ALKIBLA Cmplt-1
ALKIBLA Cmplt-1
*_HUGUMA_*
01
*dukkan godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki daya bamu aron rai da
lafiya,tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu annabi muhammad S A W*
_a wannan karon ina neman afuwan masu karatu,littafin alqibla bazai kai yawan
littafin siradin rayuwa ko alqawarin Allah,saidai ina fatan zai nishadantar ya kuma
qayatar daku in sha Allah,ASHA KARATU LAFIYA_
____________________________
Daga can gefe daya na harabar makarantar kana iya hangen yadda matashiyar ke
tsaye goye da hannayenta sanye cikin wankakku kuma gogaggun unifoarm da suka
amsheta sosai,ta zubawa harabar makarantar tasu idanu,kamar wadda aka baiwa aikin
qididdige yawan al'ummar dake karakaina a wajen,kyakkyawar fuskarta babu alamun
fara'a ko kadan.
Duk da cewa duka duka shekarunta ba zasu haura goma sha biyar ba,amma kana
iya tantance kyan zubi diri gami da siffa da Allah ya bata.
Mai matsakaicin tsaho ce,ma'abociyar doguwar fuska da fata wadda bata cika
haske ko duhu ba,ta yadda ba zaka iya kiranta da baqa ba,hakanan ba zaka kirata
fara kai tsaye ba,tana da manyan idanu wanda ba'a fiya gane girmansu ba idan ba
budesu tayi sosai ba duk sadda taso hakan,daga cikar girarta kawai zai gaya maka
tana da yalwar gashin kai,Allah ya yi mata ado da dimple guda biyu a kumatunta hagu
da dama,wadanda sukan bayyana duk sanda ta bude baki da niyyar magana,walau tayin
ko bata yi ba.
Sake gyara tsaiwarta tayi idanunta na tara ruwan hawaye,duk da basu kai ga
xuba ba amma duba daya zakayi mata ka gane hakan,iya damuwa ta damu ta kuma
matsu,burinta kawai ta ganta a gida,Tana da burin son ganin mutane a rayuwarta da
suke da gurbi na musamman a zuciyarta,duk da cewa ta rasa babban bango kuma jigo a
rayuwarta,amma duk da haka bata rasa wasu daka iya xama makwafinsa ba bawai madadi
ba.
Abinda ya qara mata zaquwa da son ficewa daga makarantar tunda wurwuri kamar
sauran dalibai shine,komawar 'yar uwa kuma qawa a wajenta gida tun lokacin yin hutu
da fitar dalibai baiyi ba,sakamakon lalura data sameta,wadda ta tilasta aka maidata
gida,banda haka,bata da wata damuwa mai yawa kan jimawar tata.
"Fatima sa'id dabo,fatima sa'id dabo" daga bayanta taji ana kwarara kiran
sunanta,a nutse ta waiwaya tana duban mai kiran nata,daya daga cikin 'yan ajinsu ce
ladifa hamza,ci gaba tayi da dubanta har ta iso dab da ita
"Anzo daukarki,tun dazu 'yan gidanku ke nemanki" da mamaki ta maida dubanta
farfajiyar da take tsayen sannan ta dawo da dubanta kan ladifa,tayi tsammanin inda
ta tsaya din zata iya ganin shigowar motar da tazo daukar nata,bata tanka ba saita
fara takawa kawai don barin wajen,ladifa ta rufa mata baya tana tsokanarta kan
rashin kuzarinta,da yadda ta zama wani sukuku kamar ba ita ba tun tafiyar munira
gida ta barta.
Tunga taja ta tsaya lokacin data kusa isa dab da motar da akace tazo
daukarta din,mamaki bayyane qarara a fuskarta,wannan ba daya daga cikin motocin
gidansu bane,duk wani ahali na gidansu yasan wannan motar waye,ya kuma san da zaman
motar,yaushe yazo?,ya akayi ya yarda ya bada motar a daukota?,shine da
kanshi?,saita girgiza kanta da sauri,bashi bane,don ko a mafarki tasan bazai taba
zuwa daukar wani daga cikinsu ba.
"Suprise ko?" Matashiyar ta fada cikin sautin qyalqyala dariya,ba tare data
shirya ba itama qaramar dariya mai qaramin sauti ya kubce mata,wadda hakan ya baiwa
dimple din dake kumatunta damar bayyana,sa'annan kamar wadda aka qarawa qaimi ta
doshi motar,tunda taga hafsat cikin motar ta tabbatar ba abinda take zargi bane
"Wallahi kun shammaceni,na farko na zaci daga gidan abban gwammaja za'azo daukana
shi yasa na zauna jiran motar gidan,na biyu kuma saina ganku anan,ya akayi
haka...?" Cikin dariya hafsat tace
"Shigo daga ciki kisha labari....dama naci alwashin koda gold akayi motar nan saina
shigeta ai"
"Mayya....saida kika shiga din kuwa" zahra ta fada tana dariya
"Sarakan surutu...zaki kama mata sauran kayan ku shige mu tafi ko kuwa har sai
lokacin da ya diba mana ya cika bamu koma ba?" Cewar daya matashin saurayin dake a
mazaunin driver,cikin shadda dinkin zamani.
Kusan wannan 'yar tsamar ba wani sabon abu bane a wajensu,sun riga da sun
saba da hakan,wanda ba komai bane ya kawo haka ba face fahimtar juna da sabo dake
tsakaninsu,duk da cewa akwai banbancin iyaye,duka sun fito daga mahaifa daban
daban.
Saida suka hau titi sosai sannan ta gyara xama tana duban hafsat
"Wai ya akayi ne haka?" Dariya hafsat tayi kafin tace
"Wallahi ya hajja ce tace ya bada a daukoki,da yaqi ma tace to bari ta kira mas'udu
ya bada tashi tunda shi ta isa dashi,to sai da yaji haka sannan ya bayar......zahra
ma tana kusa sai data saka baki" tabe baki zahra tayi tana juyar da kanta xuwa
window,tadan dubi titi kadan sannan ta dawo da dubanta ga hafsat
"Sai kace xai mani gafara motarma sai an roqeshi,ni wallahi ya hajja data sani bata
roqa ba.....bama wannan ba,na dawo hutu da farinciki da burin samun sake,musha
soyayyarmu nida hafiz,zuwansa nasan komai saiya rushe wallahi,babu wani sauran
sake,bayan shi har gida ake biyoshi,ya kuma baje kolin soyayyarshi babu jin kunyar
kowa,amma mu ya hanamu katabus babu gaira babu dalili,bayan yafi kowa sanin tsarin
gidan,yanzu daka yi candy za'a zuba maka idanu ka kawo wanda zaka aura,idan babu ya
zama jarraba,yanzun kuma kana tsaiwa dasu shiya hana ruwa gudu,haba" ta qarashe
masifar dajan tsaki,dariya hafsat keyi abinta tana qarawa,kafin tace komai shamsu
ya waiwayo yana dubanta
"Ke yarinyar nan da gaskene fa zaki qone tun kafin ki tafasa" hararar wasa ta jefa
masa
"Saimu zauna ai ku jiqamu kusha,kunfi kowa daga murya idan bamu tsaida miji ba...."
"Meye a ciki,sadaka kawai zamu bada ku a masallacin malam ayuba" ya fada cikin
shaqiyanci yana qyalqyalewa da dariya,wanda ya saka mustapha ya dara shima,baki ta
tsuke ita kuwa kana tace
"Allah ya kiyaye ya sawwaqe,wuce nan wallahi".
Da ire iren wadan nan hirarrakin suka ci gaba da tafiya cikin motar,tana
tambayar hafsat wasu abubuwa da bata nan akayi,da kuma wadanda ta tafi ta
bari,shamsu dai bai gaji da tsokanarta ba ya sake cewa
"Sai tambaya kamar makahon daya warke daga makanta,kamar wadda aka sallamo daga
gidan yari" fuska ta narke wanda da alamu lokaci zuwa lokaci tana da dabi'ar
shagwaba wanda batasan ita kanta tana dashi ba,kusan a jininta abun yake
"To ya shamsu don Allah meye maraba,kowa an barshi yana jeka ka dawo amma ni an
turani boarding saboda shawarar da wannan mutumin ya bada,kuma wai aka amince masa"
"To ya za'ayi sai haquri,kinsan shi,idan ya kafe akan abu,amma kuma da wuya idan ya
kafe din a kasa ganin alfanun hakan" baki ta zumburo tana mita
"Kaidai kawai kana goyuwa da bayanshi ne a fakaice"
"Ko kadan,ke dince kin fiya qorafi a kan lamuransa,bayan dukka mun riga mun saba da
halayyarsa"
"Ai shikenan" kawai ta fadi,don batason zancan yayi nisa,saita kamowa hafsat wani
zancan suka shiga.
Tafiyar a qalla awa daya harda wasu mintuna masu dan dama a kai suka isa
unguwar gadon qadon qaya dake qwaryar birnin kano,bakin wani gida mai manyan
kagantu tsaho da kuma fadi suka tsaya,wanda kallo daya zaka masa tun daga waje
kasan cewa ba mace ko mutum daya zuwa biyu bane kawai ke zaune cikin gidan.
Zaka sake gasgata hakan lokacin da gate din gidan ya bude motarsu ta kunnu
xuwa ciki,sassane daban daban qunshe cikin gidan,a qalla akwai sashe hudu zuwa
biyar,kowanne na mazaunin gida mai xaman kanshi.
Kamar mai jira,tun kafin ya kammala daidaita tsaiwar motar ta balle murfin
motar ta kwasa da gudu tamkar qaramar yarinya ta nufi daya daga cikin gine ginen
dake tsakiyar gidan,madaidaicin gini guda daya dake hannun dama.
Baki dukka suka sake suna dubanta,duk da cewa sun sani ba tun yau ba halin
xahra din na daban ne,quruciya da rawar kai kamar bata qara komai cikin shekarunta.
Da sauri saurinta take kutsa kai zuwa sassan 'yar tsohuwar,burinta kawai ta
cimmata,don ba qaramar kewarta tayi ba,sabo da shaquwa ne mai yawa tsakaninsu,wanda
babu makamancin irin wannan tsakaninta da kowanne jika nata koma bayan zahrar.
'Yar kyakkyawar dattijuwa tsaye gaban freezer tana yunqurin ciro wani abu
tana magana da wata matashiyar budurwa dake xaune kan daya daga cikin kujerun falon
sanye da hijabi mai hannu kalar blueblack,kallo daya zaka mata kasan shekaru sun
fara tura mata,saidai yanayin tsafta da son gayu irin nata ya qawata tsufan nata
sosai,don kana iya hangen ragowar jan lalle dake qafarta wanda bai gama fita ba,da
tajajjiyar sumarta dake cikin dankwali,wadda ke cike da furfura,saidai kuma awanke
take fes cikin tsafta da tsari,sam bata lura da shigowar xahra cikin falon ba sai
sautin muryarta daya karade ilahirin falon.
"Sarkin neman magana,idan ya jiki kuma ya hukuntaki kice wani abu daban,shin
kin shiga ma cikin gidan ma kin gaisa da mutane ko kuwa kkka zauna neman
magana...." Kafin xahran ta baiwa hajja amsa hayaniyar 'yammatan gidan ta soma
dosowa falon
"Tofa,Allahumma salli ala,aikin dawo,yanzu zaku taru ku dinga hanani sakat,sauqin
abunma dodonku yana gari shima"
"Ni wallahi hajja ki dinga hanashi zuwa duk sanda zanzo hutu,tsakani da Allah fa
hanani sakewa yake,hutun wata daya kacal din da nake samu saina qareshi cikin
rashin jin dadi" baki hajjan ta kama tana dubanta,ta rasa wanne irin abune haka
irin na zahran,qara kusantowar hayaniyar tasu alamun suna bakin falon yasa ta dauke
kai ba tare da tace komai ba har suka qaraso cikin falon riqe da hannuwan
jakankunan zahra guda biyu,wanda ta barsu a farfajiyar gidan bata samu daukosu ba
saboda tsabar zumudi.
Wani ihun murnar ganin juna suka saki kowacce na neman wajen zama
"Kai amma naji dadin dawowarkin nan wallahi,kinxo akan gaba" salma daya daga cikin
'yammatan ta fada,harara yusra ta jefa mata daya daga cikin fararen 'yammatan
"Eheen,kedai kin shiga uku wallahi"
"Ke kuma fa,tara kika shiga?" Salma ta fada itama tana maidawa yusra hararta duk da
cewa mai kama da dariya dariya ce
"Kinga manta da ita,bani nasha ya akayi?"
"Bari mu saka labule tukunna saboda 'yan saka eyes....."
"Kunga ku tashi ku bani waje tun ban kira yayanku ba" hajja ta fada saboda sanin
hali,ta sani sarai labarin nasu baya wuce na samarinsu shi yasa tayi musu
haka,sosai suke wasan jika da kaka da ita,tun tana fada da fushi harta haqura ta
qyalesu ta zubawa sarautar Allah idanu,harya zamana ma yanzu bata damuwa ya zame
mata jiki,mutum daya ne tak da idan yana nan take samun salama,saboda dukkaninsu
shakkarsa suke,kuma tsoron hukuncinsa suke.
"Idan wajen mama zaki don Allah ya zahra kice mata yanzu zan shigo na mata
bayanin aiken" yusra ta fada tana duban zahra wadda ta miqe da wayarta a hannu tana
murmushi
"Bafa can zata ba" hafsat wadda ta shigo daga qarshe ta fada
"Kema ai tunda kika ga ta miqe tana doka murmushi ai kinsan kwanan zancan" hafsat
ta sake fada tana yin fuska,cikin dan jin kunya da nauyi zahra tace
"Kamar a kunnenshi kika fada" saita soma yin gaba cikin sauri sauri yayin da hafsat
ta bita da magiyar ta tuba tayi haquri ta fice abinta tana dariya.
"Ni ina mamakin yadda soyayya ke gudana tsakanin yaya da yaa zahra"
"Ahto ai haka Allah ke lamarinsa,ku kuke masa wani kallo da bahagon hukunci,saboda
ALƘIBLARKU ta bambanta ta wajen ra'ayi,kowanne bawa komai irin halinsa akwai yadda
Allah ya sallada wanda zai iya zama dashi ya kuma rayu dashi".
Tsam zahra ta miqe tana maida hijabin unifoarm din jikinta,wanda har yanzu
bata kai ga cirewa ba tana cewa
"Bari na shiga ciki kan ku gama lacture din" don sam bata son irin wannan dogon
sharhin na hajja,gani take koda yaushe aikinta shine bashi kariya dason wankeshi a
idanunsu,bagan sun riga dasun gama sanin halayyarsa ciki da waje,kuma kowacce
cikinsu ta kwana da sanin wannan,so tana ganin babu buqatar dagiya wajen bashi
kariya da yima halayyarsa kwaskwarima a tsakaninsu.
Kamar hajjan zatayi magana sai kuma tayi shuru kawai ta bi zahran da kallo
sanda take ficewa daga falon abinta ko a jikinta,har takai bakin qofa saita dakata
"Don Allah hajja wayata,tunda na dawo nake jina ba dai dai ba,na tabbata nuruddeen
nacan yana nemana wallahi,tunda yasan yau zamu dawo" daquwa wannan karon ta watsa
mata
"Qaniyarki,yanzu nake muku nasiha kika tashi kika barni zaune wajen,shine yanzu
kikeso naje na dauko miki waya,idan kin damu ai kinsan mazaunarta kije ki dauko da
kanki" dariya tayi cike da nishadi,ita da hajjan sun saba hakan,suyi tsiya suyi
dadi,duk yadda suka kai ga shaquwa da juna amma indai akan irin wannan batunne sun
saba haurawa,ita sam dole saita sanyata sun jitu da juna,ita kuma tana jin wannan
shine abu na qarshe a rayuwarta da bazai taba yiwuwa ba,komai nasu yasha banbam,tun
kan ta mallaki hankalin kanta yadda ya kamata ta fahimci alqiblarsu tasha
banbam,hakan ya haifar da duk wani abu dake gudana a yanzu.
Kanta tsaye ta nufi dakin gadon ya hajjan,harta kusa sai kuma ta sauya
akalarta zuwa kitchen dinta,inda take jin qamshin abinci na fitowa.
A nutse ta tura qofar tana wara idanu don ganin wace a kitchen,kamar kullum
gaji ce,'yar aikin hajjan qwaya daya tilo data jima da ita,takun shigowarta ya
sanyata waiwaya tana duban qofa,cikin fara'a da washe baki ta qarasa waiwayowa gaba
daya
"A'ah,ashe kina hanya inna wuro.....marhaba da uwar dakina" murmushi zahra ta
saki,saboda gaje ta wajenta ce sosai,yadda ya hajja ke ji da ita haka itama gaje ke
ji da ita
"Yauwa inna gaje,na sameku lafiya"
"Lafiya qalau alhmdlh inna wuro,ya makaranta?"
"Mun gode Allah" zahra ta fada tana neman wajen zama saman kanta,kusa da wasu
kwanuka data gani a rufe,hannu ta miqe tana shirin budewa gami da cewa
"Me aka tanadar mana haka yaketa zabga qamshi"
"Gasunan bude ki gani,duka naki ne hajja tace a yi miki" a nutse ta dinga budewa
tana dubawa,sosai taji dadi har ranta,hakan kuma ya bayyana zuwa saman
fuskarta,batun yau ba ta shaida da soyayyar da kakar tata ke mata,bata san me yasa
ta fita daban cikin jikokinta ba,ko don sunanta taci?,ko kuma don ita din ita daya
ce ta zama marainiya a cikin tarin jikokin hajjan?,saita ture wannan tunanin ta
sanya hannu ta soma daukan abinda ke cikin kwanon tana sawa a bakinta.
Duk sai data gama dandanawa sannan ta fara lashe yatsunta tana cewa
"Ashe dai 'yar tsohuwar nan na sona haka,bari naje cikin gida na gaida mutane inna
gaje na dawo" ta fada tana ficewa da dan sauri saurinta ba tare data saurari abinda
inna gajen ke cewa ba.
*MAMUHGHEE* _UBAIDMALEEK_
*BILLYN ABDUL*
_MAKAUNIYAR QADDARA_
*MISS XOXO*_DALAAL_
*HUGUMA*_ALƘIBLA_
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
02
Falon yanzu babu kowa duka sun yoye sai ya hajjan kawai,tana zaune tana gyara falle
fallen littafin dala'ilu,da alama ta karantasu ne suka kuma hargitse mata take
gyarawa,don ita din har tsufanta bai hanata bibiyar litattafan addini ba.
Tana yawan godiya ga Allah daya sanya qauna da zumunci mai qarfi tsakanin
ahalinta,tun daga kan yaranta zuwa jikokinta,tsabar son su zamaTsintsiya madaurinki
daya ya sanya tun mijinta na raye suka yanke zaman dukka yaransu maza tattare a
waje daya,matanne basu da wannan ikon ko qarfin a kansu,hakan kuma yayi tasiri
wajen sake maida zuri'ar tata tsintsiya madaurinki daya,duk da ance zaman tare zo
mu zauna zo mu saba,hakanan baka rasa banbancin halaye da ra'ayi wanda kan kawo
sabani lokaci zuwa lokaci,saidai a nata ahalin akwai qarancin hakan sosai,don bazai
yiwu ace babu ba,kusan halayya ce tadan adam,kuma sunna ce ta zaman tare.
Duk da wannan babban abinda ke bata mamaki da daure mata kai shine rashin
jituwar dake tsakanin zahran da yayanta,kusan abune daya dauko dogon tarihi ya kuma
samo asali da tushe tun da dadewa,tun abun bai zama wani abun damuwa kallo ko
dubayya ba har takai a yanzun yana damunta lokaci zuwa lokaci,saidai tana saka ran
watarana komai zai zama tarihi,kamar akwai sauran quruciya ne jikin xahran.
Sashen yayan mahaifinta da suke kira da abba babba ta fara shiga,sashe ne mai
kyau kamar yadda ainihin ginin gidan ya nuna,babban falo wanda ya cinye set din
kujeru har guda biyu,dakuna a qasa kitchen da bandaki,sai dakunan matan gidan dake
sama,duk da kowacce tana da guda daya a qasa.
Mommy ta tadda a falon ,wanda ke mazaunin amaryar abba babba tana cirewa
yara da dawowarsu gidan kenan unifoarm,wanda dukkansu yaran gidan suna makaranta
guda ne,akan daukosu tare a kuma kaisu tare,bisa jagorancin drivern gidan a
wadatacciyar motar da aka ware musu don wannan hidimar.
Sashe na biyu ta shiga,sassan abba yusuf,wanda keda matan aure biyu shima da
yara tara,amarya nada uku,uwargidan nada shida,shima dai kamar shigen ginin waccan
sashen,komai cikin tsari,da alama kusan dabi'ar jama'ar gidan ce wato tsafta,su
dinma faran faran suka gaisa ta wuce sashen abba abu wanda cikakken sunanshi shine
abubakar,matarshi daya da yara bakwai,sai abban tsakiya shima matarshi daya,daga
nan sai sashen mahaifinta.
A hankali tayi sallama cikin falon,qannenta dake xaune suna cin abincin rana
suka amsa,cikin farinciki qauna irin ta 'yan uwantaka suka miqe suna mata
oyoyo,fuskarta washe da fara'a take amsa musu,wanda hayaniyarsu ta fito da
mahaifiyarta dake kitchen.
Duk da cewa bata rasa wani gata ko kulawa daga nata dangin ba,amma hakan bai
hanata amsar tayinsu ba,saboda tsantsar dattako irin na uwar mijinta,da yadda ta
nuna mata qauna da kulawa tun haduwarsu har xuwa yau din,bugu da qari kuma,bata jin
xata iya sake aure a sauran rayuwarta data rage,tunda ta rasa miji daya tamkar da
dubu irin sa'id uban 'ya'yanta.
Ita dinma tafison zaman can din,saboda tafi sakewa sosai fiye da
sassansu,hajjan na barinta tayi yadda takeso koma bayan ummin nata dake da tsauri
da kuma dokoki iri iri.
Kai tsaye ta koma sassan hajjan,duka sun fice da alama kowacce akwai abinda
zatayi,hakan ya mata itama saboda wanka takesonyi ta kuma rama bashin baccin da
batayi ba daren jiya a makaranta,don su kwana waqe waqe na murnar tafiya gida
hutu,gabanin asuba koma kowa ya shiga sabgarsa taci gaba da hada kayansa da kuma
bin layin wanka.
Sai data fara zuwa gun wayarta dake chargy,hopefully ta taba screen din ya
kawo haske cikin zumudi,don ta tabbatar zata iske texs ko miscal na nuraddeen kamar
yadda ya saba mata a kullum idan ta dawo hutu.
Saidai kuma ga tarin mamakinta babu kiran hakanan babu saqon nashi,sosai
abun ya daure mata kai,amma saita bashi uzuri,ta shiga ta duba balance dinta.
Naira hamsin ce tayi ragowa a layin nata,ta tuna zahra takwararta ce ta mata
transfer kyauta ana ya gobe xasu koma hutu,tunda tace ga wanda ya tura mata kudin
ta raba musu 50/50 a ciki sai taji credit din bai burgeta ba,amma yanzun zai mata
amfani,don haka kai tsaye ta shiga rubuto lambobin nuraddeen daka wanda ta jima da
haddacesu ta danna kira,take sunan my happiness ya bayyana saman screen dinta,ta
kalli sunan ta saki murmushi tana kuma sauraron yadda wayar ke ringing.
Harta gama gyaran bataji shigowar kira ba,sai data miqe tana shirin shiga
bandaki ta watsa ruwa taji sautin shigowar saqo,ta miqa hannu da hanzari tana
dubawa,saqon daga nuradden dinne
"Zan kiraki" abinda ya qunsa kenan,saita maida wayar ta ajjiye ranta tana cewa
"Lallai yau wanne irin busy happiness ya shiga haka" ta wuce bandakin bayan ta
daura towel din wanka.
Aqalla minti goma sha biyar ta shafe a bandakin sannan ta fito tana mita
"Haba,babu inda yakai gida dadi,me za'ayi da makarantar kwana,babu abinda yakai
gida dadi wallahi,inda a school ne ina ka isa ka dade haka,da tuni an matsanta miki
daki fito,mtseww...wallahi badan yaaya da kuma ummi da bazan koma ba" da wannan
qananun mitocin mata ta qarasa gefan qatuwar kafitar dake dakin ta zauna,wanda
daura da ita 'yar drower ce dake jere da kayan shafe shafenta,zahra ba daga baya
bace wajen son ado da kwalliya,hakanan idan ta fannin yawan sutura da kayan qyale
qyalen rayuwa ne tana sahun gaba cikin 'yammatan gidan,saboda ta kowanne fanni yi
mata ake dalilin maraicinta,qannen mahaifiyarta mata da yayan mahaifiyar nata dake
matuqar qaunarta,wanda dukkan abinda xaiwa yaransa to lallai fa saiya yiwa
zahran,hakanan 'yan uwan mahaifinta dake gidan,duk sanda wani xaima iyalinsa saiya
hada da ita,ga hajja a gefe itama da ba'a barta a baya ba.
Sa'annan uwa uba wani irin farinjini da Allah ya yiwa zahran tun tana
mitsitsiyarta,don mahaifanta ma sam basa yarda a karbi abun hannun kowa akan
yarinyar,haka halittarta take,tun abun na baiwa mamanta mamaki harya koma bata
tsoro,hakan ya sanya tun kan ta mallaki hankalinta ta tsaya kai da fata wajen mata
addu'ar samun kariya da samun miji na gari,don ita kanta tasan Allah ya yiwa
diyartata baiwar wani asirtaccen boyayyen kyau,tana tsoro n kada hakan ya zama wata
sila da za'a shiga rayuwar diyartata a cutata mata babu dalili,ta sani cewa sautari
baiwar kyau jarrabawa ce,qalilan ne kuma cikin mutane ke iya cinyeta,musamman mata.
A nutse ta kammala shiryawa cikin doguwar rigar atamfa cotton mai budadden
dinki,ta gyara kanta da ribbom wanda da wahala kaga kitso a kanta,duk wanda ya
santa yasan bata qaunar kitso tun yarinta har zuwa yanzu data girma,duk sanda xa'a
mata kitso saita tarawa mai kitson jama'a saboda tsabagen kuka,daya daga cikin
abinda ya sake sawa basa jituwa da yayanta kenan,yana ganin kamar an bata ta ne an
sangarta ta.
Tana tsaka da fesa turarenta mai sanyin qamshi wanda ta saba ta soma jiyo
sautinsa.
Sassanyar murya mai zaqi,amma cike da kaushi da kuma fada yake magana,da
alama wani abun ya faru ne,baki ta tabe tana aje turaren nata,maimakon ta fito
yadda tayi niyya da farko sai kawai ta fasa,ta koma gefan katifar ta zauna tana
sauraren fadan nashi,duk da cewa bata iya fuskantar me yake fada.
Dariya hafsa ta saki tana daka mata duka,tana sane ta sako wannan zancan,don
duk cikinsu kowa ya san ra'ayin mahaifansu ya dace da ra'ayin zahran,kuma ita hakan
yayi mata dai dai
"Allah ya shiryeki zahra"
"Amin....ai dan sunna bayaqi sunna ba ko"
"Wannan haka yake malamarmu"
"Kyaji dashi" ta amsa mata tana sake jawo wayarta ta fara buga game,jifa jifa suna
hira,tana kuma dakon daina jin motsinsa a falon hajjan data samu ta fita taci wani
abun kafin ta dawo ta kwanta tadan matse gajiya.
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: *KIJI TSORON ALLAH☝�?,KARKI TABA KAYAN DABA NAKI
BANE,BA KUMA MALLAKINKI BANE*
03
Kusan minti talatin kafin ta daina jin duriyarsa,zuwa sannan bacci ya soma
fisgar hafsat,saita aje wayarta ta miqe a hankali tana gyara daurin dankwalin
kanta,ta isa bakin qofar dakinta ta zura takalmanta sannan ta wuce kai tsaye zuwa
falon.
Kallo daya tayi masa ta tabe baki,duk da bata samu nasarar ganin fuskarsa
ba sai sumarshi dake gyare,ita bamai yawa ba ba kuma saisaye ba,saidai tafi kama da
saisayen irin sama saman nan,tayi wani spring kamar zubin indomie,baqa sidik tana
sheqi,da alama ana bata kulawa yadda ya kamata,don ba qaramin qara masa kyau da
kwarjini takeyi ba,ta kuma dace da kalar kwantacciyar skin dinshi da hausawa ke
cewa wankan tarwada,ga duk wanda ya dubeta yasan ya samu cikakken hutu dajin
dadi,duk da kalar aikinsa bawai na hutawa bane waje daya,saboda aikine na hidimtawa
qasa,da bada kariya da tsaro wa dukiyar al'umma da rayukansu.
Saɗaf saɗaf take tafiya saboda bata da buqatar ya ganta,dab da zata gotashi
ya daga kanshi,saida gabanta yayi mummunar faduwa,kallo daya tak ya mata ya maida
kanshi ga wayarshi,kamar baisan Allah yayi wanzuwar wata halitta ba,tilas ta fasa
qudurinta na wuceshi da tayi niyya,ta dawo da baya
"Ina yini yaa haidar" kamar bai jita ba,hakan ya bala'in ɓata ranta,ta tsani wannam
halayyar tasa fiye da kowacce,ita idan zai shekara zaune a waje baiyi magana ba ba
damuwarta bane,amma don me mutum zai gaidashi ya watsar.
Kamar tayi tsako don takaici amma tasan bata isa ba,wato saboda tsabar izza
yana jiran wanda zai zuba mishi ne,akan ya zuba da kansa ya gwammaci yayita jira
har sai mai zuba masan yazo,laifin bana kowa bane saina zahra,ita ta batashi,don
tana fara zuba abincin ta tabbatar girkin ma nata ne,ita ta dafa mishi.
Tana wannan tunanin zucin naman data debo a serving spoon daya ya subuce ya
koma cikin miyar,take ta fantsamo man dake saman miyar,ya kuma samu kyakkyawan
masauki saman farar shirt din dake jikinsa.
Da sauri ya daga kai daga danna wayar da yakeyi,ya dubi jikinsa sannan ya
maida idanunsa saman fuskarta,zallar bacin rai ta hanga qarara,ta soma motsa baki
da niyyar yi masa bayani saidai ya rigata magantuwa
"U r very stupid....baki da hankali ne?...."
"Ashsha.....inna wuro garin ƙaƙa?" Muryar hajja ta ratso falon,duk rashin tsoronta
amma sai da taji kamar anyi mata rahama,kafin ta bata amsa ta iso
"Tashi maza ki samo omo da dan toli fefa a goge mishi" tsaki ya saki kawai yana
miqewa,ba tare da yace da kowa komai ba ya soma takawa yana nufar qofar fita
"Ka tsaya a goge maka mana zaki(haka takan kirashi dashi ita da wasu
mutanen,sakamakon sunan mijinta da yaci,bata iya kiran sunanshi)"
"No,barshi kawai"
"Abincin fa?" Ta fada sanda yake gab da ficewa
"Ku amfaneshi"ya amsa a taqaice yana qarasa ficewa.
Bugu hajja ta kaiwa zahra wadda ke tsaye tana yiwa qeyarsa gwalo gamida
murguɗe murguɗen rawa
"Ja'irah,hala kina sane ko?" Dariya ta saki tana zama gurbin daya tashi,wanda ke
fidda qamshin turarensa ta soma sake bude kwanukan tana baiwa hajja amsa
"Inda ina sane ai da sai abun yafi haka.....arashi aka samu,kuma hakan yamin dai
dai"
"Zahra....zahra....kinga ki fita daga idona akan yayanku,kamar ba jininku daya ba"
"To hajja ko kinfi sonsa yanzu a kaina ne?,babu inda nake sakewa fa sai nan,haka
kawai sai nan dinma yazo ya zauna ya hanamu sakewa,idan na koma wajen ummi canma
yana nan,da nayi wani abu itama ta hauni da fada itama,don ya girmemu kawai saiya
damemu" daga haka ta jawo fulasan tahau zubin abinci Abinta tabar hajja da kallon
ikon Allah"
"Allah ya shirya" hajjan tace tana sauke ajiyar zuciya kawai,bata amsa mata
ba taci gaba da zurin abincinta.
Salma ce tayi sallama cikin falon tana tsaka da cin abincin,sanye da atamfa
dinkin A shape,sai dan kwalinta data zarga a kanta,hannunta riqe da qaramar wayarta
me keyboard itel,wanda akafi kira da rakani kashi,kusan dukka gidan zahra ce me
waya torching,ita dinma sai da aka hau rimin gafiya kafin a samu lamuncewar oga
kwata kwata haidar ya barta da wayar,a hakanma bisa goyon bayan hajja,saboda abban
gwammaja ne ya kawo mata,ita kuma tace sam ba za'a watsa masa qasa a idanu ba,tunda
wayar bawai wata babba bace can,sannan uwa uba an hanata walwala an dauketa an
kaita makarantar kwana aiko ba'a hanata riqe waya ba a duk sanda tazo hutu,tunda
hutun ai baya wuce wata guda kacal,uwa uba kuma ma rashin riqe wayar yafi riqeta
yawa,hakan yasa dole aka barta da abarta.
Saman carfet din dakin suka zauna,salma tadan dubi hafsat dake baccinta
haiqan
"Shegiya kasa,bata da aiki sai bacci" ta fada tana zungurarta,idanu tadan bude
kadan,ta gane salma
"Ki saurara min 'yar baqincikin baccin mutum" daga haka ta cusa kanta qasan filo
tana gyara kwanciyarta su kuma suka shiga hirarsu
"Wai kinsan meke faruwa kuwa?"
"A'ah saikin fada" inji zahra
"Sabon kamu fa nayi" sosai zahra ta maida kallonta ga salma
"Kamar yaya?,sabon kamu bayan sulaiman din?" Farr tayi da idanunta
"Wallahi,kuma a yadda nake jinsa a raina zan iya hada matsayinsa dana sulaiman"
idanu dukka zahra ta fiddo waje
"Keee salma.....kiji tsoron Allah,sulaiman din?" Kai ta gyada kai tsaye itama tana
dubanta
"Shi dinfa,meye abun naji tsoron Allah a ciki?,igiyar aurensa ce a kaina koko
yaya?,don kawai na zabawa raina shi a matsayin wanda raina ya amince na nuna duk
lokacin da aka buqaci na nuna wanda na tsayar?" Kai zahra ke kadawa kawai dama da
hagu cikin nuna zallar jimami
"Gaskiya nidai bazan iya ba,haba amana ai bata ce haka ba".
Dariya sosai salma ta saki har tana toshe baki kana daga bisani ta tsagaita
tana duban zahra
"Amma inna wuro na yadda lallai boarding ta dakusar da duk wani wayo da basirar da
muka sanki dashi,wai ce miki akayi su samarin yanzun tsoron Allahn sukeyi?,ko ce
miki akayi idan don saurayin yanzu yana gaya miki da nuna miki daga ke babu
wata.....idan bake ba sai rijiya,kece rayuwarsa da sauransu yana nufin hakanne da
gaske har a badininsa?,bance miki fau fau ba'a samun wanda hakan bane.....amma
sunyi qaranci qwarai,da yansu maqaryata ne,maha'inta ne,basu da *ALƘIBLA* qila kece
ta bakwai kota goma a wajensu,hakan yasanya nima bazanyi saki na dafe ba,na laru
dashi shi daya ina masa son gaskiya da dukkan zuciyata da gangar jikina ba.....na
shafa rana guda naji wayam" ta qarasa maganar tana bugun cinyarta.
Shuru zahra tayi nadan wasu sakanni tana nazari a zuciyarta,sam maganar
salma bata samu mazauni a zuciyarta ba,hasashene kawai irin nata da kuma son baiwa
kai mafaka,banda haka ita shekararta nawa da nuraddeen bata taba ganin wani abu
tattareshi dashi koda sau daya bane makamancin wanda salma ke hasashe?,a kullum
soyayyarsu qara gaba take,kishinta yake kiyaye bacin ranta yake,don me zata yarda
da zancan salma 'yar tamore
"Nikam bazan iya wannan kwamacalar ba" zahran ta amsa mata bayan takai qarshen
nazarinta tana tanqwashe qafafunta waje daya,qaramar dariya salma tayi
"Eh....kekam taki zuciyar na daɗe da sanin cewa daban take,kinayin soyayya ne
dakkan yaqini da amannarki,wanda a yanzun samun hakan yayi qaranci daga wajen mazan
har matan" kusan hirar da suka dinga yi kenan a tsakaninsu,wanda har ya kusa kaisu
ga musu.
Duk da wannan hirar da ake amma hankalinta nakan wayarta lokaci lokaci,tana
tsumayin nuraddeen kowanne lokaci,amma saidai har suka tasamma watsewa saboda
lokacin ɗora girkin dare yayi a kowanne sashe,kasancewar kowaccensu duk da akwai
masu aiki ɗai ɗai a kowanne sashe amma ba'a barsu sun zauna sun ta'allaqa komai a
kansu ba,babu nuradden ba duriyarsa,don haka ta jawo wayarta ta miqe da ita tana
tunanin zuwa wajen yaa zahra ta tura mata updated watsapp,don nata yayi expair.
Dukkaninsu sun hangeshi,duk da cewa bayanshi kawai suka hango amma babu
wanda bai ganeshi ba cikinsu,saboda haka kowacce taja bakinta ta saisatashi gami da
rage sautin muryarta.
Sanye yake da wata farar riga ƙal me gajeran hannu,wanda hakan ya baiwa
murɗaɗɗen dantsensa damar bayyana,sai dogon wando shima fari gamida wani farin
booth dake qafarsa,daga inda kake wucewa kana iya jiyo qamshin lallausan turarensa
da iska ke kwasowa tana bazashi ko ina,ba kayan dazun bane a jikinsa,da alamu ma
wanka yaje ya sake ya sauyasu saboda miyar data batashi,waya yake amsawa,kallo daya
zaka masa kasan cewa yes!,aikin da yake yayi matuqar dacewa dashi,ko shafawa kayi
kasan cewa shi din SOJA NE.
Suna gab da rabuwa kowa ta shige sashensu ba tare da sun ankara ba sukaji
muryar ya musty na nufosu yana fadin
"Yaa haidar na magana fa 'yammata" dukkansu babu wadda cikinta bai murɗa mata
ba,yusra da tafi kowa tsoro cikinsu cikin rawar murya tace
"Wa yake kira a cikinmu?"
"Dukanku" ya bata amsa yana qunshe dariyarsa,don basu ba,hatta su da suke maza ba
kasafai kiran haidar ke musu daɗi ba.
Junansu suka kalla,yusra ta sake cewa cikin qas qas da murya don kada ya
jisu
"Amma me kuma muka yi masa ya musty don Allah?"
"Idan kunzo kwaji" daga haka shima ya juya abinsa don kada yayi laifi.
"Kome zai mana ai bazai rabamu da numfashinmu ba ko?,kuzo muje" inji hafsat
qanwarsa wadda suke uwa daya uba daya,zahra ko tabe baki tayi,duk da cewa ita dinma
a tsorace take,haka suka nufeshi sum sum kamar waɗanda suka ɗauko gawa.
Gaba daya su bakwai din suka zube gabanshi,yayin dashi kuma ke tsaye abinsa
yana latsa waya kamar baisan An haliccesu wajen ba.
Saida suka tsammaci ya manta dasu a wajen,sannan ya buda baki kamar wani
saraki ya jefo musu tambaya yana ci gaba da latsa wayarsa
"Wace inna wuro a cikinku?" Tambayar duk saita zo musu wani banbarakwai,tunda
sunsan dai duk wanda ya kwana ya tashi cikin gidan ya san me sunan,hakan yasa suka
kasa amsashi suka hau kallon kallo.
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: 04
Sake maimaita tambayar yayi a karo na biyu dai ba tare daya kallesu ba,sanin
hali yasa suka fara yunqurin nunata kawai,saidai basu kai ga aikata hakan ba
tsawarsa ta mamayesu wanda ta rudasu,ba shiri kuma suka nuna zahra dake tsakiyarsu.
"Daga dawowarki yau shine kikeson maida mana qofar gida tasha?" Ya jefa mata
tambayar da batasan amsarta ba,hakan yasa tayi shuru tana nazari,tare dason gane me
yake nufi da hakan
"Am asking you!" Ya kuma fada cikin tsawar data dan razanata,wannan karon bai jira
amsarta ba ya dora da
"Wato kaiko boarding da akayi baisa komai ya canza ba ko?,su samarin da sukazo suna
son mana tumasanci qofar gida duka ina kika sansu kina kulle cikin makaranta?,koko
malaman naki ne soma biyo sawunki?,duka duka shekarunki nawa?tun baki tafasa ba
zaki qone?,to i wil deal with u,bazan dauki wannan iskancin ba tun baki riqa ba,ba
zaki fi qarfinmu ba,ki gayawa kowanne shashasha duk randa ya sake zuwa qofar gida
ya mana fada saina masa daurin da za'a kasa ganeshi,ba gidan 'yan iska bane
nan,hope kin haddace abinda nace?" Tuni hawaye ya soma ambaliya saman fuskarta
saboda tsabar bacin rai,hakanne yasa ta kasa amsa mishi,har sai daya maimaita mata
cikin tsawa
"Kinji ko bakiji ba?"
"Naji" ta amsa cikin muryar kuka
"Ku bacemin a wajen sakarkaru kawai!" Ya kuma fada cikin tsawar.
Tuni suka miqe har suna rige rigen barin wajen,sai da suka tabbatar sun bar
inda zai iya jinsu suka fara bawa zahra dake kuka haquri,kasa amsa musu da komai
tayi,ta kuma kasa zuwa tura watsapp da zuwa sassan umminta don tayata dora girkin
da mafi yawancin lokutta nata girkin dana hajja take hadawa,duk da itama hajjan
idan tayi sha'awar wani abun tana dafa abinta,sai kawai ta juya ta koma sassan
hajjan da sassarfa kuka Na sake qwace mata,maganganunsa na dawo mata.
Me yake nufi kenan?yana mata kallon 'yar iska ne koko meye?,bin maxa take a
makarantar kenan har suke biyota gidan ubanta yake nufi?ko ita ta kirayesu tace
suzo,bayan batama san kosu waye sukazo din ba,fatanta daya Allah kada yasanya da
nuraddeen dinta akayi hakan.
Saman kujera ta zube a falon tana qoqarin tsaida qwallarta duk da taqi
tsaiwa,daidai lokacin hajja ta fito daga dakinta tana riqe da carbi,da alama
zikirinta data saba takeyi.
"Ke lafiya?,kukan me kike bayan qalau kuka fita?" Hajjan ta jero mata
tambayar tana tsaiwa kan zahran tana rungume da hannunta fuskarta cike da damuwa da
fargaba.
Kasa bata amsa tayi saboda yadda zuciyarta ke suya,sai data dauki wasu
mintuna kana cikin sheshsheqar kuka ta gaya mata abinda ya faru,sannan ta dora da
cewa
"Ki masa magana hajja,ki shiga tsakanina dashi"
"Ya isa,amma karna qara jin kince haka saboda yayanki ya miki fada,kawai maganganun
daya fada dinne basu dace ba,tunda an jima ana wannan case din,kuma duk sanda irin
haka ta tashi ina masa bayani,dole su dinga haquri wata macen haka Allah ya
halicceta da farinjini,kome qoqarinta na ganin ta kaucewa samari bata isa ba
musamman idan tana kan ganiyarta,yanzu dai ki tsaida kukan nan haka,zaizo ya sameni
har inda nake".
Dan zama cikinsu tayi aka dan taba cafta,don ta tadda ya musty da
adam,wadanda dukkaninsu gwanayen raha ne da barkwanci,ba zaka ce ciki daya suka
fito da yaa haidar ba,shi kadai kusan ya fita zakka a cikinsu
"Ina yaa zahra ne?" Zahran ta tambaya unaisa dake wani assigment,duk kuma rabin
hankalinta nakan tv
"Tana ciki ita da ya hafsa"
"Abba babba fa?"
"Ya fita masallaci bai dawo ba"
"Ok" ta fada tana miqewa,kanta tsaye ta nufi dakinsu hafsat din.
Zahrar na zaune saman dressing chair dake gaban mirrow din dakin,sanye da
purple din hijabi mai hannu,ma'abociyar sanya hijabi ce,zaiyi wuya ka sameta babu
hijab,duk wanda ya santa a haka ya santa,yasira na qasan dakin zaune tana cin
abinci,hafsa na zaune saman katifa,hannun zahran riqe da wasu takaddu,fuskarta cike
da fara'a,da alama cikin farinciki take,jifa jifa suna taba hira dasu yasiran zahra
tayi sallama.
Dukkansu suka amsa mata zahra na sauke qafarta data dora daya saman daya
tana gyara takardunta dake riqe a hannunta
"Yanzu nakeson gama cin abinci naje na amso tsarabata" yasira ta fada tana dauke
hannunta daga kwanon abincin,murmushi zahra tayi wanda ya bayyana jerarrun
haqoranta tana jifan yasira da harara
"Wai wuni guda don Allah ina kika je?"
"Au basu gaya miki ba?,wallahi shirye shiryen bikin huda muketa yi,mommy tace naje
ayi dani,tunda hudan nata naci da mitar naqi cewa komai" idanu xahra ta fidda
"Wayyo,kada dai kice babu ni za'ayi sabgar?,saura sati nawa?"
"Sati biyar ya rage" saita narke fuska kamar zata sanya kuka,harga Allah taji babu
dadi,don taso ace tana nan za'ayi bikin,don suna shiri da huda sosai
"Sati daya da komawata school kenan fa?,kai ya rabb,ka rabani da wannan boarding
din" dariya dukka suka saka mata,saboda kullum bata rasa abun qorafi dangane da
makarantar,amma sun sani dole tayi haquri ta qarasa,tunda tazo tsakiya.
Neman wajen zama tayi bayan ta yiwa yasiran fatan alkhairi a bikin ta dubi
xahra
"Takwara....zuwa nayi ki turan watsapp,nawa yayi expeir.....amma naga yau fuskarki
kamar gonar auduga" caraf hafsa ta karbe
"Yo ba dole ba.....ta samu admission fa a kust wudil" cikin mamaki zahra ke duban
hafsa,abu biyu ya bata mamaki,na farko ya haidar data tsayar a matsayin wanda
zasuyi aure ita dashi ya sani ya kuma aminta cewa zatayi?,abu na biyu indai kuwa
hakanne su me yasa harda shi cikin masu dokar ba zasu ɗara daga secondry ba?".
Maida dubanta tayi ga zahra dake murmushi kawai tana dubansu,tana kuma
mamakin yadda suke sanyawa yayansu tsanani da yawa haka,duk da ta sani cewa shi
dinma ba kanwar lasa bace,baida sauqi ta kowanne bangare,hakanan bauɗaɗɗen mutum ne
me wuyar sha'ani,wanda idan baka fuskanceshi ba baka kuma karanci ALƘIBLArsa ba
zaka ci wuyar zama dashi,amma kuma yana da dadin xama qwarai idan ka ganeshi ka
kuma gane wayeshi,ka tsare doka da qa'odojinsa,ita din shaida ce,don bata tunanin
soyayyarsu xatayi tsahon rai haka ba,bata taba tunanin zasu shaqu da zazzarfar
soyayya a tsakaninsu haka ba,bata taba masa kallon qwararre kuma gwani a fannin
soyayya ba saida suka fara son junansu,bata jin a duniya akwai wani namiji da yakai
haidar dinta iya sanin makamai da matakan mallakar zuciyar mace,ya kuma tafi da
dukkan tunani da imaninta lokaci qanqani.
Tun kafin su shiga take jiyo muryoyinsu cikin raha da barkwanci,hira irin ta
'yan uwantaka,'yan uwan da kansu ke hade suke kuma ƙaunar junansu.
Cikin qanqanin lokaci Idanunta suka tara hawaye,ba abinda ya fado mata sai
mahaifinta,da tuni yanzu haka yana cikinsu anayi dashi,duk da cewa suma din sun
riqeta tamkar su suka haifeta,kamar yadda itama ta daukesun a haka,amma duk da
wannan babu wanda zai cike maka gurbin mahaifa a yayin daka rasa daya daga cikinsu.
Sallama tayi bayan mama tayi tata,dukka suka amsa,kowa kuma ya soma nuna
murnar ganinta,yayin da nauyi da kunyarsu duka ta kamata,ta qarasa tsakiyarsu ta
aje kwanukan,sannan ta matsa gefe a nutse tana gaidasu daya bayan daya cikin
girmamawa,kowanne na amsawa cikin nuna kulawa,suna kuma mata tambayoyi kan karatu
da sauransu.
Har ta nufi sassan hajja sai kuma taga ya kamata ta sake zuwa taga
mahaifiyarta,don haka saita sauya akala xuwa nasu sassan.
Da sallama ta shiga kamar yadda dabi'arta take tana saka kai cikin
falon,sai kuma ta soma rage fara'a da walwalar kan fuskarta ganinsa zaune darashe
darashe tsakiyar falon nasu yana cin abinci hankalinsa a kwance shida qaninta
rafeeq,ta gefan idanu ta saci kallonsu tana qarasowa cikin falon,ranta cike fal da
mamakin shaquwa da sabon dake tsakaninsa da umminta,kusan kaf fadin gidan bata taba
taba ganin inda yake zama ya sake haka yaci abinci ba bayaga wajen hajja sai wajen
ummi,duk da cewa dama can tun tasowarta ta budi ido da ganinsa a sassan nasu da
kuma kalar wannan alaqar tsakaninsa da ummin nata,saidai kuma bayan rasuwar
mahaifinsun wata sabuwar kulawa yake sake bawa ummin da duka qannenta.
"Bakiga mutane bane da zaki shigo ki samu waje kizauna kanki tsaye baki
gaidasu ba?" Ummintata ta jefa mata tambayar da tafi kama da akwai wata a qasa
kenan,a sanyaye tace
"Aina gaisheshi tun dazun?"
"Ok,shi yasa yanzu ba zaki qara ba kenan?" Kaita girgiza kawai dolenta a sanyaye
tace
"Ina wuni?"sai daya sha qamshi sannan yace
"Riqe abarki kawai,tunda sai kinyi jayayya da na gaba dake sannan zakiyi abinda aka
saki" wani ɓacin rai ne taji ya riqe mata wuya,cikin ranta tace
"Wato ko dakin mamarka munafiki ya rigaka shiga sai kaga sauyin fuska,yanzu gashi
babu gaira ba dalili daga zuwa ganin mamarta zai hadasu,bayan shi babu wanda ya
hadashi da tashi mamar.
A falo ta sami hajja ita da mariya da halima yaran wajen umma matar abba abu
suna kallo,dubanta hajja tayi
"Kin dawo kenan?"
"Eh wlh....yunwa bari na samo abinci" tayi gaba da sauri zuwa cikin kitchen
"Ahto tun dazu nace ki tsaya kici ai" hajja ta fada tana gyara kashingidarta,ita
dai zahra tuni tayi kitchen,ta samu faranti ta zuba abincin,sannan ta dawo falon ta
zauna sosai saman carfet.
Kafin tayi lomar farko ta soma da bude data dinta sannan ta aje wayar
gefanta ta soma cin abincin tana kallon wayar tare da jiran saqonnin su gama
shigowa,duk da wasu sun yayyanke,wasu kuma waiting suke nuna mata,don haka basu
jima ba suka gama shigowa tsaf,sai tasa hannun hagunta ta dauki wayar,daya hannun
kuma tana diban abinci dashi.
Duk yawan saƙonnin dake kan wayar bata bi ta kansu ba,sunan data sanyawa
nuraddeen taje ta lalubo ta shiga inbox din tana qoqarin duba last seen dinshi ko
kuma yana online.
