ba, don haka ba boka
bane. ‘Yan yatsun shi yake
mummurzawa tare da yin lissafi,
in ban da dole kuma babu abin da
zai sa in zo nan tunda da can ai
ban tava zuwa ba.
“Kece mahaifiyar shi ko?”
Ya yi tambayar daidai lokacin
da ya xago kai yana kallon Inna
Wuro.
Ta xan sunkuyar da kanta qasa
cikin yanayin jin kunyar amsa
“Eh”. Ita ce saboda kar Ladi ta yi
maza ta ce, “Eh, ai nice na yi
matra bayanin ita ce mahaifiyar
shi”.
Ya ce, “To gaskiya da kam
yana cikin matsala, don kuwa
gashi nan komai ya bayyana yana
son zuwa hankalinshi yana gida,

103
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
sai dai bai da halin zuwan saboda
a xaxxaure yake cikin sarqoqi”.
“Innalillahi wa’inna ilaihir
raji’un!”
Abin da ta faxi kenan cikin
zuciyarta. Ya yin da ita kuma Ladi
take tambayar neman sanin yanda
za a yi.
Ya ce, “To akwai abin da muke
yi muna daga nan mu tura masu
kwancewa su kwance shi, tunda
inda yake xin ba wuri ne da za a
tura mutum ya je ba, tunda mugun
wuri ne”.
Ladi ta kalle shi ta ce, “A
taqaice dai ba ya hannu mai kyau
kenan?”
Ya ce, “Ko kaxan, amma in
mun yi aiken ina ganin nan da
kwana bakwai zai samu isowa
gida”.
“To kuma me za a kawo?”
Ya ce, “To in da hali a kawo....”
ya xan ja kafin ya ce, “To amma ko

104
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
zan gaya muku abin ne kawai ku
nemo?”
Ladi ta yi maza ta ce, “A’a,
Malam abin saye kawai za a gaya
mana”.
Ya kintata kuxin ya faxa suka
yi godiya suka fito.
Suna tafe Ladi tana tambayar
Inna Wuro, to waxannan irin kuxi
da Malam ya ambata kina dasu
kuwa Inna Wuro?”
Ba tare da ta kalli Ladi ba ta
ce, “Ban dasu, amma ina da
dabbobi in kuma har wannan
yaron zai dawo ai zan iya fito da
abin da ya fi haka”.
Ladi ta ce, “Haka ne”.
Tana isa gida ba ta wani vata
lokaci ba tasa Hamza ya kama
tumakinta guda uku ta ce ya kai
kasuwa duk yanda aka taya a
karvi kuxin kawai.
Hamza ya tsaya yana kallon
uwar tashi ya ce, “Amma Inna ba

105
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
za ki bari Baba ya dawo ba
tukunna?”
Ta ce, “A’a, Hamza jeka kawai
su tumakan nan ai nawa ne, in ya
dawo nayi mishi bayani yi sauri
Hamza, in muka yi sa’a kwanan
nan za ka ga yayanku ya dawo”.
Hamza yana jin yayansuz ai
dawo ya yi maza ya tasa tumaki a
gaba ya fita dasu ya nufi kasuwa.
Suna zaune ne bayan sun
gama cin abincin dare Inna Wuro
ta yiwa Malam Manu bayanin da
take ganin ya kamata ta yi mishi.
Bai xaga ido ya kalle ta ba
balle ya tanka mata.
“Baka ce komai ba Malam”.
Ya yi shiru bai amsa ba tsawon
lokaci tana magana kafin ya xaga
ido yaa kalle ta cikin nutsuwa ya
ce mata.
“Ba kina gadarar awakinki
bane yasa kika zartar musu da
hukuncin sayarwa ba tare da kin
jira na dawo ba? Saboda ni kin fini
106
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
son shi kin fini sanin ciwon shi, ke
ya zauna ne a cikinki, ke kika yi
naquda kika haife shi, ni kuwa
ganin shi kawai na yi a duniya ya
faxo.
To na ji, to unguwar da kika
tambayeni gidaje dai kika je biyu
koma fiye da hakan, ban yarda ba
inda haqqina a ciki kuma ban
barshi ba. Awakin da aka sayar
kuwa aje a dawo min dasu ban
yarda da sayarwar da aka yi musu
ba, ko ba nawa abane ai a gidana
suke zaune”.
Inna Wuro ta kama kuka, shi
kuwa Malam Manu ko a jikinshi ya
barta nan zaune tana ta faman
quma.
Gari na wayewa sai ga Ladin
Inna ta zo gidan, tabbataccen
albishir ta zowa Inna Wuro da shi
na Malam ya ce a gaya mata an
kammala komai har ma kuma anyi
aiken, don haka a zuba idon ganin
shi nan da kwanaki bakwai.
107
Idan kunne yaji…….1
Sodangi

ADANTA
Wayewar garin yau juma’a ce
ta kuma kasance rana ce ta hutun
ma’aikata, saboda kasancewar ta
ranar xaya ga watan biyar. Don
haka bayan ya kammala duk wani
abu da ya kamata ya yi a gidan
nashi, sai kawai ya fito waje da
kujerar shi ta roba tare da jarida a
hannunshi yana dubawa.
Jaridar Abuja ce a hannunshi
wato The Nation. Yanayin garin
mai daxi ne kamar kullum, yau ma
lulluve garin yake cikin ni’ima mai
daxi, idan ka kalli yanayin
samaniya za ka yi zaton ba za a
xauki wani lokaci mai tsawo ba za
a fara zubar da ruwan sama, sai
dai ba haka abin yake ba.
Bai kai minti goma sha biyar a
wurin ba wani maqwabcinshi
baban Abdul ya yi mishi sallama,
ya kuma matso alamar dai ya zo
mishi hira ne.
108
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Ya miqe daga inda yake zaune
ya baiwa Baban Abdul kujerar shi
kuma ya nufi cikin gida ya sake
xauko wata kujerar robar ya zauna
a kai, suka shiga hirarsu kan
al’amuran da suka shafi qasa da
irin gwagwarmayar da talakan
qasa ke yi kan rayuwarsa.
Matar Baban Abdul ta fito daga
gida suna gaisawa da Salim, ta
kalli mijin nata ta ce mishi za ta je
cin kasuwar Umueche dake ci a
ranar.
Ta juya ta tafi bayan ya ce
mata to sai ta dawo. Salim ya bita
da kallo tare da jinjina al’amarinsu
cikin ranshi.
Shi dai Baban Abdul xan arewa
ne na asali, kana ganinshi kuma
ka san shi xin xan arewan ne ba
sai an tsaya kace-nace ba.
Ya tafi Adanta ne a dalilin aiki
ya kai shi can, amma ita matarshi
Ihouma ‘yar Ogbodo ce wacce ya
aura a dalilin ya yi mata ciki ta qi
109
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
yarda a cire cikin, to a haka dai
yanzu ‘ya’yansu biyar, biyu maza
uku mata.
Ya sake binta da kallo bai ga
wani abin sha’awa a tare da ita
ba, ita ba kyau ba, ba kwalliya ba,
ba iya tafiya ba, gata wata
kurtuveviya, gata kullum kanta a
aske tamkar wata namiji.
Nan take ya ji zuciyarshi ta
soma aiyano mishi irin matar da
zai aura, na farko dai dole ne ta
zamo mai ilimi, dole ta zama ‘yar
gaye ajin farko, don shi kam ba zai
iya zama da macen da ba ta iya
kwalliya ba, dole ta zama
wayayya, don ya ji daxin shiga
jama’a da ita, dole ta zama mai
dogon gashi da dara-daran
idanuwa.
Kai shi kama yana son gashi da
idanuwa a wurin mace, ta kuma
iya tafiya wato taku mai kyau. In
har ya samu haka, to shi kam ma
ba sai lalle ta iya girki ba ko kuma
110
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
tsabtar gida, shi zai nemo wanda
zai rinqa kulawa da wannan, tunda
shi kam burinshi wajen ‘ya mace
ai bai wuce ta jiyar da shi daxi ba
ta shagalar da shi, in har yana
tare da ita ya ganta ta yi wanka ta
yi kwalliya tana mishi yauqi suna
tarairayar juna ita da shi.
Bai jin zai samu wannan a
wurin irin waxannan matan da
basu iya komai ba sai masifan
faxa da shegen kishin su na
hauka, ga rainin hankali. A
kowane lokaci a shirye suke su yi
dambe da namiji.
Shi idan zai yi aure arewa zai
tafi ya duba yarinyar da ta gama
jami’a ta kuma mallaki waxannan
abubuwan da yake buqata baki
xaya, dan kuwa shi dai bai tava
yiwa kanshi sha’awar mata biyu
ba, don haka in ya tashi yi to zai
tsaya ne sai ya zava ya darje ya
samu irin wacce yake so tukunna.

111
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Bai wani ja hira ya yi tsawo
sosai ba tsakaninshi da Baban
Abdul, don kuwa yana da alqawari
tsakanin shi da abokinshi Sony, za
su je partin da wani abokinsu ya
shiryawa budurwarshi ya kuma zo
takanas ta Kano ya gayyace su, ya
kuma roqi su halarta, dan haka
suka shirya zuwa.
Kwalliyar da ya yi mai sauqi ce,
material trouser ya saka da litteu
longsleve, sai takalmi sawu ciki
suwet mai asalin kyau. Bai daxe
yana jiran Sony ba shima ya iso
suka kama hanya suka tafi.
Wurin partin ya qawatu ba
kaxan ba, a sarari ake yin shi an
kuma shirya shi yanda ya dace da
mutanen dake wurin, wurin ya
qawatu fiye da a ce wani Hotel aka
kama.
Bakin ruwa ne ga ciyayi
baibaye da wurin, ga tsabta, ga
kujeru da ‘yan tebura a
tsakaninsu, ga bishiyoyi sun yiwa
112
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
wurin lif-lif gwanin sha’wa, sun
sanya wurin ya zamo tamkar
Turai.
Har cikin zuciyar Salim wurin
ya burge shi, in ban da shi xin ba
mai sha’awar shiryawa kanshi
Birthday bane da ya ce in ranar
haihuwar shi ta zagayo nan zai zo
ya shiryawa abokai qasaitaccen
liyafa.
To amma duk da haka saboda
sha’awar da wurin ya ba shi sai ya
ji tamkar in yaje arewa ya yi aure
ya dawo da matarshi to ya zo nan
wurin ya tara abokai ya shirya
musu qasaitaccen buki don su
taya shi murnar auren nashi.
Masu band suna ta yi, kixi suke
yi cikin nutsuwa da qwarewa, ya
yin da gangunan nasu ke ratsa
zukatan waxanda suke wurin
saboda zaqin su.
Tunda ya shigo wurin bai
zauna ba saboda nishaxin da
wurin ke sanya shi, zuciyar Salim
113
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
ta yi wani wasai saboda kyan
wurin.
Wani irin nishaxi ya rinqa
shigarshi, ya rinqa jin kanshi
tamkar wani saurayi mai shekara
goma sha takwas don tsananin
nishaxin da yake ji.
Tuni Sony da suka zo tare ya
koma can shi da wata yarinyar da
ya samu, ya waiwaya ya sake
kallon shi sai faman zuba yake ta
yi.
Cikin zuciyar Salim ya yi
murmushi ya ce, “Ko me yake
gaya mata oho?” Ya ja wani xan
qaramin tsaki cikin ranshi ya ce,
“Mata! Baran ma dai irin na garin
nan shi kam bai sake vata lokacin
shi a kansu, don haka tsakaninshi
dasu kawai hi-hi ne”.
Daga can nesa ya hango Prisca
ta sha kwalliya cikin qananan
kaya, ya kuma tabbatar ta hango
shi don wurin shi ya ga ta nufo.

