AL'AJABIN SO Book 1 Complete.
AL'AJABIN SO Book 1 Complete.
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
*Rubutu a kan ruwa... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO... Paid*
*BOOK 1*
*Page 1*
SHIMFIƊA
Tarihi yana nuna mana abubuwan da suka faru ne kafin mu a rayuwa!
Rayuwar duniyar cike take da kalubale, haɗari, wahalhalu da musibu daban-daban,
kusan in ka ga ka gujewa hakan to fa alƙalamin ƙaddara bata zana maka ita a shafin
ƙaddararka ba, a lokacin da kaddara ke wasa da rayuwarka ya rage maka ɗaukan wannan
kalubale a matsayin darasi, ka kuma yi haƙuri da jarabawar Allah (S.W.T) a gare ka.
Ni Fatima ban taɓa sanin cewa igiyar ƙaddarar wani na iya shafan na wani har su
sarƙe wurin zama abu guda ba sai da na tsinci kaina cikin alkaba'in rayuwa, zafi da
kunci suka yawaita a gareni, farin ciki yayi min nisa irin tazarar dake tsakanin
sama da ƙasa, na kasa tantance wai ƙaddarar wanene ya shafe ni, shin na mahaifiyata
ne ko na mahaifina? Ko kuma nawa ne ni a karan kaina ba'a tsaga ni cikin masu
rabauta da duniya ba?
A mafi yawancin lokuta in har nayi irin wannan tunani, na kan samu kaina ne da
yiwa gwanin halitta godiya da bai sa mana wani tabbataccen al'amari ba, farin ciki
ko baƙin ciki yana da lokaci, komai kuma yayi farko to fa yana da karshe, wani
karin maganar ma sai ya ce abinda ya baka tsoro a yau babu shakka ko tantama a gobe
ya iya baka tausayi, rayuwar tamkar tafiyar hawainiya ce tana tafe tana chanza
launi.
Al'amuran da suka faru a rayuwata sun sanya min karsashin bayar da labarina.
*****
Cikin matsakaicin speed motar ta shigo kayatacciyar harabar gidan, a natse take
ratsa duk wasu shukoki da parking lots masu tsari da suka yi wa harabar kawanya
zuwa ainihin kofar mashigar babban parlorn gidan kan ta dakata.
Da hanzari kuma cikin sauri wata farar matsakaiciyar budurwa sanye da kayan dake
nuni da cewa daga makaranta take don baƙar skirt ne jikin ta wadda iyakacinsa
gwiwarta sai farar shirt da baƙar blazer ta ɗaura jan necktie daga wuyanta, farar
doguwar safa ce a ƙasan baƙaken sau cikin ta wadda ya shiga har karkashin skirt din
na jikinta, a kanta baƙar hula ce wadda ya rufe mata gashi tsab kan ta ɗaura baret
dinta a karkace daga sama hakan sai ya baiwa kyakyawar fuskarta daman haskawa da
kyau, a hankali ta taka zuwa seat na baya ta sanya tsiraran hannunta ta buɗe kofar.
Wata buduruwar ce again da zasu iya yin sa'anni sanye da irin uniform din wacce ta
bude kofar sak ta fito, da mugun kallo ta fara bin wacce ta buɗe kofar kan ta ja
doguwar tsaki ta hankaɗeta ta wuce.
Cikin sauri ta dafe motar don gujewa kaiwa ƙasa a kuma sanyi irin tata na tsantsar
natsuwa da zaka hanga daga gareta ta ɗago kyawawan idanunta da suka cika tab da
kwalla sbd a makaranta ita da friends dinta yau ba karamin mutunci suka ci mata ba,
haka gun shiga mota saida ta zagi iyayenta kaman yadda suka saba sanin cewa hakan
ne abun da ke ci mata zuciya yake kuma ƙona ranta a take sossai, gashi yanzu m...
"Alayah...!"
Firgigit ta maida idanunta kan drivern da ya ɗauko su ɗin ta amsa da
"na'am baba Musa"
Ya ce
"kin mance jakar karatun taki ai yarinyar kirki"
Murmushinta me kyau ta sakar masa tare da komawa inda ta fito ta buɗe ta duƙa ta
dauki jakar tata ta rataye daga kafaɗarta guda tace
"Na gode baba, bari na shiga ciki, a huta gajiya"
Alayah kuwa saida tayi ɗan tafiya mai ɗan nisa kan ta isa ɗan wani karamin sashe a
natse ta hau varender ɗin ta isa kofar tare da turawa bakin ta ɗauke da sallama duk
da ta san babu me amsa mata, ta san anfanin hakan ne sbd an sha karantar da su cewa
sallama a wuri kaman dole ce musamman in zaka shiga gida ko da babu wadda zai amsa
a zahiri mala'iku zasu amsa kuma zaka samu ladar hakan.
Idanunta take warawa tana neman hasken rayuwarta, majinginar ta kuma sanyin
idaniyarta, ganin bata parlorn yasa tayi hanzarin nufar kofa kwalli ɗaya da sashen
dake yanayi da kango wadda bazaka taɓa kawowa akwai irin wannan sashe a cikin
tamfatsetsen gidan daga waje ba ke dashi.
Tana sa kai idanunta suka sauka kan abinda take nema kayatacciyar murmushi suka
sakarwa juna, kyakyawar farar macece wacce bazata haura 40yrs ba mai tsananin kyau
da cikar kamala kai tsaye zaka iya kiran ta da mahaifiyar wannan buduruwar da aka
kira da Alaya sbd fusgan kama da suke yi.
Murmushi cike da fuskarta wadda bazaka taɓa ganin ta dashi a wani wajen ba face nan
cikin kangon nasu ta amsa da kai tana alama irin ta maganar kurame
"eh ummi na dawo, ya gida?"
Ba tare da ta tsaya sake jiran maganan ummin ba ta sake yi mata alama bakin ta na
furta wa a hankali tace
"Ummi bari nayi sauri na watsa ruwa na shiga cikin gida kar nayi laifi wurin mommy"
Kai kawai ummin tata ta gyaɗa kan ta bita da ido har ta shiga bayin nasu, saida ta
fara wanke uniform din nata ta shanya sbd bata da tabbacin samun lokacin kanta in
har bata yi a yanzun ba kan ta watsa ruwan cikin hanzari, ta ɗaura alwala a bakin
famfon da banda shi da matsuguni (squats) babu abunda aka bar musu a bayin na more
rayuwa.
Dukda hanzari take amma hakan Sam baya nunawa sbd sanyin ɗabi'a da natsuwa a jinin
ta yake kaman gado ne tayi daga iyayenta duk su biyun, da kallo ummi ke bin ta har
ta shafa mai ta nufi Ghana must go ɗin su da bayan katifa da sallaya se bakko guda
biyun babu komai cikin ɗakin.
Sallar azahar ta tayar wadda ta ja lokaci a cikinshi sossai tana sallamewa landline
dake parlorn na ɗaukan ƙara har tuntuɓe ta ci garin saurin isa parlorn ta ɗaga kar
ta kara laifi, sallama tayi a ɗarare gabanta na faɗuwa don ta tabbatar a kap
rayuwarta bata taɓa ɗaga kiran alheri daga mutanen gidan ba.
Ba tare da an amsa daga ɗaya ɓangaren ba aka soma magana cikin faɗa
"Ke! Wato tsabar kin cika cikakkiya wani sabon rashin kunyar da kika tsiro dashi
yanzu kullum kuka dawo makaranta se na buga na nemoki kan ki zo ki kama min ayyuka?
To na rantse da Allah yau ne na karshe daga wannan an gama! in kin ga dama karki zo
kin san kan wacce zan sauke iskancin naki...."
Kit aka tsinke wayar, a hankali ta kai ta ajiye zuciyar ta Sam babu daaɗi, damuwa
da gajiya na neman fin karfinta dama already sun fi karfin shekarunta ga raunin
zuciyarta, a haka ta tashi ta samesu cikin wannan tsanani, a haka ta girma cikin
bauta, hantara da zagi wadda bata san farkonshi ba bare karshen shi.
Sau tari se tayi yunkurin yi wa ummintata magana akan wannan rayuwa da suke ciki se
taji tausayinta ya danne mata zuciya, bata san daga ina matsalar take ba. Shin
ummin tata bata da kowa ne bayan waennan azzaluman mutanen? Me yasa tun tashinta
ummin kawai ta sani matsayin uwa, uba da danginta? Babu wadda zai so dawwama cikin
ukuba bare ma irin nasun nan, bata da me bata amsa hakan ysa take iya kokarinta
wurin taya ummin tata da addu'a kaman yadda ita karan kanta bata gajiya ba a neman
mafita daga mai kowa mai komai.
Dafata da aka yi yasa ta ɗago tana kokarin maida kwallar da suka cika mata idanu..
"Kin gaji ko? Ko bakya jin daaɗi ne? Ki je ki kwanta bari naje Naji abinda zaki yi
ɗin se nayi"
Ummin tata tayi mata alama da hannu wadda tsab take fahimtarta sbd Kusan shi ne
First language da ta fara koya a rayuwarta don har so yayi yayi affecing mind ɗin
ta sai ta ga kaman magana da fatar baki ciwo ne a sadda tana yarinya karama.
Siririn hawaye ya gangaro mata ummin ta sa hannu ta share, ta ɗaga ido ta sanya
cikin nata Dukda rauni da damuwa da suka bayyana mata sossai hakan be hanata
sakarwa ummin tata murmushi mai ƙayatarwa ba tace
"Ummi zan je kar na kara yin wani laifi"
Daga chan karshe ta buɗe wani kofa da ya sada ta da wani babban parlor wadda na
matar gidan ne mommy kenan, kaman wanchan shima a share kuma a tsabtace yaji
kujerun alfarma ga sanyi da raɓar Ac.
A cikin lumtsuma-lumtsuman kujerun ta samu mommy zaune ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya,
tana sanye da wani ɗan ubansun lace na manyan mata taji adon gwala-gwalai hannaye
da wuya, hannunta rike da waya kirar Samsung wadda ake cewa Fold tana latsawa, a
kan gwiwowinta Alaya ta zube tace...
Kaman ba da ita take ba, kaman ma bata san da zaman mutum a wurin ba saida ta bushi
iska don kanta bayan kafafun Alayah sun fara tsami a tsugune kan ta ce
"wato ke don uwaki tsabar kwakwalwar kanki a toshe yake kaman yadda kunnuwar uwarki
kurma suke a doɗe Sau nawa zan faɗa miki in sake nanata miki karki sake ki haura
mintuna talatin daga dawowarku daga makaranta zuwa ganin ki a parlorn nan?"
Kanta a ƙasa idanunta cike da kwallah saide bata bari sun zuba ba tace
"kiyi hakuri mommy sallah na tsaya yi"
"ke a gidan uban wa na zama mommyn naki? Ban ce ki dinga kirana Hajiya ba? Ko kin
ga nayi kala da uwarki? Sunnu limamiyar Makka! Tukuna ma me ya hanaki wankewa
jameelah bayi yau da har ta kasa shiga bayan ta dawo daga makaranta sai na ɗakina
taje ta shiga tayi wanka?"
Bata ɗago ba a duniya babu fuskar da bata ƙaunar gani irin ta Hajiya Zeenat sai
taga kaman idan ta kalleta zafin da zata ji daga zagi da cin mutuncin sai ya fi
wadda take ji idan bata kallon ta.
"Ki wuce kije ki wanke mata bayi, ki chanza mata beddings don ta ce ƙaiƙayi suke
mata ki tattara laundry ɗin ta ki je ki wanke sannan ki zo ki ɗaura dinner don
kurma ta riga ta ceceki tayi na rana ita me ƴa"
Mikewa tayi ta nufi kofan hagu daga cikin parlorn shima yana da karamin parlor da
dakuna biyu na hagu ta sake isa ta yi sallama, ba amsa, ta sake yi Dukda ta san
Meelahn na jin ta amsawa ne bata yi niyyar yi ba, in kuma ta ƙusa kai ba izini ma
wani maganan ne.
Tana zaune cikin ɗaya daga cikin kujeru guda biyu dake ɗakin hannunta rike da waya
tana latsawa haka kunnuwanta sake da babban baby pink headphone saide bata tunanin
tana using ganin baya haske, ba tare da tayi kwakwaran kwaraniya ba ta wuce toilet
ɗin ta wanke shi tsab bayan ta gama ta dawo ɗakin bata sameta ba hakan ya sa ta
fara cire zannuwan gadon ta chanza wani tare da gyare ɗakin tayi mopping da goge
goge, hannunta dauke da kayan cikin laundry basket ɗin Meelahn ta fice zuwa chan
baya inda suke wanki.
Bayan ta zube su ta koma kitchen bayan store akwai wani karamin laundry room dauke
da abubuwan shanya, washing mashings da sabulai da omo kala kala wasu a goruna wasu
a ledoji, zaɓar waenda ake yi wa Jameelar wanki dasu tayi ta koma ta hau wanki, ta
jima sossai tana yi sbd kayan da ɗan yawa saukinta ma babu wani datti sbd sawar
mugunta ce sai a sa kaya kala uku huɗu a rana, tana gama sanyawa ta tsuguna a wurin
riƙe da kanta dake sarawa, bayanta kaman ta cire ta ajiye sbd yadda yake yi mata
wani irin ciwo, hawaye masu zafi ne suka zubo mata tana jan numfashi da kyar ta sa
hannu ta goge, ta jima haka kan ta miƙe ta nufi kitchen wanke wanke ta fara na
kwanukan rana da aka ɓata bayan ta gama ta goge ta shanya kan ta matsa ta duba time
table na abinda zata yi na dare.
Miyar ganda ce ta kan Sa sai tuwon shinkafa, fiddo naman kan tayi daga freezer ta
sa a pressure pot ta zuba mishi ruwa me yawa ta ɗaura kan hot plate tare da
kunnawa, chan gefe inda ta ga kular abincin su ta nufa ta ɗauka dama ta riga ta san
ba daga tukunya yake ba wadda suka rage ne suka juye musu a kular da ya kasance
nasu, sashensu ta koma ta samu umminta ta idar da Sallar la'asar kenan, zama tayi
gefen ta cikin tsantsar gajiya ganin zaman baze yiwu ba ta zame ta kwanta a wurin
tare da lumshe idanunta da suka fi yanayi da na Larabawa farare sol mai ɗauke da
baƙi sidik ɗin kwayar ciki, zara zaran gashin har ya sauka fuskanta don tsawo da
kyaun su.
Murmushinta me kyau ta sakarwa ummi ko kusa ita karan kanta bata Fatan tashin ciwon
ta don ta san ummin zata bari da wahala da kuma damuwa, cikin yatsina fuska ta miƙe
zaune ta fara yi wa ummin tata magana
Murmushi ta saki sossai har saida fararen hakwaranta dake jere reras zuwa dimples
ɗin ta guda biyu suka bayyana.
"Ai ba wai ƙarya ba ce ummi bana so hankalinki ya dinga tashi ne" tana kai nan ta
janyo kular abincin tana yi wa ummi alama da
"wallahi Sallar nan ba zan iya yinshi ba matukar banji sauƙar abu cikin ƴar hanji
na ba, yunwa nake ji kaman in ci babu".
Murmushi kawai me cike da ma'anoni daban daban ummin da suke tsananin kama da
Alayar sai en abu kalilan da bata ɗauko nata ba ta saki kan tayi mata alamar a ci
dae da bismillah, inaaa ita kam tayi nisa a cin abincin ta, tunda take a duniya
bata taɓa jin abincin da ya kai na umminta daaɗi ba, lokuta dayawa ta kan tambaye
ta wai wani makarantar koyon girkin tayi? Lura da ta yi tambayar kan taɓo mata wani
fanni chan na rayuwarta yasa ta daena.
Sai da ta fara kai wa geji kan ta lura da ummin tata bata ma soma ci ba, da sauri
ta dakata tare da ɗago idanunta farare sol ta dubi ummin da tayi nisa da kallon ta
fuskanta dauke da murmushi sannan hawaye na zuba mata daga saman fuskanta.
"Ummi menene?" Ta tambaya cikin tsantsar damuwa Dukda ba yau ne na farko da ta kan
tsinci ummin tata cikin irin wannan hali ba.
"Babu komai Alayah, kawai kin tuna min da mahaifinki ne da abubuwa guda biyu
yanzu".
Itama Alayar yanayinta ne ya sake sauyawa jikinta a sanyaye tayi wa ummin alamar
Katsewa maganar yayi ta sa bayan hannu ta ɗauke hawayen ta Allah sarki mutuwa,
mutuwa baya barin wani don wani yaji daaɗi.
Daga nan se walwalarsu ta kau, a koyaushe dama walwalar tasu bata wuce na dakiku, a
duk sadda zasu tuna da jigon rayuwarsu kowa da abunda ze ke kitsawa a ran shi.
"Ummi a duk sadda kika yi wani zance na Abba alamu su kan nuna Yana da dukiya,
sannan yana da kirki ga mutane da kyakyawar alaƙa, yana da son mutane kaman yadda
su ma suke son shi? Ummi ina dukiyar? Ina mutanen nashi? Ummi Don Allah mai ya
ajiye mu anan cikin azaba da kuncin rayuwa??" Tayi maganar cikin zubar hawaye, da
sauri ummin ta hadiye ƴar walwalarta cikin sanyi da siga na bada umarni tace
*karki manta book 2 paid ne a naira 500 kachal ze zo muku immediately after an gama
book 1, zaki iya biya tun yanzu ta wannan asusun
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin, se ki turo shedar biyan ki ta wannan layi
*09039206763*
#comment
#Vote
🖤Gureenjoh🖤
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*
*BOOK 1*
*Page 2*
Tana Sallar tana zubar da hawaye tana kuma adu'ar Allah ya sassauta musu ya
gafartawa mahaifinta da take jin kila da yana nan da ba haka rayuwarsu zata kasance
musu ba cikin rashin gata da galihu, wulakanci da tozarci ya zame musu ruwan sha
don da yana tsiro da babu masaka tsinke jikin su, cikin matsanancin kaskanci da
rashin Ƴanci, ta san ko menene zai tsaya yayi tsayin daka don samar musu walwala da
rayuwa mai inganci a matsayinshi na mahaifi kuma miji ga ummin ta, mutuwa mai tonon
asiri.
Umminta gani take har yanzu ita ɗin yarinya ce ko gani take da already dama
zuciyarta da aka haife ta da rauni na ciwo ba zata iya ɗauka ba shiyasa har yanzu
bata iya bata labarinsu daga ita har mahaifinta ba, da yadda aka yi suke zaune
cikin wannan baƙar gida, abubuwan da zata ce ta sani akan mahaifinta kalilan ne
wadda take tsinta a wurin su baba Musa su ɗin ma se subutar baki ko in tayi wani
abu da yayi yanayi da nashi, addu'a sossai tayi kaman kowani bayan sallah tana
share hawaye da bayan hannunta se tayi looking very cute and adorable kaman baby.
Ummi ta santa sarai da shegen shagwaɓa wadda rayuwar da suka tsinci kansu a ciki ya
koya mata juriya, ta kure ta da ido tana banbance kukan ta ne na sakalta ko kuwa
daga zuciyarta yake fita? Se ta fahimci wannan ɗin hawaye ne masu ciwo da dumbin
damuwa, ajiyar zuciya ta sauke har Alayah ta miƙe ta mata alama da ta koma cikin
gida ta kama aikin dare.
Har ta fice ummin bata ce komai ba, Allah ya gani ba labarinsu bane bata son bata,
sam bata so yarinyar ta sawa kanta kiyayya ko fansa ko wani abu makamancin haka a
raunataccen zuciyarta da babu cikakken lafiya bare hutu, she cannot risk the life
of her only daughter wacce itace hapiness ɗin ta a yanzu.
Ita ko Alayah bayan ta koma kitchen din aikinta ta fara cikin son ture damuwowinta
sbd umminta, cikin kwarewa da gogewa a girki da ta samu daga umminta ta haɗa Miyar
kan San banda kamshi babu abunda yake tashi, a gefe ɗaya ta ɗaura tuwon
shinkafarta, kan Ace an kira magarib ta gama ta kuma kimtsa kitchen ɗin tsab kaman
ba'a yi komai ba, anan kitchen din tayi Sallar magarib, seda ta jira Masu gidan
suka fito tukuna hajj Zeenat ta dibar musu abincin su, godiya tayi ba tare da ta
samu amsa ba ta ɗauka ta fice.
Kaɗan ta ci ta samu tayi isha da kyar sbd tsananin gajiya da baccin dake ɗawainiya
da ita Dukda tarin assigments da take dasu gajiya be barta ta bi ta kan bokon ba,
tunda ta kwanta a sallayar ko motsi bata yi ba haka bacci ya ɗauke ta.
Ummi ta tsira mata idanu tana tuna chan shekara kusan 17 baya.....
****
*****
Tashin da Alayah tayi a firgice shi ya katse mata tunanin da ta tafi har tsorata
tayi, sai ta ga tayi wurin landline da gudu tayi picking sbd saura kiris ya tsinke,
da alamu kira ake ita ummin bata ji ba sbd babu kunnen, mintuna biyu taga Alayar ta
dawo tare da ɗaukan hijab ɗin ta ta saka fuskanta sam ba walwala, da hannu ummi
tayi mata alama..
"Menene? Ina zaki je a daren nan?"
Seda ta sauke ajiyar zuciya tace cikin alamar kurame
"Ummi Jameelah ke nema na wai dare yayi bazata iya cin tuwo ba in je in dafa mata
indomie in soya mata plantain in kuma dibi Miyar as pepper soup in kai mata ɗakin
ta"
Shiru ummin tayi kan ta ɗago ta ce
"Ki kwanta bari na je na yi mata"
Da sauri ta girgiza kai tana mata alama
"a'a ummi babu ta yadda za'ayi ina kwance kina chan kina yiwa Jameelah girki bari
naje yanzu zan dawo"
Kanta ƙasa har Alayar ta fice..
Lallai dukkaninsu Allah ya amsa adu'o'insu, ya bata mace me tsananin kama da ita
kaman yadda mahaifinta ya roka, se kuma ya amsa nata wurin bata halayya mafi
rinjayi na mahaifinta me haƙuri, juriya da kuma jin ƙanta, sanin kanta ne Alaya ta
ci sunan inkiyarta na princess, smart and beautiful, kwata kwata bata son ganin
ummintata na wahala Dukda a ciki ta tashi ta sameta, bata ƙaunar jin wani kalmar
ɓatanci in har dae akan umminta ne, hakan ya sa wahalhalu dayawa takan ɗauke mata
na ayyukan gidan da kankantar shekarunta, ɗaga hannu sama tayi tana rokon Allah
ubangiji ya kawo musu karshen wannan rayuwa da suke ciki don suna tsananin
jiggatuwa...
Cikin mintuna da basu fi arba'in ba ta gama tare da kai mata har daki, ba zata iya
jira ba tunda ta san ko yau ko gobe din ne itace dae zata fitar da kwanukan don
haka ta wuce sashensu, da kyar ta iya sauya kayanta ta koma bayan umminta ta kwanta
a take bacci yayi awon gaba da ita se lokacin ummin ta juyo ta tofeta da addu'a kan
itama ta shafa ta lumshe idanu tana sake sake har bacci ya ɗauke ta.
Washegari da safe kaman yadda al'adarsu take a gidan suna Sallar asuba suka miƙe
suka fice, ummi na tsaftace gidan yayinda Alayah ke ta zirga zirga a kitchen wurin
haɗa breakfast, tayi nisa a aikinta tana cikin soya doya taji ƙarar fashewar abu a
lokaci ɗaya ta tsinci gigitacciyar tsawar Hajj Zeenat wadda ta tabbatar umminta ce
kawai take yiwa irin wannan tsawa, wani mummunan faɗuwa gabanta yayi wadda ya
haddasa bugun zuciyarta tafiya fat fat fat kuma hakan barazana ce ga lafiyarta, da
sauri ta saki cokalin hannunta tayi parlorn Dukda ta san laifi take shirin aikatawa
amma bazata bar umminta ta muzanta gabansu ba, da gudu ta shiga gaban ummi marin da
hajj Zeenat ke shirin sauke mata ya sauƙa kan fuskar Alayah ji kake tassss, tsabar
zafin marin da karfin shi seda ta fadi jikin ummin ta baya baya, ko gama dawowa
hayyacinta bata yi ba tayi saurin zubewa bisa gwiwowinta tana cewa..
Da kallo ummi take bin su dukkansu biyu, shimfide cikin idanunta kana iya hangar
zafi da turirin zuciya da take fama dashi a lokacin, soyayya da kulawa irin ta uwa
ya wuce a ce a zabgawa ɗan ka mari me wannan zafi a gabanka ka kasa tabuka komai,
wani irin zafinsu take ji barin ma shi, duban su ta sake yi a karo na ba adadi kan
ta janye Alaya suka fice daga parlorn.
"Me kenan kake kokarin yi Abban Jameelah? Ƙaskantar da ni a gaban waennan ƙaskantun
mutanen? Ka kuwa san laifin da ta aikata min?"
Hajj Zeenat ta faɗa a kufule
"ban sani ba kuma bani da ra'ayin sani, abunda kawai na sani shine sau ɗaya tak
kika yarda kika sauke hannunki kan hawwa ranki idan yayi dubu to se ya ɓaci, duk
abunda kike kallonki kawai nake ba wai bani da ikon hanawa ko dakatarwa bane, ni na
san anfanin da hakan ke min don haka ki kiyaye, don yarinyarta ban damu ki mata ko
ma menene ba amma banda hawwa"
Yana kai nan ya juya ya buɗe wani kofa da ze sada shi da sashen shi ya shige.
Zaune hajja Zeenat ta kai tana jin zafin wannan abu da Alhj ke mata, wani irin
turirin tsanar hawwa da Alaya take ji kaman ta shafe babinsu a duniya, a kan hawwa
duk wani farin cikinta na gidan aure ta rasa shi, ga kuɗi har kuɗi amma bata da
kwanciyar hankali, menene manufar Alhj akan hawwa ne da ya zuba ido shekara da
shekaru ina mata yadda na so? Ta tambayi kanta daidai lokacin da Jameelah ta fito
tana tambayar ƙaurin da take ji a gidan gabaɗaya.
Da hanzari suka yi kitchen masifa sossai hajiya Zeenat ke yi na duk laifin Ummi ne
gashi Alaya ta ɗaura tea a glass pot dinta ruwan ya ƙone har ya fashe, tambayarta
Meelah tayi se take bata labarin abunda ya faru cikin jin haushin Alhj har yanzu.
"Ai ko wlh sun yiwa kansu yau azumin dole zasu yi babu me samun abun kari"
Hajiya ta karashe da hakan, kwafa Meelah tayi tana tunanin yadda zata ci zarafin
Alaya, mommyn ta saka ta dafa mata indomie da tea ta ci kan ta nufi ɗakinta don
ƙarasa shiryawa, mommyn ma ɗakinta tayi tana danna kiran wayan aminiyarta Hajiya
Fanta...
A ta ɓangaren Ummi kuwa cike da tausayi irin na uwa take duba fuskan Alaya bayan ta
zaunar da ita bakin katifarsu
"Alayah me yasa kika shiga marin ya same ki? Kin dae san baki da wadataccen lafiya"
"Ummi lafiya ta ƙalau i promise" tayi mata alama tana danne radadin zuciyarta.
Shiru duk suka yi babu wadda ya iya sake cewa komai kowa da tunanin da yake a
zuciyarshi, daga karshe Alaya ta miƙe tana cewa zata je ta ƙarasa breakfast kar ya
zama laifi, ummi ta ce ta shiga tayi wanka ta shirya makaranta zata je tayi da
kanta, komawa sashen ummi tayi ta fara soya doyar da Alayar ta fere, tana juyewa a
kuloli Meelah ta shigo tsab a shirye cikin full uniform din ta, wani irin kallon
kyama da tsana ta watsawa ummin kan ta nufi fridge ta buɗe ta dauki hollandia
youghut da ta shigo ɗauka ta tsiyaye cikin wani bottle flask ta zuba mishi kankara
ta juya ta fice.
Ko da Alayah ta shigo Hajiya Zeenat bata fito ba bare ta basu abunda zasu ci, se
kawai Alaya tayi wa ummi sallama akan se ta dawo kawai yanzu in ta ajiye Meelah
Abbanta ze kusa kasheta.
Rayuwa baka samun yadda kake so, ga dae abincin ummi ta gama jujjuyewa saide
babu halin su taɓa sbd gudun tashin hankali da tozarci, tana ji tana gani Alaya ta
fice ba tare da ta karya ba.
Ko a makaranta Alaya bata yarda ta shiga sabgar Meelah ba duk da yadda sukan zage
ta da kawayenta ko su zungureta bata ce musu ci kanku gudun fitina, karfe 1:30pm
suka tashi daga makarantar hadari ne sossai ya haɗu a sararin samaniya banda iska
babu abunda yake kadawa alamar ko da yaushe za'a iya tsugewa da ruwan sama, dubawa
Alayah tayi taga baba Musa be kai ga zuwa ba hakan ya sa ta nufi masallacin su don
gabatar da Sallar azahar kar ta je gidan ga aiki ga yunwa tana ji, banda ruwa babu
abunda ta sakawa cikinta gabaɗaya yinin tana kallo a break yadda Meelah ke kashewa
kanta da Ƙawaye kudi a cafteria, ita ba mai shiga mutane ba ita ba kawa ba don tana
matukar kama kanta da tsayawa matsayarta, duk makarantar ƴaƴan masu hannu da shuni
ne hakan ya sa tun farko ta kama kanta ta keɓe rayuwarta, duk duniya bata da kawar
da ta wuce umminta.
Ko da ta fito ta duba agogo biyu saura mintuna sha biyar, da sauri tayi wurin
ajiyar mota don duba baba Musa ko ya zo kar ta ajiye Meelah ta kara laifi duk
dubawar duniya bata ga Meelah ba bare baba Musa da ta san har ta shiga masallaci
bai zo ba, wurin gate man ɗin su tayi take tambayar motar gidansu ta fita?
Makaranta ce me matukar tsaro hakan yasa babu motar da zai shiga ya fita ba tare da
gate man ya tantance ba.
"Eh sun fice tun mintuna biyar baya"
Gabanta ya yanke ya faɗi sun tafi basu jira ta ba? Ya zata yi da nisar tsakanin
unguwar su da makarantar? Ya zata yi da yunwar da take ji kaman ze kasheta? Bata da
ko sisi babu dalili, ko bashi ta karɓa ina zata samu ta biya su? Su da suke rayuwa
sai abin da aka tsakura aka basu.
Iskar ruwan dake shirin zuba at any moment ne ya kara karfi, takawa tayi ta sa
hannu a karamin gate ta buɗe ta fice sbd Kusan duk school din babu kowa, takawa ta
fara bata ko yi taku biyar ba aka soma yayyafi kan ka ce kobo ruwan ya tsuge a take
ya kuwa sameta ba ɓata lokaci ya fara bugunta, bata tsaya ba kaman yadda bata fake
ba sai tafiya take, daidaikun mutane dake neman mafaka se kallon ta suke, yayinda
ita kuma tana ji bazata iya jiran ruwan ba, umminta zata shiga damuwar rashin
ganinta sannan ya ayyuka zasu mata yawa.
Ruwa ne ke zuba sossai ɗauke da walkiya da tsawa gudu yake tsugawa a bisa
shimfidadden titin sbd karancin abun hawa kuma yana sauri, sam bai zaci ko tsammaci
ganin mutum bisa titi ba a wannan yanayi na ruwan sama mai karfi dake zuba kawai se
ganin halitta yayi kaman daga sama a gabanshi kuuuuuuuuuu haka wani irin ƙara ya
karade wurin ya haɗu da wani tsawa da aka saki....
*Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same
shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi
09039206763*
#Vote
#comment
🖤Gureenjoh🖤
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*
*BOOK 1 *
*Page 3*
A matukar tsorace cikin gigita ta tsaya kyam hannayenta bisa kunnuwanta idanunta a
runtse jikinta kuma ya ɗauki kyarma, kaman yadda baƙar motar kirar jaguar XJ baƙa
sidik wacce ba'a iya kallon komai nata ta tsaya chak, jin shiru motar bata bugeta
ba har lokacin yasa ta sauke hannunta a hankali, idanunta dake rine ta ɗaga ta
kalli gefen da mota yake ganin yana nan tsaye yasa ta miƙe a sanyaye, uniform nata
a jike shakab ta cigaba da tsallakawa a hankali tunda ta tsira daga sharrin kaɗewar
motar, har ta tsallaka bata ji motar tayi wani motsi ba seda ta bar kan titin
gabaɗaya kan taji wucewar motar da karfi kaman iska, juyawa tayi ta bi motar da
kallo na second kan ta cigaba da tafiyarta.
Sai wuraren uku ta iso gida a lokacin yayyafi kadan kadan ake, jikinta babu inda
baya rawan sanyi, gabaɗaya hankalinta a tashe banda tunanin umminta babu abunda
take ta san tana nan tana jimamin rashin ganinta bayan Jameelah ta dawo tuntuni,
karamin gate nasu ta kwankwasa Malam shazali ya zo ya buɗe ganinta ya sa ya kauce
ba tare da ya ce komai ba ta shigo, cikin sassanyar murya tace
"sannu da aiki malam shazali"
Yace
"sannu Alaya haka ruwa ya jika ki? Meyasa baki hakura ruwan ya tsagaita ba kan ki
taho? Tun dazu baba Musa ke ta jimami akan ki wallahi Hajiya karama ta hana shi
jiranki kaman yadda ta mishi barazana da aikinshi Idan har ya fita ya koma don
ɗauko ki"
Wucewa tayi zuwa sashensu tana shiga ta fara kokarin raba kanta da kayan jikinta
sbd irin rawa da jikin nata ke yi na sanyi, da wasu kayan ta chanza tana kokarin
tsugunawa don tattare kayan taji kirjinta yayi wani irin riƙewa, sunan Allah ta
kira tana dafe kirjin da kaman ze tsage don azaba, cikin karfin hali ta ja ta isa
kan gado ta janyo zannin ummi ta lullebe jikinta ta dunkule hannunta dafe da saitin
zuciyarta tun tana dauriya har kuka ya kwace mata tana kiran ummi...
Ummi kuwa Dukda aiki take sede hankalinta rabi da kwata baya tare da ita, gashi dae
sun haɗu da Meelah sau biyu amma tsoron tambayarta Alayar take bama ta san ta yadda
zata fara ba don mutunci be taɓa hada ta da Jameelah ko na minti ɗaya ba, in zata
iya tunawa har miyau Jameelah ta taɓa zuba mata a fuska, wa kuma ya san irin zagin
cin mutuncin da suke sha don ma bata da kunnen ji, a gaggauce ta gama wanke wanken
da take ta nufi komawa sashensu don duba ko Alaya ta dawo.
Karo ta ci da jikakkun uniform nata daga tsakar daki seda gabanta ya yanke ya faɗi
da sauri ta ƙarasa ciki tabbas da tana da kunne zata iya jin irin kukan da Alaya
take cikin ciwo, da gudu ta ƙarasa ta ɗago ta tana kokarin maganan su irin na
kuramen nan sede babu abunda yake fita, hannun Alaya ta kama se taga ya chanza yayi
wani abu blue tinge wadda a turance ake kira (cynosis) gabaɗaya ilahirin hannun,
jijjigata tayi ta buɗe idanunta da kyar nan ma duka haka ne alamun ciwon zuciyarta
ya tashi, ganin yadda numfashi ke shirin dauke mata kaman bazaka kyapta idanu ka
buɗe ka sameta da rai ba yasa ummi Miƙewa da sauri tayi waje..
Tana fita motar Alhj Hassan Dala na parking a tsakar gidan da sauri ta nufe shi, a
gabanshi ta tsaya hawaye na zuba mata, duban ta yayi na mintuna ya san in ya
kalleta cikin wannan hali ƴar ta ce ba lafiya, baki ya taɓe kan ya koma motarshi
hankalinshi kwance yayi rubutu a jikin wani joter ya ɓalle ya fito, hannu ya sa a
aljihu ya zaro kuɗin da baza su wuce dubu talatin ba ya watsa mata da papern,
duƙawa tayi tana kuka tana tattarewa cikin sauri sauri daga haka ta miƙe tayi
sashensu.
A hannu ta riko Alayar dake tafiya da kyar da karfin hali don bata ma sanin tana
ɗaga kafa sbd azabar ciwo, baba Musa da dawowarshi kenan yake tambayan shazali me
gadi ko Alaya ta dawo shi kuma yana bashi labari ya hango Fitowar su duk hanaklinsu
seda ya tashi ummi kuka Alaya kuka, baba Musa ne yayi kundunbalar fita ya samo abun
hawa da kyar sbd irin tsaron unguwar, ya cewa malam shazali idan har aka tambayeshi
ya ce ya tafi gida an kirashi iyalinshi ba lafiya.
A napep din banda faɗa cikin tausayawa su ummi babu abunda yake, har yaushe wannan
rayuwar zaluncin? Ina ma yana da wani iko da ko se ya ga abunda ya turewa buzu nadi
akan iyalan Alhj Ahmad marafa, har hawaye yayi jin yadda Alaya ke kirar sunan Allah
cikin azaban ciwo, asibitin murtala suka isa sbd nan ne su kan je idan irin hakan
ta faru don basu da dalilin na kuɗi ɗan abunda yake basu idan ya ishesu Toh
falillahil hamd idan kuma be isa ba sede su bar jinyar a haka idan har an ɗan samu
sauƙi hakan yasa kullum Alayar take a wahale babu kuma ƙiba se rama.