Ba jinkiri ta rubuta slm ta tura mishi,yayi mata tick guda biyu alamun
yaje,saita tsaya ta zubawa sallamar data tura din idanu kamar ba ita ta rubuta
ba,tana jiran taga ta sauya launi zuwa blue,saidai kafin hakan ta faru ta lura daya
sauka.
Farr tayi da idanunta cikin jin dadin yadda take da girma da matsayi cikin
zuciyarsa,kullum kwanan duniya sake nuna mata matsayinta yake a wajensa,hakan yana
mata dadi qwarai,tana jinta cewa itama takai mace,ba kamar yadda ko yaushe ya
haidar ke nuna musu suna mata bane.
Misalin sha daya da rabi na safe ta gama dukkan abinda zatayi,tana gaban
madubi tana qarasa kwalliyar fuskarta,bayan ta shirya kanta cikin wasu riga da
skert na atamfa da suka yi mata cif a jikinta,abu na qarshe datayi gaban mudubin
shine feshe jikinta da turare,ta kalli kanta ta tabbatar komai yayi,saita sakarwa
kanta murmushi,saboda ita kanta tasan tayi kyau.
Hankalinta ta maida kan wayarta dake gefanta,tun daxun take trying number
nuraddeen,tana son gaya mishi xata fita,don kada yace zayazo kuma bata nan,gwadawa
ta sakeyi tana fatan ta sameshi,tun jiya da yace zaya kira bai biyo din ba,amma ta
masa uzuri,mai yiwuwa basu gama magana da maman nashi da wuri bane.
Cikin sa'a wannan karon ta sameshi,sai daf da zata tsinke aka daga,muryarshi
can qasa kamar mai bacci suka soma gaisawa
"Zan je gidan abban gwammaja ne nace bari na gaya maka kada kazo gida baka sameni
ba"
"Ok,babu matsala,na tarad dake acan kawai"taji dadin hakan don tana da muradin
ganinsa,amma saita boye murnar tata da cewa
"Ok fine,yayi" daga haka sukayi sallama ta aje wayar tana sakin murmushi tare da
sake duban kanta sosai,nufar ma'ajiyar sarqoqinta tayita cire dan kunnen kunnenta
ta saka sarqar da dan kunne harda abun hannu,wanda ada batayi niyyar sanyawa
ba,data sake duban kanta sai taga kwalliyar ta sake qawatuwa fiye da daxun.
"Kince karna bata mana lokaci,kuma naga kamar kedin xaki bata mana" ta jiyo
mitar salma daga can falon hajja
"Ina zuwa" ta fada da sauri tana daukar mayafinta dake saman katifa ta yafashi
saman kafadunta,ta maqala hand bag dinta a hannu ta zura takalmi ta fito.
Sassan umminta ta nufa don gaya mata zata wuce,sai data tsaya daga baya ta
bawa salma riqon mayafinta sannan ta shiga ta mata sallama ta fito suka wuce,salma
nata tsokanarta Allah yasa su hadu da ya haidar,ita kuma tana ramawa
"ƴar baqinciki,bakinki ya sari ɗanyen kashi" suna hira kadan kadan har suka isa
bakin titi suka tsaya don samun abun hawa.
Masoya ga abdulrahamaan❤️
K’aramin yaro masoyi kuma mahaddaccin alqur’ani mai girma
Yana matuk’ar son karatun alqur’ani duk kankancin shekarun sa, Ya haddace surorin
alqur’ani da dama hizb biyu na ammah.
Dan Allah a shiga a danna masa subscribe, Aunties, uncles 🥰🥰 A saurara a kalla a kuma
sanyawa channel dinsa albarka ❤️❤️
Yaro k’arami yataso da zuciar son karatun Al’Qur’ani mai girma. Kullum burin sa bai
wuce a kyalla shi a camera yana rangada karatu cikin kira’arsa mai dadi, 👏🏻👏🏻
Toh yan uwa dan Allah a hanzarta a danna kararrawar subscribe ta tashar YouTube na
ABDUL-RAHMAAN... ❤️❤️Domin samun sabon karatun da yai a duk sanda Aka dora 💝💝
He's a very young boy who's passionate about becoming one among the huffaz, he
loves reciting the Holy Qur'an even at his younger age. He has memorized so many
surahs within juz ammah.
please help him grow his channel fisabilillah and also pray for him to be come a
Hafiz in future in sha Allah. Jazakumullah khair..
*KIJI TSORON ALLAH☝🏾☝🏾☝🏾KARKI TABA KAYAN DABA NAKI BA,BA KUMA MALLAKINKI BANE*
☝🏾☝🏾☝🏾
Da sakin fuska kamar kullum umma ta tarbesu,saida suka gama gaisawa sannan
suka wuce dakin hasina suka kafa tasu hirar,wanda kusan rabi tambaya hasina take
mata kan makaranta bayan ta dawo gida jiyya
"Wallahi ji nayi nima kamar nayi cutar qarya a maidoni gida,amma nasan halin ummi
da abba,tsaf xasu gane,kuma raina saiya baci fiye da kima,shi yasa kawai na
haqura,don Allah sis ki warke mu koma tare" dariya hasina ta danyi
"Sanin hali....shi yasa nima duk tunanina yana kanki,ai naji sauqi sosai,in sha
Allahu tare xamu koma" daga haka suka shiga hirarrakin da suka shafesu,sai da akayi
sallar la'asar sannan nuraddeen ya kirata yace yana hanya,tuni ta isa bakin mudubi
ta soma gyara fuskarta,su hasina nata tsokanarta,ita dai bata kulasu ba taci gaba
da abinda takeyi.
Yaro ne yayi sallama yace ana kiran yammatan da suka shigo dazu,murmushi tayi
tace
"Kai nuradden" ta tsammaci shi ya aiko,don haka ta yafa mayafinta tace dasu
"Ina zuwa minti biyu" harararta salma tayi
"Kedai kawai sai mun ganki".
Kusan hirar tasu ma batayi tsaho ba yayi mata sallama ya wuce,ta tsammaci
zai dade dayawa tunda shine haduwarsu ta farko bayan dawowarta daga makaranta,haka
ta shiga gidan tana tunani hannunta dauke da siyayyar daya saba kawo mata lokaci
lokaci idan zaizo,basu sake wani jimawa ba suka wuce gida suma,saboda sanin dokar
gidansu na hanasu yin dare a waje.
Sanye yake da wadansu irin t.shirt da trouser masu azabar kyau,wadanda suka
dace da jikinsa,suka kuma bayyanar da kwarjininsa haiba gami da kyawun surarsa da
na jikinsa,kyakkyawar fuskarsa sanye da wani glass mai duhu daya sake qawata
adonshi ya kuma qara masa kwarjini wanda yakanyi amfani dashi lokaci zuwa lokaci
idan yaso hakan,ko kuma miskilancinsa ya motsa,qafafunsa cikin wani hadadden
takalmi both,motarshi na fake daga gabanshi kadan,da alama fita zaiyi,wayarsa daya
na a kunnensa,daya kuma yana danne danne da ita,ma'abocin amsa waya ne,da wahala ka
sameshi ba kan waya,wanda kusan fiye da rabinta yana yine kan abinda ya shafi
aikinsa.
A gaggauce ta amshi canjinta sannan ta biyo bayan salma zuwa hanyar gate din
gidan
"Barka da yamma" salma gadan russuna kanta tana gaidashi,sai itama ta motsa bakinta
kamar ta gaidashin tana mintsinin salma,so tayi kawai ta basar su wuceshi tunda
waya yake amsawa,gaidashin tana ganin kamar callig attention dinsa ne a kansu.
Hannu kawai ya daga musu ba tare daya dubesu ba,tuni zahra ta zagaye ta wuce
salma,tayi gaba zuwa cikin gidan tana murnar da baice komai ba.
Saidai kafin takai ga shigewa ta jiyo sautin dakakkiyar muyarsa mai cike
da kwarjini irin ta soja yace
"Ke!,zonan" kasa waiwaya tayi sai salma ce ta nuna kanta
"Ni?" Banza ya mata yana latsa wayarsa,hakan yasa ta waiwaya tana yiwa zahra inkiya
akan taje da ita ake.
Tilas tunda su biyu ne a wajen ya sanyata nufar inda yake tsaye,daga can
gefansa ta tsaya,tana motsa bakinta,cikin ranta tana fadin
"Allah ka rabamu da masifa da jaraba,Allah ka kadashi wannan mutumin ya koma inda
ya fito,yaje can ga qaraci baqin ranshi"tambayar daya jeho mata kan mayafin jikinta
ya katse dukka tunaninta,ta soma bin jikinta da kallo,kafin ta gama nazarin abinda
yace ya sake fadin
"Idan basu gaya miki ba nida kaina zan gaya miki,daga yau....kinji me nace?" Kai ta
gyada kawai sannan ya sake cewa
"Daga yau sai yau,kada na sake ganinki da mayafi irin wannan na jikinki,bazan
tsawaita bayani ba,amma idan kunne yaji jiki ya tsira" daga haka ya soma takawa
yana yin gaba,hannunsa daya soke a aljihun wandonsa.
Miqews tayi da sauri gana gunaguni qasa qasa ta yadda bazai jiyota ba,tana
shiga taga salma tsaye jikin gate,da sauri ta iskota tana cewa
"Bai dai miki komai ba ko?"
"Nifa gsky na soma qosawa da halinsa,fisabilillahi yayita bamu doka da order kamar
ance masa a brrack ake ko a filin daga,shikenan a gidan nan baka da damar sakewa
kamar a sansanin bada horon sojoji" dariya salma ta saki harda riqe ciki
"Kece son rayuwar 'yancin naki ne yayi yawa,hala shi yasa duk yawan qorafinki yafi
namu"
"To a prison muke da zamu dinga rayuwa haka,Allah na kusa fara murje idona ina masa
musu" dariyar salma fin ta dazu tayi
"Kema kinsan mafarki kike,amma....dama zaki gwada wallahi" ita kanta saita murmushi
ya subuce saman fuskarta duk da yanayin bacin ran da take,hakanan bata shiryawa
hakan ba
"To muguwa,ya azabtani kina gefe ko haquri babu lallai ki bayar".
Zahra suka hango na tahowa cikin shigarta tako yaushe hijabi mai hannu,a
hankali take tafiya,tadan janyo hijabin kadan yadan rufe mata rabin fuska
"Lover yaaya ina zuwa haka?" Salma ta fada cikin salon tsokana,murmushi mai sanyi
tadan saki,hakanan muryarta da sanyi tace
"Asibiti xanje"
"Waye ba lafiya?" Inji xahra tana dubanta,sai data dan dafe kanta kadan sannan tace
"Nice wallahi,ciwon kaine ke damuna tun jiya"
"Ke kadai xaki,ko nazo na rakaki?"
"Yauwa,da kin taimakeni kuwa,tare da yaa haidar zamu,ni kuma kunyar fita mu biyu
nakeji,banda ya matsanta ma dasai gobe kawai nahau adaidaita ta kaini ta dawo dani"
baki salma ta wangale
"Kaga shugabannin masoya,saikun dawo Allah ya kiyaye hanya,amma wannan rakiyar tafi
qarfin salamatu" waiwayawa tayi ga zahra
"To takwara ke taimaka don Allah" fuska ta yatsina ta nuna kanta
"Ni?,Allah suturu buƙui inji kishiyar me doro,idan kin ganni a lahira kaini
akayi,yanzu ya gama cimin mutunci,a dawo lafiya" murmushi zahra tayi tana kama baki
"Na gode dacin fuskar da kukemin Allah,babu komai watarana saina rama dukka akan
mazajenku,har yanzu kun kasa fahimtar yayanku,amma ina da yaqinin wataran idan
kukayi aure zaku fahimceshi kamar yadda su anty asiya suke ganeshi kadan kadan
yanzun,kuma gaba zaku gane cewa he is the best and d most kindly gentle man in d
world" dariya sosai suka sanya,zahra tace
"Kekam ai dole ki yabeshi,ai masoyi baida laifi sam a rayuwar masoyinsa,ta nan kam
banga laifinki ba" daga haka tayi gaba abinta.
Tana tsaye tana gayawa hajja ta dawo saiga hafsat ta shigo,kallo daya tayi
mata ta sheqe da dariya
"Allah ya qara,hala an tallo qeyarki ne?" Cikin fuskar takaici ta bata amsa tana
miqewa saman doguwar kujerar hajjan
"Inda qeyata ma ya tallo kawai da da sauqi,yarfani yayi kawai gaban abu
sufyan(abokinsa)" dariya sosao zahra tasha harda buga qafa,ta samu abun
tsokana,bata qyaleta ba har sai data yunqura takai mata dundu sannan ta wuce
dakinta da gudu hajja na musu addu'ar shiriya.
Kwanaki uku duka duka suka rage hutunsu ya qare su koma makaranta,anata mata
shirye shiryen komawa makaranta kamar kowanne lokaci,hakanan itama ta hada kusan
duk abinda tasan zata tafi dashi,saidai duk wani abu da takeyi jikinta a sanyaye
yake,saboda tabarbarewar tarayyarta da nuraddeen,wanda har yanzu batasan dalili
ba,batasan meya kawo hakan ba,bata minti goma cikakke bada wannan tunanin a ranta
ba,hakan ya janyo raguwar walwala da karsashinta.
Da yammacin ranar suna sassan abba babba,dan malele suka hada nadiya na
kitchen din tana musu,mama nata mitar suyi su gama za'a dora abincin dare,saura na
zaune a falon suna hira,hafsat na yiwa zahra kitson komawa makaranta.
Yadda yake lallamar nata ya dan sanya take samun relief kadan.
Dan qwace kanta tayi daga hannun hafsat cikin hanzari tana cewa
"Ina zuwa" ta miqe da sauri ta nufi dakinsu hafsat.
A gyare kuma atsaftace dakin yake kamar yadda kusan dukkansu haka aka horar
dasu sanin muhimmancin tsafta,duk da girman gidan da girman kowanne sashe amma
zaiyi wuya ka shiga ka tadda qazanta.
Salma ce kawai a dakin,da alama itama waya take,saita samu gefan katifar ta
zauna tana amsa wayar.
Taji dadin kiran don bata tsammaceshi a lokacin,kusan minti talatin suka
dauka suna waya kafin suyi sallama ta koma wajensu hafsat,ta tadda an gama dan
malelen,ita kadai ake jira,hannunta kawai ta dauraye ta zauna suka soma ci suna
hira.
Sun kusa rabi mai da yaji ya qare,don haka zahran ta miqe da plate din a
hannunta tana cewa
"Bari na qaro mana" mommy dake zaune a falon tace
"Eheenn,wannan dan malelen kawai kun tarkeshi ne don ku cinyema mutane yaji,idan
ance ku daka kuma ku dinga gudawa da ɗai da ɗai"
"Zamu daka mommy bari mu qoshi dai" suka fada
"Dan malelen ne baya tafiya sosai idan babu yaji" cewar xahra data doshi kitchen da
babban tray din a hannunta.
Tana sanya qafarta cikin kitchen din babu zato ba tsammani taci karo dashi
sanda yake qoqarin fita ita kuma tana yunqurin shiga.
Gaba daya farantin hannun nata ne ya kife tun daga gaban rigarshi zuwa saman
qafafunsa,duka dan malelen ya masa ado gaban riga da takalminsa.
Dukkansu suka ja baya shida ita,kallon jikin nasa ya soma yi daga sama har
qasa,zallar bacin rai yana bayyana saman fuska da idanunsa,yayin da itama tsoro ya
darsu a ranta saboda ba qaramin aika aika tayi masa ba,farar shirt da ash din
trouser din jikinsa gaba daya manja ya sauya musu kama......
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: *KIJI TSORON ALLAH☝🏾☝🏾☝🏾KARKI TABA KAYAN DABA NAKI
☝🏾☝🏾☝🏾
BA,BA KUMA MALLAKINKI BA*
Ta falon ya ratsa don isa sashensa,cikin rashin sani saboda yadda ranshi ke
a bace ba zato ba tsammani yayi fatali da sauran wanda suka bari cikin
faranti,hafsat ce ta ajeshi daga gefanta,nufinsu idan sun cinye wancan saisu
qara,take ya fantsama har saman takalmin nasa dai.
Dif falon yayi kowa tamkar anyi ruwan sama an dauke,sam basusan yana gidan
ba da basu tarki yin dan malele ba,dukkansu sunsan halinsa,ya tsaneshi wai kayan
qazanta ne,tsantsaminsa yake kuma ba tun yau ba haka yake.
Mari kawai ya kaiwa hafsat da farantin dake gefanta,wani huci yabi ta gefan
fuskarta,duk da cewa ta samu ta kauce amma sai daya dan sameta
"Uban waye yayi wannan abun!" Ya tambaya cikin bacin rai yana nuna farantin da yayi
nasa waje,kasa amsa masa sukayi saboda basu da amsar bashin
"Ok....baku da bakin magana ko?,i wil deal with u!" Ya fada yana gyara
tsaiwarshi,kowacce saida cikinta ya duri ruwa,har inna wuro dake kitchen,gashi mama
ta fita ta qofar baya bare taji abinda ke faruwa tayi masa magana.
Qasa qasa tayi masa magana ba tare da sunji me tace ba,idanu yadan xuba
mata shima na 'yan sakanni,kallon dake narkar mata da zuciya ya kuma sake sanya
mata tsananin qaunarsa a zuciyarta,wani sanyi ya mamaye ilahirin jikinta,saita dan
lumshe ido kadan tana kauda kanta cikin murmushi,takawa yayi a hankali ya nufi qofa
ya fice daga falon.
Wani irin ihu suka saki gaba dayansu,ta musu nuni da yatsa zuwa qofa da
sauri,sai kowacce ta saka tafin hannunta tana toshe bakinta gami da raba idanu,suna
tsoron kada ya jisu kashinsu ya sake bushewa karo na biyu,ihun ne ya jawo hankalin
innawuro ta dauko farantin da sauri ta fito
"Wallahi anyi babu ke sister!" Salma ta fada da sauri tana dariya sanda innawuro ta
fito,idanunta dukka a waje tace
"Aina godewa Allah da akayi babu ni din,ina kitchen ina muku jaje da addu'ar Allah
ya rangwanta muku izayar da zaku sha yau"
"Dalla banza,ba wannan ba,ke kinga wani scene da akayi yanzu tsakanin ya zaki da
yaa zahra?,gaskene da ake cewa soyayya ke sawa me qarfi ya sunkuya saman
gwiwoyinsa" bata tsaya ba sai data kwashe mata yadda akayi,zahra nakai mata duka
tana
"Banason sharri fa,banson haka"
"Allah ya zahra ki bamu sirrin,dama akwai sanda ya zaki zai russuna haka?"murmushi
kawai ta koma binsu dashi da taga abun nasu bana qare bane.
Saida suka gama zolayarsu son ransu sannan ta gaya musu abinda ya shigo da
ita
"Gida zan wuce,mama naketa nema in yiwa sallama,ta dauka na daga tafiyar,to kuma
dazun abba ya dawo,yace yana son ganina,duk da umma ma tace sunyi waya ta gaya
mata"
"Kai yaa zahra har tafiya?"cewar inna wuro data aje farantin tsakiyarsu
"Haba ina laifi,ku kun tabamin kara nema kunxo kamar haka?" Murmushi inna wuro tayi
"Nidai ayimin uzuri ba maxauniya bace"
"Eh amma ai kuna samun hutu ko?"
"Zanzo ki kwantar da hankalinki" ta tari numfashin zahran tana dariya
"Allah yasa da gaske ne" ta fadi itama tana miqewa
"Bari na shiga na fito" zahran ta fada tana yin gaba,yayin da su kuma sukaci gaba
da shan dan malelensu suna tattauna abinda ya farun yanzun,da sa'ar da sukaci yau
basu sha purnishment wajensa ba,Allah ya cecesu.
Gaba daya sai taji bata sha'awar hira da kowa,madadin ta kashe data din ta
sauka saita shiga wajen status ta fara bin status din mutane tana kalla,wani ya
bata dariya ta murmusa,wani ya bata haushi,wani kuma tayi tsokaci akai ta turawa
wanda ya dora status din.
Wani irin zabura tayi ta miqe ta zauna daram tana raba idanu,zuciyarta na
wani irin bugu,tabi wayar tata data subuce daga hannunta saboda miqewar da tayi da
hanxari da kallo.
Kamar me tsoron wayar haka ta miqa hannu ta sake dauko wayar a karo na
biyu,bugun zuciyarta na sake tsananta,addu'a take cikin ranta Allah yasa idanunta
gixo suke mata,Allah yasa saqe saqe ne na zuciyarta.
Saidai dukka fatanta bai zama gaskiya ba,don sauran hotunan har sun bude
kansu da kansu.
Cikin rawar jiki ta fara komawa da baya ta fara daga hoton farko,nuraddeen
ne shida wata budurwa,wanda kallo daya kafin kakai ga karanta rubutun dake qasan
hoton xai gaya maka tabbas ango da amarya ne cikin yanayin hotunan nan da ake kira
da free wedding pictures,rubutune a qasa kamar haka
Wani kakkarwa hannayenta suke kamar wadda aka tsoma cikin ruwan sanyi tana
ci gaba da buda hotunan ba tare data iya tsaiwa ta duba rubutun dake qasan kowanne
hoto ba,abunda ta iya dubawa shine lokacin da aka dora,6minutes ago,kenan shi ya
dora da hannunsa da kansa,tunda sanda ya sauka da sanda ya dora tazarar minti daya
ce.
Hafsa ce ta shigo tana dariya abunta riqe da hijabi tana qoqarin sawa,da
alama daga waje ta baro abunda ya bata dariyar,sam bata lura da yanayin da innawuro
ke ciki ba sai dataji tana kiran sunanta da wata iriyar shaqaqqiyar murya tana
yafitota da hannu.
Qarasowa tayi tana dubanta,ba wanda ya iya magana cikinsu sai wayar da
zahra ta miqa mata cikin rawar murya tana cewa
"Dubamin don Allah.....dai dai idanuna suke ganemin?" Hannu tasa ta karbi
wayar,hoto daya tak ta kalla saita koma saman qafafunta ta zauna itama tana ci gaba
da kallon hotonan cikin matuqar mamaki da sanyin jiki,kalamanta a sanyaye qwarai
tace
"Nura ne zahra,nuraddeen dinki fa" rasa abu na gaba daya kamata tayi tayi,sai kawai
tasa dukka tafin hannunta biyu ta rufe fuskarta dasu kamar wadda bata da muradin
ganin duk wani haske dake cikin duniya,tana jin kamar ana yamutsa
qwaqwalwarta,daidai sanda salma ta shigo,da sauri hafsat tace
"Yauwa,zo kigani don Allah,zoki tayani gani" da hanzari salman ta qaraso tana amsar
wayar daga hannun hafsat.
Wani ashar salman ta dura,da yake itadin batakai haqurin hafsat ba,ta lalubi
waje ta zauna tana cewa
"Meke shurin faruwa kenan zahra?laaa,kinga ana goge hotunan daga status.....sunyi
disappearing gaba daya"ta fada tana kallon hafsat tare da nuna mata wayar
"Tabbas gogesu akayi,don ba'afi minti goma da dorasu ba,bajci ace har lokacin
saukarsu yayi ba,me nuraddeen ke nufi?" Tambayar da bata da amsarta data cilla mata
ita ta sanyata sakin wani irin kuka me ciwo,kukan daya daga hankalinsu gaba
daya,lokacinne yasira itama ta sako kai,cikin yanayi na tsoro ta isa wajensu tana
tambayarsu abinda ke faruwa,basu kai ga bata amsa ba kira ya shigo wayar zahran,duk
da bata duba tasan me kiran,salma cikin fushi tace
"Bari na daga naji dan gidan marasa mutuncin me zaice?"kai hafsa da yasira wadda
batasan ma ainihin meke faruwa ba suka daga mata,ta daga wayar ta sakata a handfree
tayi shuru ba tare data ce komai ba,muryar nuradden ta bayyana
"Dear.....don Allah karki hukunci da abinda bakisan ainihin menene ba,ki bani dama
inyi miki bayani pls"
"Ai karka damu,saqone ka bayar ya kuma iske inda kakeso ya iske,yo meye kuma wani
abun damuwa a ciki?,kaci gaba da shagalinka kawai,amma ka sani,indai da haqqin
zahra a wuyanka Allah saiya mata sakayya"
"Ki tsaya kiji don Allah,wacece?,hafsat ce ko yusra?"
"Ban sani ba dan gaba da rainin hankali,karka sake kiran wannan number" qit daga
haka ta katse wayar,wanda kafin ta kuma cewa komai wani kiran ya sake biyo
baya,haka suka sanya wayar gaba kowa ya rasa abun tabukawa,yanata faman kira ba
qaqqautawa kamar yadda zahra ke kuka itama babu qaqqautawa,yasira ce ta karbi wayar
daga qarshe bayan sun zayyana mata abinda ke faruwa ta kasheta gaba daya,har cikin
zuciyarta tana jin wani irin suya da bacin rai,wannan wacce iriyar yaudara ce haka
kai tsaye ta rashin mutunci da cin fuska,yana sane ma yayi posting hotunan a status
dinsa?,abinda yafi tsaya musu a rai kenan.
Su hudun gaba daya suka hadu suna bata baki,harda nadiya data shigo daga
qarshe gami da maimaita zancan cike da mamaki,don dukkansu bama su ba kusan kowa
yasan da zaman nuraddeen a matsayin wanda zahra inna wuro ta tsaids zata aura,abun
yazo musu matuqa a ba zata.
Ita kadai tasan yanayin data tsinci kanta da zuciyarta a ciki,wani yanayi
da tun tasowarta bata taba jin irinsa ba saiyau,jin lamarin take kamar a
mafarki,wai ita?,nuradden?,wanne irin abu haka tayi masa dafa cancanci irin wannan
yaudarar mai ciwo?,har yana da bakin cewa ta saurareshi?,ta jima cikin wannan
rudun,daga qarshe taji babu abinda take da buqata illa kadaicewa tayi kukanta ita
kadai ko hakan zai sa ta samu gurbin da zata zuqi numfashi yakai har zuciya da
hunhunta,tana jin kamar numfashinta zai katse ne.
Bayan minti biyu tajiyo muryar hajja na rafka salati da salallami,da alama
sun gama gaya mata komai,sai kawai taja filo ta rufe kanta tana sake fashewa da
wani irin kuka,tanajin sanyi na ratsa gabbanta,kafin kace meye wannan zazzabi ya
rafketa.
Washegari duka tana kwance a daki,ko falo baga fito ba bare taga hasken
rana,tana kwance tana bitar duka rayuwarsu ita da nuraddeen,bataga ta inda ta gaza
ba da xai gujeta,bata ga me ta masa da zai saka mata d a wannan ba.
Duk yadda hajja taso ta fito da ita ta xauna koda a falo ne amma
taqi,hankalinta kaf nakan zahran,duk bayan wasu mintuna saita leqo dubata,dukka
jama'ar gidan kowa ya shigo ya dubata babba da yaro,amma banda mutum biyu,ummanta
dai tasan kara ce da kawaici ya hanata leqoww,don koda hajja ma ta aika mata cewa
tayi ace tana gaidata kawai,data sake aikawa sai tace ai tasan tana wajenta babu
komai,shi kuwa dayan dama bashi a lissafinta,tama manta dashi cikin jerin jama'ar
gidan.
Hajja da kanta ta yiwa abban gwammaja waya sanda yace zaya aiko a maidasu
makaranta ita da hasina ta shaida masa bata da lafiya,a barta koda zuwa satin sama
ne idan ta sake murmurewa,ya mata sannu da jiki,ya kuma ce zaisa a shaida hukumar
makarantar idan ankai hasinan.
Sai da akayi kwanaki biyar da komawa makarantar sannan ta soma jin qwarin
jikinta,don ta tattara dukkan wasu lamura na nuraddeen tayi qoqarin yin watsi
dasu,a yadda ta lissafa kwanaki uku kenan da daurin aurensa,yana can wala'alla
shida amaryarsa cikin farinciki,yama manta da lamarinta,hakan ya sanya washegari da
azahar tayi wanka da ruwa mai dumi sosai,tasha dukka magungunanta,ta shirya cikin
atamfa riga da zani sannan ta fito falon.
"Yauwa,ko kefa?" Hajja data taras zaune cikin falon ta fada cikin
farinciki,tana kallon yadda zahran tadan fada,hancinta da fuskarta suka qara qara
tsaho.
Da sauri sadiq ya miqa masa nasa hannun sukayi musabaha,saiya soma qoqarin
zama hannun kujera yana gaida hajja cikin girmamawa,don shi sam baya wasan jika da
kaka da ita,ta amsa cikin kulawa,don shi dinma dan gaban goshinta ne,sakamakon
sunan maigidanta da yaci,sannan ta dora da fadin
"Kamar tare kuke da sadiq?" Yana dan latsa wayar hannunsa yace
"Tun dazun na shigo,na shiga ciki ne nadan huta"
"Auto ma sha Allah,ya aikin,da fatan an samu abinda ake bida?"
"Alhmdlh" ya fada hade da ajiyar zuciya yana maida wayarsa aljihun lafiyayyen
trouser din jikinsa,wanda kallo daya zaka masa kasan me tsada ne,hakanan mai kayan
yasan takan kaya masu aji.
Ido suka hada da xahra,kamar zaiyi magana sai kuma ya janye idanunsa duka
cikin sakan biyu,ya harde hannayensa a qirji yana duban hajja dakewa sadiq bayanin
dalilin xamanta a gidan,cikin sauri tace
"Ina yini" can qasa ya amsa kamar yadda ya saba
"Wallahi yaron ya bani mamaki,a haka kamar na Allah ashe bana arziqi bane,yaudara
ce kawai ta kawoshi,yau ne mafa kawai na samu kanta ta fito falo ta zauna" ta
qarashe zancan cikin nuna jimamai qwarai kan fuskarta idanunta kuma saman fuskar
haidar,wanda ya dauke kansa zuwa yanzu daga kansu kamar ma baisan me ake ba.
Kamar saukar mashi haka zahra taji maganar a qahon zuciyarta,don sai data
kasa jurewa ta waiwayo ta dubesu,shikam shan furarsa yake kamar ma baisan me ya
fada ba,cikin bacin rai tayi gaba da sauri ta shige dakinta,batasan dai me hajjan
tace masa ba,amma ta jiyo muryarta tana magana,saidai bata iya tantance me take ce
masa.
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: *KIJI TSORON ALLAH☝🏾☝🏾☝🏾☝🏾☝�
☝🏾☝🏾 ?,karki taba kayan daba
naki bane,ba kuma mallakinki bane*
Saman madubi ta samu ta zauna cikin fushi ranta na wani irin suya
"Shifa ya haidar din nan rainin wayonsa yawa ne dashi,ya rainama mutane
ajawali,meya daukemu ne?,duk laifin hajja ne,ai tasan bana hada shirgina dashi me
yasa zata masa zancan matsalata,aikin banza kawai,don yaga mata na hauka akanshi
snine hake raina ajawalin mata,koya dauka kowa baka yake,baisan suna mata suka tara
ba,mtsewww......aikin banza kawai" a sarari tayi maganarta,kamar da wani a dakin
take magana,taja tsaki tana gyara zamanta saman madubin.
Ji tayi xaman dakin gaba daya baiyi mata bama,gwara ta shiga cikin 'yan
uwanta ko zata samu sassauci,saita zaro gogagge cikin hijabanta ta saka ta zira
silifas dinta ta fito.
Har yanzu yana zaune falon riqe da babbar abokiyarsa wato waya,ya wani
miqe qafafunsa saman center table,gefansa furar da yace a kawo masa ce,ya ajjiyeta
ba tare da yayi mata wani shan kirki ba.
Harta giftashi bai daga kai ba,sai data kusa qofar fita taji yace
"Ke!" Tasan da ita yake,dole ta dawo
"Ki tabbata gobe a makaranta kika kwana" abinda ya fada kenan a taqaice,dole ta
amsashi da to,duk da kuwa ji take kamar ta rufeshi da duka saboda takaici,haka ta
fita tana tura baki gaba,ita sam wallahi babu innamal din komawarta makaranta,so
tayi ma ta laƙe da wannan ciwon taqi komawa gaba daya,don itakam gaskiya ta
gaji,amma yana son rusa mata plan,to Allah yasa babu kowa a falon sanda ya fada
bare a tilastata,shuru kawai zatayi da bakinta,suyita wasan buya harya koma
hutunsa,tunda dak ai shima ba dawwama zaiyi ba,da wannan tunanin ta shiga sashensu
salma.
_assalamu alaiki,ina me neman afuwa da gafara daga gareki,nasan cewa na miki ba dai
dai ba,amma tuntuni naso na samu lokaci mu tattauna kafin zuwan rana irin wannan
amma Allah bai nufa,duk da haka ina mai baki haquri,ki sani matar mutum
kabarinsa,kuma Allaj yayi keba matata bace shi yasa ban aureki ba,amma idan da hali
kuma zai yiwu ki bani dama ki zamto mata ta biyu a wajena,ina dakon amincewarki_
_nuraddeen_
Shigowar yusra kitchen din shi ya tada sabon hira,haka nan suke da wuya
kaga mutun daya shi kadai,saidai idan dukka basa gidan
"Na zaci munafuntata kukayi ai kuka zauna kuna wainar fulawa aka rasa me kirana"
"To ba ita akeyi ba kwaɗai...." Dariya ta saki
"Allah qamshin manja na dinga ji,kuma naji kamar daga nan ne,kwanan nan sha'awar
wainar fulawa nake wlh,mu kuma cikinmu an rasa me soyawa,kowacce sai tace idan ta
soya ba zata iya ci ba,ai shikenan"
"Ni kinma tunamin" hafsa ta fada tana ane farantin data gama cin abinci
"Gidansu zainab ahmad din nan?" Tayi maganar da sigar tambaya tana side hannunta
"Eh" suka amsa a kusan tare
"Wallahi suna wainar fulawa da daddare,harda me qwai dame kifi,ke kinji dadinta
kuwa?"
"Wayyo Allah,har kinsa yawuna tsinkewa,yaushe zamuje"
"Yauma idan da kudinki"
"Mu bari sai gobe,yau ya usama yamin alqawarin kyautar dubu daya gobe"
"To kuwa muna aljihunki" inji salma
"Allah ya kaimu" ta amsa musu,daga haka suka sake shiga wata hirar kafin kowa su
watse.
Bata koma sassan hajja ba,saita wuce sassansu wajen umminta,tunda ta kwanta
ciwon bata ganta ba.
A hankali tayi sallama falon nasu,ita daya ce zaune qasan carfet,gabanta da
wata babbar baqar leda tana ta fiddo kayan dake cikinta,wanda suka hada dasu madara
bournvita,Klein,corn flaks,sabulai,mayukan shafawa,turaruka,maclien,cream
salad,suger na qananun jakankuna da sauran kayan amfanin gida na yau da kullum.
"Haka abu kuma ya faru?,sai ki addu'a Allah yasa hakane yafi alkhairi" ta
fada cikin yanayi na rashin bawa abun muhimmanci
"Amin" ta fada tana murxa yatsanta.
Ita ta taimakawa ummin aka raba kayan zuwa ma'ajiyarsu,kowanne abu aka sashi
a muhallinsa,tadan jima ranar wajenta,ita kuma a fakaice tana jan hankalinta tare
da sake nuna mata girman haidar din,sai da suka gama komai sannan tayi mata sallama
gab da za a kira magrib ta baro sashen.
Daga nesa ta hangoshi can inda masu gidan dake da mota ko babur suke
ajiyesu,tsaye jikin motarsa,booth din a bude ana fidda kayan ciki zuwa sassa sassa
na gidan,baki tadan tabe kana ta nufi sassan hajja.
Canma raba kayan ta tadda hajjan nayi,ita da shafa'atu husna da amira dukka
jikokinta ne,sai tayi wucewarta cikin daki,bata tsaya ba ta zarce bandaki,ta daura
alwala,saboda gab ake da akira sallah.
Kamar yadda taci alwashi kuwa a washegarin bata gayawa kowa yadda sukayi da
yaa zaki ba,sai tayi kwanciyarta luf a daki,wuni guda,hajja tana ta mita da yawo
tsakanin falon da dakin kan ta fito,ko kuma jikinne?,saitace lafiya lau take,tana
ramuwar baccin da bata samu yi ba,har hajjan dai ta haqura ta qyaleta.
Da kallo hajja ta bisu sanda suke fitowa daga dakin suna 'yar
hayaniyarsu,har sunyi gaba hafsat tadan dawo da baya
"Don Allah koda ya haidar zai tambaya ina ina kice kece kika aikemu" baki ta tabe
tana dubansu
"Babu ruwan fadimatu zahra'u,ku qarke qalau"
"Hajja mu dake fa bata baci" ta fada tana dariya tayi gaba suka fice.
Kusan awa biyu suka kwashe,har kusan bayan isha'i sannan suka fito,suna
tafe suna hirarsu har suka qaraso qofar gidan.
Salma ce a gaba,ita ta fara tura qofar gidan,da sauri ta dawo da baya har
tana bige yasira
"Dalla meye haka...kefa kin fiya abun haushi wani lokaci"
"Ya haidar.....wallahi ya dawo,suna baranda shida dasu ya abu sufyan" sak
kowaccensu tayi,aka koma kallon kallo tsakaninsu,aka rasa me magana har tsahon wasu
sakanni.
Zahra ce ta soma jan tsaki,sannan ta soma yin gaba tana jan hannun hafsat
"Tsoron wai na meye,muje don Allah,fuska kawai xamu masa" qarfafa musu gwiwan da
tayi yasa suka soma takawa zuwa ciki.
Sunan hafsa ya kira,ta amsa kana cikin hanzari ta nufi inda yake,bata wuce
sakan biyar ba ta dawo
"Ya haidar yace kuzo" ta fada tana narai narai da ido muryarta na rawa,tilas suka
taka zuwa inda suke zaunan,suna hangoshi daga inda suke yana ci gaba da danna
wayarsa,yayin da sauran abokan nasa suka dakata da maganar da sukeyi din,wasunsu
suka dauki drink suna sha,wasu kuma suka tsiyaya black tea.
"A'ah,yammata.....daga ina haka?" Daya daga cikin abokan nashi mai suna
saif ya fada cikin sakin fuska,kasa amsa masa sukayi,sai suka maye gurbin tambayar
tashi da gaisuwa cikin sanyin murya dake nuna tsoro,ba wadda ta isa tayi gigin yin
wani abun da bai dai dai ba,don dukkansu sun haddace dokokinsa da abinda bai
dauka,suna girmama abokanshi sosai kamar yadda suke bashi girma,saidai akwai dan
bambanci,kusan sunfi sakewa dasu fiye dashi,don a cikinsu akwai masu sakin fuska ba
kamar shi ba.
"Ke!...zonan" ya fada da wani dakakken sauti daya sanya cikinta bada wani
sauti na quuuu,ko ba'a fada ba da ita yake babu neman qarin bayani
"Ba daku nake ba.....ku bace daga nan kafin na tashi" ya baiwa sauran
umarni,hakanan tana ji tana gani suka wuce suka barta.
A hankali take takowa zuwa inda suke kamar kazar da qwai ya fashewa a
ciki,duk yadda taso baiwa kanta qwarin gwiwa amma ta kasa tattaroshi,batayi tunanin
zai ganta ba sam
"Kina cikinsu dama zahran hajja?" Daya daga cikin abokan nasa mai suna fahad wanda
sai yanzu yayi magana ya furta,wani kallo aliyyun ya watsa mishi kafin ya maida
dubansa a kanta yana jifanta da wani kallo yace
"A ina nace miki yau ki kwana?" Shuru kamar ba zata amsa ba sannan tace
"Makaranta"
"Da kyau!,me kike a gida yau din?"
"Babu komai"
Kanshi ya gyada shuru na wasu 'yan mintuna,sannan ya zira hannunshi a aljihu ya
ciro key din mota ya wurga mata
"Ki cewa labaran ya kunna miki ruwa ya baki mesa" muqullin tabi da kallo tana
maimaita abinda ya fada cikin qwaqwalwarta.
Ta fahimci abinda yake nufi tsaf,wato taje ta wanke mishi mota kenan koko
yaya?,so yake ya disgata gaban abokanshi,data sake daga kai ta kalleshi ya maida
qafafunsa yadda suke yaci gaba da sabgarsa.
_kuyimin afuwa jina shuru kwana biyu,hidima ce ta biki ta riqeni,naso muku bayani
amma hakan bai samu ba,Allah yayi mana jagora_
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: 8
*_Oumahmad collection's_*
*_Shin kina buqatar waje daya tattare dukkan abubuwan buqata da kike son saye ba
bata lokaci ko rarraba waje?_*
*_wadanda ke saida_*
_kayan kitchen_
_ADRESS DINSU_👇🏽👇🏽
*_Kano hotoro_*
*Ko ku dubasu a facebook da sunan*
*_Maryam muhd_*
Kamar yadda yace bata fasa ba ta isa wajen labaran din,ta kuma buqaci ya
hada mata famfon kamar yadda aka saba idan za'a wankewa wani cikin gidan mota,sai
daya gama ta kalleshi
"Ance ka bani klien"
"Ah'ah....ai indai motar yallabai Aliyyu za'a wanke yana da carwash dinsa da ake
wanke masa dashi,bari na dauko miki" har ya juya zai tafi ta dakatar dashi da sauri
tana cewa
"Klien yace a bani,shi zaka daukomin" jimm yayi kadan sannan ya gyada kanshi yayi
gaba,babu jimawa ya dawo dashi ya miqa mata,ta bishi da kallo har sai da taga
bacewarsa sannan ta taka zuwa wajen mai musu aike aike cikin gidan,wanda wani
lokaci yakan zauna a gidan na wasu kwanaki idan yana da ayyuka da yawa har zuwa
sanda zai ragesu kana ya tafi gidansu
"Soson qarfe nakeson ka bani aro don Allah hayatu" ta fada tana dan waigawa taga
yana ganinta?.
Ba tare da tunanin komai ba ya shiga ciki ya dauko ya miqa matan,ta karba
tana jin dadin samun soson sannan ta durfafi motar tana qwafa,gami da qiyasta irin
barnar da zatayi masa,yau saita fanshe dukka haushinta akan motar,koma me zai faru
ya faru.
Sosai ta zambada klien cikin wani ruwa dake cikin botiki,saboda taji ance
ba'a wanke mota da klien,don tana kodar da fentinta,to ba motar ba,shi kansa me
motar da zata iya saita kodar dashi,taga kya da gayun da yakewa taqama,kamar wani
yafi kyau,itakam ta tsani yadda mata ke kodashi,tana ganin kamar suke tunzurashi ma
suke yake sake jin kansa wani,kofi ta ciko ta miqe da niyyar soma watsawa motar
Cikin girmamawa suka gaidashi sannan suka koma suka barshi da aliyyun,juyawa
yayi inda zahra ke tsaye ta baza kunnuwa taji ya zata kaya,ya miqa mata ledar
hannunsa
"Qarasamin da ita wajen hajja" hannu biyu tasa ta karba sannan ta juya zuwa sassan
hajjan,taso ace a gabanta abban zai masa fadan taga ya zaiyi,amma ko hakan ma ai
tasha dashi,tunda ba haka yaso ba.
Dukka suna sassan hajjan kowacce tayi tsuru tsuru,tana ajjiye ledar suna
cikata da tambayar yata kaya tsakaninsu,sunga ta dawo da wuri,sai data samu waje ta
zauna sannan ta gaya musu yadda akayi,dariya harda masu saukowa daga saman kujerar
"Gaskiya na yadda ya haidar qarshe ne" yasira dake qyaqyata tata dariyar ta
fada,cikin dariyar salma ma tace
"Lallai kice ya samu babbar mawankiyar mota,ai kawai a soma biyanki cikin gidan nan
an huta biyan su labaran,to wallahi Allah ya qwaceki abba ya qwaceki,don da kin
sake kin masa wankin mota da sosan qarfe kashinki ya bushe a gidannan,ke kinsan
kudin wannan motar kuwa?" Kafada ta daga cikin rashin damuwa
"Oho,koma nawa ce ai shi ya janyo,haka kawai gaban abokan nan nashi masu shegen ji
da kansu da isa saiya yarfani saboda ya raina mana ajawali".
"Har yanzu uwata batason makarantar nan hajja" nannauyar ajiyar zuciya
hajja ta saki sannan tace
"Damuwar data shiga na jin cewa Aliyyu ne zai maidata.....yafi damuwar komawarta
makarantar yawa.....bansan wanne irin nau'in rashin jituwa bane tsakanin inna wuro
da haidar ba" shima ajiyar zuciyar ya saki a boye yadda ba zata jishi ba,sam basu
son abinda zai taba ran tsohuwar ko ya bata ranta sam sam,don haka cikin salon son
kwantar da hankali yace da ita
"Quruciya ce ke dawainiya da dukkaninsu,wataran zai zama labari" dan qaramin
murmushi ta saki tana kada kai
"Haba muhammadu.....idan kace innawuro quruciya ce na yarda shi kuma haidar fa?"
"Sai muyi addu'ar samun jituwa tsakaninsu ai hajja" kai ta gyada
"Hakane....don babu abinda ya gagari addu'a"
"Wannan haka yake" ya fada yana janyo ledar daya bawa xahra ta shigo masa da ita.
Komawarta makaranta duk data koma da tabon nuraddeen cikin zuciyarta amma
hakan bata bari yayi mata tasiri ko ya hanata karatu ba,ta tattara hankalinta
kacokam kan karatunta,musamman da suke shirye shiryen fara zana jarabawar
qualifying,duk da cewa batason makarantar amma shima bata bari ya hanata karatu ba.
Sannu a hankali lokaci ya dinga juyawa yana tafiya da wani sauri da kuma
hanzari,wanda yakan fauci abubuwa masu muhimmanci a rayuwar bayi yayi awon gaba
dasu,wasu tare da saninmu wasunsu kuma ba tare da saninmu ba.
'Yan kwanaki ya rage musu su fara zana jarabawar suka samu baquncin sabbin
malamai da aka sauyasu da wasu malaman dake koyar dasu wasu darussan,ciki kuwa
harda malamin da zai dinga koya musu yaren turanci wato english,saidai su dinma na
wucin gadi ne,sunzo ne sakamakon horaswa ta musamman da wadancan malaman suka samu
damar zuwa suyi na wasu watanni.
*_ALƘIBLARSU_*
Malam nasir,matashin saurayi,ma'abocin iya ado gayu da kuma jan aji,uwa una
qwarewa da gogewa wajen iya yaren turanci,wanda tun farkon zuwansa shine abu na
farko daya soma jan hankali dalibai mata da dama dake cikin makarantar a
kansa,yadda yake da gwalli ya hade da qwarewarsa wajen iya turanci,sai hakan ya
zame masa tamkar ado,yana da jan hankali da kuma daukar hankalin kamar mace,da dama
daga cikin 'yammatan makarantar yana burgesu,yayin da shi kuma izzar sa tasa bai
duban kowacce mace cikin makarantar,har zuwa ranar da Allah ya qaddara haduwarsa da
zahra,shigarsa a jinsu na farko,a lokacin da suka fara extra lesson saboda
jarabawar dake gabansu.
A ranar ta tashi da ciwon mara,wanda a baya ita sam bata sanshi ba,bata taba
yi bama sai a lokacin,haka ta dinga daurewa saboda nacinta da karatun,da kuma burin
samun sakamako mai kyau,duk da cewa hasina tace da ita ta zauna,bata da matsala
tunda ita zata je amma ga qiya.
Zuwanta ajin saita kasa hasala komai,hakanan ta kifa kanta saman table din
da take kai tana jin yadda mararta ke zugi.
Rabi da rabi takejin komai,har zuwa sanda jin da zaman saman teburin ya
gagareta,ta fara nishi saboda ciwo,wanda ya fara jan hankalin hasina kafin kuma
sauran daliban zuwa malamin su ankara,shi ya bada umarnin hasina da wata hasana
jibril su dagata su kaita a bata magani,sai a sannan da suka dagata yaga
fuskarta,ya kauda kai bayan sun fice yaci gaba da yiwa sauran daliban karatu.
Kwananta uku kafin ta samu sauqi,ranar da zata koma shiga lesson din,da
yammacin ranar suna shirin tafiya,ta fuskanci yadda daliban kowa keta qoqarin hada
wani assigment wanda batasan na meye ba,saita dubi hasina dake zaune gefan gadonta
riqe da nata assigent din tana sake dubawa
"Wai aikin me aka baku,naga kowa hankalinsa a tashe?" Rufe littafin tayi tana
murmushi,ta daga kai ta dubi zahra
"Wallahi malamin nan zahra ya hadu tako ina,mugun kaine dashi,da alama yana ja
sosai,ga gayu ga iya koyarwa" baki zahra ta tabe tana saka hijabinta
"Nifa ba wannan na tambayeki ba hasina" murmushi ta sakeyi
"Ko baki tambayeni ba ai dole na gaya miki,aikin daya bamu yace zamu iya cin karo
dashi a jarabawarmu,zai gani ya zamuyi dashi idan mukaci karo da tambaya
makamanciyarta,shine ya bamu yace mu gwada,bari ki gani" bude mata tambayar tayi
tana mata bayani iya yanda ta fahimta tsahon wasu mintuna,murmushi zahra tayi bayan
ta gama bayanin,saita koma ta zauna,ta jawo jakar litattafanta ta ciro littafi da
biro,dai dai sanda hasina ta miqe
"Mu wuce zahra,naga an fara tafiya"
"Jeki kawai zan taho" ido ta fidda
"Kai...wallahi ya hana,yace kowa ya tabbatar yana rigashi shigowa"
"Kije yanzu zan qaraso"
"Idan ya hanaki shiga ke kika jawa kanki,nidai nayi gaba" ta fada tana qarasawa
cikin wadanda basu kai ga tafiya ba suka rankaya suka fice tare.
Da sallama ta shiga ajin wanda ya cika da dalibai,malamin dake gaban dan
tebur da kujerar zama ta malamai,saidai shi yana tsaye ne bai zauna ba ya waiwayo
yana amsawa,dubanta yake ganin tana qoqarin shigowa,fuskarsa a hade yace
"Dakata....ina zaki?,ban hanaku zuwa a irin wannan lokacin ba?"
"Malam kayi haquri.....saida na tsaya nasha magani ne"
"Baki da lafiya?" Ya tambayeta yana dubanta,kanta a qasa ta gyadashi
"Eh,yau kwana uku ban taba samun lesson dinka ba,sai yau na samu sauqi" a sannan ya
gane itace,ya tuna fuskarta,don haka yace
"Allah ya qara afuwa.....wuce"
"Na gode sir" ta fada cikin farinciki sannan ta wuce zuwa mazauninta.
Eh tabbas hasina batayi qarya ba,ya iya karatu ya iya koyarwa kamar yadda
tace,hakanan taji dadin karatun na yau sosai,ta kuma qaru sosai.
Sai daya gama ya fara amsar aikin daya basu din,da kansan yake bin teburin
kowacce daliba ya amsa littafin,ya tsaya a wajen ya duba sannan yayi mata marking
ya wuce na gaba har ya qaraso nata teburin,ganin zai wuceta saboda tsammanin batayi
aikin ba yasa tayi saurin miqa masa nata littafin,sai daya kalleta sannan ya amsa
littafin,ya dawo da baya zuwa wajen mazauninta ya bude ya fara dubawa.