114
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Ya yi kamar ya yi maza ya bar
wurin, sai kuma ya ga to ai hakan
ba zai hana ta binshi ba, don haka
ya ja ya tsaya.
“Hi!” Salim bai kalle ta ba ya
ce, “Hi!’
Prisca ta matsa kusa da shi
tana magana bai xaga ido ya kalle
ta ba balle ya ba ta amsa, ta yi ta
maganganun ta kan abin da ya yi
mata a Hotel xin Delacruise da
kuma zuwa gidanshi da ta yi har
sau biyu maqwabtanshi sun
shaida mata yana nan ciki ta kuma
yarda don ta ma ga motar shi a
waje, amma ta yi ta qwanqwasa
qofar ya qi buxewa.
“Salim!” Ta sake kiran sunan
shi saboda shirun da ta ji ya yin ya
yi yawa.
“Nayi maka wani abune?”
Ta kalle shi yana sunkuye ta
ce.
“In ma wani abu na yi maka ka
gaya min zan iya cewa ka yi
115
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
haquri, ai ba wani abu bane don
na baka haqurin tunda ina sonka
na kuma..........”
Ba ta qarasa maganar tata ba
D.J ya fara magana a lasifika
alamar dai masu bukin Birthday
xin sun iso, don haka Salim ya
juya ya yi tafiyarshi ya barta nan
wurin a tsaye.
An karrama shi a wurin ba
kaxan ba shi da Sony, ba a wani
daxe da farawa ba aka buqaci mai
Birthday da ta yanka cake xin
birthdayn nata, ita kuma sai ta
kira masoyin nata Eze suka yanka
tare, ta kuma gutsuro wani yanka
ta saka mishi a baki.
Bayan nan ne Eze ya rako ta
suka soma zagayawa don gaida
mutanen da suka zo mata bukin.
Eze da budurwar tashi Beauty
suna tsaye tare da Salim suna
hira, don kuwa sun daxe da sanin
juna ba yau ya fara saninta ba.

116
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Sai ga wata yarinya ‘yar gaye
sosai ta nufo su cikin murmushi da
iya taku mai kyau da ban sha’awa,
tana isowa suka rungume juna ita
da Beauty cikin matsanancin farin
ciki.
Sun gama murnarsu kafin ta
waiwaya wurin Eze ta gaishe shi
cikin sanayya mai yawa, ita kuma
Beauty tana gayawa Salim wannan
qawata ce tun muna yara,
rabonmu da haxuwa bana shekaru
biyar kenan, tun kafin ita xin ta
taci A.B.U Zaria.
Nan take Salim ya miqa mata
hannu cikin murmushi, “Kin san
arewar mu kenan?’
Ta miqo mishi nata hannun
tare da rama mishi murmushin da
ya yi mata, “Kana mamaki ne?”
Tambayar da ta yi mishi cikin
harshen Hausa ya sanyasu gaba
xaya kwashewa da dariya.
“To sunana Salim”.
Ta ce, “Ni sunana Janet”.
117
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
“Kin shekara biyar a Zaria?’
Ta sake gyaxa kai.
Ya ce, “Ai bana musu tunda
gashi har yaren namu kin iya”.
Ta ce, “Ba yare kawai na xauko
ba”.
Ya yi maza ya ce, “Bayan shi fa
me kika zo da shi?”
Ta ce, “Al’adunku”.
Ya yi maza ya qyalqyale da
dariya tare da faxin “Wannan
shine wasa, al’adunmu na arewa
ba al’adun bane irin taku dake
saurin karvar baquwar xabi’a,
sannan komai na al’adun namu
kan tafi ne a qarqashin tsarin
addinin mu, kamar cimar mu,
suturar mu. Kai komai ma namu,
don haka wanne kika xauko? Ko
ba komai dai gaki a nan na kuma
ganki a yanda na ganki”.
Ta yi murmushi ta ce, “To ai
nan cikin ‘yan’uwana na zo party
kuma ake yi, don haka don ka
ganni a haka ba komai bane”.
118
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Ta qara kallon kan nata ta qara
tabbatarwa kanta kyan kwalliyar
tata, sai dai ta san wurin xan
arewa ba komai bane hakan illa
fitsara.
Ta xago ido ta kalli Salim ta
sake kashe shi da wani murmushin
nata mai ban sha’awa, kafin ta ce,
“Amma a misali in abin a ce kai ne
ka gayyace ni a matsayin ka na
xan arewa da kuma na lura na
gane kana son arewar taku, to zan
iya xauro maka zanin atamfa in
kuma zo gidanka in ci tuwon dawa
miyar kuka, sannan in xora
damammiyar fura a kai”.
Dariya mai tsanani yake yi tare
da faxin, “Lallai na yarda ban da
harshen Hausa da kika koyo a
zaman da kika yi a arewa har
al’adar Haausa kin xauko, tunda
kin iya sanya suturarsu kin kuma
iya cimarsu”.
Ana cikin haka ya hango Prisca
ta dunfaro su da saurin ta take
119
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
zuwa, babu alamar walwala a tare
da ita, ya tabbatar mu’amalar shi
da Janet ce ta yi matuqar vata
mata rai hakan ya sa shi
ranqofowa kusa da kuncin Janet ya
xan sumbace ta tare da kama
hannunta ya riqe.
Ta iso wurin daidai ya xora
hannun a qwuvin Janet ya riqe ta
sosai. Prisca ta kalle shi cikin huci
saboda tsananin vacin rai, ta xaga
ido ta kalle shi ta ce.
“Xan iska kawai, abin da ka fi
iyawa kenan yaudarar ‘ya’yan
jama’a, in ka gama da wannan ka
koma kan wannan, a haka
rayuwarka za ta qare, a haka
kuma za ka mutu”.
Salim ya kalle ta ya yi
murmushi tamkar bai ji
mummunan maganar da ta gaya
mishi ba.
“Prisca kenan, ai daga kanki
ba zan sake yaudarar wata yarinya
ba, ita wannan aurenta zan yi”.
120
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Ta yi maza ta ce, “Qarya kake
yi mayaudari, abin da kowacce
kake gaya mata kenan”.
Ya ce, “To bari dai ma in
tabbatar miki”.
Yana faxin hakan ya juyo ga
Janet wacce ke tsaye cikin
murmushi alamar ruxanin na
Prisca bai shafe ta ba, ya zuba
mata ido cikin natsuwa ya ce.
“Please Janet my love will you marry
me?”
Psisca tana jin haka wani irin
jiri ya xebe ta, ba a san yanda aka
yi ba sai kawai aka ganta ta yi
baya-baya ta faxi a haka, irin
faxuwar ‘yan bori.
Salim ya kamo kafaxun Janet
ya xan rungume ta a jikinshi ya
xan waiwaya ya kalli cikin
idanuwanta ya yin da shi da ita
dukansu suke murmushi.
Ya ce mata, “Ko zamu kauce
daga wurin nan ne mu barshi don
kar wannan mahaukaciyar ta dawo
121
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
cikin hayyacinta ta lalatawa
Beauty taro?”
Ba ta yi magana ba.
“Ba hankali ne da ita ba, kinga
kuma babu daxi ka yiwa mutum
sanadin abin da babu daxi”.
Bai tsaya yiwa Sony sallama ko
sauraron wani abu ba don gudun
kar Prisca ta wattsake ta ganshi a
nan wurin, tunda ya san halinta.
Ya xan kalli Janet kaxan ya ce
mata, “Nifa gida za ni don ba zan
jira mahaukaciyar yarinyar nan ta
dawo hayyacinta ta same ni a nan
ba, ya ya kike gani ko zamu je
ne?”
Ba ta yi magana ba, ya xan
kalle ta da gefen ido cikin natsuwa
ya ce mata, “To ko kuma kin fi so
ki tsaya ki gama gani?”
Waiwayi ta yi tana kallon
yanda mutane suke ta harkokinsu,
ya yin da shi kuma ya zuba mata
ido yana qare mata kallo, tana da
kyau ba kaxan ba, gata gwanar
122
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
kwalliya da iya magana, ga
dukkan alamu kuma tana da
natsuwa.
Abinta xaya ne akwai da yake
shi xan Adam a kullum tara yake
bai cika goma ba, gashin kai bai
wadace ta ba, amma kuma hakan
bai hanata kyan ba, bai ma rage
mata komai ba da yake ta iya
gyara wanda take da shi xin.
Ta waiwayo ta kalle shi suka
yiwa junaa murmushi.
“Waccan mahaukaciyar nake
jiye miki, in ta wattsake ta tashi ta
same ki a nan wurin ban san irin
abin da za ta yi ba, ke kuma ban
ga alamar irin wannan haukan a
tare dake ba”.
Ta yi murmushi ta ce, “Ka
kuma san ban iya dambe ba ba”.
Ya tayata murmushin ya ce,
“Ai baki dace da shi ba ma,
kyawawan mata irinki basa irin
wannan rashin hankalin”.