Cikin hanzari aka karbesu aka fidda file ɗin ta aka yi emergency da ita, ummi
zama tayi bakin wurin tana zub da hawaye masu zafi, ita kadai ta san irin tashin
hankalin da take shiga a duk sadda ciwon Alaya ya tashi irin haka, ita kadai take
dashi idan ta rasata ina zata saka rayuwarta?
Bata da tabbacin ko likitan zuciya ne ya shiga kan Alayar sun dae ɗauki lokaci a
kanta kan suka fito, baba Musa yake tambayar su ya jikin nata?
"Baba wannan ɗin ƴarka ce?"
Ya amsa da"eh"
"Kwanaki na bada shawarar zuwa wurin Dr philip sbd kwarewarshi a harkar zuciya chan
meddy specialist hospital ban san Meyasa kuka kasa daukar shawarata ba, ina me
tabbatar muku yarinyar nan tana kara shiga yanayi me hatsari ne a yawan attack da
take samu idan mun iya tseratar da rayuwarta yau gobe babu abunda zamu iya, so
prevention is better than cure"
Wucewa doctorn yayi yayinda ummi ke ta kallonsu cikin zakuwa da son jin me suke
cewa sbd gabaɗaya hankalinta yana kan lafiyar gudan jinin ta, Juyowa yayi tare da
yi mata bayani bata iya ta ce komai ba se hawayen da take sharewa a kai kai ba basu
je Meddy din bane sun je sede irin kuɗin da suka ji daga karbar kati ma zuwa ganin
Dr ba karamin kudi bane basu dashi babu kuma dalili.
Ummi ce rike da hannun Alaya dake ta aikin bacci sbd alluran da aka yi mata lokaci
lokaci ta kan kalli mutanen ɗakin, kowa da kalar ciwonshi, ward ne me ɗauke da
gadaje kusan ashirin dogo ne sossai, Malam Musa ya samu ya tafi sbd gudun matsala
zaninta ta kwance ta fiddo papern joter din da ta nannade ta ɗaure a wurin ta fara
warewa a hankali.
"Kaman yadda na faɗa miki a baya na kuma maimaitawa yanzu ma ba zan gaji ba zan
sake faɗa, hawwa duk wani abunda yake faruwa daku laifin ki ne, lafiyar ƴarki a
hannunki yake kaman yadda lafiyar kunnuwanki suke hannunki, Da kalma ɗaya tak! Zaki
ƴanta ku zuwa sabuwar duniya amma kin kasa anfani da wannan dama, a yau Idan Fatima
ta mutu karki ga laifin kowa se kanki, ke ce kika kasheta..."
Dukunkune papern tayi tare da runtse ido da karfi hawaye na gangaro mata sossai, da
sauri take girgiza kai kan ta ɗaura kanta jikin gadon Alaya ta saki sassanyar kuka,
shin ya zata yi? Har abada bata jin zata iya abunda Alhj Alhassan Dala yake so,
amma ganin ƴarta a hali irin na dazu ya sa take jin zata iya yin komai sbd samun
lafiyarta, in tace komai tana nufin komai amma buƙatar Alhassan ya zarce da
tunaninta, Allah ka min mafita... Abunda take ta nanatawa kenan a ranta.
"Ummi!"
Alayah ta faɗa tana me dafa ta idanunta da suka sauya sossai suke lumshewa da kansu
ta zubawa ummin da ta ɗago take share hawaye a lokaci ɗaya tana tambayarta ta
farka? Ya jikinta? Me take so? Duk cikin alamu irin ta maganan kurame.
"Yunwa ummi, yanzu karfe takwas na dare babu abunda ya shiga bakina tun safe banda
ruwa"
Tayi alamar cikin tsananin jin yunwa ga ciwo, bakin ta duk ya bushe.
Miƙewa ummin tayi tace mata tana zuwa ta fice, maida idanunta tayi ta kulle tana
jin yadda surutan matan masu jinya da masu kula dasu na ta tashi kaman kasuwa hakan
ne fa ya sa ta tsani asibiti, tana nan kwance har ummi ta dawo ta taimaka mata ta
wanke bakin ta, da kanta ta wanke hannu take ciyar da ita dafaffen doya da Miyar
sauce ɗin da ta saya a bakin asibiti daga cikin ledar, bayan ta ci sossai ta ɓula
farin ledar da aka kulla mata kunu ta bata ta sha sossai kan ta sha magungunan da
ta sayo duk tana bacci lokacin ta sha.
Rokar roba wurin makotarsu tayi ta saka ta tayi alwala ta rama sallolin da ake bin
ta, ummin se kallon ta take tana tunanin wani shawara zata yanke, duk wadda ta zaɓa
babu sauƙi...
Kwanansu biyu asibitin banda ma'aikatan gidan babu ƙafar wadda suka gani a ahalin
gidan dama sun saba Dukda da ciwo matuka, duk faɗar ka da mutum ai ciwo ya fi gaban
komai, yanzu haka zasu koma su ɗaura musu da bauta ba tare da kyautatawa ko na
minti ɗaya ya shiga tsakaninsu ba, banda abinci da shima se an ga dama a basu da
kuma makarantar Alaya ba zasu ce ga wani abun arziki da suke tsinta a rayuwar gidan
ba, amma ya suka iya? Ya kuma zasu yi? Nan ne kaddararsu kuma nan Allah ya zaɓar
musu su yi rayuwa.
Landline ɗin sashensu ne ya ɗauki kara ko gama tattare sashen ummi bata yi ba sbd
tunda suka tafi babu wadda ya dawo se yau, ummin kuma ta hana Alayar kama mata sbd
har yanzu jikin se a hankali, ƙarasawa tayi ta ɗauka Muryar Meelah ne ya karade
kunnenta
"Ki zo ki yi min gyarar daki"
Shine abunda ta faɗa kan ta kashe babu ko amsa sallamar da tayi mata, ummi ce ta
tambaya me take so? Nan ta faɗa mata, girgiza kai tayi tacewa Alayar ta je ta
kwanta zata je tayi mata.
Babu dae yadda ta iya ne haka tana gani ummin ta fice, zama tayi a wurin ta sanya
kanta cikin kafafunta tana tunanin abunda kaddara ya zaɓar musu se yaushe ze wuce?
Anya kuwa zasu samu chanjin rayuwa?
Kwarai ummi tayi mamakin ganin irin yadda Meelah ta maida ɗakin a kwana biyu kaman
ba mace ba? Duk wasu ledojin kwalamarta na zube tsakiyar ɗakin wasu kayan sawa wasu
takalma duk gasu nan ɗaiɗai baje a ɗakin haka ta soma tattarewa a natse ta jima kan
ta samu ɗakin ya dawo daidai ta juya ta fita ta tsaya parlorn ta gyara ta koma na
Hajiya Zeenat ta fara kenan Meelah ta fita daga dakin uwarta tayi nata ba'a yi
mintuna goma ba ta dawo ta tsaya kan ummi tana mata magana cikin tsawa.
Ganin ba jin ta zata yi ba yasa ta dauko sandar mopper da ummin ke aiki dashi ta
zungureta wai ita nan kyamar taɓa ummin take, Juyowa ummin tayi saide Meelah ba
maganan kurame ta iya ba masifarta ya fito da Hajiya Zeenat
"a'a Shalele mai ta miki ne?"
"Mommy ina sarkar da Abba ya sai min last business trip din shi daga Lagos?"
"Mommy daga shiga ta min shara kawai in fito ban ga sarka ba? Kan uban chan
kayyasaaa! Wlh sai ta fitar min da sarkata "
Meelah ta faɗa tana wani hararar ummi cikin tsantsar fitsara da rashin kunya.
Dafe kirji ummi tayi a firgice kan ta soma girgiza hannu da kai da sauri alamar ba
ita ba ce, daidai lokacin Abba ya fito hakanan Shigowar Alaya don kamawa ummin aiki
ta sani in sun matsa ko na awanni ne ayyukan da su kan samu a gidan ba na wasa ba
bare har kwana biyu, kalaman da taji ne yasa hankalinta tsananin tashi da sauri ta
ƙarasa ta rike hannun umminta tana kallon meela da mommy tace
*Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same
shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi
09039206763*
#Vote
#comment
🖤Gureenjoh🖤
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*
*BOOK 1*
*Page 4*
"Hajiya! ummi bata saci komai naku ba, don Allah kar ku fara yi mana wannan sharri,
ba halinmu ban...." Buge mata baki da Hajiya Zeenat tayi yasa ta saurin dafe bakin
tana zub da hawaye kaman yadda ummi ma kanta ke ƙasa tana hawaye.
Faɗa suke yi ta inda suke shiga ba ta nan suke fita ba har da zunguri Abban Meelah
dae be ce komai ba yana tsaye yana nazarinsu, kansu ƙasa suna aikin zub da hawaye
na wannan tozarci da ake musu da kazafi, suna cikin wannan masifar se ga Hajiya
Fanta da ɗiyarta Zaliha suma suka shiga sahu har da aje a chaje sashensu. Meelah
tace
"ba wani sashe a nan jikinta zata ɓoye don ai bata fita ba"
Tura baki tayi harda hawaye sbd ba yadda ta iya tana kallo yayiwa su ummi alama da
hannu akan su fice, kama ummi Alaya tayi suka fita daga parlorn zuciyoyinsu baƙi
kirin, hajj Zeenat kuwa haushi sossai taji tana kallon sbd wani manufar ne Alhj
Hassan ya sa suka tafi alhali sun musu sata bata damu da gaban ƴarsu ko baƙin su ba
tace cikin faɗa
"Haba Abban Jameelah ai wannan ka basu damar sake wa gobe ne, baka da hujjar saka
su barin parlorn nan alhali ka san babu wadda zai saci sarkar nan in ba su ba in
har dae ba da wata manufar ka tseratar dasu ba.."
Wani irin kallo ya watsa mata kan ya juya har ya nufi barin sashen ya sake Juyowa
"baki da hujjar tuhumata akan abunda yake ni na saya ko yanzu zan iya sayawa mamana
Goma irin shi don haka ki daena shiga min hanci da kudundini"
Gabas da yamma ta haɗa da fuskanta da ta turbune wadda yafi yanayi da na shanu zata
soma sakin zance Hajiya Fanta ta ja hannunta suka yi ɗakinta.
Meelah ta ja hannun Zaliha tana cewa
"zo kawata mu je kiga wani guy da ya tafi da imani na a intsgram ban taɓa sanin
akwai me kyau da charisma irin shi a duniya ba"
Suna shiga ɗakin ta sa hannu bedside don ɗauko wayanta se ta sauke kan sarka da ya
ɓuya a bayan flower portal dake daure bisa bedside dinta fiddo shi tayi tana nunawa
Zaliha
"Ai ke banza ta faɗi miki adana wannan daddynki ya sake sayo miki wata"
A ta ɓangaren su Alaya haka suka jima jugum cikin damuwa da tunani da Alayah ta
gaji ta dubi ummi
"Ummi don Allah bamu da kowa a duniyan nan ne? Ummi Meyasa kika dage sede mu cigaba
da zama a wannan baƙin gida? Meyasa ba zaki bani labarinku da Abbana ba? Umm..."
Dakatar da ita tayi
"Ki adana tambayoyinki akwai lokacin da da kaina zan baki waennan amsoshi Alayah.."
Hawayen ta ta share ba tare da ta sake cewa ummi komai ba.
****
Tafawa suka yi suna dariyar su irin ta asalin Ƴan siyasa kuma waenda suka gogu da
duniyanci, daga kallo ɗaya zaka san sun jiƙu da naira iya jiƙuwa da alama hirar
tasu mai daaɗi ne...
"Ai ina gaya maka Hon Hameed chanji a tafiyar da muke gab damo ke shirin isa ga
harawa"
Dariya suka sake sakewa kan Hon Hameed chanji ya ɗan tsagaita hankalinshi ya tafi
ga wani tunani da yake damun shi a rai..
Kai Alhj Hassan ya gyaɗa duk wannan ya sani ai labarin tantirancin mukhy babu wadda
be sani ba in har dae Kano kake.
"Yanzu menene matsalar baya sana'ar ne?"
"Hmm sana'a ba karamin karbarshi yayi ba yana samu ba na wasa ba sede kuɗin a banza
yake tafiya Ƴan mata, abokai, Ƴan shaye shaye, su tatooo da ya cika jikinshi dasu
da dai sauransu, da nake shawara da wani aboki na se yake ce min ai aure na nitsar
da irin Muktar ni kuma ban cika son takura mishi ba duk abunda yake so shi nake so
nayi ta bin shi ya kawo mata ya min kunnen uwar shegu, yanzu ina tunanin samun mace
dalleliya wacce ba ze iya ƙin aurenta ba in aura mishi amma ban san wace yarinya
zan samu ba, irin yaran malaman nan haka dae"
Ranshi kal yayiwa Mukhtar mata ya isa gida, parking driver ɗin shi yayi a kofar
mashigar parlorn ƙawataccen gidan da ya tsaru ya gaji da tsaruwa, kofan parlorn ya
buɗe ya shiga sanyi da kamshin da parlorn ke yi na asalin matan shuwa ya shaka ya
lumshe ido, wannan kamshi da tsabtar na daga cikin abunda yake hana shi fushi me
tsawo da hajj binta Dukda yadda take bakanta mishi rai a kullum tana mai dashi
yaron goye.
A kan kujera ya sameta kaman kullum cikin ado da kwalliyar da bata rabo dasu sanye
da laffaya me tsadar gaske hannu da kafafunta sun sha jan kumshi gata fara sol
kaman ka taɓa jini ya fito, ɗaga idanunta tayi ta kalleshi kan ta girgiza kai cikin
hausar ta da har yanzu be zama cikakke ba tace
"Alhj ban ji kayi sallama ba"
"Me yayi zafi Alhj? Ni dae na san uban kwarai ba ze taɓa ba muktar auren ƴarshi ba
wallahi, kuma ni ban yiwa muktar baki ba a kullum adu'ata Allah ya shirye shi
sannan wallahi ku guji hakkin ƴar mutane sbd wallahi haɗa ta da muktar zalunci ne
mai girma, idan har ba ya chanza halin shi ba"
Tsaki yaja yana Miƙewa
"Babu anfanin faɗa miki Binta ki sani bukin ba ze dau lokaci ba in kin ga dama ki
fara shiri, muktar dae ɗan ki ne da kika haifa da cikin ki babu abunda ze chanza
hakan, fifikon ki na banza akan Umar yaron da be ma san kina yi ba"
Daga haka ya wuce fuuu
Da ido ta bishi a fili tace
"Allah ya shirya to"
A zuciyarta kuma tun kan ta san yarinyar tausayinta ya rufeta, muktar danta ne
kaman yadda mahaifinshi ya gama faɗa saide duk halayen muktar babu na zaɓe, ga
zafin zuciya da saurin fushi, ga shaye shaye idan ya bugu iya buguwa har ita bata
tsira daga cin mutuncinshi ze iya zuwa tsakiyar parlorn nan ya gayamata duk maganar
da ta zo bakinshi se abubuwan sun sake shi kuma ya zo yana neman yafiyarta yana
cewa shi be san yayi ba, to taya ze iya zama da mace a haka? Ƴan matanshi har gidan
nan suke zuwa neman shi mahaifinshi be taɓa ganin hakan a laifi ba se ma goyon
bayan da yake bashi, duk da sana'ar da yake sede idan be nemi kuɗi a wurin
mahaifinshi ba duk ywansu haka ze bashi ba tare da ya tambayi abinda za'a yi dasu
ba, ko kwana nawa muktar ze yi a waje mahaifinshi baze taɓa tambayar inda yaje ba
bare ya binciki me yayi tun ma be kai haka ba bare yanzu, duk wani faɗa na club
mukhy amma uban ba ze taɓa tsawatar mishi ba sede ya biya kuɗi a kashe case ɗin,
ita dake yawan yi mishi faɗa da nasiha se suka maida ita makiyiyarsu daga shi har
mahaifinshi, kullum a ganin da yake mata bata ƙaunar Mukhtar wanene ze kaunaci ɗa
duniya sama da uwa?
Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke tana girgiza kai...
***
Yau sunday ummi na chan cikin gida tana aikin abincin dare yayinda Alaya ta gama
yiwa Hajiya Zeenat da Meelah wanki ta shanya se ta nufi ɗakin su ta gyare tsab, ta
fara tattare wankinsu don zuwa ta musu ta san idan ba yau din ba ummin ce zata yi
idan ranakun makaranta suka shiga, taje ta fara kenan ta ɗauko wani zanin ummi
dagawar da zata yi se taga wani ƙulli murmushi tayi tana ayyanawa kila ɗan chanjin
asibiti ne ummi ta ƙulle a bakin zanin kaman wata tsohuwa warwarewa tayi don ta
adana mata se taga paper ne, buɗewa tayi tana mamakin wani paper ne wannan ɗin..
*Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same
shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi
09039206763*
#Vote
#comment
🖤Gureenjoh🖤
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*
*BOOK 1*
. *Page 5*
Kasa riƙe balance ummi tayi suka tafi tare zuwa kan gado, a gigice ta ɗago ta ganin
tana zub da hawaye fuskanta da alamun gigicewa ko ɗimaucewa da bata taɓa ganinta
dashi ba, cikin alamar kurame take tambayarta abinda ke faruwa, ta ma rasa da wanne
zata fara, kuka kawai take na baƙin cikin kasancewar su a wannan gida kuma ummi na
da yadda zata yi amma ta zaɓa musu wannan rayuwa da rayuwar ƴancin da ake tallata
mata.
"Alaya menene?"
Ummin tayi mata alama bayan ta ɗago ta tana dafe da kafaɗun ta.
"Ummi wai ni Abban jameela yake cewa zai yiwa aure nan kusa, ummi wlh in har hakan
ta kasance ba zan iya cigaba da rayuwa ba! Ummi zuciyata zata buga da baƙin cikin
wannan rayuwa..."
Ummi da tafi Alaya gigicewa tayi saurin sake mata Alama
"ban gane ba!"
Bayani ta mata yadda suka yi cikin kuka ta kara da
"Ummi karki ce in yi haƙuri wlh ba zan iya wannan aure ba, ba zan taɓa tafiya in
barki cikin wannan gida ba!"
Kasake ummi tayi zuciyarta na fin na Alaya bugu, maganar ya zo mata wani iri, aure?
Wani irin aure? Me Alhassan ke nufi? Bata iya tayi magana ba illa kurawa Alaya
idanu da tayi tana kuka sossai.
Daga magarib har isha sun yi shi ne kawai babu cikakken natsuwa dukkaninsu a
tsorace suke da lamarin wannan aure da Abban yayi, sanin kansu ne babu kaunar su ko
na second a zuciyar Abba to taya zasu yi tsamannin zai zaɓarwa Alayar ma miji
nagari in ma ya kama ya zaɓar mata kenan, tambayar ma itace; Meyasa ze tsallake
buduruwar yarinyar shi ya zaɓi Alaya? Me manufarsa?
Har sun yi shirin kwanciya ummi da take wani nazari ta dubi Alaya dake ganin kaman
duk wani abunda ke faruwa laifin ummin ne tunda tana da hanyar samar musu Ƴanci
amma tayi shiru, ummin na kallo Alayar ta kwanta ba tare da ta sha magungunanta ba
gashi sai zub da hawaye take har lokacin.
Miƙewa tayi ta dauko magungunan da ruwa tazo ta ɓaɓallesu ta ɗago Alayar ta mika
mata, karɓa tayi ta sha tare da sake komawa ta juyawa ummin baya, kaman yadda bacci
ne ɓarawo ya dauki Alaya haka ummi da ta raya daren bisa sallaya tana zub da
sassanyar hawaye na abubuwa masu yawa da suka faru a rayuwarta Dukda bata nadamar
ko guda sede tana jin tsoron abunda hukuncin da zata yanke na gaba ze iya kawowa..
Washegari kaman yadda suka saba haka suka kama ayyukansu da sassafe saide duk
jikkunansu a mace suke aikin babu wani kuzari, har Alaya ta kamalla breakfast ta
shirya dining zata juya kenan sai ga Jameelah da Hajiya Zeenat sun fito, ƙasa ta
duƙa cikin sanyin murya ta gaishesu babu wacce ta amsa ta miƙe ta ƙarasa ta ja wa
Hajiya Zeenat kujera ta zauna, abincin ta fara serving nasu pepper soup na kayan
ciki ne sai dankali da aka soya cikin kwai aka kuma yi mishi egg sauce da tea,
pepper soup din Jameelah ta janyo ta sanya spoon ta kai bakin ta da sauri ta furzar
tana zaro ido, a ruɗe Hajiya Zeenat ta miƙe kaman yadda Alaya ta zaro ido zuciyarta
cike da fargaba.
Alaya na isa ta zube ta cigaba da kukanta tana jin radadin na ratsa ta, da sauri
ummi ta ɗago ta tana tambayarta abunda ya faru amma bata amsa ba duk laifin ummin
take gani, sai da ummin ta jijjigata da karfi tana mata alama bakin ta na irin
ɓaɓatun maganan kurame dinnan
"Alaya ki dawo hankalinki, duk abunda kika ga na yi sbd ke ne da rayuwarki, nima ba
zan zuba ido a zalunceki a ɓata miki rayuwa da gangan ba, menene ya faru? Ki min
magana..!"
Alama take mata tana sakin wani kukan a haka ta bata labarin abunda duk ya faru,
hijabin ummi ta zare mata abunka da farar mace nan da nan jikinta ya tashi yayi
jajazir daga wuyanta har kirjinta, wani abu me ɗaci ummi ta haɗiye ta miƙe ta fice
chan ta dawo da kƙullun kunu sbd ana yiwa Abban Jameelar tazo ta shafa mata duk
wurin kunar ta zauna ta sanya ta a gaba tana kallo yayinda baccin wahala ya ɗauke
ta.
Tun daga randa ta ƙone bata kara fita daga sashen ba komai ummi ke yi Dukda damuwa
da ya mata yawa, yake kuma cin zuciyarta hakan be hana tayi musu duk aikin da suka
saba yi ba, Alaya kuwa tun ranar bata iya zuwa makaranta ba duk son ta da boko
kuwa.
Yau dae ta miƙe ta shiga cikin gidan don kamawa umminta aiki tana cikin jera abinci
taji gyaran muryan Abba da sauri ta juyo se ta kai gwiwowinta ƙasa kanta kasa
gabanta na tsananta bugu.
"Muktar ze zo yau ku gaisa, make sure baki yi abunda ze zubar min da ƙima ba,
parlorn baƙi na zaku zauna and ki tabbatar kin tsaftace kanki na rana ɗaya dae"
Yana kai nan ya wuce abun shi.
Bata iya ta miƙe daga tsugunon ba tsawon mintuna kan ta yunkura kitchen da bata
koma ba kenan tayi chan baya ta fara zirga zirga...
Na shiga uku na wai da gaske Abban Jameelah ke yi? Shikenan haka zamu kare kaman
bayi a chan lokacin jahiliyya? Babu irin nazarin da bata yi ba har da tunanin ko ta
gudu se kuma ta tuna in ta gudu umminta fa? In ma ta gudun ina zata? Bata san kowa
nata ba banda gidan nan da makaranta sai asibiti bata tunanin ta san wani wuri a
fadin birnin jihar Kano.
Har aka kira la'asar bata iya ta taɓuka komai ba banda tunani da wani irin fargaba
da ya cika mata zuciya fal, ganin lokacin Sallar na shirin fita yasa ta nufi
sashensu sukuku da ita haka tayi sallah tana nan zaune ummi ta shigo ko kan tayi
maganar yadda ta ganta ɗin taji sallamar iro me kula da shuke shuken gidan alama
tayiwa ummi na ana sallama kan ta fice, a mutunce suka gaisa ya shaida mata tana da
baƙo a sitting room na Alhaji..
Dawowa tayi tana share hawaye ta faɗawa ummi har abunda Abban Jameelah ya faɗa,
bata ce komai ba har Alaya ta juya ta fice da kayan jikinta dogon riga da hijab da
ya wuce mata gwiwa kaɗan, da idanu tayi ta bin zazzafar motar tashi kirar McLaren
Mp4-12c wacce murafanta ma ta sama ake ɗagasu Red colour mirrors ɗin baƙaken sidik
banda sheki babu abunda yake yi har ta isa kofar parlorn, ta dan jima anan tana
daidaita bugun zuciyarta da fargaba hade da tsoro da suka cika ta kan ta tura kofar
da sallama.
Ba'a amsa ba kutsa kai tayi ciki bata yi gigin dagowa ba ta ƙarasa ta tsaya a tsaye
tace ina yini? Ba tare da ta ko zauna ba.
Buɗaɗɗiyar muryarshi da ta kara zurfi da amo sbd shaye shaye ya dira bisa
kunnuwanta
"Kin ƙara mintuna ashirin da biyar daga kiranki zuwa yanzu mind you next time karki
kuma, ba'a ɓata min lokaci a banza!"
Sai a lokacin ta iya ɗaga idanu ta kalleshi tana kokarin auna kalaman da yake faɗa
mata cike da gadara da isa kaman shi ya ajiyeta, bata ce komai ba se kallonshi da
take ba laifi don kyau kam kyakyawa ne na gasken gaske duk inda kake neman namiji
wannan din da Abba ya kira da Mukhtar to ya kai, saide dressing dinshi na three
quater da armless shirt ya bayyana munanan halayenshi kaman yadda baƙin lips ɗin
shi ya nuna karara hayaƙi na aikinshi a wurin, daga kirjin shi zuwa dantsen hannun
shi na dama tatoos ne da aka zana ya zanu sossai kaman kan zaki ko damisa ne oho..
Wani irin tsawa da ya daka mata yasa ta razana tayi baya tana wara kyawawan
idanunta
"ba'a yi min shiru in ina magana am I clear?"
Bata amsa ba, hakan ya saka shi Miƙewa a harzuke ya nufeta gadan gadan, a tsorace
ta fara ja baya yana kara matsowa har ta isa jikin gini ya matso sossai ya mata
rumfa yana kare mata kallo
"young, beautiful and stubborn!" Ya faɗa yana taɓe baki
"ba laifi Dad ya iya zaɓe but kina bukatar sabbin karatuttuka a wannan lunatic
brain ɗin"
Ya faɗa yana dannan saitin brain ɗin da hannunshi kauda kanta tayi idanunta suka
cicciko, ya sanya hannu ya shafa fuskanta a firgice ta Buge hannun tare da sauke
mishi marin da bata taɓa tunanin tana da wannan karfin halin ba, kankame jikinta
tayi sbd kusancinsu tana kokarin zamewa ya fusgota tare da fusge hijab ɗin jikinta,
ƙara ta saki ya Buge mata baki da gwuiwar hannunshi har saida jini ya fita yana
furta...
"Shhhhh" idanunshi kaman garwashi da alama ma wani abun ya sha kan zuwanshi nan ɗin
"Lallai yarinya kin yi kokari, Marin Muktar abu ne da ya kamata a tafa miki, trash
like you, villager, wacce ke cike da rashin wayewa yau ke kika sa hannunki a
fuskata, fuskar da mata dubu ke marari hmmm marin nan zan fanshe su ta hanyoyi
daban daban ki rubuta ki ajiye the First one za ki tantance yanzu, sauran sai kin
zo.."
Ko kan tayi wani yunkuri ya sanya hannu ɗaya gaban rigar ta ji kake Kyaaaaat ya
farke har farin vest dinta ya bayyana, ihu ta tsala tare da saka iyakar karfinta
tana kokuwar kwace kanta sede shi ɗin namiji ne da gaske ko gezau ta kasa motsa
shi, kuka da ihu take tana neman ɗauki daga Allah...
Gaban ummi ne ke ta faduwa tun fitan Alaya ɗin ta kasa natsuwa, daga karshe sake
aikin da take yi tayi ta nufi sitting room ɗin tana kuma jin gabanta na tsananta
faduwa.
Tura kofar da tayi ya ɗan yi karar alamar Shigowar mutum ne ya saka shi dakatawa
daga abunda yayi niyya chakk, jajayen lumsassun idanunshi ya ɗago ya kalleta irin
kallon zaki yi bayanin nan kan ya ja baya yana gyara wandonshi ya juyo, ita kanta
ummin wani irin kallon banza yayi ta aika mata har ya isa daidai inda take kan ya
daga hannu yayi mata alamar ta matsa, abunda ta gani ne ya daskarar da ita,
idanunta na kan Alaya da ta zube bisa gwiwowinta tana gunjin kuka bata ankara ba
taji an tureta an wuce, bata iya riƙe balance dinta ba se ta tafi a haka ta faɗi
ƙasa sumammiya....!
*Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same
shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi
09039206763*
#Vote
#comment
🖤Gureenjoh🖤
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*
*BOOK 1*
*Page six*
A hankali ummin ke buɗe idanunta da suka yi nauyi, zuciyarta na bijiro mata da abin
da ya firgitata, da ido ta bi environmemt ɗin sai ta fahimci a asibiti take babu
tantama hawan jininta ne ya tashi. Idanunta ta kai gefen ta sai suka faɗa kan Alaya
dake dunkule cikin kujera idanunta a lumshe kaman mai bacci duk sun kumbure alamun
ba karamin kuka ta ci ba, wani irin tausayin ɗiyar tata ne ya rufe ta, lumshe idanu
ta sake yi, ta gama yanke hukuncin amincewa Alhj Hassan da bukatar shi in har dae
hakan shi zai sa ya kyale Alaya daga wannan mummunan rayuwar da yake shirin jefa
ta, ko a mafarki kai ko a labarin tatsuniya bata fata ace wannan dodo da ta gani da
idanunta yana shirin keta haddin ɗiyarta a cikin gidan ubanta ya zama mijin Alaya.
Me yasa ta kasa rike amanar Ahmad? Me yasa mutuwa ta mata yankan kauna? Ita kadai
babu yadda ta iya da Alhassan, dole abin da yake so din nan shi zata yi...
Kuka ne ya kwace mata wadda ya saka Alaya da dama ba bacci take ba tunani take akan
sabuwar ƙaddarar dake shirin riskarta tayi saurin ɗagowa da hannu take mata alamar
ta tashi? Ya jikin? Ta dena kuka haka pls.
Har malam Musa ya shigo da zumar tafiya dasu gida sbd likitan da ya fita yanzu ya
sallamesu amma kaman yadda aka umurceshi Alhj Hassan ne ya kira ya sanar wa shi
kuma ya turo malam Musa ummi bata ce komai ba ta dai bar zubar da hawayen sai azkar
da take tayi, duk su biyu bayan su ubangiji ne kadai ya san abin da suke kullawa da
warwarewa, suna sauƙa daga motar ummi ta dubi Malam Musa da yake mika mata wani
takarda ta karɓa ta buɗe...
"Idan kina da magana ki sameni yanzu a parlor na"
Duban Alaya tayi tare da mata alama akan ta tafi, da kallo Alaya ta bita saide bata
saba saɓa maganar mahaifiyarta ba haka ta wuce zuciyarta a kuntace cike da tunanin
abin da ummi ke ɓoyewa a gareta sai taji bata ma son ji, kila rashin jin Alkhairin
ta ne.
A natse ta tura kofan parlorn ta sanya kai zuciyarta cike da addu'a irin adu'ar
nan na fuskantar mummunan abu daga cikin halittar ubangiji wato
a'uzubikalimatillahi tammat min sharri ma khalaka, daga tsaye ta tsaya tana
kallonshi
"hawwa kina da kafiya da taurin kai!"
Ya mata alama yana taɓe baki.
"Me kake buƙata?"
Sai da ya dara kan yace
"A tambayi kaza hanyar rafi kuwa? Hala kin mance tun ran gini tun ran zane, ba tun
yau ba kika kwana da bitar bukatata a gare ki, da Kalma ɗaya tak zaki samar muku
Ƴanci"
"idan na amince maka na kuma yi maka duk abin da ka buƙata shine kadai zai sa ka
fasa auren da kake shirin kakabawa Ƴa ta na tozarci da rashin galihu?"
"Ko kin amince abu ne mawuyaci a fasa sbd yaro ya gani ya yaba, Marin da ta mishi
kuwa daidai yake da ta yankarwa kanta tikiti na rayuwa dashi har abada, abu ɗaya na
sani ko da kin amince nayi yadda nayi muka bar maganar auren nan to ɗiyar Ahmad
bazata kara minti guda cikin gidana ba! Daga lafiyarta, cin ta, shan ta da
karatunta duk sun yanke daga kaina babu abunda zan kara iya yi mata kuma a rayuwa
sbd Ahmad be cancanci abubuwan da nake yi mata a yanzu ba.."
"Me Ahmad yayi maka a rayuwa banda hallaci? Kai butulu ne, kai azzalumi ne Hassan,
ba zan taɓa bari ka samu abunda kake so a rayuwa ba zan barka da SON ZUCIYARKA
cikin AL'AJAB NA SO kana ji kana gani ba zaka taɓa samun biyan bukatar ka ba in har
dae akan SO ne ka aikata duk abunda ka aikata, Allah yana gani kuma ya san komai
idan kaga Fatima ta auri wannan mutumi da ka kawo to haka yake rubutacce ne tun fil
azal, ba zan iya chanza mata kaddara ba, addu'a kuma shine maganin komai..."
Tana kai nan ta share hawayen dake gangara mata ta juya ta fice.
Hajj Zeenat dake tsaye tana kallonshi yadda gabaɗaya yanayin shi ya sauya Ranshi ya
kai kololuwa wurin ɓaci ta san ba komai bane sai danganta Ahmad dashi da Hawwa tayi
har tana ikirarin cewa Ahmad ya fishi daraja da komai a idanunta, taɓe baki tayi
ganin yadda ya wuce har yana buga kofa tace a fili
"Kanku aje ji wai mahaukaci ya faɗa rijiya yace kanku aje ji ni wankana nake"
Ko da ummi ta dawo bata iya tayiwa Alaya magana ba, kaman Alaya ta shiga ran ummi
ta yagi fallen takarda daga takardar ta sbd so take ummin ta fahimci maganar daga
zuciyarta yake rubutu tayi me ɗan tsawo kan ta ajiye mata ta tashi ta fice daga
ɗakin.
"Hawayen uwa abu ne me zafi da daraja a idanun ƴaƴa, ummi karki sake zubar da
hawayenki akan wannan matsalar kin manta ke kika ce min Aljanna ana kewaye ta ne da
abunda rai baya so yayinda ake kewaye wuta da abunda zuciya take so? Ko a makaranta
an koyar dani cewa a cikin suratul baqarah Allah yana cewa zai kasance kuna matukar
son abu sai ya kasance sharri a gare ku yayinda zai zamana kuna matukar ƙin abu sai
ya zama shine alkhairinku, Allah shine mafi sani amma da na zurfafa tunani sai na
ji ina da bukatar wannan aure watakila shi zai yi sanadin Chanza rayuwarmu, ba zan
kara tambayar ki abin da baki so na sani ba na san in lokaci yayi zan sani, Don
Allah karki sake yunkurin dakatar da Abban Jameelah akan auren nan idan har cutarwa
yake nufinki dashi!"
gabaɗaya hawayen Ummi ya gama jike takardar, kowace uwa bazata so jefa yarta cikin
rayuwar da tafi wadda suke ciki ba amma ta san Hassan shu'umi ne zai iya anfani da
wannan dama ya jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya kenan ko ta amince da kudurinshi sai
ya san hanyar da ya bi ya muzgunawa Alaya saboda ita ɗin ɗiyar Ahmad ce.
Haka suka kwana cikin wannan damuwa amma Alhamdulillah da yake sun fawallawa Allah
sai suka tashi wasai da safe kaman basu da wata damuwa ayyukansu suka kama kaman
yadda suka saba...
****
Kishingide yake hannunshi rike da shisha Pen yana zuƙa sa'i da lokaci, ɗayar hannun
nashi kuwa a kumatunshi daidai inda ta mareshi in ya shafa sai ya saki murmushi
yana kallon fuskar yarinyar, Red eyes ɗin shi suka sake rinewa yana wassafa yanayin
ƙirar jikinta yadda in tayi motsi komai nata yake girgiza, Allah ya zuba ƙira gata
yarinya ƙarama, wannan in har ya same ta lallai yayi zarra cikin abokanshi, kaman
yadda yake piya-piya a duk inda ya shiga baya jituwa da kananun kwari sai masu
kumbar susa haka a aure ma, dole ne ya gayyaci duk wadda ya san zai iya gayyata ya
nuna musu ya ƙere kowa...
"bala'i! This gurl is morethan beautiful.."
Gani yayi ba zai iya jira a dau lokaci ba hakan ya sashi Miƙewa daga kan sofa na
rantsatsiyar club ɗin as usual sanye da kananun kaya three quater da shirt da bashi
da maraba da vest, fitowa yayi cikin takunshi na nuna isa da jiji da kai wadda ze
tabbatar maka da lallai shi wani ne ya isa ga motar shi ya shige tare da bata wuta
yayi gida.
Kaman yadda ya fita daga club ɗin haka ya shiga cikin parlorn sai de idanunshi da
suka sauka kan mahaifiyarsu ne yasa ya ɗan seta kanshi..