Lokaci lokaci yana daga kai daga littafin ya dubeta harya gama
karantawa,saiya rufe littafin kawai ya riqeshi a hannunsa ya wuce teburi na
gaba,hakanan taji babu dadi,ko bata rubuta dai dai bane?,tasan iya bakin qoqari
tayi wajen ganin tayi assigment din daidai duk da bata zo ba a sannan,mutum ce ita
da bata bari assigment sam ya wuceta,saboda tasan hanya ce ta sake samun wani sabon
ilimi ga dalibi,hasina dake gefanta qasa qasa tace
"Hala baki rubuta dai dai bane?" Kafada ta daga cikin damuwa
"Ban sani ba nima,ina jin dai hakane" daga haka suka bar maganar harya gama duba na
kowacce daliba ya koma gaban allo ya tsaya.
"Fatima sa'id dabo" ya fada yana karanta sunan daga jikin bangon littafin
nata
"Yes sir" ta fada tana miqewa,ya kalleta sosai sannan ya mata umarni ta fito gaban
aji.
Littafin ya bata yace ta karanta abinda ta rubuta ta kuma yiwa 'yan aji
explanation,cikin sanyi jiki ta karba,tana nauyin kada ace shirme tayi,hakanan ta
baiwa kanta qwarin gwiwa ta soma karantawa tanayin bayanin kamar yadda ya
umarceta,yayin da shi kuma yaja gefe daya ya tsaya jingine da bango yana qare mata
kallo,yanajin tana wani birgeshi haka kawai.
Tun daga lokacin sai ya zamana ya ganeta sosai fiye da zatonta,yakan kama
sunanta sau tari idan suna karatu,hakanan itama takanyi tambaya har kan abinda
bashi suke karantawa bama saboda qaruwarta,hakan yasa sabo yadan soma shiga
tsakaninsu,hakan yasa ta soma samun abokan adawa daga ajinsu dama ajin sama dasu
wato 'yan ss 3,wadanda keda muradin nasir din.
Randa wata mardiyya taso takalarta da fada akan sir nasir din abun mamaki
ya bata da dariya,don itadai tasan babu komai tsakaninsu daya wuce alaqar malami da
dalibi,saitaqi biye mata,ta dinga dariya kan abinda ta fada din,saidai kafin sukai
ga rubuta jarrabawa su tafi gida hutu tuni ya bayyanar mata da soyayyarshi.
Da farko tayi dari dari da abun,saboda wasu dalilai da suka hada da dokar
makaranta,tsoron abinda ya faru tsakaninta da nuraddeen da kuma sa'idon
dalibai,amma daga baya data zauna tayi nazari,ta fuskanci dukka halaye da dabi'un
malam nasir din masu kyau ne,sannan ita kanta bawai bata sonshi ba kamar yadda ba
zata ce wai tana sonshi kai tsaye ba,amma a qalla a yanzu suna gab da shiga ss
3,wanda ba zasu wuce wata 9 ba zasuyi candy,kuma kafin suyi candy dinne kowacce
wanda zata aura zai gabatar da kanshi da magabantansa asan dashi,suna gama
makaranta kuma sai maganar aure,tana ga mafi kyau shine ta bashi dama su fukanci
juna,ba lallai abinda ya farun ya kuma maimaita kanshi,da wannan tunanin ta soma
dan bashi dama kadan,duk da ta gaya masa abu mafi kyau ya bari suyi hutu ta koma
gida tukunna,shima hakan ya masa,saboda haka bai zura jiki da yawa ba,ya bari har
zuwa sanda suka gama jarabawar suka koma gida sannan ya fara kafa kanshi a zuciyar
zahra din.
Abinda yasa ta kuma sakewa dashi shine,akwai sanayya tsakaninsa da salim dan
abban gwammaja yayan umminta,bai kuma fadi wani aibu ko mummunan hali tattare dashi
ba,hakan yasa ta sake jin cewa ta samu abokin rayuwa kamar sauran 'yan uwanta......
_to masu karatu.....ya zata kaya?,muje zuwa,mu hadu gobe da izinin ubangiji_🙏🏽🙏🏽🙏🏽
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: 09
*OUM DUFAIL!!*
_GIDAN ADO ƘAWA DA KECE RAINI_💄💅🏽
_OUM DUFAIL ta tanadar muku dukkan nau'in kayayyakin gyaran fata gashi dama jiki
gaba daya ZAHIRINKI DA BAƊININKI samfurin MAIDA TSOHUWA YARINYA_
07067943479
Tana gaban madubi tana shafa ma take tunanin zuwa gidan abban gwammaja
wajen hasina,amma kuma daxun sir nasir yace mata zaya zo ganinta,tana mamakin yadda
baya gajiya da jinta ko ganinta,har kunya yakan bata wani lokaci,ta samu tattali da
kulawa wadda ta dara ta nuraddeen,sai a yanzu take ganin ma nuraddeen kamar shidin
ba komai bane bai iya komai ba akan nasir din,ita kadai wani lokaci idan ta tunashi
da kulawarsa gareta takan saki murmushi.
Cikin doguwar rigar swiss atampha cotton ta shirya mai yarfin stone a
jiki,tana tsaka da fesa turare bayan ta taje gashinta ta daure wanda takeson hasina
ta mata kitso taji hajja na qwala mata kira,saita aje turaren ta dauki dankwalinta
a hannu ta fito.
Ita da abban tsakiya ne,sai haidar dake kallon labarai a VOA,yadda sojoji
suka samu nasara a jahar borno cikin satin kan yaqi da 'yan ta'addan boko haram
yana kuma magana da abban tsakiyan.
Bata sake fitowa ba sai da taji alamun fitarsu sannan ta fito riqe da
mayafinta,sai data shiga kitchen ta hada kayan nata karin sannan ta dawo falon ta
zauna kusa da hajja,tana tsaka da cin abincin hajjan tace
"Ina tunanin kafin ku koma makaranta fa iyayenku zasu nemi ganawa da magabatan
samarinku,saboda yayanku ya tada maganar aurensa,yanzu haka can suka nufa garinsu
yarinyar" duban hajjan tayi tana cin abincinta
"Shi zai kaisu da kanshi kenan?"
"Eh" ta bata amsa tana dauko remote don ta canza tasha,saita tabe baki
"Ey...da yake shi idanunsa da kwalli ai ba laifi bane,inda kaine da ka shiga uku"
duka hajjan ta kai mata ta kuma sameta,ta gantsare tana cewa
"Wayyo Allah na.....hajja saikin karyani tukunna?"
"Eh gwara ai na karya ki din....tunda ke baki gajiya da dan banzan qorafi,zancan da
ake miki daban wanda kike daban"
"Shikenan tunda haka kika ce,kullum nice me laifi" daga haka ta miqe da farantin a
hannunta ta wuce kitchen tana zumbura baki,ta ajjiye sannan ta fito ta yafa
mayafinta
"Zan wuce hajja" tayi maganar da alamun jin haushi har yanzu akan fuskarta,kudi
hajjan ta miqa mata tana gaya mata kada tayi dare.
Kamar yadda hajjan tace kuwa a ranar akaje dawakin tofa dangin mahaifiyar
Aliyyu haidar ko ince zaki aka tambaya masa aurenta hannun iyayenta da suke
kawunnai a wajensa,mahaifinta qanine ga mahaifiyarsa,ba tare da wani bata lokaci ba
aka basu auren,tunda shima kamar d'a ne a wajensu,suka dawo cike da farinciki da
murnar yadda akayi komai cikin girma da karamci.
Washegari abba babba ya bada sanarwar kowacce cikinsu ta yiwa maneminta
magana,indai da gaske yake yazo ya gabatar da kanshi tare da magabatansa,don suna
so nan da shekara daya su hada su duka a aurar,mata biyar namiji daya.
Saurayin salma shi ya fara zuwa rana daya dana yusra,bayan kwana biyu
saurayin yasira da magabatansu sukazo,washegari na hafsat ya bayyana shima,a ranar
ne zahra ta karbo wayarta daga gyara,wadda ta matsu qwarai ta gyara din,don tafi
kyautata zaton rashin wayar ne ya hana zuwan sir nasir kamar yadda yayi
alqawari,tana jonawa a chargy ta lalubo number dinsa ta kira.
Kunya yasa ta rasa yadda zata shaidawa su abban cewa nasir din zaizo,sai
da gari ya waye taga indai bata fada din ba zasu fice harkokinsu,dabara ta fado
mata ta shaidawa hajja,ita kuma ta gaya musu.
Saidai tana shiga falo da niyyar wucewa dakin hajjan saboda bata kai ga
fitowa ba wayarta dake hannunta ta dauki kuwwa,ganin sunan nasir yasa ta samu daya
daga cikin kujerun ta zauna tana amsa wayar.
Tun daga sallamarsa taji alamun muryarsa ba daidai take ba,kafin takai ga
tambayarsa shiya tambayeta
"Kin gayawa su abba zuwan namu ne yau?" Kai ta kada
"A'ah,yanzu dai nake shirin gaya musun" saiya sauke ajiyar zuciya mai nauyi,cikin
alamu na damuwa tace
"Lafiya?"
"Fatima.....wallahi tun jiya nake fama da mama kan maganar....ashe turani garinsu
da tayi akwai yarinyar data turawa ni wata na'ima....tunda naje yarinyar take rawar
kai a kaina take kuma dawainiya dani,ni ban kawo komai ba sai yanzu dana dawo na
kawo wannan maganar mama da abba duka sukace basusan zance ba,sun turani naga
na'ima ne don mu hada kanmu".
Kasa magana zahran tayi,tayi shuru kawai tana jin yadda zuciyarta ke
bugawa,gabanta ke faduwa
"Fatima....bana gaya miki wannan maganar bane don ki saka damuwa cikin ranki ba,na
gaya miki ne don kada muyi jinkiri wajen zuwa ki zaci wani abu na daban....ba abun
damuwa bane,nasan yadda zan shawo kan mama in sha Allah....kuma zanzo na samu abba
nayi masa bayanin komai"
"To" abinda ta iya furtawa kenan a sanyaye,sallama tayi masa da kanta,don bata da
qwarin gwiwar ci gaba da hira dashi,saita zame ta kwanta kawai cikin wani irin
yanayi data kasa tantance wanne iri ne,bata fatan fa rasa nasir sam,saidai kuma
tanajin tsoron faruwar hakan can qasan ranta.
Sannu sannu kwanaki suka soma shudewa,nasir yaci gaba da zuwa....ya kuma ci
gaba da kiranta a waya kamar yadda suka saba,saidai bai sake tada wancan zancan
ba,hakanan maganar ganin abba ma bai kuma tada ita ba,itama bata kuma ce masa komai
ba,bata sake tada maganar ba,tana gayawa zuciyarta cewa yana qoqarin sanya mamanshi
ne ta amince,tana tsoron ma a tada maganar ya zama silar rasa sir nasir kenan a
wajenta.
To daga gida ma ba wanda yayi mata maganar nata manemin,baya ga hajja data
yi sau daya,ta kuma yi mata bayanin cewa yana sane zasuzo,ya shaida musu yana jiran
su saka rana ne su magabatan nasa.
Sati hudun kuwa na zuwa suka fara jarabawa,suna gamawa sukayi gida hutu
kamar yadda aka saba sai gida,saidai ko bayan sun koma dinma dai shuru shuru zancan
turowar tashi,saidai suna waya kamar yadda suka saba dashi.
*_04:30 pm_*
Kwance take a falon umminta ita daya,babu kowa daga ita sai ilham wadda
zahran ta aikata kitchen ta juya mata miyar data dorawa ummin tata,bata nan
ummin,ta tafi barka na matar cousin dinta data haihu,ta tafi kuma da duka yaran,don
haka ta bar mata girkin,don hajja itama kwana biyu kenan bata nan,ta tafi ainihin
garinsu bikin dan qanwarta,yawanci idan zata da zahran take zuwa,hakanan wannan
karon taqi binta don haka ta dauki amira da husna daga cikin jikokinta suka rakata.
Wayarta da bata dade da gama waya da nasir ba wadda ke aje saman kanta ta
dauki tsuwwa,ta miqa hannu ta daukota tana duba lambar da aka kirata,ba suna alamun
bata da ita cikin jerin ma'ajiyar lambobinta,saita daga ta kara a kunneta cikin
sallama.
Ana amsa sallamar taji kamar tasan muryar,amma saita tambaya jin ba'a da
niyyar yi mata bayani
"Dawa nake magana?"
"Nuraddeen ne....tsohon masoyinki,kuma wanda har a yanzu yake sonki" mamaki ya
sanyata tashi ta zauna sosai,kodai da gaske ne shekaran jiya da sukaje gidan anty
aliya yusra tace mata taga nuraddeen tsaye hana kallonsu?
"Waye kuma me wannan sunan?" Ta fada cikin gatse da basarwa,murmushi ya saka
"Na tsammaci jin sama da haka ma daga gareki....amma kiyi haquri ki bawa
qwaqwalwarki dama ta tuna koni waye...don nazo da qoqon barata ne a karo na biyu a
bani dama,damar kuma da zata kaimu har ga aure....." Da sauri ta katseshi
"Kaga dakata.....ka riga daka barar da damarka tuntun tuni,abu daya zan gaya maka
shine,daga yau sai yau,kada ka qara tunawa a ranka ka sanni,kada kuma ka sake gigin
kirana harka koma va mahaliccinka" daga haka ta datse kiran ta aje wayar ta koma ta
kwanta tana jan tsaki.
Kira ya shiga yi a jejjere,da taga zai takura mata saita dauki wayar ta
danna masa block ta gyara kwanciyarta,daga qarshe ta sake jan tsaki ta miqe ta nufi
kitchen,ta jawo salad din da bata yanka ba ta soma gyarashi tana cewa ilham ta kawo
mata ruwa a roba,tana aikin cikin ranta tana mamakin qarfin hali da rainin hankali
irin na nuraddeen,gami da zallar rashin kunya da yake tunanin yana da sauran
dama,yana kuma da qwarin gwiwar da zai iya fuskantarta ido da ido ya gaya mata wata
maganar.
Washegari sha biyu na rana kiran nasir ya shigo mata,tayi mamaki don basu
fi awa biyu da gama waya ba,duk da cewa ta sani mayen kiranta ne shi a waya,baya
gajiya,amma yadda tazo ta tadda tarin miscal ya bata mamaki,don lokacin bata kusa
da wayar,ba bata lokaci tayi masa flashing ko daqiqa uku ba'a rufa ba ya kira.
Cikin zallar mamaki ta samu gefan katifarta ta zauna tana sauraren masifa
da bala'in da nasir ke kwararawa cikin waya,wanda ta kasa fahimtar inda zancan ya
dosa,ta gane dai akanta yake maganar,kuma duka zallar kishi ne,amma bata gama gane
da waye yake ba,har sai daya qara mata haske ta hanyar cewa
"Wallahi saina nuna masa kurensa....ni zai rainawa hankali,harda dora hotonki saman
dp?,to idan ma kuna tare ki gaya masa yayi saurin saukewa ya kuma fita daga
harkarki tun ba'a ji kanmu ba"
"Wai waye don Allah....kayi haquri kamjn bayani mana"
"Nuraddeen yake ko waye....whatever ma ake kiransa dai ki gaya masa ke ba tashi
bace" ita dariya ma zancan ga bata,tana mamakin yadda yake kishinta,ita sam ko
wayar jiya ma ta manta sunyi ta dashi bare shi kansa nuraddeen din
"Ka kwantar da hankalinka mana" ta fadi sannan a hankali ta warware masa komai.
*_ALƘIBLARSU_* � ?
Kwana biyu tsakanin wayarta da nasir din ta shirya zuwa gidan abban
gwammaja zata dubashi ciwon qafa ya matsanta masa,ita da yusra suka shirya sai
ilham,adaidaita sahu sauka dauka direct har can gwammajan,har qofar gida saboda
mota tana iya shiga har qofar gidan.
Ta taras da jikin abban da sauqi,harta zauna suka dan taba hira sannan ta
wuce dakin umma suka dasa tasu hirar da hasina,ba jimawa suka shige kitchen suka
dorawa umman abincin rana,har suka gama suka zuba suka zauna suka soma ci salim din
bai dawo ba,sai da suka gama sun dan miqe suna hira suka jiyo sallamarsa.
_OUM DUFAIL ta tanadar muku dukkan nau'in kayayyakin gyaran fata gashi dama jiki
gaba daya ZAHIRINKI DA BAƊININKI samfurin MAIDA TSOHUWA YARINYA_
07067943479
Mintina ashirin habibu ya shigo har falon umma,a lokacin zahra na jingine
kawai ba tare da wani magana ko motsi ba,tana jin yadda suketa tattauna batun a
tsakaninsu.
Kamar wasa sai gashi a ranar kwanan gidan abban gwammaja ya kamasu saboda
wani matsanancin ciwon kai daya saukar mata,umma ce ta dinga aikin bata
maganganu,da kuma kwatanta mata cewa matar mutum kabarinsa,tayi addu'a idan har ya
zalunceta Allah ya fidda mata haqqinta,tana jinsu sanda suke waya da umminta,sai
kuma washegari bayan sallar magariba abubukar yayanta yazo da kanshi ya daukesu ya
maidosu gida.
Data shiga bata samu hajja ba,saita wuce dakinta,saboda yadda kanta yake
sara mata,har yanzu kunnuwanta na jiye mata sanda habibu ya kira nasir din,yake
gaya masa saura sati daya daurin aurensa,tana iya jiyo kamar wani sauti mai kama da
zumudi zumudi cikin muryarsa,babu alamun bacin rai ko damuwa tattare da
sautinsa,saidai bata jima ba hajjan ta shigo cikin jimami,inda ta takura mata sai
data tattara ta zuwa dakinta,tace gwara su zauna tare har ta samu sassauci.
Saidai kuma abinda ya bata mamaki shine,a daren ranar saiga nasir ya
kirata,kamar ba zata daga ba sai kuma ta daga,don tunda abun ya faru tsakanin jiya
da yau bai kira ba sai yanzun,tana son taji da wacce kalma shi kuma zaiyi
amfani?,me zaya fada?,zai kare kanshi ne kamar yadda nuradden ya kare?,ko kuwa zai
tabbatarwa da kansa laifinsa?.
A yanayin sallamarsa kawai ta fahimci baisan mai afkuwa ta afku ba,da irin
salon daya saba yi mata magana yayi mata,sai daya gama sannan a hankali tace
"Ango" dif yayi na wasu sakanni sannan yace
"Wanne irin wasa ne wannan zahra?,waye kuma angon?" Wani bacin rai ne ya taso
mata,wato ita zaya ninke a baibai kenan?ya shirya saidai kawai taji an daura
aurensa?,saita miqe ta zauna tana tuna irin kalaman daya jima yana amfani dasu a
kanta,tana tuna yadda yake nuna kaffa kaffa da zallar kishi a kanta,tana tuna yadda
koda yaushe yana tafe da kyaututuka domin ta,wanda koda taqi amsa zai tilastata ta
karba din,zaice tukuicin soyayya kenan kyauta,ashe babban tukuici yana tafe
"Nasir....bude kunnenka da kyau!,idan zaluntata kasoyi to ubangiji yamin kariya da
katanga dakai saboda ya bayyana min gaskiyar abinda kake boyewa,ka zalunceni
nasir!,kaso ka yadaureni kaje kayi aurenka ba tare da na sani ba?,to na godewa
Allah daya bayyanamin shirinka" cikin wata rudewa da dirircewa yake cewa
"Calm down fatima....ki tsaya kiji mana,wallahi Allah ba haka bane,yarinyar nan
auren hadi akayi mana da ita.....zabin hajiya da alhaji ce....."
"Watanni nawa?,kwanaki nawa?,amma kullum nuna min kake bata da muhimmanci a
wajenka?,hakanan maganar itama bamai muhimmanci bace?,ka gayamin cewa ka gamsar da
hajiya ta aminta da naka zabin,amma abun mamaki saiga sauti farinciki daga
maqogwaronka kana sanarwa da duniya daurin aurenka,a hakan zakace baka ita
akayi?,ahaka kakeso na yarda dakai,bayan an ganemin babu wani damuwa ko kadan
tattare dakai?"
"To naji,amma fatima....ina sonki ki yarda dani.....kuma in sha Allah zan aureki a
matsayin matata ta biy....."
"Allah ya tsareni da hada hanya da mayaudari....har abada ni dakai nasir na barka
kenan,kaje....ina roqon ubangiji yayimin sakayyar abinda kayimin,Allah ya isarmin"
daga haka ta kife layin ta sake sakin kuka.
Kuka tayi mai yawan gaske,wanda kafin tayi controlling kanta fa sassauta
kukan nasir ya hada mata massages da kiraye kiraye babu adadi har ta kasa irga
yawansu,sai kawai ta kashe wayar baki daya ta cusata qasan filo.
Duk da ta cinyewa ranta komai amma hakan bai hana rama bayyana a jikinta
ba,saboda ita damuwa tana da tasirin bayyana gangar jiki koda an danneta a
ruhi,hakan yasa ta faɗa sosai kafin komawarta makaranta.
Wannan karon hajja da kanta tayi mata tayin zama a gida ta qara koda sati
daya ne ta qara murmurewa kafin sannan amma tace a'ah,saboda jarabawar qarshe ta
wa'ec da neco da suka fara jiyo qamshinta,gwra ta tattara hankalinta ta samu
sakamako me kyau,don yadda qaddararta ta fara zuwa mata a hagunce ya sanyaya mata
jiki.
Da yammacin ranar ana ya gobe zasu tafin haidar ya iso gidan,tana falon
hajja tana goge sauran kayanta da zata wuce dasu yayi sallama falon ya shigo.
Kai ta daga ta dubeshi na sakan daya kana ta amsa tana maida kanya ga
gugar,har yanzu yana nan da gayunshi kwarjini izza da isa,saima cika da 'yar qiba
da kuma murjewa daya sakeyi,hakan ya qara masa kyau sosai,kusan watansa biyu baya
nan,sai yau ya dawo.
Wannan karon ma ta fito zata sha ruwa a kitchen taji hajjan na gaya masa
abinda ya faru da ita,itakam bataso harga Allah hajjan na gaya masa
"Allah ya sawwaqe" kawai taji yace,qwafa taja a ranta tana cewa maganin hajjan da
take gaya masan,aiba matsalar data shafeshi bace dama.
Gab da zata isa gadonta ta hangi ladifa hamza zaune riqe da takarda cikin
hannunta,gefanta kuma maryam mustapha ce riqe da hannun ladifar dake digar hawaye.
Ba laifi suna zaman mutunci sosai dasu,kasancewar zahran mai faran faran
da jama'a yasa take da yawan jama'a,banda yanzun da walwalarta taja baya ba kamar
da ba,don ko da take shugabar dalibai kusan iya mu'amalarta yasa dalibai ke
sonta,musamman juniors da bata yadda a zaluncesu ba don suna qasa dasu,hakanan suma
basu isa su raina na sama dasu ba dole su basu girma.
A hankali ta koma gefansu itama ta zauna tana fidda murmushi mai ciwo,wanda
iyakarsa saman labbanta,ta ninke takardar sannan tace
"Ashe bani kadai bace ba?,bani daya keda irin wannan matsalar ba,gayamin ya kuke
dashi" muryarta da sautin kuka take bata labarin yadda yake nuna mata soyayya,amma
sai gashi tashi guda ya yaudareta,yayi aurensa ba tare ma data sani ba,sannan kuma
saboda tsabar qwarewa yaci gaba da soyayya da ita,sai a yanzu data kusa tonashi ya
bayyana mata yayi aure a sanda suke tare,ya tsallaketa ya auri wata,bayan ta kori
kowa a kansa,bata sauraron kowa saishi,wannan wanne irin yaudara ce?,wanne irin cin
amana ce?.
*_IBRAHEEM_*
Bayan dawowarsu hutu babu jimawa suka zana jarrabawar fita daga
makaranta,cikin iko da taimakon ubangiji,duk da irin qalubalen da suka dinga kawo
mata tarnaqi amma hakan bai dakushe karsashi da karatunta ba.
Kyauta ta qarshe data samu itace wadda daliban makarantar suka hada
mata,saboda yadda sukaji dadin shugabancinta,da yadda ta tsaya tsayin daka akansu
wajen kwatanta adalci da gaskiya.
Tana rungume da kyautar suka sake hada ido dashi,wannan shine kusan karo
na biyar,duk sanda ta hau step din ta amsa kyauta tazo saukowa saita tsinci
idanunshi a kanta,qaramin tsaki taja tana jin haushi har cikin ranta,ita sam ta
tsani dabi'ar kallo,bama kuma kamar yanzun data yanke tsammani wa maza,tayi musu
kudin goro.
Dukkaninsu suna tsaye gaban motocin gidansu,wanda kaso mafi yawa na 'yan
gidan nasu sunzo mata,ciki harda hajja,bata da wasu kaya masu yawa da zata koma
dasu,don kusan duk ta kyautar dasu,kamar su katifarta botiki house wear dinta da
sauran tarkacenta ciki harda jakar goyo ga wadanda basu da qarfi,yau jinta take
kamar wadda aka 'yanta daga kurkuku,kana kallon fuskarta zaka shaida hakan.
Cikin yaran da sukayi sabo dasu suke kuma mata kallon yayarsu ta qaraso
tana cewa
"Anty fatima.....ance anason magana dake" ta fada tana nuno wata mota,daga kai tayi
ta kalli motar,babu kowa kusa da ita,hakan yasa ta tambaya waye?
"Wai mamar qawarki ce"
"Mamar qawata?" Ta maimaita cikin mamaki,kafin tasan amsar da zata bada hajja tace
"Yi maza kije ki dawo kuzo mu wuce kada muyi rana a hanya" saita waiwaya ta cewa
salma tazo ta rakata,suka jera tare har zuwa jikin motar.
Suna tsaiwa aka bude murfin motar aka fito,kallo daya tayi masa ta
shaidashi,saurayin dazu ne,wanda yaketa faman binta da kallo,sanye cikin shadda
dinkin zamani,kanshi babu hula,kallo daya zaka masa kasa cewa wayayyen mutum
ne,wanda ilimin zamani ya rasashi,da murmushi yake dubanta
"Ayimin afuwa,nayi qarya da maman qawarki ko?,naga alamun idan ba hakan nayi ba
babu lallai na samu ganinki,mai yiwuwa ma nayi asarar dama ta" itadai batace komai
ba sai dubanshi da take,gami da son jin ba'asin kiranta,ganin kamar yana bata musu
lokaci yasa ta tambayeshi kai tsaye
"Allah dai yasa lafiya,ko yarinyar tayi batan kan wadda kasa a kira ma?,don mi
bansanka ba" murmushi ya saki yana dubanta
"Ni na sanki,tun ba yau ba,saidai kuma yau din idanuna suka fara ganinki" bata
fahimci zancansa ba,kuma taga alamar kamar yana son maida zancan wasa ya kuma bata
mata lokaci,don haka tace
"Zaifi kyau ka fadi saqonka,don na bar iyayena na jira" gyara tsaiwarsa yayi
"A'ah,aiko ba za'ayi haka ba,ya zamu barsu mama na jiranmu?,inaga kawai ki bani
lambar wayarki sai muyi magana"
"Baka da abin cewa,don haka sai anjima" ta fada tana yin gaba.
*OUM DUFAIL!!*
_GIDAN ADO ƘAWA DA KECE RAINI_💄💅🏽
_OUM DUFAIL ta tanadar muku dukkan nau'in kayayyakin gyaran fata gashi dama jiki
gaba daya ZAHIRINKI DA BAƊININKI samfurin MAIDA TSOHUWA YARINYA_
07067943479
Tunda ta koma gida ibrahim ya samu nayi,kiran safe daban rana daban dare
daban,har sai da duk wanda yake tare da ita yasan da xaman ibrahim din,tun tana
sharewa itama har ta soma dagawa dole tana saurarensa.
Ibrahim din irin samarin nan ne 'yan hira,ya iya labarai kala daban
daban,sau tari koda ba zatayi magana ba zaice babu komai,yau shi zai mata hira,zata
tsaya tana saurarensa yanata bata labarai kala kala,saidai kawai tayi murmushi idan
wani abun ya bata dariya,haka zasu kwashe kusan awa guda,saidai tace ta gaji.
Cikin haka maganar auren yammatan ta taso,an soma da kawo kudin hafsat da
yasira,naira dubu hamsin hamsin kowaccensu,aka saka rana kamar yadda aka tsara za'a
tsaida rana guda daya.
A daren ranar su abba suka kirata,kira na farko tsakaninsu tunda aka fara
zancan aurensun.
Tunda ta shiga falon taga zaki a ciki sai taji kamar ta koma,batason ana
tattauna personal issues dinta a gabanshi ko kadan,harta shiga ta zauna ta gaida
abba babban dashi bai daga kai ya dubeta ba,itama tafison hakan,da da hali ma
fiddashi zatayi daga falon.
A hanya tana tafe tana tunani,hakanan sam maganar ibrahim bata kwanta mata a
rai ba,amma babu yadda zatayi,ba zataso ace duka sa'anninta kowa babu shi ba saura
ita kadai a gidan.
Tana shiga daki saiga kiranshi,ta dauka tana zaman gefan katifa suka fara
magana,kafin takai ga gaya masa nata saqon yace
"Baby....ya kamata ace mun soma ganin juna fa,yin waya a iya waya kawai abun ya
isa,ya kamata mu canza tsari....a ina zan ganki?"
"A gidanmu.....akwai maganar dama da nakeso muyi dakai" cikin 'yar dariya dariya
mai kama da murmushi yace
"Ah haba.....ai yanzu an daina wannan yayin,haduwa a gida kamar zamanin da,mudai
samu wani waje haka,wanda zamu sake sosai,mu mori soyayyarmu da lokacinmu,inda babu
abinda zai dinga razanamu" sosai mamaki ya kama zahra,amma saita danne mamakin nata
tace
"Razana kuma kamar wasu marasa gaskiya?" Ta fada sound din muryarta yana sauyawa
"Eh mana,kinsan ita soyayya tana buqatar kebewa da nutsuwa" tsaf ta fahimta inda ya
dosa,kuma bata taba tsammatar hakan daga gareshi ba,don haka ta kaurara muryarta
sosai
"Ina jin baka shiryawa ganina na ba,a qa'idar gidanmu duk wanda keson ganinmu zai
samemu cikin gidanmu ne,idan ka shirya zuwa saina gaya maka saqon gaba daya" daga
haka ta katse wayar,ta koma da baya ta kwanta tana nazarin kalamansa,ba shakka ya
bata mamaki,saidai kuma ba zata yanke masa hukunci haka da wuri ba,tunda wannan
shine karon farko da hakan ta faru.
Ga mamakinta zancan ya wuce,sai gashi bai haqura dayi mata maganar inda
zasu hadun ba,harda bata list na sunayen guraren shaqatawa yace ta zabi duk wanda
takeso a ciki.
Yanzu ya daina bata mamaki saima tsoro,randa ta gaji da jin zancan ta buda
baki cikin bacin rai tace masa
"Ibrahim,wannan maganar da kake yawan gayamin itace take tabbatar min da cewa ba
sona kake ba!" Cikin dirircewa yace
"Hana baby....ki daina fadar haka,waye yace miki bana sonki,kinsan yadda nake jinki
a zuciyata kuwa?"
"Ban gani a qasa ba,idan ka damu dani....idan har sona kake da gaskiya ka tako kazo
ka riskeni gaban mahaifana mana,baka dinga neman kebewa dani a wani waje da babu
idon naka ko nawa ba!" ta fada da zafinta
"Shikenan,is ok" shima ya fada cikin sanyin murya ganin yadda ta dauki zafi
"Allah ya baki haquri,yanzu ki gayamin saqon da kika ce tun rannan an baki"
"Ance na gaya maka cewa ka fito"
"Na fito ina?" Ya fada da wani irin sauti
"Aure mana" ta fada itama kai tsaye tana sauraren amsar da zata fito ta gaba daga
bakinsa,don tuni ta gama hasashen amsarsa ta qarshe
"Ok...ok...am really sorry,sai yanzu na fahimta" sai kuma yayi cool da muryarsa
sosai
"To ai baby shi yasa nakeson mudan hadun,mu fahimta juna kafin akai ga batun
aure,tunda kinsan shi batun aure ba qaramar magana bace,zamane na dindindin,kinga
dole saimun fahimci juna face to face tukunna" shuru tayi kawai,wani abu mai tauri
yana tokare mata wuya,abun akwai zallar rainin hankali da ban mamaki,ada kullum
shine bashi da zance saina aurensu,amma a yanzu tazo da batun yana neman noqewa.
Tun daga ranar saiya zamana bashi da zance saina gini yakeson ya fara,mota
yakeson ya canza,yanzu kasuwa babu ciniki komai ya zamana sai a slow,gininsa ko
linter baikai ba,ga hada lefe da sauransu,kullum cikin qorafin ya fada financial
crisis iri iri.
Tuni tayi masa aji sukutum da guda ga ajjiyeshi,gefe guda kuma shirye
shiryen biki ake a gidan haiqan,kowanne sashe suna nasu shirin,itama bata zauna
ba,ta shiga anayin komai da ita,don 'yan uwanta ne da bata da tamkarsu.
*_ALƘIBLARSU |||_* �?
Ana gab da sallar magariba suka dawo daga kai dinkunansu na biki,wanda
ta hada dana hajja ummint ilham harda nata duka takai musu zoo road,kasancewar duka
duka bikin sati biyar ya rage.
A gajiye libis take,saboda sun dan sha tafiya a qafa kafin su samu abin
hawa,saboda yau ana wahalar abun hawa wanda batasan dalilin da ya kawo hakan ba.
Bandakin tsakar gidan hajja ta daura alwala ta shiga dakin hajjan ta tada
salla,tana idarwa wayarta ta fara tsuwwa,ta shafa addu'ar da takeyi ta janyo wayar
tana duba mai kiran.
Gaisawa kawai sukayi ta shigar masa da qorafin da taci alwashin gaya masa
"Ibrahim.....sam banga alfanu ko ma'anar ci gaba da tarayyarmu ba a haka.....aure
shine ribar kowacce alaqa da dangantaka,ya kamata mu fuskanci reality,kayi abinda
ya kamata" ajiyar zuciya ya sake cikin wani yanayi ya soma magana mai kama da ko in
kula
"Abinda na kira na gaya miki dama kenan,don kada ki zargeni....kin ganni
nan.....wallahi kakata ce wadda ta haifi ubana tayimin mata,ta kuma ce lallai
lallai kona aureta kota tsinemin,ni kuma naga babu yadda zanyi ko don na farantawa
babana,shi yasa na kiraki na baki haquri don dole nayi musu biyayya,Allah ya hada
kowa da rabonsa" daga haka ya katse wayar.
Tamkar mutum mutumi haka tabar wayar a kunnen tana sauraren shuru,duk da
cewa tasha qiyasta haka qarshen alaqarsu zata kasance,amma bata taba kawowa zatazo
ta wannan sigar ba.
Sallamar salma ita ta taimaka ta dawo da ita hayyacinta harta samu nasarar
cire wayar daga kunnenta,kallon fuskar zahran yasa salma ta fahimci akwai
matsala,saita qaraso tana tambayar zahran lafiya?
"Mun rabu da ibrahim shima salma" ta amsa mata da yanayin data kasa tantance wanne
ne?,baqinciki ne ko tashin hankali?".
Duk abinda salman ke fada tana jinta ne kawai ba tare da tana fahimta
ba,har tayi ta gama,saita zama kamar wata mutum mutumi,abu na qarshe data ji shine
qwalla dake saukowa a idanunta masu dumi,wanda yayi dai dai da shigowar hajja.
Wannan karon itama hajjan hankalinta tashi yayi fiye da baya,ta dinga salati
tana salallami,ita kanta salma hankalinta ya tashi,wannan wacce iriyar qaddarace
haka daya bayan daya?.
Ƙarfe tara na dare ta isa sassan umminta bayan kiran datayi mata kwanaki
uku da faruwar al'amarin.
A dakin gadonta ta sameta ita kadai zaune gefan gado,bayan ta baro qannenta
a falo zaune,zata zauna qasa ummin ta nuna mata gefanta gami da cewa
"Zauna nan"babu musu ta zauna din tana duban mahaifiyartata
"Zahra'u....kalleni nan" ta fada tana dubanta,kanta ta daga tana duban ummin
tata,ta hangi da gasken gasken zata gaya mata koma menene zai fito daga bakinta
din,saboda ba kasafai take kiran sunanta haka kai tsaye ba,da wahala ta kirata haka
da wannan sunan kai tsaye,don sunan hajja ne fatiman,sunan dake da daraja a
idonta,don haka ta sake tattara mata hankalinta
"Zahra'u....inason ki gayamin,tsakaninki da mahaliccinki wanne abu kike aikatawa da
dukka manemanki suke barinki haka bagatatan?" Take idanunta ya tara hawaye,muryarta
tana rawa tace
"Ban sani ba ummi,bani da masaniya"
"Ki gayamin inna wuro....tun wuri ki shaida min,meke faruwa?"
"Ki yarda dani ummi,wallahi babu wani abu" shuru ne ya biyo baya na wani dan
lokaci,sai sautin sheshsheqar kukan zahran tsahon wani lokaci sannan ummin ta sake
cewa
"Inason ki sake dagewa da addu'a,bawai ki zauna haka ba,ki gayawa Allah
matsalolinki da buqatarki,a shirye yake ya amsa miki buqatunki,ya kuma yaye miki
matsalolinki" kai take gyadawa a hankali,sosai tausayin 'yar tata ya kamata,sai
tace
"Tashi kije...Allah ya shige mana gaba".
***********
A hankali a hankali suka soma jin sautin salatin daga sassan abba babba,sak
dukkaninsu sukayi suka kasa kunne,tabbas daga can sautin salatin yake fitowa daya
nabin daya a jejjere.
_kuyi manage da wannan,mu hadu gobe in sha Allah dan jin meke faruwa?......_
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: 12
*OUM DUFAIL!!*
_GIDAN ADO ƘAWA DA KECE RAINI_💄💅🏽
_OUM DUFAIL ta tanadar muku dukkan nau'in kayayyakin gyaran fata gashi dama jiki
gaba daya ZAHIRINKI DA BAƊININKI samfurin MAIDA TSOHUWA YARINYA_
07067943479
Minti biyu saiga hafsat ta fito tana hawaye hannayenta a ka,dukkansu suka
nufeta cikin sauri kuma cikin tashin hankali,don dukkansu sun kasa shiga sashen har
sai data fito
"Yaa zahra.....yaa zahra,ya zahra ta mutu" ta fada tana rushewa da kuka.
Sak kowaccensu tayi tana jin maganar tana shigarta,babu wadda ta kawo
faruwar hakan cikin ranta a cikinsu,zahra ce tayi qarfin halin cewa
"Yaa zahran da take makaranta?,me ya sameta haka?,rashin lafiya tayi?"
"Maciji.....maciji ne ya sareta"
"Innalilahi wa inna ilaihi raji'un" kowaccensu ke maimaitawa.
Cikin ƙanƙanin lokaci duka matan gidan suka shirya suka fito saboda nuna
kara ga mama,uwa uba kuma ga surukuta da take shirin shiga tsakani,gidan ya zamana
babu kowa,daga 'yammatan sai yara,su dinma zaman jugum jugum sukayi,kowanne a
cikinsu yana tuna yaa zahran da irin kirkinta,haquri gami da sanyin hali.
Sai washegari su suka je gidan makokin bayan sun girka abinci mai yawa sun
tafi dashi kula kula,ko acan ma kusan baya ga mahaifan zahran haidar shine mutum.na
gaba da aka tausayawa,kowa yaje ya masa gaisuwa ya dawo saiya fadi irin halin daya
ganshi,wata mata dake matuqar kama dasu mama,wanda da alama danginsu ce tace
"Dole aliyyu ya shiga wani hali,a gabansa ajalin zahra ya risketa,kuma a gabansa ta
mutu,ai dole,mutuwar masoyinka gaban idanunka aiba qaramin al'amari bane da zaiyi
saurin barin zuciya da tunani nan da nan".
Shuru inna wuro dake gefe tayi tana nazarin al'amarin,tabbas jikinta yayi
sanyi sosai,komai saiya sake fice mata akai,musamman sanda ake dawo da kayan zahra
daga hostel,yau ga komai na zahran amma babu ita,tana can duniyar da babu wanda ya
isa ya dawo da ita,ta tafi kenan tafiya ta har abada saidai tarihi.
Rasuwar zahran yasa aka qara wata daya kan yadda aka tsara bikin,zuwa sannan
ana saka ran zuciyoyi sun huce,an dan samu nutsuwa da dangana akan lamarin.
*_SAUYIN RAYUWA_*
Tun daga sanda abun ya faru gaba daya tamkar an sake canza haidar din daka
wanda dacan suka sani zuwa wani na daban,ya sake zama miskili na qin qarawa,bai
damu da zama ko rayuwa cikin mutane ba,magana saita zama dole ko ta shafi
aikinsa,ya sake zama mutum mai zafi qwari da gaske fiye da baya,har kowa cikin
gidan na shakka da dari dari na taboshi ko shiga cikin sabga ko huruminsa,bama su
da suke qannensa mata ba,harda su ya musty kowa shiga taitayinsa yake idan ana
maganar ya haidar,hakanan ya sake rungumar aikinsa,ya rabu da komai.
Ganin abun bana qare bane yasa tace su sashi kawai a addu'a,ubangiji ya
sanyaya masa zuciyarsa,ya cire masa wannan tunani daga qwaqwalwarsa.
Biki akayi gagarumi wanda yabar tarihi cikin zuri'arsu,baqi na kusa dana
nesa duka sun hallara,ansha hidima sosai,a hakanma an rage wasu abubuwan saboda
rasuwar da akayin,amma hakan bai hana wasu hidimomin ba,tunda yaran bana sashe daya
bane ba.
Xahra tamkar zata raba kanta gida hudu,saboda kowacce idan ta tashi ita take
nema,baga yasira ba,baga yusra ba,baga hafsat ba,hakanan ba ga salma ba,a qarshe
dai bayan amare kowacce an miqa ta gidanta sai data kwanta zazzabi na kusan kwana
biyar.
Gaba daya daga bikin xuwa daurin auren babu wanda haidar yazo,ya kira ya
musu Allah ya sanya alkhairi,ya kuma ce aiki ne ya tsareshi bazai samu zuwa ba.
Hajja ce mutum ta farko data fara lura da hakan,duk itama sai taji babu
dadi,tasan cewa kewa ce ke damunta na 'yan uwanta da suka rayu tare suka taso
tare,don haka tayi wani tunani,ta nemi abban gwammaja da babban danta abba babba ta
zauna dasu,ta bada shawarar baiwa zahran damar ci gaba da karatu,idan yaso duk
sanda Allah ya kawo mata manemi sai ta yanke tayi aurenta,don yafi wannan zaman da
zatayi,domin zaman bashi da wani alfanu,hakanan babu abinda zai qara mata sai
damuwa.
Dukkaninsu sunyi na'am,don result din zahran ba qaramin kyau yayi ba,don
haka abban gwammaja ya nemi a bashi takardunta amma abba babba yace sam wannan
karon shi zaiyi wannan aikin,hakanan abban gwammaja ya sallama din,tunda sun bashi
damarmaki a baya sosai kan yarinyar,bai kamata a yanzu shima yaqi basu tasu damar
ba.
Wani irin farinciki da bata taba tunanin zata jishi ba shi taji a sanda
labarin ci gaba da karatunta ya risketa,duba da cewa ita sam bata da sha'awar ci
gaba da karatu tun a baya,hafsat da yasira sun fita wannan kwadayin,tayi murna
sosai,ta kuma tabbatar da qaunar da hajjanta ke mata ta daban ce,hakanan 'yan uwan
mahaifin nata mutanene da samun kamarsu a wannan zamanin sai an tona,wannan shine
ya zamto silar ci gaba da karatun zahran,mace ta farko a tarihin gidan data taba
tsallakewa zuwa makarantar gaba da secondry.
*_SABUWAR DUNIYA_*
Kamar kowacce daliba,ta shiga makarantar cike da baqunta da rashin
sabo,komai nata idan ka gani irin na farin shiga ne,sannu a hankali har ta fara
gogewa tana kuma gane kan abubuwa.
Iyayen hindatun 'yan boko ne na gasken gaske,ba irin 'yan bokon muna boko
ba,kusan hatta kakan hindatun asalinsa dan boko ne,irin 'yan bokon da turawan
mulkin mallaka suka koyar tun duniya tana kwance,don haka idan ana gadar boko xa'a
iya cewa sun gadon,don kuwa hatta da dabi'unsu da al'adunsu irin na nasara ne,akwai
'yancin da zabar rayuwa cikin gidansu hindatun,hakan ya sanya kome zakiyi kina da
right,babu me tauyeki ko hanaki,wannan yasa sau tari zahra kan xauna tayi ta
mamakin rayuwarsu,domin ita nata ahalin don boko sunyishi,ba za'a gaya musu shi
ba,amma basu yarda hakan ya janyesu daga kan tsari da al'ada ba,da kuma dabi'u na
musulunci.
Sannu sannu sai qawayen hindatun suka soma zama na zahra,domin kusan ko
yaushe kuma kullum suna tare,dakinsu guda saboda kwanan hostel takeyi,hindatu nada
shaqiqan qawaye guda hudu da bata da kamarsu,dukkaninsu suna 'ya'yan manya
ne,kowaccensu tana ji da arziqin ubanta wayewa uwa uba kuma gayu,akwai
batula,nadiya,farida da kuma jannah,wadanda kansu ya bude sosai,hakan idanuwansu
kusan a bude yake.
*_ABDUL_YASAR_*
Tun asali bata fiya son fitar dare ba,kada ma ace wannan unguwar
zatazo,domin titin indai dare yayi akan samu qarancin zirga zirgar ababen hawa
musamman na haya,saboda manyan gine gine dake cike a unguwar yawanci saidai motocin
gida dake wucewa ɗai ɗaiku.
Abinda ma yasa ta yanke taje din,ganin anyi gyaran titin na yahaya gusau
din,hakan bazai bata matsalar dawowa gida ba,tunda tazarar dake tsakanin unguwarsu
da unguwar bamai yawa bace,zata dawo da wuri.
Saidai kuma tunda ta fito titin adaidaitan data wuce basufi a qarga ba,su
dinma akwai mutane ciki,haka ta soma takawa a hankali don rage tsayin
tafiyar,gabanta na dan faduwa kasancewar titin akwai fitilun titi,amma basu da
maraba da tirken awaki,tunda ba'a kunnasu bare su bada hasken da ake buqata,sai
hasken gine gine jifa jifa dake bakin titin,da kuma hasken ababen hawan dake
wulgawa.
Sai yanzu take jin hushin kanta me yasanya bata taho da dan rakiya ba
cikin yaran gidansu?,tana tsaka da wannan tunanin wayarta ta dauki qara alamun
kirane ya shigo,ta dago qwayar tana duba me kiran nata.
Hafsat ce,saita saki murmushi najin dadin ganin kiran 'yar uwartata
"Aini nayi fushi wallahi,babu abinda zakice dani" hafsan ta fada zahra na daga
wayar
"Wayyo Allah na,me kuma nayi?"
"Au baki ma sani ba?,to bari na gaya miki,kinga na farko tunda mukayi aure zuwanki
gidajenmu baifi a qirga ba,kowa qorafi yakeyi,na biyu kuma bani da lafiya,kowa yazo
ya dubani,wasu sun kirani amma keda ya haidar baku zo ba banga kiranku ba,to wai
don Allah meye marabarki da ya aliyyun ma?"
"Na yarda na miki laifi,amma ki daina hadani da wannan dagen....sannan kimin
uzuri,rashin zuwa na gidanku wallahi hafsat makaranta ce,kuma kin sani,sannan
lalurarki ni dana dawo babu wanda ya gayamin baki da lafiya"
"Eh ai saboda ansan ma ba zuwa zakiyi ba" murmushi tayi mai sauti
"Kiyi haquri....haba hansatuwa,aiba haka tsakaninmu,in sha Allah gobe ko jibi zaki
ganni,kuma wannan karon bazan koma ba saina jewa kowa na kashe mitarku,ke ina
tunanin ma da qyar idan ba strike za'a tafi ba wani satin,kinga idan hakan ta faru
kwana daya daya zanwa kowa"
"Heee....na dai jiki kawai,a samu kizo dinma"
"Waima meya sameki?" Zahran ta fada tana qunshe dariya cikin salon tsokana saita
dora da
"Kodai an gamu ne?"
"An gamu dake ba....idan kinzo kya gani"......
"Wanne layi zaki shiga?" Taji ya tambaya,saita nunawa mai napep din har
suka qarasa qofar gidansu sannan ta sauka,tana niyyar biyan mai abun hawan yace
"A'ah hajjaju ki barshi,inason in samu ladan"
"Na gode" ta fada kawai ta fada gida,don har yanzu tsoron data shiga dazu bai
saketa ba,batasan sanda suka bar qofar gidan ba.
_OUM DUFAIL ta tanadar muku dukkan nau'in kayayyakin gyaran fata gashi dama jiki
gaba daya ZAHIRINKI DA BAƊININKI samfurin MAIDA TSOHUWA YARINYA_
07067943479
Ganin doguwar riga ce a jikinta mai dogon hannu,kuma budadde ne dinkin babu
ta inda ya kama jikinta saita sanya qaramin mayafi tayi rolling dashi sannan ta
fito.
Hajja kam baki ta kama sannan ta saki tana ruqo hannun zahran
"Karka sake gayawa jikata haka,a ciki ni banga abun laifi ba,indai ba daga bracck
aka bata kama rai ba zaka zo ka juyeshi a nan ahto" qaramar ajiyar zuciya ya sauke
"Ke tashi ki bamu waje" ya fada cikin sigar bada umarni,saita miqe da hanzari,ta
murguda baki bayan ta juya musu baya cikin ranta tana mita.
Sai a sannan zahra dake labe ta fito da hanzari muryarta na rawa kamar
zata sake kuka tace
"Kinji ko hajja....kinji sharrin da yakeson yimin,ni ba'ace komai a kanshi ba
saboda zaman bariki ba saini don ina makaranta"
"Kinga dagani....na gaji da wannan iskancin naku keda zaki,yara kamar mayu?,kamar
masu ganin hanjin juna?,to wallahi idan bakuyi wasa ba aure zan saka iyayenku su
daura muku naga qaryar iskanci" wani irin tsalle zahra dake zaune a jikin hajja ga
buga kamar wadda aka dorawa kunama a jiki,ita kanta hajjan saida tayi sak cikin
tsoron tana duban zahra dake fadin
"A'uzu billahi minash shaidanir rajim,hajja....wacce irin masifa kike ambata da
yammacin juma'ar nan?" Ta fada idanunta duka a waje,tafin hannu kawai hajja ta saka
tana rufe bakinta dashi tana fadin
"La'ilaha ilallahu,muhammadurrasulullahi,sallallahu alaihi wa sallam inna
wuro?,kamar wadda tace miki tsohuwarki ta mutu?,wannan zancen ne masifa?,anya
zahra?" Ganin yadda bacin ranta ya bayyana yasa ta sassauta nata,ta qarasa wajen
hajjan ta zauna tana narke murya
"Kiyi haquri hajja,ba haka nake nufi ba,don Allah ki haquri,amma.in sha Allah na
daina shiga huruminsa,dama ni ba shiga nake ba,shine haka nan ba gaira ba dalili ya
matsantamin"
"Kema ai bajin magana kike ba,ko don kinga ina baki kariya?"kamar zatayi kuka tace
"kiyi haquri dai don Allah abar zancan,na daina in sha Allahu" shuru tayi kamar ba
zatayi magana ba,sai kuma ta sake ajiyar zuciya
"Ai shikenan....Allah ya kyauta" jin haka don kada ta sake jan wata maganar saita
miqe kawai tayi dakinta,a ranta tana juya zancan
"Itama.hajjan nan wani lokacin wlh tuburarriya ce,haka kawai da yammacin ranar
juma'a,dai dai sanda ake amsa addu'a ki fadi wannan mummunan kalamin kisa 'yan amin
su amsa?" Ita daya ta qaraci mitarta cikin daki harta haqura.