123
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
** **

BABI NA TAKWAS

T
ana tsaye a tsakiyar xakin
shi yayin da shi kuma yake
qoqarin haxa mata abin da za
ta sha.
“Me zan kawo miki?”
Ta xaga kafaxunta nuna rashin
damuwa ta ce, “Ko meye amma
light drink nake buqata kawai”.
Faxin haka ne yasa shi kawo
mata ‘Don Simon’.
Ta karva dai-dai ta zauna tana
buxe kwalin, ta ce, “Nice place,
wurinka ya yi min kyau ba kaxan
ba”.
Ya xan yi murmushi tare da
zagaye wurin da idanuwanshi, shi
kanshi ya san wurin nashi mai
kyau ne, don kuwa yana samun

124
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
natsuwa da nishaxi a duk lokacin
da yake hutawa.
Ya kalle ta ya ce, “Bana son
tarkace ne shi yasa”.
Ta ce, “Hakan ya yi kyau, sai
dai the place is still lacking”.
Ya yi murmushi ya ce, “To kina
nufin in yi gyara irin wanda za ki
yi? Ai yanzu dai tunda kin zo gidan
duk wani abin da kika ga yana
buqatar gyara sai kawai ki gyaran
shi, ni in kika barni a hakan ma ai
qoqari kawai na yi ba wai na iya
bane. Wane kos kika karanta ne a
jami’a?”
Ta ce, “Food and Nutrition, ina
so in baiwa iyalina cikakken
kulawa na lokacina a duk lokacin
da buqatar hakan ta taso”.
“Kina nufin za ki zama
cikakkiyar matar aure kenan ba
tare da kin yi wani aiki ba?”
Ta ce, “A’a, ba abin da nake
nufi kenan ba, ina dai nufin ne in
auri mutumin da zamu samu
125
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
cikakkiyar fahimtar juna da shi ta
inda zamu zamo muna taimakon
juna, in taimake shi shima ya
taimake ni”.
Salim ya yi murmushi ya ce,
“Symbiosis relationship kenan”.
Ita ma ta yi murmushin ta ce,
“Eh, haka nake nufi muyi da
mijina”.
Ya ce, “Yana da kyau, to amma
ta ya ya za a yi hakan?”
Ta ce, “Yauwa, ni xin ina so ne
ya zamo ina gudanar da al’amura
na kaina ba in yi aiki a qarqashin
wani ba, in zama ina ba da kaya
kamar a wurin buki ko suna ko
Birthday, wurin binne gawa da dai
sauransu, ya zama ina samun
kwangilar yin abubuwan ci da na
sha na ciyar da mutane ko kuma
bayar da kayayyaki a wuraren sai
da abinci irin su Mr. Biggs, kamar
su meat pie da duk wani abu
makamancin wannan, babu abin
da ban iya ba.
126
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
To ka ga hakan ba zai yiwu ba
sai da cikakken goyon baya na
maigida, to kuma ka gani ta haka
sai in zamo cikakkiyar matar aure
a gida”.
Ya kalle ta ya ce, “Kama dai”.
Ta yi murmushi ta ce, “To
kama tunda ba kowane lokaci ne
zan fita ba”.
Ya ce, “To haka ne’.
Ta ci gaba da shan abin da ya
kawo mata na sha, ya yin da shi
kuma ya zuba mata ido yana
kallon ta, bai san dalili ba ya samu
kanshi da tambayar ta.
“Kina sha’awar mutanen
arewa?”
Ta kalle shi ta yi murmushi ta
ce, “Ina kuma sha’awar mutanen
kudu”.
Ya ce, “To na ji, a cikin biyun
idan aka ajiye miki ga na arewa ga
na kudu wanne za ki xauka idan
aure ne?”

127
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Ta ce, “Me yasa ka yi min
wannan tambayar?’
Ya ce, “Ban sani ba, haka
kawai na ji ina son yin tambayar”.
Ta ce, “To shi kenan mu bar
maganar sai a lokacin da ka san
dalilin da yasa ka yi ta sai in baka
amsar. Kawo min hotunanka in
gani ina so in yi kallo”.
Ya xan yi murmushi ya ce,
“Bana ajiye hotuna saboda bana
son tarkace a xakina”.
Ta xan yi motsi kaxan kafin ta
kalle shi ta gefen ido ta ce, “Ko
kuma kana gudun kar watarana
wata ta zo ta gani ba, saboda ai
na ji abin da aka gaya maka xazu
cewar a haka za ka qare, kenan
kana dasu da yawa”.
Ya xan kalle ta cikin natsuwa
ya ce, “Ina ganin ni dake mu
baiwa juna lokaci don samun
kanmu maimakon amfani da jin
abin da wani ya faxa a kan wani”.

128
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Ta xan motsa kafaxa tare da
tave baki ta ce, “Well! Ban ga
laifin ka ba ma fa kana da kyau,
mata za su soka, babu wata mace
da za ta ganka ba ta yiwa kanta
sha’awar samun namiji kamar ka
ba”.
“Babu wacce za ta ganni ba ta
yiwa kanta sha’awata ba kika ce?”
Ta gyaxa kai ta ce, “Eh, abin
da na faxa kenan ba kuskuren
faxin kuma na yi ba”.
Ya sake kallon ta a ickin
idanunta, “Kina nufin har da ke
kenan a ciki?”
Ta yi dariya mai qarfi tare da
faxin, “Ka fiye yin tambayar
qwaqwa, ban ci abincin rana ba
ina jin yunwa”.
Ya kalli kicin xin nashi, “Ban yi
girki ba sai dai in za ki girka
mana, don nima zan so in ci
abincinki in ji da ni da na karanta
Economics dake da kika karanta

129
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Food and Nutrition wa ya fi wani
iyawa?”
Tana tsaye a kicin xin tana
yiwa tumatir yankan kwabo-kwabo
a kan chopping board, ya sunkuyo
da kanshi kan kafaxar ta daga
bayanta a hankali ya buxe baki
cikin nutsuwa ya ce mata, “Har
yanzu fa baki ban amsa ba, na ce
har dake a cikinsu?”
Ba tare da ta kalle shi ba ta ce
mishi, “Mu’amalata da kai daban
mu’amalarka dasu daban, mu xin
bamu wani daxe da sanin juna
ba”.
Ya xan motsa kafaxarshi ya ce,
“To sai me don bamu daxe da fara
sanin juna ba?”
Ya qara matsarta ta yanda
suka zamo jikinsu yana tava na
juna, “Kina nufin ko yau aka haxu
zuciya ba ta san abin da take so
ba? Abin da nake aiki dashi shine
abin da na ji zuciyata tana gaya
min game da mutumin da nake
130
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
tare dashi, in ina sonka ina sonka,
in bana sonka bana sonka”.
Ba ta kalle shi ba ta ce, “In ka
dena dai”.
Ya yi maza ya ce, “Eh, in na
dena sonka na dena sonka, don
haka kema a yanzu ya kamata a ce
a shekarun ki kina ganin abin da
kike so ko za ki so za ki gane”.
Ta ce, “Uh-uh! Ni ba haka nake
ba, da soyayya da abota ni ba
farat xaya nake yin su ba, na kan
baiwa kaina lokaci in yi nazari tare
da yin tunanin abin da zai fi
dacewa dani, yin ko barin”.
“Kenan kina son gaya min
cewar ina cikin waxanda kike
nazarinsu?”
Ta yi murmushi, kan ta buxe
baki ta bashi amsa ya ce mata,
“To ai anyi rashin dace, ni xin
bana jira don haka yau za ki bani
amsa, za ki fara zartar da
hukuncin abota ko soyayya farat
xaya a kaina”.
131
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Ya xan kishingixa kaxan jikin
kujerar ofishin nasu a dalilin
gajiya da aikin nasu da ya yi,
gashi kuma ya xan samu
tsagaituwar jama’a.
A cikin satin nan yana yawan
samun kanshi cikin nishaxi,
annashuwa da farin ciki, bai kuma
san dalili ba.
Nonso dake zaune a kan
teburin ta na aiki a gefen office
xin tana kurvan kofi ta ce, “Mr.
Salim! Wai ni meke faruwa ne? Ina
ganin kamar akwai wani abin da
kake voye mini”.
Ya yi dariya ya ce, “Kamar me
Nonso?”
Ta zuba mishi ido tana yi mishi
kallo irin na nazari ta ce, “Ka cika
murna a ‘yan kwanakin nan, xan
qanqanin abu kuma yana saka
dariya”.
Salim ya sake yin wata dariyar
kafin ya kalle ta ya ce mata, “Gaya
min dai abin da kike son gaya min
132
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Nonso, a taqaice a nazarinki me
ake nufi kenan?”
Ta ce, “A taqaice abin da
tunanina yake nuna min ana nufin
ka faxa tarkon soyayya”.
Salim ya qyalqyale da dariya
kafin zuwa can ya kalle ta cikin
nutsuwa ya ce mata, “Gaskiya ban
sani ba Nonso, ban san me zan ce
ba ko na faxa tarkon soyayya ne,
ko me na faxa oho. A taqaice dai
zan gaya miki na gamu da wata
yarinya a wani wurin party da na
je ta bani sha’awa, saboda ta iya
kwalliya kuma tana da kyau.
Sai kuma muka xan yi hira da
ita a dalilin ta san arewa, har ma
ta zauna a Zaria shekara biyar don
ta yi karatu ne a A.B.U Zaria, ta
kuma samu lokaci ta zo gidana
ban sani ba iyakar abin da na sani
kenan, shine kuma zan gaya miki
da soyayya a ciki ko babu, wannan
shine abin da ban sani ba.