"Sannu da gida Maami"
Girgiza kai tayi tana kare mishi kallo ba tare da ta amsa ba, ze wuce tace
"Mukhtar"
Juyowa yayi ya dawo ya samu kujera ya zauna nesa da ita
"wani magana ne nake ji daga bakin mahaifinka?"
"Wai zancen aure? Na je na ga yarinya kuma na yaba ni yanzu ma so nake ko gobe ne
tunda juma'a ne a ɗaura kawai"
"ban gane a ɗaura gobe ba! Ƴar tsana ce? Ba ma maganan nan ba me kayiwa ƴar mutane
da har zata mareka a cikin gidansu?"
***
A natse ta sanya kafafunta ƙasa ta sauƙa daga cikin motar bayan driver ya buɗe mata
kofar, karewa gidan kallo take tana nazari, gidan dae ya fi ƙarfin irin wannan aure
da ake shirin aiwatarwa a gobe, tafiya take tana ɗan kalle kalle ko zata hadu da
wani ko wata ta nemi iso, chan ta hango wata farar kyakyawar yarinya tana tafiya ne
kawai amma daga dukkan alamu hankalinta yayi nisan kiwo, idan ta kula da kyau ma
kaman yarinyar na sa yatsa sa'i sa'i tana dauke kwallah, sam yarinyar bata kula ba
har seda tayi karo da ita kan tayi mugun komawa baya a firgice idanunta da suke
fari tas a waje gabaɗaya.
Alaya kam ita ta zata irin cikin kawayen hajj Zeenat ne yanzu su juye abu su ci
musu mutunci, a tsorace ta zube ƙasa tana baiwa hajiyar da kai tsaye ta saka ta a
top class hajiyoyi masu naira da isa haƙuri, bata taɓa ganin irin ta cikin ƙawayen
hajj Zeenat ba don duk yadda zata misalta kyau da haiba irin na wannan mata me cike
da annuri ba zai misaltu ba.
Cikin ƙasaita Hajiya ta fito Dukda ganin wannan gansamemiyar hajiyar ta san ba irin
wacce za'a dagawa kai bane hakan be sa ta saita kanta ba ta samu wuri ta zauna a
hakimce tana lura da kyau da kayan alatun dake jikin matar.
"Sannu da zuwa"
"yauwa Hajiya, kece mahaifiyar yarinyar da Abban muktar ya nemarwa aure?"
Daidai Alayah ta fito don tambayar hajiyar abinda ta ce za'a ƙara bayan na time
table yau.
Idanu duka ta fitar kaman an danganta ta da wani mummunan abu tace
"Allah ya tsare ni da haihuwar mugun iri, kin ganta chan sai ta dangana ki da
kurmar uwarta tunda dae kun ji kun gani, a sauƙa lafiya in kin tashi!"
Tana kai nan ta fice daga parlorn babu ko waiwaye, da farko jin irin gidan da za'a
aurar da Alayah ta so ya haɗasu da jamila ne saide jin irin hallayyar yaron tayi
tirrr da aurenshi, don a ganinta bashi da wani anfani, ko da uban ya faɗi ya mutu
ko uwar dukiyar da zai gada bazasu je ko ina ba zasu ƙare a shaye shaye da bin
mata, bata Gaza ba wurin tabbatarwa da Abban jameelar cewa in har dae suna da wani
ɗan natsatse sai yayi kokari wurin ganin ya haɗa jamila da shi, be dae tanka ba
amma ta san zai yi nazari akan hakan.
A chan parlor kuwa, idanu mami ta zubawa Alayah da kanta ke ƙasa cike da kunyar
matar sai a lokacin ma ta fahimci kamanni dake tsakaninsu da muktar din, amma me ya
kawota?
*Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same
shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi
09039206763*
#Vote
#comment
🖤Gureenjoh🖤
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*
*BOOK 1*
*Page seven*
Cikin tsananin tausayi da mamaki take kallon sashen nasu sai de tayi matukar kokari
wurin boye yanayinta har ta kai zaune tana ɗan kallon kofan ɗakin da Alaya ta
shiga, bata fi minti ɗaya ba sai gata da matar da bata bambance dayan biyu
mahaifiyarta ce sbd kamanni Dukda Alaya ta zarta ta kyau nesa ba kusa ba.
RANAR JUMA'A
Tunda gari ya waye gaban ummi ke aikin faɗuwa sbd Maami ta faɗa mata a yau ne suka
yanke za'a ɗaura auren, ta kwana kan sallaya ta kwana tana kaiwa Allah kukanta, da
safen kuwa lokaci lokaci ta kan share hawaye, ba irin tunanin da bata yi ba idan
har suka tsallake suka bar gidan nan shikenan tayi sallama da Ahmad da komai nashi,
idan suka bar gidan saide su koma kaman sauran Abzinawa masu bara a titunan
Nigeria, bata da wadda zata komawa a yanzu bata da kowa da zai iya rungumarta a
wannan yanayi.
Aiki take saide lokaci lokaci ta kan ɗaga idanu ta kalli Alaya hawaye na zuba a
idanunta, daidai sadda Abban Jameelah ya shigo da karfi ya jefa mata ledar
hannunshi wadda yayi sanadiyar watsewar alawa da goro dake ciki, a firgice Alaya ta
miƙe tsaye tana kallonsu yayinda ummi ta runtse idanunta daidai lokacin da Abban ke
cewa Alaya
"Ga Alawar aurenki an ɗaura yau kuma ki shirya da dare zaki bar min gida, nayi
matukar jinjinawa kokarin da nayi akan ki alhalin ke ɗin ɗiyar wadda ban taɓa so
bane a rayuwata, ke ɗin ɗiya ce da mahaifinki bai taɓa ƙaunata ba, duk wani dama da
ya ga zan samu ya kan yi hanzarin sha min gaba ya karɓe hatta kaunar iyayena bai
barni da shi ba! Ki sani daga sadda kika fita daga gidan nan ko da sunan ziyara
bana kaunar sake ganinki cikinta bare ki kashe aure ki dawo min, in kin fita duk
abin da zai same ki ya kare a chan don Wallahi kika shigo min gida duk ya faru dake
kiyi kuka da kanki"
Razananniyar kukan da take ta yanke daga karshe tana kallonshi irin kallon da bata
taɓa tsayuwa tayi mishi ba, kalamanshi ba abunda zata iya aiwatarwa ba ne taya yana
tunanin zata tafi ta ƙi juya baya alhali ta san ta bar mahaifiyarta cikin wannan
gida?
"Alhaji mahaifiyata fa? Da kake wannan magana taya zan rayu cikin kwanciyar hankali
in kasa waiwayen gidan nan alhali ka san duniyata na cikinta?"
Zubewa tayi akan tile ɗin kitchen din tare da ɗaura hannu a kai tana me sakin sabon
kuka, da sauri ummi tazo ta ɗaga ta tare da sanya ta jikinta tana jin yadda jikinta
ke ɗaukan rawa kuka take kaman ranta zai fita, bata san me tayiwa wannan rayuwa ba,
shin ummi bazata faɗa mata abin da mahaifinta yayi mai zafi haka ba?
Da kyar ummi ta samu hankalinta ya ɗan kwanta Dukda bata bar zubar kwallar ba,
idanunta gabaɗaya sun sauya haka numfashinta da zafi zafi yake fita, wani mumman
zazzabi da ciwon kirji ya kwantar da ita haka ummi ta saka ta a gaba tana zub da
hawaye babu mai taimako, Dukda ta sha duk magungunanta saide hakan be kwantar da
ciwon da ya fara barazanar ganin karshenta ba, addu'a ummi ta dinga yi har Allah
yasa bacci ya ɗauketa na wahala.
Haka ta koma cikin gidan ta ƙarasa aikin da suka bari ta dawo ta zauna jugum tana
tunanin rayuwa, Dukda ta kasance marar gata irin Alaya saide aurenta bai zo a haka
ba, aurenta da rufin asiri da kuma taron mutane aka yi shi, sallah ne kawai ke
dagata har dab magarib kan Alaya ta farka, da taimakon Ummin tayi wanka ta sake
shan magunguna abinci kam ya kasa shiga cikinta, a kwance kan cinyar ummin ta
lumshe idanu bayan ta idar da sallolin da aka biyo ta ta fara jin Shigowar motoci
da ƴar hayaniya kaɗan na mutane.
Bata motsa ba har aka yi musu sallama, da gangan ta ƙi amsawa kila in bata amsa ba
su juya su koma inda suka fito a yau me rabata da ummi kilan sai mutuwa bare in ta
tuna irin furucin Abban Jameelah a kanta, Shigowar Maami ne ya sa Ummi sakin ɗan
murmushi bayanta mata ne akallah zasu yi ashirin.
Danginta ne kadan sai dangin mijin da suke ta kananun maganganu na mamakin zuwanta
ɗaukar amarya alhali ɗan ta ne na fari kuma kowa ya san rashin jituwarsu saide tayi
kunnen uwar shegu dasu kaman bata san suna yi ba wai an tsikari kakkaura, a hankali
da taimakon ummi Alaya ta samu ta zauna tana zub da hawaye ta gaida Maami, cikin
kulawa ta amsa kan tace
"Binti ya baki shirya ba?"
Murmushi me ciwo tayi ina wani kayan shiryawan mutanen gidan kaman basu san da
zaman su ba bare su yi tunanin kyautata mata a yau dai ɗaya.
"Maami bani da lafiya ba zan iya tafiya ba, ba zan iya tafiya in bar ummi a wannan
gida ba Maami don Allah ki ce ya barni ban shirya aure yanzu ba, don Allah karki
rabani da ummi wallahi zan iya mutuwa"
Tayi maganan cikin sanyinta da kuma alamar roƙo da sallammarwa rayuwar gabaɗaya.
Da kyar Maami ta iya mayar da hawayenta tana karbar farin takardar da ummi ta miƙo
mata
"ƴata na haifeta da ciwon zuciya! Don Allah ki kula min da ita da lafiyarta, ki
riƙe min amanarta, ban san ko zamu sake haɗuwa nan kusa ba amma don Allah ina roƙon
ki alfarma guda ɗaya a matsayinki na uwa kema, ki yi min kokari kan karatunta idan
kika min wannan alfarma zan kasance me saka miki da addu'ar rahama da jin kan
ubangiji har illa ma sha Allah..."
Kasa rike hawayenta tayi ganin yadda Alaya ta koma jikin ummin ta rike hannunta gam
tana kuka sossai, Aure yakin mata hakane amma wannan kukan na Alaya ba na auren
bane kawai harda na taradaddadin yadda zata rabu da mahaifiyarta alhali an gindaya
mata sharudar sake ganinta gashi ummi ba fita take ba, matan wurin dangin mijin
Maami sai kananun maganganu suke wasu na taɓe baki saɓanin dangin Maami da tausayi
da kuma jin kai aka raine su Dukda iyayensu suma masu arzikin ne sossai da sossai.
Duk yadda Maami ta rarrashi Alaya ta kasa samun galaba a kanta, yadda ta rike ummi
seda kowa yayi mamaki duk yadda akyi ta sake ta ta ƙi banda kuka babu abunda take,
ummin ma sai hawaye take da kyar da sudin Goshi aka raba su ummi tayi saurin yin
daki aka fita da Alaya a yadda take.
Maami ta kasa yin shiru kaman yadda tayi niyya har a sadata da gidan ta ta kalli
drivern tace
"Ghali juya motar nan mu tafi gidana"
"Aisha sa hannu kiji jikin yarinyar nan, ciwon zuciya ke gareta in muka kaita
Mukhtar da haukashi ya kashe wannan yarinya me zan cewa mahaifiyarta? Bana tunanin
an yiwa waennan bayin Allah adalci wannan zalunci ne wallahi"
Ta karashe tana share hawayen fuskanta tana kuma sake rungume Alaya da har lokacin
kuka take sossai.
Duk wasu kananun maganganu da aka yi tayi bata kula kowa ba kuma sun santa babu
wadda ya fuskance ta yace komai har ta sada Alaya da ɗakin baccin ta ta kuma
sallamesu akan sai ta shirya amaryar zata kaita da kanta.
Bayan watsewar kowa ta koma ɗakin inda ta barta nan ta sameta dunkule bisa
tsararriyar gadon na Maami, a natse Maami ta ƙarasa ta ɗago ta
"Fatima.. Don Allah ki daena wannan kuka haka, kin san condition naki Its not good
for your health kin ji?"
Maamin ta faɗa tana share mata hawaye wasu sabbin na zuba tace
"Maami hankalina ba zai taɓa kwanciya ba, ba zan taɓa farin ciki ba ba kuma zan
taɓa daena zubar da hawaye ba matukar mahaifiyata na wanchan baƙin gidan, Maami
zasu kashe min ita wallahi babu imani a zuƙatan su ko na second guda ya zanyi? Wani
mataki zan bi in iya taimakonta a wannan rayuwa da na tsinci kaina? Wayyo Allah na
na shiga uku!"
"Baki shiga uku ba ɗiyata, umminki bazata mutu ba, abunda nake so dake shine ki
fara ceton kanki da lafiyarki kan kiyi tunanin hanyar ceton umminki, babu ta yadda
zaki iya yi mata komai idan har kika faɗa cikin wani hali, Fatima ina en uwanku? Ko
na mahaifiyarki ko naki? Wani irin aiki ne wannan da babu encin kai a ciki?"
"A yadda kika gan mu haka nima na tashi na same mu cikin wannan hali, Ummi bata
magana alhali tayi magana a baya, ummi bata da dangi kaman yadda ta shaida min
mahaifi na ma bashi da kowa, da ciwon zuciya aka haife ni me naci da ciwon gaske na
tashi cikin tsangwama, kyara da mugunta iri iri, ummi bata taɓa bani labarin wani
rayuwa nata na baya ko na mahaifi na ba, abunda dae kawai na fahimta shine me gidan
na mugun jin zafina da tsana ta sbd wani abu chan da ya hadasu da mahaifi na kaman
yadda yake da mugun nufi akan mahaifiyata, matar gidan ta tsani mahaifiyata fiye da
kowa a duniya sbd laifin da har yau ban san menene shi ba, muna rayuwa akan wani
baƙin siradi a cikin gidan yanzu ya min iyaka da gidanshi alhali na san kashe ummi
na zasu yi da bauta wadda basu taɓa godiya akai ba, ummi karfinta ba kaman da ba
Maami abubuwan zasu mata yawa, babu ta yadda zan iya ji daga gareta bare in san
halin da take ciki, Maami taɓa zuciyata kiji ji nake kaman ze fita daga kirjina sbd
azabar bugu da ciwo..."
Hawaye Maami ta share tana shirin magana aka yi knocking a take ta bada izinin
shigowa family doc din su ne da suka yi magana kan Shigowarta ta kuma bada umarni a
chan kasa akan yana zuwa a mishi iso har ciki.
Allurai ya haɗa yayi mata a take ta fara lumshe idanu kan wani baccin wahala ya
sake daukar ta.
"Hajiya ya kamata a kaita asibiti sbd yanayinta yana nuna tana wani stage me girma
na ciwon nata kuma in tana sa damuwa a rai hakan ka iya kara shi fiye da yadda ya
kamata ya tafi"
"za'a yi yadda kace doc, in ta ɗan yi kwari zan nemi appointment ko a waje ne sai
muje in shaa Allah"
Godiya yayi kan ya fice.
Miƙewa tayi ta fito daidai lokacin da muktar ke shirin tura kofan ɗakin nata, hade
rai tayi tana kare mishi kallo
"lafiya?"
"Ina fa lafiya Maami Meyasa kika hana a kai min matata chan gida aka kawota nan?
Akan me?"
"Toh Ubana ka shakeni sai kaji amsa, ɓace min a kofar daki tun muna shaida juna"
Ashar yake shirin wawurowa tayi hanzarin kai hannu ta kuwa samu bakin ta Buge da
karfinta, ni dae baya na matsa don na ga kokarin Maami chan fa sama take kallon
muktar sbd tsawo da kuma murdewarshi don yana ɗaga karfe ba na wasa ba kuma shi ɗin
dan dambe ne mafadacin gaske ne amma Maami ko a gyelenta yana shirin mata rashin
kunya zata kai hannu, tana kuma saurin kwaɓarshi ne sbd gudun zunubin da ya ke
tarawa kanshi yaji da iya na abubuwan da yake yi mana kar ya hada da fushin Allah
akan taɓa iyaye iyayen ma uwa for that matter...
Hanyar da ta nuna mishi take kuma kallonshi cikin fushi ya bi kaman zai tashi sama
yana sauka yayi ɓangaren mahaifinshi da hanzari ya san shi kam ya isa da ita kuma
zai kwatar mishi yanci wannan ai ba yi ba bane haka kawai yadda yaci burin wannan
dare ta kama ta lalata mishi wlh ba'a isa ba, saide duk abunda ze faru ya faru har
yana haki ya fara mayarwa Dad ɗin su yadda aka yi.
"Wani lokaci Binta na abunda be dace ba wallahi ta bugeka akan matar da take
mallakinka? Ai yanzu ko iyayen yarinyar ka fisu daraja a gaban Allah bare ita
bintan, to baze yiwu ba sam, bari naje naji me take nufi? Don a saka ta a daki a
kulle aka yi auren? Ina itace ta nuna bata son auren kuma yanzu don bakin ciki tasa
ƴa a gaba ta kulle ta hana ka ita? Ina zuwa ko kuma wuce muje kawai.."
Haka ya tasa ɗan a gaba suka yi ɓangaren Maamin.
(hmmm wallahi maza mu ji tsoron Allah mu sani 'ya'yayen nan kaman amana suke a
hannun mu, su ɗin kiwo ne da Allah ya bamu kuma ze tambayemu akai a ranar gobe, ba
ina magana bane akan duka maza saide ina magana ne akan mazan da basu taimakawa uwa
wurin tarbiyartar da yaro, iyaye mazan da suke wofintar da duk wani kokarin uwa
akan ganin yaro ya zama nagari, iyaye mazan da duk abunda uwa zata yiwa yaro basu
ganinshi as kauna sai mugunta alhali duk duniya babu wadda ya kaita son wannan
yaro, iyaye mazan da suke gurbatawa yaransu tunani suke nuna musu babu kaunarsu a
rayukan iyayensu mata alhali ba hakan bane, iyaye mazan da basa taimakawa uwa wurin
tarbiyartar da yara. Wallahi mu gyara mu saka idanu akan ƴaƴanmu ko zamu samu
rayuwarsu ta inganta... Single mothers Allah ya saka muku da alkhairi).
*Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same
shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi
09039206763*
#Vote
#comment
🖤Gureenjoh🖤
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*
*BOOK 1
*Page Eight*
"Alhj for goodness sake kar ka sa na fara yi maka musu a gaban yarinyar da yau ne
ta soma shiga cikin mu, yarinyar nan bata da lafiya kuma ciwon zuciya ke gareta
idan ta mutu a yau wallahi Mukhtar bashi da asara tunda ba darajar ta ya sani ba,
ni ban hana a kai mishi matarshi sbd jin daaɗi ba idan ta samu sauƙi da kaina zan
sadata da ɗakinta"
Maami ta faɗi hakan idanunta akan Alhj da ta janye shi zuwa ɗaya ɗakinta na saman.
Dukda shi be wani ji tausayin yarinyar ba sede ya amince tunda bata da lafiya ne
kuma ciwon irin ciwon da akan rasa mutum farar ɗaya ne don hakan yasa dole yayi
shiru ya fito ya janyo hannun muktar suka yi ƙasa yana faɗa mishi situation ɗin
cikin lallami kaman shine uban shi kuma Alhj ɗan, tana tsaye tana jin muktar da be
gamsu ba yana alaƙanta hakan da son ranta ne in yayi ra'ayi sai ya kwana da mata
sama da biyar a daren kuma ba abunda zai faru akan banzar talaka ana ƙona mishi
rai.
Duk da zafin kalaman da Maami taji hakan be sa ta barshi ya kai zuciyarta ba adu'ar
shiriya ta mishi kan ta nufi ɗakinta, har asuba bata yi wani baccin kirki ba Sbd
Alaya, cikin ikon Allah kuma da kanta ta tashi kiran farko tayo alwala ta zo ta
fara nafila don ba'a binta sallah, da murmushi Maami ta shiga bayi tana godiya ga
Allah, bayan sun yi sallah komawa Alaya tayi ta lafe sbd magungunanta da basa
barinta ido biyu cikin sauƙi sam bata san ma fitan Maami ba, ba ita ta farka ba se
11 na safe.
Wanka tayi ta sake mayar da kayanta ta zo ta zauna daga bakin gadon zuciyarta fal
tunanin halin da umminta ke ciki lokaci lokaci ta kan share hawaye ta san ummi na
chan aiki sun mata yawa ga jama'ar gidan sam basu san imani ba, Shigowar Maami ne
yasa ta suluɓe ƙasa tana cewa
"Ina kwana Maami?"
"Lafiya klau bintie ya jikin dae?"
"Bana jin komai maami".
Karasawa Maami tayi ta kama hannunta ta miƙar da ita tsaye tace
"kinga Ɗiyata ki daena wannan nuku nukun ki saki jikinki ki ɗauke ni tamkar umminki
kinji?"
Kai Alaya ta gyaɗa, Maami ta janye ta akan suje su yi breakfast suna tafiya tana
kara nunnuna mata gidan tana sake jadadda mata ta saki jikinta nan ɗin kamar
gidansu ne.
Breakfast me rai da motsi Maami ta zuba mata itama ta zuba kaɗan sbd ta baiwa
Alayar kwarin gwuiwar ci, saide inaa kaɗan taci Dukda daaɗin shi sbd tunanin ummi
da yayi mata yawa ganin abincin kadai yasa ta fara tambayar kanta ko ummin ta ci?
Yanzu kila tana kitchen tana wahalar dahuwar rana..
Da hanzari Alaya ta ɗaga kai tana kallonshi mahaifiyarshi yake magana da ita cikin
kafin harshe da rashin tauna magana? Ya subhallah lallai akwai aiki me girma a
gabanta innalillahi ta shiga nanatawa, Maami da ta jima tana kallonshi ta girgiza
kai...
"Kaje gidan naka ka gyara mata sashe allura ban amince ka saka ba, za'a kawo mata
kaya saboda haka karka kuskura ko da wasa ka sake yi mata gori, kai kuma dole ne ka
bada kuɗi enough a yi mata lefe"
A wurin ya ɗaga waya yayi call ya bada umarnin gidan shi na jambulo a fitar da
kayan part ɗaya da tsantsar mamaki Alaya ke kallonshi kallon dani kike zancen yayi
mata kan yayi kwafa yayiwa Maami transfer ɗin kudi masu yawa, ta taɓe baki tace
"duk sadda na shiryata zaka ganta, bintie tashi mu tafi"
Kunkumi yayi tayi na wlh duk abunda Maami ke mishi akan yarinyar ze rama..
Da yammacin ranar Maami ta ja ta suka tafi kasuwa sayayya me tarin yawa suka yi,
kasuwanni har uku suka je bata bar komai ba tsab ta haɗa mata lefenta kan ta saya
mata wasu ready mades da kuma egyptian abayas da zata ke anfani dasu kan a yi mata
dinki, daga nan suka tsaya wurin telan Maamin ta bada dinkunanta atamphopi masu
tsadar gaske da kyau har goma sha biyar, se lesuna guda goma da shadda irin ta mata
duk ta zaɓi irin zubin da take so guda biyar, tace sauran zata ɗinka a hankali.
Lokaci lokaci Alaya ke kallon Maami tana yaba irin kirkinta ashe akwai masu irin
wannan halin karamcin a masu kuɗi da suka saura a duniya? Lallai Maami mutuniyar
kwarai ce Adu'a tayi ta mata a sadda suka tsaya shagon wayoyi ta zaɓa mata IPhone
Xs max sai ta sayi wani tecno madaidaici take ce mata
"gobe da kaina in shaa Allah zan kaiwa Umminki wannan sai ku dinga exchanging
messages ko hankalinki ze kwanta"
Adu'ar gamawa da duniya lafiya tayi ta mata da cikan burukanta na alkhairi.
A gajiye tilis suka dawo duk kayan da ma'aikatan gidan suka kwaso ɗakin Maamin suka
zube su yayinda duk suka yi alwala suka gabatar da magarib, suka dan yi karatu a
tare sai bayan isha suka sauka dining.
Alhaji hammad da Mukhtar na zaune suna cin abinci har ƙasa Alaya ta duƙa ta gaishe
shi ya amsa ba yabo ba fallasa, ta ja kujera ta zauna tana jin idanun muktar a
kanta, ita tayi serving Maami ta saka kaɗan zata juya Maami tace
"Ah ina zaki daughter? Zauna nan ni fa har na gaji da faɗamiki yanzu duk daya muke
we are family already"
Zama tayi a kunyace ta soma ci duk ɗagowar da zata yi se ta haɗu da firgitattun Red
eyes ɗin shi yana aika mata wani kallo, lokaci lokaci Maami kan yi magana da Alhj
amma shi baya sa musu baki.
Bayan sun tashi sama Alaya ta koma sbd gujewa irin kallon da yake mata, wayoyin su
da ummi ta sa a chargy cikin murna take Allah Allah gobe yayi ko zata samu taji
lafiyar ummin tata, a nan ta zauna gadinsu har Maami ta same ta ta ɗan zolaye ta
kunya ya sakata Miƙewa taje ta fara shirin kwanciya bata yi ko mintuna biyar da
kwanciya ba bacci me daaɗi ya ɗauke ta gabaɗaya jinta take cikin wani sabon rayuwa,
sai yanzu take jin ta samu Ƴanci kamar kowa matsala ɗaya in ta tuna yake ɗaga mata
hankali shine auren muktar dake kanta, da irin zaman da zasu yi sannan babban
abunda ke damunta yadda baya baiwa mahaifiyarshi daraja, taya yake tunanin ganin
haske a al'amuranshi ta lura babu wadda ya raina irin Maami, uwa tagari irin wannan
Allah ya jarabceta da samun ɗa irin Muktar kuma kaman bata da wasu da akwai da kila
ace zakka ya fita, saboda irin kyautatawar Maami garesu taji a ranta zata iya zama
da muktar da zuciya ɗaya kila ta sauya shi zuwa mutumin kirki...da waennan
tunannuka bacci yayi awon gaba da ita.
Kaman yadda Maami tayi alkawari Washegari ta aika aka kaiwa Ummi wayar, Alaya dake
ta kimtata lokaci a jikinta taji wayar ta isa hannun ummi da sauri ta rubuta text
message sai ko ga reply na ummi tayi ta murna barin ma da ummin tace mata lafiyarta
ƙalau kuma bata wani aikin sossai don an kawo sabbin ma'aikata girki kawai take
musu, sai sannan hankalin Alaya ya kwanta ta miƙe kafa a gidan Maami ta ma manta da
zancen aure in ba ta ga muktar ba, banda gaisuwa babu abunda yake hada su wani
lokacin ma ko tayi niyyar sauƙa in taji muryarshi sai ta koma, sai ta tabbatar ya
tafi ta fito.
Satin ta biyu Maami ta kaita wani school me kyau fiye ma da ainihin school dinta
aka mata registration ko da aka zo interview babu questions da bata amsa ba har
Maami seda ta burgeta sbd akwai kwazo da tarin ilimi akan yarinyar, class ɗin ta
aka barta bayan an bata uniform a makarantar Maami ta barta akan driver ze zo ya
ɗauke ta in an tashi.
Sossai take jin daaɗin makarantar sbd babu bullies ɗin ta su Meelah da kawayenta
kuma kowa a makarantar harkar gabanshi kawai yake, yau juma'a da misalin karfe sha
biyu na rana drivern da ya zama nata yayi parking kofar makarantar da ɗan hanzarin
ta tazo ta buɗe ta shiga da sallama suka gaisa a mutunce kan suka kamo hanyar gida,
a daidai parking lots yayi parking ta sauƙa tana mishi godiya tare da fara takawa
don isa cikin gidan, spot car dake parke a tsakar gidan Red Color BMW a tunaninta
ma ba kowa don bata ji karar injin motar ba se kawai gani tayi kofa ya buɗu, ko
bata kai idanunta zuwa ga fuskar ba daga kafar ta riga ta shaida waye ne.....
"Ke!"
Ya faɗa a kausashe chak ta tsaya gabanta na faɗuwa tana da ilimi kuma ko makaho ya
shafa ze san cewa muktar baya cikin cikakken hankalinshi.
"Don kaza kazarki ba dake nake ba?"
Ya antayo zagin yana kara kakkafeta da jajayen idanunshi, idanunta dake rawa ta
sauke bisa tattos ɗin jikinshi Farin fatar shi tas duk ya lalata kaman akwai wani
sabo ma daga wuyanshi....
"Na'am"
Ta faɗa tana ɗan matsowa kaɗan a kuma tsorace
"na biya sadakinki don ki zama min hoto ne? Ke wallahi tsohuwar chan tana jaza miki
don sai na tabbatar na ladabtar dake bisa wannan biye mata da kike, sai kin zamto
min kariya babu maganan wadda zaki iya ji idan ba na uban gidanki ba, wuce ki shiga
mota mu tafi!" Ya daka mata tsawa
Jikinta na tsuma tana rawar leɓe tace
"Maami bata ce in tafi ba, and plz ka daure ka daena faɗin munanan kalamai akan
Maami ko ba komai ta ɗauki cikinka na wata tara chur ta kuma yi nak....".
"Shut up bloody fool, ke har kin isa ki gayamin abunda zan yi? U r like a servant
to me, na aureki ne kawai don kyaun surarki ku kuma don kwadayi irin na talaka kun
ga kuɗi kuka amince, for ur own information ko Asawanyarki bata kaini daraja ba don
haka ke baiwa tace na fanshe ki kuma da kuɗi wuce mu tafi tun muna shaida juna.."
Baya baya ta fara ganin yana nufo ta, kan yayi wani yunkuri ta runtumi na kare,
taku biyu yayi ya.....
*Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same
shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi
09039206763*
#Vote
#comment
🖤Gureenjoh🖤
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*
*BOOK 1*
*Page Nine*
Haki take saki tana juya bayanta ganin baya binta yasa ta dafe kirjinta, in wannan
ɗan daban ya riƙe ta ai kashinta ya bushe, seda ta daidaita kanta kan ta kutsa
cikin parlorn Maami ta gani zaune idanunta da hawaye, da sauri ta isa ta duƙa a
gabanta kaman zata saki kuka aka ce zuciya tana son me kyautata mata jin matar take
kaman Ummi tace
"Maami me ya faru kike zub da hawaye?"
Shiru Maami tayi, babu me fahimtar halin da take ciki se uwar da Allah ya jarrabe
ta da ɗa irin Mukhtar, ace kana ji kana gani yaro ya nemi gagararka? Allah kaɗai ya
san me ya je ya sha ya zo yake mata rashin kunya akan matarshi, duk zafinta akan
muktar ne tana da sanyin hali da tausayi shima kuma da farko ta bi dashi da lallami
da nasiha saide abun yaci tura, ganin hakan mahaifinshi ke mishi yasa ita ta karɓi
ragamar zama uwa da uban saide duk a banza man kare, zafin dake kirjinta ya wuce
misali bata fata ta mutu ba tare da ta ga chanzawar Mukhtar ba, tana mishi tsoron
fushin ubangiji tana kwaɗaita mishi rahamarsa...
"Maaami"
Alaya ta kira sunan hawaye na cika idanunta.
"Babu komai ɗiyata, je ki cire uniform ɗinki kizo ki ci abinci"
Gudun musu da Maamin yasa ta miƙe ta tabbatar be wuce muktar bane matsalar Maami,
saƙe-saƙe kawai take har ta watsa ruwa ta sauko ta ci abinci bata samu Maami ba
kila tayi wurin Alhj, wayanta ta ɗauko ta fara texting ummi sun jima suna magana
kan ta miƙe ta shiga kitchen, ita tayi musu girkin daren ranar sbd gujewa tunanukan
Muktar da ya addabe ta ta rasa me take ji a game dashi, tsoro ne, tausayin Maami da
halin da yake jefa kanshi da fushinta ne ko zeal na son ganin ta kyautatawa matar
da duk duniya itace mace ta farko da ta fara kyautata musu a rayuwa?
Bayan gama cin abincin nasu ne Alhj ya mike yayi sama yana cewa
"Hajiya in ganki mana minti biyu"
Miƙewa tayi tabi bayanshi yayinda Alaya ke tattare kwanukan, tana kai na karshe
zata juyo kenan taji tayi mugun karo da mutum, kafafunta suka Harɗe baya baya tayi
zata faɗi yayi hanzarin riƙota, hannunshi yasa ya kama nata hannun ya matse kara ta
saki tana me duƙawa kaɗan
"Zafi Don Allah"
Idanunta a runtse hawaye wani na bin wani, ganin azabar yayi mata yawa ne yasa
cikin kuka tace
"Na amince wlh zan mata mag..."
"MUKTAR"
Maami ta katse shi tana jin kaman ta rushe da kuka ko ta rufe shi da duka ko zata
ji saukin abunda take ji akan shi.
"Ga nan irin abunda nake tsoron yasa na ki baka ita, amma zan kai maka ita cikin
wani sati sai ka shirya ko ka riƙe ta saboda Allahn da ya halicce mu ko kuma ka
zalunceta, Allah baya bacci kuma baya barin zalunci kuma ina faɗa maka kaji tsoron
Adu'ar wadda aka zalunta don bashi da shamaki, fice ka bar min gida!"
Ta karashe da karfi tana nuna mishi kofa.
Tsayawa yayi yana kallonta sama da mintuna biyu kan ya wuce yana gunguni, da sauri
ta ƙaraso wurin Alayar tana rike hannun tace
"Sannu daughter, ya ji miki ciwo ko?"
Girgiza kai tayi tana me Miƙewa tace bari ta shiga ɗaki.
Da tunanin tarewar ta cinye satin ko fahimtar abin da ake yi a class bata yi tsabar
tsoro, amma ya zata yi abu sede in ba'a sa mishi rana ba sai ga ranar ya zo,
sisters ɗin ta guda biyu ta kira akan su rakata gidan ta don already an gama haɗa
mata komai da komai har akwatunan an riga da an kai chan, tana kuka tana komai aka
kaita gidan muktar a chan suka barta bayan doguwar nasiha.
Ta jima zaune bisa gadon har ta gaji ta kwanta bacci ya fara fusgarta taji ana bugu
kaman hauka, a tsorace ta tashi tsaye tana zare idanu ganin tsayuwar ba zai mata ba
gashi sai karuwa bugun ke yi yasa da sauri ta fita, duba agogon parlorn tayi karfe
ɗaya saura mintuna.
"Waye ne?"
Ta faɗa muryarta na rawa
"Wayewa! Ke dallah ki buɗewa mutane kofa in zaki buɗe.."
Muryar mace taji, a tsorace ta buɗe yarinyar na sarkafe da hannunta a kwankwason
muktar ɗayan hannunshi na zagaye da kafaɗarta, ko be ɗago ba ka san ba karamin
buguwa yayi ba, da sauri Alaya ta koma baya tana kama bakin ta da hannayenta, kukan
sai ya ƙi zuwa sai idanu take bin su dashi har yarinyar ta shigo dashi tana karewa
gidan kallo tana taɓe baki.
"Ke wato kin raina mutane ko? Waye ya baki iz....nin rrrrufe kofar nannn"
Cikin tsantsar maye yake maganar yana nuna ta da yatsa.
A tsorace taje ta fara kokarin riƙe shi yarinyar tayi tsaki tace
"Muky am sleepy, good night"
A maimakon Alaya taga ta fice sai gani tayi tayi wani ɓari na gidan wanda ba inda
Alayar ta fito ba, tana tunanin tana layi sbd yadda yake sakar mata jiki shima kuma
Layin ne yake yi, a haka suka nufi ɗakinta hawaye na wanke mata fuska warin giyar
kamar zai kashe ta, galau galau suka yi kaman zasu faɗi kokarin tare shi take sai
kawai taji amai a jikinta, wani irin tashin zuciya ne ya kamata, hawaye wani na bin
wani haka ta jefa shi kan gadon bayan ya gama amaye mata jiki, bata iya ganin amai
ba hakan seda yayi sanadiyar nata aman babu komai cikinta, tayi ta wahala a bayin
kan ta fito tana kau da ido ta samu ta kwashe.
Kayanta ta cire tayi wanka tana fitowa ta ganshi zaune yana kallonta.
"Ke zo nan!"
Har lokacin mayen be sake shi ba
"na'amm"
Ta ƙasan jajayen idanunshi yake kare mata kallo kan yace
"kika bari na maimaita sai na lahira ya fiki jin daaɗi"
Cike da tsoro take takowa ko kan ta ƙaraso ya fusgota kaman wata ƴar tsana haka ta
faɗa kirjin shi, toshe hancin ta take sbd gudun sake amai warin giyar gigitata yake
ga tsananin tsoron abunda zai iya mata ko kan ta gama tunani taji hannunshi ya fara
yawo a jikinta, idanunta ta zazzaro cikin sautin kuka tace
"Me...menene Ya muktar?"