Da magariba zata gurin me gadi amsowa hajja goro da me gadi yace tazo
ta amsa taga qofar gidan nasu cike da jama'a,kusan hakan ba sabon abu bane
wajensu,duk randa aliyyu ya sauka a garin gidansun baya rabo da mutane,duk da cewa
ko baya nan din ba'a rasa mabuqata jifa jifa masu neman taimako,amma kuma cikarsu
bata kaiwa yadda take a yanzun.
Ta sani cewa wani lokaci akan zo ma su hajja godiya kan wani abu da aliyyun
yayi cikin unguwar,saidai su amsa don babu wanda yasan ma yayi din,kusan haka
dabi'arsa take idan zaiyi wani abun alkhairin,itakam tana dauka kawai shashanci ne
irin na mutane,don bataga alamu a yadda aliyyun yake da baqar zuciya,zai iya wani
abun arziqin da zai farantawa wani rai ba.
*************
Kamar da wasa kuwa wata washegarin ta gama wankewa hajja qananun kayanta ta
fito ta falo,tana tsaye gaban tv taji kamar muryar hindatu tana magana,da alama
yaran gidansu ne da yau gaba dayan 'yan mazan da matasan abba babba ya raba musu
gyaran flowers da farfajiyar gidan,tunda an yiwa wanda yake musu wannan hidimar
rasuwa,ya tafi qauye.
Aje remote din tayi tana tafa hannu cikin mamaki da jin dadi
"Na zaci zancanki ne kawai fa da kika ce zaki zo" itama tana murmushin tace
"Kin taba ganin na saba alaqawari" kai ta girgiza tace
"Ina sara miki ta wannan sashen ai".
Sai data gabatar mata da ruwa da lemo sannan ta yiwa hajja magana ta fito
suka gaisa,ba wannan bane zuwanta gidan na farko ba,ta taba zuwa sau daya,wannan ne
na biyu,hindatun ta jima sosai suna hira,don a nan taci abincin rana ma,sannan ta
kira jannah batula nadiya da farida suka hada kira na bai daya suka sha hira har
zuwa sanda akayi sallar la'asar,ta shiga nan bandakin zahra din ta daura alwala.
Tana saman abun sallar zata tayar kenan ta waiwayo ta dubi zahra
"Yauma fa na sake ganin yayankunnan,ya hakimce saman kujera qafa daya saman daya
yana karatun jarida,duka yaran kowa cikin hankalinsa yake aikinsa ba hayaniya da
alama shike gadinsu,bakiga yadda tsare gidan da yayi yayi masa kyau ba"hindatu ta
fada,kallonta zahra tayi
"Wanne fa?,ya musty ko ya shamsu?"
"A'ah fa....sojan nan....wallahi nikam idanuna basu taba ganin namijin da yamin
kwarjini,ya kuma burgeni,na kuma ji na shirya aurensa ba irinsa....don Allah qawata
ki shigemin gaba mana" ta fada cikin karyar da murya.
Tsaki zahra taja
"Don girman Allah ki tada sallarki ya fiye miki arziqi,wannan maganar taki ki nema
abokin yinta amma ba zahra'u ba" saita sanya filo saman katifarta ta kwanta rub da
ciki,hindatun dai bata haqura ba tace
"Saboda me kika ce haka?"
"Ki barni don Allah hindatu" da taga ta matsa da maganar,da zancan saita gaya mata
dalili sai tace
"Ba ya haidar ba?,ai nan ne gidansu,kuma yana cikin gidan,kina iya gwada
sa'arki,kije ki gabatar masa da kanki mana qawata"
"Au haka kika ce?,zakiga aiki kuwa da cikawa"ta fada tana kabbara sallarta
"Da dai yafi" itama ta amsa mata tana gyara kwanciyarta.
Tare suka fito don mata rakiya,zuwa sannan sun gama gyaran sai ganyayyakin
da suke hadawa,ya mustapha na nuna musu inda zasu zuba za'azo a kwashe daga wajen
kwashe shara.
Har yanzun haidar din na zaune inda yake,saidai wannan karon maimakon
jarida wani littafine a hannunsa yana dubawa,mai kalar kakin soja,tabo zahra
hindatu tayi,saita matsar da hannunta ba tare data dubi zahran ko inda haidar din
yake ba,don ta fuskanci abinda take nufi,sai tayi gaba hindatun na biye da ita.
Bata ankara ba taji hindatun na gaida haidar cikin wani salo,saidai bai
amsa ba sai data sake magana karo na biyu sannan ya amsa ciki ciki da qyar kamar
wanda aka tilasta.
_OUM DUFAIL ta tanadar muku dukkan nau'in kayayyakin gyaran fata gashi dama jiki
gaba daya ZAHIRINKI DA BAƊININKI samfurin MAIDA TSOHUWA YARINYA_
07067943479
Za'a iya cewa abdulyasar ya samu shiga wajen zahra saboda halayen daya
nuna,wadanda suka sanya tun tana dari dari dashi harta saki jikinta,saidai shi
kansa yadan dauki lokaci kafin ya samu ta sake dashi,saboda tana ganin kamar za'a
koma 'yar gidan jiya ne,saidai yadda yake kaffa kaffa da ita,da yadda yake nuna
tsananin kishinsa a kanta,da kuma yanda yake yawan jan hankalinta kan rayuwa kamewa
da kula da mutuncin kai yasa ya sake samun fada a wajenta.
Sau tari idan yaga wata halayya ta wasu yammatan yakan qalubalancesu,don
hatta su hindatu sai daya so ya rabata dasu,saidai data zauna tayi masa bayani da
kuma alfanun zamansu tare ta yadda zata ci gaba da nusashshesu yasa ya fahimta ya
kuma haqura.
Ta nata fannin sosai take qoqari wajen ganin ta kyautata masa shima,saboda
yadda ya damu da dukkan lamuranta,ta lura mutum ne maison cima mai dadi,saidai ba
kowacce iri ba,hakan ya sanya duk sanda zaizo wajenta girki na musamman take
masa,koda bazaizo bama,sau tari idan akwai kudi hannunta zata kirashi ranar taji
abinda yafi sha'awar ci,shi zata dafa masa ya aiko a karba masa,ko yazo da
kansa,yawanci yafison cimar gargajiya,kamar dambu,danwake,alala,wainar fulawa da
sauransu wani lokaci harda dan malele,to koda su din zata masa,zata kashe kudi
sosai ta qawata masa su,misali alala,na 'gwangwani baifi uku ba,zata zuba masa qwai
wadatacce,hakanan wainar fulawa zata cika mata qwai,harka dinga jin kamar wainar
qwai qwai,fulawa fulawa,kirkinsa da yadda ya samu fada wajen hajja saboda dabi'unsa
yasa koda batayi niyyar yi ba hajja da kanta zatace tayi masa,da kudinta
kuma,takance
"Abudulyassar akwai kirki akwai hankali,ai babu abinda ba za'a yiwa yaron nan
ba,yana da nutsuwa da sanin ya kamata,ni ba abinda yake burgeni irin yadda yake
tsaronki,kamar yadda yayanku haidar yakeyi".
Hatta fita siyan katin waya idan yaji tayi ranar babu zaman lafiya,ya dinga
fushi kenan da ita,bare kuma ya kira sama da sau biyu yaji busy,alamun tana waya
kenan,ya dinga mita da qorafi da binbini,tun bata saba ba har halayyarsa ta zama ba
baquwa bace wajenta,abokai da na kusa da ita kance
"ki gode Allah,mai yiwuwa sauyi alkhairi ubangiji zai miki,shi yasa dama ya kore
dukka wadancan ya kawo miki wannan".
Na biyu tana jin dadin aduk sanda tayi girkin ya tafi dashi gida yake cewa
mama(mahaifiyarsa)taji dadinsa,harma wani lokaci yakan kirata ya bata maman su
gaisa ta kuma yi mata godiya
(A baya nasa abdulyasar dan kaduna ne,afwan zamu canza mu barshi a dan kano ne
saboda wasu dalilai da anan gaba zan fadesu).
Bata mantawa akwai wani lokaci da wasu 'yammata suka zo suka wucesu,sosai
sunyiwa fuskarsu bleeching wanda koda yaro qarami yana kallonsu zai gane,tasan
halinsa,don haka tayi sha'awar tsokanarsa
"Nima man nan xan fara shafawa fa.....dama duk cikinmu da muka tashi na fisu duhun
fata,kaga nima saina fito washar abuna" fuska ya tamke sosai yana dubanta
"Zahra'u,kice min kawai lokacin rabuwarmu ne yayi" idanu ta fiddo tana boye
dariyarta
"Kamar yaya?"
"Eh mana....,ai daga randa naga kalar fatarki ta canza,ko naga qibarki tafi yadda
kike a yanzu,hakan na tabbatar min kina amfani da wasu magunguna kenan,todaga ranar
bana jin alaqarmu zata ci gaba da wanzuwa" dariyarta ta sake,tana sake jinjinawa
tsantseni irin na abdul yassar din,da kuma yadda yake kiyaye doka da qa'ida,da
qoqarinsa na azata bisa turba kowanne lokaci
"Ka kwantar da hankalinka,nima duka irin wadan nan ababen basa birgeni sam,saboda
dukka alqawari ne da shaidan yayi kan saiya batar da 'yan adam,ya sanyasu sun
aikata hakan,Allah ya bamu labarin hakan cikin suratun nisa'i wato surar mata
kenan,saboda ubangiji yasani cewa mu mukafi kowa saurin dulmiya daga kaidin
shaidan,suratun nisa'i,aya ta dari da sha tara.
Ba'a rufa minti ashirin ba auwal ya iso saman babur dinsa lifan
"Na fatima zahra,bada kanka a sare kaje gida kace ya fadi" ya fada yana dariya kana
ya bashi hannu suka cafke,kana ya maida dubansa ga zahra
"Dama ai nasani,bazai wuce nan din ba....gaskiya fatima kin dace da masoyi na
gaske,kowa yasan abdulyasar yasan ki,ba wanda baida labarinki,ya dagawa kowacce
mace red card saboda ke,wai don Allah meye sirrin?" Murmushi tayi tana cewa
"Um um auwal banda ziga,irin wannan koda abokinka haka?,kada fa naga ba haka ba"
dukka hannayensa ya daga sama
"A'ah....aini bana shakka....bana shakka kan maganata,ke kike shakka saboda bakiga
yadda ya damu dake ba ya kuma damu da zancanki ba....amma lokaci yana nan zuwa da
zaki yarda"
"To Allah ya nuna mana". Baifi minti goma suka qara ba auwal din ya daukeshi suka
wuce.
Cikin haka watan azumi ya sake kamawa,shima yazo musu a sanda ASUU suke
halin nasu,don haka wannan karon ma a gida sukeyin azumin.
Sosai abdulyassar kuwa yake nuna yabawa da dawainiyar abincin,a haka har
aka sallace azumin gaba daya,saidai ita abinda yake bata mamaki,duk da ba damuwa
tayi da komai nasa ba,abdulyasar din ba gwanin kyauta bane,amma da sukayi maganar
da salma sai tace
"Kada ki damu,wani haka yake,saikin shiga gidansa sannan zaki gane ba rowa
bace,gwaji ne" da wannan ta share zancan.
Itakam zahra ranta a bace yake,don gaba daya dinkunanta babu wanda telor
dinta yayi mata,saboda rainin wayo ma data matsa sai yaran shagon sukace ya tafi
ittikafi lagos,badon takai zuciyarta nesa ba a ranar su kansu yaran da sun sha
ruwan zagi,Allah yasa tana da wasu kala hudu da maman hindatu ta dinka musu iri
daya da hindatu ,dasu ta dinga amfani,amma ana ya gobe 'yan gidan nasu suzo,saboda
wani dan qaramin taro suke ranar kowa zaizo,ta daga hankalinta,saboda akwai kayan
da takeso sakawa a ciki,don haka ta shirya da safe da wuri ta iske hajja a falo.
Ita da haidar ne zaune,sai umaima 'yar abban tsakiya da nuratu dake gefe
gaban tv suna goge kayansu,da alama suma su zasu saka yau ko goben da kowa zai
hallara
"Ummm.....kaga 'yammatan gidan nan,wadan nan kayan na yaushe ne?" Da ido umaima ta
mata nuni da sashen da haidar din ke zaune,don ita bata lura dashi ba,daga kai tayi
ta dubi wajen,magana suke da hajja,hannunsa riqe da kudade,yayin da hajjan ke riqe
da wata takarda wadda kamar list din sunayen mutane ne a jiki,ta kuma tabbatar da
hakan sanda hajjan ke fadin sunayen yana irgo kudin yana miqa mata tana ninkesu,da
alama su za'a baiwa kenan,saita yatsina fuska ta dawo da dubanta kan yaran,wato
kowa indai da haidar a wajen baida sukuni?,for god sake zai dami kowa ne ahaan....
"Waye zai rakani amso dinki?" Duk sai sukayi matsa gefe
"Anya ko yaya zahra zaki samu dan rakiya yau,wallahi ya musty ne yace kowa ya
shirya zai kaimu shoprite mu zabi abinda mukeso,daga nan mu wuce minjibir park" ta
fada qasa qasa don kada haidar din yaji saita kama baki
"Yau ni ake qin rakawa?....to ai gobe ma rana ce" suna 'yar dariya suke cewa
"Ki haquri yaa zahra...Allah yace duk wanda yaje wani gun bazai jirashi ba" batace
komai ba ta qarasa wajen hajja,a sannan har haidar din ya miqe,hannunsa empty,da
alama ya rabar da kudinne gaba daya.
Sanda ta iskeshi a ma'ajiyar motoci har ya kunna motar,ta bude gidan baya
ta zauna,a nutse ya waiwayo ya mata wani kallo daya sanyata tilas ta fito daga
bayan ta dawo gaba,don ga fahimci manufar kallon nasa sarai.
Luff tayi cikin motar,wani irin qamshi mai taushi da sanyawa zukata nutsuwa
ke tashi cikin motar,ga sanyin ac daya karade motar,shi kansa wani qamshi yake
busowa kamar an zuba iskar wani abu,yayin da wani slow music ke tashi qasa qasa
yadda bazai takura me sauraro ba.
Basuyi nisa ba suka tsaya qofar wani gini,wanda baiyi kama da gida
ba,yafi kama da qawatacciyar ma'aikata,parking yayi da kyau,sannan ya buda murfin
motar yayi ficewarsa,ta bishi da kallo har aka bude masa qofar ya shiga.
Ajiyar zuciya ta saki ranta na baci sanda ta kalli agogon hannunta taga ta
kwashi minti talatin zaune a motar babu shi babu dalilinsa,Saita fara neman abinda
zata rage zaman kadaicin dashi,tunda ta baro wayarta a gida,a tunanin yanzu yanzu
zataje ta dawo.
_Abune mai matuqar ciwo ne a rayuwa rashin masoyi ko kuma wanda yake qaunarka,zaka
yita tunawa cewa yayi maka nisa,kullum idan rana ta fito ta fadi ya maka nisan da
babu masaniyar ranar da zaka taddoshi,sannu a hankali saika soma manta yanayin
murya dariya ko murmushinsa,kome yawan damuwarka ba zata taba dawo maka da shi
ba,amma sai zuciyarka ta kasa gasgata hakan,kayita hasashe da fatan zai dawo
gareka_
Tana tsaka da maimaita rubutun taji tsaiwar mutum a kanta saitin window
din da take,aliyyu ne tsaye,harde da hannayensa a qirji yana dubanta,kwarjininsa da
tsoro yasa ta diririce,ta soma qoqarin maida littafin inda yake,sai taga kawai ya
miqo mata hannu,ba musu ta sanya masa littafin a hannun nasa a sanyaye,sai kuma
taga ya bude murfin sit dinta,da idanu ya mata alamun ta fito,a sanyaye ta fito
cike da tsoron me zai mata,tana tsaye ya zagaya ya shiga nashi sit din,ya sanya
hannu ya rufe daya murfin bayan ya rufe nasa,sannan ya kunna motar yaja yana barin
wajen,zahran ta bishi da kallon mamaki har sai daya fice daga layin.
Ranta a bace ta isa shagon,abinda yadan sanyaya mata raima taje ta taras ya
gama mata duka dinkunan,tana amsa tayo gida,saidai batayi niyyar gayawa hajja ba
sam bare tace wani abu da zai sake dagula mata lissafi.
*_BANKAƊA_*
_abun ɓoye!_
A hankali take takowa daga cikin gidan zuwa qofar gida sanye da doguwar riga
marron mai sulbi,duk da ba kwalliya tayi ba amma tayi mata kyau sosai,hakanan
jikinta na fidda wani qamshi mai aji da tsayawa a rai.
Masu karatu
*ALƘIBLARSU!* �?
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: 15
*_ina 'yan uwa musulmai masu kishin addinin islama???_*
*_Ɗanku kuma dan uwanku kuma qaninku wato ABDURRAHMAN,yaro mai hazaqa gami da
kwadayin haddace littafin Allah mai tsarki,ya bude YOUTUBE CHANNEL nashi na qashin
kansa,ku tallafa masa ta hanyar shiga wannan shudin rubutun ku danna masa
subscribe,ba abunda xai rageku dashi saima samun dimbin lada dalilin KARFAFA MASA
GWIWA,MUN GODE 🙏🏽🙏🏽🙏🏽_*
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
https://youtu.be/WWIGq5Jbtb0
Tana komawa cikin gida shirin kwanciya tayi saboda a gajiye take yau
din,duk da tana son zuwa susha hira da hafsat wadda tazo dazun,zata kuma kwana har
uku,saboda me gidan nata wata tafiya ta kamashi,da qyar kuwa ya haidar ya barta
saida yaji daga bakin mijin nata,sun yiyyi baqi yau din sosai,bata zauna ba hakan
yasa ta gaji da yawa.
Sai data kwanta sannan ta kira hafsat tace karta jirata,tayi kwanciyarta
gobe da sassafe zata shigo ta tasheta
"Ba komai wuron hajja,Allah ya kaimu"
"Aha" tace tana datse kiran.
Tun tana cijewa tana kallon har idanunta sukayi nauyi,batasan sadda bacci ya
dauketa ba.
Sanda ta farka da sauri ta jawo waya tana dubawa,a zatonta zata samu
miscal din abdulyasar din,babu miscal babu kuma saqo,ta kalli agogo,sha biyu na
dare har da rabi,kenan ya saba lokacin da yace zaiyi kiran nata?,hakanan sai taji
idanunta ya bushe,baccin yayi nasa guri,saita miqe ta shiga bandaki ta daura
alwala,ta dawo ta tada salla.
Ta kusa kaiwa qarfe biyu saura na dare tana zaune saman abun sallahn,har
bacci ya sake dibanta taji qarar wayartata,saita miqa hannu ta dauko wayar,idanunta
ya sauka kan agogon qarfe biyu da rabi na dare,ga mamakinta lawal ne abokin
abdulyassar yake kiran,sosai hakan ya bata mamaki,wata mummunar faduwar gaba ta
ziyarceta har batasan sanda ta daga wayar ba.
Muryar lawal dince ta bayyana cikin tsantsar tashin hankali yake fadin
"Zahra....abdul ya mutu,abdul ya rasu,qarfe sha biyu na dare yayi hatsari a
hanyarsa ta tafiya,Allah yayi masa cikawa a take" dif wuta ta dauke mata,saita
daina jin abinda lawal din yake fada,sai wata qara dake ratsa kunnenta kamar an
buga qarfe da qarfe,ita dai batasan mintinan data shafe a haka ba,batasan kuma
sanda lawal ya katse nashi kiran ba,batasan yadda akai ta kai kanta dakin hajja
ba,sai ganinta tayi ta fada saman hajjan tana wani irin numfashi.
A matuqar firgice hajjan ta miqe ta zauna,don dama bata jima da gama sallar
dare ba ta koma ta kwanta
"Zahra'u....zahra'u!....mene ne?,innalillahi wa inna ilaihi raji'un,yi kuka....kiyi
kuka zahra'u,barshi ya fito" ta fada taba danne mata qirji,ganin yadda yake sama da
qasa numfashinta kuma na wahalar shaqa,cikin ikon Allah ta fusgo numfashin da qarfi
sai kuma ta saki wani qaqqarfan kuka ta fada jikin hajja gaba daya ta qanqameta
"Innalillahi" hajja keta maimaitawa,cikin ikon Allah itama zahran saita kama,tsayin
wasu mintuna masu tsaho sannan ta iya magana cikin sheshsheqar kuka
"Hajja.....abudul....yassar ya.....mutu,yayi hatsari baya.....n nyabar wajena,ya
rasu hajja!" Ta qarashe cikin gunjin kuka.
Sosai hankalin hajjan ya tashi,ta sake qara qarfin salatinta tana kuma
maimatawa,wannan dare ya zamewa zahra dare mai tsaho duhu da kuma qunci,haka suka
zauna ita kuka hajja lallashi,kafin gari yakai ga wayewa tuni idanunta suka suntuma
suka kumbure,qwayar idanunta dukka sun shige ciki.
Suna idar da sallar asuba hajjan ta daga waya ta kira abba yusuf,saboda
abba babba baya gari,cikin lokaci qanqani ya iso,bayan su gaisa ta shaida masa
zancan rasuwar
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" shima ya dinga maimaitawa
"Yanzu abinda za'ayi....inaga idan gari ya sake shaaa,ka bawa mustapha ko shamsu
muqulli sukaita gidansu yaron,don hankalinta bazai taba kwanciya ba,ba zata zauna
ba,in yaso idan ya dawo daga kaitan zuwa lokacin mu mun kintsa saiya miqa mu,idan
mukaje saimu duka mu dawo tare,ku kuma ko zuwa yamma haka zuwa dare kwa leqa ku
yiwa iyayensa maza ta'aziyya"
"To shikenan,Allah yayi masa rahama,yasa ya huta".
Ko a cikin motar ma dai kukan take yaqi tsaya mata,ta dora kanta saman
kafadar hafsat tana shashsheqa
"Kiyi haquri zahra ki masa addu'a,a yanzu ita yafi buqata"
"Shikenan hafsa...shima ya tafi ya barni,hafsat nice mutum ta qarshe da yazo
wajenta,nice mutum ta qarshe daya kira da wayarsa,ashe da yazo bankwana yazo
yimin?,ashe ya tafi kenan?" Sosai ta karyarwa da hafsat zuciya,haka taci gaba da
lallashinta har suka isa qofar gidan su abdulyasar da taimakon kwatance da lawal ya
dinga musu.
Babu kowa qofar gidan sai daidaikin mutane,da alama an tafi kaishi
makwancinsa na gaskiya,hafsat din ita ta riqe zahra har zuwa cikin gidan.
Cike gidan yake da mutane,wasu kuka wasu tagumi,hafsat ce mai qarfin halin
gaidasu,sannan ta tambayi inda hajiyan abdulyassar din take,aka nuna musu wani falo
dake cike da jama'a suka nufi can.
Kana kallonta zaka gane mamansa ce saboda suna kama,tana zaune saman
kujera,sanye da ash din hijabi da carbi a hannunta tana ja.
A yanzun layin a dinke yake da jama'a,da alama har sun dawo kenan,haka yasa
sabuwar qwalla suka zirarowa zahra,yanzu haka abdul nacan kwance,nacan kwance qasan
qasa,babu kowa saishi kadai,babu kowa sai halayyarsa da ayyukansa.
"Zahra duka shagunan layin nan a rufe suke" taji hafsat na fada,kai ta
gyada tana share hawayen fuskarta
"Eh na gani,amma layin nan kamar layin gidansu rabi'ah ishaq ko?,da kika tana
rakoni?"
"Eh tabbas,aiga gidan nasu can ma qarshen layi"
"Yauwa,mu qarasa nasha ruwan a can kawai"
"Ok" hafsat ta fada,kai tsaye suka miqe zuwa gaba,wanda gidan ke jerin gidajen dake
jikin gidansi abdulyasar din,tsakaninsu da gidansu abdulyasar din gida biyar ne
kacal.
Da sallama suka shiga gidan,wata mace dake duqe bakin fanfo tana wanki ta
daga kai tana amsa musu sallamar
"Ku qaraso mana" ta fada tana dagowa daga duqen da tayi.
Tuni ta miqi hanya ba tare dako waiwaye ba,ita kanta hafsat din sai
cimmata tayi a hanyar
"Zahra....da kin tsaya ya shamsu ya dawo ya maidamu" kaita girgixa idanunta na
sauka kan gungun abokan abdulyasar dake zaune qasan wata rumfa,can ta hango auwal a
tsakiyarsu,wani abu ya caki zuciyarta,tsanar auwal din ta kamata,tabbas babu shakka
yasan komai,yasan duk abinda ke wakana tunda amininsa ne,dashi aka hada baki,dashi
aka rufeta
"Muje kawai hafsa,ma hadu a hanya" a yanayin data ga ta shiga,tasan cewa koda
bayani tayi mata babu lallai ta fahinta,don haka taci gaba da binta a baya suna
tafe zafin rana na dukansu.
Basuyi nisa ba suka soma jin hirar wasu mata biyu a bayansu
"Kai mutuwa....mutuwa masu gari,babu ruwanta da babba ko yaro,tsoho ko tsohuwa
kawai dauka take"
"Hmmm....kedai Allah yasa mu dace,mutuwa ma irin wannan ta abdul ai tafi ratsa jiki
da daga hankali,mutuwar saurayi?,sati biyu kacal da kai kudin aure ashe ba za'ayi
auren ba,babu ma abu mafi tausayi irin yarinyar daya kaiwa kudin,kamar zata shide
wallahi abun tausayi"
"Ai da tausayi,Allah yasa mu cika da imani".
A zafafe zahra ta soma takawa tana koma zuwa layin da suka baro,hafsa ta
cafki hannunta
"Ina zaki?"
"Zanyi magana da auwal" daga haka ta zame hannunta ta koma.
Suna nan inda ta barsu,harda qarin wasu abokan nashi wadanda yakanje dasu
lokaci zuwa lokaci,dukkansu tasan fuskarsu sunsan fuskarta.
Wani yawu mai tauri take hadewa cikin motar,gaba daya ji take zuciyarta ta
bushe ta qeqashe,lamarin maza ya fice mata fit a ka,me yasa ne basu da *ALƘIBLA?*
me yasa kowanne da kalar zaluncinsa ga 'ya mace?,saboda muna da rauni?,saboda ba
zamu iya aurar da kanmu ba saidai a auremu?,me yasa mazan zamanin nan suka zama
fitina ga rayuwar 'ya'ya mata?,me yasa duk wani bala'i,shiga ha'ula'i da tashin
hankalin mace mafi akasari kan ɗa namiji ne?,baki auren ba baki huta ba,kinyi auren
baki huta ba,sai yaushe diya mace zata hutama ranta?,ba a iya kanta ba,akan mata
'yan uwanta da yawa taga irin hakan,me yasa suka maidashi kamar anko ko gasa,sun
maidashi abun kwalliya,YAUDARA!....shin basa tunani ne?,basa tunanin cewa suna
wataran iyayen wasu ne?,basa tsoro da fargabar kada abinda sukayi a fanshe kan
diyoyinsu wadanda basuji ba basu gani ba?,inda ta godewa Allah....babu wanda ta
saidawa mutuncinta,babu wanda yayi nasarar tarwatsa mutuncinta,yau inda acw ta
aikata hakan ta tabbatar nadama da dana sanin da take ciki ta zarta ta yanzu,sai
Allah yasa bata watsar da tarbiyyarta ba,bata bari rudi da zaqin soyayya ya jata ta
aikata babban kuskure mai tarwatsa rayuwa ba,kuskuren da bashi gyaruwa har abada,
yanzu kam takai qarshe.....takai maqura,enought is enough....ta dauki iya abinda
zata iya dauka,ya isa haka!,ya isa!......
Ire iren wadan nan tunane tunane su ta dinga yi har suka qaraso gida,wanda
ko tsaiwa a biya mai napep din kudinsa batayi ba,batasan ya suka qarke da hafsat
ba.
Ji tayi an rungumeta,hajjanta ce
"Me haka zahra'u?,ki nutsu mana,kita maimaita Allahumma ajirni fi musibaty,wa
akhlifni kairan min ha" da muryar kuka ta kama addu'ar tana ta maimaitawa har ta
soma samun nutsuwa,don haka hajjan ta zaunar da ita gefan gadon tana shafa bayanta
kadan kadan tana tayata nanata addu'ar.
*_wajen daya kamata a tsaya mu fafata kan wanda yafi iya yaudara cikin samarin nan
uku yayi,da kuma matakin daya kamata budurwa ta dauka idan ta samu kanta cikin irin
wannan situation din,idan kuna da buqata ku sanar min domin bude grp musamman
saboda haka,karku manta,dama munce akwai fafatawa da tattaunawa kan mai zafi kan
kowanne littafi,ma'assalam_*
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: 16
Kallo daya ta yiwa sawwaman tasan cewa lallai tasha kuka itama ba na wasa
ba,gaba daya idanunta sun tasa har lebunanta,zahran ta qarasa a hankali ta zauna
gefan sawwaman
"Ashe kema kinsan abdulyasar?" Kai ta iya jinjinawa kawai ba tare da tace komai
ba,saboda wano ciwo dake taso mata a qirji
"Ashe bani kadai bace?....bani kadai ya yiwa haka ba?" Maganar da taja hankalin
zahra kenan da ta daga kai ta dubi sawwaman,kallon da take mata yake nuna tana da
buqatar qarin bayani
"Abdul yayimin alqawarin aure....infact ma yau sati daya da tura magabatansa
gidanmu,amma abun mamaki sai nakejin yau sati biyu dakai kudinsa wajen wata
walida....baya ga haka ashe kema...." Hannu ta dagawa sawwama murmushin takaici na
fita daga fuskar zahran,a take wasu kalamai da abdul din yake yawan gaya mata suka
dinga dawo mata aka tar kamar a sannan yake furta mata su
"Duk duniya akwai wata bayan ke?,duk duniya akwai wata diya mace data isa ta rabani
dake?,me kike fargaba a kaina?,akwai wata mace data isa na bata lokacina akanta na
tafi zance wajenta idan bake ba.....zahra duk kyan mace....duk ajinta....duk
gayunta saidai tabi bayanki"
"Duk abinda kika fada haka ne....hakane sawwama" kuka sawwaman ta fashe dashi,wanda
da alama zallar baqinciki da bacin rai yake cin zuciyarta
"Abdul ya cuceni,ya zalunceni...abdul..." Da sauri hajja data fito tace
"Kiy shuru karki sake cewa komai,kuyi haquri ku masa addu'ar Allah ya yafe masa
kuskuren daya tafka" miqewa zahra tayi ta koma daki don ba zata iya ci gaba da
tattauna wannan maganar ba,hajja da hafsat sune suka sallami sawwama.
Kwanyarta tana iya tuna mata sanda abdulyasar din yake musanyan waya da
ita,ya aje mata wayarsa yacw ta bashi tata aga wanda yafi gaskiya a cikinsu,aga
wanda saurayi ko budurwa zasu kira,ashe a sannan wala'alla sabon layi kenan yake
sakawa?,ko layin da ba'a sanshi dashi ba?.
Sannan tana iya tuna sanda yakan rufeta da masifa cikin zallar kishi,yana
cin alwashin duk randa yaga wani ya kulata ko ta tsaya dashi,ba shakka saiya masa
diban karen mahaukaciya ya sadashi da qasa ya take wuyansa,kome zai faru indai a
kanta ne saidai ya faru,tana iya tuna sanda yake tsaidata ya rakata makaranta ko
wani guri da kansa,tana iya tuna sanda fafur ya hanata shiga kasuwa,ashe duk bogi
ce?,qarya ce?,ashe bayan ita hadda sawwama wadda yakai magabatansa?,anya ko
magabatan gaske ne bana haya bane?,anya kuwa bana bogi bane?,saboda babu iyayen
arziqin da zasuje maka maganar aure wannan satin,wani satin kuma suje maka gidan su
wata da saninsu,to bayan ita da sawwama mata nawa ya yaudara?,wannan Allah ne kawai
masani.
Cikin daren ta yiwa kanta da kanta fada,ta gayawa kanta cewa da batasan
abdulyasar ba,kafinshi kuma wasu sun yaudareta,ta kuma ci gaba da rayuwarta ba tare
da komai ya sameta koya sauya ba,hakanan a yanzun ma zataci gaba da rayuwa babu
shi,zata dora daga inda ta tsaya,ba zata bari damuwar wanda baisan da damuwarta ta
dameta ba,damuwar wanda baya doron duniyar ma gaba daya,kai koda yana
raye.....dukkan namijin da zai miki haka bai cancanci ki damu kanki saboda shi
ba,saboda ya nunawa duniya cewa u r a zero behind decimal point,baki da wani amfani
a tare dashi,keda babu duka daya,don me zaki damu da irin wadan nan?,me yasa irin
wannan namijin zaki dora damuwarki a kanshi?,a daren,a kuma sannan ta yiwa kanta
alaqawarin cire dukkan damuwar wani abun banza namijin daya yaudareta,ta kuma
dasawa kanta takunkumin tserewa soyayya da kuma nisantarta bakin iyawarta,har sai
taga abinda ya turewa buzu nadi,ko kuma abinda alqalamin qaddararta ya rubuta ya
tabbata.
Godiya ta yiwa ummin sannan ta baro sashen,tun a ranar sata soma addu'o'in
ta dinga jin sukuni da nutsuwa yana ratsata,ta sake jin zuciyarta wasai kuma
fes,haqiqa ubangiji yayi gaskiya da yace ku saurara,da ambaton Allah kawai zukata
suke samun nutsuwa,lallai babu abinda yakai ambaton ubangiji sanya nutsuwa a
zuciyar mai damuwa.
Zaune take cikin dakin kwanan dalibai wanda ya zama mallakinsu ita da
hindatu batula da jannah,yayin da nadiya da farida suke daki daya daura da nasu
suda wasu mutum biyun,to amma idan baka sani ba zaka zaci dukkansu daki guda
suke,saboda kusan komai a nan dakinsu zahran sukeyi,hatta da abinci daya sukeyi,duk
da basi fiya ma girma abinci ba,saidai suyo takeaway,idan kaga girkakken abinci to
aikin zahra ne,sau tari sukan mata qorafin tana walahar da kanta da wani girki,ta
bari kawai suyo takeaway suci,takan ce
"Ni ban saba bafa,abincin da zaka girka da kanka yafi albarka,sannan kayan anincin
da nazo dasu daga gida saina jibgesu su lalace?,ko kuma na maidasu gida idan an
tambayeni nace qawaye suna siya min ina ci?" To su dinma idan ta dafa kowa dafifi
yake wajen ci,saboda ita din ba baya bace wajen iya girki.
Kamar yau dinma dakin nasu cike yake da hayaniyar 'yammata,kasancewar suna
cikin ranakun qarshen mako ne,kuma wannan karon kusan dukkaninsu basuje gida
weekend ba,ita zahra saboda CA da zasu fara,kuma a satin zasuyi kusan gudan
hudu,shi yasa taga gwara ta zauna waje guda tayi karatu sosai.
Yau dinma ita ta dafa musu abincin,kowa yaci ya qoshi,da suka kammala saita
taja takardunta da system dinta saman gadonta ta barsu nan tsakar dakin kan carfet
din da suka malale dakin dashi
"Yar allazi boko" taji su suna tsokanarta,bata kulasu ba sai murmushi kawai datayi
taci gaba da karatunta,batason ta tsaya tankasu su dauke mata hankalinta,suma
sukanyi karatun,amma saidai baiko kai nata ba,sukance sun gaji basu iyawa,da sun
taba iya yadda zasu iya suke ajewa su shiga sabgarsu.
Yanzun ma hira suke masu charting nayi,harda qawayen su batula daga wani
dakin,ana tsaka da haka taji mardiyya qawae farida ta luqa ashar
"Ferry....zoki gani....maza maza zo kiga" da sauri farida ta aje tata wayar ta
matso kusa da mardiyya,saita zare glass din fuskarta,da qarfi ta furta
"What.....muhsin ne fa,wata fa naga ya dora yana furta kalaman soyayya a qasan pic
dinta,kan bala'i" saita fada tana dauko wayarta da sauri tana duba wajen status
dinta
"Zo kiga,ni bai nuna ajerin nawa status din ba,babu status dinsa" dariya wata
rabi'ah dake zaune kusa dasu tayi,ta tashi ta zauna tana cewa
"Wai baku gane meke faruwa bane,ai na taba gaya miki farida tun kwanaki kika qi
yarda,kinzo kina wani jin kin isa kinkai,wai waye ya gaya miki ma cewa a yanzu ana
cika baki kan namiji?,ai wannan lokacin ya wuce,lokacin cika baki da alfahari,da
basu amanna dari bisa dari.....everybody listen to me" ta fada tana gyara zamanta
sosai a tsakiyarsu tare da miqe qafafunta,hakanan maganar da rabi'ah din ta soma
fada ta dauki hankalin zahra,bata sauke littafin hannunta ba amma hankalinta na
kanta
"Luggar mazan yanzu.....zasu iya yin budurwa dari ko dubu ta watsapp....kuma zasu
iya dora hotonta a status...amma kuma,duk sanda zasu dora hoton daya,tofa zasu cire
dukkan sauran su sanyasu a jerin wadanda a ranar ba zasuga status dinsu ba,ba zasu
ciresu ba har sai hoton yayi disappering,ko kuma ranar naki pic din zasu saka,saisu
cilla waccar cikin inda suka ciroki ke kuma a fito dake,donki gani,kiji dadi,ki
kuma qara amanna dasu...so dukka abun bugene,duk ta yadda suka biyo miki ki bi musu
ta haka,kada ku saurara kunji....kuyita musu yadda suke muku kawai,dakun samu na
dauka ku dauka ku watsar dasu" ta qarasa fada tana sheqewa da dariya.
Maganar status din ta baiwa zahra mamaki,wato kullum sabon salo suke
fiddawa?,saidai fatan samun shiriya,amma kuma zancan gogayya da samari barkatai sam
shawarar batayi mata ba,saita tabe bakinta kawai taci gaba da karatunta,gefe guda
hayaniyarsu tana cika mata kunne,da Allah ya taimaketa zuwa wani lokaci suka fara
raguwa da kadan kadan,har dakin ya rage daga ita sai hindatu wadda ta haye gado ta
kwanta zata dan rage bacci a cewarta kafin ta tashi tayi karatu.
Turo qofar dakin da aka sakeyi da qarfi yasa zahra dagowa tana fatan ba
sune suka sake dawowa ba,basu din bane yanzun jannah ce,sanye da straight gown da
hill shoes,sai qaramar hand bag da qaramin mayafi data nade wuyanta dashi,kusan
shigarta kenan wanda kusan kullum sai sunyi rigima da zahra akan haka.
Yau din fuskarta sam babu alamun walwala,gefan gadonta ta samu ta zube tana
zare mayafin kanta cikin masifa take magana
"Ni hisham zaiwa haka?,ni zaiwa wannan akuyancin?" Hindatu dake kwance bacci ya
fara dibarta ta daga kai tana dubanta
"Ke kuma meya hadaki da hisham din naki yau?" Iska ta furzar daga bakinta sannan ta
zame 'yar hular dake kanta ta sabule takalminta ta zauna sosai saman gadon tana
harde hannayenta
"Yau ni hisham zai fito qarara yacemin nayi haquri da maganar aurenmu....shi
matarsa ta gida ta isheshi" sosai hindatun ta tashi ta zauna
"Hisham din da kansa da bakinsa?" Kai ta jinjina cikin tsananin jin zafi
"Shi din fa....shi yasa ya kasa zuwa ya gaida dad,ko mami ma danace yaje cewa yayi
wasu shirye shirye yakeson ya kammala tukunna...."dauke kanta hindatu tayi zuwa
sashen da zahra ke zaune
"Kinji fa zahra?" Saita ture littafinta gefe
"Naji" ta fada tana saukowa daga saman gadonta,ta daura dankwali sannan ta fita
zuwa toilet,mintina kadan ta dawo ta samesu suna tattaunawa,ta koma bakin gadonta
ta zauna sannan ta dubi jannah.
"A inda kullum muke fada dake kenan fadan gaskiya....ita kuma gaskiya daci
gareta,hakanan fure take bata 'ya'ya,ita kuma rayuwa duk abinda ka shuka shi zaka
girba,ba zaka taba shuka qaya ba kace inibi kakeson cira,jannah.....na dade ina
miki nuni da waye hisham,illa da dafin dake tattare dashi,hisham yayi amfani da son
da kike masa yayi fooling naki,ya kuma yi amfani da damarsa a kanki,a yanzu ya gaji
dake ne shi yasa ya fito miki ta wannan hanyar kai tsaye,don ya ajjiyeki ya kuma
lalubi wata mai tsautsayin me qaramin tunanin....kiyi haquri da harsh word da nake
amfani dasu a kanki,kawai ni duk inda gaskiya irin wannan tazo gittawa ta gabana
saina fadeta,abinda yasa na kira dame qaramin tunani shine....babu ta yadda wanda
yakeson ya aureki ki zame masa uwar yaransa kuma mace ta gari abar alfahari ya
daukeki cikin motarsa yana yawo dake,ya daukeki ba cikin gidanku ba,ba gaban
iyayenki ba,ku hadu a wani waje ya saki gaban mota kuna yawo,yaje ya killace
'yarsa,yaje ya killace matarsa,yaje ya killace mamarsa....amma kefa?,saboda baki da
wani daraja,baki da wani matsayi da za'a baki,shi yasa bai dauki hakan a bakin
komai ba,daga sanda wanda yace miki yana son aurenki yazo miki da magana kan
matarsa qazama ce,matarsa bata iya soyayya ba,matarsa yar qauye ce,kece kika iya
komai,matarsa ta gaza ta kowanne fanni,amma kuma ko yaushe yana nanuqe dake,yana
fasa miki kai,ta wani sashen kuma a dabarance yana qoqarin ku dinga hulda ta hada
jiki romance da kissess amma kuma ko sau daya bai taba tunanin kiyi aure ba,ke koda
ya taba tunanin hakan ko furtawa toba shakka na yaudara ne,daga sannan kuma kin
samu babbar matsala,a haka da kike yawo dashi janna,cikin irin wannan shigar da
wannan rayuwar kike tunanin zaya daukeki yakai gidansa a matsayin matar aure?,me
zaya killace?,me zai burgeshi har yakai ga aikata hakan?,bakayi haka bama da
sautayi a wannan zamanin ya kuka qarke dashi bare ace kinyi?,ni na isheki manuniya
da ishara,kafin kice hisham ya yaudareki ya kamata ki fara cewa kin yaudari
kanki,idan maganata ta miki zafi jannah kiyi haquri"sosai taga yadda jikinta yayi
masifar sanyi,saita kasa cewa komai,sai dogon nazari da tunani data fada,bama ita
kadai ba har hindatu dake kwance.
Cikin sati sunyi CA sa yawa kamar yadda ta zata tun wancan satin,to satin
gaba ma kusan akwai sauran tarin karatuttuka,hakan ya sanya kowacce ta sake haqura
da zuwa gida weekend,saidai kuma sun shirya zuwa daya daga cikin masaukan baqi
hotel don su huta a can a cewarsu.
Sanda suke shirya tafiyar zahra na zaune tana jinsu bata tanka ba,tadai
yanke idan sun tafin gida zata wuce ko kwana guda ne ta rage ta dawo.
Saida suka gama hayaniyar yadda zasu gudanar da ranakun qarshen makon
sannan suka soma raguwa sannan hindatu ta iso kusa da zahra ta zauna
"Amini....ko sau daya baki taba karar binmu bafa" kallonta tayi
"Ko sha'awa wajen banayi,me zai kaini nikam,kuma ina mamakin yadda kuka maida wajen
kamar ba'a bakin komai ba zuwanshi" dariya sosai hindatu tayi
"Kinga,mufa mutanenmu ne suka yiwa wajen mummunan fassara,amma a qa'ida wajene da
iyali ma suke iya zuwa su kama daki suyi dukka iya kwanakin da sukeso,su huta daga
hayaniyar gida data jama'a,ni kusan duk qarshen wata bazan manta ba kafin nakai
haka,sannan abubuwa basu yiwa daddy yawa ba muna zuwa muyi kwana biyu haka ko
uku,ba wani abu bane me muni,saidai idan mutum dama da mummunar niyyarsa yaje,don
Allah kizo muje wannan karon,sau daya dai tak" kai zahran ta girgiza
"Naji bayananki,amma am sorry bazan iya zuwa ba hindatu saikun dawo" ranta ta bata
da alamun bataji dadi ba
"Shikenan....tunda baki yarda dani ba,komai kika fadamin ina qoqarin yi dabi,bana
tsallakewa shawararki saboda nina aminta dake....na gode,dama sunatamin dariyar
cewa ni kadai na damu dake,yau na gasgata hakan" saita sauka daga gefan gadon ta
koma nata tana hada kayan da zasu je dasu.
Ganin yadda harta gama hada kayan bata kalleta ba dakin shuru yasa taji
duk babu dadi,ba kaifi hindatun tana daukar duka shawarin zahran da qoqarin ganin
tayi abinda zahran keso,da gaske taji haushinta kenan sosai,har ta isa bakin qofa
zata fita zahran ta kira sunanta
"Haushi kikaji kenan?" Kafada ta daga
"Saboda me?,bayan baki yarda dani ba?,akanme zan takuraki kiyi abinda baki niyya
ba" kaita kada tana murmushi
"Zanje....shikenan ko?" Cikin murna ta dawo
"Na gode sosai....ina mai tabbatar miki zakiji dadin tafiyar da zamuyi,gobe da
kanki zaki ce muje" murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba.
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: 17
Ƙarfe hudu na yammacin ranar suka dunguma su shidda cikin motar gidansu
hindatun suka tafi.
Ɗaya daga cikin tsadaddu kuma qawatattun hotel sukayi masauki,suka kama daki
guda babba wanda zai ishesu a wadace,itakam tana zaune daga gefe tana kallonsu
yadda suka sake tamkar suna cikin gida ko cikin makaranta,ita kam har cikin ranta
bata jin wani walwala ko karsashi ko kuma wani jin dadin zuwa wajen,sai take ji
acikin zuciyarta duka wani irin babu dadi,sai takejin kamar ta aikata wani mummunan
abu mara kyau,haka kawai takejin babu dadi har qasan ranta,har sai da farida ta
ankara da haka
"Ki sake mana haba zahra,mu kadai ne fa a dakin,babu wanda yake shigo mana ko ya
isa ya shigo" murmushi kawai ta musu,sai tabi lafiyar lafiyayyen gadon dake dakin
tayi kwanciyarta akai,don kafin su fito tasha karatu sosai,tana son ta huta kafin
ta sake dora wani,don ta taho da dukka litattafanta,har suna tsokanarta cewa ba
hutawa zataje yi ba kenan,tunda ba zata bar qwaqwalwarta ta huta ba.
Suna ta hayaniya da walwalarsu har zuwa sanda akayi knocking qofar aka
kawo musu abincin dare,kowa ya fara diban nasa duk da cewa akwai sauran lokaci
kafin ma ayi sallar magariba din,hindatu ce ta dubi zahran
"Zahra....ga abinci,ki sauko kowa nacin nasa" kaita kada tana hamma
"Kai a'ah,sai an idar da sallah" daga haka ta sake gyara kwanciyarta,tun tana jin
hirarrakinsu sama sama har ta fara daina jiyosu,babu jimawa kuwa bacci mai nauyi ya
debeta.
Sanda ta farka hindatu ce kawai tayi saura a dakin,tana niyyar saukowa daga
gadon tana duba agogo,qarfe bakwai da ashirin na dare,inda Allah ya taimaketa tana
hutun sallah
"Duka ina suka shiga?" Ta jefawa hindatun tambayar wadda ke tsaye gaban madubi tana
gyara sumarta da mayukan gyaran kai
"Duk sun fice,amma sun kusa dawowa"
"Fita kuma?,nan duka bai ishesu yawo ba?" Ta sake tambayar hindatun
"Nan kusa da inda muke nefa,aka bude wani sabon wajen cin abinci daxun,to na wani
abokin farida ne,shine ya gayyacesu" baki kawai ta tabe,ba shakka duk inda wayewa
tayi yawa matsala ce,su a wajensun wannan normal ne,ba wani abu bane,amma a asalin
tarbiyyar malam bahaushe wannan din mummunar illa ce,saita miqe ta shiga toilet ta
canza pad ta kuma daura alwala ta dawo ta zauna bakin gadon tana karanto azkar
dinta na maraice da bata samu damar karantowa ba,tana yi tana duban hindatu daketa
shiri da alama fita zatayi,batace mata komai ba har sai data ga ta daga waya tayi
magana na 'yan mintuna ta aje,ta dauki mayafinta tana yafawa
"Ina kuma zaki kema?" Waiwaya tayi tana duban zahran
"Waya zamuje siya nida mudassir a glass show,minti talatin ta isa munje mun dawo"
sosai zahran ta hade fuska
"Yanzu kina ganin kamata ce ki fita da saurayi takwas saura na dare siyan
waya?,cikin motarsa daga ke saishi?"
"Babu komai qawata kada ki damu,ko a gida dana sanarwa mommy muke tafiya" maganar
ta ratsata,batasan illar boko xallah ba sai yanxu,gaba daya duk wani abu daya
kamata a kalleshi amatsayin abun qyama suba hakan bane a wajensu saboda rashin
tasirin ilimin addini,saita miqe ta isa inda hindatun ke tsaye.
"Hindatu,a koda yaushe inason ki dinga tuna cewa kina rayuwa ne a qasar
hausa,ina son ki dinga tuna cewa qa'ida da kwaikwayo kan tafarkin addini shine gaba
da komai,na miki uzurin rashin tashi kan irin nawa bigiren,wala'alla har a
zuciyarki ba komai bane hakan,amma idan baki sani ba bari na gaya miki
illar.....akwai babbar illa a wajen 'ya mace ko ince ganganci wajen shiga motar
wani da namiji,nasha maimaita miki wannan maganar....abinda yasa na nace mata
shine,shiga motar da namiji ki yadda ya tuqaki shine mafarin komai,shine sila da
dalili na faruwar komai,komai zai iya faruwa,idan nace komai ciki harda rasa
budurcinki gaba daya....." Idanu hindatun ta qwalalo
"Ki yarda dani qawa.....wallahi ban taba zina ba,ban taba bada kaina ba" murmushi
zahra tayi ta dafa kafadarta
"Haba hindatu....ta yaya zan miki wannan mummunan qazafin,amma idan kin kubuta daga
zargina sauran mutane fa,kin isa ki wanke kanki?,akwai abubuwan da zaka dinga
aikatawa da zasu iya ja maka mummunan zargi da zato daga mutane,zargi mai wuyar
wanke kai,irin wannan rayuwar,ku kunsan bakwa wani mummunan aikin,amma shaidar da
mutane zasu muku itace ku bana gari bane,idan kin shiga motarsa komai bai faru ba
zaki iya kubuta daga riqe miki hannu da zaiyi?,zaki iya kare kanki daga yunqurin
miki kiss ko runguma?,idan yaso cutar dake kin isa ki bawa kanki kariya?,sannan
kome ya miki baki da hujja,laifinki ne,ke kika kai kanki hindatu" sosai jikinta
yayi sanyi,ta daga kai tana duban zahran
"Gaskiya kika gayamin qawata,na kuma fahimta maganarki,sannan na gode miki qwarai
da gaske,ban dauki hakan a wata babbar tawaya ba sai da kika nusashsheni,in sha
Allah irin hakan ba zata sake faruwa ba" ta qarashe maganar tana cire
mayafinta,sannan ta dauki wayarta ta tura masa tex ta koma ta zauna.