133
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Nonso ta yi dariya tare da galla
mishi uban harara ta ce, “Za ma
ka sani, za kuma ka faxi gaskiya”.
Kafin ya sake yin wata magana
wayarshi ta xan yi motsi, ya yi
maza ya xuaka yana dubawa ya
xan yi murmushi cikin ranshi ya
ce, “Bai san abin da yasa yarinyar
nan take son ja mishi rai ba, kusan
dukkan ‘yanmatan da ya yi
mu’amala dasu tun zuwan shi
garin har kawo gamuwar shi da ita
bai tava gamuwa da yarinyar da ta
ja mishi rai irin ta ba, zamanta a
arewa ya sata ta zama daban ko
kuma ya ce ta zama da bambanci
tsakaninta da mafi yawancin
‘yan’uwanta, gashi dai ita da
kanta ne ta gaya mishi cewar babu
wata yarinyar da za ta ganshi ba
ta so shi ba, amma har a yanzu da
suke kusan wata gida da haxuwar
tasu ta qi ta ba da kai bori ya hau.
Ban da ita cikin ‘yanmatan da
suke kamuwa da son nashi ko
134
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
yaya? Me take nufi da irin
waxannan abubuwan da take yi
mishi? Tun a ranar da suka fara
haxuwa ya fara yi mata tayin
kwana gidanshi amma har a yau
xin nan ba ta yarda ta amsa tayin
ba, kullum ya yi mata tayin za ta
kawo mishi hujja na cewar zuwan
kanta ta yi gidan nashi ba shine ya
gayyace ta ba, in kuma shi xin ya
gayyace ta sai ta kawo mishi wasu
uzurori da za su hana ta zuwa a
wannan ranar.
Bai san abin da ya sa ya kasa
haqura da ita ba, duk da ja mishi
ran da take yi, bayan kafin
gamuwar shi da ita ya yiwa kanshi
alqawarin fita harkar ‘yanmata
duka saboda ya yi nazari ya ga bai
gano amfanin da ya samu a
mu’amalar da ya yi dasu ba in ban
da cutar dashi da suka yi ta yi.
To amma wannan ta fita
daban, xabi’unta daban,
halayyarta daban, nutsuwarta
135
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
daban, kamun kanta daban. Hatta
fasalin ta ma daban ne da na
sauran, gata daban a kan kowa
ma, ganinta yake yi daban ce.
Yana so ya sake jarraba
wannan don yana ganin tamkar ita
xin ba za ta cutar da shi ba, tunda
ita xin ya lura ya gane har
hankalinta ma daban ne da na
sauran, don haka ba za ta yi duk
wani rashin hankali irin nasu ba.
Ya jawo wayar tashi da niyyar
kiran ta yana danna lambobin nata
ta xauka, “Na ga saqon ki wai me
kike nufi dani ne?”
Cikin natsuwa ta ce, “Bana
nufinka da komai, ni dai kawai ban
san alaqar dake tsakaninmu bane
da haka kawai zan rinqa sintirin
zuwa gidanka”.
A hankali ya ce mata, “Ai haka
kawai ne, ina ce ni na gayyace ki
zuwa gidan? Ai ina ganin da sai ki
mututunta ni ki amsa gayyatar
tawa, atleast sai ki zo ki kwana ko
136
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
da sau xaya ne. Ina ce na yaba
dake ne yasa na yi hakan?”
“Ka yaba dani?”
Ya yi maza ya ce, “Eh mana,
Janet in ban yaba ba ai ba zan
matsu dake ba, ko kuwa dai kin fi
so ki yi ta barina ni kaxai kewarki
tana damuna? Ko don in ji daxi sau
xaya haba Janet me yasa kike so ki
yi ta barina cikin kewa da
kwaxayin ki? Kin san abin da nake
ciki game dake kuwa?”
Ta ja tsaki a hankali cikin
natsuwa ta ce mishi, “In wani ya ji
kana irin wannan kalaman sai ya
yi zaton kai xin kai kaxai ne cikin
zuciyarshi”.
Wani sanyi ya xan shige shi,
don ya soma hango ta inda ta
karkata. A hankali cikin sanyin
murya ya tambaye ta.
“To ba ni kaxai bane Janet ni
da waye?”
Ta ce, “Tarin ‘yanmatan ka fa
ina suke?”
137
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Ya yi murmushi ya ce, “To da
tuntuni kika gaya min matsalar ki
ai da sai in yi miki bayani”.
Ta ce, “Ai ni bani da matsala”.
Ya ce, “A’a, kina da ita tunda
ta riga ta bayyana na gane ta”.
Ta ce, “Mene ne matsalata?”
Ya ce, “KISHI!”
Ta ce, “A’a, ni kishin me zan
yi? Ai ina ganin babu irin wannan
maganar a tsakaninmu”.
Ya ce, “To idan har kin san
babu irin wannan maganar a
tsakaninmu sai ki yi qoqarin amsa
gayyatar da nake yi miki”.
Ta ce, “To zan yi tunani”.
Ya ce, “To yaushe zan sa ran
ganin ki?”
Ta ce, “Gaskiya ban sani ba”.
Nonso ta zuba mishi ido tana
kallon shi cikin tsananin mamaki,
ta yi murmushi bayan idanuwansu
sun haxu da na juna, shima ya
sakar mata nashi murmushin kafin
ya ce mata.
138
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
“Ya ya dai Nonso?”
Ta ce, “Mr. Salim kenan, kana
cewa baka san mene ne
tsakaninku ba, to mene ne
wannan?”
Ya xan yi murmushi ya ce, “To
gashi nan dai Nonso”.
Ta ce, “Ai duk da a yarenka ka
yi wayar yanayinka ya nuna abin
da kake ciki, to kuma na ji kana ce
mata Janet, Janet a Hausa?”
Ya ce, “Eh, ai na gaya miki
A.B.U Zaria ta yi ta iya Hausa
sosai”.
Ta yi murmushi ta ce, “Kenan
har da yaren naku da ta ji ya qara
baka sha’awa da ita”.
Ya yi murmushi ya ce, “Janet
dai kawai ta shiga raina”.
Ta ce, “Yana da kyau ai dama
kuma haka rayuwa take, wani
lokaci sai ka ga ka haxu da
mutumin da ya shiga ranka”.
Ya kalle ta kawai ya yi shiru ya
kuma kawar da hirar tasu ta
139
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
hanyar faxin, “Yau da wuri zani
gida in mun tashi don miyata ta
qare sai na yi sabuwa”.

** **
Yana tsaye a kicin xinshi sanye
da singilet da gajeren wando, tare
da tunanin abin da zai ci saboda
yunwar da yake ji, kasala ce ma ta
fi damun shi, bai kuma san dalilin
ta ba.
“Me ma zan girka ne?” Ya yiwa
kanshi tambayar.
Jinjiri mai tsire ya faxo mishi
cikin ranshi, ya daxe yana son
ganin shi don ya yi mishi nasiha
kan abin da ya ga yana yi wanda
bai dace ba, amma bai samu halin
zuwa ba saboda yawan
harkokinshi.
Bari ya yi amfani da wannan
damar, ma’ana ya jefi tsuntsu biyu
da dutse xaya, ya je ya ci abinci
daga nan ya yi mishi nasihar da

140
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
zai yi mishi. Haxa tea ya yi ya xan
sha don rage yunwa.
Kwalliya sosai ya yi ga
qamshinshi mai daxi na kullum a
tare da shi, a haka ya shiga motar
shi, wurin Jinjiri mai tsire ya nufa.
Bai daxe da zama wurin Jinjiri
ba sai ga wani dattijo ya zo wurin
zai iya kaiwa shekaru saba’in ko
zuwa da biyar koma tamanin, cikin
girmamawa Salim ya gaishe shi.
Nan take kuma ya baiwa Jinjiri
yiwa dattijon irin haxin da shima
ya yi mishi.
Nan da nan Jinjiri ya yiwa
dattijon haxi ya kawo mishi tare
da faxin, “Baba Tsoho ka fa yi xa
rana a tsaka”.
Salim ya xaga ido ya yiwa
Jinjiri mai tsire wani irin kallo
saboda rashin jin daxin sunan da
ya kira dattijon da shi. Me Jinjiri ke
nufi da kiran wannan dattijo Baba
Tsoho? Baba Tsoho cikin kalmar
Hausa ai ba wani suna bane na
141
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
girmamawa, shi kuma Jinjiri ya fi
kowa ikirari da cewar ya fi kowa
jin Hausa, saboda iqirarin da yake
yi na cewar shi xan Bashalelewa
ce, sannan wai hausarsu ta
Sakkwato ta fi kowace Hausa
zama Hausar asali.
Baba ya karvi haxin da aka yi
mishi tare da sawa Salim albarka
mai yawa, kai xan nan Ubangiji ya
sa ka rabu da iyaye lafiya.
Salim ya ji daxin addu’ar da ya
yi mishi, cikin ranshi kuma ya
tsunduma ckin tunanin iyayen
nashi da ya rabu dasu lokaci mai
tsawo babu amo babu labari.
Ganin Salim ya zubawa wuri
xaya ido ya sa dattijo matsowa
kusa da shi ya xan xora hannu kan
kafaxarshi tare da faxin, “Ya ya
dai na ganka haka yaro? Kana osn
su ne?’
Da sauri Salim ya kalle shi, “Su
wa Baba?”

142
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Baba ya yi maza ya qiftawa
Salim ido, wato signal ya ce, “Su
waxancan xin mana, ai na ga ka
zuba musu ido kana kallon qurrrrr!
Baka ko qiftawa shine na ce bari
in gaya maka akwai wani a nan
wurinna a tare dani haxin mai
kyau ne mai kuma qarfi samari
matasa majiya qarfi irinku nake
baiwa, ka jarraba shi ka gani za ka
yi mamaki, don in kana tirip uku
ne ma, to za ka iya ninkawa,
kyauta kuma zan baka shi saboda
alherin da ka yi min.
Salim ya kalli dattijo wanda a
yanzu ya soma gano dalilin da
Jinjiri mai tsire tare da sauran
waxanda ke wurin ke yi mishi
laqabi da Baba Tsoho, kan ya san
abin da zai gaya mishi kan irin
maganganun nashi.
Sai ya ci gaba da gaya mishi ai
maganin farin jini ne dani na
sadidan, don na ga su waxancan
xin da alamar sun burgeka ka
143
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
qyasu, koma ka yi ta yi sun qi
sallamawa.
Salim ya kalle shi cikin sanyin
jiki da kaxuwa, “Wa kenan Baba?”
Baba ya yi maza ya nuna ta da
fatar baki ya ce, “Waccan mana
mai tuwon, ai na lura tuntuni kake
kallon ta, ai ja’ira ce yangar tsiya
ce da ita, don ko kwanaki ma sai
da na shiga tsakaninta da wani
saurayi na sasanta su sannan ne
ta haqura ta ba da kai bori ya hau.
In kana so in yi maka magana da
ita”.
Ya yi maza ya ce, “A’a, Baba
qyale ta kawai”.
Salim da mamakin Baba ya
maimaye shi ya cika mishi zuciya,
kallonshi ya yi ya yi murmushi ya
ce, “Baba kenan, kaima dai kana
xan tavawa kenan da alama?”
Baba ya yi dariya har haqoran
nan da suka saura mishi a bakin
suka bayyana, ya ce, “Qwarai
kuwa mana. Yo to yaro wasa zan
144
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
tsaya yi a ci duniya ba dani ba? Ai
garau nake nan xin nan, inda kake
kallona in baka yi hankali ba aikin
da zan yi sai ka yi qoqari ka yi shi.
Sanda nake yaro matashi
kamarka kuwa!” Ya jinjina kai don
nuna al’amarin ba qarami bane,
kafin ya buxe baki ya ce, “Ba
qaramin bugawa aka yi dani ba a
garin nan”.
Cikin sauri Salim ya kalle shi
saboda mamakin da maganar
tashi ta bashi ya ce, “Yanzu nan
Baba kana nufin tun kana xan yaro
qarami kake zuwa garin nan amma
har yanzu da ka tsufa baka daina
ba?”
Fuskar Baba ta xan sauya,
wataqila don jin Salim ya kira
mishi tsufa, nan da nan kuma ya
wattsake da fuskar tashi, wataqila
don ganin har a lokacin bai qarasa
lamushe alherin da Salim xin ya yi
mishi ba.