Bakinta ya rufe da nashi ta datse nata tana kakari sbd yadda abubuwan maye ke tashi
a cikin bakin shi, kokarin kwatar kanta take Dukda ta san karfi ba ɗaya ba shima
kuwa nuna mata ya fara yi cewa karfi ba ɗaya ba, dambe ne ya kaure a tsakaninsu,
duk kokarin da tayi wurin ganin be samu abunda yake so ba ta kasa dakatar dashi,
tayi kuka kaman zata cire ranta ta jefar, kirjinta yayi matukar nauyi, numfashi
yayi mata wahalar shaƙa, ji tayi inama ta mutu a lokacin, be saurara mata ba seda
ya samu natsuwa ya zube a kanta ya fara baccin hauka, nauyinshi ya kara mata nauyin
kirjin da take ji, idanunta na kallon seiling yayin da hawaye ke ganganrawa gefen
fuskanta wani na bin wani ta fara cewa cikin jiggata
"Ya Allah kaine Allah, Allah kai kaɗai ka san dalilin hadani da Mukhtar a matsayin
miji, Allah kana gani kuma na san kana ji na, ka bani haƙuri da juriya a kanshi ya
Allah, idan kuma mutuwata ce hutu daga wannan radadin zuciyar ya Allah ka ɗauki
raina a yanzu ya rabbi, idan kuma a rubuce yake a cikin kaddarata Ya Allah ka
shiryar dashi ka kuma bani ikon yi mishi biyayya...."
Kuka me karfi ta fashe dashi ta saka ɗan karfin da ya rage mata ta fara kokarin
ture shi, saide ta kasa duk yadda ta so tashi ta kasa, kaman yadda taga rana haka
taga dare tayi kuka har ta rasa hawaye, jikinta ya dauki zafi, numfashinta ya fara
nisa sbd tsananin ciwon da zuciyarta ya ɗauka, cikin tsananin rauni cike da ban
tausayi take cewa chan ƙasa ƙasa
"Ummina ashe ba zan sake ganinki ba? Ashe ba zan taɓa jin muryarki a zahiri ba?
Ashe ba zamu sake saduwa da ke ba! Ki yafemin in n...na taɓa saɓa miki, ummi ki yi
min Adu'a zan tafi in samu Abbana....."
Ta karashe cikin jan wani wahalalliyar numfashi.
Mukhtar kuwa Ba shi ya farka ba seda gari yayi haske tarr, hantsilawa yayi gefen ta
yana buɗe rinannun idanunshi ya zuba mata, ko motsi bata yi ba, fuskanta ya kurawa
ido yayi wani haske yayi fayau, da sauri ya miƙe zaune ya ɗaga hannunta se yaga ya
koma ya faɗi yaraf, kanshi ya ɗaura a kirjinta babu bugun zuciya..bai san sadda ya
dirko daga gadon ba ya ɗauki boxers ɗin shi ya saka babu abunda yake tsoro se
Maami, ya san idan har ya kashe yarinyar nan ko da me yake takama sai tayi shari'a
dashi...
Da gudu ya kaita mota bayan ya sa mata riga wacce be tantance bata da tsawo ba seda
suka shiga asibiti, a asibitin ma da gudu aka karɓeta zuwa emergency, likitan da ya
iso cikin hanzari ya fara examining ɗin ta, girgiza kai yayi, yana saurin riƙo
hannunta ya fara jin pulse ɗin ta....
*Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same
shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi
09039206763*
#Vote
#comment
🖤Gureenjoh🖤
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*
*BOOK 1*
*Page Ten*
Kallon Mukhtar dake tsaye ya zurawa gangar jikin Alayah idanu yayi yana cewa
"wannan fa? What is he doing here?"
Muktar da duk tunanin shi na ga Irin badakalar da zasu yi da Maami, sai kuma
tunanin irin garɗin ni'imar da ya kwasa daga Alayah ace har ta mutu? Sau ɗaya kawai
fa yayi?..
Idanunsa ya maida kan karamin likitar dake cewa babban
"her heart stopped beating doc, babu wani pulse dake harbawa a jikinta"
"blood?"
Ya faɗa ba tare da ya jira amsar Mukhtar da har lokacin yake tsaye ba, kallon kallo
suka yi suka sake kallon muktar zuciyoyinsu na bijiro musu da abubuwa daban daban..
"Meke damunta? Did you raped her? Gsky ba zamu iya taɓa ta ba sai da Police, this
case is serious"
Jin hakan yasa doc saurin bawa nurses dake tsaye cirko cirko umarni, a take suka
turo automatic external difibrillator, aka zuba mishi cream din ya dirza kan ya
ɗaura mata a kirji, fusga tayi daga ita har gadon suka sake komawa yaraf, cikin
gogewa a aiki ya sake murzawa ya danna mata ta kara jan numfashi tayi sama ta dawo
kasa, a na huɗu ne ta ja wani dogon numfashi wadda ya dawo mata da numfashinta
gabaɗaya, taimakon gaggawa suka fara bata yana kallon nurses biyu yace
Kaman mintuna goma sai ga wasu doctors guda biyu nurses din na biye dasu, rufuwa
suka yi a kanta suka fara bata taimako barin ma Abdulrahman da ya kasance kwararren
likitan zuciya, seda ta daidaita kan Eshrat dake gynae ta duba jikinta da sauri ta
runtse idanu tana me Miƙewa tsaye, idanunta ta maida kan Muktar dake tsaye ya zura
musu idanu bazaka tantance halin da yake ciki ba, a ranta ta raya dole hakan ta
kasance daga kallo daya da ta mishi ta san yana apawa, ga ingarman jikinshi da ya
watsawa tattoos na ban mamaki, cinyoyinshi dake waje sbd wandon jikinshi ƙarami ne
a mummurɗe.
"She needs stitches” ta faɗa tana kallon likitocin, Abdulrahman da ya gama daidaita
mata bugun zuciya da taimakon Allah yace
"She also need an urgent heart surgery, the heart is so weak and fragile"
"Dr Eshrat yi aikinki, before then relatives ɗin ta su yi duk wani abu da ya kamata
har da blood da komai we will prepare for the surgery"
Yana kai nan ya fice.
Juyawa Drn farkon yayi wadda suke kira da Dr Ahmad ya kalli Mukhtar yace su je
waje, ficewa suka yi zuwa office nashi, jallabiyarshi ya ɗauka ya miƙawa muktar
wadda sabo ne tsaraba ce ma aka kawo mai sai ya mance a office ɗin, da wani irin
kallo muktar ke bin jallabiyar shi fa ba sa irin abubuwan yake ba.
"Babu daaɗi kana yawo a kan patients haka, you need to wear this ka zauna in maka
bayani"
Karɓa yayi ya bare a ledar ya saka, coffee Brown ce me sulɓi, wani irin amsarshi
yayi shi ko se taɓe baki yake yana tsaki ƙadan kaɗan.
Bayani likitan ya fara mishi sai ya nuna idan kudi suke bukata ko nawa ne ze iya
bayarwa ayi komai, tsoronshi Allah tsoronshi Maami kuma baya so yarinyar ta mutu
don yana da buruka a kanta, yana so ya nunawa abokanshi daban daban cewa ya kere
sa'a, yana kuma kwadayin sake ɗanɗanata.
Wani paper Dr Adam ya mika mishi bayan dogon typing, Miƙewa yayi ya fice zuwa
reception anan ya biya duk abunda ake bukata, ko jinin ma seda wata nurse tace ko
za'a gwada nashi yace a'a a saya a blood bank, bayan ya tabbatar babu wani abu ya
fice abin shi.
Gida ya dawo yayi wanka ya sa kananun kayanshi as usual wando baya kaiwa ƙasa in ko
ya kai to irin wasu mahaukatan crazy jeans ne da suke nan kaman palazo, da karamar
riga marar hannu, daga nan ya leka Rita buduruwarshi bata nan ya tabbatar tana club
don haka chan ya wuce, hayaniyar ganinshi ta hautsina club ɗin a take ya fara rabar
da kyaututtukan giya sai rawa en mata suke yana shafasu cikin kwarewa da barikanci.
A asibiti kuwa aiki aka mata dukda anasthesia da take kai da kuma rashin hayyaci
daga ka kalli fuskanta zaka san tana jin zafin stitches ɗin har aka gama, aka fara
shirya batun surgery babu kowa nata aka shiga da ita theater, seda suka shafe sama
da awanni bakwai kan suka fito, Alhamdulillah aiki yayi Kyau atleast zata ji saukin
ciwonta ba kaman baya ba Dukda ba warkewa gabaɗaya tayi ba, abun mamaki har lokacin
mijin be dawo ba kuma babu wadda yazo a family.
Aminity da ya bada umarni after the surgery nan suke so aka turata babu abunda take
sai baccin wahala da gajiya, wasa wasa har dare sede nurses su zo su duba ta su
tafi haka ta kwana be dawo ba, Washegari da misalin karfe goma na safe ta fara buɗe
idanunta cike da kokonton kasancewar ta a duniya har a lokacin, ɗakin take karewa
kallo a hankali hankali se ta fahimci asibiti ne nan ɗin, ga wasu na'urori jikinta,
lumshe idanunta da suka faɗa sossai tayi ta sake buɗewa daidai lokacin wata nurse
ta shigo ganinta ido biyu yasa ta koma ta kira Dr.
Checkup suka yi mata sossai kan suka rage na'urorin jikinta, Dr. Eshrat tace
"Fatima..."
Kaman yadda ta gani a rubuce a jikin file nata, da idanu Alaya ta bita.
Ta san mutum na karshe da ta kasance tare dashi Mukhtar ne, runtse idanunta tayi da
karfi tana jin kuka na son zuwar mata tuna irin azabar da tasha a daren, a hankali
cikin rawar murya tace
"mi..jinaa"
Da mamaki suke kallonta, taya mahaifiyar mijinta zata iya taimakonta alhali ɗan ta
ne ke da kaso mafi girma cikin abunda ya faru da ita?
Dr Ahmad ne ya karɓi Layin Allah ya sa ma ta riƙe sbd numbern special number ce,
kira yayi cikin hikima ya sanar da ita komai nan take cikin tashin hankali tace
gata nan zuwa.
Ba'a yi mintuna Talatin ba sai ga Maami, hawaye tayi ta zubarwa na tausayin Alayah
wadda seda ta saka Alayar kuka, ƙanwarta ta kira tasa ta dafa mata abinci irin na
marar lafiya ta kawo mata yanzu, Alhj hammad ta kira ta sanar dashi halin da ake
ciki, sam ta ƙi ambaton sunan muktar sbd gudun mummunar kalma akan shi, iyayenmu
mata kenan(ki kasance me gudun mummunar kalami akan yaron ki musamman idan ya
kuntata miki sbd duk maganar da zaki yi a lokacin walau sharri walau alkhairi Allah
na iya amsawa a take).
Har misalin sha ɗaya da wani abu sistern ta ta zo da abincin, da taimakon Maami
tayi brush ta taimaka mata ta fara bata kakkauran shayin kan taci dankalin turawa
da aka sarrafa shi cikin kayan ciki(offals) kaɗan, magunguna nurses suka zo suka
bata, da wasu Iv injections aka sake ɗaura mata drip, wayan Maami ne yayi kira a
hankali ta duba sunan se ta lumshe idanu kana ta sake buɗewa ta miƙe ta fice.
Sama da kusan mintuna Talatin ta dawo, bayanta Alhaji hammad ne, shi karan kanshi
be ji daaɗin abunda Muktar yayi ba, barin ma watsar da ita a asibitin da yayi yanzu
da bata rike Layin Maami ba fa? Sede fa Dukda haka ba wai ze mishi faɗa bane ko ya
nuna mishi rashin kyautawarshi tana bacci don haka be zauna ba ya fice, a harabar
asibitin ya tsaya ya kira Layin muktar, dagawa yayi cikin alamun baya ma cikin
natsuwar shi.
"Kai kuma haka ake yi? Toh wlh ka tanadi abunda zaka kare kanka dashi a wurin
maaminku ni kam ba ruwana"
"karka damu ai tunda kaine ke da igiyar aure a hannunka zancen maaminku ta raba ku
be taso ba, amma fa ranta ya ɓaci kuma ta zub da hawaye sossai"
Cikin rashin nuna damuwa da hawayen mahaifiyar tashi yace.
"Maami kuma hawaye na mata karanci ne Abba? Bari dae ina wani abu zan shiga
asibitin zuwa anjima, duk bala'i babu zancen rabani da Fatima daga Asibiti kuma se
gidana"
Alhj hammad na gyara zamanshi yana kallon gefen titi sbd driver dake ja a natse
yayi murmushi ya katse wayar, Abban Meelah ya kira ya sanar dashi an yiwa Alayah
aikin zuciya sede be wani yi Adu'a ko nuna damuwa akan ciwon ba, kuma yace ba ze
iya gayawa mamarta ba sbd baya so hankalinta ya tashi, sallama suka yi Alhj hammad
na tayiwa Alhj Alhassan kirari.
Mukhtar be tashi shiga asibitin ba sai dare, Maami ta tafi sai Aunty rukayya da me
aikinta da zata kwana asibitin, an ɗan ɗaga gadon Alayah na kwance a kishingiɗe
idanunta a lumshe amma ba bacci take ba, tana masifar kewar umminta gashi ko sanin
halin da take ciki ummin bata yi ba, wayanta na chan gida bare tayi mata message ko
bata faɗa mata ba ta ji lafiyarta, kai tsaye ya shigo ɗakin ba tare da ya damu da
sallama ba tunda yayi knock.
Aunty rukayya dake ta kallonshi ta kasa cewa komai, kafada ya ɗaga yaje ya tsaya
gaban gadon yana kallonta, sarai ya fahimci ba bacci take ba baki ya sake taɓewa,
abunda ya hana shi zuwa asibitin kenan don be san uban da zs tsinana mata ba tana
wannan abu kaman taga dodo, tsaki yaja ya juya ya fice abunshi a cewar shi yana da
abin yi.
Haka ta shafe kwanaki goma curr a asibitin duka duka zuwanshi biyu shima se chan
dare lokacin me aikin dake kwana da ita ce kawai, Maami tayi kokari sossai wurin
ɗawainiya da ita hakan yasa dole ta koyawa kanta shanye damuwarta saboda damuwar
matar, fargabarta ɗaya yadda zata koma gidan muktar, zata iya kuwa? To in bata koma
ba ina zata je ga Abunda Abban Jameelah ya faɗa mata, sannan kuma bata Yiwa Maami
kara ba Dukda har lokacin Maamin bata ce mata komai akan abunda ya farun ba.
Yau da take cika kwanaki goma sha biyu muktar ya zo da misalin karfe 12 na dare kai
tsaye office na Dr in charge ya wuce
"Ina so ka bani takardar sallamar matata"
"wani irin sallama by this hour? Kuma ai tana da sauran medication da checkups"
"Yau bazata ƙarasa kwana a asibitin nan ba, duk kuma abunda ya saura ko ma menene
zata zo daga baya"
Ganin fa baya ma cikakken hankalinshi kuma ze iya hautsina musu natsuwa anymoment
sbd yanayin shi yasa babu yadda likitan ya iya duk yadda ya nuna mishi ya barta sai
ko safiya ce ya ƙi haka ya bashi sallamar.
Tana kwance bacci ya fara ɗaukar ta bayan doguwar hira da idanunta suke yanzu kawai
taji Shigowar mutum, da farko ma ta zata nurses ne sai taji muryarshi yana ce mata
"ke tashi mu tafi"
Mummunan faɗuwa gabanta yayi, taji gabaɗaya numfashi na shirin barin jikinta, ko
kwakwaran motsi bata iya yi ba bare ta buɗe idanunta har ta fahimci shin shi ɗin ne
ko ba shi bane, kuma da ita yake yi ko da wata....
"Kika sake Kika bari na maimaita kaina wallahi sai na lahira ya fiki jin daaɗi.."
*Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same
shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi
09039206763*
#Vote
#comment
🖤Gureenjoh🖤
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
*Rubutu a kan ruwa... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*
*BOOK 1*
*Page Eleven*
Wani tunani ne ya faɗo mata, tayi saurin sa hannu ta murda handle ɗin sede motar a
rufe, da sauri ta sa hannu cikin sanɗa ta duba wayanshi ta taɓa screen ɗin ba
password, hannu ta kai jikin kofanshi ta buɗe motar daga madannin wurin, jikinta na
rawa kaman wacce aka sato ta buɗe ɓangaren ta ta sa kafafunta waje hannunta dake
rawa na dialing Layin Maami, kaman an tsikareshi ya farka wani irin fusgo hannunta
yayi ta dawo da karfi har tana buguwa dashi ya tsinka mata mari yana kashe wayan da
har ya soma ringing..
"Will you shut up! In ji wa yace u r not my slave? Ko baki san duk mace baiwa bace
a gidan miji? Oya come and remove this clothes for me zan yi wanka"
Miƙewa tayi gudun kar ya kara taɓa lafiyarta taje jikinta na rawa ta cire mishi,
hannunta ya ja suka yi toilet wankan ma ita ya saka tana kuka ta mishi, yace tayi
nata ta same shi yanzu.
Haka tayi don miji irin Muktar ta fahimci in tace zata ke musu dashi watarana
kakkarya ta ze umminta ce kuma da asara.
"Fatima tun da nayi sallama da ƙasata na shigo wannan na san nayi sallama da farin
cikin rayuwa, na fuskanci kalubale iri iri da damuwa kala daban daban kan Allah ya
haɗa ni da mahaifinki ya maida ni tamkar sarauniya ya bani duk wani farin ciki da
na rasa a baya amma shima Allah be bar min shi ba, tafiyar shi ga rabbissamawati ya
sarar dani, na ɗauka nima zan bishi a kowani lokaci amma tunda na tsallake baƙar
wahalar da na sha daga rasuwarshi zuwa haihuwar ki na sa a raina cewa komai ze zo
ya zama tarihi, iko na rabbi ne kawai dawwamamme, na sa a raina zan raineki kila
sirrin farin cikina na gareki, sai kuma gashi yadda kema Allah yayi dake.
Dukda haka ban sare ba, kema ina me karfafamiki gwiwa da kwantar miki da hankali a
kan cewa in shaa Allahu zaki wayi gari kiga duk wannan sun wuce, imani da yaƙini
akan ubangiji yana riskar da bayi zuwa ga magantuwar matsalolinsu, wallahil azeem
ubangijinmu na sane da lamuranmu kuma ina da tabbacin wata rana ze fidda mu daga
cikin wannan jarabawa, ko ban riski lokacin ba in shaa Allahu wata rana zaki yi
farin ciki, zaki yi murna zaki tuna kuma da cewa na faɗa miki hakan"
Hawayenta ta share ta zurawa muktar ido, kila watarana shine ze zama farin cikinta,
kila kuma karshen zaman su na iya zuwa ko kusa ko nesa, amma ka fin nan tayi
alkawarin yunkuri wurin chanza shi, zata kasance me yi mishi Adu'a a ko wani
motsinta zata taya mahaifiyarshi yakin mai dashi mutumin kirki da yardar Allah ko
da kuwa ita baza ta samu ribar komai ba.
Anan kan sallayan tayi bacci da asuba ma jin mutum kawai tayi ya ɗauke ta zuwa
gado, bata mishi tirjiya ba ta hakura saide fuskanta be huta da ruwan hawaye ba don
ba daaɗin abun take ji ba banda azabar ciwo, seda ta sake wanka na ruwan zafi
sossai tayi na tsarki ta fito tayi sallah, yana kwance yana bacci, a hankali ta
matsa kusa dashi ta sa hannu ta na ɗan bubbuga kafafunshi
"ya Mukhtar! Ya muktar ka tashi kayi sallah don Allah, lokacin sallah na wucewa"
Ko motsi be yi ba, da ta matsa mishi ya ja dogon tsaki tare da kaiwa hannunta harbi
da kafa da sauri ta ja baya ya samu iska, tagumi ta zuba tana kallonshi har bata
san sadda bacci ya kwashe ta a wurin ba.
Sai misalin karfe goma ta tashi, yunwa ne ke dawainiya da ita kuma har lokacin
bacci muktar ke yi, idanu ta zuba mishi tana aikin kallo, da zai shiryu muktar ba
karamin kyau yake dashi ba, tana nan tana kallonshi tana sake-sake, ya buɗe idanu.
"Ya Mukhtar namiji fa daga cibiyar shi zuwa guiwowinshine al'auranshi, Kaga zaka yi
sallah kuma wandon be kai guiwa ba be kamata ba"
Ta faɗa a tsorace
"karki karɓa in nayi" ya faɗa yana jan tsaki tare da tada Sallar shi ita dae ta san
sallahn nan kam se a hankali karfe sha ɗaya sallahn asuba sannan da gajeren wando.
Knocking aka yi ta miƙe ta buɗe, tray ne me ɗauke da abinci kala uku da ruwa da
wani energy drink, karɓa tayi ta zo ta ajiye ta zauna jiranshi har ya idar ya juyo.
"Muktar ina ka kai ƴar mutane Maaminka ta kasa natsuwa? Kana so sai ka tayar mata
da hawan jini ko?"
"Hotel"
Ya faɗa yana haɗe rai.
Ita dae tausayin Maami ne ya rufe ta ta san duk don ita ne hankalin Maamin yake a
tashe, a hankali tace
"ya Mukhtar ka bani Maamin zan yi magana da ita don Allah"
Harara ya zabga mata kan yacewa mahaifinshi da ya gama ce mishi su dawo yanzu
"gaskiya ba zan dawo ta rabani da matata ba, ni ban rabata da mijinta ba haka
kawai"
Wayan ya jefa mata har yana dukan kirjinta ta dauka tana gaida Alhajin cikin
girmamawa ya amsa yana tambayar lafiyanta tace da sauƙi Maamin na kusa?
"Lafiya ta ƙalau Maami, eyaa Maami ki mana alfarma ki kwantar da hankalinki kinji
don Allah, in sha Allah babu abunda zai faru"
Ta faɗa a karye cikin son karfafawa Maamin gwiwa, Maamin da taji hawaye na son zuba
mata ne tace
Karɓa yayi yana kau da kai daga kallonta yana taɓe baki
"Ina kwana?"
"Baka damu da kwana na ba ai muktar da ka damu da ba haka ba, ka ɗauki yarinyar nan
ka maida ta gidanta ka bar Hotel da ita, sannan ka tabbatar ta cigaba da zuwa
makarantar ta ranar Litinin"
Tana kai nan ta kashe wayan, hawayenta ta share Alhj dake tsaye yace
"menene kuma ne Maamin su? Ina dae yarinyar nan tace miki babu komai ki rabu da ita
da mijinta mana"
"Subhallah"
Ta ambata chan ƙasa, ba don tana tsoron yin magana ya zama laifi ba da tace yayi
saurin tuba da wannan kalma da ya je fi mahaifiyarshi dashi in har yana son rabauta
duniya da lahira iyaye ba abin wasa bane amma inaa.
Da sauri ta miƙe tabi bayanshi, a cikin harabar gidansu yayi parking, ajiyar zuciya
me karfi ta sauke ko ba komai zata je ta samu tayi magana da Mahaifiyarta, bata
jirashi ba tayi ciki zuwa ɗakinta ta ɗauko wayanta ta fara turawa ummi text
message.
"Alaya ina kika shiga kwana biyu nayi sako shiru babu amsa? Kina lafiya dae ko? Ko
ciwonki ne ya tashi? Ina ma ina da bakin kiranki in ji muryarki don tabbatar da
lafiyanki... Don Allah kar ki min karya baki da lafiya ko?"
Kuka ta fashe dashi a fili tace
"Ummi bani da lafiya, ummi bana son wannan aure bana son shi, mugu ne, ummi marar
tsoron Allah ne, bashi da ibada be san menene addininshi ba, ummi abubuwan da nake
son faɗa miki kenan amma ba zan iya ba..."
Typing tayi
"na ɗan yi rashin lafiya amma da sauki Maami ta kula da komai yadda ya kamata"
"Alhamdulillah ummi babu komai yanzu, Ameen thumma Ameen kefa ummi? Babu wani
damuwa? Su Hajiya Zeenat basa takuraki? Aiki be miki yawa ba ummi?"
A hankali tace
"Toh"
Har ya juya ya ce
"Ki tabbatar mutane akallah ashirin zasu ci su koshi"
Yana kai nan ya fice, bata kawo komai ba bayan tayi la'asar ta shiga kitchen dinta
Allah ya sa tana jin karfin jikin nata sossai Alhamdulillah, sossai ta zage tayi
girkin har kala biyu jollof nd fried Rice pepper chicken sai ta ɗan yi snacks ta
haɗa fruit drinks masu daaɗi, dab Magrib ta fito daga kitchen din wanka ta sake da
alwala ta zo tayi sallah, ta jima tana karatun alqur'ani da rokar wa kanta mafita a
wurin rabbisamawati har aka yi isha ta tashi ta gabatar kaman wasa tana zaune nan
ta soma jin hayaniya a ranta take ayyana baƙin sun zo kenan.
A hankali tace
"Amma Ya muktar abincin ai yana dining naga be kamata sai na fita na sassa......"
"Kina so in wanka miki mari?"
Shiru tayi ta miƙe shine ya shiga drawer ɗinta ya duba ya zaɓo wani pencil gown ya
wulla mata, seda ta gama kallon kayan kan ta saka a hankali babu shape na jikinta
da be nuna ba.
Hijab ta fara dubawa yayinda shi kuma yake sake da baki yana kallonta don ba
karamin gigita shi tayi ba sai gani yayi ta saka hijab
"Ya Mukhtar ba zan iya fita da wannan rigan cikin maza ba hakan ya sabawa Addi...."
Wani wawan mari ya sauke mata har seda ta faɗi
"ke wai yaushe na zama sa'anki da zan faɗa ki faɗa?"
Tana dafe da kunci cikin gunjin kuka ta miƙe
"Babu biyayya a bijirewa ubangiji ya Mukhtar ba zan iya..."
Sake kifa mata mari yayi ya ja hijab ɗin ya fisge ya yar kan ya janyo hannunta suka
yi cikin parlorn tana tirjewa.
Chak ta tsaya tana karewa parlorn kallo, mata da maza ne daban daban cikin shiga
irin ta rashin sanin darajar kai wasu na rurrungume da juna yayinda kwalaben shiha
suka yi bakwai a parlor hayaƙi har ya fara cika parlorn yana maida wutan wani fari
fari baki baki, ganinsu tare yasa aka hau ihu sai kallon maita mazan suke mata da
sauri ta koma bayanshi ta ɓoye.
Rita wacce tsab Alaya ta gane ta ita ce ta kawo shi daren farkonsu a Buge tace
"Ga dae kyau sede babu wayewa duhun kai yayi yawa"
Shewa suka ɗauka don a yadda tayi maganan har da kishi.
#Vote
#comment
🖤Gureenjoh🖤
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
*Rubutu a kan ruwa... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*
*BOOK 1*
*Page Twelve*
*Sometimes idan muna karanta labari mu kan ji kaman almara har mu kan yiwa kawunan
mu tambayar cewa anya hakan na faruwa? Wannan Page is a dedication to waenda suke
cikin ibtila'in auren mashayi, masu haƙuri da juriya da kaddararsu. Sadaukarwa ce
ga uwar da Allah ya jarraba da haihuwar ɗa wanda jarrabawarshi ta zama shaye-shaye,
Allah kana ji kana gani ya Allah ka shirya mana zuri'a, ya Allah ka kara musu
haƙuri da juriya, ya Allah Alfarmar annabi da alqur'ani ka musanya musu
kaddarorinsu daga baƙi zuwa fari*
(Ni kaɗai na san what i went to wurin rubuta wannan Page, a painful True life
story)
A wurin wani wahalallen bacci ya kwasheta ba ita ta farka ba sai da aka kira
assalatu, Miƙewa tayi ta shige toilet ruwa ta fara watsawa kan ta ɗaura alwala tana
jin yanda zuciyarta yayi mugun nauyi haka dae tayi sallah ta nemi magunguna ta sha
kan ta kwanta, bacci ta sake yi ba ita ta fito ba sai karfe tara sanye da hijabin
da tayi sallahn asuba dama da shi ta kwanta, a parlorn ta tsaya tana kallon yanda
suka maida shi, kyamar parlorn gabaɗaya ya shige ta, haka dae ta daure iya dauriya
ta soma tattare parlorn har ta gama ta share ta fesa air freshner kan ta nufi
kitchen don neman abinda zata ci.
Bata gama dafa indomie din ba taji motsi, da sauri ta juya tana kallon kofan
kitchen ɗin a tsorace sai suka haɗa idanu, babu kaya a jikinshi daga shi sai
karamin wandon jeans, daga dukkan alamu har lokacin ba wai ya dawo daidai bane daga
abubuwan da ya ɗurawa kanshi.
"ke wato ma ina wasa dake ko? Ni zaki dizga? U are very stupid...don ubanki sau
nawa na buga miki kofa kika barni shanye ana min dariya?"
A tsorace take matsawa ganin yana kokarin cire belt din jikinshi muryarta na rawa
tace
"Kayi haƙuri, don Allah ka saurareni ya Mukhtar..."
Tun kan ta sauƙe sunan ya fara zuba mata belt ɗin, be ji tausayinta ko na minti
ɗaya ba sai da yayi mata duka har da kafa kan ya juya ya fice yana cewa gobe ta
kara...
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun! Innalillahi wainna ilaihi rajiun" abinda take ta
nanatawa kenan tana kuka, da kyar ta iya lallashin kanta ta miƙe ta nufi daki bayan
ta kashe gas ɗin indomien da bata ci ba kenan, tana hawaye tayi wanka idonta ɗaya
yayi jajazir jini ya kwanta gefen fuskanta ga shatin belt nan har kusan uku jikinta
yayi wani irin Red abin ka da farar fata.
Cikin uniform ta shirya don ta yankewa zuciyarta duk wuya zata yi karatu ko don nan
gaba ta iya tsayuwa da kafafunta idan Mukhtar be yi sanadin ta ba, ji take kaman
zata mutu kwana kusa a yanda take jin kirjinta da ciwonshi da ya dawo sabo fiye ma
da na baya, tafin hannunta ta ware ta ɗan zubawa idanu kan ta gimtse tana sake
ajiyar zuciya me nauyi na tsantsar damuwa a haka ta tafi makarantar, dayake bata
kula kowa babu wanda ya damu ya tambayi me ya sameta ko ya akayi ta ji rauni har
aka tashi bata iya ta ci komai ba.
Bayan ta dawo ta haɗa custard ta sha ta sake shan magunguna kan ta janyo wayanta
don jin lafiyar mahaifiyarta.
Wani irin sabon baabin wahalar rayuwa ne ya buɗe mata, Mukhtar bashi da tausayi ko
imani ko na miskala zarratin, ga zafin zuciya matukar ya sakata yin abinda ya
saɓawa addininta in ta ƙi haka yake mata dukan mutuwa, marin shi a gareta ya zama
kaman man shafawa da da matukar wuya a wayi gari a yini be kai hannunshi jikinta
ba, ga bautar yi masa girki da abokansa wanda ba kadan ba idan suka tashi zuwa, a
kullum se sun nemi ganinta ita kuma bata fasa ƙin fita ba ta kulle kofan ta gam shi
kuma da safe ya mata dukan mutuwa, ko yaushe in yana bukatarta haka ze je mata
walau yana hayyacinshi walau yana cikin maye, duk wani alwashi da ta ci a farko
akan Mukhtar bata iya ta soma tabuka komai ba don gani take har Abada Mukhtar baze
chanza ba, bata da lafiya sossai don zuciyarta ya sake rauni kan rauni sede babu
wanda ta faɗawa haka take lallaɓawa kuma take karatu.
Yau suke gama waec ta yi jamb tun sati biyu da suka wuce, Alhamdulillah sun
gama lafiya da Fatan jiran sakamako me kyau, a koyaushe tana jinjinawa Maami da
irin jajircewarta a kanta Dukda wani sa'in idan muktar ya mata wani abin sai wata
zuciyar ta raya mata dole ne ai Maami ta so ta don ta san zama da ɗan ta sai wanda
iyayenshi suka sallama, da sauri kuma sai ta yi a'uziyya ta kawar da tunanin don ta
san Maami da zuciya ɗaya take mata hidima kuma take tausayinta, babu wanda ze ganta
ya shedata sbd wani irin rama da tayi a watannin da ta durfafi yi gidan muktar,
tayi wani irin haske har kana ganin kalar green green a jikinta in kana kallonta,
idanunta sun kara girma da haske haka hancinta ya sake fita zirrr, bata wani ado
bare kwallaya in tayi wanka ta shafa mai ta sa kaya shikenan.
Yanzu da ta gama Waec zaman gidan ya zame mata kaman wacce take rufe a prison na
karkashin ƙasa, Rita a gidan take rayuwa daga parlor zuwa kitchen duk nata ne
yayinda Alaya ke ɗaki a koyaushe abinda ke fitar da ita yunwa sai kuma idan shine
ya zo ya sakata girki amma bata yi ta ajiye kam don ba lallai ma wasu ranakun yana
kwana a gidan ba, kaman yau, gabaɗaya yinin tayi shi ne ba daaɗi sbd hayaniyarsu da
suka yini yi bidiri kala kala a gidan, kaman wani kwarya kwaryar lifaya ne suke yi
a gidan, daga inda take a ɗakinta babu irin warin ababen Mayen da bata ji, tana
dukunkune kan gado, tana bukatar shan sassanyar iska marar surki irin wannan, ji
take kaman zata mutu ne sbd wari da tashin zuciya.
Kofan ta da ta kulle ne yinin ranar gabaɗaya don ko abinci bata iya fita ta nema ba
taji ana bugawa da karfi, chan ta jiyo dakakkiyar muryarshi yana kiran ta da sunan
da shine ya raɗa mata wato
"ke! Ke!!"
Gabanta ya faɗi, zuciyarta ya hau tseren bugu me zata mishi a wannan yanayi da yake
ciki? Kallon jikinta tayi idan tana son lafiyan jikinta kuma abu me sauƙi shine ta
bude kofan taji me yake tafe dashi sede tsoro kaman ta narke ta ɓacewa gani da
sauraranshi ya lullubeta, jin kaman ze ɓalla kofan ne yasa ta sanya kafafunta ƙasa
kaman wacce kwai ya fashewa a ciki ta nufi kofan hannunta ɗaya na kan zuciyarta da
bugawarshi har ya shafi numfashinta, hannunta na kakkarwa ta miƙa ta buɗe, banko
kofan yayi sai gata gabanshi ya fisgo ta riƙo na mugunta yayi mata
"yarinya in ba zaki bi abinda nake so ba kina cikin wahala, buɗe bakinki ki karɓa"
Girgiza kai tayi tana kauda kanta daga wani abu da yake shirin bata.
"Ya..m...mukhtar menene?"
Kashe idanu yayi yace
"ko kin san menene ko baki sani ba dole zaki sha"
Ya karashe yana janyota zuwa fili abokan shi suka ɗauki shewa.
"Game muke kin san Truth or dare?"
Be jira amsanta ba yace
"an yi daring ɗina na bugar dake don haka buɗe baki malama"
Idanunta gabaɗaya ta fitar, a lokaci ɗaya jikinta ya ɗauki mazari, me yaya muktar
ke nufi? Shayar da ita abun maye ze yi? Hawaye ne suka soma zuba babu birki cikin
girgiza kai tace
"Don Allah yaya Mukhtar kar ka yi, kar ka cutar dani, ya muktar hannuna
zafi...kirjina ciwo don Allah kar ka sa ni saɓawa mahallicina a dole, karka
zalunceni dayawa mana have a pity on...."
Bakin ya murɗe se sowa suke suna ambaton sunanshi ya soma bata, duk yanda tayi
ganin ta kubce ko bata sha ba hakan be yiwu ba, gimtse hancinta yayi seda ta sha
kaɗan kan ya sake ta ganin yana shirin kisa, a wurin ta zube ta tura yatsa cikin
bakinta ta soma amai, tun tana yi har ta gigice ta fice hayyacinta gabaɗaya, wata
ce a cikinsu da jikinta yayi sanyi da tausayin Alayar tace
"Gaskiya baku kyauta ba, tunda bata sha me na shigo da ita cikin wannan game naku?
Kullum baku da buri da ya wuce ku wulaƙanta ta, mu faɗawa kan mu gaskiya mana kai
Mukhy kaine babban wawa, wanda be san abinda yake yi ba, taya zaka shigo da matar
aurenka na sunna cikin wannan irin rayuwa, wani irin jahil....."
Gigitaccen marin da Muktar ya sake mata ne ya saka ta kwala ƙara ta yanke maganan,
kan tayi motsi saurayinta ya tashi ya rama mata, kwalba mukhy ya janyo ya rotsa
mai, a take jini ya fara tsiyaya kaman wasa sai gashi wurin na shirin zama karamin
Abbatoir don faɗa ne sossai ya kaure tsakanin saurayin chan da shima ɗan wani ne da
kuma Mukhtar kowanne kuma yana da abokan zagi, ita dae Alaya ta samu ta rarrafa ta
faɗa ɗakinta ta datse kofa a wurin ta kwanta, kanta se juyawa yake da alama de
kayan Mayen ya taba ta, tayi kuka har ta rasa hawaye, tana ta rokon Allah ya yafe
mata yana gani ba laifinta bane, an fi awa biyu kan taji gidan yayi tsit, a wurin
tayi bacci Washegari ma seda ta kai wuraren sha biyu kan ta farka sbd buga mata
kofa da ake tayi kaman za'a ɓalla.