Daya daga cikin halayen hindatun da suke burge zahra kenan,sauqin kai da
kuma saurin daukan shawara.
Tana zama saiga sauran suna shigowa,kafin kace me sun sake hautsina dakin
"Kai....kai jama'a,ku bakwa gajiya dan Allah da hayaniya?" Inji zahra da suka hana
kunnuwanta sakat,dariya suka saka gaba daya jannah tace
"Kamar yadda baki gajiya da karatu ba" saita saki murmushi kawai tana gyada
kai,tasan me hali dai bazai fasa halinsa ba.
Washegari a daki dukka suka yini a tare,saidai da yammaci lis suka shirya
dukkansu domin zuwa siyayyan kayayyakin amfani da kuma kallon wani sabon hausa film
da za'a haska a film house cinema dake ado bayero mall.
Fir tace ba zata bisu ba,hakanan idan suka jima basu dawo ba saidai suzo
suga ta tafi,basu ji dadi ba,saboda sunce ba jimawa zasuyi ba,hakanan bai kyautu su
barta ita kadai ba,amma tace sam itadai sai sun dawo,hasalima akwai sauran
karatunta da bata qarashe ba,haka suka shirya suke fice a motar jannah.
A qalla ta shafe kusan minti ashirin tsaye a haka har duhu yadan fara yi
sannan taji tsaiwar ta soma isarta,saita janye idanunta da niyyar juyawa tabar
wajen,saidai caraf idanun nata suka fada kansa.
Saidai duk wadda ta kira din tana shiga tana kuma ringing amma ba'a
dagawa,babu kuma amsa,haka ta qaraci kiransu gaba dayansu babu wanda ya daga,zuwa
sannan tara da rabi na dare agogo ke nuna mata,ga yunwa tana ji,duk da sun gaya
mata taje tayi order din abinci a reception idan tana da buqata kowanne iri ne,to
batason fita shi yasa bata karbo ba,ga wayar dakinsun daxu ta samu matsala bare ta
kira daga daki a kawo mata,zuwa yanzu kuma yunwa takeji bata wasa ba,hakan yasa ya
zame mata tilas ta fita ta karbo din kenan,saita sake tashi ta gyara yafenta ta
kuma fito daga dakin.
Cikin tuqi mai cike da nutsuwa ya sako kai farfajiyar hotel din,hannunsa
daya yana tuqin dashi,yayin da daya hannun yake amsa wayar cikin nuna girmamawa ga
ubangidansa da gazo gani cikin hotel din,wanda ganawa ce ta sirri da zasuyi dashi
gabanin taron qasa sa za'a gabatar na dukka ma'aikatan tsaro na qasa,kama daga
sojojin sama dana qasa dana ruwa gaba daya,yanzun yana amsar direction ne na daki
da inda zai ganshi,har ya qaraso wurin ajiyar motoci sannan ya ida wayar yana mai
cewa
"Yes sir!" Sannan ya sauke wayar daga kunnenshi ya kasheta gaba daya,ya janyo
aljihun motar ya zurata,sannan ya zauna na wasu mintuna yana karantar yanayin wajen
a matsayinsa na qwararren jami'in tsaro,sai daya tabbatar komai na wajen yayi masa
sannan ya bude murfin motar ya fito.
Duk wanda ya kalleshi saiya kuma,duk da cewa babu wata alama da zata nuna
maka yanayin aikinsa,amma shigar da yayi da wasu shegun qananun kaya masu kyau da
aji sun amsheshi,takawa yake zuwa reception cikin wata tafiya me cike da kuzari
mazantaka da kuma karsashi,hannunsa daya riqe da key din motarsa,daya hannun kuma
wata 'yar mitsitsiyar waya ce da yake iya rumtseta a tafin hannunsa guda daya.
Yana magana da daya daga cikin receptionist din sanda ta qarasa saukowa,a
nutse itama ta tsaya saitin daya ma'aikacin wajen tana gaya masa abinda ya sauko da
ita.
Ido hudu sukayi,cikin matuqar tsoro da razani taja baya tana kallon cikin
idanunsa,yayin da shima ya kafeta da idanun yana mata wani kallo daya sanya taji
kamar an maida qafafunta sama ne kanta kuma a qasa,tashin hankali da gigita suka
bayyana tun daga zuciyarta zuwa saman fuskarta.
_IDAN KAJI GANGAMI DA LABARI....! INA MASU ZUBIN ADASHEN DA BA RANAR DAUKA NA DATA?
_
_TO KU MARMATSO KUJI, KU KUMA SHARE HAWAYEN KU, MUNZO MUKU DA SABBIN TSARE TSARE NA
DATA, WADDA KOWA ZAI IYA SAYA DAI DAI KARFIN SA. A FARASHI MAI RAHUSA_
_TSAYA KUJI, A RANO NET ZAKA IYA ZAMA RESELLER KO WHOLESALER KAI MA, EH ZAKA/KI IYA
ZAMA MA SAYAR DA DATA A FARASHIN SARI MUKE BAYARWA, KAI/KI KAFA KASUWANCIN KU KUMA.
DA KUDI KALILAN._
_MUNA KUMA SAYARWA AKAN ‘DAI DAYA, KOWANE NETWORK MUNA SAYARDA DATA PLAN DINSA AKAN
KUDI KALILAN, MASU FARASHIN SARA KUWA MA KU KUDIN BAI KAI HAKA BAMA_
_AIRTEL_
_9MOBILE/ETISALAT_
_MTN_
_GLO_
_DUK MUNA SAYARDA TSARIN DATA DINSU. KAMAR MISALI MTN MUNA SAYARDA 1GB.24MB AKAN
FARASHIN NERA 300 KUMA YANA KAIWA WATA DAYA, GWARGWADON YADDA KAKE AMFANI DA DATA,
2GB 600, 3GB 900!!_
_DUKA WADANNAN TSARIN DATA DAMA NA SAURAN LAYIKA MUNA SAYRWA AKAN FARASHI MAI
RAHUSA, WANDA KOWA ZAI IYA YIN TSARIN DAI DAI ALJIHUN SA_
_Ranonet.com.ng_
_GA SITE DINMU NAN DAKE YANAR GIZO, KAI TSAYE ZAKI/KA IYA SIYAN NAKA TA NAN. _
_KO A TUNTUBE MU TA NAMBAR TARHON MU: +234 803 081 1300/+234 808 540 5215_
_KYAU, INGANCI, RAHUSA, ADADE ANA YAWO A YANAR GIZO SAI RANO NET._
_RANO NET..!!!!_
_____________________________
*_BA ZATA!_*
_Baya da qura_
Tana tsaka da sallah sau biyu inna gaje na leqowa dakin da zummae ganin ta
idar din?,a zuwa na uku ne ta sameta tana zaman tahiya,saita tsaya tana dakon
zahran har zuwa sanda ta kammala ta kuma yi sallama.
"Uwar masu gida anason ganinki a falo" inna gajen ta fada tana duban
zahra,saita saki addu'ar da takeyi tadan ja tsaki
"Anty uwani ko?,ni sam banison zuwanta gidan nan wallahi,haka kawai baka taka mata
ba baka zubar mata ba ta saka maka idanu" kai inna gaje ta kada
"Ba ita bace,hajja ce....da alhaji babba" haka kawai taji wani faduwar gaba da
batasan meye dalilinta ba,haka nan sai jikinta yayi sanyi
"Tom,ina zuwa" ta fada tana qarasa addu'o'inta ta shafa sannan ta miqe.
Tun kafin ta qaraso gabanta ke dukan uku uku saboda fuskokin data hanga
cikin falon,abba babba abba yusuf,abban tsakiya haidar da kuma hajja,sai umminta
daga gefe
"La haula wala quwwata illa billah" shine abinda take maimaitawa,take dukka
qafafunta sukayi wani irin sanyi kamar ba zasu iya daukar gangar jikinta ba,hakan
yasanya tafiyarta ta koma slow harta qaraso cikin falon.
Cikin girmamawa kamar kowanne lokaci ta gaidasu,suka amsa mata fuskar
kowannne babu komai a samanta,ko kuma ace ba zaka karanto wani sauyin yanayi
tattare da ita ba.
Itama ummin nata nata kan yana qasa,bata zargin diyarta ko daya,saidai tana
da tarin fargaba,tana tsoron zamani,tana tsoron qawaye,tana tsoron gurbacewar
muhalli,tana sane da cewa a yanzun tarbiyya ta zama wani abu mai tsananin tsada
wanda sai wajen wane da wane ake samunta,tsadar tata taki jallin da hirar wanda ya
rabauta da samunta ake,farautar masu ita ake,tsada suke da kuma wuyar
samu,tattalinta kuma abune mai hatsarin gaske,wanda idan ka tsira da ita ba tare da
wani yayi nasarar fauce maka ita ba to abun ayi maka sambarka ne,tana fargabar
yadda diyarta ta kafa tarihin soma karatun gaba da secondry cikin gidan ya zamana
ta kafa wani tarihin na daban,tarihin da bata fata ko burin samuwarsa,a kullum
kwanan duniya dama takan kwana da tashi cikin fargaba,koda yaushe burinta shine
diyarta ya zamana tana gidan nata mijin kamar yadda aka tsara ko kuma aka gina
gidan akan hakan,wannan zai fiye mata kwanciyar hankali fiye da ace tana can tana
karatu,tunda jarrabawa ta soma samun diyartata bata taba samun nutsuwa ko sukuni na
sakan ba,idanunta basa barci,zuciyarta bata hutawa,bakinta baya gajiya da yi mata
addu'a ako da yaushe,a kullum takan wayi gari cike da buri da kuma fatan Allah ya
fiddo mata da miji na gari,koda kuwa zai zama silar datsewar karatunta,a yanzu kam
a wannan bigiren....tana jin ya kamata ta motsa,tana jin ya kamata ta magantu,tana
jin ya kamata tayi wani abu da zai sama mata nutsuwa ko yaya ne.
Sai da suka gama fadan sannan sukayi mata jan kunne da gargadi mai
qarfi,saida suka gama gaba daya sa'annan umminta da tunda aka fara batace komai ba
tayi magana
"Hajja.....yaya(haka suke kiran abba babba tun tale tale,dukka matan qannen nasa
"Na'am halima muna saurarenki"
"Yaya dukkan fada da qoqarin da kukeyi akan zahra'u duk da cewa diyarku ce.....amma
ya zama dole ga duk wanda ya gani ya yaba muku...idanma har akwai abinda yafi yabo
din kun cancanci samunsa,a yau sau daya tak ina neman wata alfarma....alfarma guda
daya da nake fata da kuma burin xan sameta daga gareku" shuru ya dan ratsa kafin
abba babban ya bude baki yace
Fadeta halima....in sha Allah ba zata gagara ba"yayi furucin tare da yaqinin haka
yake cikin zuciyar mahaifiyarsa hajja,domin halima takai mace,duk inda mutum mai
tsananin kawaici kan diyoyin cikinsa da sanin ya kamata yakai takai,suna da
tabbacin tunda har yau ta iya buda baki tayi magana to ba shakka lamarin ba qarami
bane a zuciyarta.
Cikin wani irin amo da salo daya tabbatarwa da duk wanda ke dakin da gaske
hajja ke magana,da gaske hukunci take zartawa mai zubin KAIFI DAYA!,MAGANA
DAYA!,cikin salo na umarni kai tsaye tace
"Kin wuce ki nema alfarma akan diyarki halimatu,baki ma taba nema ba sai yau,kuma
zaki samu da izinin Allah,zahra ba zata koma makaranta ba saida igiyar aurenta
akanta....zahra zata koma makaranta cikin satin nan a matsayin matar aure....a
matsayin matar Aliyyu,rana ita yau nakeson inga zahra'u a matsayin matar aliyyu!"
Takai qarshen zancan tana sauke idanunta kan abba babba,wanda hakan ke nufin cewa
tana da buqatar ya zartar da umarnin data bayar kenan.
Da wani irin sauri itama zahran ta miqe tayi dakinta saboda ji da tayi ta
kasa zaman falon,kamar idan ta tashi tabar musu falon ta tserewa wannan mummunan
hukunci na hajjan,amma data shiga dakin saita kasa zaune ta kasa tsaye,kamar wata
zararriya haka ta dinga jin kwanyarta na yamutsawa,ta dinga leqensu abban tana so
suyi subar falon,tana da tabbacin barazana ce kawai hajjan keyi amma zata
janye,tasan cewa da taje ta kwantar da kai ta lallabata shikenan za'a wuce
wajen,duk da tafi kowa sanin halin hajjan tunda tafi sauran zama da ita,sau tari
tana da kafiya da zafi kan wasu abubuwan,wanda idan ta juye maka zaka tsammaci ba
ita bace.
Kansa yake gayawa cewa babu wani abu da zai faru sansa yake dosar nahiyar
da dakunansu suke,dukkan abinda hajjan ta fada barazana ce kawai saboda tana
tunanin ya qetare abinda ta gaya masa,tana so ne ta kaɗashi kawai saboda
haka,saidai can can qasan ranshi ya kasa samun nutsuwar da yakeson samawa kansa,ya
kasa gamsuwa da dukka kalaman kwantar da hankali da zuciyarsa ke jero masa,ya kasa
daukar kowanne daga ciki,indai har kuwa hajja na nufin abinda ta fada da gaskene
har cikin zuciyarta....to a karon farko wani mummunan al'amari zai iya faruwa wanda
shi kansa bai sanshi ba,bai kuma san qarshensa ba.
Har ya saka key zai bude gefen nashi wayarsa ta dauki tsuwwa,tun kafin ya
ciro ya saki tsaki,don sai yaji qarar wayar kamar wani qarin damuwa ce cikin
kwanyarsa,ya zaro yana duba mai kiran,general hamza ne,babu uzuri matuqar kira daga
wajen irinsu ne,don haka ya daga,ya gaidashi cikin girmamawa kamar yadda ya saba
"Abu biyu yasa nayi kiranka aliyyu.....na farko akwai wani gagarumin al'amari daya
tunkaroka,wanda kyanta idan ka samu dama ka sameni saboda kaji kai tsaye daga
bakina.....na biyu kuma batu ne na auratayya" saiya dan saki murmushi
"Ina farincikin shaida maka cewa ina saka ran nan gaba kadan xamu hada zuri'a,zamu
hada jini da familynka....,duka dai idan ka samu dama kazo na ganka" kusan bai
fahimci dukka maganganunsa ba,ya sani kuma a yanzun yadda yake jinsa ba fahimtar
zaiyi ba,don haka kawai yace
"Sir...in sha Allah zan shigo gobe da safe" godiya general ya yiwa aliyyun kamar ba
shine samansa ba,sannan ya katse wayar......
_(MASARAUTAR KAMSHI)_
_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma
da ingataccen had’i yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa..._
_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_
_carpet spray_
_air-fresheners_
_scented pebbles_
_body sprays_
_oil perfumes_
_Perfumes_
_kabbasa_
_burners_
_coal igniter_
_tong_
_kasko_
_kujerar tsugunno_
_english coal_
_dilke&halwa set_
_scented body mist_
_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata ba, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura
kayayyakin su ko’ina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram:
_@yerwaincense_and_more. Ko _Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta
number su: ___08095215215/09044191709! _
_(MASARAUTAR KAMSHI)_
_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma
da ingataccen had’i yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa..._
_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_
_carpet spray_
_air-fresheners_
_scented pebbles_
_body sprays_
_oil perfumes_
_Perfumes_
_kabbasa_
_burners_
_coal igniter_
_tong_
_kasko_
_kujerar tsugunno_
_english coal_
_dilke&halwa set_
_scented body mist_
_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata ba, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura
kayayyakin su ko’ina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram:
_@yerwaincense_and_more. Ko _Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta
number su: ___08095215215/09044191709! _
Da wani irin zafi ya soma takawa inda take tsayen,tamkar ma ya manta da cewa
gap din dake tsakaninsu ba wani me yawa bane,itama sai tayi yunqurin ja da
baya,wanda hakan yasa yakai mata cafka da zafinsa,ya samu nasarar riqe singalalin
hannunta,abinda ya sake rudata kenan ta sake daburcewa,tsoro ya kuma cikata,yayin
daya bude baki cikin wata tsawa
"Me ya kawoki nan!" Ya fada da dakakkiyar murya mai qarfin amo da sauti,irin ta
sojan daya saba karba da bada umarni a fagen daga.
Yadda dai daikun mutane suka juyo suna kallonsu ya ankarar dashi,saiya
sake mata hannun nata da sauri,fuskarsa na gauraye da wani irin bacin rai,ya zare
muqullim motar daya maida aljihunsa ya cilla mata,ya kuwa sauka saman qafafunta,duk
da taji zafin amma ba shine a gabanta ba,tashin hankalin dake a gaba take
hararowa,tasan cewa abinda zai biyo baha din ba dan qarami bane,ta kuma fahimta me
yake nufi,don haka ga duqa ta dauki key din ta fara takawa tana ficewa daga wajen
kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki.
Sai data fice sannan yabi bayanta ba tare daya tsaya amsar number dakin
da yake nema din ba,tana gaba yana bayanta amma ba zaka zaci tare suke ba har ta
isa bakin motar,daidai lokacin matashin da tun dazun yake dawafi cikin hotel din
yana nemanta tare da burin sake ganinta ya hangeta,don haka da sauri sauri ya sauko
a nufosu idanunshi a kansu,yana ganin sanda haidar ya fisge muqullin ya buda motar
ta shiga baya ta zauna.
Yana zare key din yaji an dafe hannunsa,ya daga kai a nutse don ganin
waye
"Me haka kake?,zaka kama yarinya ka rufe cikin mota saboda me?" Wani banzan kallo
haidar din ya kafeshi dashi,cikin ransa yana tambayar kansa da kansa shi din
waye?,sosai ransa ke tafasa baiso ya huce masa laifin da bashi ya aikata ba,amma
kuma yanajin wani sabon bacin ran na taso masa dangane da rainin hankalin da
yakeson zuwar masa dashi,shi waye nata da zai qalubalanceshi kan hakan?,ya santa
ne?,shi ya kawota?,ko tare suka zo?.
Zare key din yayi ba tare daya sake bi ta kansa koya dubeshi ba,ya juya ya
soma takawa zaibar wajen saurayin ya mara masa baya yana ci gaba da cewa
"Malam ka budeta nace tun kafin ka gano kuskurenka.....bakasan waye ni ba ko?" Ya
fada cikin zafi dason nuna nashi qarfin qwanjin.
Wani irin juyowa haidar din yayi a zafafe har hana take masa rabin qafa da
ingarman takalminsa
"Idan kaci gaba da bina kana min wannan ɓaɓatun sai na saka kayi nadama kai da
banzan matsayinka,kuma zaka gane kuskuren aikatamin hakan kafin ni na gane nawa
kuskuren,stay awa frm me tun ban rugurguza kwanyarka" tabbas ya hangi wani strong
abu cikin idanunsa,ya kuma hangi yadda yake furta maganar bilhaqqi,ya kuma tabbatar
ba'a banza yake magana kan yarinyar with confidence haka ba,amma a amtsayin da
mahaifinsa keda shi a nigeria yafi qarfin wani da baisan ma ko waye ba ya gaya masa
magana irin haka ya qyale ba,don haka zai jira yaga yadda za'ayi ya fita daga hotel
din ya kulle 'yar mutane cikin mota
"Zan gani ta yadda zaka fita daga wannan ginin" ya furta sanda haidar ke komawa
zuwa ciki,sai daya sake bi ta reception aka gaya masa dakin sannan ya wuce.
Saida Aliyyun ya soma shan lemon sannan suka soma maganar daya sanya ya
kirashin,general hamza adamu gusau kenan,mutum mai kirki qwarai da tausayin na qasa
dashi,kusan shi ya zama kamar role model na aliyyu,saboda yadda yake da hazaqa da
gaskiya riqon amana da aiki tuquru,yana son aliyyu sosai,hakanan yana
mu'amalantarsa kamar dan cikinsa,saboda yadda Aliyyun keda jajircewa sadaukantaka
gaskiya riqon amana da rashin tsoro,duk wani abu na ci gaba yakanyi qoqarin kawo
aliyyun ya sakashi agaba,tun matsayinsa baikai wajen bama,hakan ya sanya cikin
qaramin lokaci ya dinga samun qarin girma har zuwa matsayin da aliyyun yake kai a
yanzun,yana samun kulawa da horaswa ta musamman daga wajen general hamza din,hakan
yasa Aliyyun ya zama gagara badau,kuma qwararren soja daya iya aikinsa ya kuma san
me yakeyi,dalili kenan da yasa su kansu sukeji dashi,domin kamar sun horeshi ne
yazo ya kuma fisu qwarewa da sanin dabarun aiki kala daban daban,don haka ko ame
akace akwai haidar din a ciki basa haufi.
Daga kai aliyyu yayi daga duba wani map da daddy ya bashi kamar yadda yake
kiransa yana amsa sallamar,idanunsa ya sauka kan saurayin,sun gane juna fes,sai
kowanne ya daure fuskarsa,aliyyun yaci gaba da duba map din saurayin kuma ya qaraso
ciki lokacin da daddy hamza ke cewa
"Daga ina haka?,kusan awanni biyu?" Shafo kansa yayi yana cewa
"Am sorry dad....wani abune ya tsaidani,but am back ai" kai ya jinjina yana nuna
masa haidar
"Da daya yarona nan,Aliyyu mas'ood dabo" da sauri ya cira kai yana duban
aliyyun,saboda koda fuskarshi boyayya ce to sunansa sananne ne a kunnuwa mutane
ciki harda shi,bare ya jima yana jin sunan a bakin baban nasa,da kuma yadda yake ji
da haidar din
"Ku gaisa mana haisam" yayi maganar yana maida kallonsa ga aliyyun,wanda ya aje
takardar hannunsa saboda girmamawa ga daddyn ya miqe tsaye,yayin da haisam din
shima ya tako inda aliyyun yake ya miqa masa hannu,shima miqa masa yayi sukayi
musabaha,murya can qasa haisam din yace
"Nice to meet you!" Kai kawai haidar din ya kada masa yana zame hannunsa daga na
haisam din ya koma ya zauna.
"Ka ganshi nan,yaqi aikin soja,yafison kasuwanci" inji daddy yana nuna
haisam da baki,fuskar aliyyu ce kawai tadan motsa alamun murmushi yayi,sam
hankalinsa shi bai wajen,Ya qagauta ma su gama maganar da zasuyin yabar wajen.
Sai daya qara kusan wata awa dayan sannan general ya sallameshi,ya miqe
ya sara mishi ya qame sannan yamiqa masa hannu sukayi musabaha,ya dubi haisam
"Ka raka dan uwanka haisam zuwa mota,kwayi musayar lambobin waya ko?"general ya
fada bayan sun gama sallama da aliyyu
"Ok daddy"ya fada yana miqewa,ya gyara zaman shirt din jikinsa yana bin bayan
aliyyu.
Yadan masa rata amma ya dage ya cimmasa,ya tsaya daga gefan kadarsa,saidai
duk da tsahonsa ashe aliyyun ya zartashi a tsaho,duk da yayi masa kallon nashi
tsahon yafi nasa,ashe cika da murjewar jiki da haidar din ya fishi yasa yayi
tunanin ya zarta tsahonsa
"Yaronmu kake ashe?,sai kabi a hankali ko?" Haisam ya fada yana duban haidar ta
gefan ido.
Cak haidar din ya tsaya,ya zube hannayensa cikin aljihun wandonsa yana dan
fidda wani murmushi na gefan baki,tsahon sakan biyar sannan ya waiwayo sosai yana
duban haisam din,sai daya nuna hanyar da suka baro da hannu sannan yace
"Wancan da muka baro....girmansa nada yawa a dunun haidar....banda haka daka
fahimci cewa ko jimina ta saka kanta a tabo...ba za'a kira kaza ba,amma duk da
hakan zan gaya maka wani abu guda daya wataqila yayi maka amfani.....yaro tashi ka
nemi suna....karka raba kanka da kowa,zaifi maka kyau da cikakken alfahari ka
shaidawa duniya kai tsaye cewa kaine wane wane kamar yadda kullum nake alfahari da
cewa nine Aliyyu mas'ud dabo....bawai ka cewa duniya kaine ɗan general hamza tahir
ba" saiya murza yatsunsa saman fuskar haisam sannan ya qara da cewa
"Ka kiyayi shiga gonar haidar ta irin wannan sigar.....i repeat my self....ka
kiyayi shiga gonar haidar" daga haka ya juya yaci gaba da tafiya ya barshi nan a
tsaye.
Maganganun haidar din sun masa ciwo sosai,yana son ya nuna masa nasu qarfin
ikon amma abu daya ke masa shamaki,yarinyar daya sanya cikin mota ya kulle,wanda
tunda ya ganta yaji nan duniya ya samu matar aure,baisan alaqar dake tsakaninsu da
ita ba,yana tsoron kada yaje ya bata rawarshi da tsalle,don dai yasan tabbas ba
shakka baya ga macen bariki,babu wanda zaiwa macen da bai isa da ita haka ba ta
bishi ta kuma yi biyayya,amma koma meye zaibi a sannu ya bincika,saboda haka ya
nufi tashi.motar da sassarfa ya bude ya shiga,yayi ready yana jiran yaga tashin
motar aliyyun don ya mara masa baya.
Duk da rashin mashiga da mafitar iska cikin motar amma a cure take waje
daya,duk da gumin daya gama jiqeta saboda tsabar tunanin data fada yasa sam batajin
jiqewar,tunanin mafita da makomarta take,harta hango kanta a gabansu abba
tsakiyarsu suna tuhumarta meya kaita hotel,da wanne baki zata kare kanta?,wanne
irin wawanci da dolanci haka ta aikata?,me yasa?,me yasa?,haka take tuhumar
kanta,hankalinta a wani matuqar tashe.
Sanda taji yana bude qofar sai da hantar cikinta ta kada,wani matsanancin
tsoronsa da bata taba jin irinsa ba ya rufar mata,tana nan a yadda take har zuwa
sanda ya bude motar ya shiga,ya maidata ya rufe sannan ya tada ita ba tare da yace
mata kanzil ba,abinda bata taba tsammata ba,tana jiran taji hukunci ko wata magana
daga bakinsa amma saidai tunda suka fara tafiya har suka isa gidan babu abinda yace
da ita.
"Fita!" Ya fada cikin daka tsawa data sanyata kama murfin motar ta fito da
hanzari,cikin gudu gudu sauri sauri tayi sassan hajja,saidai tana gab da shiga
sukayi karo da anty uwani,taja da baya da sauri,haka itama anty uwanin,mace guda
daya tilo da halayyarta kan zahran ta bayyana,tana matuqar adawa da yadda hajjan
kewa zahran,kulawa qauna da soyayya da take nuna mata,ko dama can macace mai
fada,masifaffiya ce ita din,ita 'yace ga qanwar hajjan,tayi aure tana da yara
hudu,uku maza sai mace guda daya autarta suwaiba,wanda itama ta dauki son duniya ta
dorawa suwaiban,ji take sosai da ita,mijin nata ya rasu,koda kuma bayan rasuwar
tasa bata sake wani auren ba.
"Me haka ke kuma kamar wadda aka biyo?" Ta fada cikin masifa tana qare mata
kallo
"Ina kwana yakumbo" ta fada kamar yadda suka saba gaya mata,ko amsarta bata tsaya
ji ba ta qara wuta zuwa ciki,sai anty uwanin ta bita da kallo ta kuma fara masifa
"Eyeee....ni zaki gaisar a haka?,lallai yarinyar nan iskancinki kullum qara gaba
yake,koda yake kina da daurn gindi ne shibyasa,amma zamu hadu dake bari naje na
dawo" ta fada tana buga cinya gami da yin gaba.
Sam bata kula da umminta dake falon hajjan ba sai data isa gaban
hajja,saboda abune baqo a wajenta,ba kasafai ta saba ganinta din ba
"Lafiya?" Hajjan ta jefa mata tambayar tana duban qwayar idanunta,saboda yadda ta
ganta kamar a birkice,yayin da ummin tata itama hankalinta gaba daya yake kan
zahran a fakaice,don a zahiri ba zaka ce hankalin nata yana kanta ba.
Ko kafin tace komai haidar yayi sallama,a nutse yake takowa zuwa cikin
falon,yana qoqarin rage zafi da radadi da yake ji daga cikin qirjinsa zuwa
maqoshinsa,kallo daya ummin ta yiwa fuskarsa tasan ba lafiya ba,don idanunsa nakan
hajjan da zahran,hakan ya sanya ta miqe don basu waje,duk da can qasan zuciyarta
hakanan ya cika da zulumi da fargaba,sai taji batason tafiya,amma saita tanqwara
zuciyarta ta duqa ta dauki carbinta ta fice ba tare da sun ankara bama.
Tana barin cikin falon taji ta kasa sake daga qafarta,abinda bata taba
yiba kaf tsahon rayuwarta ta tsaya sauraren zancan wasu koda kuwa ya shafeta,amma a
yau din sai taji tabbas tana son jin me ya faru?,wanda jikinta ya bata kan zahra
ne,don ba haka ta saba zuwa gida weekend ba.
Saiya juya kawai yaci gaba da takawar,hajjan nada wani irin girma da qima a
idanunsa,amma yana jin sam hukuncin bai kwanta masa a rai ba,saidai kodon saboda
girmanta da matsayinta bazai iya tsayawa yayi ja'inja da ita ba,a haka ya fice ba
tare daya sake cewa komai ba.
************
Kwana uku da dawowartata amma sam hajja taqi tsaiwa ta saurareta ko taji
bayaninta,wanda hakan yayi mugun daga mata hankali,don hajjan itace last chance
dinta,tana da yaqinin koda kowa yaqi saurarenta,koda kowa yaqi yarda da ita zata
samu dukkan wadan nan abubuwa daga wajen hajjan tata.
Cikin kwana ukun ta rame ta fada saboda fargaba,sai a rana ta ukun hajjan
ta tsaya da qyar ta saurari bayaninta,ta yarda da ita ta kuma gamsu,saidai tasha
fada da masifa daga wajen hajjan irin wadda bata taba yi mata irinsa ba,duka bai
damu zahra ba,tunda ta samu abinda takeso,sai data gama fadanta tsaf ta miqe sannan
tace cikin dari dari da tsoron amsar da zata bata
"To hajja makaranta,anata CA bana nan" wani kallo mai kama da harara tayi mata
"Saiki jira kiji abinda yayanku zaice,don shurun da yayi kan zancan bazan sake
tilastashi kan makomar makarantarki ba"
"Sai kace shine uban kowa cikin gidan nan?,koshi ya haifi kowa?" Abinda zahra keson
fada kenan,amma tasan fadin hakan shi zai sake dagula komai,bata ma isa tace din
ba,haka taja bakinta tasa masa zip ta zuge ta zubawa sarautar Allah ido,cike da
fargaba kada ta rasa abubuwa masu muhimmanci acan makaranta.
Tun randa ta dawo a daren hindatu ta nemeta basu ganta ba,washegari tazo
gidan,ta gaya mata lafiya lau,kada ta damu karsu nemeta,zata nemeta da kanta.
Tunda hajjan ta fita take kwance tana saqa tana warwara kan yadda lamarin
zai warware mata cikin sauqi ba tare da wata matsalar ga sake sawo kai ba,tunda
tana fatan wannan ta mutu,a haka har bacci yayi nasarar yin awon gaba da ita.
*_ABINDA KA SHUKA_*
A nutse take tafiya kan hanyarta zuwa gida,tun daga nesa take hango mutum
biyu,daya a tsugunne daya a tsaye bisa saman kansa,haka taci gaba da tahowa tana
matsar inda suke harta qaraso dab dasu,sai a sannan taga fuskokin mutum biyun
sosai.
Firgigit ta farka daga baccin daya dauketa din,ambaton sunan Allah ta shiga
yi tana tunawa daya bayan daya dukkan abinda ya faru cikin mafarkin,a yanayin da
taga abdulyasar din yana cikin damuwa babu ko shakka,saita miqe ta soma cire kayan
jikinta ta shiga bandaki tayi wanka ta fito ta shirya,har a sannan mafarkin na
maqale cikin ranta,saboda haka koda ta fito falo ta zuba abinci tana ci hajja ta
soma baiwa labari.
"Zai iya yiwuwa haqqinku ke tambayarsa,ki yafe masa idan kinsan a baya baki
yafe masa ba" baki zahran ta tabe
"Ni na yafe masa mana hajja,yaji da haqqin sauran da bansan adadinsu ba,da marasa
zuciyar tausayi da zasu kasa mancewa bare su yafe masa".
Tana kammalawa tace bari taje wajen umminta,don tunda tazo bata je wajenta
din ba,saidai yanayin yaddata amsheta,da yadda ta amsa gaisuwarta ta ya daga mata
hankali ya bata mamaki,ta kuma shiga wasu wasin anya kuwa ba wani abu taji kan case
din daya dawo da ita gida ba?,tunda haidar din mutuminta ne,to amma ita kanta tun
ranar bata sake ganin haidar din ba,asalima kamar taji suna waya da hajja na masa
fatan alkhairi kamar ma tafiya yayi wani waje,wannan abun saiya sake sanyata a
rudanin data fita,ko sansa ta koma sassan hajjan saita kasa sukuni.
*_BA ZATA!_*
_baya da ƙura_
_IDAN KAJI GANGAMI DA LABARI....! INA MASU ZUBIN ADASHEN DA BA RANAR DAUKA NA DATA?
_
_TO KU MARMATSO KUJI, KU KUMA SHARE HAWAYEN KU, MUNZO MUKU DA SABBIN TSARE TSARE NA
DATA, WADDA KOWA ZAI IYA SAYA DAI DAI KARFIN SA. A FARASHI MAI RAHUSA_
_TSAYA KUJI, A RANO NET ZAKA IYA ZAMA RESELLER KO WHOLESALER KAI MA, EH ZAKA/KI IYA
ZAMA MA SAYAR DA DATA A FARASHIN SARI MUKE BAYARWA, KAI/KI KAFA KASUWANCIN KU KUMA.
DA KUDI KALILAN._
_MUNA KUMA SAYARWA AKAN ‘DAI DAYA, KOWANE NETWORK MUNA SAYARDA DATA PLAN DINSA AKAN
KUDI KALILAN, MASU FARASHIN SARA KUWA MA KU KUDIN BAI KAI HAKA BAMA_
_AIRTEL_
_9MOBILE/ETISALAT_
_MTN_
_GLO_
_DUK MUNA SAYARDA TSARIN DATA DINSU. KAMAR MISALI MTN MUNA SAYARDA 1GB.24MB AKAN
FARASHIN NERA 300 KUMA YANA KAIWA WATA DAYA, GWARGWADON YADDA KAKE AMFANI DA DATA,
2GB 600, 3GB 900!!_
_DUKA WADANNAN TSARIN DATA DAMA NA SAURAN LAYIKA MUNA SAYRWA AKAN FARASHI MAI
RAHUSA, WANDA KOWA ZAI IYA YIN TSARIN DAI DAI ALJIHUN SA_
_Ranonet.com.ng_
_GA SITE DINMU NAN DAKE YANAR GIZO, KAI TSAYE ZAKI/KA IYA SIYAN NAKA TA NAN. _
_KO A TUNTUBE MU TA NAMBAR TARHON MU: +234 803 081 1300/+234 808 540 5215_
_KYAU, INGANCI, RAHUSA, ADADE ANA YAWO A YANAR GIZO SAI RANO NET._
_RANO NET..!!!!_
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: 20
_(MASARAUTAR KAMSHI)_
_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma
da ingataccen had’i yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa..._
_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_
_carpet spray_
_air-fresheners_
_scented pebbles_
_body sprays_
_oil perfumes_
_Perfumes_
_kabbasa_
_burners_
_coal igniter_
_tong_
_kasko_
_kujerar tsugunno_
_english coal_
_dilke&halwa set_
_scented body mist_
_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata ba, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura
kayayyakin su ko’ina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram:
_@yerwaincense_and_more. Ko _Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta
number su: ___08095215215/09044191709! _
Qaramin murmushi hajjan ta saki tana girgiza kai gami da sakin ajiyar zuciya
"Duka kwayi ku gama 'yan nema,duk tsiya mutum ai bayaqi jininsa haka ba" tayi
maganar a fili amma qasa qasa,cikin ranta tana jin sakayau,wani irin dadi da
karsashi takeji,ji take kamar ma ta janyo rana ita yau din ayi komai a wuce
wajen,don daurin auren yanzu ita shine a gabanta,koma meye ya biyo baya.
Tsaye yake a tsakiyar yalwataccen bedroom din nasa daure da towel yana
sharce ruwan wankan dake diga daga kansa zuwa sassan jikinsa dake cike da
gargasa,wata iriyar kasala yakeji sosai,banda haka tun sassafe yaso zuwa wajen
general yaji neman da yake masa,amma gashi har kusan sha daya da rabi na safe yau
din bai fita ko ina ba,duk da tarin abubuwan yi da ya shirya zaiyi a yau din.
Sai daya shafe kusan minti talatin yana shiryawa,cikin qanqanin lokaci ya
fito fes cikin wasu qananun kaya da sukayi masifar amsarsa,saidai fuskar nan a
dinke take tsaf,yakanji yanayi na bacin rai ya mamayeshi a duk sanda ya tuna
zantukan hajja na jiya,duk da cewa yana sake gayawa kansa wasa ne,kuma bazai taba
yarda ko lamuntar hajjan taci gaba da irin wannan wasan gaban yarinyar ba har yaja
masa raini a nan gaba,don bazai dauki raini ba,wayarsa da key din mota kawai ya
dauka ya fice a dakin.
Sassansu ya fara shiga ya gaida mahaifiyarsa da momy abokiyar zamanta,a can
ya samu anty uwani ta dubeshi bayan ya gaidata
"Kana nan dai zaune kana sake cinye shekarunka a gida,tun mutuwar yarinyar can
zahra'u,banda abinka ai dole haka zaka haqura,ka sake zabar wata cikin dangin
mahaifinka kuma tunda an gwada na mahaifiya,ko 'yar uwarka ma suwaiba ai baqi
zatayi ba aliyyu sai a jarraba ko?" Kallo daya ya mata ya kauda kai,tamkar ma
badashi take ba,shi dama ko can ba wani shiri suke sosai ba,don bai sakar mata
fuska,ita kuma shakkarsa take,bare kuma 'yarta da ko kallo bata isheshi ba,yana
shirin fita mama tace masa
"Idan ka dawo kazo ina son magana da kai"
"To" ya amsa mata ba tare daya kula da a dawo lafiyar da anty uwanin ke masa ba.
Yana taka sassan hajjan amma ji yake kamar ya koma kada ya shiga,saidai
bazai iya ba matuqar yana garin,da haka ya iske babban falon tsohuwar,babu kowa
ciki amma yana jiyo motsi daga kitchen,saiga jidda jikarta na fitowa hannunta riqe
da wasu farantai.
***********Kai tsaye a yau din aka masa iso cikin katafaren falon general
hamza,wanda ya tsaru qwarai,ga hotunan iyalinsa nan manne a kowanne bango na falon
nashi,wanda ya wadatu da iskar ac mai ratsa jiki.
Zaune suke su biyu tak cikin falon daga haidar din sai general,gaban
aliyyun cike yake da kayan ciye ciye iri daban daban,saidai yadda yakejin zuciyarsa
babu sukuni baijin sha'awar cin komai
"Kaci wani abu mana haidar" general ya fada yana murmushi
"Alhmdlh daddy....a qoshe nake"
"To shikenan....ba laifi" ya fada yana zaro takarda daga cikin takardun dake
gefansa,wadda akayi sealing nata cikin envalope ya miqa masa
"Wannan.....kada ka bude sai bayan kaje gida ka nutsu tukunna....yanzu magana ta
biyu zamuyi dakai" kai ya gyada bayan ya amsa takardar ya aje saman cinyarsa
"Nasan kasan haisam zuwa yanzu,don na gabatar maka dashi" kai aliyyun ya sake
gyadawa yatsunsa soke cikin na juna yana duban general gami da saurarensa
"To haisam dai ya sameni da zancan yaga wata yarinya yana sonta....ya kuma tabbatar
min da 'yar gidanku ce,duk da bansan ya akayi suka hadu kuma yasan yar gidan naku
bace,amma dai yacemin sunanta zahra" ya qarasa fada yana duban haidar.
Baiyi wani mamaki sosai ba najin zancan musamman idan ya tuna da abinda ya
faru ranar daya taso zahran zuwa gida daga hotel,saiya gyadawa general kai
"Eh....qanwata ce"murmushin farinciki general ya saki
"Ma sha Allah....muna da uwa a bakin murhu.....yanzu dai ni hamza ina nemawa yarona
auren zahra'u....duk da ban gaya maka ba....haisam ba dan cikina bane,amma baida
maraba da dana dana haifa,saboda dan qanwata ne data rasu awa daya tak bayan ta
haifeshi,so a wajen iyalina ya taso,baisan wani uba ba bayan ni,bai kuma san wata
uwa ba bayan mai dakina" kai haidar ya kada cike da gamsuwa,ta wani gefen kuma sai
yaji kamar an rage masa nauyin dake cikin zuciyarsa,saboda hango mafita da yayi ta
hanya mai sauqi kan zancan aurensa da zahra,indai har nema mata mijin ci gaba da
zuwa makaranta ne zaisa su laqa masa auren da bai shirya ba,auren da baiji ba bai
gani ba,to ga miji nan ta samu,saisu sake masa mara yayi fitsari,duk da yaron bai
wani kwanta masa ba tun a wancan ranar da sukaso samun matsala da juna,don haka da
karsashinsa yace
"Indai ni zan aurar da ita....to na bashi,saidai bazanyi saurin fadin hakan kai
tsaye ba,zan isar da saqonka zuwa garesu,kuma ina da fatan cewa za'a dace"
"Ma sha Allah,ma sha Allah" general keta fada cikin nuna farinciki,sun taba hira da
haidar din kan abinda ya shafi aikinsu,sannan haidar din ya masa sallama ya fito.
Iska haisam ya kaiwa naushi,me ya yiwa guy din nan tun karon farko ne haka
suke samun sabani?,amma koma meye zai lallaba su bashi auren zahra,kome zaiyi masa
zai iya shanyewa indai zasu bashi zahran,saboda ta gama yi masa a rayuwa,bai taba
ganin macen data masa dari bisa dari ba irin zahra'un.
A hankali yake tuqin kamar wanda baida lafiyayyen injin mota,da hannu daya
yake murza sitiyarin motar,daya hannun kuma ya aza yatsunsa saman labbansa yana dan
shafasu a hankali,yayi nisa cikin tunani da kuma lissafin yadda abubuwa zasu
kasance da yadda zai tunkari su abba da maganar haisam,shi a karan kansa cikin
idanunsu yaga gasken gasken son qulla lamarin daga garesu,amma kuma ta wani fannin
yana da hope na cewa zasu karbi zancan haisam din.
Bai dawo gida ba sai bayan sallar isha'i,sai daya fara sauke abu sufyan da
suka wuni tare a gida sannan yayo gida.
Kai tsaye sassansa ya nufa,yana shiga ya zaro wayarsa ya kira musty yace
ya sameshi daki,babu jimawa ya iso,order din abinda zaici ya bashi yayo masa a wani
gidan cin abinci dake kusa da tasu unguwar ya hada masa da key din motarsa,yana
murna ya fice kuwa da sauri,don yana masifar son aiken ya haidar din,ko banza akwai
qaruwa,baya amsar canji da sauransu.
Wani tunani da yayi shi ya sanyashi daukan wayarsa dake ajiye ya kira
mustaphan
"Ka kiratanne?"
"No yaya....yanzu dai zan shiga"
"Manta kawai,bar kiran"
"Ok to" saiya datse kiran ya ajiye wayar ya jawo tarkacen takeaway din ya soma
ci,saidai sam abincin bai masa test a baki,saboda ba sabonshi bane cin abincin waje
matuqar yana gida,don haka cin abincin bai wani nisa ba ya aje ya wanke hannunsa ya
sake daukar wayarsa ya fice zuwa sassan mahaifiyarsa.
Yana tafe zuwa sassan hajja bayan ya baro sashen mahaifiyarsa yana tuna
maganganun da suka kusa kwashe awa guda sunayi da ita,wai da gasken kenan hajja
take?,har maganar takai kunnen mamanshi?,har tana jaddada masa matsayi da girman
hajjan a idanunsu?,da cewa hukuncinta dai dai yake da hukuncinta kona
mahaifinsa?,da ire iren wannan tunanin ya isa sassan hajjan.
Sai daya jirata ta fito daga daki yana zaune yana kallon labarai a gidan
tv,fuskarta babu yabo ba fallasa ta zauna daura dashi,shima saiya bar dukkan abinda
yakeyi din ya tattara hankalinsa kanta
"Kince kina nema na,gani....amma kafin naji abinda zakice,bari na sauke nauyin saqo
da alqawarin dana dauka" ya fada yana gyara zamansa sosai cikin kujerar yana duban
hajja
"Nasan kinsan boss general hamza ko?" Kai ta gyada a nutse,idanunta kyam akan
aliyyun,saiya lumshe ido ganin ta fahimta da wuri
"Yaronsa ko ince dansa....yaga fatima yana so....dazun naje wajen mahaifin
nasa,yace na roqa masa alfarma wajenku kan a bawa dan nashi dama" daga haka ya
tsagaita yana kallon hajjan.
" ka gama soki burutsun naka?"ta tambayi haidar kai tsaye tana duban
tsakiyar idanunsa,shuru yayi yana dubanta shima ba tare da yace komai ba,yana
karantar yadda al'amarin keda qarfi da girma a zuciyarta
"Ni fatima dabo.....na isa na sanya ubanka ma ya auri duk wadda naga dama ba tare d
wani dalili ba bare kai,saboda haka ka fita daga idanuna....ka kiyaye ni
haidar,zaka hadu da fushina irin wanda baka taba ganin irinsa ba,aure ne babu
fashi,ruwanku kaida ita ku shirya,ruwanku kada ku shirya,dani da ku shege ka fasa!"
Ta fada da qarfin murya.
Kusan tare suka runtse idanu shi da zahra dake tsaye bayan labulen daya raba
dakunansu da falon
"Ya salam!" Ya furta yana jin wani ciwo a qirjinsa,ko kusa ko alama babu wani abu
da ya taba hadashi da hajja makamancin hakan,sai kawai ya miqe ya nufo qofar
fita,yayin da xahra take daki itama ta zube a qasa tana sakin sabon kuka.
Da kallo anty uwani tabi haidar sanda ya fice daga sashen hajjan,saita
saka kai ita kuma,tana ji a jikinta akwai wani abu da yake faruwa,kuma koma meye
saita jishi.
Sanda ta shiga hajjan na waya da wani dan uwanta daga can garinsu,saita
samu daya daga cikin kujerun ta zauna tana jiran hajjan ta gama
"Eh saura kwana bakwai daurin auren haidar da zahra ne......wallahi abunne ya taso
bagatatan,don Allah ashaida musu.....daurin aure ne kawai....biki sai daga baya
idan sun gama shirinsu za'ayi,don haka karsu damu,da lokacin bikin yayi za'a sanar
saiku shaida musu".
Idanu dukka anty uwani ta fidda tana zare ido,da tasan wannan mummunan
labarin zataji da babu abinda zai shigo ma da ita sassan,ai bata bari hajja dake
qoqarin kashe wayar ta kashe ba ta jefa mata tambaya
"Hajja....wai da gaske ne abinda naji yanzu kina gayawa su kawu inusa?"ajiyar
zuciya ta saki
"Wallahi uwani....na gaji da ganinsu suna yawo a gabanmu,shi babu sa'ansa....ita
babu sa'anta,naga gwara kawai ayi me gaba daya haihuwa da hanji"wani bacin rai ne
ya tasowa uwanin,da gaske dai halima ita da diyoyinta masu gata da babbar fada ce a
wajen hajja da babu wanda ke kaiwa matsayinsu?,daure ranta tayi sannan ta sake cewa
"Hakan yayi kyau....amma hajja suna son junansu kuwa?,kinsan zamanin nan.....ba'a
tilastawa yara auren da babu son ransu,suna soma ya aka kaya bare basaso" isashen
murmushin hajja ta saki tana miqe qafarta dake damunta da ciwo yau kusan kwanaki
uku kenan,bata gayawa kowa bama bare su dameta da batun zuwa asibiti a hadata da
tarin qwayoyi
"Uwani kenan.....har yanzun suna dana gaba dasu aiko?,kuma idan kasan irin
tarbiyyar daka bawa naka baka shakkar komai" kai kawai take gyadawa tana kallon
center carfet din da take kai.
Suwaiba keson haidar tamkar tayi me,hakan ya sanya anty uwani shigewa mama
sosai tsahon lokaci donta sama musu fada ta yadda komai zaizo da sauqi,tunda shi
din me son iyaye ne da qoqarin kyautata musu,sai gashi hajja ta yanke musu
hanzari,inda tasan hakan zata faru takan hajjan zata fara neman fadar,shaf ta mance
da cewa iyalin na matuqar qaunar tsohuwar,kuma suna a shirye kowanne lokaci domin
bin umarninta kamar yadda take iyakar qoqarinta itama ko yaushe don ganin
farincikin iyalin nata,tabbas ba zata bari,zata qoqarta,mai rai ai baya rasa
motsi,don haka tace
"To Allah yasa ayi damu"
"Amin amin uwani" yunqurin miqewa ta soma yi hajjan ta dubeta
"A'ah,ina kuma zaki,ki shiga ki debi abinci kici mana"
"Ina zuwa hajja,nayi mantuwa me sashen babban yaya,zan dawo yanzu naci"
"Au to....idan kin shiga kicewa hadiza(maman haidar)ta baki saqon ki kawomin"
"Toh...toh" ta fada tana ficewa daga falon da sauri.
_IDAN KAJI GANGAMI DA LABARI....! INA MASU ZUBIN ADASHEN DA BA RANAR DAUKA NA DATA?
_
_TO KU MARMATSO KUJI, KU KUMA SHARE HAWAYEN KU, MUNZO MUKU DA SABBIN TSARE TSARE NA
DATA, WADDA KOWA ZAI IYA SAYA DAI DAI KARFIN SA. A FARASHI MAI RAHUSA_
_TSAYA KUJI, A RANO NET ZAKA IYA ZAMA RESELLER KO WHOLESALER KAI MA, EH ZAKA/KI IYA
ZAMA MA SAYAR DA DATA A FARASHIN SARI MUKE BAYARWA, KAI/KI KAFA KASUWANCIN KU KUMA.