145
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Sai ya xora zancen nashi da
cewar, “Ko kaxan, ai ni tunda na
zo garin nan ban tava komawa
arewa ba, bana shekaru kusan
hamsin kenan ina garin nan, tun
zamanin Biyafara, tun zamanin
ban fi kamar ka ba yanda ka
gankan nan kuma nima lokacin
nan haka nan xin nake, ga tsayi ga
kyau, ga farar fata. Kai ni in ka
barni ma sai in ce maka na xara ka
farar fata”.
Salim ya xaga ido ya sake
kallon shi cikin zuciyarshi ya
tabbatar da gaskiyarshi, don ko a
yau xin nan da ya tuqurqushe
barasa ta huda shi ta ko’ina, kana
kallon shi ka san sanda yake yaron
ba qaramin kyau ya yi ba.
“Ai ni nan ba qaramin abu na
yi ba na ci duniya ta, na kuma
gwangwaje ta son raina”.
Salim wanda mamakin tsoho
ya sanya shi tsunduma cikin wani
irin matsanancin tunani game da
146
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
rayuwa, kau da kanshi ya yi zuwa
gefe ya bar Baba Tsoho yana
zancenshi kaxai.
Zuwa can wata tambayar ta
sake ciwo shi, ya waiwaya ya kalli
Baba ya tambaye shi, “To Baba
baka ma tava aure ba kenan ko?”
Baba ya yi dariya ya ce, “To
yaro me ake nema a aure ne? Ina
ce dai in ya yi albarkar ‘ya’ya ne,
to ai na haife su sun fi hamsin,
don kuwa ko nan xin nan inda
muke zaune na ga wasu suna
zirga-zirga, to ba shi kenan ba?
Na yi quruciyata mai kyau mai
kuma daxi, don a lokacin nan sai
matar da na ga damar mu’amala
da ita nake yi, saboda baiwar kyan
da aka yi min.
Kamar mu xaya ni da kai,
yanda ka gankan nan nima lokacin
haka nake, ga kuma qarin laqani.
Eh!” Ya xan kashe mishi gira.
Salim ya yi murmushin qarfin
hali ya ce, “Baba kenan”.
147
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Suna cikin hakan ne wani yaro
saurayi ya zo wucewa Baba ya yi
maza ya xan tava Salim tare da
faxin “Yauwa-yauwa, yaro dubi
nan, dubi nan da sauri kar ya
vace, wannan mai jar rigar ka
ganshi?”
Salim ya ce, “Eh, na ganshi”.
Ya ce, “To ai shima xana ne,
nine ubanshi mahaifi”.
Salim ya ce, “A’a, Baba xanka
ne amma ya zo ya wuce ka haka
bai ko xaga ido ya kalle ka ba?”
Baba ya ce, “Wayyo, ai ‘yan
cikin nuna yana yin tausayawa, ya
ce ai bai sanni ba bai san nine
mahaifinshi ba, nine dai kawai na
san shi xin xana ne, saboda a
lokacin da aka samu cikinshi ni
kaxai ne nake tare da uwarshi,
uwarshi ta haqura ne ta fita
harkata ba ta dunfare ni da shi ba
sanda ta haife shi, saboda wata
irin balahirar gumurzun tsiya da
muka yi da ita a kan cikin”.
148
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Salim wanda hirar ta Baba ta yi
matuqar gundurar shi, har yake
yiwa Baba wani irin kallo tamkar
na wani dabba, dabba ba mutum
ba.
Sai ya miqe ya nufi wurin Jinjiri
yana faxin “Jinjiri in ganka mana a
gefe ni zan tafi”.
Jinjiri ya ce, “To oga Salim gani
nan zuwa, kai Tasi zo ka dafa min
nan wurin bari in ga maigida
Salim”.
Salim dake tsaye can gefe
saboda ta hanyar sirri yake son
yiwa Jinjiri nasihar, sai ya kalli
Jinjiri da ya riga ya iso wurin shi
yake tsaye.
“Gani oga Salim, in ce ko dai
lafiya babu wata matsala?”
Salim ya gyara tsayuwa ya ce,
“A’a, babu komai Jinjiri wurinka
dai kawai na zo”.
Jinjiri ya ce, “To madalla”.
Su dukkansu biyun suka xan yi
shiru saboda tunanin ta inda zai
149
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
fara yiwa Jinjiri maganar, don ta
zamo mai sauqi kuma ta fahimta,
musamman ma da yake ya riqo
alheri mai xan nauyi da yake nufin
baiwa Jinjirin don ya qara jari.
“Kai nake sauraro Oga Salim,
ka ce wurina ka zo”.
Salim ya ce, “Eh, ai ta inda zan
faro maganar nake tunani”.
Jinjiri ya ce, “Faro ta kawai ta
ko’ina ni da kai ai babu haka a
tsakaninmu, mun riga mun zama
xaya, mu xin tamkar ‘yan’uwa
muke, don haka faxi duk abin da
za ka faxa kar ka ji shayin komai”.
Tabbacin da Jinjiri ya baiwa
Salim na kusancin da ke
tsakaninsu shine ya fi komai
qarfafawa Salim gwiwa ya gayawa
Jinjiri abin da ya kawo shi.
“Kana ji ko Jinjiri?”
Jinjiri ya ce, “Ina jinka maigida
Salim”.
Salim ya ce, “Wani abu na ga
kana yi wanda bai yi min daxi ba,
150
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
saboda a matsayin mu na masu
addini, addinin nan kuma mai
tsabta ai bai kamata mu rinqa yin
wasu irin halaye qazamai da ko
mara addini in yana da hankali ba
zai yi ba”.
Cikin natsuwa Jinjiri mai tsire
ya tambaye shi “Me ya faru Oga
Salim?”
Salim ya qara rage murya don
maganar ta qara zama sirri, kafin
ya ce, “Wurin nan naka ne ina
nufin xakinka da ka ce min kana
baiwa yaran nan xani suna biya,
na ji abin bai yi min ba.
Haba Jinjiri, yaushe a ce
mutum ya yi haka? Matarka? Aure
na sunna ka kora ta qauye ka
maida ita can da zama ba a kan
son ranta ba sannan xakin da kuke
kwana a ciki kai da ita, katifar da
kuke kwanciya a kai ka rinqa
baiwa ‘yan iska suna shiga ciki
suna zina saboda a baka kuxi.

151
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Lalacewa fa suke yi in sun
shiga, tunda karuwan sune. Sai
kuma dare ya yi kai ka shiga baka
qyama, to in kai baka da matsala
ita fa?
Haqqinta da yake kanka ya ya
za ka yi dashi? Mu rinqa yi muna
tunawa da rayuwa za ta qare
mana-mana”.
Jinjiri ya kalle shi cikin natsuwa
fuskarshi ta bayyanar da tsananin
mamakin maganganun nashi, a
hankali ya buxe baki ya ce mishi.
“Oga Salim kenan, gwano baka
jin warin jikinka. Ashe har kana
iya yiwa wani nasiha? Yanzu kai
xin nan a inda kake da irin abin da
kake aikatawa ashe har kana iya
ganin kuskuren wani ka gyara
mishi?”
Ya gyaxa kai don nuna
tsanantar al’amarin da yake ciki.
Ya ce, “Uhh! Dama fa wani Malami
gwanin hikima ya yi wasu baitoci
na waqoqin Infiraji a ciki yana
152
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
cewa, “Shifa laifi tudu ne naka
wanda ka tattara ne ka hau kai
hangen wanin ka wanda bai kai
kamar ka a kuskure ba”.
Ya ce, “To na ji nawa laifin,
amma dai kuma ka sanni sarai ni
bana shan barasa, kai kuwa kana
sha, bana yin zina, kai kuwa
kullum gidanka da mace a ciki,
tunda har dambe ake yi a kanka.
Babu abin da ban sani ba, don
ina da labarin komai. Xakin nawa
ne dai kawai laifina da nake ba da
haya ana yi a ciki.
To da mai ba da haya da mai yi
wanne ne gaba a laifi? Sannan ko
ba komai ka yi maganar iyalina,
wannan ina dasu, to kai kuwa fa?
Iye? Ka sha barasa, ka nemi mata,
ka kwana Hotel.
An kuma gaya min rabonka da
zuwa garinku don ka dubo
iyayenkam da suka haifeka suka yi
wahalar ka ka je don ka samu
ladansu an manta suma ka yi
153
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
watsi dasu, tunda sunyi mai wuyar
sun gama sunyi sanadin zuwan ka
duniya, sun yi maka wahala da
xawainiya, ka kawo qarfi
qadangarun bariki sun karve,
tunda dama su suka haifarwa.
Ai kai ya kamata a tsayar Oga
Salim a yiwa nasiha, ka ji tsoron
Ubangiji ka gyara halinka,
musamman iyaye ka kula dasu,
don in ba haka ba ka ga Baba
Tsohon nan, ai ka ji shi yana gaya
maka sanda yake yaro kamannin
ku xaya ko?”
Salim ya juya ya kama hanya
ya nufi inda ya yi parking xin
motar shi zuciyarshi cike da
tsananin vacin rai na maganganun
da Jinjiri ya sossoka mishi.
Yana tafiyar kuma yana jiwo
wasu maganganun na Jinjiri, wai
har lokacin bai gaji ba.
“Mu kam ko ba komai ai mun yi
aure mun haifa, iyalinmu da
‘ya’yanmu duk suna can tare da
154
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
iyayenmu, kullum muna musu aike
suna yi mana addu’a.
Wannan abin da kake gani duk
a cikin buga-bugan nema ne na
yanda za a yi asiri ya rufu, kai
kuwa fa?”