Dafe kanta dake sarawa tayi ko Sallar asuba bata yi ba, hawaye ya gangaro mata ta
sanya hannu ta share kan ta motsa a hankali ta miƙe dafe da gini ta miƙa hannu ta
buɗe kofan jin bugun ba na ƙare bane, woman Police ce tsaye tana kallonta
"Madam ko zaki iya ara mana mintuna biyu a cikin lokacin ki?"
Kaman bazata yi magana ba tace cikin dasashiyar muryarta
"Lafiya?".
"Shin kina cikin gidan nan gabaɗaya yinin jiya zuwa dare?"
Kai ta gyaɗa ba tare da ta amsa ba
"ko kin shedi hatsaniyar da ya faru a jiyan?"
Nan ma ta girgiza kai tana kallon matar da take ta karantarta..
"Ba zaki samu ko wani sheda daga gareni ba, ko ma menene kike so pls ki samu waenda
suka asassa abun, ina da uzuri se anjima"
Ta ƙarasa a sanyaye kan ta tura kofan ta rufe ta juya zuwa bayi, seda tayi wanka ta
zo tayi sallah tana rokon yafiyar Allah kan ta fita ta nemi abinda zata ci ta sake
dawowa ta rufe ɗakin ruff ko bi ta kan wargajejjen parlorn bata yi ba, idan tace
yanzu bata soma developing wani irin tsana na Mukhtar ba to wlh tayi ƙarya, a ƙasan
ranta tayi ta ja mishi Allah ya isa kuma tana fata ya saka mata, ashe a chan kam
case sossai aka yi sbd karfe da karfi ne suka haɗu sai da shudin Goshi case din ya
mutu, nan Alhjnsu yayi ta mishi faɗa akan hakan ze iya ɓata mishi siyasa kar ya
sake, ya dae ji ne ko da ya dawo ya tarar parlorn haka buga mata kofa yayi ta buɗe
ba tare da ta kalleshi ba sai shima ya ji shakkan kallonta don fuskanta ba digon
walwala ko farin ciki.
Yammaci ne sakaliya tun safe bata fita daga ɗakin ba, bata jin karfin jikinta sam
ganin yunwa ze iya mata illa don daga kwance ma jiri take ji yasa ta miƙe ta fito
sanye da dogon hijab as usual ta shiga kitchen.
Rabin taliya ta dafa da kwai dafaffe guda biyu ta zuba a plate, ta juya frigde don
ɗauko ruwa se ga Rita ta shigo kai tsaye plate ɗin ta ɗauka zata fice, shan gabanta
Alaya tayi tana jin ranta na ɓaci
"Ai kuwa gwara da ni sau dubu saba'in in ma na amsa ni village girl din kenan, ko
ba komai village girl ta fi ashawo...."
Watsa mata abincin gabaɗaya Rita tayi jiki yayinda ita kuma Alayah ta dauketa da
zazzafar mari.
hango Mukhtar bayan Alayar yasa ta dafa kumatu ta saki razananniyar ihu, cikin
kuka tace
"Wallahi yau zan bar maka gidanka Mukhy, har ni matarka zata ɗaga hannu ta mareni
akan banza taliya? Ni dae?"
Da sauri Alayah ta juya zata yi magana ya kifa mata mari, yayi ball da ita bata san
ta tafi kaman wacce iska ya ɗauka ba seda taji ta sauƙa a kafafun mutum, ɗagowa
tayi bata gani daidai sai taga Maami ce da sauri ta miƙe ta faɗa jikinta ta soma
kuka me cin rai, kan Maami tace tayi wani yunkurin kawai Alaya ta yanki jiki ta
faɗi ƙasa...
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun Mukhtar ka kashe musu ƴa ka huta, nace ka huta.."
Tana nufo shi ne take maganan
"wani irin zuciya ne da kai? Wani irin baƙin zuciya ne Allah ya halicceka da ita?
Ashe baka da tausayi Mukhtar dubi yadda yar mutane ta koma"
Kwalan riganshi ta chakwamo
"Allah ya saka mata, wallahi Allah se ya bi mata hakkin ta, Allah ya mata sakayya
tun a duniya, mugu azzalumi.."
Hawaye take yi bibbiyu, hannunta yake kokarin cirewa a wuyan shi tana sakin shi
kuwa ta soma zuba mishi maruka hagu da dama tana kuka.
Ganin hakan baze mata ba ta soma neman abinda zata kwada mai ko zata huta bata yi
taku biyu ba itama ta yanki jiki ta faɗi ƙasa. Se a lokacin ya gigice cikin hanzari
y dago ta yana kiran Maami Maami, sede Maami tayi nisa, daukanta yayi da gudu zuwa
motanta driver ze ja yace ya jira shi, da sauri ya koma ya ɗauko Alayah da banda
haushinta babu abinda yake ji dama tsakanin shi da mahaifiyar yaya gashi tana kara
ɓatawa, ta wannan ne kawai zasu iya samun matsala da Abbansu don yana son matarshi.
A motanshi ya saka ta yana gaba drivern Maami na bin su a baya har asibiti, cikin
gaggawa aka Karɓe su emergency, likitoci suka rufu a kansu wasa wasa har aka yi
Magrib kan suka samu kan Maami, Alayah kam se kusan bayan isha ma likita mace ta
fito tana kallon Mukhtar
"kaine mijinta?"
Kai ya gyaɗa yana kallonta
"Toh Congratulations matarka tana ɗauke da ciki na tsawon sati biyar sede akwai
karancin nutrient a jikinta, and ciwon zuciyanta yana so ya tsananta kaman yadda
jininta ke hawa duka wannan illah ne ga lafiyarta a gaskiya ya kamata ku kiyaye, a
ka'idar aiki ma bayan an mata wanchan aikin zuciyar be kamata kuma ya sake hitting
haka ba"
Shi duk sauran jawaban ma baze ce ya ji ba banda batun cikin nan da ya ji.
"Ciki???"
Ya maimaita kan ya sake cewa
"do you mean pregnency?"
Kai ta gyaɗa, ya ja wani dogon tsaki ga ta inda ya tsani auren ai, yarinya ta zo
banda gidahumanci babu abinda take mishi kwata kwata ko shekara bata rufa ba ace
wani ciki, shiyasa ya fi son hulda da wayayyun mata shi be shiryawa haihuwa yanzu
ba...
"MUKHTAR"
Maami ta kira sunan, se kawai ta sulale ta zauna a wurin tana hawaye a ranta tana
istigfari bata san me zata yiwa Mukhtar ya shiryu ba, babu me fahimtar ciwon ranta
babu me gane abinda take ji da takaici da haushin ɗan da ta haifa a cikinta se
wacce jarabawa irin wannan ya faɗarwa, muryarta a rarrabe tace
"ka fice daga asibitin Mukhtar wallahi na tsani ganinka"
Da sauri ya ɗago ya kalleta, ze yi magana ta daka mishi tsawa tana dafe kanta dake
juyawa.
Miƙewa yayi ya fice, da sauri likitar ta ƙaraso ta riketa ganin tana shirin sake
collapsing.
"Se hakuri Aunty, Adu'a itace maganin komai ki kara akan wanda kike"
Maami na hawaye tace
"Wallahi ina yi Likita, ina yi bana bacci amma kaman bana yi astagfirullah Allah na
tuba Allah"
Tausayinta sossai ya rufe likitan, ita tayi ta kwantar mata da hankali amma ta koma
ɗakinta firr ta ƙi tace zata zauna da Alayah gudun sharrin Mukhtar.
Se kallon yadda kasusuwa suka yiwa yarinyar sarka take yarinyar gwanin tausayi,
rayuwarta duk ya daidaice sbd Mukhtar, matakin da ta yanke kawai shine na riketa ta
nema mata saki wurin Mukhtar shine kwanciyar hankalinsu duka, in ya ga dama ya tara
matan duniya a gidanshi yana zina dasu tunda abinda yake so kenan, share hawayenta
tayi ganin Alayah na motsi ta riƙe hannunta....
"Juna biyu???"
Bata san a fili ta maimaita ba seda Maami ta ɗago ta kalleta tace
"Eh, kina dauke da juna biyu na tsawon sati biyar..."
Dibbbbbb haka duniyarta ya tsaya, komai nata ya tsaya chakk kaman robot ta sake
maimaita
"Juna biyu dai?"
*karki manta book 2 na kuɗi ne, da Naira ɗari biyar kachal zaki mallaka, a sha
karatu lafiya*
3118518476 First bank Fatima Muhammad Gurin sai ki tura shaidar biya ta
09039206763*
🖤Gureenjoh🖤
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
*Rubutu a kan ruwa... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*
*BOOK 1*
*Page Thirteen*
*A cikin satin nan ina da hidima sossai so it depend da yanayin comments naku, in
yi Page ban ga comments na arziki ba ga gajiyar hidima ga al'amuran yau da kullum
gaskiya ba zan iya ba, sai in bari sai sati na sama in cigaba*
Yanayin fuskanta sai ya so ba Maami tsoro don ƙiri-ƙiri ya nuna bata na'am da
lamarin cikin, lumshe idanunta tayi tana jin hawayenta na sake yi mata nisa sbd
tsabar zubar dasu da ta ke, sai ciwon zuciya mai tsanani da take ji kaman ko yaushe
zai iya yin ajalin ta, sam bata yi farin ciki da cikin ba, ba wai bata so bane ba
kuma wai ta tsani ɗan bane kawai bata shirya haihuwa da Mukhtar bane cikin wannan
hali da suke ciki na rayuwa, bazata taɓa so ɗan da zata haifa ya tashi ta nuna mai
muktar a matsayin mahaifi ba, sam be chanchanta ya zama uba ba bashi da nagarta da
wannan nasabar taya zai iya baiwa yaronsu tarbiya da taimakon da ya dace?
Shigowar ruqayyan ne ya katse su, da kanta ta zubawa Alayar abinci Maami ta taimaka
mata ta zauna kan ta soma bata abincin, cikin natsuwa take karɓa har seda ta ƙoshi
kan ta ce ya isa Maamin ta mika mata ruwa ta sha, kan ta sake kwanciya sai bacci,
Aunty ruqayya ce tace
"Amma yarinyar nan na da tsananin haƙuri Adda, ina tsoron kar shiga hakkin nata
yayi yawa, idan mariƙinta ya mata muguntar haɗa ta da muktar mu da muka san
halayyarsa maras kyau kuma be kamata mu zuba idanu tana shan wahalarsa ba kiyi
hakuri in abinda na faɗa ya ɓata miki rai"
Tattaunawa suka cigaba da yi duk akan matsalar Mukhtar, chan sai ga Alhj ya shigo
yau kam seda yayiwa Mukhtar faɗa akan abinda yayi wanda hakan be wani ɗaɗa muktar
din da ƙasa ba wayan ma ya ajiye a gefe hands free yana zuƙar shisha ɗin shi
hankali kwance, bayan ya gama ya kashe.
Ita Maami bata wani yi maganan Alayar da shi ba don ta san duk inda aka je aka dawo
yana bayan Mukhtar don ba ganin laifin shi yake ba sam, saida ta kwana biyar a
asibitin kan aka sallameta, a wannan karo Maami ita ke yini ta kuma kwana duk yanda
ruqayya tayi da ita akan ta bari su kwana ko ta kawo mai aikinta su kwana ta ƙi
tace bata so ko kusa Mukhtar ya sake yunkurin cutar da ita, daga asibitin gida suka
yi direct ɗakin dake gefen nata Maamin ta mata masauki don ta sake.
Da kanta ta tura aka haɗo mata kaya akwati har biyu da wayanta da take ta
magananshi sbd son jin Umminta da take, ɗaki ne me girma da tsari babu abin more
rayuwa na kuɗi da babu ciki, Maami ta mata umarni da ta dinga kulle kofan in an yi
knocking sai ta tabbatar da waye kan ta buɗe don ta san Mukhtar farin sani, ita
kuma zata cigaba da kula Dukda ta saka securities hana shi isa sashenta tace duk
shigowan shi iyakaci sashen mahaifinshi bata amince ya zo mata sashe ba.
Zaman Alaya a gidan ya matukar yi mata daaɗi duk wani kulawa na me juna biyu tana
samu daga Maami, da kanta take shiga kitchen take dafa mata duk wani abu da ta san
zai ƙara mata lafiya, haka a asibiti ma an yi recommending ta yawaita cin irin su
vegetables, jan nama da dai sauransu, laulayinta ba mai yawa bane saide zazzafar
zazzabin yamma, sai kuma wani sa'in amai shima ba sossai ba, kaman yadda ta ɓangare
ɗaya Mukhtar ya gigice don duk yanda yake tunanin hukuncin Maami ya wuce nan tayi
rantsuwa ko ya kawo mata takardar Alayah ko su haɗu a court ya bata ta karfin tuwo
tunda yarinya bata son shi, Alhj hammad din ma bata ragar mai ba gashi yana ɗan
busy sbd siyasa da ya kawo kai gadan-gadan.
Damuwar Alayah guda ɗaya takkk na rashin jin mahaifiyarta duk text message da zata
yi mata ba reply tayi ta kira tun yana shiga har ya daena, wannan na daga cikin
abinda ya shigar da ita sabuwar damuwa da zaƙuwar son ganin mahaifiyarta, suna
zaune da Maami suna ɗan taɓa hira yayinda Maamin ke chat kaɗan kaɗan tana murmushi
me sanyi sbd da sanyin zuciyarta take magana, Dukda ɓacin rai yake nunawa ita kam
lallashin shi take ta kuma lura har da Shagwaɓar da baya rabo dashi in dae yana
gabanta kaman ba shi ba.
Duban Alaya da sai juya wayanta take tayi tana karantar damuwar fuskanta kaman ma
bata san da wayan da Maamin ta gama yi ba tace
"Binty"
Bata amsa ba ta sake cewa
"Fatima.."
Nan ma shiru, Miƙewa tayi ta isa gareta ta taɓa ta sai tayi firgigit ta zubawa
Maami idanunta dake cike da ruwan hawaye, Maami tace
"Binty yawan tunani hatsari ne ga lafiyarki, menene? Me damuwar?"
Murmushi mai ciwo Alaya ta saki ita kam ta riga tayiwa Abban Jameelah farin sani
babu ko shakka abinda ya faɗa ɗin har ranshi ne sede zata je ɗin, ko yanka naman
jikinta yake zata je taga mahaifiyarta.
Washegari da misalin karfe huɗu na yamma Maami ta ɗauketa suka nufi family house
ɗin su, babban gida ne me sashuka uku, matan gidan ba dae karamci ba haka ma'aikata
da kalilan yara dake gidan wasu na kiran Maami yapendo yayinda wasu ke cewa Goggo
ta fahimci duk masu ce mata Adda ɗin kannenta ne, anan taga daga inda Maami ta samu
zuciyar daraja ɗan adam ko yaya yake, ba karamin kudi ne dasu ba daga tsarin ginin
zuwa kayan ciki kaɗai ya isheka shedar hakan amma ji yadda suke Haba Haba da ita.
A sashen mahaifiyarta suke dattijuwa ce me tarin ilimin addini, kana ganinta zaka
iya kiranta da Ba'abziniya ko kuma shuwa cikin biyu dae kaman yadda Maami take kama
da ita sak, haka ma Mukhtar, sai bayan Magrib baba ya aika kiransu.
Cikin natsuwa suka zauna daga ƙasa a gabanshi, ita dae Alayah tayi farin gani don
dattijon duk inda ake son samun kamillale natsatsen dattijo ya kai, wannan shine
tsufa me riba a tsufa da mutunci karkashin inuwar addini, bayan sun gaisa ya dubi
Maami yake ce mata yana sauraren ta, tiryan-tiryan ta soma bashi labarin abubuwan
da suka faffaru nan ma bata san wasu ba kaman na ɗura mata kayan maye da yawan duka
kaman jaka, ga siyar da mutunci.
Ita dae Alayah kanta ƙasa ko daga shirun da wurin ya ɗauka bayan gama bada labarin
Maamin ta san ran dattijon be mishi daaɗi ba
"Muktar sam be kyauta ba, hukuncin da kika yanke ma ban ga laifinki ba, ba zai yiwu
a bashi mace da ciki yaje garin duka ya raunatata ba, ina zuwa"
Ya ɗaga waya ya kira muktar yace ya same shi a gida yanzun nan.
Tambayoyi ya dinga ɗan jefowa Alayar tana amsawa da iyakar gaskiyarta akan gidansu
da sauransu, duk abinda ta taɓa fadawa Maami haka ta faɗa mishi ba chanji, suna nan
zaune sai ga Mukhtar, ba Alaya kaɗai ba hatta maami seda ta shiga tsantsar mamakin
ganinshi da wani half jumpa blue yadi me taushi har da hula da ya rufe tsinannen
askin kanshi, dama ta san duk duniya mahaifinta kaɗai yake iya yiwa wannan tsoro da
ladabi, a hankali ya zauna gaban baban, bayan shiru na sama da mintuna biyu baba
yace
"Muktar na raina wayonka, kwarai baka kyauta ba anan ɓangaren dukan macen aurenka
kuskure ne babba, Allah be amince da wannan ba ko kusa ko alama, mace da aka sani
da rauni Abar a tausaya mata a riritata, a lallaɓa rayuwarta ita ce zaka dinga
sakarwa kwanji? Haba Mukhtar! Yanzu da ka kawo ƙara me kake bukata?"
Daga Maami har Alaya ba wai sun yarda da zancen shin bane sbd sanin hali da suka
yi, duka wannan ladabin na en wiwi ne
"Ashe baka san hadithin da yake magana akan dukkan shugaba abin tambaya ne akan
kiwon da aka bashi ba? Kana tunanin in an ce shugaba ana maganar kawai masu mulki
ko sarauta ne? La la la kowani mutum mai kiwo ne akan iyalansa kuma abin tambaya
ne, shari'ar musulunci ta tsoratar akan duk wani me take haƙƙin wani ɗan uwansa na
kusa ko na nesa kai hatta akan dabbobi bare matarka ta sunna, ka san wanene addinin
musulunci ya ƙira da dayyus?"
Kanshi a ƙasa jikinshi ya ɗan yi sanyi ya girgiza kai.
"Wato sakarai, shashasha wadda baya kishin matarsa kwata kwata ya ɗauketa ne kawai
a matsayin wacce zata mishi girki ya ci sai in bukatar shi ta tashi ya sauƙe ko
kuma yaje yayi ta mu'amala da wasu matayen wannan sharri ne mai girma, domin irin
wannan ne yake janyo shaidan ya ci galaba kan matar ko a samu akwai ƙarancin tsoron
Allah sai itama ta halaka, ko ka san dayyus basa taɓa shiga aljanna? Ko kamshin ta
bazasu ji ba, sahihin hadithi ne ya zo daga manzon Allah cewa mutane uku bazasu
shiga aljanna ba an karboshi ne daga Abdullahi dan umar, mutane uku Allah ya
haramta musu aljanna wadda ya dawwama yana shan giya har ya mutu..."
Da sauri Alayah ta ɗaga kai ta kalleshi kaman yadda Maami ma da hawaye ya zubo mata
take kallonshi, gabaɗaya kaman ruwa ya ci shi haka ya ɗago ya kalli matar tashi da
mahaifiyarshi.
"idan har ba tuba yayi ya daina dukkan waennan abubuwan da na lissafo ba, tuba na
gaskiya da gaskiya tsakanin shi da Allah, Mukhtar kaji tsoron Allah! Ina ƙara
nanata maka wannan kaji tsoron Allah a dukkan lamuranka ka tashi ka tafi zan neme
ka da kaina"
Baba ya ƙarasa!
Shiru ya sake yi chan dae ya gyaɗa kai, ba tare da ya sake cewa komai ya miƙe ya
fice daga parlorn.
"Fatima!" Baba ya kira ta, shesheka take saki a hankali ta riga tayi developing
tsanar Mukhtar bata son shi, bata ƙaunar shi, bata jin ko kaɗan zata iya son shi
bayan duk abubuwan da yayi mata, bata tausayin shi saboda shine ummul aba'isin duk
halin da yake ciki he's responsible for that don bazata ɗaurawa Maami ba mutumiyar
kirki!
Cikin muryan kuka ta amsa, gabanta na faɗuwa tana Adu'ar kar ya mata dole zama da
Mukhtar a yanzu bata ko ganin ƙimar shi.
*Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same
shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi
09039206763*
#Vote
#comment
🖤Gureenjoh🖤
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
*BOOK 1*
*Page Fourteen*
Godiya sossai ta mishi Dukda ba daaɗi take ji ba a haka suka fice daga gidan, saida
suka biya asibiti saboda Maami ta kasa gane mata a take likitan da take gani yayi
referring ɗin su to meddy specialist hospital wurin Doctor Philips saboda ya
tabbatar musu lamarin ta sai a asibitin za'a iya tackling ko kuma waje, godiya suka
mishi daga nan suka yi gida dare yayi sossai so bata wani zama ba ta watsa ruwa ta
kwanta, duk yadda ta so bacci ya ɗauke ta ma ya ƙi sai juyi take tana tunanin
rayuwarta, ita bata zama mai sa'a ba sam babu mai mata ƙaunar tsakani da Allah
bayan mahaifiyarta sai Maami haka zata cigaba da rayuwa?
Shin ya zata je ta tarar da ummi? Wani irin tarba zata samu daga mutanen gidan
barin ma Alhj Hassan dala? Wani irin ma tunani zata yi akan Mukhtar da zama dashi
bayan ta riga ta sakawa ranta ba zata iya cigaba da zama dashi ba?
Washegari haka ta yini duk jikin babu daaɗi da misalin karfe huɗu ta shirya tsab
cikin atampharta da aka mata ɗinkin riga da skirt Dukda ramarta sai dae tayi haske
yanzu ta ɗan yi kyau sbd karan hancinta da ya kara fitowa idanunta suka kara girma,
she's so pale bata da wani walwala, daga ɗakinta ta fito sai ta tsaya chak tana
shakar daddaɗar turaren da kamshin shi ya danne duk wani kamshi na Maami da baya
rabo da babban parlorn saman, bata taɓa jin turaren ba, ko dae Mukhtar ne ya sauya
turare? Da wannan tunanin ta tura ɗakin Maami ta shiga Maamin ce kawai zaune tana
duba wani littafi da ya fi kama da na addini.
Kamshin ya fi yawa a ɗakin hakan yasa tayi tunanin dae wani sabon turare ne Maami
ta buɗe mai daaɗi, a gabanta ta zauna tana mata sannu da gida, cikin kulawa ta amsa
tana tambayarta babu abin da yake damunta? Ta girgiza kai kan tace
"Maami zan je dubo ummin"
Maami tace
"Toh Binty ki gaisheta kin ji? Sannan ga wannan dama tun jiya na tanada ki kai mata
in akwai wani matsala kiyi gaggawar ƙirana kin ji?"
Kai ta gyaɗa tana karɓar jakar tare da godiya da Adu'a ga Maamin kan ta miƙe, har
ta isa kofa Maami ta kirata ta dawo.
Kiran me aikinta tayi dattijuwar mata Maama Laami tace su tafi tare da Habu driver,
babu gardama suka fice a tare.
Banda faɗuwar gaba babu abin da take ji har dafe kirji take akai akai har suka isa
gate ɗin gidan, Habu yayi horn shazali ya buɗe mai gate din ya kutsa kanshi ciki
yayi parking, idanunta ne suka sauƙa akan Alhj Hassan dake zaune riƙe da jarida a
rumfar shaƙatawarshi wanda hakan yasa gabanta sake bugawa da karfi, Habu ne ya buɗe
mata kofa sai ta kasa sauƙa ganin Hajj Zeenat sun fito a tare da Jameelah kaman
wani wuri jameelar zata ita kuma Hajiya wurin alhaji ta nufa bayanta me aikin da
bata sani bane rike da tiren kayan marmari.
Rashin fitan ta ya dawo da hankalin Alhj Hassan kan motar, har jikinta na rasa ta
sanya kafa ta sauƙa daga cikin motar dukkaninsu Dakatawa suka yi suka zuba mata
idanu, baba Musa ne cikin mamaki da wani ɗan farin cikin da ya bijiro mishi yace
"Alayah kece?"
Wannan suna da ya kira yasa dukkanin fara'ar fuskokin iyalan gidan ya kau, Miƙewa
Alhj Hassan yayi ya nufo ta yace
"Ke! Uban me ya kawo ki gidana? Me na faɗa miki randa aka ɗaura miki aure?"
"Don Al...."
"I Said get out...!!"
Ya daka mata tsawa yana yiyowa kanta, da sauri Maama lami ta riƙe ta tace
"Hajiya mu tafi"
Girgiza kai tayi tana me sakin kukan da take riƙewa
"Maama mahaifiyata ce fa... A nan ciki... Ba..n sa..n ha..halin da take c..ciki ba,
ba za.."
Marin da Alhj Hassan din ya kawo mata ne ya sameta tayi baya saura kaɗan ta faɗi
baba Musa da yake kusa ya tare ta chan ƙasa yace
"idan akwai wadda zaki iya tara ya taimaka miki karki je ki zuba ido mu karan kan
mu bamu da tabbacin lafiyar mahaifiyarki"
Ɗagota yayi, hajj Zeenat tace
"ka ganka Musa!! Kai shashashan ina ne da Alhj na hukunci zaka shiga? Da ka tare ta
uban me ya haɗa ku da zaka bata kariya? Ashe ma goyon baya zaka bata tayiwa uban
gidanka rashin kunya? Shiyasa na tsane ku ku din nan ma'aikatan tsakar gidan nan,
akwai wani abu daban cikin ranku to ya ƙare a kanku"
Habu da ya buɗe mota ne yayiwa Maami Laami magana tayi saurin saka Alaya da har
lokacin kuka take tana tirjewa bata son tafiya cikin motar, yayi saurin shiga suka
bar gidan hajjiya Zeenat na cigaba da surfa bala'in ta son rai.
"Binty kiyi shiru in shaa Allahu ina tare dake, ina nan tare dake kuma ba zan taɓa
bari su ida mugun nufin su ba, a jikina ina jin ummin ki babu abin da ya sameta, ki
natsu kin ji? Kin ga ba ke kaɗai ba ce, ki bani hankalinki in shaa Allahu yanzu zan
soma ɗaukar mataki"
Ita dae ta san Alhj Hassan fuskantarshi ba abu bane mai sauƙi tunda Ummi nunawa
take Abbanta ma ya gaza, sannan abokin Alhj hammad ne baban su Mukhtar baze iya
bari Maami tayi wani abu ba, idan kuma bata yi ba shikenan ta rasa ummi kenan ko
yaya?
Ire-iren tunanin da ta zurfafa kenan ta daena kukan sai ajiyar zuciya, Maama lami
ke faɗawa Maami duk yadda aka yi tana jinjina rashin darajar mutanen gidan, da
lallamin Maami ta ɗan ci wani abu sai dawo mata maganganun baba Musa yake, yana
faɗa mata ne akwai damuwa, har ta kwanta bayan isha sai saƙe-saƙe take bata da
yadda zata yi, babu gata cikakke babu galihu, wanda hakan ya sakata kuka mai yawan
gaske daga karshe ya haddasa mata zazzafar ciwon kai me tafe da zazzabi, da kyar ta
ga safiya ko da Maami bata ganta ba bayan sallah saboda tana idar da sallah take
zuwa gaisheta hakan yasa ta shigo ɗakin don dubata yanayin da ta sameta ne yasa
kawai suka yi asibiti, gabaɗaya tausayin rayuwar Alayar ne ke rufe da Maami har
kusan bayan awanni biyu ma kan Dr Philips din ya fito yake mata bayanin stage din
da take na da hatsari tana bukatar kwanciyar hankali da natsuwa, hakan ne kawai zai
sa da taimakon magani sai ta samu sauƙi tunda ba'a jima da mata aiki ba kuma it was
successful.
Duk Maami ta ji kuma ta san hallayyar Muktar gareta ne yayi triggaring ciwon da
ya kamata ace ya lafa sossai da sossai, sai kuma wannan Alhassan ɗin da babu mugun
abu nashi da bata sani ba, bashi da imani ko na miskala zarratin, godiya ta mishi
kan ta ƙarasa ɗakin da aka kai Alaya din baba ne ya kirata don jin jikin Alayar sai
ma yaji suna asibiti hakan yasa yayiwa Daada magana ta sa driver ya kai musu abin
kari.
Riƙe da hannunta Maami ta zuba mata idanu, wani irin tausayinta na sake ninkuwa a
ranta, hawaye ta tsinci kanta da yi tana saka kanta a sahun Alayar, kiran da ya
shigo wayanta ne yasa ta share hawayen kan ta miƙe ta fita tana danna recieve...
*Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same
shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi
09039206763*
#Vote
#comment
🖤Gureenjoh🖤
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
*Rubutu a kan ruwa... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*
*BOOK 1*
*Page Fifteen*
Wani nannauyar ajiyar zuciya ya sauƙe tare da buɗe idanunshi dake runtse tuntuni,
club ɗin ya zubawa idanu a hankali yake bin mutanen wurin ɗaya bayan ɗaya da kallo
kaman yau ɗin ne rana na farko da ya soma shigowa a rayuwarshi, daga masu tiƙan
rawa rungume da Ƴan mata, zuwa kan masu kiɗan da suke buga beat suna ihu, zuwa kan
waenda suke rage zafi da Ƴan matan da ba muharramansu ba babu wani kayan arziki
zuwa masu busa hayaƙi da shan barasa, duk yadda yake tunanin anan yake samun
natsuwa sai yaji gabadaya natsuwar ma ta ƙi zuwa, tsanar wurin ma yake ji a ranshi
hatta da mutanen cikinta, idanunshi ya ɗaga sama yana shafa dadar kanshi tambayar
kanshi yayi a lokaci ɗaya menene jin daaɗin wannan rayuwa? Mecece ribarta?
Sake lumshe idanun yayi sai fuskan Maami ya faɗo mishi tana zub da hawaye tana
mishi karyayyen kallo mai cike da tausayi, jimami da damuwa, da sauri ya buɗe yana
kallon Rita dake tsaye a kanshi a maimakon ya ga fuskanta sai fuskar Alaya ce take
faɗo mishi, magana take mishi amma sautin sassanyar Muryar yarinyar yake ji yana
shiga kunnuwanshi, da karfi Abokin shi Pepe ya jijjigashi yana ƙiran sunanshi wadda
hakan ya dawo dashi natsuwarshi
"Kana lafiya kuwa?"
Ajiyar zuciya ya sake sauƙewa kan ya ɗan girgiza kai sai kuma ya gyaɗa kawai.
Rita tayi saurin cewa
"Ko dai Maaminka ce ke pressurizing ɗin ka? Matar abin da take yi bata kyautawa,
kaman babu zuciya a ƙirjinta? Anya ita ta haif..."
"Shut uppp! U are very stupid mahaifiyata kike kokarin jefa da kalaman raini? I
won't take that wlh kika sake ko da ambatan sunanta ne sai kin sha mamaki na.."
Yana kai nan ya ture ta ya fice daga wurin kujerun ya koma gaban table da masu kula
da wurin ke ta sarrafa barasarsu ana cigaba da bawa masu siye wasu har da ƙanƙara
ciki.
"Ko sha'awar jin sunansu bana yi bare har in raɓesu, I hate everything wallahi tun
jiya ko runtse idanuna na kasa da sunan bacci"
Shiru suka ɗan yi kan Nawwaz yace
"maybe you need space for Little bit ka ɗan huta, da dai zaka iya da mun koma ka
zama high sai ka fi samun natsuwa da bacci yadda ya kamata"
Kai ya girgiza ya juya zai shiga mota smart ya riƙe hannunshi
"ba zamu barka kake driving kai kaɗai cikin wannan hali ba, zamu dinga kasancewa
tare da kai har ka dawo daidai ko ya kuka ce?"
Ya tambayi saura suka ce hakane a tare suka shishiga motar, Smart ya ja suka fice
daga harabar wurin.
****
Hawayenta ta share tare da ɗaga kai ta kalli saman ɗakin mutane are very wicked a
wannan zamani namu, su kan manta cewa duniyar kwata-kwatarta bata da wani girma
kuma aron rai aka bamu muke zama cikinta, bata san me zata kira iyalan Hassan dala
dashi ba, menene suke dashi against waennan bayin Allahn? Ko rantsuwa tayi bazata
yi kaffara ba akwai tsantsar son zuciya, hassada da baƙar kyashi a tare dasu waenda
duk mugayen ciyuka ne masu zaftare imani ya ɗaiɗaita natsuwa da farin ciki, godiya
ta cigaba da yiwa Allah da ya sa umar na gari da bata san yadda zata fuskanci
Alayah ba idan ta farka, dole hankalinta ya tashi ta shiga damuwa saboda uwa ai
wata giɓi ce da rasa ta rayuwa babban asara ce wadda mai da irin ita babu har
Abadan Abada.
Banko kofan da aka yi ne yasa ta buɗe idanunta tana kallon Alhj hammad da ya shigo
har huci yake sbd fushin da bata san a ina ya kwaso ba yake shirin zuwa kanta ya
juye mata kwandunansu.
"Lafiya kuwa Alhj? Ya zaka bangaje kofan asibiti haka kuma babu sallama ka s...."
"Shut uppp!! Ki dakata min Fatima, uban wa ya baki izinin kutse cikin ahalin Hassan
dala? Menene naki da rayuwar gidanshi? Ina ruwanki da komai na gidan?"
"kin san me kike kokarin aikatawa? Kin fa san siyasata idan ba Hassan kaman babu
ita ne, taya zaki yi kokarin yi min asarar mutum irin shi a gab sa'ar da burin
raina ke gab da cika? Har ki aiki wanchan banzan ɗan n..."
Da sauri ta katse shi
"Umar ba banza bane Muhammad, kuma ba zai taɓa zama banza ba, ina zuciyar imaninka
ya shiga ne? Cikin fa najasar kashi da fitsari, ɗauke da zazzafar stroke da hawan
jini ya haddassa wanda ya assassawa matar chan shiga cikin come ya fiddo ta, shin
wannan be zama abin alfahari ba? Menene laifin umar da ka ɗaura mai karan tsana
saboda kawai ya saka idanu kan al'amuranka ya kuma tsaya tsayin daka wurin hana ka
aikata mummunan laifin illata rayuwar matasa a cikin al'umma? Kar ka zama Hassan
din mana! Kar zuciyarka ta yaudare ka wurin auren duniyar nan mana Abban Mukhtar.."
Ta ƙarasa da karyayyen hawaye.
Juyowa yayi ya watsa mata wani irin kallo kan ya juya ya fice yana sake buga kofar,
kanta ta maida ƙasa ta sake silalar da hawaye kan ta share ta juya ta fice don duba
Ummi dake ICU tun jiya ko motsi bata yi ba kaman yadda Alayar ma take ta bacci tun
a jiyan don daga ta tashi za'a sake mata allura ta koma tana bukatar cikakken hutu.
Maami na fita ta buɗe idanunta tare da kurawa kofan, hawaye ne taji yana cika mata
ido wato in ka hangi Maami daga waje zaka rantse da Allah cewa ta gama samun komai
a rayuwa tana cikin daula da hutu ga kuɗi masu maganin matsaloli amma ba hakan ba
ce mai ɗaki shi ya san inda yake mishi yoyo, ashe bayan jarrabawar Mukhtar tsakanin
ɗaya ɗan ta da mahaifinshi babu zaman lafiya? Amma kaman maganan ummi ake? Sai
yanzu kalaman ya ɗaukota cikin najasar kashi da fitsari da stroke wanda hawan jini
ya haifar sanadiyar hakan tana cikin coma da wani irin hanzari ta miƙe zaune tare
da fisge ruwan ba tare da ta damu da jinin da ya cigaba da bin tsintsiyar hannunta
ba tayi saurin saka takalmi tayi waje.
Bayan Maami kawai ta hanga hakan yasa ta haɗa da gudu tana kiran sunanta, da sauri
Maami ta juyo tana ganinta ta nufeta tana salati
"Menene haka Alaya? Meyasa zaki fusge ruwa daga jikinki haka? Dubi fa jinin dake
zuba?"
"Maami Ummi na ce? Ummi ce kuke maganar Shiga coma? Me ya sameta ummi? Garin yaya?
Taya hakan zata kasance.....innalillahi wainna ilaihi rajiun..""
Gabaɗaya ta ma ruɗe ta gigice
"Ki natsu Alayah tana cikin salama in shaa Allah Adu'a kawai take buƙata a halin
yanzu daga gareki ba wannan kukan da ɗaga hankalin ba, in shaa Allahu yanzu ummi ta
dawo wurina kenan har Abada ko da tana so ba zan bar ta komawa cikin uƙubar da ta
fito ba"
Maami ta ƙarasa da alhini, da sauri Alayah ta rungumeta
"Na gode Maami mun gode sossai Allah ya saka miki da alkhairi, Allah ya biya miki
buƙatunki na alkhairi ya saka ki cikin aljannah maɗaukakiya"
Har lokacin bata daena hawaye ba, tana cikin wani sabon damuwar duba da yadda
saɓani ke shirin shiga tsakanin Maami da Abban saboda su kuma.
Jan ta Maami tayi zuwa ɗakin da aka kwantar da ummin, daga jikin window suka tsaya
Alayah ta ɗaura hannunta bisa kai tana sake zub da hawaye, ummin ta ce haka? Me ya
faru bayan barin ta gidan? Taya duk waennan abubuwa suka faru ba tare da ummin ta
sanar mata tun wuri ba? Ummin ta aka bari da najasa Allah andi tsawon lokacin da ta
ɗauka a hakan, kuka ta sake saki.