DA KUDI KALILAN._
_MUNA KUMA SAYARWA AKAN ‘DAI DAYA, KOWANE NETWORK MUNA SAYARDA DATA PLAN DINSA AKAN
KUDI KALILAN, MASU FARASHIN SARA KUWA MA KU KUDIN BAI KAI HAKA BAMA_
_AIRTEL_
_9MOBILE/ETISALAT_
_MTN_
_GLO_
_DUK MUNA SAYARDA TSARIN DATA DINSU. KAMAR MISALI MTN MUNA SAYARDA 1GB.24MB AKAN
FARASHIN NERA 300 KUMA YANA KAIWA WATA DAYA, GWARGWADON YADDA KAKE AMFANI DA DATA,
2GB 600, 3GB 900!!_
_DUKA WADANNAN TSARIN DATA DAMA NA SAURAN LAYIKA MUNA SAYRWA AKAN FARASHI MAI
RAHUSA, WANDA KOWA ZAI IYA YIN TSARIN DAI DAI ALJIHUN SA_
_Ranonet.com.ng_
_GA SITE DINMU NAN DAKE YANAR GIZO, KAI TSAYE ZAKI/KA IYA SIYAN NAKA TA NAN. _
_KO A TUNTUBE MU TA NAMBAR TARHON MU: +234 803 081 1300/+234 808 540 5215_
_KYAU, INGANCI, RAHUSA, ADADE ANA YAWO A YANAR GIZO SAI RANO NET._
_RANO NET..!!!!_
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: 21
💫💥💫💥💫💥💫💥💫💥💫
Maganin sanyi sahihi Mai fatattakar sanyi cikin kankanin lokaci na maza Dana Mata
Maganin gyaran nono domin dawo da martaban nononki hadin gargajiya da bashida illah
ajiki
Maganin kiba Wanda zaisa ki ciko dai dai misali kiyi kyau kema ki shigo cikin jerin
Mata masu aji
Maganin rage kiba da tumbi Wanda zaisa ki sace ki koma Yar dai dai abin alfaharin
kowane namiji,
Maganin matsi masu ciko da gaba da matseki Kamar Yar budurwa uwa uba zasu Baki
dandano Mai gamasar da maigida
Kalolin tsumi Sha yanzu magani yanzu dasa Mai gida ihun Dadi
Zumar mallaka
Zumar goron Tula
Zumar ridi
Zumar Mai rubutu
Hadin mallaka
Turaren mallaka
Shu'umar humra
Turaren AL'AJABI
Matan gaske
Ak 49
Sirrin tafin k'afa
Turaren fuska
Hatsabibin turare
Kwallin mallaka
Zoben mallaka
Jigidar maida tsohuwa yarinya
Maltinar Mata
Karya gado
Yajin Mata (yajin Mai ciko da mace)
Yajin maza (domin Karin k'arfi)
Akwai sirrika sosai da muke hadawa ga wacce kishiya ta addabeta ko wadda take fama
da butsarin namiji ko mafadacin namiji ko namiji Mai yawon dare ko Wanda yake bin
Mata insha Allah duk zaku samesu Kuma da yardar Allah za'asamu biyan bukata
Abubuwan da yawa gsky Wanda in nace Zan lissafasu sai nakwashi tsawon lokaci maiso
tabini PC don ganin kalolin kayan da muke dasu ,
Karku manta mace Mai gyara kanta Bata boranci taku ce maman yusuf Yar mutan sokoto
07069711327
.
Don Allah wadda Bata shirya ba tabari sai ta shirya sannan tayimun magana🙌🏼🙌🏼🙌🏼🙌🏼🙌🏼
ngd
07069711327
_____________________________
Sanda ya koma daki ma kasa zama yayi,yakai ya kawo tamkar wanda ake kadawa
kugen yaqi,cikin qanqanin lokaci idanunsa suka kada suka sauya launi.
A gaggauce ta koma sashen abban babban,ta dubi nasma dake falo yin wani
assigment da aka basu,gefanta mommy ce zaune tana duba wani dan qaramin english
novel da yake meson karance karance ce,duk da shekaru sun dan tura
"Ke ina tsohuwarki?" Ta tambayeta,saita daga kai ta dubeta da mamaki,tunda tasan
bata jima da fita daga sassan ba
"Tana dakinta" sai kawai ta wuce zuwa ciki,mummy tadan bita da kallo sannan ta
dauke kanta ta maida ga abinda take.
Tana shiga maman na fitowa daga wanka,gefe daya kuma tana sauraren wata
lacture ta dr malam umar sani fagge,gefan gadon maman ta zauna tana cewa
"Lallai hadiza,ke har kina da lokacin sauraron karatu ma ruwa yana shirin cimmaki
kina zaune dafa'an" da mamaki maman ta dubeta
"Ruwa kuma uwani?,wanne irin ruwa?"ta fada tana dakatawa daga goge jikinta da take
wanda takeson ya bushe ta shafa mai
"Hmmm.....wai dan Allah da saninki koda amincewarki za'a bawa danki auren
sangartattar yarinyar can zahra'u?"murmushi ne ya subucewa mama
"Ni wallahi tsoro kika bani ma uwani.....na sani,zahra'u ai diyata ce itama kamar
yadda yake dana,sannan kuma gwara hakan,ai ina ganin hakan shine kawai maganinsa
tunda bashi da niyyar yin aure" matsowa anty uwani tayi kamar wani na kusa dasu zai
iya jin abinda zata fada
"Amma dai hadiza don Allah banda abinki.....kaf 'yammatan dake cikin dangi tsala
tsala,dama wadanda ke yawo a gari,a rasa wadda za'a bashi sai yarinyar da kowa yazo
guduwa yake ya barta yaqi aurenta,ke ko kishin kanki dana danki bakyayi?,kin taba
tunanin meye ya hanata auruwa ma tukunna?,tunda dai banza bata kai zomo kasuwa,haka
nan ruwa baya tsami banza,sannan bakiyi tunanin idan ma hadasun akeson yi saboda
Allah da ma'aiki ba....me ya kawo wannan gaggawar?,daura aure nan da kwanaki bakwai
kamar wadda ta aikata wani abun kunya da ba'a so ya fito?,haba hadiza,kiyi tunani
mana,ga yara nan masu sonshi wadanda babu wani kokwanto a kansu?,ko suwaiba wannan
tawa bakiga yadda take son yaron nan ba,kwanaki har jiyya ta kwanta,tsabar kamun
kai da kunya ne yasa ta kasa bayyanawa".
"ƙnnnn,ai shikenan,wanda ke sonka dai shi zai hango abun cutarwa ya gaya
maka tun baikai ga cutar dakai din ba,idan kinji haushina kiyi haquri"
"A'ah wallahi,ba wani haushi uwani,haba aliyyun da inna wuron ai duka yaranki ne
kema" jin haka bata sake cewa komai ba sai kai data sanya ta fice.
Ajjiye man hannuta maman tayi ta koma ta zauna shuru na wami lokaci tana
tunani,kafin ta miqe tana fada a sarari
"Dukkan alkhiairi ubangiji ya tabbatar dashi,ya kade dukkan wani sharri,yayi mana
jagora" sai taci gaba da shiryawa abunta.
Da sallama ya shiga falon ummin,ta amsa masa tana daga zaune saman
kujera,sanye da hijabi hannunta kuma riqe da carbi tasbih counter,wanda bata rabo
dashi.
Yana gaidata su ilham suna gaidashi,ya amsa yana riqe da hannun sulaiman
"Ummi nace don Allah zan samu wani abu haka da zan iya ci?" Dan murmushi ta fitar
"Ai kuwa mutuminka muka dafa....ilham....tashi maza ki hadowa yayanku abinci"
"To" ta fada tana aje littafinta ta miqe ta mufi kitchen.
Sai daya nutsa sosai a cin abincinsa sannan ummin tace cikin yanayi na
nutsuwar nan tata
"Haidar.....dama inatason na aika ayimin kiranka" kanshi yadan daga kamar zai
dubeta saiya fasa,shima anutsen yace
"Ba wata matsala bane ko ummi?" Kaita girgiza
"Matsala ce....kuma wadda na jawo maka,inason na baka haquri ne bisa matsalar dana
ja maka,wanda inda nasan alfarmar dana nema wajen hajja sakamakon zai juye ne a
wuyanka da ban nema ba,gaba daya maganar ma da nasan zata ja maka zargi wajen hajja
da ban tadata ba....."
"Ummi....don Allah karki sake cewa komai" ya fada cikin matuqar jin nauyinta,anya
kuwa bata karanci duk abinda ke cikin zuciyarsa ba?,anya bataji maganarsu da hajja
ba,wani irin nauyinta ya dabaibayeshi,yana iya tuna tun daga zuwanta gidan a
lokacin da take amarya,yana iya tuna yadda ta riqeshi da,ɗan data tsugunna ta
haifeshi,ta nuna masa qauna sosai,irin qaunar da sai daya baro dakin mamanshi ya
dawo sassanta,bai bar sassan nata ba har sai daya kai munzali sannan ya koma sashen
da aka tanada saboda yara maza na gidan,duk da cewa a sannan shine da namiji na
farko a gidan,bayan kuma ta samu tata haihuwar babu abinda ya canza,qauna da
kulawar da take nuna masan bata ragu ba,kuma har kwanan gobe hakane....bayajin ya
kamata ko sau daya tayi wannan furuci na ban haquri agareshi komai bata masan da
tayi,bare ma babu wani laifi nata guda daya da ya gani kan lamarin gaba daya.
"Kina sani jin nauyi da jin cewa kamar kinga wani abu tattare dani dake
sakaki tantamar baki isa....komai daya faru rubutacce ne kuma ya riga ya wuce" kai
ta kada
"Nasan na isa haidar....amma lamarin aure ba qarami bane da za'a ce an yankeshi
haka katsam babu nutsuwa ko yardar zukata...."
"Ummi....don Allah kiyi shuru kada ki sake cewa komai,kiyi mana addu'a"kai ya
rausayar
"Shikenan.....ubangiji ya shiga lamarin" abu na qarshe data fada kenan.
Sanda ya koma daki sake shiga rudani yayi,sai yanzu yake hango girman
dabaibayin da hajja tayi masa,tako ta ina shidin a qulle yake bashi da wata
mafita,ya jima gaban window din daya fita waje daga dakinsa yana kaiwa hunhunsa
sassanyar iskar dake kai kawo cikin fadin duniya,kafin ya samu nasarar waftar
qanqanuwa daga yankin nutsuwa,sannan ya dawo cikin ainihin dakin.
Yakai hannu zai dauka idanunsa suka sauka kan dan qaramin hoton marigayiya
zahra dake cikin wani qawataccen frame ruwan gold,saiya fasa daukan envalope din,ya
soma kai hannunsa ya shafi fuskar hoton dake dauke da fuskar zahran,sannan qasa
qasa ya furta
"Rest in peace" ya miqa hannu ya dauki takardar ya koma saman kujera guda daya dake
dakin ya zauna ya farketa ya zaro takardar dake ciki.
Girman saqon da takardar ke dauke dashi ne ya sanyashi miqewa tsaye qyam
cikin mamaki,gefe daya kuma wani farinciki na son kunnuwa tsakiyar bacin ran da
yake ciki ya kuma shafeshi cikin mintuna qalilan.
Har ya nufi qofa da niyyara isa ga hajja da wannan albishir din sai yaja ya
tsaya saboda tuna abinda ke wakana,rasa wanda zai raba labarin dashi yayi,don haka
ya zauna ya lalubo wayarsa yana neman su abu sufyan,yana da yaqinin labarin bai
fasu ba tsakanin manya da qananun sojoji da tuni sun kirashi.
Ya dan jima suna waya dasu,kafin wani lokaci kuma sai wayoyin mutane suka
soma turereniyar shigo masa,da alama labari ya fasu,dole ya katse duk wani kira,ya
shiga cikin gida ya shaidawa mama da abba babba,amma saiya share 'yar tsohuwar bai
shiga ya gaya mata ba.
Kafin ya kwanta sai daya kira general yayi masa godiya sosai bayan ya
hadashi dasu abba sun masa tasu godiyar,jin bai tada masa batun su haisam ba yasa
ya share shima baici komai ba,saidai ya gaya masa ana buqatarsa a office saboda
wasu akwai shirye shirye na amsar office da kuma bikin qarin girman,shi a gobe zai
koma wajen aiki,ya amsa masa da yana tafe da yardar Allah.
*********washegari***********
Gaba daya fuskarta ta kode ta jeme kai kace zaman takaba takeyi,saidai
abinda ta fuskanta shine babu wanda ma ya damu da damuwarta,tun bayan da zancan ya
soma zaga gidan duk wanda ta kalla sai taga fuskarshi a sake take da walwala,bugu
da qari kuma saiga kira daga hafsat yusra yasira da salma,duk wadda ta kira tana
kiranta ne da ihun murna gami da tambayarta ya akayi haka ta faru?,baqinciki bai
iya barinta cewa komai,saidai ta datse kiran,kuma ba zata sake daga kiran su
ba,saidai suyita kira su gaji,daga qarshe saidai ta jisu suna waya da hajja daga
falo,daga nan babu me sake kiranta,da alama ta gaya musu yadda aka qulla abunne ba
bisa son ran kowannensu ba.
A kullum idan gari ya waye dama bata da wani aiki zaman daki tun daga
wancan lokacin,saidai wanka sallah da kwanciya,abinci kuwa sai taji kamar cikinta
zai hade da bayanta sannan zata dan tsakura ta koma ta kwanta.
Yauma kamar kullum,tana nan zaune gefan katifarta bayan ta gama wanka ta
saka riga da zani na atamfa hajja ta turo qofar dakin ta shigo dauke da kwanukan
abinci,wanda kullum ita da kanta ke kawo mata koda ba zata kulata ba,zata kawo mata
ta ajjiye ta juya ta fita abinta ta barta.
Yau din data dora abincin saman inda take ajjiye mata saita qaraso inda
zahran ke zaune ta zauna gefanta
"Ki zauna dai kiyita sanyawa ranki damuwa....ki hadu da wani ciwon tunda qananun
shekarunki" karon farko tun bayan zancan da hajjan tabi ta kanta harma ta tanka
ta,sai qwalla ta cika mata idanu,ta zumbura baki murya a dasashe tace
"Idan ma ciwon ya kamani aiba damuwa kikayi dani ba,kinga saina mutu kowa ma ya
huta" murmushi ne ya kunbcewa hajjan
"Au Allah....saboda na miki gata na baki dandasheshen jikana....shine zaki ce
haka?,au ashe?,sakayyar ma da zakimin kenan,maimakon ki bani danqwalelen goron
albishir?"
"Ni so nake.....haka kawai ina zamana....saboda Allah bai kawomin miji ba shine
za'ayi sadakata" ta fada tana fashewa da kuka,jikin hajjan sai yayi sanyi,saita
koma cikin seriouse dinta bayan ta dafa bayan zahran
"Zahra'u,ki tsaya ki nutsu kiji abinda zan gaya miki,na tabbatar dama da farko
zakiji babu dadi,zakiji na takuraki,zakiji ban miki adalci ba,saboda kaf cikin
'ya'yana ko jikokina babu wanda na taba yiwa irin hukuncin dana miki....amma abinda
nakeso ki sani shine,soyayya da qauna ce tasa nayi miki hakan,na tabbatar ko ba
dade ko bajima zakimin godiya,zakiji kuma dadin wannan abun dana miki,alfarma daya
nake nema a wajenki idan har na isa,idan har ina da kima da mutunci a idanunki"
shuru hajja tayi tana kallon zahra da kukanta ya tsagaita,saita dora
"Na sani cewa a yanzu baki da wani daya shiga zuciyarki bare kice na miki karan
tsaye....da wannan nake neman alfarma daga wajenki daki sassauta zuciyarki,ki cire
wannan quncin takura da takunkumin da kika sanyawa ranki,ki yi juriyar maida komai
ba komai ba....ki bawa aliyyu dama....na miki alqawarin cikin shekara daya indai ya
kasa shiga zuciyarki da kaina zan amsar miki takardarki kije ki auri dukkan wanda
yayi miki,kuma babu wanda zai tada hukuncina....abinda nakeso shine kawai ki
kwantar da hankalinki" shuru tayi tana nazarin maganar hajjan tare da
kokwanto,saidai cikin hikima da dabara irin tata ta tsofaffi ta samu tadan sauketa
kadan,aka samu canji duk da ba wani me yawa bane.
_hello assalamu alaikum zafafa fans,kuyi haquri da jina shuru jiya,bana jin
dadine,yauma da qyar na hada wannan,so idan kun jini shuru gobe kuyimin uzuri,amma
in sha Allah ma zan qoqarta,kuci gaba dai dayi mana uzuri kamar yadda kuka saba,mu
din 'yan adam ne kamar kowa,mun gode da yadda kuke fahimtar damuwoyinmu_🙏🏽🙏🏽🙏🏽🥰🥰🥰
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: 22
_*LAVENDER RESTAURANT..*_
_(Palace of mouthwatering food/delicacies)_
_IDAN KUKAJI GANGAMI DA LABARI, INA MASU SON INDA ZASU SAMU INGATACCEN ABINCI MAI
DADI DA LAGWADA? KAI BA ANAN MUKA TSAYA BA, INA SABBIN AMARE? MAMAs, YAYYU? DA
KANNEN MU MASU SON KOYAN GIRKUNAN YAN GAYU NA KASAR NIJERIYA DA KETARE?_
_*TO KU MATSO...! AT LAVENDER RESTAURANT GOTS YOU COVERED. ABINCIN KASASHE DA DAMA
MUKE KOYARWA,,COME LETS UPGRADE YOUR FOOD TIME TABLE, MATSO KUSA YAR UWA GA DAMA DA
ZAKI CANZA YANAYIN ABINCIN GIDAN KI, KOWA YASAN IYA SARRAFA ABINCI NA TAKA RAWAR
GANI A GIDAJEN AURE. KAI KO BUDURWA CE INDE KIN IYA GIRKI ZAKIGA KOWA YANA HABA
HABE DAKE.._*
_*ZA’A FARA CLASSES RANAR 14/10/2021. WATO SHA HUDU GA WATAN OKTOBAR DA MUKA SHIGA
YAU._*
_*GIRKE GIRKE GUDA 30😫😨AKAN DUBU 40 KAWAI, HARDA BONUS NA SNACKS, DESSERTS,
TRADITIONAL AND MODERN DRINK, GARGALIYA DA ZAMANI🥂WATA DAYA CHAS ZA’AYI ANA KOYAN
GIRKE GIRKEN. _*
_*Nigeria @ 61 _*
_*COOKING COMPETITION!!!_*
_*from lavender Catering ina masu son koyon girki ga dama zaku shiga gasarmu ta
girki bayan kunyi register damu akan 10k,wanda yazo na 1zai shiga ajin mu free
hade da wasu prize din na 2 da na 3 kuma zasu bayar da rabin kudine da wasu prize
suma saura kuwa zasu ayi musu ragin 5% da wasu prize wannan gasa zamu yita ranar
lahadi ne 3/10/21 zamu rufe registration na gasar ranar asabar_*
_*LAVENDER RESTAURANT: NA GARIN KANO, CLASSES DIN AKWAI PRACTICAL AND ONLINE CLASS
GA WANDA KE NESA_*
________________________________
Cikin kwanakin ikon Allah kawai zahra take kallo,yadda aka tada shirye shiryen
daurin aure gadan gadan,saiga dinkuna hajjan tayi mata na shaddodi da atamfofi,ko
kallon inda suke ita dai batayi ba,saboda ta fuskanci kamar ma kowa goyon bayan
abun yakeyi.
Ta fannin aliyyu kuwa shiryen shiryen qarin girma da za'a masa ya janye
hankalinsa sosai,don har wani lokacima yakan sha'afa da batun idan ba wani bane
daga gida ya tada masa zancan,baya ma samun zama sosai,wani lokacima ba'a gidan ko
a garin yake kwana ba.
Ana ya gobe daurin aure saiga baqi sun fara cika gidan,tun zahra na daukar
abun me sauqi harta fahimci babba ne,saiga su yusra ma duka sun hallara,salma ta
soma mata zancan itako ko qunshi da gyaran kai mana ayi mata a ranar dai.
Yadda ta rufe ido tayi ma salman tas da duk wanda ya goyi bayan zancan
salman ya tabbatar musu da cewa lallai a wuya zahran take,ta dinga balbala masifa
da bala'i har sai da kowa ya dare ya barta,ta buga tsaki ta sakawa dakinta key tayi
kwanciyarta,bata sake bude dakin ba har zuwa washegari da safe,data tashi tana jin
yunwa,sassan hajjan kuma akwai baqi,sa'annan haushin kowa takeji,batason yiwa kowa
magana bare ta buqaci abinci a wajensa,don haka ta zurma hijabinta babu wanka ko
kwalliya tattare da ita,kamar ba ita ake shirin daurawa aure ba tayi sassan
umminta.
Abinda ya sake daure mata kai haushi ya cikata shine samun ummin nata da
tayi tayi wanka abinta ta shirya cikin dinkin shadda sabuwa gal,daga ita har ilham
da yusuf da sulaiman dukka iri daya.
Can dinma akwai baqi,duk da baikai cikar sassan hajja ba,saita gaisa dasu
suna kiran amarya amarya,ba wanda ta tankawa,abincinma ji tayi ya fice mata a
ka,don haka ta koma da baya zuwa sassan hajjan.
Mutane ta tarar yanxun a dakin nata ciki harda suwaiba,koma bayan dazu
data fita babu kowa a ciki,hasina dake zaune gefan katifarta ce tace
"Ah,hala sabani mukayi,ummi tacemin kina nan,na shigo kuma ban tadda ki ba"
"Eh" ta amsa a taqaice tana isa bakin madubi ta dauki brush da maclien tayi
bandaki,da hanzari hasina ta miqe tabi bayanta cikin bandakin.
Tana zama saiga anty alawiyya ta shigo itama dauke da qaramin yaronta
"Ina amaryar?" Ta tambaya suwaiba,saita yatsina fuska ba tare data amsa ba,hasina
dake danna waya ta dago kai
"Tana wanka anty alawiyya"
"Toh....bari ina zuwa" ta fadi tana fita.
Kusan minti ashirin sannan zahran ta fito,wanda yayi dai dai da dawowar
anty alawiyya,ta nema duka mutanen dakin su bata waje,sai hasina ce kawai ta rage.
Fada ta soma yiwa zahran sosai kan yadda ta maida kanta,ta kuma tilasta
mata ta shirya,hakanan tana baqin rai da dacin rai ta shirya din,abinda yadan rage
mata baqincikin shine zuwan hindatu,wanda bata tsammaci zuwan nata ba,tana bata
labarin yadda suke kula da komai nata na makaranta,harda su CA da suke mata,wanda
taji dadin hakan,saidai hindatun ta tambayeta dama zahran tasan aure zatayi shi
yasa bata kula kowanne namiji,amma kuma koda wasa bata taba gayawa wani ko bashi
labarin auren nata ba,harda ita karan kanta,duk da yadda suke?
"Uhmmm" kawai ta iya cewa hindatun ba tare data bata amsa ba.
Su ukune rak cikin katafaren dakin hotel din da suka sauka a daren
jiya,haidar dake kwance rigingine hannunsa riqe da waya yana dannawa,sai Fahad dake
zaune a gefansa yana latsa system din dake gabanshi.
Turo qofar akayi aka shigo,saif ne dauke da wata baqar leda dake dauke da
tambarin wani kamfanin dinke dinke daya shahara a nigeria,inda suke saida kaya
ready made kowanne iri.
Ganin fahad xai jiqa musu aiki yasa saif ya koreshi waje
"Ka bamu waje da Allah malam" ya fada yana hade rai,saiya tattara tarkacensa ya
fita yana fadin
"Ana so ana kaiwa kasuwa"
"Ka gaya masa....ni ba abokin wasansa bane wallahi ya shiga hankalinsa....if not
zai raina kansa"
"Calm down mana aboki"cewar saif yana zama kusa dashi
"Ni ina mamakin wannan abun da kakeyi....banda abunka ai an wuce wannan qarnin,kada
fa ka manta koda baka so kana da right na qara auren wadda kakeso,a yanzu bayan ita
akwai uku a gaba ba zata tare maka komai ba,sannan kome zakayi kada ka duba hajja
mana,ka duba iyayenka da aljannarka ke qafarsu,kada kayi abinda zaka watsa musu
qasa a ido,wannan nasarar qarin girma daka samu duka sirrinta shine yadda kake
kyautata musu da binsu,kada ka watsa albarkarka akan wannan minor issue din
mana...and mamar zahran,ko yaya uwa uwace,haka ɗa ɗa ne,ko yaya tana son diyarta,ko
yaya wani abu mara dadi ya bullo akan diyarta koda ta boye a fuskarta lallai tana
jin ciwo a zuciyarta,da kanka ka gayamin matar she mean alort to you....."
"Ya isa" ya dakatar da saif,tsahon mintuna biyar sannan ya aje wayar hannunsa ya
miqe kana ya wuce bandaki kai tsaye.
Shudewar wasu qididdgaggun awanni da basu da tsaho unguwar tayi wani irin
cikar kwari na ban mamaki,dimbin jama'a masu tarin yawa suka shaida daurin auren
ALIYYU MAS'OD DABO da FATIMA SA'ID DABO bisa sadaki naira dubu dari,wanda abban
tsakiya shi ya biya lakadan.
Dashi da zahra dake cikin gida dukkansu jin sanarwar daurin auren suke
kamar a labarin tatsuniyoyi,kamar wani mafarki suke da babu dadewa zasu farka suga
ba gaske bane,don haka shi haidar dinma ana gama dauraws maimakon ya shiga cikin
gidan saiya shiga mota kawai,ya umarci drivern daya fara yawo dashi ya kaishi wani
masaukin baqi na musamman ya kama daki na kwana biyu,babu irin nema da duban da
ba'ayi masa ba babu shi babu dalilinsa,koda aka gayawa hajja cewa tayi
"Da ita data kwanta ciwo,dashi daya gudu duk ku qyale 'yan kan uba,duk zasuyi su
ware,ƴaƴan yau ne fa?,muna nan daku zasu baku mamaki,munafukan banza" haka suka
gaji suka haqura da neman nasa,tunda sunsan koma ina yaje yana sane ya tafi din
kamar yadda hajjan tace.
Tuni gidan ya zamana babu kowa sai mutanen gidan,kai kace ba'ayi wani taro
bama daya danganci biki,ta bangaren zahra tuni ta tattara auren da aka daura mata
ta aje lamarinsa gefe,ta auna ta auno bata ga ta inda zai takura ta koya zame mata
matsala ba,saidai dama da zai bata ko kuma ya zame mata tsani ko matattakala da
zata taka ta cimma burinta na qarasa karatunta da take kan gaba,baya ga haka kuma
sasan yadda zasuyi da sauran matsalolin,don dai bata manta da maganar hajja wadda
ta sake sanya mata relief a rai ba,indai har haidar din ya kasa shiga zuciyarta to
ta mata alqawarin amsar mata takardarta,maganar ma dariya take bata,don bataga ta
wata hanya da haidar din zai shiga zuciyarta ba,ta yaya ma?,yadda yake jin kanshin
nan,saidai kuma an samu arashin yadda yakeji da kansa itama dai dai take dashi,da
ire iren wadan nan tunanukan yasanya ta sawa auren nata suna MATACCE,ta kuma fara
tsara yadda zata koma makaranta abinta ba tare da wata damuwa ba.
******************
Kimanin qarfe takwas da wasu mintuna na dare,ita da hajja zaune a falon hajjan
suna taba jira,ta tanqwashe qafafunta saman kujera tana yankan farcenta da nail
cutter,ilham da husna na zaune daga gefe sun bada himma a kallo.
Kadan kadan kuma kamar daga dan nesa kadan da qofar shigowa sassan hajjan
take jiyo muryarsa,tayi tsam da ranta,tabbas shine,don haka ba tare da kowa ya lura
da abinda ta jiyo din ba ta miqe ta nufi dakinta,hajja da batasan wainar da ake
toyawa ba ta dubeta
"Ke kuma meye haka?,wanne irin tashine haka kamar wadda ake kira?"
"Ina zuwa hajja" ta bata amsa tana shigewa dakin gami da turo qofar.
Ko minti uku batayi ba kuwa ta jiyo muryar nan tasa yana sallama cikin
falon,a dake muryar take wanda hakan zai alamta maka fuskarsa na nan yadda kowa ya
santa koma fiye da haka,babu digon fara'a ko walwala kenan,saita lumshe idanunta
tana sakin tsaki,ta koma ta kwanta rigingine tana jin yadda zuciyarta ke daka.
Yana shirin xama su husna na gaidashi,ya amsa musu,duk sai suka miqe suna
barin falon,sai ya zamana daga shi sai hajjan a falo,muryarshi a dake ya soma
gaidata
"Barka da dare hajja....an yini lpy"
"Qalau muke" ta amsa masa a kaikaice
"Ka gama guje gujen naka?" Ta tambayeshi tana tsareshi da ido,dubanta yayi kafin ya
amsa mata
"Gudun me fa?...ba inda naje,kawai shiryen shiryen bikin qarin matsayin nan ne ya
sanyani gaba,yazo kuma ya hade da wannan"
"Kai ka sani,nidai ina sake jadda da maka wallahi ka fita idanuna....ka kuma kiyaye
ni,idan ba haka ba...bakai kawai ba,har tsohonka bazai ji da dadi ba" ta furta
maganar tana kanne ido gami da nunashi da yatsa,sumeshi ya shafa yana furzar da
iska
"Ya salam....to nikam hajja bansan me kikeso ba dani kuma,duk abinda kika tsara
anyishi,saura me kuma?,me ya rage?" Zamanta ta gyara sosai tana kallonshi
"Ai kafi kowa sani,tunda dai kasan cewa cikin satin nan matarka zata koma makaranta
ko?"
"Matata?" Ya tambaya yana jin kalmar wata banbarakwai,da confidence dinta ta gyada
kai
"Eh,matarka zahra'u.....kana nufin mu ko dangin uwarta ne zamu ci gaba da dawainiya
da ita?,ko bakasan haqqoqin mata akan mijinta ba na kira malami su karanta maka?"
Ta qarashe da tambaya gami da zuba mishi idanu,idanunsa kawai ya dauke daga kanta
ba tare da yace komai ba,kamar bazai magana ba sai kuma ya amsata
"Nima cikin satin nan zan koma,saboda 'yan kwanaki ya rage na karba sabon
matsayina" kafada hajjan ta daga
"Oho maka....kaika jiyo,ka fara sallamarta tukunna da dukkan abinda ya dace,idan
yaso kafi ruwa ma gudu"
"Hajja hajja" ya kira sunan nata har sau biyu,tsohuwar tana son takai masa iya
wuya,itama sai tace
"Ali...ina jinka,da magana ne?" Kai ya kada yana miqewa
"A bani abinci idan akwai"
"Zakaci iya na kwanakin dana diba maka ne kawai wlh,don bazanci gaba da aikin baban
giwa ba" ta fada kamar me qunquni,yaji me ta fada amma sai yace
"Magana kike hajja?"harara ta dalla masa,saboda ta fuskancin yanzun so yake ya
tsiro da wasan jika da kaka tsakaninsu
"ban sani ba,nace ka quce dakinka za'a kawo maka"
"Godiya nake" ya fada yana ciro wani turare daga aljihunsa ya aje gabanta,tabi
turaren da kallo kana ta raka aliyyun da ido.
Tare da inna gajen suka fito,tana dan rarraba idanu a falon ga zatonta yana
nan saboda qamshinsa daya barwa falon,sai data tabbatar baya nan sannan ta qaraso
tana sakin jikinta.
"Dauki abincin nan ki kaiwa yayanku" tace da ita tana murtuke fuska don
kada ma ta kawo qabli da ba'adi,ido tadan fiddo
"Waiya musty ko ya abubakar?"
"Zaki" hajjan ta amsa mata a taqaice,ba shiri ta nemi wajen zama gefan kujera
saboda yadda maganar taxo mata ba zata,wanne irin masifa hajja keson janyo mata
tana zaman zamanta ne?,meye hadinta da kaiwa ya aliyyu abinci?,ita kaf rayuwarta ma
zata iya tuna sau nawa ta shiga sashensa,shigarta ta qarshe ma kusa shekara
goma,don duk abinda zai kaita dakinsa bata yarda ya hada da ita,iyakarta dakinsu ya
musty,ko su dinma ba'a barinsu suje saida dalili,
"Amma hajja da kin baiwa su ilha..."
"Ban isa na aikeki ba kenan?" Ta jefa mata tambayar tana kallonta,xancan umminta ya
dawo mata,saita saita fuskarta tana girgixa kai
"A'ah ba haka nake nufi ba,bari na dauko mayafina" ta fada tana miqewa,hajjan tabi
bayanta da kallo cikin ranta tana dariya gami da cewa
"Kyayi kya gama".
Yaran gidan kusan hudu ta hadu dasu kafin takai,saidai kowa ta nemi yakai
abincin sai taga yaja baya,abun saita lura kamar hadin baki,ko suna tsoron wani
abu,tunda dai tasan yaran gidan kaf da tsananin bin na gaba dasu,koda kuwa ba wasu
shekaru masu yawa ka basu ba,hakanan basu da qiwa sam koda ga jama'ar waje bare na
cikin gidan,da haka da haka tana haduwa dasu kowa na bata uzurinshi har ta isa
kofar dakin nashi.
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: 24
*_Are you guys looking for where to buy ur skincare product @ mg's skincare is the
best plug for you🤗_*
*_Do you wish to have that flawless skin that's free of all skin prblm_*
*_Do you wnt to achieve that milky skin that turn heads wherever you go😉_*
*_Try mg's product nd I assure you you'll never use any other product except mg's
product✅_*
*_Mg's will gv you the best out of all_*
Chat:08062991549
Call:08064532391
Soap price:3k
set:11k
Follow us on
Instagram@glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare
karfe biyu na rana suka fito daga aji,sauri take tana Allah Allah ta isa
daki ta cire kayan jikinta ta samu ta watsa ruwa saboda zafi da rana,tuni ruwan
sama ya fara samuwa a wasu garuruwan kamar legos abuja da sauransu,ya zuwa sannan
kano da kaduna suma suna saka ran samun nasu ruwan saman na farko.
Tana tafe tana qiyastawa a ranta,a qalla wannan satin tanason taje gida
weakend,don tunda ta dawo bataje din ba,saboda kuma raguwar karatu da fara shirye
shiryen jarabawa tana tunanin zata dauki kwana goma kafin ta dawo,don yanzu sam ba
kasafai take jin dadin zama tare dasu hindatu ba,takatsantsan take,batason wata
matsalar ta sake kunno kai,saidai duk da haka bata fasa gaya musu gaskiya ba,kuma
alhmdlh tana ganin hasken hakan,don da yawa daga dabi'un da basu daukesu a bakin
komai ba a baya zuwa yanzu babu mafi yawa daga cikinsu.
Tana aje jakarta tana musu sannu gami da zare mayafinta,sannan ta soma
qoqarin canza kayan jikinta zuwa na wanka,hindatu ta dubeta
"Ga abincinki fa..."
"Ai hindu inajin saina dawo zanci,yanzu ya shamsu yakirani hajja ke nemana wai kuma
a airport...ko lafiya" hindun nakai lomar abinci bakinta ta amsa masa
"Lafiya mana,dadai asibiti akace shine zaki tsammaci ba qalau ba"
"Hakane" ta fadi tana sanya hijabinta gami da daukar shower gel dinta ta nufi
bandaki.
Suna tafe a mota suna taba hira,duk da yawanci duk tsokana ce yake mata
kamar yadda ya saba,kusan haka halinsa yake saidai idan ba'a hadu ba,ba yadda
batayi dashi ya gaya mata meke faruwa ba yace shima bai sani ba,yana gida aka bashi
wannan umarni,idan taje ta gani,sai tayi shuru kawai tana dan nazari a zuciyarta.
Babu jimawa suka iso filin sauka da tashin jiragen sama dake garin namu na
kanon dabo,kai tsaye ya mata jagora tana biye dashi har zuwa inda yace mata hajjan
nacan a zaune.
Tun daga nesa ta hangi hajjan,gefanta mama ce da umma matar abba yusuf,daga
daya side din kuma abba babba ne da abban tsakiya,gabanta ne yadan fadi kadan,ta
ambaci sunan Allah a ranta,sannan ta qarfafawa kanta gwiwa ta isa inda suke.
'Yar kallo kawai zahra ta koma tun daga shigarsu jirgi zuwa
saukarsu,tsoron ma da akace akanji a hawa jirgi karon farko ita bai wani dameta
ba,saboda inda zatan yafi komai damunta a ranta,ji take kamar ta rufe ido ta bude
ta ganta a makaranta.
Suna sauka tun cikin airport din abujan aka taresu,wani matashi sanye da
kakin soja ya musu jagora zuwa wata galleliyar sabuwar mota,wanda kallo daya zaka
mata kasan cewa sabuwa ce da gaske,shi ya bude musu dukka suka shiga ya shigar da
kayansu booth sannan shima ya shiga.
Gaishesu ya soma yi da tattaciyar hausarsa pure bisa dukka alamu dan arewa
ne bahaushe,yanayin girmamawarsa garesu ke nuna yasan kosu din su waye a wajen
aliyyun,saida suka gama gaisawa sannan ta yada motar suka fice,yayin da kunnuwan
zahra ke biye dasu,tana jin yadda suke hirarsu,abba babba na nuna musu wasu guraren
da ya sani cikin abujar idan sunzo wucewa ta wajen.
Wata madaidaiciyar rumfar adana motoci ya shiga ya faka motar kusa da wata
mota dake a rufe ruf,da alama ita dinma sabuwace,zaka gane hakan kota iya
tayoyinta.
"Ma sha Allah....ma sha Allah" kawai kowa ke fada,saboda yadda gidan ya tsaru
ya kuma qawatu,duk da cewa ba wani qaton gida bane,saidai yana da yalwa dai dai
misali,akwai haraba madaidaiciya wadda ke dauke da wata rumfa ta bunu da wasu irin
kujeru qasanta da teburi saboda dora kofuna da lemuka,akwai balcony mai kyau da
wasunirin kujeru guda hudu da wani irin qarfe da aka zube a cikinsa bayabga furanni
wanda ta cikinsa balcony din zaka isa falon gidan,wanda ya dauki set din kujeru
biyu sai dining area,daga daya bangaren akwai gajeran corridor wanda ke dauke da
dakunan bacci guda biyu da bandaki a tsakiyarsu,duk da kowanne daki yana da
bandaki,uwa uba kuma akwai wani spare dakin cikin falon.
Akwai ma'aikata maza guda biyu da suka tadda cikin gidan,daya shine kukun
sa,daya kuma me gyara falon gidan da bandakuna,banda bedrooms dinsa.
Dakin dake cikin balcony din nan aka budewa su hajja,yayin dasu abba babba
kuma aka bude musu na ainihin falon.
Tunda ta samu gefan qatuwar katifar dake yashe a dakin bata ce uffan ba,duk
hirar da suke tayi a tsakaninsu nata idanu,abu daya tayi shine ta shiga tayi alwala
bayan sunyi tasu,hajja kuma ta hada da watsa ruwa,don ita jin zafi gareta.
Duban zahra tayi sanda take fitowa daga bandakin,tana ware mayafinta zata
lullube jikinta don yin sallah
"Banga alamun wanka a tare dake ba,ko kina nufin yadda muka taho a haka zauna"
sosai hajjan ta bata kunya,ta saci kallon umma dake sallah kana ta maida dubanta ga
hajjan tana kyabe fuska qasa qasa tana mata qorafi
"Au....yoni Allah na tuba hadiza baquwata ce?,ki koma kiyi wanka kinjiko?"sauri
tayi kawai ta tada sallah,don tasan idan ba hakan tayi ba hajjan ba zata qyaleta
ba.
Kafin ta gama sallar umma tuni ta gama,saita tattara abun sallar ta fita
daga dakin,da alama itama nauyi takeji,hakan ya baiwa hajjan damar tsigale zahra
tasss,saidai tayi kunnen uwar shegu da hajjan,charting dinta ma take abunta,harta
gaji ta haqura.
Kafin sauran suyi wanka su huta tuni an cika teburin gidan da nau'in abinci
kala kala,cikin girmamawa da gurbatattar hausarsa yake shaida musu an gama komai,su
abincin ke jira
"To....to sannu da qoqari yaro kaji" abba babba ya fada,sai yayi murmushi cikin
girmamawa yace babu komai.
Ganin an kusa sallar la'asar sai suka yanke suyi sallah dukkansu a jam'i
sannan su zauna cin abincin,don basuga masallaci nan kusa ba,haka kuwa akayi,abban
tsakiya ya jasu sallar,suka idar sannan suka hallara kan dining din,ita dai hajja
mita ta soma kan ba zataci abinci kan teburi ba,don haka zahra ta diba mata nata ta
shimfida mata ledar cin abinci a qasa sannan ta aje mata
"Yauwa,yanzu naji batu....ke ya kika samu waje kika zauna?" Tace da zahra wadda ta
koma saman kujera ta zauna maimakon ta koma wajen cin abincin
"Na qoshi" ta amsa mata ciki ciki
"Ungo nan" ta fada tana watsa mata daquwa
"Sauko kici tun banci mutuncinki ba" soma saukowa tayi dai dai sanda qarar bude
gate din gidan ta riskesu,ba jimawa saiga biyu cikin yaran gidan suna shigowa da
kayayyakin amfani na gida suna jibgewa,suna kammalawa muryar sallamarshi ta cika
falon,hakan ya sanya zahra janye yatsunta daga abincin da take ci din,saboda ji
take kamar zai mata kallon makwadaiciya,saboda zuwa gayyar sodin da hajja ta jawo
mata,bugu da qari ta tilasta mata cin abincin gidansa,wanda ita sam bataso hakan
ba.
Saidai yadda suka gaisa a tsaitsaye ma ya nuna akan uzuri yake,don ko nuna
ya ganta cikin falon bata ga alamunsa ba akan fuskarsa,ya tambayesu zai koma sai
wajen dare zai sake shigowa,yanzu ma ya tsaida wasu abubuwanne yazo yaga isowarsu
lafiya,idan da abunda suke buqata suyi magana,addu'a sukayi masa da fatan alkhairi
ya miqe yana musu sallama cikin kuzari da hanzari irin na namijin soja,taku bibbiyu
ya juya ya fice daga falon.
Zahra ita ta gyara komai da suka bata,su abba babba suka buqaci fita gari
wajen wasu daga cikin mutanensu da suke harka dasu,saiga driver ya taso da
hanzari,motar da aka kawosu cikin gidan ya bude musu yace su shiga,oga yace duk
inda zasu ya kaisu,hakan ya musu dadi da kuma sauqi.
Cikin gida suma hirarsu suke abunsu,zahra ce kawai ta shiga daki ta kwanta
saboda gajiyar da takeji a jikinta,bata farka ba sai ana gab da sallar
magariba,koda ta leqa falo duka suna can sun daura alwalar salla,da alama su abban
ma sun dawo,ga mamakinta sai taga ya musty,idanu ta fiddo
"Kai,yaushe kazo?"
"Sanda kikayi nisa a duniyar bacci,yarinya taji hadadden gida" ya amsa yana dariya
gami da sauke hannun rigarsa dake tattare,shima da alama alwala ya daura,da idanu
ta masa nuni da mama dake wajen,dariyarsa ya gumtse yadan matso inda take
"Yaushe aka fara kunyar mama wai haka?,anya kuwa?,ba'a fara yi da danta ba?" Tabbas
da zata iya duka zata kai masa,to amma saboda ba halin hakan saita bishi da harara
shi kuma ya fice yana dariya,yayin data koma ciki itama ta soma haramar sallar.
Sai bayan sallar isha'i sannan ta shiga tayi wanka,ta dawo ta jawo jakar
kayanta ta buda.
Da ɗaya da ɗaya take duba kayan da ilham ta hada mata,gaba daya haushin
duniya ya cikata,tabbas da ilham na kusa saita mammaketa,gaba daya riga da skert
dinta wanda bata sakasu saita dora after dress akai,sannan babu bra ko pant a ciki
sai qwara daya,gefe daya taje ta debo mata kayan bacci cikin wadanda ta fara tarawa
a baya,sanda take saka ran aurenta tare da 'yan uwanta
"Lallai yarinyar nan ta rainani....Allah saita raina kanta,bari muje gida" ta fada
tana cire daya daga cikin kayan baccin doguwar riga ce wadda kadan ya rage ta isa
idon sahunta,ita kadaice me dama dama,saita dauki aron hijabi daya cikin hijaban
hajja ta zumbula bayan ta shafe jikinta da turaruka kamar yadda ta saba duk sanda
zatayi shirin bacci.
Falo ta dawo ta iskesu suna hira,mama da umma su suka fara tashi,dama tuni
abba babba suna waje,da suka shigo kuma sai suka musu sallama,don abba babba yace
ya kama musu masauki acan zasu kwana,ya rage a falon daga hajja sai zahra sai
musty,sai a sannan zahran ta samu sukunin zubo abinci ta zauna tanaci suna kwasar
dariya,saboda wata drama da ake haskawa,hajja ta dage saita fahinta abinda
akeyi,musty na fassara mata yana hadawa da yi mata tsiya suna kwasar dariya abunsu
harta gama,ta maida farantin ta dawo sukaci gaba da hirarsu.
Qarfe goma na dare aka sake bude gate din mota ta shigo,zahra dake zaune
daura hajja sai taji tasha jinin jikinta,dukkansu sunji shigowar motar,saboda haka
babu damar tace zata waske ta tashi,tilas taci gaba da zama a wajen,har zuwa sanda
muryarsa ta fara ratso falon yana amsa waya kafin isowar gangar jikinsa,hannunsa
daya dafe da waya,dayar kuma baqar leda ce dauke da tambarin wani wajen saida
abinciccika.
Musty ne ya miqe ya amsa ledar yana masa sannu da zuwa,da hannu ya amsa
masa yana qarasowa,ya samu waje ya zauna yana yin sallama da wanda suke wayar ya
kashe ya maidata aljuhun gefan wandonsa yana duban hajja bayan yadan sauke ajiyar
zuciya,da alamu a gajiye yake sosai
"Sannu da gida....ya naji gidan shuru?"
"Duk sun kwanta saura mu,babanka kuma yaqi kwana,yaa kama musu masauki sun tafi
can" goshinsa ya dafe
"Ya Allah....daya fadi hakan yakeso ai da nayi waya an basu daki"
"Wallahi....sun jima aida tafiya".
Bai rufe minti goma da shiga ba hajja ta dubi zahra tana hade rai
"Ke inna wuro....hada abinci ki kai masa" kamar zata musa saita fasa,ta miqe tana
jin kamar ta bace hajjan ta daina ganinta,ta isa bakin dining din ta hada komai
saman wani qawataccen babban tray ta durfafi dakin.
A hankali kamar wadda ta shigo sata ta tura qofar dakin,tana saka qafarta
cikin dakin ta lume cikin wani kallausan carfet daya rine da sanyi,baya ga qamshi
na musamman daya ziyarci kafofin hancinta,zata iya cewa dakinsa nacan gida kango ne
akan wannan,duk da bata da nutsuwar da zata iya tsaiwa qarewa dakin kallo amma a
kallo daya kawai idanunta sun kaiwa qwaqwalwarta saqo da dama game da kyau da
tsaruwar dakin,qarar ruwa da takeji daga wata qofa dake hannun hagu na dakin ya
tabbatar mata yana bandaki,kamar an mata rahama haka taji,don haka da dan sassarfa
ta isa ga wani dunqulallen qawataccen table ta dora plate din,ta koma da baya tana
ficewa daga dakin da sauri.
Sanda ta koma tana ankare da irin kallon da hajjan ta bita dashi,amma batace
da ita komai ba,itama saita share kamar bata gani ba,hajjan bata jima ba ta tashi
ta barsu ita da musty sukaci gaba da hirarsu,ba'a jima ba itana taji bacci ya soma
daure mata idanu saita miqe tana masa sallama,shima kayan kallon ya nufa yana
kashewa gami da cewa
"Nima kwanciyar zanyi,saboda gobe na tashi fresh,kinsan goben nan fa babu
sauqi,zamu hadu da manyan mutane....Allah yasa nayi babban kamu nima...." Harararsa
tayi
"Ai anan kuka fi kauri"
"Kinga laifina?" Saita saki dariya tana yin gaba,sau tari sai ta dinga ganun
mustapha kamar ba cikinsu daya da haidar ba,saboda tsananin sauqin kansa.
Abun saiya girmami kan zahran,da mugun sauri ta juya ta fice daga dakin,don
tasan indai hajjan ta miqe to taja mata jagwal,don sai ansha daga kafin a sha
kanta.
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: 23
*_MUN TANADAR MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA WADANDA BABU NA BIYUNSU KAMAR HAKA_*
*Step 1*
1_maganin sanyi
2_maganin niima set
3_maganin nankarwa
4_maganin kiba babba 8kkkarami
5_maganin hips
6_maganin gyaran nono
7_maganin rage kiba
8_maganin saka feeling
9_maganin cida kwai
10_zuma yar asali
11_maganin basir kowanne iri
12_hodar niiama
13_maganin mallaka
14_gumbar nonon rakumi 10k boket😨
15_gumbar madara 10k boket😨
16_turaren farin jini
17_kaza Mara kwai
18-turaren mallaka 3step
19_hadin matar minister
20_ kaza me kwai
*Step 2*
08121491609
dadai sauransu serious buyer yabiyoni private
me shawara ta bari saita gama karki batamun lokaci please
08121491609
Tana tura qofar dakin wani bala'e'en sanyin Ac da qamshin freshner ya mata
sallama tun kafin takai ga shiga,ashe da gaske ne ranannan data ji su hafsat na
gulmarsa kan yadda yake babbakawa kansa ac,saita maida hannayenta cikin hijabi
saboda sanyi,sannan ta sake tura qofar ta shiga sosai bakinta dauke da sallama
qasan maqoshinta.
Haidar dake zaune saman daya daga cikin kujerun ya daga kanshi ya amsa
sallamar,suka hada idanu saiya maida kan nasa qasa yana ci gaba da duba takardun
daya barbaje a gabansa.
Yau daya sai taji ya mata wani irin kwarjini daya ratsa har cikin
qasusuwanta,duk da cewa ba yaune karon farko data saba ganinsa ya hade girarsa haka
ba,a'ah....dama dabi'arsa ce hakan.
A nutse ta qaraso gabansa ta aje kwandon,so tayi ta tafi amma suna hada ido
sanda take shirin tashi saita koma ta zauna,kaf gidan sunsan tsarinsa baya sarving
abinci da kansa,tuntuni sun saba al'adarsa haka,yana da wata izza da jin sarauta a
jininsa.
Har zata wuce hajjan ta kirata ta miqa mata key din,wanda dama can hajjan
nada shi,daya a wajensa daya a wajenta,daya kuma a wajen mamarshi,ta amsa ta wuce
tana fadi qasa qasa
"Kya ci gaba da share masa idan na komawata makaranta"
"Idan na barkin kin koma ba" hajjan ta bata amsa,sai tayi turus ta dakata da
tafiyar da take tana dubanta kamar zata saki kuka
"Haba hajja,bafa haka mukayi dake ba"
"Zaki wuce ko saina iskeki?" Kamar zata dora hannu aka haka ta juya ta fice.
Kamar waccar ranar dakin ba wani dauda yayi ba,sai squeezing da beadsheet
din yayi alamun an kwanta akai ne,mayafin ta daura saman kanta sannan ta fara kauda
kayayyakin da suke ba'a muhallinsu ba.
Ta isa gefan gadon bayan ta gama gyara qasan,tasa hannu tana janye zanin
gadon wasu frames masu kyau suka fado,cikin fargaba ta zagaya inda suka fadin,tana
addu ar Allah yasa basu fashe ba,ta tsugunna ta soma daukesu.
Sai data kalli bandakin ta tabbatar komai ya fita fes sannan ta murda
qofar ta fito.
Jin taku ya sanyashi juyawa a hankali,sai suka hada ido na sakanni kafin ya
dauke idanunsa ya maida ga abinda yakeyi ba tare daya ce komai ba,sai tabi ta
bayansa itama ta fice daga dakin.
Batafi minti biyu da fita ba ya shiga wajen hajjan yana hadiye zuciya riqe
da envalope a hannunsa
"Hajja....me yarinyar can kemin cikin daki bayan bana nan?"