** **

155
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
BABI NA TARA

S
alim yana kwance a gida in
ban da ciwo da taqaicei na
baqin ciki da matsanancin
vacin rai babu abin da zuciyarshi
ke yi.
Ya yi nadama ya fi kwando
dubu kan nasihar da ya je ya yiwa
Jinjiri, kai mutanen duniyar
wannan lokacin mafi yawancinsu
basu so a gaya musu gaskiya, wai
daga gyara kayanka abin ya zama
sauke mu raba.
Ya xan qara juyawa a kan
gadon nashi zuciyarshi ta yi
matuqar quntata, bai tava ganin
mutumin da ya ci mutuncin shi irin
cin mutuncin da Jinjiri ya yi mishi
ba.
Kai lallai Jinjiri ba mutumin
kirki bane, gori? Ai xan halal baya
gori. In har akwai abin da ba a
tava yi mishi ba shine cin fuska
irin wanda Jinjiri ya yi mishi mai
zafi, irin wanda bai tava zaton
156
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
wani zai iya tunkarar shi ya yi
mishi ba.
To amma babu komai shi ya kai
kanshi wurin Jinjiri, shi yake
mu’amala da Jinjiri irin mu’amalar
da ta baiwa Jinjirin damar yi mishi
irin wulaqanci da cin mutuncin da
ya yi mishi a yau, an kuma yi an
gama.
Hausawa suka ce wai ‘ta yanke
ta guntsule, daga yau sai yau ba
zai sake ba, ba Jinjiri ba ko ma
waye ba zai sake ganin shi yana
yin abin shi ya ce zai gyara mishi
ba.
Teburin Jinjiri mai tsire kuwa
ba zai sake zuwa ba, tsiren ma ya
daina ci wanda ya ci ma a baya da
yana da halin fidda shi a jikinshi
da ya fitar, tunda dai shi xin ya
gane Jinjiri ba kowa bane face
wani mutumin banza da bai yarda
a gyara mishi kuskuren shi.

157
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Wayewar garin yau tunda aka
tashi ake tsaga ruwan sama kamar
da bakin qwarya.
Kasancewar ranar ta asabar ce
ta sanya Salim yana daga cikin
mutanen da matsanancin ruwan
saman ya zaunar dasu a gida.
Kwance yake a kan gadon shi
lulluve cikin lallausan bargonshi,
tun bayan da ya idar da sallar
asuba ya hau gadon ya kwanta,
bai sauko ba saboda sanin in ma
ya saukon to me zai yi?
Yana kwance cikin jin daxi,
‘yan tunane-tunanen shi yake yi
masu xan sauqi da daxin, yana jin
tunanin gida zai faxo mishi yake
yin maza ya kawar dashi tare da
gayawa kanshi cewar ai ya gama
da wannan tunda dai ya riga ya
tsai da shawarar bana a Yola zai yi
hutun shi na shekara.
In kuma ya ji zuciyarshi tana
qoqarin lissafo mishi adadin
yawan watannin da suka saura
158
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
mishi kafin hutun shekarar ya zo,
tunda ba wani daxewa ya yi da
kammala shi ba, sai ya yi maza ya
gayawa kanshi cewar ai babu
komai tunda ma dai masu karin
magana sun ce, wai shekarar
kwana ce.
Idanuwanshi suka kai kan
agogon dake xakin daidai lokacin
da ya ji motsin qwanqwasa mishi
qofar gidan nashi, goma ne da
minti talatin da biyar, kenan sha
xaya saura ashirin da biyar.
Safiya ce ga kuma ruwan
saman da ake kwarawa wane
fitinannen mutumin ne yake nufin
fitar da shi a yanzu?
Ya yi kamar ba zai motsa ba,
sai kuma ya yi tunanin to ko jikin
maqwabcinshi Baban Amedi ne ya
xan motsa? Tunda a sanin shi bai
ji daxi ba.
Da sauri ya diro daga kan
gadon daga shi sai wandon dake
jikinshi three quater, ko singilet babu
159
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
ya nufi qofar falon cikin sauri ya
buxe tare da tunanin ko za su
buqaci ya kai su asibiti ne, tunda
shi da kanshi ya gaya musu in
buqatar hakan ta tashi a sanar da
shi.
Janet ya gani tsaye a bakin
qofar a cikin ruwa ta sha kwalliyar
atamfa riga da siket da suka yi
matuqar fiddo da surarta, ta kuma
kashe xauri da zanin atamfar,
lemar da ke riqe a hannunta ta yi
matuqar dacewa da takalmi da
jakar da take sanye dasu.
Shagalan da ya yi yana kallon
ta ne ya hana shi yi mata tayin
shiga xakin har sai da ta gaji ta
buxe baki ta ce mishi.
“Oh! Am I not wellcomed!”
Ya yi murmushi, “Of course
you re”.
Ta wuce ta tura kai zuwa cikin
xakin ta barshi a bakin qofar a
tsaye na wasu ‘yan mintoci yana
kallon ruwa da yanayin da garin
160
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
yake ciki, kafin ya rufe qofar ya
juyo gare ta.
Sai a lokacin ya lura da
bishiyar fulawar da ta je ta ajiye a
kusurwar xakin wanda da bai lura
ya ganta ba, xan tebur ya jawo ya
zauna gabanta suna fuskantar
juna.
Ya miqa hannu ya kamo ‘yan
yatsunta yana murzawa, cikin
zuciyarshi kuwa tunani yake yi, ai
kuma na gano ki.
Ya kalle ta cikin murmushi ya
ce, “Kina da kyau Janet, baki yi
laifi ba in kin yi min yanga kin ja
min rai”.
Ta xan harare shi da gefen
idon ta tare da tave baki, “Baka yi
laifi ba kaima in ka faxi hakan,
wataqila abin da ka saba gayawa
‘yamtanka kenan kana samun su a
hannu”.
Ya yi murmushi, “Wai ke
yaushe ne za ki fara barinmu
muna yin maganarmu mu biyu ba
161
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
tare da kina tsoma wasu a ciki ba,
daxin abin dai shine tunda kike
zuwa baki tava zuwa kin samu
wata a gidan ba, ina ganin da sai
mu yi sha’aninmu kawai”.
Kallon shi kawai ta yi ta kawar
da kanta gefe, can cikin zuciyarta
kuwa qara tabbatarwa kanta kyan
halittar Salim take yi.
“Inda za ki iya taimakona da
wani abu guda xaya da kin daina
yin maganar kowa sai tamu mu
biyu”.
Ta ce, “To, na ji amma kaima
ya kamata ka daina kallona kana
cewa ina da kyau, tunda dai ai duk
kyan nawa ban kai ka ba”.
Ya yi murmushi ya ce, “Haba
Janet, barni kawai in yi ta cewa ke
xin mai kyau ce, tunda dai abin da
ya dace da ke ne kika yi, amma
namiji don ya yi kyau sai me?
Baki ji wani mawaqinmu na
Hausa ba yana cewa wai, ‘mata
kuxi suke so ba farin ido ba”.
162
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Ta yi dariya ta ce, “Har da
kyan ma muna so”.
Ya sake kallon ta, “Ban tava jin
abin da nake ji game dake ba
Janet, a duk sanda na matso kusa
dake sai in rinqa jin wani abu
kamar mayen qarfe yana fisgata
zuwa gare ki”.
Ta xan kawar da kai gefe ta ce
mishi, “Sha’awa kenan?”
Ya xan lumshe ido kaxan tare
da faxin, “Uh-uh! Ba shi bane, in
ma kuma shine to da wani abu
kuma can daban da ban san ko
meye ba, tunda ai ba yau na soma
girma ba”.
Ta miqe tsaye tare da zare
hannuna cikin nashi a hankali,
kicin ta nufa ya yin da shima ya
miqe ya bi bayanta.
“Yunwa nake ji”.
Ya faxi hakan daidai lokacin da
ta ji saukan hannunshi a gare ta,
hannu biyu ya saka ya danqi
qugunta ya riqe.
163
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Cikin sauri ya juyo da ita gare
shi suna fuskantar juna.
“Yunwar me kike ji?”
Ya yi tambayar daidai ya kai
bakinshi ga nata. Da sauri ta xan
ture shi ta kaucewa abin da ya yi
nufin.
Suna tsaye suna fuskantar
juna ya yin da ta sunkuyar da
idanuwanta kan lallausan gashin
dake kwance a kan qijinshi tana
wasa da shi da ‘yan yatsunta.
“Ba wani vata lokaci mai yawa
zan yi a gidan ka ba”.
Ta faxi hakan ba tare da ta
kalle shi ba, ba kuma tare da ta
bar abin da take yi ba.
“To me kike nufi da waxannan
abubuwan da kike yi? Kina nufin
haka za ki tafi ki barni?”
Bai jira ta ba shi amsa ba,
hannu biyu ya saka ya sure ta.
Yana fitowa daga wankan da
ya yi mai haxe da alwala
jallabiyyar shi ya sanya, ya
164
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
shimfixa dardumar sallar shi. Sai
da ya idar ya fito ya same ta a
kicin xin.
“Me kike shiryawa?”
Ba ta kalle shi ba, shima bai
sake magana ba hannu kawai ya
saka ya taya ta kwashe farantan,
suka fito falon nashi suna zaune
suna karyawa tare da yin hira ‘yar
kaxan-kaxan, mafi yawancin
zancen nasu kuwa kan bambancin
dake tsakanin kudu da arewa ne.
Ya xan kalle ta cikin natsuwa
ya ce mata, “Yau kam ai kwana za
ki yi ko?”
Ba ta kalle shi ba ta ce,
“Saboda me?”
Shima shiru ya yi ba tare da ya
ba ta amsa ba.
Jimawa kaxan ya sake kallon
ta, “Kina nufin ba za ki iya yin
komai saboda ni ba?”
Da sauri ta xago ido ta kalle
shi, “Ban gane ba”.