"Ashe ba zaki ji magana ta ba Binty? Ban ce ki daena ɗaga hankalin nan ba saboda
yanayin ki? Toh shikenan kiyi ta yi"
Ta ƙarasa tana juyawa alamar tayi fushi da sauri Alayah ta riƙe hannunta tana
anfani da ɗayan hannun wurin share hawayenta tace
Bayan tsawon lokaci hira tsakanin en uwan na tashi Aisha ta dubi Maami tace
"Adda Bintu yanayin ki kaman kina cikin damuwa, Mukhtar ne?"
Girgiza kai tayi sai yanzu ma ta tuna da Mukhtar din tun jiya bata ganshi a nan ba,
ta san ba zai taɓa chanzawa ba ai.
"Aisha wato dukda abubuwan Mukhtar na damuna sai dae abinda ke damuna a yanzu ya
shallake wanchan, na rasa wani hanya zan bi wurin shirya tsakanin Umar da
mahaifinsu da basa jituwa sam sam, Dukda ban taɓa ganin laifin umar ba duk na Abban
nasu ne sai de abin na ci min rai sossai wallahi"
Ruqayya tace
"har yanzu ne rashin jituwar nasu? Na zata bayan doguwar nasiha da faɗan baba komai
ya wuce?"
Maami tace
"kusan an samu sauƙin hakan amma daga sadda umar ya kama masa wani kaya ya kirashi
ya cicci mishi mutunci shi kuma umar yayi rantsuwar har Abada idan har zai yi wani
hulɗa da ya shafe lalata rayuwar al'umma ba zai taɓa bari ba, daga shi har Mukhtar
ko inuwa basa haɗawa dashi saboda kowa da abinda ya fassara irin kariyarshi, yana
nuna jarumta akan lamarin sai dae na lura abin na damun shi shiyasa sam baya son
zaman ƙasar nan"
"Ya cigaba da haƙuri wata rana duk zasu fahimce shi in shaa Allah, yanzu ki duba
irin taimakon da yayi a kan baiwar Allahn nan, kina tunanin ko Abbansu Mukhtar ya
isa fidda matar chan daga gidan Hassan a yadda ya kafa tarko yake kuma da gogewa da
duniya? In ba irin umar ba bana tunanin zata tsira cikin sauƙi haka"
Cewar ruqayya a hankali.
Aisha tace
"Allah ubangiji ya kyauta amma tabbas akwai wata rana da duk zasu yi nadamar hakan"
Lumshe idanu Alayah tayi ta sake maimaita sunan Umar a ranta, ya taimaketa ita kam
bata da abin da zata saka mishi anan duniya sai dae da Adu'a, lallai zuciyarshi a
wanke take ko bata ganshi ba tunda zai iya saka hannu ya ɗauki umminta cikin najasa
ya sakata a motar shi har ya kawo ta asibiti bayan ya fuskanci barazana daga Abban
Jameelah.
A haka bacci ya sure ta, bata farka ba sai dab Magrib, a hankali take motsi ta ɗan
shaki numfashi tana jin kamshin turaren da taji rannan a sashen Maami me daaɗi,
waigowa tayi don ganin me wannan kamshi sai suka haɗa idanu da Mukhtar, wani
kakkauran miyau ta haɗiye cikin kokarin danne fargaba da tsoron da ya bijiro mata
musamman idan ta tuna abinda ya mata kwanaki a asibitin chan da aka mata aiki.
*Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same
shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi
09039206763*
#Vote
#comment
🖤Gureenjoh🖤
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
*Rubutu a kan ruwa... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*
*BOOK 1*
*Page Sixteen*
*Na riga na yi alkawari in ba haka ba ina zan iya typing karfe 12🥲 sorry guys class
nayi da ba zan iya dodging ba*
Da yammacin ranar aka bata sallama, gida suka dawo Dukda ta so tsayawa asibitin sbd
ummin ta amma kuma ba hali don har yanzu tana ICU ne ba'a yarda ba ma da isa kanta
bare a fara jinyar ta, likitoci da nurses ne kaɗai ke zuwa kan ta, ko da suka koma
gida ma bata bar zazzabin laulayi ba, kuma ta fahimci har lokacin babu shiri
tsakanin Maami da Abba kai tsaye zata iya cewa sune sanadi, iya kokari Maami na yi
wurin nuna mata komai lafiya ai dae bata san ta riga ta fahimta ba.
Kwance take kan kujera hannunta yalo ne take ci Dukda wani irin zazzabi da ya
rufeta tana dukunkune sai rawan sanyi take kuma ta ƙi kashe Ac ko rage wa, Maami ta
fita sai mama lami ne ke zuwa jin ko akwai wani abin da take buƙata ta kawo mata,
bacci ne ya fara fusgar ta sam bata san Shigowar mutum ba ashe har ya kashe Acn
bayan taɓa fuskanta da yayi ya ji jikinta raurau, baya baya yayi ya zauna kan
kujera Red eyes ɗin shi ya zuba mata a ranshi yana ayyana dama haka mata suke fama
ne ko ita ce kaɗai?
Tun da aka ce tana da cikin nan ba zai ce ga sadda ya risketa lafiya ƙalau cikin
ƙarfi da kuzari ba, ko yaushe gata nan dai ajiyar zuciya ya sauƙe a hankali yake
jin duk wani rayuwarshi na baya ya fita kanshi fit, iya kokari yayi na daina shaye-
shaye haka matan ma rabon shi da mace zai iya cewa ya manta, bashi da wani aiki sai
na tunanin wannan yarinyar, wani sa'in ma yana son zuwa ɗin ya kalleta sai kuma
wani sashe na zuciyarshi ya mishi nauyi, kunyar Maami ya lalaɓo ya rufe shi ruff ta
yadda baya so ko haɗa idanu su yi.
Shisha Pen da smart ya bashi ya fitar yana ɗan jujjuyawa sun ce zai rage mishi
wannan damuwan da ya shiga a kwanakin sai dai yana shakka don ya san zasu iya sa
wani abu na bugarwa ciki, bakinshi ya kai kaman ya sha sai ya ja tsaki yana ƙoƙarin
sauƙewa suka haɗa idanu, girgiza kai tayi tare da Miƙewa bata ce mishi ci kanka ba
ta zo zata wuce yayi saurin riƙe hannunta kula da yayi kaman ranta ya ɓaci kuma
hakan ya nuna har a fuskanta, fisgewa taso yi ta mance ma riƙon maza ba irin na
mata bane...wani zafi ne ya ratsa ta mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin shanu
a take ta fashe mishi da kuka sossai har sai da ya tsorata.
Kaman wadda kwai ya fashewa a ciki haka yake jan kafafunshi jin gwiwowinshi na
shirin sagewa su butulce mishi wurin kasa ɗaukar gangar jikinshi, zubewa yayi kan
kujera zuciyarshi na wani irin yamutsuwa tare da kwakwalwan kanshi dake ta aikin
tariyo kalamanta, wani irin sanyi yaji yana ratsa shi a hankali zazzafar zazzabi ya
soma sauƙo mishi, kalamanta sun mishi nauyi sossai, rashin fahimtar shi da bata yi
ba sai ya so haukata shi,
Miƙewa yayi don barin gidan ko zai shaki iska mai kyau sai ga Maami ta shigo.
A hankali yace
"sannu da dawowa Maami"
Kallon shi tayi da mamaki don ba halin shi bane hakan, sai kuma ta kula kaman bashi
da lafiya ne kaman bazata yi magana ba sai kuma tace
"yauwa! Lafiya kake kuwa? Ko dai cikin shaye-shayen ka shayo abin da yafi karfin
ka?"
Idanunshi ya runtse da ƙarfin gaske wani zafin ya sake ratsa zuciyar shi, dama haka
ake welcoming wadda ya ɗauki hanyar tuba? Dama wannan na daga cikin kalubale da
illar shaye-shayen ko kuma daga mahaifiyarshi da matar shi ne?
Be iya ya tanka ba ya fice daga gidan, da kallo ta bishi har ya bace kan ta haura
stairs, ɗakin Alayah ta tura don dubata sai ta sameta zaune tana game a wayanta
kaman ma bata yi kukan matsalar gidan aurenta ba, taji sauƙin abin sossai da ta
samu fitar da abin da ke ranta kuma da gaske ta gama zama da Mukhtar.
"Sannu da dawowa Maami"
"yauwa binty ana hutawa ne?"
Kai ta gyaɗa tana murmushi
"Maami kin yi waya da asibitin? Sun yarda zasu bari a ganta nan kusa?"
Kai ta gyaɗa tace
"Eh mun yi magana, baba ma dai ya bada shawarar a fitar da ita waje kawai amma dai
muna nazarin hakan da umar, kar ki damu zata samu sauƙi in shaa Allahu. Yanzu dae
albishir"
Da dare ta isa jikin kofa don rufewa kenan taji kaman ana magana murya sama,
idanunta ta lumshe babu shakka muryan Abba ne kuma ta tabbatar da Maami yake don
kaman magana ne da ya dangancesu Dukda bata jin shi clearly, da jikin kofan ta
jinginu ba zata taba son su kasance tasgaro ga rayuwar Maami ba, ita ce mutum na
farko a rayuwarsu da ta nuna musu suma mutanene kaman kowa suna da muhimmanci kuma
suna da Ƴancin rayuwa yadda kowane mutum ke yi, ita ta basu mafaka a sadda suke
tsakiyar rana da kunar zafin ta, da ba don ita ba da kila yanzu babu Umminta don ta
tabbatar ba jinya Abban meela ze yi mata ba, sannan ga damar karatu ta bata wadda
zai sauya mizanin rayuwarta, amma su kuma suna kokarin dakile farin cikinta da
zaman lafiyanta, tana jin irin barazanar Abba har da aurenta yayi mata kan ya zo ya
wuce kaman iska.
Ta jima tsaye wurin kan ta isa ga gadonta ta kwanta idanunta runtse tunaninta ya
tafi gabaɗaya ga neman mafitar wannan matsalar kuma, cikin bacci ta ji ana buga
mata da sauri kuma a ɗan tsorace ta miƙe zaune, idanunta ta kaikaya kan ta sauko
gabanta na faɗuwa ta tsaya nesa da kofan
"wa....waye?"
Shiru aka yi sai aka sake knocking
"waye ne?"
****
Zaune su ke a club ɗin shi dae ko idanunshi baya buɗewa in banda ma matsawar su
Nawwaz babu abin da zai kawo shi club ɗin amma sune kaɗai abokan shi su ne masu
debe mai kewa cikin sabuwar rayuwar da ya tsinci kanshi, En matan dake ta damunshi
ne ɗaya ta matso ta shafa shi
"Mukhy whats wrong with you? We dont like this mukhy we want our old mukhy back,
menene kake so? Ka zo mu debe maka kewa mu mantar da kai duk wani damuwa, mu baka
farin cikin da ka jima baka samu ba..."
Hannun da take shafa shi ya ture ba tare da ya buɗe idanun ba
"don't you dare touch me again"
Ya faɗa chan ƙasa ƙasa har yanzu kalaman Alayah ne ke farautar rayuwarshi,
idanunshi ya buɗe ya sauke kan smart dake rungume da yarinyar da ta gama lafaza shi
a yanzu tsaki ya ja me karfi barikin fa kenan, Tsam ya miƙe tare da miƙawa smart
din hannu ya bashi key.
"Wlh ban sani ba mukhy ko zaka duba mana don ko na je babu abin da idona zai gani?"
Gaban motar ya buɗe ya fice yayin da smart ya buɗe mai bonet daga ciki, ganin ya
ɗan jima yasa duk suka fito, wurin shiru sannan hasken wurin ba sossai bane, layi
ne a chakude da gidaje kala uku akwai na masu kuɗi jefi jefi haka akwai na daidai
misali sai kuma na talakawa da suka fi yawa.
Wata yarinya ce da bata wuci 16 ba ta taho hannunta riƙe da tray tana kuka, kuɗin
cinikin ta ta ɓatar gashi matar ubanta bata da sauƙi akan sana'arta shiyasa ta kai
yi warhaka bata koma gida ba, ta sa baban ta da Yayanta yanzu sun dawo idan kum
yaddikonta ta kanainayesu da maganganun ta ɗaure ta zata kara yi yau ta shiga uku
da babanta tunda duk abinda yaddikonta ta faɗa daidai ne, har ta wuce su ma bata
maida hankali kansu ba sbd nata matsalar.
Nawwaz ne yace
"kai yarinyar nan tayi smart, anya ba zamu latsa ba?"
Area ɗin suka dudduba jin shiru sossai yasa babu wani tunani yadda suka saba
kayansu sa'i da lokaci suka bi bayanta, da bakinta suka fara da karfi suka ɗaure
suka jata gefen ciyayi, sam Mukhtar be san me suke ba don hankalinshi na kan duba
motar sbd babu abinda yake so a yanzu irin ya je gida ya kwanta ya cigaba da
tunani.
*karku manta book 2 na kuɗi ne, muna gama book 1 zamu ɗaura in shaa Allah zaki iya
yin payment ɗin ki anan kan a gama ɗin
0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin
Sai shedar biya ta
09039206763 in shaa Allah za'a saka sunan cikin list na paid da muke dasu ƙasa.
Thank you sai na ji ku
🖤Gureenjoh🖤
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
*Rubutu a kan ruwa... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*
*BOOK 1*
*Page Seventeen*
"Me kuka aikata Nawwaz? Akan me zaku yi raping yarinya alhali kun bar yammata sama
da hamsin waenda suke shirye da tayin ku? Why? Why??"
Gabaɗaya hankalin shi ya tashi irin yadda ba'a zato, su karan kansu sun shiga
mamaki, sun ga dae har a ƙasar da ma ya fi Nigeria tsaro da komai yayi raping
yarinya wanda ma sanadiyar zamanshi prison kenan har aka kore shi ya dawo Nigeria
da karatu, to me zai dame shi anan da ma ba lallai a bi diddigi ba ko ma an bi suna
da kuɗi wadda sun tabbatar a ƙasar nan zai musu maganin komai.
Ganin suna kokarin tursasashi maida komai ba komai bane yasa ya daka wa smart
tsawar ya tsayar da motar kuma su fitar mai daga cikin mota, haka ya baɗe idanunshi
da toka sai da suka fita ya zagaya ya figi motar kaman baya son ranshi, har lokacin
wani irin tension yake ji a cikin jikinshi gidanshi ya ƙarasa a parlor ya zube, ya
rasa ma kalar tunanin da zai yi me yaran nan suka aikata haka?
Bai san iya adadin lokutan da ya ɗauka a haka ba, a hankali ya buɗe idanunshi da
suka sake shanyewa wayanshi ya zaro ya duba sai ya ga biyu saura, contact ɗin shi
ya shiga ya samo Layin Maami ya zubawa idanu, a hankali abinda be taɓa zaton ze yi
ba a rayuwarshi tun tashin shi wato hawaye ya cika idanunshi, damuwar da yake ciki
yana son jin ko da muryarta ne kila ya samu sassauci, kira ya danna mata ya zubawa
wayan idanu ba lallai ta ɗauka ba, dab zai tsinke ta ɗaga, a hankali ya sa a kunnen
shi ya ji muryarta cikin bacci tana furta
"Assalamu Alaikum warahmatullah Mukhtar? Lafiya?"
Idanunshi ya runtse hawayenshi suka zubo, a hankali yace
"Wa'alaikissalam warahmatullah Maami..."
Sai yayi shiru ya rasa ma me zai ce mata, bayan duk abubuwan da ya mata a rayuwa ya
kuwa chanchanci ta taya shi shiga damuwa saboda damuwar shi?
"Uhmm ya aka yi? Menene?"
Uwa kenan, ya faɗa a ranshi yana sake jin wasu sabbin hawayen sharr, zuciyarshi na
wani irin chunkushewa cikin tsananin damuwa da karaya, gaɓɓan jikinshi duk sun yi
sanyi saboda rashin natsuwa da bashi dashi gabaɗaya kwanakin, har zafi zafi yake ji
a cikin jikinshi kaman me masassara.
"Maami ina cikin damuwa ne, na kasa bacci, na kasa samun natsuwar zuciya na rasa
abin da zan yi na ji daaɗi, ki taimake ni please"
Wani abu taji ya tsarga mata har cikin ranta, Allah sarki uwa bata san ta miƙe
zaune ba, a hankali tace
"baka da lafiya ne? Ka je asibiti?"
Girgiza kai yayi
"Maami lafiyata ƙalau kawai komai ne baya min daaɗi Maami"
Shiru tayi na seconds kan a hankali cikin son tabbatarwa tace
"ka sha wani abu ne da ya fi karfin ka ko?"
Da karfi ya runtse idanunshi dama ya san zata yi tunanin hakan, kuma ya ji a
jikinshi ba zasu taɓa fahimtar nadama da tuban shi a kusa ba, yayi mamaki ma da ta
saurare shi, a hankali yace
"Maami wallahil azeem rabona da in sha wani abu tun ranar da muka zauna gaban baba"
Nannauyar ajiyar zuciya da har ya ji daga inda yake ta sauƙe.
"Ka je kayi alwala ka faɗawa Allah matsalolinka in shaa Allah zaka samu natsuwa"
Kai ya gyaɗa kaman karamin yaro kan yayi mata godiya suka kashe wayan a tare,
Miƙewa yayi ya nufi ɗakinshi har ya shiga sai kuma ya tsaya kaman me nazari,
wardrobe nashi ya nufa ya duba ya ɗauki three quater da wani armless Black shirt
tare da sabon towel ya fice daga ɗakin don be yarda da ɗakin ba har wani kyamar
ɗakin yake ji.
Ɗakin Alaya ya shiga lumshe idanu yayi yana sake jin sabon hawayen tausayinta, anan
ya mayar da ita prisoner a cikin wannan ɗakin ya shigo ya jata gaban abokai ya ɗura
mata abin maye ba tare da ya damu da cewa ita ɗin tsarkakkekkiya ba ce, bayin ta ya
nufa yayi wanka ya sanya kayan ya zo ya tsaya kan sallaya, a hankali ya ji Muryarta
a sadda take ce mai a lokacin da ya ɗauketa daga asibiti zuwa Hotel zai yi sallah.
"Ya Mukhtar namiji fa daga cibiyar shi zuwa guiwowinshine al'auranshi, Kaga zaka yi
sallah kuma wandon be kai guiwa ba be kamata ba"
Yana iya tuna yadda take mai magana a lokacin ma cike da tsoro.
Ɗakinshi ya koma jallabiyar nan da Dr ya taɓa bashi kyauta ya ɗauka ya saka kan
kayan ya dawo ɗakin ya kabbara sallah cike da Fatan Allah ya amsa ya sassauta mishi
abin da yake ji yana damunshi.
***
"Ki buɗe"
Abin da taji kenan da ya sanya gabanta dokawa.
Cikin rawar murya tace
"Abba? Lafiya?"
A harzuke yace chan ƙasa
"na ce ki bude kofar nan"
Hannunta na rawa ta buɗe da sauri ta ja baya ganin ya afko ya rufe
"ke! wace irin mutum ce ke? Dama Alhassan ya min gargadi duk inda kuke babu
alkhairi a tare daku musamman ma ke, kin san me kike shirin aikatawa?"
Girgiza kai tayi tana jin tashin hankali na bijiro mata.
"Zaki kashe auren macen da ta taimake ki ta taimaki mahaifiyarki ta so ki tsakani
da Allah, kin mata adalci kenan? Kin san me uban su ya fi tsana? To babu abin da ya
ƙi jini a duniya irin saki, barin ma na ƴar cikinshi, me kike tunanin zata fuskanta
ta koma ga mahaifinta tsofai-tsofai da ita da takardar saki?"
Zuwa wannan gaɓar tuni hawaye ya wankewa Alaya fuska, sai ta ji murnar karatunta ya
koma ciki, in tayi wa Maami haka bata kyauta ba, sai dae ina zasu je? Ya zata yi da
ummin ta?
Kaman ya shiga zuciyarta yace
"Zan ba ki makudan kudade da zai ishe ku rayuwa, kuyi nesa da mu da rayuwarmu dama
Mukhtar ba soyayya tsakaninku zan sa shi sakin ki a gobe ku yi nesa da mu na har
abada"
Kanta ta mayar ƙasa hawaye ya silalo mata.
"Kin amince?"
Kai ta gyaɗa a sanyaye
"daga yau bana so ki sake kwanar min cikin gida a gobe zan sallame ki"
Yana kai nan ya juya ya buɗe kofa ya fita, a wurin da ya barta ta sulale ta zauna
tare da fashewa da kuka, sake tura kofan da aka yi ne yasa tayi saurin ɗagowa a
firgice ta miƙe tsaye!
****
Mahaifin wannan yarinya da aka yiwa fyade ne ya riƙe hannun Yayanta dake kuka kaman
ranshi, a hankali cikin lullube tsananin tashin hankalin shi yace
"karka taɓa ta Bashir, barta bari na ƙira dan uwana"
Cousin nashi ne comissioner of Police iyayensu mata sun haɗa uba, kuma kusan kaman
abokai suka tashi Dukda tazarar arzikin ubanninsu ya banbanta nesa ba kusa ba,
ringing uku ya dauka
"Ɗan Uwana yau kuma da mu aka tuna?"
Hawaye ya sirnanowa dattijon cikin karaya yace
"Ɗan Uwana wannan kiran na neman agaji ne, ka taimakeni ina da da bukatar ka a
yanzu, an wulakanta ni an tozarta rayuwar ƴata an illata min yarinya"
Hankalinshi ya dugunzuma ya tashi jin dattijon na kuka sossai, tabbacin gashi nan
ya bashi da ambulance bayan jin mummunan ta'asar da aka yi mata.
Ba'a fi awa ɗaya ba sai gasu har lokacin daga baba har Bashir an rasa me ba wani
haƙuri sai kuka suke yi, da ambulance da wasu polisawa aka zo, Allah sarki yarinya
abin tausayi haka aka ɗaga ta zuwa motar asibiti da wasu Police mata ya haɗa su
inda ya tsaya gun ɗan uwanshi don jin kanun zancen.
Be ɓoye mishi komai ba duk ya faɗamai har da plate number ɗin, kwarai ya jinjina
kokarin baban a take a daren suka soma bin hanyoyin da duk za'a bi don gane me
wannan motar, abin ka da comissioner of Police ne ke ciki tsundum ba'a kira
assalatu ba sai da aka gano motar Mukhtar ce, su ba ɓoyayyun mutane bane, don haka
a take ya bada umarnin a je a kamo mishi Mukhtar dama kuma yana da ajiyayyen record
a interpol, me hali ba zai taɓa fasa hali ba, maza maza a kawo shi.
Makara yayi, a sadda ya buɗe idanunshi yaji ana sallama a masallaci, da sauri ya
miƙe be tsaya wanka ba yayi alwala ya taho ya zo yayi sallah, anan ya zauna duk
wasu Adu'o'i ba wai ya iya bane tunda karatun islamiyyar shi na je ka na yi ka ne
yayi, zafin mahaifinshi yake ji har ranshi, yana tuna a lokacin in an bugeshi ya ce
ba zai kara zuwa ba Maami na masifa haka Abba zai baɗe idanunshi da toka ya bashi
goyon baya kuma ya hana shi sake zuwa sai ranar da ya ga dama, yana tuna har a gida
an sha kawo malamai musamman don shi yana korarsu da sharri kala kala Abba be taɓa
cewa hakan ba daidai bane, be taɓa gyara mishi ba, be taɓa tsawatar mishi ba...
Door bell ake ta dannawa wanda hakan ya sa ya miƙe yana duba time, shidda ma be
cika ba lafiya?"
Yana isa ya buɗe sai idanunshi suka sauƙa kan polisawa kusan guda biyar dake
tsatsaye gaban kofan parlorn they are even armed gasu manya manya, murmushin
takaici yayi dama ya san hakan na iya faruwa, sai dae kuma gabanshi dake ta faɗuwa
da tsoron halin da zai jefa Maami da Alayah idan maganan ya riske su, karamin ciki
ne da ita idan yayi sanadin shi fa? Sai yanzu yake jin wani irin son abun cikin
nata na shiganshi, bakin Police ɗin ya zubawa idanu a sadda yake cewa
"Mukhtar hammad you are under arrest for the suspect of rape, u have the right to
keep quit as anything you utter will be Proof against you in d court"
Hannayenshi ya dunkule ya miƙa musu suka sanya ankwa, sai da suka fito ya ga ashe
akwai wasu zagaye da motar da ya dawo dashi jiya, daga shi har motar aka ja sai
Police station.
*Kuyi hakuri da Page na yau, ban wani zauna bane. Thank you*
*karku manta book 2 na kuɗi ne, muna gama book 1 zamu ɗaura in shaa Allah zaki iya
yin payment ɗin ki anan kan a gama ɗin
0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin
Sai shedar biya ta
09039206763 in shaa Allah za'a saka sunan cikin list na paid da muke dasu ƙasa.
Thank you sai na ji ku
🖤Gureenjoh🖤
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
*Rubutu a kan ruwa... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*
*BOOK 1*
*Page Eighteen*
"Maami"
Ta kira sunan da tunanin kar ta ga fitan Abba daga ɗakin nata ne, gabanta ta iso ta
riƙo hannunta..
"Binty me ya faɗa miki?"
Shiru tayi kanta ƙasa ba tare da tayi magana ba sai hawayen da ya cigaba da zuba
mata
"kar ki damu na jima da tashi sanadiyar kiran Mukhtar to sai na kasa komawa bacci,
ina cikin nafila na jiyo motsi da kuma buɗe kofa hakan ya sa na fito, har ya fice
bai san da tsayuwata ba kuma ba zan taɓa faɗa mishi na ga zuwan shi ba, abinda
kawai nake son sani shine me yake so da ke?"
"So yake mu yi nesa da ku"
Girgiza kai tayi ta sake riƙe mata hannu
"kar ki ɗaga hankalinki Alaya, ban shigo rayuwarku don in lasa muku zuma a baki in
kuma janye ba, na san kila har barazanar da yayi mini ɗazu ya faɗa miki don ki ji
ba daaɗi karki damu na fi kowa sanin Alhj, gidan shi dae zaki iya bari amma ba dae
rayuwar mu ba, mun riga mun zama en uwa, har gobe ni matsayin uwa nake a gareki
yaya a wurin umminki kinji?"
Rungume Maamin kawai tayi tana murmushi me haɗe da hawaye, Maami ta zama komai na
rayuwarsu, da gaske Allah ya turo musu ita ne don ta taimaka musu ta fitar da su
daga uƙubar da suke ciki, lallashinta Maami tayi ta yi har sai da ta ga ta koma
bacci kan ta fice daga ɗakin, bata iya ta yi baccin ba ita kam haka ta kwana kai wa
Allah damuwowinta, da asuba tare da masu aikinta ta shiga kitchen suka kama aikin
breakfast, tsab suka gama ta bar su su shirya ta haura sama tayi wanka, tana fitowa
Alaya ma na fitowa, gaishe ta tayi ta amsa fuskanta da fara'a as always tana mata
ya jiki, ita dae Alaya na matuƙar mamakin hallayyar Maamin sam bata yarda da sa
damuwa a ranta har ya nuna ga fuskanta ba.
Suna isa dining da niyyar cin abinci sai ga Abba ya shigo, Maami ne ta fara gaishe
shi ya amsa ba yabo ba fallasa, Alaya ma ta gaishe shi ya amsa da kyar, Maami ce
tayi serving nashi ya ja gabanshi ya soma ci, ita dae Alaya juya spoon ɗin kawai
take kaman yadda ta kula Maami ma ba wani cin kirki take ba, Tv dake aiki daga
parlor ne aka soma labaran safiyar...
Da wani hanzari duk su uku suka miƙe tsaye, Abba ne gaba wurin isa cikin parlorn
daidai me kanun labaran na cewa
"Mukhtar dai ɗa ne ga ɗan takarar Gomna wadda aka fi sani da honourable Hammad
Abdulhameed chanji... In ba'a manta ba Mukhtar dae na da tabo a hukumar na en sanda
inda ya ci firsuna na wa'adin shakaru takwas a ƙasar waje to dai gashi nan labari
ya sake maimaita kanshi ku biyo ni don jin cikakken labarin"
Kokarin zubewa ƙasa Abba yake Maami da ita ma take jin bata da wani karfi, firgici
da damuwa haɗe da wani irin tashin hankali suka rufeta tayi kokarin tura shi a
madadin ya kai ƙasa sai ya zube kan kujera yana jiƙewa da wani gumin tashin
hankali.
Alayah ce da ita ma karfin hali tayi wurin riƙe Maami suka zauna a tare, babu wadda
ya iya magana sai tvn da suka ƙurawa idanu suna jiran kanun labaran kaman kuwa a
mafarki aka hasko hannayen Mukhtar ɗaure da ankwa
"A safiyar yau ne en sanda suka yi tattaki har gidan ɗan ɗan takarar nan honourable
hammad Abdulmajeed chanji wato Mukhtar hammad chanji inda babu ɓata lokaci suka
kame yaron nashi bisa zargin aikatawa yarinya karama ƴar shekara 16 fyade a daren
na jiya, inda suka bar yarinyar cikin mawuyacin hali ga wakiliyar mu nan daga
asibitin da aka kwantar da yarinyar"
A take aka hasko iyayen yarinyar mahaifinta na kuka, haka en uwanta tsiraru da suke
asibitin ɗaukewa aka yi aka dawo kan ɗan jaridan ya cigaba da cewa
"a wannan lokaci da siyasa ke gab da wanzuwa a jibi jibin nan jama'a dayawa da suke
ƙarƙashin tafiyar ta honourable sun soma janyewa, ga kaɗan daga bakunan jama'ar"
Wani aka hasko yana cewa
"mutumin da ya gaza ba ɗan shi tarbiya taya zamu yi zaton zae tafiyar da mulki,
wannan halaka mu zai yi bama yi.."
Na bayanshi suka amsa da bama yi bama yi, aka sake hasko wani haka dae aka yi ta
hasko mutane suna fadin albarkacin bakin su duk babu wani daaɗin ji..
Wayan Alhj en jam'iyyarsu suka soma kira sai dae motsin kirki ya gaza, jikinshi
banda rawa babu abin da yake, shikenan abin da yake gudu yana tunanin yana da ikon
dakatarwa ya faru, wannan shine ta faru ta ƙare ga ƙoshi ga kwanan yunwa! Ya gama
shiryawa da Alhj Hassan akan in ya kori su Alayah dole in sun tagayyara su koma
mishi tunda shi kadai suka sani sai gashi ɗan da ya fifita ya ɓallo mishi ruwa,
ruwan da zai mishi ɓarnan da baya tunanin zai taɓa taruwa ɓallewa zai yi ya shiga
gari, da sauri ya ɗauko wayanshi dake ringing ya duba, chairman na party din su ne.
Wani irin faɗa yake da masifa, akan me Abba ba zai tare danshi ba in ya san bunsuru
ne yanzu suna ji suna gani haka partynsu zata ci kaye, sun yi duk yadda zasu yi sun
danne batun baya amma wannan ya tashi musu kamar wutan daji kowa sai gani yayi a
duniya, shi dae ya kasa cewa komai tunda hankalin Ƴan partynsu ya riga ya tashi
haka wannan abu ba mai gyaruwa ba ne, Maami da ke zaune kaman mutum mutumi da Alaya
da kanta na ƙasa zafin da ranta yayi ba sossai ba tunda dama ta riga ta cire rai da
Mukhtar ta san ba zai taɓa gyaruwa ba, girgizan da tayi ma na don abun cikinta ne,
hannunta dafe da cikin tana tunanin me wannan ɗa zai ɗauketa a rayuwa? Kawai sai
faɗuwar Abba suka gani...
****
****
Daga Maami har Alayah babu wadda ya motsa tun da suka shigo asibitin, dangin Maami
da na Abba na nan birjik Abba na halin mutuwa ko rayuwa sbd jininshi da yayi
hitting fiye da ƙima, Ƴan uwan Maami sai jimami suke yayin da Ƴan uwan Abba ke jefo
kananun maganganu wadda kai tsaye Maami suke alaƙantawa da lalacewan Mukhtar, ita
dae tana jin su bata tanka ba kuma ta gode Allah da yaddikonta dake wurin ta hana
duk sisters din ta magana, Baba ne ya shigo ward ɗin da sauri Maami ta miƙe ta isa
gabanshi hannunta ya riƙo
"Faɗimatu!"
Kaman jira take ya kira sunanta kawai ta zame ta fashe da wani irin kuka dake cin
ta a rai, Mukhtar kila sai ya kasheta ne hankalin shi zai kwanta, in ta bar mishi
duniyar sai ya fi jin daaɗinta, zuciyarta ya riga ya kuntata fiye da tunani, ita
kaɗai ta san me take ji a ranta kunnuwanta kawai ke jin duniya gabaɗaya na tsinewa
Mukhtar, kukanta sai da ya sa mutane dayawa kuka ciki har da Alayah, mahaifinta ya
ɗago ta suka isa kujerun gefe guda suka zauna nasiha ya dinga yi mata akan
jarabawar Allah, har misali yake bata da ƴaƴan annabawa suma Allah be bar su ba, ko
ta manta jinin Annabi Adam shi ya fara kisa a duniya? Ta mance ƴaƴan annabi Yakub
ɗan uwansu suka so halakarwa mahaifinsu yayi kuka har idanunshi suka makance? Ko ta
mance ɗan annabi nuhu da ya kafurce yayi ikirarin hawa tsauni zai taimaka mishi
wurin gujewa fushi da azabar Allah kuma Allah ya halaka shi a kan idanun
mahaifinshi? Ta natsu ta cigaba da Adu'a idan yana cikin masu shiryuwar Allah zai
shirya shi, sossai hankalin ta ya kwanta da nasihun baban, inda ya duba jikin Abba
kan ya ɗauki yaddikonta suka tafi kafin ya tafi sai da ya sake kwantar musu da
hankali ita da Alaya.
Masallacin asibitin suka je suka gabatar da azahar, Adu'a sossai Maami tayi kan
suka fito zuwa ɗakin abinci da aka yi ta kawowa ta saka Alaya a gaba ta ci ita kuma
ta sha baƙin shayi, call ne ya shigo ma Aunty ruqayya ta duba kan tace
"Allah sarki umar ne, kila labarin ya je mishi hankalin shi kuma zai dawo kan Adda
ruqayya gashi jiya jiyan nan da safe ya koma"
Maami ce ta mika hannu ta karɓa dama ita ma tunanin shi take a ranta, ɗagawa tayi
tare da Miƙewa ta matsa daga inda suke sun jima sossai suna magana kuma shi ma ya
sake bata kwarin gwiwa, so ma yayi ya zo Dukda ba don Yayan shi ko Abbansu zai dawo
ba don Maami ne kawai to amma ba zasu bar shi a wurin aiki ba, abubuwa dayawa na
hannunshi.
"Babu wata uwa da zata yi farin ciki da lalacewan ɗan ta, amma ko babu komai yau na
ji daaɗi da muka raba ɗacin lalacewar Mukhtar wadda kai ne sanadi, ko babu komai
Allah ya nuna maka ba sai ka zalunci wasu ne zaka yi nasara ko ka fadi ba, Allah
baya zalunci kuma ba ya barin me yi, ko ka nufi gyara kuskuren da ka tabka daga
yanzu ko kuma ka cigaba da girban abin da kai ka shuka dama na sha faɗa maka akwai
ranan ƙin dillanci"
Tana kai nan ta juya ta fice tana goge kwallar ta, idanunta ke haska mata kaman yau
ne tana shirin tarbiyatar da yaronta Alhj na rusawa daki-daki, shi karan kanshi be
ga laifinta ba sai ma kunya da nauyi da suka rufe shi, idanunshi gabaɗaya sun rufe
ya cutar da rayuwar Mukhtar sossai wadda sai a yanzu yake jin be kyauta ba, kunyar
mutanen duniya ya rufe shi, tsoro da shakkar kamuwar tsinuwar bakinsu ya lulluɓe
shi, shine da kaso mafi tsoka ya sani amma shi a ganinshi duk soyayya ce ashe ba
haka ba ne, hawaye ne ya gangaro mishi.
"Yaya ka yi haƙuri kayi kokarin cire damuwa a ranka in shaa Allah komai zai wuce"
Zaid ya faɗa, murmushi kawai yayi me ciwo be sake cewa komai ba.
****
C.P ta kaiwa report din yana dubawa yace a je a sake tuhumar muktar har sai ya faɗi
sauran, duk yayi ignoring calls da yake samu daga sama saboda wannan case ɗin ba
mai kasuwa ba ne, ko ba familynshi aka taɓa ba sai inda karfinshi ya kare bare na
gida ne, cikin kokarin cika umarni wasu daban suka sake nufan ɗakin na Mukhtar don
tambayar shi da kyau..