"Sata ubana" ta amsa masa itama tana tsareshi da idanu,saiya lumshe
idanunsa,tsohuwar tana bashi ciwon kai yadda ya kamata,ita kadai duk duniya ta isa
tayi masa karen tsayen da take masa,saiya juya kawai ba tare daya sake cewa komai
ba ya fice daga sashen
"Zanyi maganinku" ta fada a ranta,tana dauke idanunta saiga zahra
"Wai hajja ma tuhumata yake da shigar masa daki?,nidai wallahi hajja kina jamin ina
zaman zamana" ta fada kamar zata saki kuka
"Yanzu ma na fara jaza miki" tuni ta tara qwalla a idanunta
"Bazan sake masa shara ba Allah,ayiwa mutum aiki sannan ya rasa me zai sakamin
dashi?,to dakin nasa dakin wa yafi cikin gidan nan?"
"Idan bakije kinyi ba nida kaina kuwa zan dauki tsintsiya naje na share masa,idan
kuma banje ba zansa daya daga cikin iyayenki yayi"saroro zahra tayi kafin ta juya
zuwa cikin dakinta da sauri.
Mita take ita daya kamar zataci kanta,tana qissima sauran kwanakin daya rage
tayi tafiyarta makaranta,ita gobe ma gidan salma ko hafsat zata,sai kuma ta tuna
idan tace zata din sai hajjan nan tace saita tambaya,ita kuwa data tambaya gwara
haqura da zuwan.
Ana ya gobe zata koma makarantarta,tana falo tana sake goge wasu kayan da
zata tafi dasu atamfofinta,musaddiq jikan gidan yayi sallama shi da nurain,hannunsu
dauke da leda suka zubw gaban hajja
"Gashi inji yaa zaki,na yaya zahra ne"
"Shi yana ina?" Hajja ta tambaya
"Yana waje yana sallamar wasu baqi ne" inji nurain yana hayewa saman kujera
"Jeka kace min idan ya gama yazo ina son magana dashi".
Jin haka ya sanya zahra a gurguje ta gama goge kayan nata ta miqe zata
shige daki
"Ke....dawo ki kwashe wadan nan kayan daga gabana" tana zumbura baki tana fushinta
haka ta dawo ta kwashe ledojin ta jasu har cikin daki,ta musu waje ta jibge ta
shiga sabgarta.
A gurguje ya leqo saboda kiran da hajjan tace tana masa,bayan sun gama
gaisawa tace dashi
"Qarfe nawa zaka miqata makarantar a gobe?,don inason na qarasa hada mata abinda
yayi shaura" kansa ya daga ya kalli hajjan
"Oh....ai dama bani ke kaita ba ko?"
"A sanda take babu igiyar kowa a kanta kuma ba matar wani bace ba ba...banason
dogon magana,ka shirya gobe da wuri ka maidata makaranta" yasani cewa koda ya fada
wani abun ma babu abinda zai janyo masa sai bala'en hajjan,wanda ya lura da cewa
yanzun wani bala'i ta koya,motsi kadan zata ce anemo mata tsoho da tsohuwarshi.
******* *WASHEGARI********
K'arfe takwas da wasu mintuna ta gama shirinta tsaf,ta shiga tayi sallama
da umminta sannan ta shiga sashen abba babba shima tayi masa sallama,sannan ta wuce
dakin mama,maman haidar ta mata sallama
"Allah ya kiyaye hanya,ya bada ilimi me amfani" ta miqa mata wata baqar leda da
batasan meye a ciki ba,hannu biyu tasa ta karba tayi mata godiya sannan ta fito.
Tana takowa zuwa bakin motar tana kallon yadda ake sanya mata kayanta
bayan motar tashi,shi yana zaune daga ciki ba tare da ya ko motsa ba,tana tsaye har
aka gama sanyawa sannan ta matsa ta bude gaban motar ta shiga a hankali.
A hankali ya tada motar kana ya saitata ya fice daga gidan,kafin subar layin
ya sanya hannunshi gaban motar ya dauko wayarsa yayi kira ya sata handsfree ya
aje,bugu biyu aka daga
"Ka sameni a nasarawa sardauna cresent" daga haka ya katse kiran ba tare daya jira
amsar da za'a bashi ba.
Tafiyar kurame da takura daga wajen zahra ta mintuna ba dasu gaza ashirin ba
ya tsaya qofar wani gini wanda ake gab da kammalashi,kashe motar yayi ya zare key
din ya fita daga cikinta y kulle sannan ya jingina da murfin,ita dai batace komai
ba tana kalloshi ta cikin glass din har zuwa sanda ta hangi shigowar ya musty a
napep na haya,bataji me suka tattauna ba,saidai taga ya miqa masa.key din,kana ya
matsa daga jikin motar zuwa ginin gidan dake gabansu,shi kuma mustapha ya bude
motar ya shigo.
Ko kadan hakan bai bata haushi ba,saboda tasan cewa inda shine zai kaita
babu komai cikin tafiyar face zallar takura har su isa,wala'alla ma sai yayi ko ya
gaya mata abinda ranta zai baci a banza.
Sanda ta shiga dakinsu kamar hadin baki duka roommate din nata suna nan,har
da sauran ma,ihu suka saka suna kiran ga amarya ga amarya,bata tanka su ba saima
harara data watsa musu
"Duk ku iya bakinku wallahi" don har ga Allah har cikin zuciyarta tana jin sune
sila,su suka jaza mata komai,saidai ko kadan basuji gargadin nata ba,saima ci gaba
da zolayarta da suke,hindu tace
"Erhmmm....erhmmm...ashe ashe dai....yayan dai da aketa nunamin sam baida
kirki.....ashe dai kece zaki wufffff da abinki akemin hannunka me sanda" kicin
kicin zahra tayi da ranta sanda take aje jakankunanta saman katifarta
"Kinga hindatu....idan baso kike aji kanmu ba ki aje wannan maganar....am seriouse
bana sonta" saida suka gama kidansu da rawarsu sannan suka qyaleta.
_*LAVENDER RESTAURANT..*_
_(Palace of mouthwatering food/delicacies)_
_IDAN KUKAJI GANGAMI DA LABARI, INA MASU SON INDA ZASU SAMU INGATACCEN ABINCI MAI
DADI DA LAGWADA? KAI BA ANAN MUKA TSAYA BA, INA SABBIN AMARE? MAMAs, YAYYU? DA
KANNEN MU MASU SON KOYAN GIRKUNAN YAN GAYU NA KASAR NIJERIYA DA KETARE?_
_*TO KU MATSO...! AT LAVENDER RESTAURANT GOTS YOU COVERED. ABINCIN KASASHE DA DAMA
MUKE KOYARWA,,COME LETS UPGRADE YOUR FOOD TIME TABLE, MATSO KUSA YAR UWA GA DAMA DA
ZAKI CANZA YANAYIN ABINCIN GIDAN KI, KOWA YASAN IYA SARRAFA ABINCI NA TAKA RAWAR
GANI A GIDAJEN AURE. KAI KO BUDURWA CE INDE KIN IYA GIRKI ZAKIGA KOWA YANA HABA
HABE DAKE..*_
_*ZA’A FARA CLASSES RANAR 14/10/2021. WATO SHA HUDU GA WATAN OKTOBAR DA MUKA SHIGA
YAU*._
_*GIRKE GIRKE GUDA 30😫😨AKAN DUBU 40 KAWAI, HARDA BONUS NA SNACKS, DESSERTS,
TRADITIONAL AND MODERN DRINK, GARGALIYA DA ZAMANI🥂WATA DAYA CHAS ZA’AYI ANA KOYAN
GIRKE GIRKEN.*_
_*Nigeria @ 61 _*
_*COOKING COMPETITION!!!*_
_*from lavender Catering ina masu son koyon girki ga dama zaku shiga gasarmu ta
girki bayan kunyi register damu akan 10k,wanda yazo na 1zai shiga ajin mu free
hade da wasu prize din na 2 da na 3 kuma zasu bayar da rabin kudine da wasu prize
suma saura kuwa zasu ayi musu ragin 5% da wasu prize wannan gasa zamu yita ranar
lahadi ne 3/10/21 zamu rufe registration na gasar ranar asabar*_
_*LAVENDER RESTAURANT: NA GARIN KANO, CLASSES DIN AKWAI PRACTICAL AND ONLINE CLASS
GA WANDA KE NESA*_
_____________________________
Sadaf sadaf ta tura qofar dakin,yan nan da duhunsa da alama kashe qwan
hajja ta sakeyi bayan fitarta,saita kunna fitilar wayarta ta haska a hankali ta isa
bayan hajjan tayi kwanciyarta nesa kadan da ita,ta tofa addu'o'in baccinta ta rufe
idanunta tana addu'ar kada Allah ya farkar da hajjan.
Washegari tana kallon yadda hajjan ke maka mata harara,saita maze ta kuma
dauke kai kamar batasan abinda ke faruwa ba,tasan idan tayi fushinta ta gaji dole
ta sauko,shirye shiryen tafiya wajen gabatar da taron ma saiya janye hankalinta
zahran ta sake samun sukuni.
Tayi mamakin ganin kitchen din,ya hada komai da komai na buqatar girki,ta
bude fridge ta debo ruwa da lemo ta hado da tea da aka dafa tun dazun a flask da
sauran farfesun kayan ciki ta aje mata,sannan ta wuce ciki kiransu hajja.
Ta fito da kayan akwatinta duka tana duba wadanda zata saka,ranta a bace
kawai yake,banda zuwan nasreen da kuma idanun hajja itafa babu inda zata je.
Hira suka shiga yi inda ita kuma ta hau shiryawa cikin wani lace army green
da yayi masifar haduwa,dinkin riga da skert daya zauna mata sosai a jiki,tana
shiryawa tana sauraren hirar tasu,da alama itama dr nasreen 'yar hira ce,hakanan
bata da wahalar sabo,don kuwa idan ka ganta a lokacin saika tsammaci ta dade da
saninsu,cikin qanqanin lokaci suka saba da ita.
Tana gama shiryawa dukka suka rude da zolayarta kan irin kyan data
yi,haushi ya cikata ta kasa magana,bugu da qari kuma ma da idanun nasreen dake
wajen,wadda ke zaune gefe tana ta murmushi tana kallonsu,yanayin zamantakewarsu da
hadin kansu,yadda suke haba haba da juna,da alama akwai saboda shaquwa mai qarfi a
tsakaninsu.
Motoci uku masu tsananin kyau da tsari ne suka debesu daga gidan aliyyu
haidar zuwa inda za'a gabatar da taron a babbar headquater sojoji dake garin abuja.
Tun daga waje xaka fahimta lallai babban taro ake,abu nasu maganin a
kwabesu,ko ina jami'aine dake bawa wajen tsaro da kariya,tako ina komai na tafiya
kan tsari,duk abun mutun idan yaga tsari da yanayin wajen sai yaji sun masa
kwarjini,lallai soja ba wasa bane,dole ya haidar ya dinga yi mana kwarjini tanaji
su salma suna fadin hakan,ita dai nata idanu ba tare da tace komai ba.
Babban wajene budadde wanda aka tanada saboda taro irin wannan,kujeru ne
bisa tsari,wajen baqi da manyan baqi daban,wajen zaman sojojin dama wadanda za'a
qarawa girma daban.
Suzo akan lokaci ne,hakan ya sanya suka samu waje mai kyau da zasu iya hangen
dukkan yadda abubuwan zasu wakana,wanda hafsat ce ta haura ta hango musu ta jasu
wajen suka zauna
"Da kyau hafsat,gaskiya kin iya zaben wajen xama,xanga dear da kyau wallahi" cewa
dr nasreen tana gyara zaman hand bag dinta tare da gyara zamanta da kyau,wanda
zamansu babu wuya wajen ya soma cika da jama'a,aka kuma fara gabatar da 'yan wasu
abubuwan kafin a shiga muhimmin taron.
Mai gabatarwa ne ya amsa abun magana ya tabbatar da wajen ya hau tsari bisa
doka da yadda suke gabatar da tarukansu,take wajen ya dauki saiti,kowa ya bada
hankalinsa kan abubuwan da aka soma gabatarwa.
An yiwa manyan baqi maraba da zuwa,sai parade na musamman ada aka shirya
saboda su,sai da aka fara gudanar da parade din sannan zahra tadan dago daga danna
wayar da takeyi ta dubi wajen.
Sai abun ya dauki hankalinta fiye da yadda ta zata,don wannan shine karo
na farko da aka fara parade a gabanta,a nutse take binsu da ido,yadda suke komai a
nutse sannan kuma a tare,duk wanda yake wajen sai abun ya bashi sha'awa ya kuma
qawatar dashi,musamman idan shi din ba ahalin abun bane.
Suna kammalawa wadanda zasu karbi qarin girman suka soma shigowa da daya da
daya,kusan inda ta zauna din yana kallon inda aka tanadar musu domin zama,sannan
kuma daura da wajen qofa ce,hakan ya bata damar ganin duk wanda zai shigo din.
Murmushi tayi itama wanda ya tsaya iya cikin zuciyarta,ko ba'a fada mata ba
tasan cewa dr nasreen da mijin nata narkakkun masoya ne,idanu kawai sun isa baka
amsa,tana shirin dauke idanun nata daga wajen ta hangi shigowarsa,wanda shigowar
tasa tayi dai dai da sakin wani take daya dauki hankalin jama'ar dake wajen.
Taso qaryata idanunta da suka nuna mata yadda shigar kakin dake jikinsa ta
amsheshi fiye da duk wani wanda yake sanye da kaki dake wajen,hakanan taso qaryata
kanta data hangi zallar kwarjini dake kwance saman daurarriyar fuskarsa da ayau
tadan sassauta daga yadda aka santa zuwa matakin daurewa na qasa qasa,batasan kaki
na yiwa mutum kyau ba sai a lokacin,saidai ta alaqanta hakan da cewa rashin taba
ganinsa cikin shigar da bata taba yiba yasa dukka taga hakan,saita janye qwayar
idanunta sanda shi kuma nashi idanun ya sauka a kanta ba tare daya shiryama hakan
ba,ya lura da dr nasreen daketa aikawa lieutenant jafar kallo wanda a yanzu xai
koma matsayin captain,saiya lumshe idanunsa gami da yin bismillah ya zauna a
mazauninsa.
Bayan gama gabatar da komai,abu na kusa da qarshe daya rage shine saka musu
igiyoyi da stars daga commanders dinsu,hakan yasa wajen ya sake nutsuwa kowa ya
sanya idanu yaga nashi wanda yazo dominsa.
Daki daki aka dinga bi ana saka musu alamun qarin girmansu,cike da ban
sha'awa karramawa da kuma girmamawa kan yadda suka sadaukarwa da qasarsu rai da
lafiyarsu.
Aliyyu mas'ud dabo shine mutum na biyar bisa layi,general hamza shine zai
saka mishi nashi,ya matso kusa da haidar din,saidai tsahonsa bazai iya kaiwa ba ga
haidar din ba,cikin barkwanci yayi maganar a nemo masa abunda zai taka wanda hakan
ya baiwa mutane dariya,murmusawa aliyyun yayi ya duqa dai dai yadda hannun general
zaikai ya saka masan sannan akaci gaba.
Duka sai da aka gama sanya musu da sauran jawabe jawabe,sannan akayi
sanarwa ta musamman akwai mutum biyar a cikinsu da za'a karrama da wasu lambobi
masu siffar kwabo da za'a rataya musu,saboda sadaukantaka gaskiya riqon amana da
kuma qwazon aiki,bayan wajen ya nutsu aka fara kiran sunayensu,mutum na farko ya
isa wajen,saiya nema alfarmar iyalinshi ce zata sanya masa,duk da cewa shekarunsa
sun kusa arba'in da wani abu hakan ya burge mutane,cikin nutsuwa ta taso ta rataya
masa sannan ta tsaya aka musu hoto ta wuce,hakan ya sanya aka maida rataya abun
wuyan ga iyalan sauran,marasa matan aure a ciki kuma mahaifi ko mahaifiya,abun
saiya dinga bada qawa da burgewa,saboda kowacce mata in a romantic way take sanyawa
mijinta,tana jin yusra na cewa
"Gaskiya ne,ban sake yarda soja akwaishi da son matarshi ba sai yau....jiba don
Allah abun sha'awa,sun sadaukar da farincikinsu ga qasarsu...ma sha Allah,Allah ya
dafawa sojojinmu".
Lieutenant jafar wanda a yanzu ya koma captain jafar aka kira,dr nasreen ta
damqi hannun zahra cikin farinciki ba tare dama ta sani ba
"Ma sha Allah my happiness....lallai yau ranarmu ce" ta fada tana duban zahra,itama
zahra dubanta tayi,tana mamaki cikin ranta wannan wacce irin soyayya ce?wadda bata
boyuwa,saita sakarwa dr nasreen murmushi kawai na qarfafa gwiwa,ta gyada kai
"Thanks" ta cewa zahra tana miqewa a nutse ta sauka daga wajen zuwa inda yake tsaye
yana jiranta.
Sam zahra bata damu ba bata kuma kawo komai ba,don bata tsammaci zuwan
sunan Aliyyu ba,sannan tunda daga mama har abba babba na wajen,sun kuma fita
cancanta,saidai me?,cikin sakanni sunan aliyyu dabo ya karade abun maganar,wanda
kamar qiftawa da bismillah duk sojan daya kasance junior dinsa dake wajen saida
suka miqe,sukayi salute nashi sanda yake takowa zuwa inda kowa yake tsaiwa cikin
nuna zallar girmamawa,da alama akwai akwai alaqa mai matuqar kyau a tsakaninsu
"Ma sha Allah" 'yan uwa dake kusa taji suna furtawa,lumshe idanunta tayi tana duban
wajen yadda suke tsaye,abun ya qayatar da duk wanda yake wajen
"Get up mrs aliyyu dabo" dr nasreen ta soma fadawa zahra cikin fara'a,yayin da
dukka su salma suka waiwayo suka sanya mata ido,kai ta kadawa dr nasreen
"Mama tana nan....haka abba ma"
"Tashi kije inna wuro" ta jiyo muryar mama,wanda sam bata zaci taji ba,saita miqe a
hankali tana jin wani nauyi na saukar mata,qafafunta sukayi sanyi kamar ba zata iya
tafiya ba,wanda wannan ya qarawa tafiyar tata zama slow,hakan saiya qarawa yanayin
takun nata ado,da wani salo na daban mai qayatarwa.
Tunda ta taho ya zuba mata idanu da wani salon kallo,wanda ba lallai kowa
ya fahimta ba,saif dake tsaye daga gefansa ya soma masa magana qasa qasa
"Smiling please....,just once" banza yayi dashi,saidai idanunsa yana kanta sanda
take ci gaba da takowa,taqi kallon koda saitin inda yake,saidai tana sauraren salma
dake bayanta tada n tako mata tana mata magiyar karsu bada 'yan uwansu.
Sai data fara amsar abun wuyan sannan ta juya zuwa direction din da yake
tsaye,saif ne cikin zaquwa yace
"Please zaki....i beg you mana,kaga fuskarka?,don't behave like......." Qafarsa
yasa ya take gefan qafar saif da qarfi,wanda hakan ya sanyashi yin shuru tare da
runtse ido
"Mugu" ya fada yana cije lebe,dai dai lokacin da zahran ta qaraso gaban haidar
din,sai a sannan idanunsu suka shiga cikin na juna,kowannensu na iya ganin qwayar
idanun dan uwansa kai tsaye.....
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: 26
Taku biyu ta sakeyi zuwa gabansa,wanda hakan ya qara adadin kusancin dake
tsakaninsu,a hankali ta daga hannunta da niyyar zira masa abun,saidai kuma
ina,tsahonta bazai taba kaiwa ba,don kanta a dai dai qirjinsa ya tsaya
"Madam kina buqatar qara motsawa kadan,don maigidan naki sadauki ne da gaske tako
ina" dukka sai aka sanya dariya,taku daya ta qara ta mannu da jikinsa,qamshin
turarukansu suka soma gauraya da juna,gaba daya numfashinta yaso daukewa,sosai
bugun zuciyarta ya qaru,ta lumshe idanu tana daga hannunta zuwa saman kansa.
Tana isa gabanshi idanuwa suka mata yawa saita fara qoqarin durqushewa a
gaban nasa,da hanzari yasa hannu ya dagota,wanda hakan ya sabbaba mata fadawa
jikinsa gaba daya,so yake tayi ta gama ta sauka daga wajen,saboda yadda ya fuskanci
sunyi calling attention din mutane da yawa,tsintsiyar hannayenta dake riqe da
igiyar ya kama,yanajin yadda tsigar jikinsa ta zuba har gefan fuskarsa,saiya
ranqwafo kaman dazu,wanda hakan yasa yayiwa fuskarta rumfa fiye da dazun,ya daga
hannunta har zuwa wuyansa sannan ya barta ta zura.
Gaba daya jin jikinta take yana rawa,tayi baya kamar daxu zatabar wajen,sai
qafafunta suka lanqwashe,ta tafi luu kaman zata fadi,da sauri yakai mata cafka,ya
samu nasarar riqo qugunta,ya tsaidata ta tsaya sosai,idanunta a nashi tasa hannunta
tadan zame hannunshi daga qugunta da taga kamar baya da niyyar sakinta,sannan ta
juya ta soma sauka daga wajen,wanda tuni tafi ya karade wajen,ita kuwa ji take
kamar tayi tsuntsuwa ta isa mazauninta,saboda yadda duk inda ta gifta ake binta da
idanu,haka duk inda ta gifta sai taji anyi magana akansu qasa qasa
"Beautiful couples"
"Ma sha Allah perfect match"
"Wow ma sha Allah" da dai sauransu,bata iya waiwayawa bare taga wanda ya furta
maganar,harta isa mazauninta ta zauna tana fidda ajiyar zuciya me qarfi,tana jin
yadda jikinta tacan ciki ya jiqe da gumi
"See love don Allah.....no wonder mata ke macewa murus kan Aliyyu,madam kin musu
zarra fa da kikayi wufff dashi,anan wajen naga fuskokin abokan adawa da yawa" caa
din dasu salma suka juyo sukayi mata ma yasa bata samu amsa maganar dr nasreen
ba,duk da tanajin bata da amsar da zata bata din,sai kawai ta miqe ta soma ratsawa
tana fita daga wajen,saboda wani iri da takejin kanta yayi,har yanzu kuma mode
dinta bataji ya koma dai dai ba.
Tafiya tayi kadan tabar wajen dake da hayaniyar,gurin akwai qarancin zirga
zirga da hayaniyar jama'a sosai,saita samu bayan wata qaramar mota ta hau samanta
ta zauna saboda bata da wani tudu sosai motar.
Idanunta ta rufe dukka,ta shaqi iska sosai takai har cikin huhunta sannan
ta fesar,a hankali ta soma bita na abinda ya faru yanzu a wajen.
(Ba lallai haka suke gudanar da taron qarin girmansu ba,na tsarashi a hakkane
saboda yafi dacewa da abinda zai qayatar dame karatu,ya kuma tafi da salon
labarin,ya alaqantu da abinda zaizo a gaba,so pls idan akwai soja ko sojanniya
😂,ko matar soja sai ku karba a hakan🙏🏽)
Sam batasan lokaci yaja haka ba tana zaune a wajen,har aka tashi taron,sai
a sannan 'yan gida suka fara neman inda tayi,saidai har suka gaji da neman babu
wanda ya ganta,ga kuma wayarta na wajen dr nasreen bare su kirata suji inda
tayin,dole wadanda zasu koma a ranar sukayi gaba,su hajja ma daga baya suka
bisu,akabar mustapha ya lalubota tunda haidar din ma bai tafi ba
Tare suka jero shida abokin aikin nasa,suna tafe a hankali da alama
tattaunawa sukeyi,hannunsa zube cikin aljihun wandonsa,ya zuwa yanzu babu hula a
kanshi,da alama cireta yayi.
Da sauri ta bude idanun nata,sai ta zubesu saman tashi fuskar,take suka hada
ido,sai kowa ya janye tashi qwayar idanun,saita kuma ta soma yuqurin saukowa daga
saman motar,a lokacin dashi kuma ya juya baya kamar wanda baison ganin saukowar
tata ya zaro waya daga aljihunsa
"Kazo maza ina ta baya" ya fada kawai yana kashe wayar,sannan har ta soma takawa
zata bar wajen
"Karki dara ko ina....don idan kika batan da gaske babu wanda zaki kuma wahalarwa"
iya abinda ya fada kenan,saita waiwayo ta dubeshi ta watsa masa harara,saidai ta
makara,don tuni ya sake juyawa ya bada baya,don haka ta dauke kanta ta samu wata
motar daban ta jingina,yayin dashi kuma ya koma wajen abokin aikin nasa da suka
taho tare,suka jera har zuwa bakin motar haidar din,ya budeta ya shiga ciki duk da
qafafunsa na waje,da alama akwai abinda yake daukowa.
Hanyar da motar tabi har yanzu idanunsa suna kai,saida major inusa ya
taba kafadarshi sannan ya dauke idanunsa ya maida kansa
"U r lucky dabo....komai naka na zuwa cikin nasara da kyawun yanayi,ka godewa
Allah,ka samu muqamin da an jima ba'a samu matashi kamarka daya riqeshi ba,ka fito
daga babban family masu sonka da qaunarka,masu tarbiyya da kuma hadin kai,lastly ka
auri princess charm,she captured all the people's......" Kallon da haidar din ya
masa yasa bai qarasa ba,saiya cike zantukan bakinsa da murmushi kawai ya waske
zancan,shi kam baima san ya masa kallon ba,kawai abinda ya sani major din ya qware
sosai wajen bin mata,abinda yasa sam basa shiri ko jituwa shida haidar din,duk da
yadda haidar ke sonshi,saboda mutum ne shi da baya jituwa da duk wani wanda ya
kaucewa hanya ko yake ba dai dai ba,matuqar bazai gaya masa gaskiya ya yarda ya
dauka ba,idan ka gansu tare da major inusa to sabgar aiki ce,saiya soma takawa
yabar major din tsaye a wajen yana bin aliyyun da kallo.
"Shegen yaro......kana ganinsa haka kullum idanunsa a qasa kamar bai kallon
kowa,amma yasan takun kowa,the worst part dinma....matan da ake gani bai kallo kuma
basa gabansa,yayita yarfasu su kuma da shegen nacin son mai kyau da aji suyita
binsa,ashe yana qare musu kallo a fakaice,banda haka ina yaga wannan har yayi
wuffff da ita....gaskiya yasha kwana yaron nan" major inusa yake fada shi kadai
kamar wani zautacce.
Data wuwwulga idanunta bata ga jakarta ba,sai tabi bayan salma data koma
dauko jakar hannun hajja,ta isketa tana neman jakar a inda hajjan tace mata tana
nan
"Don wulaqanci a dauki jakar kowa amma banda tawa,saboda ni bani da gata da
galihu?"
"Ai an debi kayan da za'a koma miki dasu,an kawo miki wasu" duban salman tayi sanda
take zuge zip din jakar
"Kamar yaya?"girarta ta daga
"Eh to....bari na tsegunta miki,kamar naji hajja tana fadin anan ke za'a barki,zaku
taho tare da ya haidar ko?"
"Kambun bala'i!.....ni!,wallahi bazan zauna ba,tabdijan,ai itama hajjan ba haka
mukayi da ita ba" ta fada tana jin wani tashin hankali yana ratsata,dafata salma
tayi tana boye dariyarta
"Easy mana zuhra."
"Anqi easy din.....naga alama hajja wani abu daban takemin ba so ba,in banda haka
ta yaya zata ce na zauna da wannan mutumin a cikin gidansa?,ya kasheni kenan akai
musu gawata ko?,dama haka takeso".
"eh haka nakeso don ƙaniyarki....indai wannan shine rashin son to bana
qaunarki fadi ki qara fada,ke salma tsaiwar me kikeyi ke kuma daga daukomi
jaka?,miqomin driver yazo,ko mu wuce mu barki anan ki tayata zama" wani zillo salma
tayi sai gata kusa da hajjan tana cewa
"Rufamin asiri kada ya zaki ya cillani ta window nayi kwanan qofar gida,a jawa
yarona da mijina asara" kuka zahra ta saki harda dora hannu aka
"To wallahi nima bazan zauna ba,kowa tsoronsa yake amma haka kawai ni an hadani
dashi?,saboda niba mutum bace?,idan ma cinyeni zaiyi ya cinyeni?"
"Eh haka nake nufi don gidanku,ja'irar yarinya" hajja ta sake cewa tana qwalalowa
zahra idanu gamida tamke fuskarta kaman bada xahra'un tata take magana ba
"Wuce muje" ta fada tana nunawa salma hanya,tuni salman tayi gaba,tana danne
dariyar dake taso mata,ita ta tseguntawa hajja cewa gobe zasuyi liyafar cin abincin
dare dukka wadanda aka qarawa girma,kuma kowa da matarsa yake zuwa,idan ma akwai
yara harda su,nan take hajjan tace dole haidar dinta shima asan ya zama babban
mutum,dama a wajen taga idanun wata qabila yana haka haka akan jikan nata,duk inda
yayi tana binsa da wani kallon yaudara na banza da wofi,tota Allah ba tataba,ba
qaramin dariya akaci a motar ba da wannan ruɗu da hajjan ta hada ba,tuni itama
hajja tabi bayanta,ai kuwa itama zahran saita kwashi jakarta ta rufawa hajjan baya.
Kacibus sukayi da umminta wadda ta sake shigowa ta rage mararta kada fitsari
ya dameta a mota,duk sai suka ja baya,ta dubi ummin itama ummin ta dubeta,kallon da
tayi mata shi ya sanyayar mata da jiki,saita tsugunna saman jakartata a wajen,ita
kuma ummin ta wuce ciki abinta.
Batafi minti biyu ba ta fito,a lokacin zahran ta dawo bakin qofa ta tsuguna
kamar me neman gafara ko taimako
"Kiyi duk yadda zakiyi,kiyi duk qoqarin da zakiyi ki nunawa duniya ban baki
tarbiyya ba,ki nunawa duniya na sama dake basu isa dake ba,nayi imanin kaf fadin
duniya idan na mutu kika laluba daga farko zuwa qarshe baki da masoyiya kamar hajja
har abada,hakanan ko yanzu na mutu zan kwanta cikin kabarina hankalina kwance game
da aurenki,don nasan ba zaki tozarta a hannun haidar ba,bazai taba wulaqantaki
ba,ba hannun gama garin mutum kike ba,shi din na musamman ne wanda yasan da daraja
da mutuncin dan adam,wanda ya kulaa ya kuma girmama rayuwar mahaifiyarki,ruwanki
kiga girma da mutucinsa saboda haka,ruwanki kisa qafa ki shure.....zakiga kamar
ba'a sonki,tako ina an matsa miki.....soyayya ta gaskiya itace ka tsaya tsayin daka
wajen ganin naka ya gyaru kafin kowa,sannan matsalar zamantakewa a hausance sunan
mace ke fara fitowa kafin na da namiji....baki da hurumin yankewa haidar hukunci
sabida tsohon tunaninki na ba *ALƘIBLARKU* daya ba,akwai banbancin ra'ayi
tsakaninku ko?,wannan rusashshiyar hujja ce.....a yanzu ina miki magana da harshen
uwa zuwa ga diyarta......ki nutsu ki fara dora komai kan muhallinsa da
saitinsa.....sai angwada ake sanin na qwarai" daga haka ummin tayi gaba abinta ba
tare data waiwayo ba,ita kadai tasan me takeji a cikin zuciyarta,ita kadai tasan
wanne fata ke gareta,ita kadai tasan adadin sau nawa tana hana idanunta bacci don
ingantar rayuwar yaranta.
Da qyar ta tashi daga wajen ba tare data dauke jakarta data janyo wajen
ba,a hankali tana jin yadda hayaniya da surutunsu keyin nesa da gidan,da alamu
ficewa sukeyi,da qyar takai kanta bakin katifar ta zube,duka zantukan ummin nata
sun tsaye mata kamar qusa a qahon zuci,hakanan sun kashe mata duk wani qwari na
jikinta.
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: 27
Tsahon awa guda gidan ya dauki shuru,duk da lokaci zuwa lokaci tana dan jiyo
motsi da maganganu sama sama daga falo zuwa kitchen,wanda ta tabbatar da ma'aikata
ne.
Tun azahar take kwance bayan ta gama hawayenta son ranta ta godewa
Allah,kota kan abinci bata biba,duk da karin safe ne kawai a cikinta,abu daya ke
tada ita shine sallah,sai ruwa kawai data ke sha wanda shima cikin dakin yake jiya
da dare suka shigo dashi basu shanye ba,haka ta dinga juyi ita kadai,har zuwa
lokacin da duhun magarib ya sako kai,aka fara qwala kiran sallahr magariba,saita
miqe tana jin yadda tsakiyar cikinta ya qulle,da alamu ulcer dinta tana son tashi
kenan idan batayi wasa ba,hakan ya sanya sai data fara fitowa parlour ta bude
fridge ta dauki fresh milk mai sanyi babban gora daya tana duban yadda falon ya
koma fes,ko ina ɗas ɗas dashi yana fidda qamshi,kamar ba'a taba yin baqi ba,ba
abinda ke fita sai wani samfurin qamshin freshner na musamman,ga abinci a jere a
cikin tsari saman dining table,saita dauke kanta ta koma daki,ta zauna ta zuqe
madarar tas sannan ta shiga bandaki,tana fitsari taji gefan mararta na qullewa
"Ya salam" ta fada,alamun period na iya zuwa anytime kenan,haka ta daura alwalarta
ta dawo dakin ta tayar da sallar.
*Aliyyu Haidar*
Sosai yayi relax a bayan motar bayan ya aje hularsa a gefe yana furzar da
iska daga bakinsa,yana jin yadda sanyin ac ke ratsashi tare da qara haifar masa da
kasala da kuma tayar masa da gajiyarsa ta zirga zirgar wunin yau.
Zuciyarsa da qwaqwalwarsa tayi nisa wajen tuna abubuwan da suka faru yau
wayarsa dake aje tare da hularsa ta dauki tsuwwa,dan qaramin tsaki yaja,ba kasafai
ya fiya son kira ba,saidai yau yasha kiran har ya gode Allah,a hakama don yana
kashewa ne baya amsa wani.
Ganin sunan me kiran yasa ba shiri yakai hannu ya dauka,labbansa suka motsa
cikin ransa ya furta
"Rigimammiyar tsohuwa" saiya kara a kunnensa
"Badai har kunje gida ba?"
"Harma mun huta yanzu haka?"
"Ma sha Allah,sannunku da qoqari,Allah ya qara girma da nisan kwana me amfani"
"Amin ya rabbi...amin Aliyyu,Allah yayiwa rayuwa albarka"
"Amin hajja"
"Yauwa.....dama na kiraka ne na gaya maka,nabar amanar jikata a gidanka" fuska
yadan yamutse yana son ya fahimci maganar tata,kamar kuwa tasan tunanin da yakeyi
tace
"Matarka zahra....zaku taho tare idan ka gama abinda kake...."
"Amma hajja....bamuyi maganar ba....sannan ma kuma karatunta fa?"
"Kai da ita ku kukasan wani karatu.....,jan kunne na kiraka nayi maka,aronta na
baka,bance kuma atabamin ita tun yanzu ba ehe" tun kafin takai ga kashe wayar shiya
kashe,saiya jefata gefe yana dafe kansa,hajjan ta soma wuce tunaninsa,tunda harta
fara masa manya manyan maganganu irin wannan,banda abinta ma shi da bashi ya nemi a
barta ba su suka barta don raɗin kansu har tazo da wannan maganar,shikam wannan
sabgar gada dayanta akwai qwara a cikinta.
Da ire iren wannan tunanin daya ci gaba dayi har suka isa gidan,ya fita
yabar drivern yana kulle motar,yayi cikin gida,ma'aikatan dake harabar gidan suna
masa sannu da dawowa.
Ya kusa minti talatin yana sakarwa jikinsa ruwan dumin sannan ya cuda sabulun
wanka ya dauraye ya hada da alwala ya fito.
Sai daya tsane jikinsa da towel sannan ya nemi doguwar riga me gajeran
hannu ya sakakkiya ya saka,ya feshe jikinsa da turaruka bayan ya taje kansa,sannan
ya koma ya zauna saman kujerar dake dakin ya dauki wayarsa ya soma laluben 'yan
gidansu,yanason yi musu ban gajiya,don wayar yakeson ya kashe gaba daya,don idan ya
kwanta ya tabbatar salla ce kawai zata tasheshi,saboda yadda yake jin jikinsa.
Tsahon wasu mintuna yana a haka ba tare da yasan me yake tunani ba,saiya miqe
ya zura slippers dinsa ya fito falon.
Dai dai lokacin da yunwa sosai ta dinga sakadar zahran,ta dinga juyi tana
jin yadda ulcer dinta ta fara motsawa harta fara sanya mata ciwo tsakiyar
cikinta,saita koma rub da ciki ta kwanta qwalla na sauko mata,ita koma meye ya faru
hajja ce sila,ita ta jawo mata komai.
Qarfe hudu na dare ya farka kamar yadda ya saba tashi duk dare,wansa baya
komawa daga sannan kuma sai bayan sallar asuba,a nutse ya miqe ya shiga bandaki ya
dauro alwala,saiya janyo wayarsa zai duba lokaci,saboda dakin ba'a sanya mishi
agogo ba tukunna,don gaba daya cikin kwanaki biyu aka zuba dukka furniture din
gidan qarqashin jagorancin wani kamfani,duk da ya kashe kudo sosai shi kansa ya
sani,amma yadda suka tsaran gidan da kaya masu kyau da inganci kadai ya isa ya gaya
maka sunsan aikinsu.
SMS ya gani wanda da alama tun daren jiya ya shigo,dannawa yayi ya bude
saqon,daga ummi ne,saiya zauna saman abun sallar tashi sannan yabude saqon ya fara
dubawa.
Ko ba komai,ko yaya tana buqatar yayi mata kara a rayuwa,koda komai bazaije
ko ina ba,koda komai taqaitacce ne,amma ta cancanci ya nuna mata wannan karar.
Saboda ita bai jima a masallacin ba,ana idar da sallar yayi addu'o'insa da
basu wuce minti goma ba yafita a masallacin.
A hankali ba tare daya shurya ba idanunsa suka sauka kan sumar tata da
kallo,wanda duk da gida daya suka taso zai iya cewa bai taba ganinta ba sai
yau,saboda tunda can zahran ma'abociyar zama da dankwali ce ko hula,cikin biyu baka
rasata da daya,ummi ta riga data sabar mata da hakan,koda za'a kamata da kowanne
laifi ayi mata hukunci banda na zama babu dankwali,baya ga haka ma duk sunsan
halinsa,kada ki sake ya sameki babu dankwali akanki.
Har yakai hannunsa zai tattare mata gashin kanta,saiya janye hannun da
sauri ya maidasu baya kamar wanda aka sawa shocking,tsahon second biyar sannan ya
sake kai hannunsa.
A nutse ya bude murfin motar ya shiga sannan ya rufe,yana shirin saka key ya
kunna motar idanunsa suka kai kanta,ya dubi yadda ta cure waje daya,sai haka ya
tuna masa da zahra....lokaci na qarshe a rayuwarta daya dauketa cikin
motarsa,lokacin da take nemam agaji a sanda bashi da abinda zai iyayi mata,a haka a
cure waje daya a sit din da wannan zahran ke kai,sai yaji wani abu ya tsarga masa
tun daga kanshi har zuwa qafafunsa,sai daya furta can qasan maqoshinsa
"La haula wala quwwata illa billah" sannan ya bude idanun nasa ya tada motar suka
fice daga wajen cikin tuqi a hankali saboda yadda ruwan saman yake qara qarfi.
A qalla sun shafe kusan minti talatin sannan suka qarasa unguwar tasu,yayi
horn aka bude musu ya sanya motar tishi ciki ya ajeta a wajen adana motoci na
gidan,saiya kashe motar,ya zubawa waje idanu ta cikin glass din motar yana kallon
yadda ruwa ke gudu yana sauka da qarfinsa,a irin wannan yanayin da lokacin
zuciyarsa na masa wani irin fes,tamkar ruwan na sauka ne saman zuciyarsa,saiya
sanya hannunsa ya bude murfin motar ya fita,ya ware lemar hannunsa.
A kasalance itama ta bude murfin motar ta zura qafafunta tana rufe ido
saboda yadda ruwan ya soma feso mata,duk da haka bata fasa fitowar ba,don babu
abinda take buqata a yanzu irin ta samu waje ta kwanta sosai ko zata rage azabar da
takeji.
Qanqame jikinta tayi waje daya ta soma nufar cikin gidan,saidai batayi taku
biyar cikakke ba taji an lulluba mata abu saman kafadunta.
Kanta ta dago sanda yake dora mata lemar hannunsa tsakanin hannayenta,kafin
takai ga kallon qwayar idanunsa tuni yayi gaba,cikin kuma ruwan saman dake saukowa
yana dukan suit din jikinsa daya cire 'yar saman ya rufa mata,mamaki ya
tsaidata,sai kuma tasoma takawa itama zuwa cikin.
Zagayeta yayi ya matsa bakin qofar ya sanya key din ya bude,sai yaja baya ya
tsaya,taja qafafunta ta shige,da qyar ta qarasa dakinta ta zube saman katifa tana
juyi.
A qalla ta kusa minti talatin babu wani sauqi,kadaici da zama ita kadai ta
qara ta'azzara mata ciwon,sai qwalla ta cika mata idanu,nan da nan suka fara
gangarowa,tana rayawa a ranta inda yanzu ace tana gida babu shakka da tuni an sama
mata magani,koda babu magani akwai kai kawon jama'a da zai dauke mata wani abu daga
ciwon komai qanqantarsa.
A nutse yake takowa cikin falon bayan yayi wanka da ruwa me dumi sosai ya
sanya kaya masu dan kauri saboda ruwan daya dakeshi daga gun ajiye mota zuwa cikin
gidan,har yanzu ruwan ake tafkawa bai tsaya ba bai kuma sassauta ba,garin gaba daya
ya fara daukar sanyi,saman dining ya qarasa ya samu abinci yaci,ya gama yana sauko
ya nufi daki don sanyin daya soma busawar ya fara sashi jin takura,bargo kawai yake
da buqatar shiga.
Yana shiga ya sanya hannu da sauri yana kashe fankar dake faman wulwulawa
kamar babu sanyin ruwan sama,sannan ya dauki remote yayi controlling sanyin da acn
ke bayarwa sa'annan ya waiwaya saman katifar dakin.
Can ya hangota cikin bargon tana mutsu mutsu,duk da baka iya ganin koda
kanta
"Wayyo Allah na" daya kasa kunne yaji tana fada qasa qasa,saiya qarasa da sauri ya
haura zuwa saman katifar ya tankwashe qafafunsa,sannan ya saka hannu yana yaye abun
rufar dai dai sanda ta qaraso dab da ita yake zaune garin mirgin mirgin din da
takeyi
"Ya Allah" ya fada a hankali yana duban yadda take riqe da qirjinta,tun asali shi
mutum me mai tausayin mara lafiya,abu na farko dake daga masa hankali,lalura da
kuma raunin 'ya'ya mata.
Miqewa yayi tsaye da sauri yana ciro wayarsa daga aljihunsa,idan bai manta
ba ya taba zuwa hutu gida lokacin bata da lafiya irin haka,yaji hajja tana cewa
ulcer ce,da alama yanzun ma itace.
Bai wuce minti biyar ba ya dawo dauke da wata butar shayi me qananun
kofuna,ya ajeta inda ya aje wancar ledar a hankali yana furxar da iska daga
bakinsa,saiya dubeta still dai tana kwancen bata tashi ba,sake maimaita mata yayi
ta tashin,saita girgiza masa kai alamun a'a
"Ki tashi nace....ina wasa dake ne!" Ya fada a dan tsawace,wanda hakan ya tilastata
yaye bargon da take ciki,hawaye ne jage jage a idanunta,da gumi daya jiqe mata
fuska,da alama zazzabin daya soma rufeta ne yake sauka,saita zauna sosai ba tare
data miqe din ba.
Taku biyu yayi ya hade tazarar dake tsakaninsu,kafin ta ankara ya jata zuwa
qirjinsa kamar mai shirin rungumeta,ajiyar zuciya ta subuce masa a sirrance,ya dora
hannunsa a hankali a bayanta yana lalubar zip din rigarta,saita sandare a tsaye
tana raba idanu,jikinta ya dauki rawa gaba daya lokacin da taji ya kama zip din ya
soma zugeshi zuwa qasa
"Zzzzzan...." Take fada bakinta yana rawa kamar yadda jikinta yakeyi,ko harafi daya
ya kasa fitowa daga bakinta,har sai da taji yakai zip din qasa,rigar ta rabe gida
biyu,taji hannunsa saman kafadarta,yana nufin sabule mata rigar xaiyi?,ta tambayi
kanta da kanta,ai batasan sanda ta cafe tsintsiyar hannunsa ba cikin hawaye tace
"Zanc.....zan cire da kaina" nannauyar ajiyar zuciya ya saki yana zame hannunsa
daga cikin nata,don dama yana tunanin ta yadda zai qarasa aikin da yake pretending
din yin,saiya taka da baya da baya,sannan ya juya bayansa,ya tafi zuwa window din
dakin ya yaye labulen ya bude glass din ya saka kanshi a ciki yana sake sauke
ajiyar zuciya gami da fidda iska daga bakinsa zuwa hancinsa,yana jin wani irin
yanayi cikin jikinsa.
Kamar wata sakarya ta riqe wuyan rigar gam,tana tsaye tana rawar sanyi,tana
kuma satar kallon yadda ya juya mata baya,yana nufin yana dakin xata canza kaya
kenan?,idanunta ne suka sauka kan qofar toilet,sai tayi sauri ta nufi bandakin
itama tana sauke ajiyar zuciya.
Kowanne waje idan ya saka wiper ya goge saiya kalleshi,sosai yake ganin
kamanninta wanda a baya ko za'a tsireshi baisan ya fuskarta take ba,manyan idanu
dake qawace da gashin ido dogaye,daga samansu kwantacciyar gira ce mai yalwar suma
itama wadda ta kusa hadewa da juna,a hankali harya gangaro kan lips dinta da suka
jambaki,saiya sauya sabuwar wiper,ya saka dan yatsansa a cikinta ya dora saman lips
dinta ya fara gogewa.
Jikinta ta qanqanme saboda ji take kamar yana mata tafiyar tsutsa,ta gefan
aliyyu kuwa haka ya dinga goge jambakin ainihin kalar labbanta na fitowa,baisan
cewa ya jima yana gogesu ba sai da zahra da har yanzu idanuna ke rufe tace
"Zafi"saiya janye hannunsa da sauri yana sake daure fuska,sai yaja tsaki qasa qasa
sannan ya aje abincin gefanta,ya miqe ya fice yana yarfe hannu,gami da tuhumar
kansa,me yasa bai bar mata kwalliyarta ta goge da kanta ba?,daga bisani ya aza
hakan a matsayin kyautata zai gwada yi mata kamar yadda mahaifiyarta ta gwadawa
tashi rayuwar.
A hankali take cin abincin kamar ta rusa kuka saboda yadda sam baya mata dadi
a bakinta,ga numfashinta dake wani irin nauyi,bata ci da yawa ba ta ture kwanon ta
koma rub da ciki,a yanzu duk yadda taso ta daure dauriyarta ta qare,ta soma raki a
bayyane don ta kasa yin shurun.
Dai dai sanda ya sake dawowa dakin bayan ya gama shirin barcinsa yaga iya
abincin data ci din,sauri yadan qara zuwa inda take kwancen,sai yaja da baya,ya
zuba ruwan dumin daya tafasa ya barshi yadan sha iska cikin cup din daya dauko,ya
sanyata ta sake zama tana sharar qwalla.
Kallo daya yayi mata ya dauke kanshi yana tuna zahra,lokacin da qwalla ke
fita daga idanunta kamar haka,tana cewa ya yafe mata mutuwa zatayi,bai taba kawo
mata mutuwar ba a sannan sai gashi ta tafin,wannan tunanin yaji ya motsa
zuciyarsa,wannan tunanin yasa yaji baiso yabar dakin,hakanan ya di ga jin idan
yabar dakin kamar wani mummunan abu zai biyo baya,saboda haka ya koma dakinsa ya
dauko duk abinda yasan zaya iya buqata ciki harda sytem dinsa da wayoyinsa ya dawo
dakin,a lokacin tayi rub da ciki cikin bargo,bata juye juye kamar daxu,saidai
lokaci zuwa lokaci takan motsa,da alamu ta samu relief ne daga ciwon.
Saman kujerar dakin yayi zamanshi bayan ya maida dakin dim light,saiya bude
system dinsa ya soma rage aiki,aikin yadda zai gudanar da office dinsa,da kuma
bataliyar rundunar sojin dake qarqashin jagorancinsa,ya soma tsara komai bisa
hikima,saidai baya daukar wasu mintuna masu tsaho bai daga kai ya dubeta ba.
A hankali ya zare gilashin idanunsa da yake amfani dashi idan zai dade
saman screen na waya ko system,ya ajeshi gefe yana miqa,ya sake duban inda take
kwance sau babu adadi,har yanzu dai ba alamar bacci ya dauketa,saiya tattare komai
waje daya,ya taka a hankali har ya isa saman katifar,ya zauna sosai,saita rintse
idanunta tana jin yadda ya zauna gefan nata kamar tayi kusanci da yawa,gabanta ya
dinga faduwa,sanda ya dora hannunsa saman goshinta da wuyanta bayan ya yaye bargon
data rufa numfashinta ya sake yi mata wahalar shaqa,hakan yasa yadan firgita,saiya
dagota daga kwanciyar da tayin,ba tre da tunanin komai ba ya zira dukkanin hannunsa
cikin rigarta ta baya,ya kama maballin bra dinta yana qoqarin balle mata wai ko
zata samu damar shaqar numfashin sosai,kamar yadda yaga suna yiwa juna sometimes a
gida ko a battlefield idan tsautsayi ya ritsa da dayansu numfashi ya fara masa
wuyar shaqa,suna cire masa duk damarar dake jikinsa don a rage masa wahala.
Ji tayi kamar zuqa daya ya rage mata na iska a duniya sanda taji dumin
hannunsa a bayanta,kawai saita tafi luu gaba daya zuwa jikinsa tana jin wuta na
dauke mata,bai damu ba,hakan ma saiya rage masa aiki,ya balleta gaba daya ya saka
hannu ya zareta ya wurgata gefe,sai kawai ya gyara mata kwanciya saman cikinsa ta
rub da ciki yadda ya fuskanci tafi jin dadin kwanciyar,bata da wani zabi da ya wuce
tayi likimo,babu qarfin zame kanta daga gareshi,sannan tsoro da tsananin mamakin
jinta kwance tsakiyar qirjin mutumin da bata taba kawowa kanta hakan ba yasa
batajin akwai wata kalma guda daya da zata iya fita daga bakinta.
_IDAN KAJI GANGAMI DA LABARI....! INA MASU ZUBIN ADASHEN DA BA RANAR DAUKA NA DATA?
_
_TO KU MARMATSO KUJI, KU KUMA SHARE HAWAYEN KU, MUNZO MUKU DA SABBIN TSARE TSARE NA
DATA, WADDA KOWA ZAI IYA SAYA DAI DAI KARFIN SA. A FARASHI MAI RAHUSA_
_TSAYA KUJI, A RANO NET ZAKA IYA ZAMA RESELLER KO WHOLESALER KAI MA, EH ZAKA/KI IYA
ZAMA MA SAYAR DA DATA A FARASHIN SARI MUKE BAYARWA, KAI/KI KAFA KASUWANCIN KU KUMA.