165
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Ya ce, “Eh, ba za ki gane ba
tunda baki shirya ganewar ba”.
Tana son shi ta ko’ina ya yi
mata daidai, a kan komai kuma ya
yi mata yanda take so. To amma
kuma ba zai yiwu ta yi saurin ba
da kai gare shi kan komai ba,
tunda ba yau ne ranar farko da ta
soma hulxa da samari ba, na
kudun da na arewan, daidai
gwargwado ta san wani abu game
da halayyarsu.
“Ban fa zo da niyar kawowa
irin wannan lokacin ba”.
Ya kalle ta, “Eh, ai na ji, kuma
tunda kika kawo yanzun ai ko za ki
tafi sai kin girka mana abincin
dare in ya so sai in sauke ki”.
Cikin nutsuwa ta kalle shi
bayan ta kalli agogon dake wurin
ta ga lokaci.
“To me kake so in girka
maka?”
Ya xan yi tunani kaxan kafin ya
ce, “Sakwara da miyar wake”.
166
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Ta kalli Salim kamar za ta yi
magana, sai kuma ta fasa ta miqe
ta shiga kicin xin don yin girki,
shima ya miqe ya bi bayanta yana
shirin taya ta.
Ga abubuwan da ta shirya yin
amfani dasu don ta birge sabon
saurayin nata a matsayinta na
wacce ta je har jami’a don ta koyi
girke-girke da makamantan haka.

1 = Wake 1
Gwangwani
2 = Nama Yanka 10
3 = Macaroni ½ Cup
4 = Cabbage Kwata
¼
5 = Ganyen Persle
6 = Tumatur Guda 4
7 = Kayan Qamshi
8 = Albasa Mai
Ganye
9 = Manja ½
Gwangwani
10 = Tattasai 4
167
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
11 = Karas 1
12 = Maggi 2
13 = Gishiri
14 = Ruwa

Ga yadda ta yi ta sarrafa
abubuwan: ta jiqa wake ya jiqu ya
daxe a cikin ruwa mai Maggi, ko
ruwan stocze mai yawa. Ta xora
mai ta saka albasan da ta
yayyanka ‘yan qanana, ta zuba
magi, ta xauko naman da ta yiwa
qananan yanka a ciki ta juye
jiqaqqen waken nan da ta riga ta
wanke ya wanko a kan naman, ta
kawo murfi ta rufe.
Sai da ya yi tsawon awa xaya
kafin ta buxe, ta kawo ganyen
albasa yankakke da karas da
tumatur da kayan qamshi ta zuba,
ya yi minti goma sha biyar sannan
ta zuba yankakken kabeji tare da
garin makaronin nan da aka daka
a tukunyar sai da ya yi laushi.

168
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Sannan ta kayo ganyen Parsley
ta haxa da maggi da gishiri ta
zuba ta rufe na minti biyar, kafin
ta sauke ta xora doyar.
Tun a kan wuta Salim ke sa
cokali yana xiban miyar yana sha
tare da faxin wannan miyar ai ma
ba sai an tsaya yi mata wata
sakwara ba, ko a haka aka bar min
ita can shanye ta in qoshi.
Tana goge hannunta da ta
wanke towel xin dake kicin xin ya
shigo yana tambayar ta “Za ki yi
wanka ne?”
Ta kalle shi ta yi murmushi ta
ce, “Har yanzu dai baka gane abin
da nake nufi ba kenan”.
Ya juya ya fita ya shiga toilet
ya yi wanka, sannan ya tsaya ya
shirya ya fito cikin wata fitted T.
Shirt fara sol da brown xin wando,
sai takalminshi shima brwon
snikkers.
Yana riqe da mukullin motarshi
ya miqa hannunshi na hagu ya
169
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
riqo nata na daman tare da faxin
“Muje ko?”
Ta xaga ido ta kalli agogon
dake sagale, qarfe goma da rabi
ne na dare. Ta sake juyo da kallon
gare shi.
“Dubi agogo, ni da nake ta
cewa ba zan daxe ba wai sai yanzu
za ka mai dani?”
Bai tanka mata ba. A hanya
suna tafiya cikin natsuwa da
nishaxi tare da hira mai daxi irin
ta ma’abota soyayya, bai tsaya a
ko’ina ba sai a qofar wani
katafaren gini mai matuqar girma
da ban sha’awa, ta ko’ina kuma
wutar shi sai kamawa yake yi.
Janet ta xaga ido ta kalli abin
da ke rubuce a saman ginin
“CHANGE” abin da ta gani kenan.
Wani hamshaqin Hotel ne da
ya riga ya yi suna wajen tara
gogaggun ‘yan boko, ya nemi wuri
ya yi parking xin motarshi ya fito
ya zagayo ta inda take ya buxe
170
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
mata tata qofar ya miqa hannu ya
kamo ta ya fito da ita suka nufi
hanyar shiga ciki yana riqe da ita.
“Amma ai da ka gaya min ko a
ce ka kaini gida tukunna na yi shiri
ba a haka ya kamata in zo nan
ba”.
Ba tare da ya kalle ta ba ya ce,
“Babu damuwa a wurina, ke xin
kawai nake so babu ruwana da irin
rigar dake jikinki ko kalar ta, ni in
kin barni ma wannan shigar taki ta
fi yi min kyau a kan ta waxannan
fingilallun rigunan”.
Ya xan kalli fuskarta bayan ya
sallami service xin da ya kawo musu
list xin abubuwan da suke da su
don ganin ko yanayin fuskarta ya
canza bai gano komai ba tana nan
a yanda take.
“Ba zai yiwu na yi ta roqon ki
ki kwana gidana ba ban tava yin
hakan ba shi yasa na xauko ki na
kawo ki nan, will you kindly soend
the night with me?”
171
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Ba ta kalle shi ba balle ta ba
shi amsa, shima kuma bai sake ce
mata komai ba.
Jimawa can ta yi magana cikin
sanyin murya tare da tambayar
shi, “To amma me kake so kuma?”
Ya xan yi murmushi kaxan
kafin ya miqa hannu ya kamo nata
ya riqe suna fuskantar juna, yana
magana a hankali tare da yin wasa
da ‘yan yatsunta.
“Don na xan tava ki ba shi
kenan ba Janet, in kin fassara ni a
haka zan xauka kina kallona a
matsayin mai sha’awa ne kawai, I
need to knwo you more, kin gane?
Muna buqatar lokaci na zama
tare da kusantar juna sosai don
mu qara fahimtar juna da kyau,
wannan jeka ka dawon da kike
mana ba komai zai kawo ba illa
qarin vata lokaci”.
“To ai ni ban gayawa Mama
zan kwana ba”.

172
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Ya galla mata harara, “Ki ce
min kawai har yanzu ke xin ‘yar
qanqanuwar baby ce a gaban
Maman, da safe in na sauke ki zan
shiga in gaya mata a wurina kika
kwana”.
Janet ta xaga ido ta kalle shi
shima ya rama mata kallon tare da
xaga mata gira. Ya ce, “To mene
ne in anyi hakan? Ai ba komai
bane in anyi mun kai mu yi ne
yasa muka yi, tunda we are
matured enought”.
Da qyar ya iya tashi da asuba
ya ba da faralin dake kanshi
saboda tsananin ciwon da kanshi
ke yi a dalilin rashin baccin da
yake buqata, gashi kuma ya
kwankwaxi barasa fiye da adadin
abin da ya saba sha a ‘yan
tsakanin nan.
A farkon shigar shi cikin harkar
sharholiyar ya kan sha ta babu
adadi, amma daga baya da ya
gane matuqar bai shiga taitayin
173
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
shi ba, to za ta iya haifar mishi
xan da ba ido a kan aikin shi, sai
ya shiga ‘yan kaffa-kaffa da ita,
baya yarda ya sha fiye da kwalba
biyu zuwa uku.
To amma ban da jiya, don
kuwa a jiya kam shanta ya yi ba
tare da lissafin adadin abin da ake
shan ba, saboda ya gamu da
gwanar sha.
Ya waiwaya kan gadon yana
sake qare mata kallo, har a
lokacin baccinta take yi cikin
natsuwa da kwanciyar hankali.
Ya zuba mata ido cikin
matsanancin kallo mai xauke da
tunanin abin da ya faru a
tsakaninsu a daren jiyan, wani irin
al’amari ne na soyayya da
mutuntawa, don kuwa sun
tabbatarwa kansu cewar su
dukkansu biyun ja’irai ne na qin
qarawa.
Kallon da yake yi matan ya
qara mishi sonta, tun farkon ganin
174
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
da ya yi mata ya tabbatarwa
kanshi da cewar akwai wani
al’amari a game da ita.
A daren jiya kuwa ta tabbatar
mishi da abin da ya yi zaton,
yanda ta bambanta da sauran
‘yanmatan nashi a natsuwa da
hankali da kamun kai, haka ta
bambanta dasu a mu’amala.
Shi mutum ne da ya kan rabu
da mace a dalilin gamsuwa da
mu’amalarsu ta dare guda, amma
wannan ba haka bane, yana
buqatar sake yin wani daren tare
da ita.
Yarinya ce mai natsuwa wacce
ta san yanda za ta yi ta biyar da
wanda take tare da shi ta gamsar
da shi irin gamsuwar da zai yi
wuya ya samu irin wannan
gamsuwar a wani wuri matuqar ba
ita xin ba ce.
Wani tunani ya sake faxowa
cikin zuciyarshi na game da
alqawarin da ya yiwa ranshi na fita
175
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
harkar ‘yanmatan kudu gaba xaya,
saboda vata mishi rai da suka yi
bisa mummunan kishinsu na
rashin hankali da rashin mafaxi,
gasu da wata banzar xabi’a ta
rashin sanin girma da daraja irin
ta xa namiji, bai zamo musu komai
ba su warware hannu su yanke shi
da mari komai girman shi, ko
kuma su sa hannu su cakume
kwalar rigarshi.
Yana kawowa nan sai ya ji
zuciyar tashi tana gaya mishi
cewar, “Kai wannan daban take da
sauran, ai ba ma zai yiwu ka haxa
su gaba xaya ka yi musu hukunci irin
na fyaxar ‘ya’yan kaxanya ba, ai
yanda suka bambanta a suna da
kamanni na jiki da mu’amala,
zamantakewa tsakanin mace da
namiji, haka nan dole za su
bambanta a hali, ko ba komai
wannan mai nutsuwa ce da kamun
kai, tunda ai ba yau kuka fara
gamuwa ba, lokaci mai tsawo aka
xauka kafin ayi hakan.
176
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
Su kuwa fa? Duka xauka sunan
su. Don haka ba ta lokaci kawai kai
da ita ku qara samun lokacin sanin
juna ta yanda za ku fahimci juna da
kyau da kyau.
Ba ta farka ba sai wajen sha biyu
da rabi na rana, a lokacin nan kuwa
har ya fita ya dawo. Tana buxe ido ta
kira sunan shi, “Kai ni gida Salim dan
ina so zan yi wanka’.
Bai tanka mata ba miqa hannu
kawai ya yi ya sure ta ya je ya tsoma
ta a cikin kwamin wankan.
“Oh! Dear bani da rigar sakawa”.
Ya kalle ta cikin yanayin
murmushi ya ce, “To ki saka tawa
mana”.
Lokacin ne ta xaga ido ta kalle
shi sosai ta gane rigar jikin nashi ba
ita ce wacce yake sanye da ita ba a
daren jiya.
“Kar dai ka ce min ka fita ban
sani ba?”
Bai tanka mata ba illa sanya
hannu da ya yi yana cuxata ta ko’ina,
sai da ya tabbatar ya gama yi mata