🖤Gureenjoh🖤
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
Book 1
*Page Nineteen*
*Assalamu Alaikum warahmatullah, Fatan duk muna lafiya? Ina ganin ya kamata mu
dinga yiwa juna adalci, ina nufin tsakanin makaranta da marubuta, lallai a tafiyar
da muke zuwa yanzu na fahimci cewa makaranta ku ke da kaso mafi girma na sanya
marubuta aran halin da ba nasu ba su yafa, kuma kun fi kowa yayata cewa marubuta na
da girman kai, this and that, ina magana ne based on experience ba da ka ba so duk
wadda be ji daaɗi ba yayi haƙuri kuma a gyara, Marubuci zai ɓata lokaci kwarai
wurin bincike da rubutu, ya kashe duk wasu abubuwa masu muhimmanci nashi ya zauna
don faranta muku dayawa kuna bibiya kuma ana ƙaruwa amma kalmar an gode ma ya zama
matsala bare comment, ana tafiya dai a haka saboda burin kowani marubuci ya isar da
saƙon da zai anfani al'umma, muna cikin wannan tafiyar na ce yarona ba lafiya zan
kai shi asibiti billahi wasu ba su iya cewa Allah ya yaye ba, amma suna gaba gaba a
wurin bi na Pc ana cewa ana ta jira shiru, a'a ana kashe musu kwarin gwiwar karatu,
an shanya su this and that! Sister ashe babu daaɗi? Yanzu idan na buɗe na ga wannan
saƙo saboda bin cewar Manzon Allah na ka faɗi alkhairi ko kayi shiru na ƙi magana
sai fa a ce girman kai ne ko wulakanci ko? Toh Allah ya kyauta. Na kawo wannan ne
ba don rashin ɗa'a ba don nan ɗin gidan tarbiya ne ba haufi sai don mu tattaru mu
gyara, mu zama masu adalci a tsakanin juna, adalcin ne yasa duk ba zan yi Page ba
sai na zo na faɗi dalili, don Allah mu karfafawa juna gwiwa wurin zamantakewa da
kuma cigaban juna don kowa na da ƙaruwarshi a duk wani tafiya na duniya. Bissalam*
••••
"Astagfirullah"
Ya furta bayan ya shafa dogon adu'ar da ya jima yana yi tun bayan sallame Sallar
asuba da ya gabatar, ya godewa Allah maɗaukakin sarki da ya kasance adalin adilai,
maji ƙan bayi wadda bai taɓa tantance da yaren da za'a roƙe shi ya amsa ba, don da
be san ta yadda zai fara ba, Sallar ma yayi shi ne babu tabbacin isar shi saide ya
roƙa akan Allah ya shirya shi ya ɗora shi hanya madaidaiciya, ya kuma bashi ikon
gyara kura-kuranshi tun kafin ya koma gareshi a zero, Shigowar wani kurtun Police
ne ya sa shi sa hannu ya kare haske tarrrrr da ya bayyana mishi yana kokarin illata
jijiyar ganinshi don ɗakin duhu ne yake zaune ciki.
"Mukhtar"
Baba ya faɗa bayan ya gama kallonshi, babu abinda ya firgita shi irin tatoos na
jikinshi kasancewar bashi da riga duk wani tatoo da ya kashewa makudan kuɗaɗe wurin
zanawa gasu nan raɗau akan farin fatar shi, gashin kanshi da nashi ne yaje aka
murde tsakiya ya zama dada aka kuma penta shi kalar ƙasa daga sama duk gasu nan
zube har wuraren goshinshi, ɗaga idanu yayi ya kalli Baba ba tare da ya motsa ba,
hannu baba ya miƙa mishi sai ya soma takawa kaman me tsoron tafiya ya isa gabanshi
ya durkushe bisa gwiwowinshi a karo na biyu bayan fahimtar waye shi a duniya ya
fashe da kuka me cin rai, kukan tsantsar takaicin rayuwarshi da nadamar abubuwan da
ya aikata gabaɗaya rayuwarshi, kukan baƙin cikin kasancewarshi mashayi, mazinaci,
azzalumi tunda yana iya zaluntar kowa ya kwana lafiya hakan kuma ya zamar mishi
abin tinkaho a baya, hatta matar aurenshi ya zalunceta to me zai zauna duniyar
yayi?
Ya fi mintuna ashirin yana wannan kukan wadda duk jama'ar da suke wurin suka shiga
tsantsar mamaki babu wadda zai yarda sbd wannan fyade ne yake kuka kaman yadda Baba
ya katse mishi kukan da cewa
"Mukhtar na tabbatar ba kukan halin da kake ciki ba ne kake yi, a duk abin da zai
faru kana da yaƙinin mahaifinka zai fidda ka, shi ma kuma bashi da wani tunani in
dae akan ka ne ko nawa zai iya kashewa tunda kudi ba matsalar shi bane, Mukhtar
kalli jikinka kaman ba na mutane ba? Ka kuwa san haramci tatoo?
Kalli gashin kanka irin askin da annabi ya hane mu dashi ka kwashe rabi da rabi ka
bar tsakiya, Mukhtar baka tsoron hukuncin Allah a kanka? Baka tsoron fushin shi ya
haɗu da na mahaifiyarka ya haifar maka da babban iftila'i? Ko ka san kuɗi ba zasu
taɓa ceton ka daga fushin ubangiji ba?"
Idan Maami bata ce ta jijjiga da kalaman Mukhtar ba tayi ƙarya, sai de tana tsoron
kar mafarki take, ko kuma wasa yake, shiriya take gani yana sauƙowa ɗan ta? Kuka ta
fashe dashi na rasa abin yi, C.p, iyayen yaran da sauran manyan hukuma dake tsaye a
wurin basu yarda da zancen shi ba, Baba kuwa hamdala yake adu'o'insu sun karɓu.
Haka suna gani aka maida shi, Maami jikinta yayi sanyi sossai tana kallonshi har
aka tafi dashi, ita da baba suka fito baba na sake yi mata nasiha har suka sauƙe ta
gida drivern shi ya ja zuwa gidan shi.
Da sauri ta ɗago kai, one thing da zata iya cewa ta sani akan Mukhtar shi ne da
matukar wuya yayi ƙarya
"Kuma Maami a baya ya aikata irin haka aka ce?"
Shiru Maami tayi sai Alayah ta ga kaman tambayar be dace ba
"haka ne, maƙasudin ƙarasa taɓarɓarewar rayuwar shi kenan Alaya, kila da be aikata
hakan har ya shiga prison a chan Kasar ba ya haɗu da manyan thugs kila da hakan be
faru ba, kaddara ta rigayi fata. Amma a yadda Mukhtar yake magana a yau har cikin
raina na gamsu na kuma amince da be aikata ba ɗin, Fatana shine Allah ubangiji ya
sanya ya shiryu a gasken"
Alaya ta amsa da Ameen.
Sun ɗan tattauna akan jikin ummi inda Maamin ke faɗa mata umar ya ce bayan lafawar
komai in har babu wani cigaba za'a fitar da ita waje, tana cikin total coma ne
tsakanin rai da rayuwa.
"Ban taɓa ƙin ku ba, ba kuma zan taɓa hakan ba, zan nesanta kaina da ku Dukda hakan
ya zame min wani babban giɓi da abin baƙin ciki musamman in na duba cewa kun tura
ni nesa da farin cikina wato mahaifiyata, hakan ba zai taɓa sa na bari kuyi abin da
kuke so ba Abba, ku sani in har baku neme ni ba ni ba zan taɓa neman ku ba sai dae
idanuna suna kanku, haka kuma a duk sadda na yi ra'ayi zan tako har cikin gidanka
in ga mahaifiyata don ita bata ƙi ni ba, bata sanya min bakin cikin da zai farauci
farin cikina da nesanta kaina da jama'a ba"
Har ya miƙe sai ya juya yayi taku biyu uku kan ya ja tunga ba tare da ya juyo ba ya
soma cewa.
"Idan Yaro ya faɗi tashi yake ya ruga a guje, idan babba ya faɗi ya kan waiwaya ne
ya ga me ya kayar dashi, idan ba ku yi nazarin jiya ba gobe ba zata taɓa yi muku
kyau ba, ku daurewa zuciyoyinku kuyi rayuwar da zata zamto abin koyi ga na baya
abin sha'awa ga na tare da ku, abin kishi ga makiya sannan abin alfahari ga dukkan
masoyanku, ku kiyaye saɓani da mutane watarana za'a yi shaida walau da rai walau
babu, wannan ɗin kusan saƙon mahaifiyata ne gareni inda take bani kwarin gwiwar
zama Kunkuru cikin macizai na zaɓi na raba da ku ne saboda kuma ku rabauta... Na
barku lafiya"
Daga wannan rana ba zai ce ya sake ganin umar ido da ido ba, shekaru sama da Goma
sha biyar, ya wofintar da rayuwarshi saboda kawai yana gyara musu tasu, umar ya kan
zo har cikin gidan amma baya taɓa bari ko da a hange ne su hangi juna, hakan be
taɓa damunshi ba sai a yau, hawaye kawai yake zubarwa motsin kofan shi ya ji, be
damu da share hawayen ba har Maami ta shigo, kusan yanzu tana rayuwa dashi ne akan
dole, haushi da takaicinshi karara yake gani cikin idanunta, abincin hannunta ta
ajiye ba tare da ta tanka ba ta juya ta ɗauki na safe yadda ta ajiye shi be taɓa
ba, taku uku tayi tace
"Ban sani ba ko har yanzu wannan soyayya ta Mukhtar na nan dankare a zuciyarka, na
shiga dumbin mamakin sanin cewa har yau baka iya zuwa inda yake ba baka kuma damu
da halin da yake ciki ba, hasali ma maƙiyinku shine yayi uwa yayi makarbiya wurin
ganin cewa ba'a zalunci ɗan uwanshi ko an illata shi ba, duk ba wannan ne ya sa na
tsaya ba, na tsaya ne in ce maka gobe da misalin karfe takwas za'a shiga court an
tsagaita sabd zaɓe, ban roƙi ka shiga lamarin don ɓinne gaskiya ba sai dae akwai
buƙatar zuciya ta ɗanɗani azabar aikinta..."
Tana kai nan tayi gaba, kanshi ya shafa yana huro iska, rudanin da yake ciki yasa
be san komai akan abin da ke faruwa da Mukhtar din ba, be ba Mukhtar laifi duka ba
ya raba ne a tsakaninsu hakan yasa ya mance Mukhtar din na ɗan lokaci, kuma a yanzu
bashi da wani kwarin gwiwar fuskantar kowa da wannan lamari...
COURT
A yadda aka fito da su zaka yi tsammanin babu wadda ze iya magana cikinsu sbd
yanayin wahala da suke ciki wadda ba sabon su bane, shi Mukhtar be iya ya kalli
kowa ba, yayinda Alayah ta maida hankalinta kanshi tana kallonshi, har yau bata jin
komai akan Mukhtar bayan ƙimar mahaifiyarshi da kakanshi, tunaninta na kai kawo ne
akan shin ko shi ya aikata ko ba shi ya aikata ba zata iya cigaba da zama da shi
kuwa? Zuciyarta ta riga ta kuntace shi, duk yadda tayi kokarin chusa tausayi da
soyayyar Mukhtar a ranta ta kasa bata san cewa duk daɗewar sanda a ruwa baya taɓa
zama kifi ba...
"A ƙarshe bayan duk wasu hujjoji da shaidu da suka gabata, kotu ta yankewa waennan
matasa huɗu shekaru goma goma gidan yari tare da azaba me tsanani, da kuma tarar
naira miliyan ɗaiɗai daga kowannensu zuwa ga iyayen yarinya don a cigaba da kula da
lafiyarta"
Hannu ya sa ya ɗauki kulkinshi ya buga aka miƙe gabaɗaya, alkali ya juya don komawa
office nashi hankali kwance. Yayinda polisawa suka yi kansu tare da ma'aikatan kotu
don tabbatar da isansu prison lafiya.
Littafin nan ba kyauta bane, book 2 na kuɗi ne a yanzu mun fara jin ƙamshin karshen
book 1 ku hanzarta biya saboda yanzu muka soma tafiyan, zaku iya biya ta wannan
asusun
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai shaida ta wannan layi
09039206763
🖤Gureenjoh🖤
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
Book 1
*Page Twenty*
Gabanshi ta isa ta kalle shi cikin idanu ta ɗago ta kalli alƙalin cikin Muryar roƙo
da karaya ta ce
"Don girman zatin Allah me shari'a ka taimaki macen da take dauke da juna biyu na
wadda aka yankewa shekaru goma gidan firsuna, ka taimaki uwar da take shirin shiga
tsananin tashin hankali saboda yanke wannan hukunci bisa kuskure, ka bamu dama ta
biyu ina me tabbatar maka babu hannun mijina ciki..."
Be tanka ba don yanayinta ya fi kama da mahaukaciya wacce take cikin sabuwar kamu,
bata damu ba tunda dae yana tsaye ta juya ga Mukhtar da banda kallo babu abinda
yake binta da shi ta sanya hannu ta riƙe nashi, cikin karyayyen murya me cike da
tausayi a gauraye da son da bata san tana mishi ba saida taji hukuncin da aka yanke
mishi ta soma cewa
"Ya Mukhy a rayuwa muna kuskure, kowa yana kuskure kawai abinda ya kama ce mu a duk
sadda hakan ta kasance shine muyi imani, mu kuma rayu da wannan consequences ɗin da
kuskuren mu ya janyo mana, tunaninmu ya karkata ga tunanin tayaya! Ta kuma wani
hanya zamu bi wurin gyara wannan kuskure"
Hannunshi ta kara gimtsewa tana roƙonshi da idanunta
"you don't have to blame yourself all for that Yaa mukhy, ba sai ka shigar da kanka
cikin bala'in da baka da masaniya bane za'a san ka chanza wlh we all believe you...
Ko Maami?"
Ta juya tana kallon Maami da banda hawaye babu abin da take zubarwa sai ta gyaɗa
musu kai, da sauri ta juyo tana mishi kallon ka gani ko? Sai ta sake cewa da sauri
"Duk yadda kaddara ta zo a haka zamu karɓa mu kuma cigaba da rayuwa, karka nesanta
kanka da mu da tunanin mun tsaneka, halayyarka ce bama so kuma ka sauya don Allah
kar ka bari in haifi yaron da zai shekara goma cikin duniya ɗaya da mahaifinshi ba
tare da ya san shi ba, maraici akwai ciwo Don Allah"
Ta haɗa hannayenta wuri guda tana kuka.
Nawwaz ne yace
"Be aikata ba wallahi, hasali ma be san sadda muka yi hakan ba sai bayan mun gama"
Smrt ma ya ce
"hakane wallahi, Mukhtar baya cikin mu"
Alkalin da gabaɗaya jikinshi yayi sanyi da tausayin Alaya da irin maganganunta sai
ya dawo ya zauna, kowa ya koma ya zauna shari'a ta sake dawowa daga baya, kai tsaye
duk su ukun suka bayyana gaskiya inda yarinyar m ta tabbatar da cewa mutum uku ne
ba huɗu ba, shari'a saɓanin hankali sai gashi an wanke Mukhtar, Alayah kaman ta
tiki rawa sai ta koma inda mazauninta suka rungume juna da Maami.
Har suka iso gida bayan kammala komai Alaya bata iya ta ce komai cikin motan ba
saboda yadda duk ya cike wurin, lallai natsuwa wani rahama ce ta daban, ɗakinshi na
sashen ya wuce yayi wanka Maami ta tura a kai mishi Abinci, a chan ya ci ya kwanta
bacci ba shi ya tashi ba sai azahar yayi wanka ya fito a wurin mashigar suka haɗu
kiribb da Abba, kallon juna suka yi na seconds kan duk suka nufi ciki don karyawa.
Abin mamaki wai na kwance ya faɗi yau Abba ne da Mukhtar suka hadu babu wadda ya
iya yiwa dan uwansa magana, Alayah da Maami already sun ci hakan ya sa Alayah isowa
gaban dining ɗin Sin serving ɗin su.
Banda kallo da idanu babu abin da yace da Mukhtar din wadda hakan ya saka
zuciyarshi hasala ya fara watsawa mahaifin nashi baƙaƙe maganganu cikin ɗaga murya,
da gudu Alayah ta ajiye maheer ta tare Mukhtar tana mai rufe mishi baki a lokaci
ɗaya tana girgiza kai cikin firgicin kalaman da yake jefawa mahaifin nashi...
🖤Gureenjoh🖤
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
Book 1
*Page Twenty one*
"Fatima kyale shi, barshi ya faɗi duk abinda ke ranshi ko me zai faɗa na tabbatar
babu ƙarya cikinta, na riga na cuci rayuwarshi na mishi illah, ban nemi yafiyarshi
bane ba don ban yi nadama ba, nayi shiru ne saboda ban san me zan ce ba, ban kuma
san ta wani hanya zan bi wurin taya shi gyara kuskuren da nine silar faruwarsa ba,
amma ke ina rokon yafiyarki akan kalamaina na jiya"
Cokalin ya ajiye ya miƙe zai fita Alaya tace
"Abba!"
Tsayawa yayi daidai kusa da Maami ba tare da ya juyo ba tace
"abin da na faɗa a kotu ɗazu shi zan sake maimaitawa, kowa yana kuskure hakanan
kowa na laifi saidai wadda ya fahimci laifin shi ya kuma tuba yayi niyyar gyarawa
be yi kuskure ba, hasali ma abin da ake fata kenan, Don Allah karka saka damuwa a
ranka Abba.
Ya Mukhtar na fahimci yadda kake ji a ranka, sai dae ba hakan ne ya baka daman
aibata mahaifinka ba, babu inda ya bamu wannan daman idan har da gaske ka gyara
kuma ka chanza daga Mukhtar na da to kayi kokarin saita harshenka wurin magana da
iyaye don Allah ya ɗaga darajarsu.
Maami Don Allah da manzonsa kiyi haƙuri, fushi ko rashin yafiya duk ba zai chanza
komai ba, mu haɗu duk mu gyara abin da ya ɓaci a baya adu'ar ki ce a yanzu Allah ya
ƙarba, muyi kokarin zama one Big happy family Don Allah"
Mukhtar da kanshi ke ƙasa hawayenshi na ɗiga bisa kan dining ɗin a ranshi yake jin
Alayah is too good for him, be yi abinda Allah zai bashi ita matsayin mata ba,
bayan duk abubuwan da suka faru ji yadda take magana kaman be gallaza mata ba, har
ta yafe mishi kenan? Lallai idan zata iya yafe mai kuma har ubangiji zai iya yafe
mai ya barshi da mace irin Alayah to shi me zai hana shi yafewa Abba? Maami ya ɗago
ya kalla tana zub da hawaye itama idanunta na kan Alayah, har ranta take son
yarinyar Allah ya mata baiwa na daban, idanunta ta maida kan Abba da jikinshi yayi
matukar sanyi, kwarai suna bukatar cikakken farin ciki na tsawon shekarun da suka
rasa a gidan ko da kuwa ba zai tabbata ba, shiyasa yake ganin gazawarshi ya kuma
tabbatar komai ya faru tun farko daga shi ne, idanunshi ya lumshe yana jin kanshi
na sarawa babu tantama hawan jininshi ne.
Mukhtar ne ya yanke sad moment ɗin don tunda Alayah ta gama magana tayi shiru kowa
da abinda yake saƙawa cikin ranshi, a hankali yake jan kafafunshi har ya isa gaban
Maami ya zube bisa gwiwowinshi kanshi a ƙasa yace
"Na san ni gagarumin me laifi ne a gareki Maami, tabbas a da na zama wawa, jahili,
marar amfani na bi sahun waenda Allah ya ƙira da Ƴan wuta nayi ta saɓa miki cikin
sani da kuma rashin sani, kin yi kuka har ba adadi, kin shiga damuwar da har ki kan
yanki jiki ki faɗi, amma duk da haka baki tsane ni ba, baki daena min adu'ar
shiriya ba, baki zare hannunki a kaina ba ba kuma ki yi min mummunan furuci ba
saboda ke uwa ce! A yanzu ina tsananin jin kunyar kaina da na mahallacina, ina jin
nauyin neman gafararki saboda abubuwan dayawa, Don Allah Maami ki yafewa Mukhtar
ɗinki, ki yafe mini ko zan samu kwarin gwiwar tunkarar mahallacina da neman gafara,
Maami ki ɗaukeni kaman jinjirin yaron ki da kika haifa a tsumman goyo in baki
ragamar rayuwata ki yi min sabon tarbiya uwa ta gari, na tuba don Allah"
Yadda yake kuka sai ya sa su duka kuka har Abba hawaye yake yi, kafaɗanshi ta kamo
ta ɗago shi kawai ta rungumeshi Allah ya sani kukan farin ciki take, kukan jin
daaɗi yau Mukhtar ya zama mutum, ɗagowa tayi tare da sanya hannu tayi cupping
fuskanshi tana kallonshi cike da sabuwar soyayya tace
"Na yafe maka Mukhtar, har Abada na yafe maka duk wasu laifukanka gareni da wadda
na sani da ma wadda ban sani ba, Allah ya yafe maka... Ina so ka zama kaman ɗan
uwanka a kusa dani duk abinda ya shige maka duhu a sabuwar tafiyar nan taka da zaka
fara kar ka ji nauyi ko kunyar tambayata kaji?"
Hugging ɗinta ya sake yi, Abba ya sanya hannu ya share hawayenshi kan yayi taku
kaɗan ya ƙaraso gabansu, Maami ya kalla
"Fatima ki yafemin na cutar dake a iya zaman mu, nayi kuskure me girma wadda ban
farga ba sai a yanzu, bayan lalata tarbiyar Mukhtar na kuma nesanta ki da wadda
zaki gani ki ji haske, lallai na tabbata mugu, azzalumi ban yi la'akari da cewar ke
ɗin uwa ce ba, ban duba kasancewar ki mace me raunin zuciya ba ƴaƴa biyu da Allah
ya baki duk na wargazasu na tauye farin cikin ki na tsawon shekaru na tuba"
Kai ta gyaɗa tace
"komai ya wuce Abba, in shaa Allah zamu ƙarasa sauran rayuwarmu wurin gyara duka
waennan kuskuren"
Mukhtar ya kalla zai yi magana sai yayi hanzarin rungumeshi, a rungume dashi yace
"Abba kayi haƙurin kalamaina na dazu, na san duk abubuwan da kayi min a yadda ka
ɗauki soyayya kenan baka min da niyyan zalunci ko don in lalace ba, hasali ma mune
muka zalunci Umar, na riga na yafe maka Abbana, Allah ya bamu ikon gyara laifukan
mu"
Duk da Ameen suka amsa, sai a lokacin kowa ya iya sakin murmushi a cikinsu, dawowa
suka yi Maami ta sake serving Abba sbd wanchan yayi sanyi, Alayah kuma tayi serving
Mukhtar dake ta kallonta wadda hakan yake sakata jin kaman ta nutse cikin ƙasa.
Basu zauna ba suka yi cikin parlor suka zauna da Maami, Maami ce ta nuna mata
cinyarta sai ta zame ta kwanta tare da yin matashin kai da shi, a hankali ta zame
dankwalin kanta tace
"Binty dai Allah yayi ki irin Maaminku, kema bakya son kitso sam"
Murmushi tayi tace
"Maami ai tsoron kai ne da ni, daa ummi sai tayi da gaske take min kitso saboda
rigima daga baya tace na girma in ma naki ni na sani, shikenan sai dae in wanke in
shafa mai"
Murmushi Maami ta sake tana cigaba da ɗan sosa mata kan tace
"Lallai Binty ke ɗin wata haske ce a cikin rayuwarmu, ina Alfahari da samun ki
matsayin ƴa Allah ya albarkace ki ya ba ummi lafiya"
Tana lumshe idanu saboda baccin da yake son kwasheta don susan kan daaɗi yake mata
tace
"Bani da abin da zan saka miki Maami, illa iyaka a duk sallata na kan sanya ki a
Adu'a Allah ya miki abin da zato be taɓa zato ba, tunanin ɗan Adam be taɓa kaiwa
ba, Allah ya miki muhalli na musamman a cikin gidan Aljanna, haƙiƙa nayi matukar
dacen samun ki a matsayin uwa"
Murmushi Maami ta saki, a hankali ta ɗaga kai sai ta ga Mukhtar da Abba ma hira
suke ɗan yi a hankali, idanunta ta lumshe ina ma da umar yana wurin da farin
cikinta ya zama cikakke, amma ta san irin zuciyarshi ga yanayin aikinshi Allah ya
sa ya yafewa babanshi da ɗan uwanshi har su yi zama da mutunci.
Ko da Suka gama wurinta suka dawo, tuni Alayah tayi bacci kan kafafun Maami, hira
suka cigaba da yi su ukun kaman komai be faru ba, shawaran karatuttukan da zai fara
suka yanke inda a kullum da yamma zai tafi wurin baba sai goman dare ya dawo, tuni
ya kira kakan nashi ya shaida mishi ze fara zuwa ɗaukar karatu har yar raha suka yi
baban na cewa ya faɗi gaskiya ko furanshi na dare zai ke zuwa shanyewa kullum suka
ɗan yi dariya, ya kula kowa so yake ya ja shi a jiki, kwarai hakan ya mishi matukar
daaɗi don hakan ne kawai zai kasance ya san eh zai iya, zai iya zama na kirki,
shima zai iya gyara kura-kuranshi, kuma he is accepted a welcome a familynshi.
Idanunshi gabaɗaya zube a kanta, murmushi ya ɗan saki yana kallon yadda ta sake
lafewa jikin kujeran kaman mage, haƙuri na musamman yake son bata, sai dae baya
tunanin a yanzu ne zai yi hakan, duk yadda yake jinta a ranshi da yadda yake jin a
yanzu ita ce bugun numfashin shi zai mata adalci, dole sai ya zama nagartaccen
mutum kaman kowa zai iya sake fuskantar ta da kokon barar matsuguni a cikin ranta.
Abin da be taɓa faruwa ba shi ya faru yau, sun yi hira sossai har la'asar cikin
raha, sai tuno baya ake Maami na hiran yarantanshi yana dariya, dariyanshi ne ya
tada Alayah, ta buɗe idanunta dake cike da bacci ta watsa mishi, shima da baya
mintuna biyu be kalleta ba idanunshi na kanta, bakinta ta turo mai na tana baccinta
me daaɗi ya tashe ta, murmushi me kyau da bata taɓa gani a fuskanshi ba ya sakar
mata, da sauri ta ɗauke kai tare da kokarin Miƙewa zaune.
"Sannu Fatima"
Abba ya faɗa tayi murmushi, Maami tace
"kin tashi Binty? Ko yunwa ce ta tashe ki? A kawo miki wani abu ne?"
Jinta take ƴar gata, a da ana musu kallon kaskantattu marasa galihu babu wadda ya
damu da damuwarsu, cin su, shan su ko lafiyar su amma duba a yau yadda waennan
ahali suke mata, ai ko menene tayi musu bata faɗi ba.
Maami bayan ta idar da sallah Umar ta ƙira, a natse suka gaisa take bashi labarin
abinda ya duk ya faru, ya taya ta farin ciki don da farin cikinta shima yake samun
farin ciki.
"Yanzu yaushe zaka shigo?"
Kofan ɗakin aka yi knocking ta bada izinin shigowa, Mukhtar ne ya shigo zai yi
magana daga chan tayi saurin miƙa mai hannu ya iso ya riƙe ta nuna mishi kusa da
ita bakin gado ya zauna, ta san sabo sai a hankali amma with effort komai zai zama
tarihi.
*kar fa ku sha'afa tafiyar yanzu aka soma ta, akwai sauran rina a kaba, tsugune
kuma bata ƙare ba, har ila yau dae muna nan book 1, book 2 zai muku a naira 500
kachal zaki iya biya ta wannan asusun
0545475847
Gt
Fatima Muhammad Gurin
Sai shaidar biya ta nan
09039206763
🖤Gureenjoh🖤
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
Book 1
*Page Twenty Two*
A hankali ta buɗe idanunta da suka sauya sossai ta zuba mishi su, zare hannunshi
yayi daga goshinta chan ƙasa yace
"Are you alright? Da wata matsala ne?"
Da idanu ta amsa shi don bakinta yayi mata nauyin buɗewa.
Gefe ya ɗan kalla sbd yadda idanun suke wani irin tasiri a jikinshi, Miƙewa zaune
tayi a hankali tace
"zaka fita ne?"
Sai a lokacin ya ɗan kalleta yace
"zan je wurin baba, me kike so in taho miki dashi in zan dawo?"
Murmushi ta ɗan saki shima yayi, Dukda babu wani shakuwa na musamman a tsakaninsu
babu tsoronshi a ranta kaman kwanaki, hasali ma tausayinshi ya fi komai tasiri a
gareta sai kuma tausayin ɗan cikinta.
"Nama"
Ta faɗa a tsakanin lips ɗinta
"wani iri?"
Idanunta ta ɗan juya da alamun tunani kan tace
"ko wani iri me daaɗi dai"
"an gama maman unborn, na tafi"
"Allah ya tsare"
Ya amsa kan ya fice daga ɗakin, ajiyar zuciya ta sauƙe kan ta ɗan yi murmushi.
Tuƙi yake a natse yana murza siterin motar tsakanin hannuwanshi, wani irin yanayi
yake ji a jikinshi da ma zuciyarshi, jinshi yake sabon mutum a hankali ya miƙa
hannu ya kunna karatun alqur'ani da ɗazu yayi downloading Dukda manyan surorin da
be iya bane sai dae jinshi akwai saukar da natsuwa, gidan baba malam ya isa saida
ya shiga ciki suka gaisa da kakkaninshi da wasu Aunties din nashi kan ya tafi
parlorn baba, maraba ya mishi suka zauna aka kawo abinci fura kaɗai ya sha, da
tambayoyi baba ya fara abubuwa dayawa be sani ba hakan yasa baba ɗauko komai daga
farko, Allah ma ya sa shi ɗin akwai kwakwalwa da kam ba karamar wuya ze ci ba wurin
koyon addini, kuma abin ka da wadda ya saka kai sossai ya natsu ya ɗauki
karatuttukan ranan, sai goma na dare ya mishi sallama ya fito.
Sai da ya tsaya ya sayi kaji gashin oven da aka yi su cikin wani hadaddiyar sauce
na albasa da kuma Irish guda huɗu da su youghurt kan ya nufi gidan, a parlor ya
sami Maami dake ta zuba ƙamshi tana kokarin tafiya part din Abba, da murmushi ta
tare shi tare da wara hannunta ya matso yayi Hugging ɗinta tace
"ka dawo?"
"Eh Maami na dawo"
"ya karatun? Fatan an yi abin arziki"
Yana murmushi yace
"Eh Maami, na koyi dayawa har fa baba na mamaki"
Kai ta jinjina cikin jin daaɗin da ya kasa boyuwa mata tace
"Masha Allah, Allah ya sa a ɗore a haka"
Ya amsa da Ameen
Ledar hannunshi me kaji biyu ya miƙa mata
"Maami gashi a tafi wa Abba da shi"
Karɓa tayi ta mishi Adu'a kan ta juya kitchen zama yayi yana jiran ta fita don
kunyar haurawa wurin Alayah yake a kan idanunta, a tray ta haɗa musu kan ta fito ta
mishi sai da safe.
Sai da ta fice daga sashen ya miƙe ya shiga kitchen ɗin, yadda ya ga ta haɗa ya
haɗa Dukda be iya ba duk ya ɓata jikin plate ɗin haka dae ya kokarta kan ya saɓi
tray din ya haura sama dashi, a hankali ya ɗan yi knocking kan ya buɗe ya shiga
tana tsaye ta gama saka night gown ɗinta kenan wadda dogon Cotton gown ne har ƙasa
da tsagu gefe da gefe, cikinta ya ɗan tasa kaɗan akan rigar ya mata kyau sossai,
murmushi yayi mata ta ɗan mayar mishi kan ta nufo shi ta karɓi tray din.
"Sannu da dawowa"
"yauwa fatee"
A ƙasa ta ajiye tray ɗin kan tattausan rug carpet dake shimfide a wurin, ya ƙarasa
ya zauna ita ma ta zauna, shi yake cire mata ƙashi sai ya bata tsoka, Dukda ba wani
hira suke ba moment ɗin ya mishi daaɗi ashe haka samun cikakken natsuwa yake?
Godiya kawai yake yi wa Allah da ya bashi daman zama mutum a karo na biyu, sai da
tace ta ƙoshi kan ya kyaleta ta miƙe ta shiga toilet ta barshi yana ci, brush tayi
ta fito ta isa kan gado ta kwanta lamo gabanta na faɗuwa Allah Allah take ya gama
ya tafi, tana kallonshi ya gama ya tattare wurin ya kai bakin kofa ya ajiye kan ya
dawo ya shiga toilet ɗinta ya wanke hannu tare da kuskure baki ya fito.
Yana fitowa tayi hanzarin rufe idanunta tana damke blanket da take ciki dukda
iyakarshi kan kwankwasonta ne, taku yake yana nufan gadon inda yake tafiya da bugun
zuciyarta, murmushi ya saki ganin yadda take mirmisa idanun sai motsi gashin
idanunta ke yi wai ita a dole tayi bacci, a ɗan space da ta bari ya ɗosana
duwawunsa ya sanya hannu daga gefenta kan gadon ya tokare hakan ya bashi damar yi
mata rumfa da faffadar kirjinshi, fuskanta ya zubawa ido yana ƙare mata kallo,
tsawon dakika goma, kasa juran kallon tayi ta fara buɗe idanun a hankali har suka
faɗa cikin nashi, murmushi ya ɗan saki yace
"Yana fita?"
Kai ya gyaɗa mata
"A da ne ba'a samo technologyn cire shi ba, amma yanzu ana iya gogewa"
Ta haɗiye miyau tace chan ƙasa kaman yadda shima yake mata magana
"Da me ake gogewa?"
"Da wuta kaman yadda aka yi shi da wuta"
Idanunta ta ɗan zare
"kuma ba zafi?"
Cikin kwaikwayan maganan ta ya ce
"akwai amma mijinki jarumi ne"
Murmushi tayi, shiru ya ɗan ratsa su idanunshi dake ta yawo bisa kanta duk ya bi ya
tsarga ta, har gwara suna maganan ma da suna zaune shirun nan.
Karfe huɗu da rabi alerm ɗin shi ya tashe shi, a natse ya miƙe ya shige toilet yayi
alwala ya zo ya sanya Black jallabiya da ya mishi kyau sossai ya amshi skin dinshi
dole yau zai je ya nemi kaya don da ya tsaya gaban kayakinshi na gidan duk babu na
kirki, duka kyauta da su zai yi a yau, fita yayi ya tafi ɗakinta ya tashe ta kan ya
fito, a haraba suka haɗu da Abba suka nufi masallaci dake kofan gidansu anan suka
yi raka'atanil fajir wallahi be taɓa jin natsuwa irin na daga jiya zuwa yau ba a
rayuwarshi, har suka yi sallahn asuba wani irin nishadi yake ji, ko da mutane suke
fita shi qur'ani ya ɗauko ya cigaba da bitar ƙarin su na jiya, sai wuraren bakwai
ya bar masallacin ya dawo ɗaki ya ɗan kwanta.
Karfe goma daidai ya fito a shirye cikin half jumpa ruwan ƙasa da ya kama shi ya
mishi kyau sossai, tuni ya aske kanshi don haka hular shi ta zauna sossai ya fito a
babban mutum me cike da natsuwa da haiba, a parlor ya same su, itama ta shirya
cikin baƙin lace me adon peach ya mata kyau sossai, gaishe shi tayi ya amsa yana
tambayar lafiyanta kan ya duƙa ya gaida Maami itama ta amsa cikin kulawa
A chan ma cikin natsuwa yake shigar da kanshi gareta, har ya gama ci suka fito
magana yake mata a hankali tana bashi amsa, anan ta yafa babban mayafinta ta ɗauki
jakanta tace
"Maami mun tafi"
Maami tace
"Allah ya tsare ya bada sa'a, sai kun dawo"
Suka fice a tare gwanin sha'awa, shi ya buɗe mata hadaddiyar motar tashi sport car
ce BMW ta shiga shima ya zagaya ya shiga ya ja suka fice, kaman yadda ya faɗa
campanin motocin shi suka tsaya suka shiga, ana ta miƙa gaisuwa cike da tsoro
saboda sanin shi masifaffen marar haƙuri, kuskure kaɗan kashin ka ya bushe, ga
mamakin su yau sai gashi sai murmushi yake saki ba wannan hayaniya da hargagin, har
kyautar kuɗi ya musu suna ta mishi godiya cikin jin daaɗin sauyin da suka gani a
tare dashi.
Wata coffee hyundai ta zaɓa ya mata kyau sossai, a take ya bada umarnin ayi wa
motar duk wani checking kan yamma a kai mishi gida, daga nan school suka nufa duk
yadda ta so ya barta daga haraba ya tafi zata yi duk abinda bata gane ba ya ƙi, a
tare dashi suka yi ta yin komai, duk inda da bin layi zai nema mata seat ta zauna
shi ya bi Layin sai an iso ya kirata ta zo su yi abinda zasu yi su kara gaba, kowa
kallonsu yake gwanin sha'awa lallai haƙuri na da riba, duk masu yi mata kallon ta
dace ta tsinci dami a akala basu san irin tsanin wutan da ta taka zuwa wannan wuri
bane.
Karfe ɗaya suka gama komai, sai da suka tsaya masallacin makarantar ta shiga
ɓangaren mata shi ya shiga cikin masallaci suka yi sallah kan suka fito, restuarant
me kyau ya kaita suka ci abinci kan suka nufi asibiti, har yau ba'a bari an shiga
wurin ummi ba, hanganta suka yi ta fara hawaye tuni ya jinginata da jikinshi yana
lallashinta, sun ɗan jima kan suka fito a reception yace ta ɗan jira shi anan yana
zuwa, wayanshi dake ta ringing tuntuni yana rejecting yanzu ma shi ya sake ɗaukar
ringing wayan ta bi da kallo har ya ɗan yi nisa kan ta ga yayi picking ya ɓace
mata.