177
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
wankan ta fita fes sannan ya surota
ya fito da ita ya ajiye ta kan gadon.
Mai da ita ya yi tamkar ‘yar
jaririya, Janet ta shiga noqe-noqe da
goce-goce don ganin tamkar abin
nashi yana nema ya wuce gona da iri.
Ya xaga ido yana kallon ta cikin
natsuwa, sai da idanuwansu suka
haxu wuri xaya sannan a hankali ya
buxe baki ya tambaye ta.
“Ban gane wannan noqe-noqen
da kike yi ba,a she daren jiya ban jiki
kina cewa komai nawa ne ba?”
Ta qyalqyale da dariya tare da
rufe idonta, cikin zuciyarta tana
tunanin Salim shine mijin da ya dace
da ita, irin mijin da take buqata take
fata da kuma burin samu, gashi ta
same shi.
Sai dai matsalar ita ce, za a yi
harka ne kawai a rabu tunda ta
ko’ina an sha bamban, tunda yanki
da addini da qabila duk sun
bambanta a tsakanin su.
Sabuwar rigar da ya fita ya sayo
mata ta sanya, ta yi matuqar yin
kyau da ita, kalarta ta dace da fatar
178
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
jikinta, ta yi mata cib-cib gwanin
sha’awa, tamkar dai ita da kanta ne
ta zavowa kanta ita.
Service ya kawo musu abincin da
Salim ya yi musu oda, suna zaune
suna ci tare suna kuma hirarsu.
“Daga mun gama sai ka sauke ni
a gida, kar ka manta kuma ka ce za
ka ga Mama”.
Ya kai cinyar dake hannunshi
bakinshi ya yaga kafin ya kalle ta ya
ce mata, “Ba zan manta ba, zan
kuma yi kamar yanda na ce xin. Sai
dai ina ganin ba yau ne zan yi hakan
ba sai gobe”.
Janet ta yi maza ta kalle shi, “Me
kake nufi? Kana nufin tun bamu yi
nisa ba za ka fara canza magana?”
Ya ce, “Ba canza magana na yi ba
Janet, ina dai nufin ne ke xin ba yau
za ki koma gidan naku ba, za ki jirani
a nan sai gobe saboda ban gaji dake
ba, ina buqatar qara sanin al’amura
masu yawa a game dake”.
Janet ta lanqwaso ta kwanta a
jikinshi cikin yanayin shagwava da jin

179
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
daxi a dalilin ita ma ba rabuwar tasu
take so ba ta ce mishi.
“Me kuma kake son sani bayan
duk abin da ka sani, ai komai ya riga
ya qare?”
Ya yi murmushi ya ce, “Ban yarda
ba Janet, barni kawai in san abin da
nake buqatar sani”.
Kwanaki biyun da Salim da Janet
suka yi, kwanaki ne na gwangwajewa
da morewa, tare da qoqarin gamsar
da juna.
Shi ka Salim a ta vangaren shi ya
riga ya gamsu har ma yana ganin
tamkar ita xin ta ishe shi ba kuma za
ta tava gundurar shi ba, ita ce irin
matar da ya yi ta fata da burin samu.
To gata ya same ta, sai dai
matsalar kawai ita ce, shi da ita sun
haxu ne suka bambanta, sun haxu ne
a kan son juna. To amma a vangaren
addini da qabila da wurin da suka
fito duk sun sha bamban, gashi kuma
shi da kanshi ya san iyayen shi ba
wasu mutane bane da suka waye,
don kuwa ko karatun bokon da suka
sanya shi ya yi tare da sauran
180
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
‘yan’uwanshi ba wai sun saka shi
bane a dalilin wayewarsu ta kai su
fahimci sanin muhimmancin bokon,
sun dai yi hakan ne kawai don sanin
darajar ilimi da sanin shi ilimin
kowane iri ne baya muni, ko da kuwa
na sihiri ne. To balle wannan da
zamani ne ya zo da shi.
Shi da kanshi Salim ya san in ban
da dacen da ya yi da iyayen da suka
san darajar ilimi da bai je boko ba,
inda don ta wayewa ne.
Cikin ‘yan makonni kaxan
makonnin da basu zarce huxu ba,
Salim da Janet suka yiwa juna
mannewar da ta kaima kusan kullum
sai Janet ta je gidan Salim, tuni ma
dai har ta fara gudunar da al’amuran
da take ganin ya dace ta fara kulawa
dasu.
A wannan lokacin Salim ya bar
kowa ya rungumi Janet ita kaxai,
saboda yarda da amincewar da ya yi
cewar ita xin daban ce da saura.
Tuni kuma ya fara tunane-tunane
saboda ganin yanda take tafiyar da
shi take tattalinshi, da gudun vacin
181
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
ranshi, komai ya yi daidai ne, in ta yi
mishi kuskure ta yi ta tuba tana ba
da haquri.
Tuni ya soma tunanin shin wai
mene ne aure ne? Yana ce zaman
lafiya, fahimtar juna da kwanciyar
hankali gami da mutunta juna kawai
ake. To shi kam ma me zai hana shi
auren Janet ne? Tunda tana son shi
tana girmama shi, tana gudun vacin
ranshi.
Kowane lokaci a cikin tattalinshi
take, a wannan lokacin ne ya soma
fahimta da daina ganin beken maza
‘yan asalin arewa dake barin ximbin
matan da suke arewan tamu suje
suna auren na kudu. Ashe-ashe suna
da dalilin su, ashe-ashe sun san abin
da ya sa suke yin hakan.
Cikin zuciyarshi ya ce, “Dama fa
Hausawa suna cewa wai banza ba ta
kai zomo kasuwa”.
Shi kam Salim a yanzu yana
ganin don ya auri Janet bai yi wani
kuskure ba, ba kuma wani laifi bane
yin hakan. Zai yi addininshi ta yi
nata, ‘ya’ya kuma za su tsaya
182
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
matsayin su, in yaso tunda shi shine
maigida kuma jagora sai ya san duk
yanda zai yi ya tsare girma da
martabar addininshi da asalinshi a
wurin ‘ya’yanshi.
Duk abin da zai yi daidain yi
wajen ganin ‘ya’yanshi sun zamo
‘yan salain arewa, ta inda duk aka
gansu ko aka hango su kuma a
shaida hakan, don haka zai tsaya ya
jajirce wajen ganin ya zama jarumin
maigida ba maigida na jeka na yi ka
ba, maigida mai faxi a ji a kuma
aikata ta yanda za a zamo ana haifar
mishi xan mace ne kuwa ko namiji.
To zai sunkuto su su zo nan
arewa gidansu gaban iyayenshi ayi
suna a kuma samu wani gwanin
wanzami da zai zauna a ranar sunan
ya sanya askarshi ta yi zane ya zane
mishi fuskar ‘ya’yan nashi, ko da
kuwa da zanen uku-uku ne, wato
gefen fuska da gefen kumatu, duk
kuwa da shi xin ba gadon irin
wannan zanen ya yi ba.
To amma shi zane-zanen da duk
inda aka ganshi an san zane ne na
183
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
mutumin arewa, don haka ba sai ya
ce ba, hasalima ai duk xan arewa xan
arewa ne, don haka in dai zai biya
mishi buqata, to shi kenan magana
ta qare.
Su Inna Wuro kuwa dasu Baba
Manu da Baffa Idi dama sauran
dangin da ya san ba za su haqura su
zuba mishi ido haka kawai ba, zai san
yanda ya yi ya yi musu bayanin da
zai fahimtar dasu su fahimci cewar
shi aure yanda suka fahimce shi a
da, to ba haka yake ba wurin
mutanen yanzu, su sun riga sunyi
mishi fahimta ce ta hanyar tsohon
zamani da suke faxin wai ba komai
ne auren ba face haquri da bin
umarni irin yi na yi bari na bari.
A wurin mutanen yau ba haka
maganar take ba, farko dai ana
buqatar soyayya mai qarfi, na biyu a
xan samu lokacin zama tare don
nazarin halayyar juna.
Don haka tunda basu za su zauna
mishi da matar ba, gashi kuma shi
xin ba yaro xan qarami bane yana
ganin zai je ne kawai ya tsaya ya
184
Idan kunne yaji…….1
Sodangi
yiwa iyayen nashi bayanin da zai
gamsar dasu su haqura su barshi ya
auri wacce yake so, wacce take ita ce
farin cikin shi, ko ba komai ma kuma
ai ya yi sa’a tunda ba yi mishi auren
za a yi ba shine zai yiwa kanshi, don
haka yana ganin damuwar ba za ta
zamo mai yawa ba.
Qarshe!!
Mu sake bin Mr. Salim Sulaiman
Jalo cikin littafi na biyu na “IN KUNNE
YA JI.....” to jiki zai tsira in ji
Bahaushe. Fatan alheri gareku dukan
ku, Ubangijinmu ya saka muku da
alheri bisa haqurin da kuke yi dani,
ya kuma sada mu cikin rahamarsa a
gobe qiyama, amin summa amin.
Na gode.
Taku.
Hafsat Chindo Sodangi.
(Mrs. Yunus Abdullahi Dabai).
Tare suka fito da na biyu.

185

You might also like