"Rita i Said leave me alone! Ki kyale rayuwata na fita daga cikin sabgar rayuwarku
daga ke har su Zee wacce ta sake kirana wallahi sai na mata rashin mutuncin da baku
taɓa tunani ba, rubish"
Yana kai nan ya yanke wayan ba tare da ya jira amsar ta ba sim zai chanza bazasu
dagula mai lissafi ba, yana kokarin zare sim ɗin saƙo ya shigo, kalma ɗaya da ya
gani shi ya ja hankalinshi wurin dubawa, wani irin jiri ne ya kwashe shi da sauri
ya dafe gini don ƙoƙarin zubewa ƙasa yake, a take zufa ta karyo mishi a kan lips
ɗin shi ya furta
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun.."
*Kar ku sha'afa Al'ajabin So littafin kuɗi ne part 2 din zai zo muku akan naira 500
kachal har yanzu muna da gagarumin tafiya a gabanmu.
Zaki iya biya ta wannan asusun
0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin
Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi
09039206763
Sai na ji ku*
🖤Gureenjoh🖤
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
Book 1
*Page Twenty Three*
Yana isa wurinta ya sakar mata murmushi tare da miƙa mata hannu ta kama ta miƙe
yace
"Sorry madam na ajiye ki ko?"
Girgiza kai tayi tana murmushi, bata tambayeshi abin da yaje yi ba sai dae ta
fahimci kaman akwai abinda yake damunshi, yanayinshi ya sake sanyi har suka isa
gida babu wadda yayi magana, a tare suka shiga parlor Maami na musu maraba da
dawowa, duk amsa mata suka yi suka mata sannu da gida kan kowa ya nufi ɗakin shi
don freshening, sai bayan la'asar ta fito ta zauna da Maami a parlor suna hira.
Chan shima ya shigo yayi joining ɗin su Dukda ba wani magana yake ba, a kusa da
Maami ya zauna ya ɗaura kanshi akan shoulder ɗinta, tsoro ne fal ranshi,
hankalinshi rabi baya jikinshi rabuwa da Alayah shine fargabarshi a yanzu ba ciwo
ba, Maami ta tambayeshi ko akwai wani damuwa ne yace babu, yana ji suna maganan
Ummi akan yadda babu wani improvement saboda sun ce damuwa yayi mata over ta yadda
jinin da ya tashi hitting yayi sama ba na wasa ba kuma laluranta ma na rashin ji da
magana kaman musababbin BP ɗinta ne.
Adu'ar samun lafiya duk suka mata, dab Magrib ya miƙe yace
"Maami zan ɗan fita zan tsaya wani wuri ina ga daga chan zan wuce wurin baba kawai"
Suka mishi Adu'ar dawowa lafiya ya fita.
"Maami baki lura kaman yana cikin damuwa ba?"
Alayah ta faɗa tana kallon Maami
"Kwarai kuwa na kula, sai dae kila tunanin rayuwa ne with time zai sake in sha
Allah"
****
Wasa wasa haka rayuwa ta zo ta sabar mishi da wani yanayi na daban, duk yadda yake
karfafa zuciyarshi damuwarshi ba wani boyayye bane, yana iyakacin kokarin shi wurin
bautar ubangijinshi kaman yadda yake matukar kula da Alayah da kuma Maami, bashi da
wani buri illah ya shigo ya tarar dasu su biyu suna hira da raha hakan na kautar
mishi da duk wani matsaltsalu na duniya, har ya sabar musu duk dare baya dawowa
daga gidan baba hannu banza, ita kanta Alayah ta riga da ta saba bata cin komai sai
ya dawo ya kawo ko balangu, tsire, kifi ko kaza gashi daban daban, yana riritata
yana bata duk wani kulawa tsabar yadda hankalinta ke kwance Dukda yadda karatu yayi
nisa wani irin kyau take narkawa tayi fresh abin ta.
Ta fannin mu'amalar aure bai taɓa nemanta ba wata huɗu ake nema kenan bata damu ba
kasancewar ita wahalar abin kawai ta sani, ya kan rage zafi idan ta ciyoshi da
gaske Dukda yana yawan shan tea me lemon tsami da gishiri, bata da wani matsala
banda ciwon ummi da har yanzu babu wani cigaba, jiya e yau, duk ta tashi makaranta
shi yake zuwa ya ɗaukota daga nan wucewa suke yi koyon tuƙi tun bata iyawa har ta
soma kwarewa wani lokacin ma ita ke dawo dasu gida, in tace a watannin nan basu yi
wani irin shakuwa na ban mamaki ba tayi ƙarya, yana bata duk wani kulawa da mace
take fata ko buri, cikinta ya shiga wata na bakwai kenan duk zuwanta awo a tare
suke zuwa, har yau babu wadda ya mishi maganan su koma gidansu ko ya ɗauke ta su
tafi saboda daga Maami har Abba basa so su takura shi, kila ya fi so su zauna nan
ɗin don duk wani shakuwa da be samu ba da Maami a yanzu ya same shi Dukda ya san ba
kaman na umar da ita ba, amma kwarai zuwa yanzu sun shaku matuka.
Wani abu da yake yi yake ƙara burgesu shine yawan sadaka da taimako, har an san shi
sai dae idan be ji taimako ba zai yi, abinci duk Litinin da juma'a yana ciyar da
akallah mutane ɗari biyu zuwa uku, kuma lafiyayyen girki ba laga laga ba don a
babban restuarant yake da contract, wani lokaci ma har ya ɗauketa su kai ziyara su
orphanage, asibiti da sauransu a yanzu in ya ga rayuwarshi sai ya tsinci kanshi
cikin zub da hawaye, lallai Allahnshi yana son shi.
***
Tsaye take gaban dressing mirror tana shafe tattausan skin ɗin ta da mai fitowanta
wanka kenan, wani irin zafi take ji sannan kirjinta ya tokare sossai wadda rabon da
ta ji ciwon zuciyarta ya motsa ta mance sai dae rashin ƙiba da nauyinta na nan, ta
dae murje ta ƙara kyau sossai, cikinta ya fito sossai sossai bayan ta gama ta
feffeshe jikinta da turarukan ta mabanbanta a take ɗakin ya bule da sassanyar
kamshin, night gown da be da wani nauyi da tsawo ta saka tana kokarin tufke gashin
kanta ya turo kofan ya shigo, ta madubi suka sakarwa juna murmushi.
A hankali ya ƙaraso ya ajiye tray din hannunshi kan ya nufeta slowly yayi Hugging
ɗinta ta baya very tide yana zagaye hannunshi bisa kan cikinta a lokaci ɗaya ɗan
cikin yayi motsi suka saki dariya a tare
"ka ji min yaro da gulma"
Yace
"kyaleshi ya marabci babanshi watarana sai labari"
Kallonshi tayi sai ta ga ya ɗan faɗa mata, sajen da ya tara ya mishi kyau ainun,
tafin hannunta ta sanya ta ɗan shafa sajen tace
"Ya Mukhy menene yake damunka? Jikinka da ɗan zafi kuma ramarka tun bata fita har
tana nunawa, can you please share ur problem with me? Karka manta turawa fa sun ce
a problem shared is a problem solved"
Sakinta yayi ya karɓi ribbon ɗin hannunta yana tufke mata gashin yace
"bani da damuwar komai Fatee, in da ina dashi ba zan ƙi faɗa miki ko Maami ba
saboda har duniya ta nade bani da tamkarku"
Bayan ya gama ya ja hannunta suka zauna bakin gado sbd zaman ƙasa na mata wahala
yanzu, ya buɗe soyayyayiyar Irish da aka yi ta da liver sauce ya fara bata tana ci,
sai da ta ƙoshi ta karɓi spoon ɗin ta dibo zata kai mai baki ya riƙe yana saukewa a
hankali yace
"bani da apetite ba zan iya ci ba"
Tace
"kuma dai? Ya Mukhtar kullum fa haka kake cewa da matukar wahala ka sha wani abu ma
bare ka ci abinci me nauyi"
Murmushi ya sakar mata.
Sai da ya bari tayi nisa a baccin ya maidata kan pillow ya kwanta, baya so ya tashe
ta cikin dare sbd ya san kanshi, juye juye kawai yake sbd baccin da baya samu a
kwanakin gabaɗaya, chan kuma zufa yake ta karyo mai Dukda Ac dake ta aiki a ɗakin
kusan kure wa tayi, ya yaye bargon yana cigaba da ɗan juye juye, wuraren sha biyu
ta farka fitsari idanunta suka sauƙa kanshi.
Taɓa shi tayi sai taji hannunta ya sauƙa kan zufan dake ta gangara a jikinshi, wuta
ta kunna sai suka haɗa idanu
"Ya Mukhtar zafi kake ji haka? Ko mu kunna standing fan?"
Yace
"No karki damu zan watsa ruwa yanzu ina jira ne ɗaya yayi gabaɗaya in miƙe
nafilfili na"
Sauƙa tayi ta shiga toilet tayi fitsari kirjinta ke damunta da ciwo tana tunanin
dole gobe taje meddy, ta fito ta zo ta kwanta ya kashe wutan don ya san bata iya
bacci da wuta a kunne.
Bata iya ta yi baccin ba, tana ta kallonshi ga dukkan alama duk daren be yi bacci
ba, ya kwana biyu da tayi noticing rashin baccin shi, in yayi ma baya wuce awa guda
duk tsanani, tana ta kallonshi har ya sauka ya shiga toilet ya jima wadda ya
tabbatar mata da wankan yayi kan ya fito ya sanya jallabiyanshi ya tafi wurin
sallahnts ya fara nafilfili, tun tana kallon shi har bacci ya sure ta.
Karfe uku ta sake tashi fitsari ta samu yana karatun alqur'ani da yanzu yayi nisa
sossai kuma yana fitar da duk wani makharij da kiyayewa sossai a karatu, ta
jinjinawa namijin kokarin shi don yanzu ko ita bazata nuna mishi ibada ba, taje
tayi fitsari itama tayi alwala ta zo tayi raka'a huɗu kan ta koma ta kwanta, sai
asuba ya tashe ta ya wuce masallaci.
Masu aikinta ne suka fitar da abincin zuwa dining daga shi har Maami suka je suka
yi wanka kusan a tare su huɗun suka fito, Mukhtar ya ja wa Abba kujera yana zama
yace
"Abba yau zaka ci girkina na san sai ya kai maka karo bari na tabbatar da lafiyar
kujerar nan kar santi ya kwashe ka"
Dariya suka yi Abba yace
"tafi nan, da de bamu san asalin balbela bane kai yaushe ka iya ko kunna gas din
ma? Ko binty ya iya?"
Ya faɗa kaman yadda ya riƙe bakinshi saboda yawan faɗan Binty da Maami take. tana
dariyar yadda ya kwabe fuska tace
"Babu abin da ya iya Abba"
Yace
"Maami faɗa musu don Allah ba ni nayi ba?"
Tace
"kwarai kuwaaa"
Yadda ta faɗa da alamun tsokana a muryarta yasa suka kwashe da dariya Abba na cewa
"faɗi gaskiya dai daga jin wannan amsawan naki da walakin goro a miya"
Abincin suka fara ci cikin natsuwa, jujjuya cokalin kawai Alayah take yi, Mukhtar
da ya lura yace
"Fatee lafiya? Ko wani abu na damun ki ne?"
Shima ba ci yake ba ruwan zafi yake ɗan kurba.
Maami tace
"Binty akwai matsala ne?"
A hankali tace
"Maami kirjina ke ciwo sossai"
Abba yace
"Subhallahi Meyasa baki yi magana tun ɗazu ba? Mukhtar tashi maza mu wucenku
asibiti"
Duk abincin suka bari Maami taje ta ɗauko musu mayafi zuwa lokacin ko tsayuwa
Alayah bata iya yi tuni suka yi meddy specialist hospital hankalinsu a tashe.
*Har yanzu dae ana nan a free pages karku manta book 2 na kuɗi ne zaki iya biya ta
wannan asusu
0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin sai ki tura shaidar biya ta wannan layi
09039206763*
🖤Gureenjoh🖤
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
Book 1
*Page Twenty Four*
Dr Philips ne ya yanke musu tsawon lokacin da suka ɗauka suna jiran tsammani, da
hanzari duk suka isa kusa dashi kowa na rige-rigen tambayar ya take?
"Akwai contraction between her illness nd the baby, dole za'a yi mata aiki a cire
shi a watanni bakwai in ya so a bashi duk wani kulawa a incubator she cannot take
it for completely nine months”
Duk jikinsu yayi sanyi, sai da ya basu kwarin gwiwa ya tabbatar musu da ikon Allah
in an cire they will be all safe, tuni aka kawo papers Mukhtar ya saka hannu.
Bai sani ba ko don saboda firgicin da yake ciki ne ko kuma wani abu na daban wani
irin hajijiya ya kwashe shi saura kiris ya faɗi Abba ya tare shi, suka zauna suka
shiga kwantar mai da hankali, nurse ce ta fito tace zasu iya su ganta kan a shiga
aikin, duk suka miƙe suka nufi ɗakin, murmushi ne kwance a fuskanta ta kalli Maami
ta miƙa mata hannu, da sauri Maami taje ta riƙe Alayah tace
"Maami ko a yanzu na mutu kun gama min komai, kun bani farin cikin da na rasa
tsawon shekaru, Maami ko da wani abu ya sameni ina da tabbacin zaku cigaba da
kulamin da ummi, idan kuma Allah yayi ikonsa bamu yi sallama ba ku tabbatar mata da
cewa na mutu da ƙaunarta kuma ku ce don Allah ta yafemin"
Ajiyar zuciya ta sauƙe tana zama cikin sanyi ta soma jero mata adu'ar samun lafiya
tana kuma godiya wa autan nata, ta san ko Abban shi ne zai yi wannan dole za'a samu
delay ba kaman shi ba da yake da connections masu yawa, bayan sun kashe take yiwa
su Abban bayani adu'ar samun lafiya suka yi mata da kuma burin a fito da Alayah
lafiya bayan ta warke su tafi chan gabaɗaya.
Dawowansu Abba daga Sallar azahar kenan likitoci suka fito suna musu albishir samun
ƙaruwar ɗa namiji yana ma nursery a incubator zasu iya zuwa su ganshi.
Mukhtar yace
"maman fa?"
Cikin murmushi suka ce itama lafiyanta ƙalau bacci ma take, sai a lokacin tsantsan
farin cikinsu ya bayyana a take Maami ta karbi wayan Abba ta soma kiran en uwa tana
gaya musu matar mukhtar ta sauƙa lafiya, an sha mamaki kam don bakwaini ne aka
haifo musu, kan ka ce karfe biyu en uwa da abokan arziki na ta zuwa sai dae a ga
yaro a incubator tarr kamanninshi da Mukhtar kaman an tsaga kara.
Shi kam ba'a tantance wani yanayi yake ciki, yana nan zaune tare da Alayah har
bayan la'asar ma Abadan kan ta farka, lafiya ƙalau ta tashi jikin kuma da ɗan ƙarfi
dayake plaster ne aka mata ba ɗinki ba, ta ji daaɗi kwarai da ta samu labarin ɗan
ta lafiyanshi ƙalau, saida aka kimtsata ta ɗan ci wani abu kan Mukhtar ya taimaka
mata zuwa nursery don yaron ya ci abinci sai kuka yake, sun so ta matse aje a bashi
sai dae Maami tace gwara dae ya ji ɗumin mahaifiyarshi.
Da ita da shi ne gaban incubator ɗin wata nurse ta ciro musu babyn, Mukhtar ne ya
soma karbar shi ya rungume a kirjinshi sassanyar hawaye na bin fuskanshi a kan lips
dinshi yake ta furta
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!"
Adu'a yayiwa yaron don musamman ya koya saboda burin kaiwa ranar da zae ga ɗan
nashi a duniya Dukda bashi da wani kwarin gwiwa.
Miƙa mata ɗan yayi saboda nurse ta gama taimaka mata ta wanke bakin nonon kar yaro
ya sha bacteria saboda kula irin tasu barin ma wannan da yake bakwaini dukda
lafiyayye ne, saida ya ba yaron zamzam da dabino kan ya taimaka mata ta soma
feeding nashi Dukda zafin da ya ziyarceta, ya sha kuwa yana ta sauke ajiyar zuciya.
Sun jima sossai wurinshi dab Magrib suka fito, ya kaita har ɗaki kan ya wuce
masallaci.
Kan ka ce kwana bakwai tuni ta koma normal tana komai da kanta har wanka, sai su sa
leda a bakin wurin su ɗaure da zani ta yadda ruwa ba zai taɓa ba tayi wankanta,
yaddikon Maami ce ta zauna da ita tana kula da ita sossai kuwa, kullum asibitin a
cike, Mukhtar ya ce ba za'a yi taron suna ba walima ce a ci a sha ayiwa yaro Adu'a
so a gidan Maami aka yi dukda ba yaro bare mahaifiyarshi, yayi hakan ne saboda
sanin cewa haka annabi ya umurta da a yi ba irin na yanzu ba da za'a tara jama'a a
saka dj wurin suna bayan albarka ake nemawa yaron.
Kowa ya shiga mamakin jin sunan ɗan wai Mukhtar sai dae babu wadda ya ce don me
tunda uban shi ne ya sanya mishi hakan, ganin bashi da wani matsala a duk checkups
da aka yi sai kawai suka sallame su bayan sun ƙara week kuma har lokacin Alayah
bata san ummi bata ƙasar ba, a duk sadda Maami zata yi waya da Autanta ficewa take
kuma yana tabbatar mata da tana samun sauƙi sossai yanzu har tana iya gane wadda ke
kanta.
A sati biyun sau wurin uku yana zuwa daga wurin aikinshi a Lyon ya koma, taji daaɗi
kwarai yadda ya ɗauki ummin da muhimmanci Dukda be san ma wacece ita ba bayan
surukar gidansu, wannan tausayi a jininshi yake.
Yau bayan Maamin ta gama yiwa baby komai yayi bacci a lokacin tabawa suka fito da
Alayah daga bayi a bakin gado ta zauna ta soma kokarin shiryawa, ɗakin banda
ƙamshin turaren wuta babu abin da yake fitarwa, wani kalar kunu ne da bata ma san
ko sunanshi ba banda wani fitinannen kamshin kayan yaji da yake babu abin da yake
Dada ne ke aiko mata kullum kuma tana jin daaɗin shan shi, ƙamshin shi da taji ne
yasa ta kalli gefen gadon Maami ta tsiyaya mata sai turiri yake murmushi ta saki,
jegon gata take ita kam bata da abin cewa ga Maami don ko ɗiyar da ta haifa a cikin
cikinta karshen abin da zata yi kenan.
"Maami don Allah dae ba sai na je ba, bari na ƙira Dr Ahmad ma kawai zai zo ya duba
ni a gida"
Ba don ta gamsu ba ta miƙa mishi wayan ya ƙira Dr Ahmad akan ya zo gida ya duba shi
please, shakuwar dake tsakaninsu a yanzu ya wuce na patient da Dr sai na friends
sun zama abokai sossai don a yanzu bashi da abokin da ya wuce Dr. Ahmad, ko kayan
suna na ban mamaki ya aiko matar shi dashi kuma sau kusan uku tana zuwa asibiti da
abinci niki-niki wa me jego har za'a iya cewa sun ɗan saba da Alayah.
Komawa ɗakin Alayah Maami tayi ta samu ta gama shan kunun, dubanta Alayah tayi tace
"Maami ya jikin Ummi? Har yanzu ba wani chanji ko? Kullum da ita nake kwana nake
tashi har na haihu ummi bata sani ba"
Ta ƙarasa hawaye na gangaro mata
"Ummi ta farka Alayah tana cigaba da samun kulawa"
Wani irin zabura tayi
"tana iya magana? Tana iya gane komai? Maami don Allah zan je asibitin na ganta! Na
san tana chan tana tunanina babu bakin da zata ce a kira ni"
Maami tace
"in shaa Allahu zaki je Alayah, yanzu dae ɗauki Wannan mijin nawa ku je ya gaida
babanshi babu lafiya likita ma na hanya"
Tana cikin farin ciki kwarai da jin ummi ta farka tana samun kulawar da ya dace,
Adu'a tayi ta yiwa su Maami, cikin jin daaɗi ta miƙe ta saka kayanta plain riga da
zani, duba system ma dama take son yi sbd lectures dake ta wuce ta nan ma don
farkon semester ne da a tsakiya ne ta haihu da ta ga bone, ba laifi kuma dayake
tana da fahimta sossai ko a hakan tana ganewa sossai, dama su suna online class
sossai sbd yanayin course na su.
Yaron ta ɗauka yana ta muimui da baki, ta lakaci hancinshi da sak na babanshi tace
"dube shi, yanzu ya sha baccin shi anjima yace bamu isa mu yi bacci ba"
Murmushi ne kwance a fuskanta in ta ga wannan yaron sai tace oh yau ni Alayah ce na
haihu, ni ke da yaro kyakyawa irin Wannan Alhamdulillah!
Ɗakin Mukhtar ta nufa, a natse ta sanya hannu zata tura kofan ta ji yayi magana da
ɗan ƙarfi
"Dr. Ahmad Don Allah ka kyaleni ba zan yi ba! Ba zan yi ba nace! Me ya saura? Kar
ka sake min barazana da sanar da iyalina saboda a yanzu bana buƙatar tashin
hankalinsu, don Allah ka rabu dani da zancen nan..."
"Mukhtar ka yiwa Allah ka bari a gwada, sai fa an gwada ake samun dacewa, zamu dace
don Allah ko ɗan uwanka mu sanar wa in ya so ko ba anan ba sai ayi, its getting
late please don't let it be worse than this u really are sufferring"
*****
Zaune take cikin tantsamemen parlorn nasu, iyayenta na kan dining suna cin abinci,
a yanzu ta san babu wacce ta kai mommy jin daaɗi saboda hankalin Abbanta da ta
kawar kan Waenchan banzayen, yanzu burinsu ya cika suna rayuwa cikin jin daaɗi su
ukun su babu wata matsala, hankalinta ya rabu gida biyu tana jin hiran irin kayen
da Abban su Mukhtar ya sha saboda abinda Mukhtar ya aikata Dukda daga baya an gane
ba sa hannunsa sai dae baƙin alƙalami ya riga da ya bushe.
Mommy tace
"ko dae farar kafafun waennan sadaka yallar da ya kwasa ba, ai sun ban mamaki daga
shi har matar tashi da basu san menene ma'anar arziki ba ai arziki shine a ci a sha
a nunawa talaka wutsiyar rakumi tayi nesa da ƙasa"
Abban Meelah yace
"nayi mamaki daga baya wai akan mutanen nan Alhj Hammad Abdulhameed yake gayamin
magana hmm gashinan nan wadda be ji bari ba ya ji hoho"
Wani irin Miƙewa da Meelah tayi tare da buga salati tana wani zazzare idanu shi ya
firgita su suka yi kan tilon er ta su a rikice suna tambayar me ya faru? Ta kasa
magana sai kawai ta sake fasa ihu
"Baki shiga uku ba! Zaki aure shi Jameelah na miki alƙawari!"
*Kar dae ku manta book 1 na gab da karewa wadda be wuci shafi biyu bane suka saura
in ma na samu lokaci a goben zan gama su, ku yi hanzarin yin payment don karatu na
gaba, in shaa Allah ba zaku yi dana sani ba.
0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin
Sai shaidar biya ta nan
09039206763
500 Naira kacal*
🖤Gureenjoh🖤
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
Book 1
*Last Page of book 1*
Ba zata ce ga yadda aka yi aka gama duk wani formalities na karɓar gawa ba, ba zata
iya fasalta halin da take ciki ba har aka gama komai da ya kamata a yi, idanu kawai
take bin taron mutanen da kaman yayyafinsu ake, a take ilahirin gidan Maami ya cika
maƙil wasu na Adu'a wasu na zub da hawaye, lallai duk wadda ya san Mukhtar a
watanni bakwai zuwa takwas da yayi bayan shiryuwar shi ya san ya rabauta, gabaɗaya
alkhairanshi na kwanakin ake tunawa, da kyar take fidda numfashi bata sanin duk
abinda mutanen da suke zagaye da ita ke cewa, ita dae gata nan ne ga yanayinta.
Adu'o'i ta cigaba da jera mishi ana amsawa, saida taji bata iya jan numfashi kan
ta dakata, babu wadda ya tsaida ta saida ta gama da kanta ta kai zaune tare da
ɗaura hannunta akan gawan ta saki sanyayyiyar kuka da ya kara ɗaga hankalin mutanen
wurin, Maami ce da itama hawaye take ta zo ta ɗaga ta, haƙiƙa mutuwa akwai ɗaci
kuma akwai zafi sannan aya ce me girma a garemu ga duk wadda ya san labarin Mukhtar
zai gasgata faɗin Allah na ɗayanku zai kasance yana aikata sharri har sai gab da
zai mutu sai ya aikata alkhairi ya shiga aljanna, haka idan babu rabo ɗayanku zai
kasance yana aikin alkhairi dab zai mutu sai ya aikata sharri ya shiga wuta. Allah
ka sa muna da rabo a aljanna.
Suna ji suna gani dumbin al'umman musulmi suka sallaci Mukhtar bayan an idar da
sallahn juma'a aka tafi da shi gidan gaskiya, gidan da kowa zai je shi, a jikin
Maami numfashin Alayah ya ɗauke rushing ɗinta aka yi zuwa hospital sanin condition
ɗinta.
****
A hankali take buɗe idanunta da suka yi mata nauyi ainun, dishi dishi take gani
hakan ya sa ta ɓata lokaci sossai idanun nata zube a ceiling kan ta fahimci asibiti
take, daki-daki haka hoton rayuwarta daga farko zuwa yanzu ke dawo mata kaman wacce
aka kunnawa magiji(television) har zuwa kan fitar da Mukhtar da aka yi wadda shine
ƙarshen abinda zata iya tunawa, idanun ta maida ta lumshe hawaye na bin gefe da
gefen kuncin ta, hannu taji ana share mata a hankali ta waiga sai idanunta suka
faɗa cikin na Meelah.
Bata san ina ta samo ƙarfin tashi zaune ba tsabar mamaki da ya so kasheta daga
kwance.
"Jameelah?"
Ta maimaita a kan lips ɗinta
Da sauri Aunty ruqayya dake zaune kan sallaya ta miƙe
"Alayah? Kin farka? Sannu ya jikin?"
Kallonta tayi ta sake kallon jameelar dake ta zabga mata murmushin da ya fi kama da
na mugunta ko na makirci a hankali tace
"da sauƙi Aunty"
Ficewa Aunty ruqayya tayi da niyyar kiran Dr yayinda Jameelah tace
"Sannu Sis, sai kawai kika ganni, mun samu labarin rasuwar mijinki ne yasa nace
bari na zo na miki gaisuwa sai kuma muka tarar kema ba lafiya gashi har yau
kwananki goma sai dae ki farka ba cikin hayyaci ba a sake miki allura ki koma,
sannu Allah ya gafarta masa"
Ta ƙarashe da fuskan damuwa.
Dukda abin da take ji ya tokare mata zuciya hakan be hana ta yin murmushin dake
bayyana zallar takaici ba, wannan kuma wani sabon salon wasan kwaikwayon ne? Baya
ta matsa ta jinginu da gini a hankali kan ta furta
"Ameen"
A kan labbanta bata sake magana ba har likitan ya shigo, ko duniya zata naɗe bazata
taɓa yardar wa kanta saboda Allah ne Jameelah take zaune a wurin ba, ta riga ta san
su farin sani son zuciyarsu kawai ke kaisu gangar wadda suka ɗauka makiyi, kuma ita
bata ga dalilin sake shigowa rayuwarsu da take kokarin yi a karo na biyu ba ka guji
soyayyar maƙiyi don da matukar wuya ya kai zuci.
Sossai Dr Philips ya dubata kan ya cire mata karin ruwan yace ta watsa ruwa ta ci
wani abu sai a mayar, Jamila ta miƙe don taimaka mata tayi saurin ɗaga mata hannu,
a ranta ta saka zata nunawa jameelar yanzu da da akwai bambanci komin ƙanƙantarshi
kuwa, duban Aunty ruqayya tayi tace
"Ayyah Aunty ruqayya ɗan taimakeni zuwa bayin"
"Ok Binty"
Kusan haka bakinsu ya riƙe sbd yadda Maami ke yawan kiranta da hakan, da taimakonta
ta shiga bayi tayi wanka da ruwa mai zafi, ko da ta fito ta samu Maami a ɗakin da
Mukhtar Junior da kuma Tabawa, sannu duk suka mata har ta zauna sai a lokacin
Jamila ta musu sallama ta fice, da kallo duk suka bita kan Alayah ta kalli Maami
"Maami ko me ya kawo ta?"
Maami tace
"yadda kika gansu haka na gansu Alayah, Abbanku ma har mamakin ganin Alhj Alhassan
ya zo gaisuwa yayi itama matar tashi tana zuwa gida, bamu dae ce musu komai ba kuma
ina so ki kiyaye don bamu san da wani sharrin suke tafe ba"
A hankali Alayah tace
"In shaa Allahu Maami"
Daga nan ta shirya aka ɗaura mata Mukhtar Junior kan kafafunta ta soma bashi
abincinshi ya ƙarba kuwa da gudu bawan Allah, haka ta zubawa fuskanshi idanu ranta
na kunar tuna Mukhtar sai dae tayi alkawari bazata sake mishi kuka ba don haka bata
yin ba sai Adu'a da tayi ta mishi a ranta.
Haka ta ƙara kwanaki kusan biyar a asibitin kan aka sallameta ta dawo gida, Takaba
take ga goyo hakan yasa lokaci ɗaya ta chanza rama ya sake mata sallama Dukda Maami
na kula dasu sossai, kullum da tunanin Mukhtar take kwana take tashi, karatunta da
take online ma sai da Maami tayi da gaske kan take ɗan bibiyan wasu abubuwan da
tace sai de tayi deffering, kowa ya san yadda mutuwa yake a hankali ta rungumi
kaddara da sabuwar rayuwar da littafin kaddara ta buɗe mata, burin ta guda ɗaya
yanzu shine ta fita takaba ta ziyarci mahaifiyarta wadda Maami ta mata alƙawari
tana fita takaba ba zasu kara sati biyu ba zasu tafi.
A lokacin da zata fita ɗin a lokacin zata soma exams kuma paper takwas zata yi
cikin sati biyu zasu gama sai su wuce, sossai take kula da mukhtar Junior da yake
girma so masha Allah.
Tana kwance akan sallaya Maami ta turo kofa da sallama ta shigo ɗakin, a hankali
Alayah ta miƙe zaune tana gyara hijabin jikinta hannunta na cigaba da jan casbinta.
"Sannu Maami"
"yauwa binty, wannan yarinya ta zo wurin ki"
Sama Alayah ta ɗan kalla da alamun tunani don bata san wace ba sai da Maami ta ce
"Jamila"
Gira ta haɗe in confused way tace
"Me yarinyar nan kuma take nema da rayuwata?"
Maami ta matso ta zauna bakin gado tace
"shiyasa ban barta ta iso har nan ba, ina so ki yi taka tsan-tsan da lamarin ta don
haka kawai ba zata soma shige miki ba bayan abubuwan da suka faru a baya, ki kiyaye
kin ji?"
Kai Alayah ta gyaɗa ai ko Maami bata faɗa ba bazata taɓa son mutanen ba, da ma ita
kaɗai suka kuntatawa da sauƙi amma har mahaifiyarta babu irin cin kashin da basu
mata ba sannan yanzu su zo suna buɗe mata haƙori kuma ta aminta dasu? Never.
Miƙewa tayi ta fito a hankali ta sauƙa stairs tana kallon Jamila dake zaune cikin
kujera hannunta riƙe da juice da aka kawo mata tana sha, tana ganin Alayah ta hau
murmushi
"sannu sis"
Ita Alayah dariya ma abin yake bata ikon najahu ji take abin na mata banbaraƙwai
wai namiji da suna Hajara shine wannan.
"Yauwa sannu"
"sai kika ganni, zan ɗan wuce ne nace bari na shigo dae mu gaisa"
Alayah da take ta kallonta abubuwan da suka faffaru wasu na dawo mata ta girgiza
kai
"eyyah na kuwa gode"
Shiru ne ya ratsa wurin kan Jamila tace
"yauwa ni ko nace akwai ƙanin mukhtar da tunda nake zuwa ban haɗu dashi ba na kuwa
so in mishi gaisuwa a matsayin relative naki"
Sai a lokacin ma wani suna umar yayi clicking mind ɗin ta, murmushin takaici tayi
ita ma bata ganshi ba bare Jamila, haushin shi ma taji tana ji da wani irin takaici
da ta rasa na menene, babu shakka kila na abubuwan da yayiwa Mukhtar ne bayan tuban
shi, kuma ace har Mukhtar ya mutu bata ji labarin ya zo gaisuwa ba.
Wasa wasa sakanni kan juya ya zama minti, mintuna su juye zuwa awanni, awanni su
zama kwanaki, kwanaki zuwa satittika zuwa watanni wai yau Alayah take cika watanni
huɗu da kwana goma cifff da mutuwar Mukhtar inda a yau din take fita takaba, kaman
yadda al'adarmu take an yi mata hidima na kayayyaki sossai da kyaututtuka kan aka
yi sadaka aka ɗan taru aka yi Adu'a, sai a lokacin Abba ya aika a kira Alayah.
A natse ta shigo babban parlorn baba ne da wasu da bata sani ba waenda suka haɗa da
aminan baban sai en uwan Abba da wasu abokan shi sai Maami, a ƙasa ta zauna kanta
ƙasa, haka kawai ta tsinci kanta da matsanancin faɗuwar gaba.
Bayan sallama da ƴar nasiha da kuma Adu'a da aka sake bin Mukhtar da ita Baba ya
dubi Alayah yace
"Mun kira ki nan ne akan abubuwa guda biyu zuwa uku Fatima, muna fata zaki bamu
haɗin kai"
Kai ta gyaɗa baba ya cigaba
"akan maganan gadon Mukhtar, kasancewar yana da ɗa kuma namiji kowa anan ya san
dukiyar kusan duka nashi ne illa iyaka za'a cire miki naki sai na iyayenshi, menene
kike tunani akan gadon yaron?"
Kowa yayi na'am da haka sai de ita Alayah ta ɗan ji wani iri, Allah ya sani zafin
wannan umar ɗin take ji.
Maami tayi murmushi dama ta san Alayah ba zata watsa musu ƙasa a ido ba, Baba yace
"Masha Allah, dama amincewar shine babba je ki Maaminku zata miki bayanin komai a
ciki"
Miƙewa tayi ta fito yayinda maami ta bi bayanta, a ɗakin Maamin suka zauna don
gidan akwai tsirarun en uwa, hannunta Maami ta kama a hankali tace
"Fatima hakika mahaifiyarki tayi matukar kokari wurin gina miki tarbiya, kowacce
uwa zata yi fatan samun sirika irin ki wacce zata taya ta son ɗan ta ta kuma taya
shi gyara tsakanin shi da Zuri'ar shi, wacce zata kula da dukiyar shi ta kare
martabarshi, wannan nagarta naki na duba na ga ba zan bari nayi asarar ki ba, ba
zan bari Junior yayi agolanci ba, ba zan iya bari ki subuce mana ba hakan yasa na
nemi da a ɗaura miki aure da umar a yau kuma Alhamdulillah baki bani kunya ba kin
amince, nayi matukar farin ciki ina kuma fata da burin mutuwa ce zata raba ku...."
Tun da Maami ta ambaci aure da umar bata sake fahimtar sauran zantukan ba saboda
wani irin tashin hankalin da ya ziyarce ta... AURE?
bata dawo daidai ba ɗan Aunty Aysher ya shigo da hanzarin shi yana ba Maami Alewa
"Maami gashi yanzu Abba ya bani wai na auren Uncle umar?"
Murmushi me kyau Maami ta saki tana furta
"Alhamdulillah har an ɗaura kenan"
Wani irin sarawa kan Alayah yayi jiri taji tana gani.
Gwarama!
*jama'ar Allah jama'ar kwarai anan na kawo karshen book one1, kaman yadda muka sani
book 2 na kuɗi ne zai zo muku akan Naira ɗari biyar kachal har yanzu akwai sauran
tafiya akwai kuma tufka da bama mu fara warware shi ba, shin umar ya san da zancen
auren? In ya sani zai karɓa kuwa? Ita kanta Alayar ba farin ciki tayi da wannan
aure ba, ita kenan haka ƙaddarar ta? In shi umar din na da wani hali fa kaman yadda
aka haɗa ta da Mukhtar a farko karfi da yaji? Ya labarin umminta zata farfado kuwa
har ta warware musu tufkar dake tsakanin Hassan da Ahmad mahaifin Alayah? Ina Ƴan
uwa da danginta? Shin kuna ganin Jamila zata yi hakuri ta bar wa Alayah Captain
Cold ko kuwa haka zata ƙare kaman yadda mahaifiyarta ta kare cikin AL'AJAB Na So?
Ta yadda tana ji tana gani abinda take so ya fi karfinta? Ku biyo ni ku sha karatu*
🖤Gureenjoh🖤