DA KUDI KALILAN._
_MUNA KUMA SAYARWA AKAN ‘DAI DAYA, KOWANE NETWORK MUNA SAYARDA DATA PLAN DINSA AKAN
KUDI KALILAN, MASU FARASHIN SARA KUWA MA KU KUDIN BAI KAI HAKA BAMA_
_AIRTEL_
_9MOBILE/ETISALAT_
_MTN_
_GLO_
_DUK MUNA SAYARDA TSARIN DATA DINSU. KAMAR MISALI MTN MUNA SAYARDA 1GB.24MB AKAN
FARASHIN NERA 300 KUMA YANA KAIWA WATA DAYA, GWARGWADON YADDA KAKE AMFANI DA DATA,
2GB 600, 3GB 900!!_
_DUKA WADANNAN TSARIN DATA DAMA NA SAURAN LAYIKA MUNA SAYRWA AKAN FARASHI MAI
RAHUSA, WANDA KOWA ZAI IYA YIN TSARIN DAI DAI ALJIHUN SA_
_Ranonet.com.ng_
_GA SITE DINMU NAN DAKE YANAR GIZO, KAI TSAYE ZAKI/KA IYA SIYAN NAKA TA NAN. _
_KO A TUNTUBE MU TA NAMBAR TARHON MU: +234 803 081 1300/+234 808 540 5215_
_KYAU, INGANCI, RAHUSA, ADADE ANA YAWO A YANAR GIZO SAI RANO NET._
_RANO NET..!!!!_
________________________________
Gaba daya ya danne fiye da rabin jikinta,da sauri cikin cool voice dinsa
yake fadin
"Calm down....calm down" saidai ina kunnuwanta ma basu iya jin me yake fada
ba,burinta kawai tama ture koma wanene,ganin ta kasa gane me yake fadi,saiya sa
hannunsa guda daya ya kama habarta ya riqe,cikin daga murya ya sake fadin
"Wakeup mana...nine fa,ke....ke!" Sai a sannan ta dauki muryarsa,gabanta yayi wani
mummunan faduwa,saita tsaya cak da ihun data soma,yayin daya tsaya shi kuma yana
kallon fuskarta na wasu sakanni,ganin ta tsaya yasa ya zare jikinsa a hankali ya
miqe tsaye,har yanzu bata bude idanun nata ba,saidai ta mirgina daya side din ta
yadda zata juya masa baya,tana jin yadda bugun zuciyarta ya dadu,hakanan qirjinta
ya qara riqewa,tana fidda numfashi a hankali
"Ki tashi kiyi sallah" ya furta yana ficewa daga dakin.
Hancinta ta ringa budawa tana jin yadda qamshin turarensa ya kama jikinta
adan shigarsa dakin,babu niyyar wanka a tare da ita,amma tasan cewa dole ta rabu da
rigar,idan ba haka ba ba zata daina jin qamshin turaren ba,hakan yasa ta fidda
rigar ta hada ruwan wanka tashiga.
Yana fidda kayan jikinsa zuwa na motsa jiki yana jan tsaki kadan
kadan,tunanin yaqi barin ransa,me yasa bai qyaleta ta fadin ba?,da ba zata qara
irin wannan kwanciyar ba,me yasa ma ya damu saiya gyara mata kwanciyar?,haka nan ya
gama shiryawa cikin riga armless da wando iya gwiwa,wanda hakan ya sake fidda qirar
jikinsa ta qaqqarfan namiji,da sassarfa ya fita daga dakin,yabi ta falo ya bude
wata qaramar qofa data sadashi da dakin motsa jikin.
Babban daki na gym wanda ya hada duk wani nau'in qarafa da na'urori,kai tsaye
ya haye saman daya daga cikin kayan motsa jikin,yanayi yana sauraren labaran duniya
daga babbar tv din dake manne a dakin,daga wancan channel din idan sun gama ya juya
zuwa wata,a haka sai daya shafe kusan awa daya da rabi sannan ya sauko ya ciro daya
daga cikin towel dake rataye a dakin ya soma goge gumin jikinsa yana zama kan wata
cushion chair dake dakin,sai daya huce sosai sannan ya dauki ruwa ya soma sha,yana
duba wayarsa da bai jima da kunnata ba.
Minti goma sha biyar a haka sannan ya fito daga dakin,zuwa sannan ya tadda
falon fes dashi,daidai lokacin kukunsa dake dauke da warmers guda biyu a hannunsa
da alamu girkin safe yake hadawa ya fito daga kitchen,cikin matuqar girmamawa ya
zube yana gaidashi,ya amsa mishi yana yin gaba,sai kuma ya dakata ya dawo da baya
yana dan wani nazari,yana ganin ya kamata ya dakatar da williams da Andrew,ya cansu
da mata,duk da cewa shi din yafi jin dadin aikin mazan
"Williams" ya kirashi
"Yes sir" ya fada da sauri yana aje kwanukan hannunsa saman table din,sannan ya
garzayo da sauri ya zube a gaban haidar din
"Inason na dan baka hutu na wata daya,ba don ka yimin wani abu ba,bayan wata dayan
zanyi magana dakai saika dawo,ka jirani na shirya idan na fito zan baka abinda zaka
riqe na wata gudan kai da andrew" sosai hankalin William ya tashi,don kowa fadi
yake yayi sa'ar gidan aiki,ya kuma yi sa'ar uban gida mai kyauta da tausayi
"Sir....ina fata dai ba wata matsala bace?" Hannunsa ya kada
"Eh....kada ka damu,zaka dawo bayan wani lokaci"
"To na gode mai gida" ya fada cikin nuna girmamawa,yanajin dadi daya kasance ba
wani abu ya aikata ba da zai rabashi da gidan,daga haka aliyyun ya wuce shi kuma ya
kama wajen dining din yaci gaba da gyarawa.
Tunanin da take ne yasa bataji tahowarsa ba,sai qamshin turarensa daya cika
mata hanci,hakanne ya ankarar da ita ta daga kanta,ashe tsaye yake a wajen yana
buda kwanukan gami da duba abunda aka dafa din.
Sanye yake da wata fara qal din shirt cotton mai gajeran hannu,sai wando
three quarter shima fari tas dashi,hakama slipper din qafarsa,duk wanda yasanshi ya
sanshi dason farar tufa tun asali,saita ajjiye cup din hannunta tana fadin
"Ina kwana?" Ba yabo ba fallasa ya amsa,saidai bai dubeta ba,kana yaja kujera ya
zauna ya fara kurban tea din shima.
Zata bar wajen yana duba uban saqonnin taya murna da suka cika mishi waya,yana
amsa wasu wasu kuma ya wuce,don yawan saqonnin da 'yammatan sukayi mishi ma yasa sa
yaga alamun mace bai budewa saiya wuce gaba
"Ki zauna ki rubuta duk abunda zaki iya buqata" ya fada a taqaice,saita amsa tana
yin gaba,ta qarasa wajen wayarta zata dauka,dai dai sannan Williams ya buda qofar
kitchen din zai fito,haidar dake cin chips ya kalli qofar ya maida idanunsa ga
farantinsa,sannan yace masa ya koma ya fita ta baya,ya jirashi a waje zai sameshi a
can,a ladabce ya amsa ya maida qofar ya rufe din.
Tana cire wayar saiga kira ya shigo,dr nasreen ce wadda tun a jiya sukayi
musayar numbers na juna,sai taji taji dadin kiran nata,don haka ta wuce da a
hannunta zuwa daki.
Minti biyar minti goma ashirin talatin awa daya biyu uku shuru dr nasreen
bata kira tace komai ba,hakan sai yasa hankalinta ya kwanta taci gaba da sabgarta
cikin dakin.
Cikin awa ta hudu taji ana knocking a qofar falon,saita share saboda tana
tsammanin yana cikin gidan,jin knocking din na sake daduwa saita aje wayarta ta
miqe.
Shuru falon babu kowa,saman table dinma babu komai duka an kwashe,dauke
idonta tayi ta isa qofar ta bude,macace a tsaye sanye da uniform na sojoji,fara ce
'yar tsamurmura mai qaramin jiki,gefanta wata ce sanye da kayan gida,saidai ita
waccan din tana da garin jiki,cikin fara'a suka soma gaidata,ta amsa musu fuska a
sake sannan suka fara mata bayani
"Oga ne ya aikomu,za'a shigar da kaya,sannan kuma idan kin shirya zamu kaiki"
matsawa tayi suka fara shiga da kayan abincine dasu lemuka da drinks,saidai kuma
bata gane idan ta shirya ba,don haka ta jawo wayarta saiga kiran dr nasreen
"Dear yace zakizo....amma fa ki hanzarta,wata takewa,daga ita saimu"
"Ok to" ta fada badon ranta yaso ba,dondai kawai bataso tayi wani abu dazai fallasa
abinda ke tsakaninsu ne da haidar din,sannan bugu da qari idan ta fitan ko banza
taga gari,ta huta da wannan zaman kurkukun data wuni yi.
Babban gurine wanda kana kallonsa kasan ya tattara mata masu aji da
wayewa,tana shiga masu karbar custumers suka tareta,ta tambaya inda dr din take
suka mata jagora.
Dr nasreen din tace a fara yiwa,tana ta addu'ar Allah yasa lokaci ya qure
kafin azo a kanta,don har ga Allah bata so,saidai addu'ar tata bata ci ba,nan da
nan aka gama yiwa dr din akazo kanta
"Lite makeup pls sis" ta fadawa me yi mata kwalliya
"Ok" tace tana gyada kai.
Cikin qalilan din mintuna saiga zahran kamar an sauyata da wata ne,bakin dr
nasreen yaqi rufuwa,cewa take
"Kefa kada ki bada 'yan maza yau,wallahi kada kisa oga haidar yayi abun kunya gaba
mutane,kinganki kuwa?" Murmushi kawai tayi bayan ta kalli fuskar tata a mudubi
itama,tana sake dubawa nasreen din ta aje mata wata leda gabanta
"Ga kayanmu da xamu saka.....tunda ba'a gayyacemu biki ba da dear yacemin sun hadu
dasu hajja tace masa kinzo na tanadar mana don mu saka iri daya...."
"Kai kai,duka dai dr?"
"Haba babu komai,mu saka sai suyi mana dauri,don naga tex din dear yace suna hanya"
tayi maganar tana ware zaninta.
Wani irin lace ne mai azabar kyau da daukar idanu butter colour,dinkin da
aka masa yayi masifar dacewa dashi,hakanan zahran kamar don ita aka dinka shi,kamar
yadda ya zaunawa dr nasreen din sosai itama,sai duka kallo ya koma kansu sanda aka
gamawa nasreen dauri aka fara yiwa zahra nata.
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: 29
_*YERWA INCENSE & MORE**_
_(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_
_(MASARAUTAR KAMSHI)_
_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma
da ingataccen had’i yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa..._
_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_
_carpet spray_
_air-fresheners_
_scented pebbles_
_body sprays_
_oil perfumes_
_Perfumes_
_kabbasa_
_burners_
_coal igniter_
_tong_
_kasko_
_kujerar tsugunno_
_english coal_
_dilke&halwa set_
_scented body mist_
_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata ba, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura
kayayyakin su ko’ina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram:
_@yerwaincense_and_more. Ko _Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta
number su: ___08095215215/09044191709! _
Dai dai sanda aka gama kira ya shigo wayar dr nasreen,ta dauka da hanzari
"An gama dear....gamu nan" saita sauke wayar tana duban zahra
"Ke....oganki ya matsu....yanata mita,muje" duk yadda zahra taso dr nasreen ta
barta ta biya kudin kwalliyar qememe taqiya,haka ta biya sannan suka dauka kayansu
suka fito.
Yaja saki gami da kallon agogon hannunsa yafi a qirga,idan banda kada jafar
yaga kamar ya watsa masa qasa a idanu baiga abinda xai dakatar dashi xaman jira
ba,shi totally ma bai shirya zuwa wajen dinner din ba gaba daya,hakanan yakejin
baison yadda matansu ke karakaina a tsakiyarsu,sai yakega sam hakan bai dace ba.
Karo na qarshe daya kalla agogonsa,ya yanke ma ransa indai basu fito ba
zaiyi tafiyarsa ne,saidai shi jafar din da ya daurewa qaryar zuwan qarqashi ya
daukosu,ya daga kai da niyyar duban bakin qofar,saiya hangi fitowarsu sun jero a
tare,dauke idanusa yayi daga kan dr nasreen ya maida kanta,murmushi ne kwance saman
fuskarta,har fararen haqoranta na bayyana,da alama wata magana dr nasreen din ta
fada data bata dariya.
Janye idanunsa yayi ya maida daya side din,har cikin zuciyarsa yaji inda ya
maida din baiyi masa ba,ya sake canza waje,nan ma yaji baiyi masa ba,saiya dauke
idonsa ya kuma maidawa inda suke tahowar.
Zuwa yanzu sun iso dab da motocin,kana iya ganin fuskokinsu tarwai ta hasken
fararen qawayen da suka haske wajen,haka kawai ya samu kansa da xubawa fuskarta
idanu,wane sashe na ranshi yaji yana baci ba tare da yasan dalili ba,saiya dauke
idanunsa daga wajen,yama rufesu gaba daya sanda take qoqarin bude gidan baya ta
shigo.
A tunaninta yana gaba,sai data shiga ta zauna ta maida murfin ta rufe sannan
ta lura dashi,duba daya tayi masa ta kauda kai,kamar mai bacci,saidai kuma yanajin
komai,fuskarsa kamar ko yaushe a hade dai,tabe baki tayi cikin ra ta tana mita,tana
kallo motarsu dr nasreen ta wuce gaban tasu kadan,sai suma suka tsaya,dai dai
sannan wayarsa dake aje tsakiyarsu ta dauki kuwwa.
Bai buda idanun nasa badai still ya laluba hannunsa ya dauka ya kara a
kunne,murya can qasa taji yace
"Kuje kawai" sai kuma yayi shuru yana saurare na sakannin da basu wuce biyar ba
sannan ya kuma magana
"Banjin zamu iya zuwa" still dai wayar tashi tana kunnensa na wasu sakanni,da alama
akwai abinda ake gaya masa,saiya sauke wayar,ya bude idanunshin kana ya shiga ya
rubuta gajeran sms ya tura sannan ya maida wayar inda take,shi kuma ya gyara
zamanshi,kamar wanda dama can ya shiryawa zaman cikin motar ne.
A qalla sun kusa minti goma a tsaye anata kira yaqi dagawa,yayin da zaman ya
ginshi zahra,ji take kamar ta fita a motar ta bashi waje,don batasan ma'anar zaman
ba,shi bai bada umarni a tafi ba,shi bai maidasu gida ba,a haka ta hangi fitowar
jafar ya doso motarsu.
Knocking din glass din side din haidar yayi,saiya sauke glass din yana
dubansa,hannayensa ya hade waje daya yana murmushi
"Am sorry boss,we apologize you.....madam ma tace a baka haquri a madadinta"
bakinsa ya bude zaiyi magana jafar din yayi saurin tararsa
"I know....i know...ka share kawai,yau ne fa,just some few hours an gama an wuce
wajen" bai sake cewa komai din ba,saiya dage glass din kawai,jafar din ya koma
motarshi,shi kuma ya bawa drivern umarnin jansu,zahra na gefe tana gulma ita da
zuciyarta
"Me shegen baqar zuciya...kome akayi masa oho,ni dama ya fasa zuwan ai gaba ta
kaini,mtsewewww" tsakinta na qarshe ya fito fili ba tare data sani ba,saiya waiwaya
ya dubeta,suna hada ido kowa yayi saurin janye qwayar idanunsa,ta tsammaci zaice
wani abu ko zai tanka,saidai babu abinda yace,haka suka ci gaba da zaman kurame har
suka isa wajen taron.
Kowacce na fitowa daga mota ta nufi 'yar uwarta,tun kafin ta qaraso taga
nasreen na danne dariyarta,saida tazo gab da ita qasa qasa tace
"Allah ya somu,da tuni muna gida yanzun,ashe kishin 'yan maza ne ya motsa,to da
heavy makeup akayi miki kenan zuciya zai hadiya?,wannan kwalliyar da ba wani abu
aka qara miki ba sosai,abar da aka yita sama sama,lallai sai yanzu na sake gane
aliyyu,yana da abun ban mamaki" jin zancan zahra tayi wani banbarakwai,dama abinda
ya tsaidasu kenan?,lallai nasreen batasan waye ya haidar din ba,ba wani kishi,kishi
a ina?,zallar iya mugunta ce kawai irin tashi data motsa,amma a sarari sai kawai
tabi dr da murmushi.
Cikin hakanne ta lura da wata qabila cikin kakin soja,da alama ita sojan
ce,tana ta bibiyar aliyyun a gindi a gindi,duk inda ya sanya qafarsa,saidai babu
alama ko daya data nuna yasan Allah yayi ruwanta a wajen,haka kawai ta dinga jin
qunci da rashin dadin xaman wajen,har zuwa sanda dr tace
"Tabdi....wato dai tawa ba zata haqura ba.....zahra....see dis woman" ta fada tana
nunata da yatsa,sanda aliyyun ke tsaye yana amsar wani award da qananun sojoji suka
bashi da certificate of honour.
Cikin lokaci kadan bayan an gama ciye ciye wajen ya soma hargitsewa,kowa na
hoto da familynshi,walau matarsa kawai ko kuma da yaransu,wanda yara daya zuwa biyu
dama aka bayar da damar zuwa dasu.
Dai dai sannan jafar yazo ya janye nasreen dinsa,saiya zamana inda take din
ita kadai ce zaune,hakan ya bata damar nutsuwa tana bin kowanne abu dake faruwa a
wajen da kallo a nutse,gefe daya tana jin yadda qirjinta keson ya dawo da ciwon da
yake mata data samu dazun ya lafa,wala'alla kodon tun tea din safe bata sake kai
komai bakinta bane.
"Bakaga mutuniyar bane?taawaa" Saif dake tsaye kusa da haidar ya rada masa
a kunne dariya na taso masa,baice masa ci kanka ba,saidai yana sane da yadda take
binsa din,ya tsani matar sosai,saidai ta rufe ido ta kasa fahimtar hakan,yakanji
wani lokaci kamar yayi mata dukan tsiya,saidai ba dabi'arsa bace,hasalima yana
kallon duk wani namiji da zai daki diya mace a tsayin wawa mara tunani kuma lusarin
namiji,wanda ya kamata a kama ayita duka sai an jigatashi,yadan waiga suna magana
da wani suka hada ido da ita,ya daure fuskarsa,bayason naci ko kadan a
rayuwarsa,dama daya ce ta rage masa da xaiyi amfani da ita ya koreta kwata kwata
daga dukkan sha'aninsa,yanzu kuwa zaiyi amfani da damar,saiya soma takawa yana
lalubar inda take zaune da idanunsa,yayin da taawaa taci gaba da binsa a baya,tana
tsammanin zai fita ne daga jama'a ta bisa ta fake da yi masa Allah ya sanya
alkhairi wanda ta tura masa saqonni ta email dinsa sms da WhatsApp dinsa sunfi guda
nawa amma bai amsa ko guda daya ba
Can ya hangota sanda saurayin ya sake dawowa yana tambayarta zai kuma daukar
kujera daya kamar daga gidansu tazo da ita ta raya cikin ranta,saidai banza tayi
masa bata ko kalleshi ba bare ta kulashi,ganin hakan yasa ya dauka yayi gaba,Aliyyu
ya bishi da idanu yana bibiyar inda zai zauna,saidai tuni ya bace cikin mutanen
dake kai kawo a wajen,wani abu ya hadiye har ya isa inda take zaune.
Hannu kawai taga an miqo mata,ta daga kai don ganin waye,sai tayi arba
dashi da kuma tawakkalt dake tsaye daga bayansa,duk da fuskarsa a dinke take
tsaf,saidai wadda ke bayan nasa bata iya hangen hakan,cikin second ta karanci
komai,saita daga nata hannun ta sanya cikin tafin hannunsa da yake miqo matan,saiya
maida hannun nasa ya rufe,ya runtse hannun nata tsakiyar nasa,wanda hakan ya sanya
tsigar jikin kowannensu zubawa,dumin da tafin hannunta ke dashi ya ratsa duk wata
jijiya ta jikinsa cikin sakanni,saiya dagota yana cewa
"Am sorry.....na barki ke daya ko?" Yanayin yadda ya dagotan gaba daya kamar wadda
ya fusgo cikin salo yasa babu yadda zata iya tsaiwa da qafarta dole saidai ta fado
gaba,shine kuma tsaye a gabanta,don haka jikinsa ta fada gaba daya,saiya sanya
hannayensa ya riqe qugunta,a hankali cikin salo na rada yace mata
"Just a plan....karki zurfafa da yawa".
Rasa abun cewa tayi saboda gaba daya a rude take,jikin ya Aliyyu?,ya
haidar yau itace rungume cikinsa?,kuma unexpected?,sannan uwa uba yadda taga nan da
nan idanun wasu sunyo kansu,da alamu dama tun dazun suna bibiyarsu ne
"Nasan da zaman kowanne....and i want expel them daga rayuwata".
Gaisaw yaci gaba dayi da mutanensa,kusan duk wanda ya gansu tare saiya
tsaya,duk wani taku da zasuyi jikinsu na gogar na juna,hakan ya dinga weakening
dinsu gaba daya ba tare da kowa ya sani ba,wanda kafin wani lokaci zahra ta rasa
duk wani qwari daga jikinta,kusan riqon da yayi mata shike riqe da gangar
jikinta,wannan shine karon farko data fara raba jikinta da wani da namiji,kamar
yadda shima yake karin farko a rayuwarsa.
Hakan da yayi ba qaramin kada da yawa daga mutanen da yakeson kadawar yayi
ba,a hankali yaga fuskokin suna canzawa,wasu kuma suna zamewa daga wajen,ciki harda
taawa din data rasa inda zata tsoma ranta,ganin har a lokacin tana cikin
jikinsa,hakanan duk inda zai zagaya tana tare dashi.
Da gaske yake bazai saketa a yanzun ba,riqonshi a gareta wani abune na daban
da bata saba dashi ba,so take ya saketa ko zata rage wani abun,duk inda ya dora
hannunsa a jikinta tana jin saqon saukar hannun har cikin qasusuwanta,kamar wanda
keda wani abu na musamman cikin tafin hannunsa
"Cikina" yaji ta furta kalmar a hankali,saiya waiwaya ya dubeta kadan,suna hada
idanu saita lumshesu,sam ya zuwa yanzu batason kallon qwayar idanunsa
"Ok" ya fada bayan ya dauke idanunsa daga ka ta na wasu sakanni,a hankali yayi
niyyar zameta,saita tafi talau saboda yadda da gaske qirjinta ya riqe da ciwo,bai
zaci haka ba cikin zafin nama ya riqota ta dawo jikinsa
"Are you serious?"kanta ta daga masa a hankali sanda take kwance a qirjinsa tana
sauke numfashi,idanunta a runtse gam,hancinta na cika da qamshin turarensa,dumin
jikinsa na ratsa fuskarta,tana iya juyo bugun zuciyarsa sosai
"Ok....ok" ya fada a hankali yana dan duban fuskarta dake cikin qirjinsa yana
tunanin yadda zaiyi mata zuwa mota.
"Bani hannunki" ya fada calmly cikin qarfin hali,saita miqa masa hannun ya
sake matseshi cikin nasa a hankali yana jin yadda tsigar jikinsa ke tashi tun daga
qwaqwalwarsa zuwa gangar jikinsa,wanda sam baisan yaushe ya samo irin wannan
feeling din ba,sai suka fara takawa a nutse har zuwa bakin motar.
_IDAN KAJI GANGAMI DA LABARI....! INA MASU ZUBIN ADASHEN DA BA RANAR DAUKA NA DATA?
_
_TO KU MARMATSO KUJI, KU KUMA SHARE HAWAYEN KU, MUNZO MUKU DA SABBIN TSARE TSARE NA
DATA, WADDA KOWA ZAI IYA SAYA DAI DAI KARFIN SA. A FARASHI MAI RAHUSA_
_TSAYA KUJI, A RANO NET ZAKA IYA ZAMA RESELLER KO WHOLESALER KAI MA, EH ZAKA/KI IYA
ZAMA MA SAYAR DA DATA A FARASHIN SARI MUKE BAYARWA, KAI/KI KAFA KASUWANCIN KU KUMA.
DA KUDI KALILAN._
_MUNA KUMA SAYARWA AKAN ‘DAI DAYA, KOWANE NETWORK MUNA SAYARDA DATA PLAN DINSA AKAN
KUDI KALILAN, MASU FARASHIN SARA KUWA MA KU KUDIN BAI KAI HAKA BAMA_
_AIRTEL_
_9MOBILE/ETISALAT_
_MTN_
_GLO_
_DUK MUNA SAYARDA TSARIN DATA DINSU. KAMAR MISALI MTN MUNA SAYARDA 1GB.24MB AKAN
FARASHIN NERA 300 KUMA YANA KAIWA WATA DAYA, GWARGWADON YADDA KAKE AMFANI DA DATA,
2GB 600, 3GB 900!!_
_DUKA WADANNAN TSARIN DATA DAMA NA SAURAN LAYIKA MUNA SAYRWA AKAN FARASHI MAI
RAHUSA, WANDA KOWA ZAI IYA YIN TSARIN DAI DAI ALJIHUN SA_
_Ranonet.com.ng_
_GA SITE DINMU NAN DAKE YANAR GIZO, KAI TSAYE ZAKI/KA IYA SIYAN NAKA TA NAN. _
_KO A TUNTUBE MU TA NAMBAR TARHON MU: +234 803 081 1300/+234 808 540 5215_
_KYAU, INGANCI, RAHUSA, ADADE ANA YAWO A YANAR GIZO SAI RANO NET._
_RANO NET..!!!!_
___________________________________
Yadda yaji numfashinta na sauka a hankali cikin nutsuwa ya tabbatar masa da tayi
bacci,hannunsa yasa zai sauketa saita motsa,hakan yasa ya fasa ya maida hannunsa ya
ajiye,tsahon minti biyar ya sake daga hannun nasa zai sauketa,hakanan wannan karon
a karan kansa yaji ya kasa,saiya sake maida hannun nasa ya ajiye yana maida
numfashi gami da runtse ido,wani irin yanayi yakeji cikin jikinsa,irin wanda tunda
yake bai taba jinsa ba,wani nauyin jiki da kasala yakeji,minti daya biyu saiya
kalli fuskarta,duk da baya iya ganinta sosai saboda fuskar na kife a saman wuyansa
ne,gaba daya jikinta dake manne da nashi ya soma takurashi gami da rikita masa
lissafi.
Yayi tsammanin zai jure amma saiya kasa,don haka tilas tasa ya zameta daga
jikin nasa cikin dabara,ya koma gefe yan furzar da iska daga bakinsa,ya kuma kulle
idanunsa,sannu a hankali jikinsa ya soma nauyi shima,bacci ya qara maaa rauni da
kasala,saiga bacci ya fisgeshi ba tare daya sani ba.
A nutse ta sauka daga gadon zuwa bandaki tana tuna abinda ya wakana daren
jiyan,dukka jikinta babu abinda yake sai fidda qamshin turarensa duk motsin da
zatayi,duk sai taji wani irin kunya da nauyinsa sun saukar mata wanda bata taba ji
ba sanda ta tsaya gaba madubi ta tuna shi ya cire mata bra,ita kadai a bandakin
amma sai ta dinga ji kamar yana kallonta,tasa hannu ta cukuikuye rigarta ta nufi
gaban sink ta daura alwala sannan ta fito.
Tana fitowa daga bandakin sanda ta miqa hannunta ta baya tana rufe qofar
toilet din shi kuma yana shigowa,kai tsaye idanunsa suka sauka a kanta,rigar
jikinta ta kwanta sosai a fatarta,ta yadda duk wanda ya kalleta yasan babu brazier
a jikinta,hakan ya baiwa albarkatun qirjinta damar tsayawa sosai kowanne a
muhallinsa.
Kamar wanda aka sanyawa shocking haka yaji,ya dauke kansa da wani irin sauri
yana qarasa shigowa ciki ya kuma nufi kan gado kai tsaye,yayin da ita kuma ta qame
a tsaye cukuikuye da gaban rigarta,gabanta na wani irin faduwa saboda lura da tayi
da inda yake kalla din.
Saman katifar ya haura,ya dage filo ya dauki wayarsa,da alama ita ya manta
ya dawo dauka,saidai yana miqewa yaci tuntube da breezier dinta,saiya janye qafarsa
a hankali ya sauko ya fice.
Da sauri ta qarasa ta sakawa qofar key tana sakin numfashi,wai wannan wane
irin abun kunya ne haka,sai data kusan makara sannan ta samu tayi sallar bayan ta
tattare katifar.
Har wajen sha daya saura na safe tana dakin bata fita,duk da tayi
wanka,amma nauyin haduwa dashi yasa ta kasa fita,uwa uba kuma mararta daketa qulle
mata,addu'a take Allah yasa kada period din yazo sai ta koma gida.
A hankali ta bude qofar sanda taji anyi knocking,saita labe daga bayan
qofar ta yadda bazai iya hangota sosai ba,haka itama.
Haka taci gaba da raba idanu da tunanin me zatayi,tana jin kuma yadda jinin
ke flowing a jikinta,har zuwa sanda ya aiko mai gadi ya tsaya daga qofar falo yace
mata ta fito inji oga,saidai tashin ya gagara,don ta tabbatar ba jikinta kawai
ba,har kujerar da take xaune a kai ta baci.
Zabura ta kusa yi sanda ta tsinci muryarsa daga bayanta,ta waiwaya a
hankali ta dubeshi,qwayar idanun nashi ne masu nauyi samanta yana dubanta
"Karki batamin lokaci fa...." Abinda kawai ta iya ji kenan daga bakinsa,bata da
wata sauran dabara kuma,don haka ta miqe kai tsaye kawai ta tsaya cak ba tare data
iya ce masa komai ba.
Tana tsaye waje daya a tsakar dakin tana tunanin me zata saka ta tare?,ko
dankwalinta zatayi amfani taji an turo qofar dakin,duk sai ta duburbuce,ta rasa
inda zata boye kanta.
Shi dinma dai kamar dazun,inda idanunsa suka sauka daxu yanzu ma haka
"Ya salam" ya fada yana aje mata ledar gamida juyawa yabar dakin,annan wanne irin
jarraba ce yakeson dorawa kanshi?,wani mugun haushin kansa ya kamashi,yaja wani
dogon tsaki kamar zai tsinke harshensa,ya shiga motar yana rufe murfin da qarfi
kamar ita tayi masa,sumarshi yaje shafawa da hannu daya yana furzar da iska daga
bakinsa,can cikin zuciyarsa kuma yana jawa kansa warning,tare da son gayawa kansa
da zuciyarsa hakan bazai sake maimaituwa ba.
Sai daya fita taja ledar ta som duba abinda ke ciki,pad ce da pants masu
yawa,wanda tasan sundi qarfin buqatarta na dan lokaci,sai ta cira wanda zatayi
amfani dashi,ta dora ledar saman akwatinta sannan ta bareta ta saka,tayi mamakin
yadda akayi size na pant din yayi mata dai dai.
Tafiyar kurame dai sukayi kamar kullum,har suka isa ginin da kallo daya tayi
masa ya gaya mata asibiti ne,private asibiti,daga yanayin tsarinsa da gininsa kadai
ya isa ya gaya maka kudin da ake lasa na marasa lafiya,saidai kulawar da suke baiwa
mara lpy ya cancanci kudin da suke karba.
Da alama nan yake zuwa idan yana garin,duk da cewa akwai na sojoji,saidai
wala'alla kayan aikinsu da ma'aikatan ne basuyi masa ba.
Tare suka shiga ganin likitan,yana tsaye ta gama bayani ya rubuta mata
magani,da kansa ya tsaya a pharmacy na asibitin ya amshi maganin.
Ita kam komai yayi mamaki yake bata,tamkar ba ya haidar din data sani
ba,bata taba kawowa ranta akwai ranar da zatazo ta samu koda kallon mutunci sau
daya ba bare akai ga kula da lafiyarta.
Bayan sun baro asibitin saiya tsaya a wani babban kanti yayi musu siyayya
bisa radin kansa,ya zaba abubuwan da yake tunanin zata iya buqata sannan ya dawo
suka tafi.
*_washegari_*
Tun qarfe shida na safe ta kasa komawa bacci saboda yunwa da takeji,wani
lokaci ulcer dinta tana yi mata haka,sai ta sanyata jin yunwa kamar hauka,uwa uba
kuma zaman banza data gaji dashi,wanda daga kwanciya sai danne danne a waya,gaba
daya zaman ya gama gundirarta,babu wani abu na debe kewa.
Parlour din shuru babu kowa,saita wuce kitchen din kai tsaye,wanda wannan
shine shigarta ta biyu tunda tazo gidan,sai a sannan ta qare masa kallo,babu abinda
babu a ciki,babun ce kawai babu,hakanan komai atsare yake,da alama kuma tun
tafiyarsu hajja ba'ayi girki a ciki ba.
Da iya cikinta kawai tayi niyyar dafa abinda zata ci wanda bazai ja mata
lokaci ba,amma saita tuna gida,daga umminta har hajja basa gaba yin girki iya
cikinsu,dole sai sunyi da al'ummar annabi,da kuma wanda rabonsa ya tsaga zaici,data
duba store da fridge din kuma saita tadda akwai duk wani kayan buqata na amfanin
girki,zata iya dafa kowanne abinci,don haka ta diba duk abinda tasan zata buqata ta
fara sarrafawa.
Gas din waje hudu ne dashi,saita kunna biyu yadda komai zaifi mata sauri ta
dora,ganin bata da sauran abinda zatayi saita fara tattare kitchen din,duk da bawai
datti yayi ba,amma akwai qura na rashin shiga kwana biyun,data gama taga har yanzu
abunda ta dora baikai mata ta sauke ba,saita miqa falon.
Tas ta gyareshi,ta kuma gyara guraren da baiyi mata ba,dama wani aikin sai
diya mace,nan da nan sai gashi ya sake tarwai kamar an qara masa kyau,zuwa sannan
ta koma kitchen taga abunda ta dora yayin,saita dora da aikinta daga inda ta tsaya.
A gaggauce ya fito daga dakin yana sake kallon agogon da yake daurawa a
hannunsa,cike da mamakin yadda lokaci ya kufce masa haka yanata aikin bacci,sam
baisan lokaci yaja haka ba,sai daya soma jiyo qamshin girki a hancinsa,wanda da
farko ya zaci a mafarki ne,sai daya farka yaji cikin gidan ne,bai kawo zata shiga
kitchen ba,don haka ya barwa ransa daga maqota ne,abinda ya sanyashi gaggawar kuwa
daya tuna babu abinda zataci cikin gidan,jiyan dama nasreen ce ta kawo musu shi.
Ido suka hada dashi,saita dauke qwayar idanunta da sauri gabanta na faduwa
hakanan,sannan wani kyau taga ya mata a ido yanzun da yake sanye da wasu kaya,saita
koma takawa a hankali tana wassafa yadda zata wuce ta gabanshi,saboda yana tsaye
qyam ne,kuma dole ta giftashi,uwa uba ma kuma riga da skert din dake jikinta na
roba ce mai rawa,ya zauna yabi kowanne lungu da tudu na jikinta,kanta ne kawai keda
dankwali,shi kansa dan kwalin rabi ne,dukka sumarta ta baya da goshinta ana gani.
Sannu a hankali idanuwansa suka bar fuskarta data dan yi fayau saboda
ciwon kwama biyun da tayi,sai suka zarce suka sauka a muhallin da tun daxun yake
gargadarsu a kanshi,hannunsa ya damqe waje guda yana dauke idanun nasa daga
kanta,saidai shi kansa baisan yadda akayi ba yaji qarar faduwar flask din hannunta
a gabasa,gab da yatsunsa,saura kadan su sauka a qafarsas,sannan ta daki jikinsa ta
zame zata kai qasa.
Allah yasa ya rufu sosai,babu abinda ya zuba sai dan abinda ba'a rasa ba ta
gefen murfin,da sauri ta dauke ta nufi dining din qafafunta na rawa,ta dorasu
akai,ta yagi tissue tana goge bakin nasu,da zimmar bata lokaci har yabar
wajen,saidai duk yadda ta dinga laqai laqai din gamawa don ya tafi aikin banza
tayi,don sai jinsa tayi ya hauro wajen,yaja kujera daya ya zauna abinsa,fuskarsa a
dake kamar bada shi abun dazu din dazu ya faru ba.
Gaidashi tayi a gurguje tana bari wajen,saita fasa komawa kitchen ta dauki
abincin,ta fada dakinta kai tsaye.
Gefan katifar ta zauna tana maida numfashi,har yanzu tana jin dumin hannunsa
saman jikinta,sai takejin kamar bai dauke hannun ba,don haka ta koma rub da ciki ta
kwanta tana rufe idanunta tana kuma sauke numfashi ɗaya ɗaya.
Hanyar data wuce yabi da kallo sai data wuce,shima saiya sauke numfashi me
nauyi daga qirjinsa,baisan me yasa koda yaushe idan ta fito ko baiso saiya
kalleta,kamar wanda ake jan idanunsa da magnet,abinda sam ba halayyarsa
bace,hasalima yana daya daga cikin jinsan mutanen da suka tsani yawan kallo.
Sosai ya lodi abincin,duk da dama shi din ba baya bane wajen baiwa cikinsa
haqqinsa,to amma ya dade rabon daya zauna yaci abinci mai yawa irin haka,sanda ya
kammala ya duba agogonsa,yayi dai dai da lokacin da zai fita din,saboda meeting na
gaggawa da aka kirasu,ya miqe yana gyara tie din wuyansa yana dan duban qofar
falon,kamar ya shiga kamar ya fice,to amma idan ya shiga din me zaya ce da ita?,don
haka saiya doshi qofa kawai ya fice,ya samu drivernsa yayi ready shi yake jira,ba
bata lokaci suka fice daga gidan,dai dai sanda zahran ta saki ajiyar zuciya,ta miqe
zaune sannan ta tashi a kasalance zuwa kitchen don ta dauki nata abincin.
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: 33
Karo na qarshe da suka hada idanun saiya saki hannun nata,yaja mata kujera ya
mata nuni da idanu kan ta zauna a kai,a sanyaye kuma a hankali ta zauna din,saiya
juya ya tsugunna yana tsince barin da tayi,ya gyara komai,kawai sai tagq yaci gaba
da girkin
"Ya rabb..." Ta fada tana lumshe idanunta cike da zallar mamakin ya haidar din,dama
zai iya amsar mata girki saboda kawai ta qone?,sauqin kaine ko ganin dama?,saboda
dai su sun riga da sunsan halinsa,mai fada da kaushin hali shine tambarinsa a
wajensu,bata gushe ba tana binsa da kallon mamaki har sanda ya kammala,yana juyowa
suka hada ido,karon farko data ji wani abu me kama da kunya ya kamata,saboda kamata
da yayi tana kallonsa,sai ya basar kawai yana riqe da plate din ya miqa mata
daya,sauran kuma yayi hanyar fita dasu.
Komai yayi daidai,kamar ita ta zuba seasoning din,a hankali tana ci tana ci
sai gashi taci da dan yawa,ta ajjiye plate din tana duba hannunta,bai tashi ba har
yanzu saidai alamun quna,hakan yayi mata dadi,tasan kuma sirrin fatihar daya dinga
karanta mata ce.
Da kanshi ya dinga gayawa kansa akwai matsala,yana jin tsoron faruwar wani
abu,yana ga ya kamata ya maidata gida tun baiyi abun kunya ba,abun kunyar daya
tabbatar da cewa hajja saita masa tareren kaf dangi da 'yan uwa.
Bai taba yarda da zantukan abokansa ba sai yanzu,wani lokaci idan suna irin
wadan nan hirarrakin da suka danganci aure,yana dauka shirmensu ne kawai da kuma
batawa kai lokaci,har suna ganin ko lafiya ce baida ita?,saboda sun riga da sun
saba,dai daiku ne cikin wanda zai zama soja,ya kuma kai mataki da matsayin da
haidar din ke kai ba tare da yana mu'amala da mata ba ko kuma shaye shayen abubuwan
maye,sai gashi shi din Allah ya tsarkake shi,ya kubutar dashi,ko sigari baya sha
bare akai ga barasa da sauransu,game da mata kuwa bai ma tsaiwa ya musu wani dogon
kallo,ko yayi dogon nazari a kansu da zaya dami rayuwarsa,hakan ya kawo masa sauqin
al'amuransa sosai,ya kuma sake kauda masa duk wani abu game dasu,duk da yasha
tsallake tarkunansu,saidai suma suna kama kansu saboda sunsan halinsa,bashi da
sauqi sam.
Yana gama cin abincin yayi wanka ya fice,bai dawo ba sai gab da
magariba,ganin an kusa kira saiya daura alwala kawai,da niyyar idan ya dawo yayi
wanka,sannan ya leqa yaga hannun nata,ya kuma nema musu abinda zasuci,saidai yayi
mamaki da yazo tafiya sallah yaga kwanuka kan dining,harta samu qarfin halin yin
girki kenan.
Tana dakin taji dawowarsa,saidai bata sa sha'awar fitowa don ta gama duk
abinda tasan zai maidata falon,ana kiran sallah ta shiga wanka,ta fito ta shirya
cikin hight waisted skert ta shirt mai gajeran hannu wadda ta dace da skert din,ya
fidda qugunta sosai tare da plate tummy dinta,gashinta ta taje sosai wanda ta
tsefeshi saboda tana period,yawanci haka takeyi,saita tsefe idan zatayi wankan
tsarki ta wankeshi sannan a maida mata kitso idan tana ra'ayi.
Kamar daga sama taji sallama a falonsu,saita aje comb din hannunta da take
kwantar da gashin nata cikin sauri ta bude qofa ta nufi parlour din.
Sai data cikata da kayan ciye ciye sannan ta dubeta cikin mamakin me yasa
har yanzu bata zauna ba
"Zauna mana kinata tsaye haka?" Murmushi tayi ta girgiza kai
"Ai banga ta zama ba,dear tana waje fa a tsaye" ido zahra ta fitar
"Kai!,ya shigo mana,me yasa kuma zai tsaya a waje" kai ta girgiza tana qwalalo ido
"Ah wai....ai bazai shigo ba,yasan fa waye mai gidan nan,wannan boss din naki akwai
ban tsoro,yasan halinsa sarai....,ki fara shaida masa dai yana da baqo ko?" Saita
dan daburce,tana nufin ta shiga dakinsa kenan ta masa magana,tunda ta tabbatar yana
dakin tunda ya dawo gidan,dakin da tunda tazo bata taba gigin shigarsa ba,batason
tace wani abu da zata dago kome ke tsakaninsu,don haka cikin fara'ar yaqe tace
"Yanzu kuwa zan sanar mishi,ai ba'a bar masoyi a waje ba" tayi qarfin halin
tsokanarta,sai ta sake fadada fara'arta tana cewa
"Kema kya fada,shi yasa na kasa zama ai".
Inda zai yiwu zata faki idanun nasreen ne taje ta sanyo hijabi,to amma yin
hakan zai sanya ta saka mata ayar tambaya,dole qanwar naqi tayi qundunbala takuma
yi shahadar quda ta durfafi dakin.
Fitowarsa daga wanka kenan daure da towel iya qugunsa,yana tsaye gaban
mudubi yana sharce ruwan jikinsa,duk da cewa daga wanka ya fito kuma a tube yake
amma ac ke kwarara cikin dakin,kamar baya jin yawan da tayi.
A hankali ta bude qofar dakin ta saka kai,ta daga idanunta a hankali tana
wulgasu cikin dakin,saiko suka sauka a kansa yana taje kansa da wani cumb,idanunsa
cikin madubin yana kallota,ko kadan bata tsammaci samunshi a yanayin data ganshi
ba,yanayin qira da duk wata siffa ta jikinsa ta fito muraren,mai tsayayyen jiki da
siffa dake nuna qarfi da mazantaka,da kuma alamun ya horu sosai kan aikinsa,kana
ganinsa kasan yana daga qarfe.
A nutse yake qare mata kallo tun daga yatsun qafarta har zuwa kanta dake
gyare cike da baqa qirin din suma,fuska a hade yake dubanta
"Uhummm....,me yasa ko yaushe kike firgita kanki?,tell me,meke baki tsoro a
jikina?" Gam ta rintse idanunta,don har ga Allah ba zata iya kallonshi a yadda yake
tsaye a gabanta ba,don ita a wajenta bashi da maraba da tsirara,gashi hanya takeso
ta samu ta tsere,saiya kada yatsanshi saman fuskarta
"Niba dodo bane?....kinji ni?" Kai ta gyada,sotake kawai ya bata waje ta fita,amma
a maimakon haka ma sai taji yana saka lock na jikin qofar yana rufe qofar,saita
bude idanunta da sauri,sai kuma ta sake kauda kai,cikin rawar murya tace
"Pls....zanje wajenta....jira take" baiko bi ta kanta ba yayi gaba abinsa,ya bude
ma'ajiyar kayansa ya dauko wanda ya dace da ra'ayinsa,ya dawo gaban mudubin yaci
gaba da shiryawa,tilas taci gaba da tsaiwa tana jiran tsammani,saidai kuma ta bashi
bayane tana duban qofa,hakan ya bashi damar qare mata kallo,lokaci lokaci,yana
dubanta yana shiryawa.
Ta taras suna gaisawa da nasreen din,daga yanda suke gaisawa kawai ya isa
ka gane tana ganin girmansa sosai,cikin 'yar dariya kasancewarta mai yawan
barkwanci tace
"Ai cewa dear nayi yazo muje dubiya....Allah yasa qaruwa muka samu" dan murmushin
gefan baki kawai yayi,saidai ya maida dubansa ga zahra,sannan yace
"Wata qila,gatanan kya tambayeta" saiya miqe yana ficewa daga falon.
Tunda ya isa farfajiyar gidan yaga tare suke da major ya sake tamke girarsa
sosai,duk da cewa akwai saif a wajen
"Yallabai....irin wannan shanyamu haka?" Major ya fada yana washe baki,wani kallo
haidar ya masa sanda yake bawa jafar hannu suna gaisawa,sai da yazo kansa sannan ya
amsa mishi
"Da kasan kana da abubuwan yi da yawa ma da baka zo ba,incase nan gaba kaga irin
haka ka dinga tafiyarka kawai" saif dai na danne dannen waya yana boye
dariyarsa,shi yasan qarshen alewa qasa,don major ya dage ne kawai saiya biyosu,amma
yasan haidar din bazaiyi maraba da zuwanshi ba,jin amsar daya bashin sai yayi shiru
baice komai ba.
Daga nan inda suke tsaye haidar din ya qwalawa mai gadi kira,ya bashi
umarnin bude guest room sannan suka dunguma zuwa ciki.
Yana fita saif ya qyalqyale da dariya yana kallon yadda haidar din ya hada
girar sama da qasa
"Mai master....wannan wai duka kishin ne haka?,lallai fatima ta ciri tuta...wannan
so ba qarami bane" dashi da saif din duka sunsan magana yake gaya masa a
fakaice,saiya masa wani irin kallo ya bude baki
"Sosai,ko laifi ne hakan?....akan me ma zaku daukomin wannan kwarton ku shigomin
dashi gidana....kai J,haka ka hadoshi da matarka a mota daya kuka taho?" Ya jefawa
jafar tambayar,bai amsa mishi ba shima illa danne dariyarsa da yakeyi,sai haidar
din ya jijjiga kai
"Next time zan gaya mata,duk sanda zaka dauki wani qato a motarka to saika sama
mata abun hawa,koka bata motar tayi driving ku kuje ku hau ta haya....kai kuma" ya
nuna saif
"Ka kiyayi haduwarmu wallahi" saiya miqe yana ficewa don sawa a amso musu drinks.
Sun dan jima don basu tafi da wuri ba,sai daya sallamesu sannan ya koma
cikin gidan.
Cikin sauri take kammale falon da kwashe kwanukan zuwa cikin kitchen,don
bataso yazo ya risketa,nauyi yake sanyata ji haka kawai duk sanda suka hada wajen
zama.
Kallo daya ya mata ya dauke kai ganin yadda ta zumbula uban hijabi
"Ki shirya jibi zamu wuce gida" ya fada sanda take qoqarin wucewa kitchen,daidai
sannan wayarsa ta dauki ruri ya soma qoqarin cirota daga aljihu.
Ajiyar zuciya ta sauke tana jin dadin zancan komawarsu,tayi kewar 'yan
gidansu gaba daya,musamman yasira dake ranta,wadda sukayi sallama randa zasu koma
haihuwa ko yau ko gobe,tana ta zuba idanu amma shuru bataji ance ta sauka
ba,wayarta kuma ya rasa me matsalarta yau kwana uku taqi daukan layi,so take duka
saita koma ta bayar a duba mata.
Sunan hajja daya gani saman wayar yasa ya samu waje ya zauna sannan ya daga
wayar,a aladabce yayi sallama kana ya soma gaidata,saida suka gama gaisawa sannan
tace
"Kai daga baka aron diyar mutane sai ka yiwa mutane dif?,an gaya maka haihuwar
yasira yau kwana uku ba'a samunta a waya amma banji daga gareku ba,halama baka
shaida mata ba.....to ka dawomin da jikata maza maza ayi taron suna da ita" ya soma
gajiya da rigimar tsohuwar,yana ji cewa zai fara nuna mata shima dan yaune ko zata
dinga shafa masa lafiya,don haka cikin dakakkiyar muryarsa yace
"Zamu dawo,amma ba yanzu ba"
"Me kace?,to baka isa ba,ai dama aro na baka,na taimaka wa wannam shegen baqin ran
naka,wala'alla idan kanajin motsin dan adam kusa dakai ka rageshi"
"Nidai dawowa ba yanzu ba,matatace....kuma qarqashin ikona take" daga haka ya yanke
wayar,saboda iya tsiya ma saiya kashe wayar gaba daya,yadda ko zata sake kira ba
zata sameshi ba.
Yana sane yayi mata haka,kuma a niyyarsa a wasance ne,amma sai yaji zancan
daya gaya matan ya zauna har cikin zuciyarsa,saiya tsinci kansa da yin mita shi
daya
"Wai aro....kaman wani yaro" ya furta qasa qasa a fili,wannan karon shima sai yayi
wasa da hankalin tsohuwar,zata ga dan zamani kuwa,da haka ya miqe ya dauki duk
abinda yake buqata a falon ya wuce.
Har zai shige dakinsa saiya tuna hajjan ta gaya masa ba'a samun wayarta,don
haka ya sauya akalarsa zuwa dakin nata.
Daga bakin qofar ya tsaya yayi knocking,ba'a jima ba aka bude qofar a
hankali,fuskarta tarwai a hasken qwan dake corridor din,tayi rolling da wani pink
mayafi saman doguwar rigar baccinta mai kauri da laushi data sauka har qasa,sosai
mayafin ya haska fuskarta,qamshin turarenta na busowa tun daga cikin dakin da kuma
wanda ke jikinta zuwa inda yake tsaye,saiya sauke boyayyar ajiyar zuciya,muryarsa
tayi laushi qwarai qwayar idanunsa cikin nata yace
"Me ya sami wayarki?" Dan yamutsa fuska tayi wanda hakan ya qara mata kyau ba tare
data sani ba
"Hakanan ta daina daukan layi"
"Me yasa baki gayamin ba?" Yayi mata tambayar dashi kansa yasan batayi ma'ana
ba,qila hakanne ya sanyata yin shuru itama tana juya maganar,saiya waske da fadin
"Daukomin ita" juyawa tayi a nutse ta koma cikin dakin,yabi takunta da kallo.
Batayi koda minti guda ba ta qaraso da wayar,hannu biyun data sanya ta miqa
masa yasa ya bita da kallo,garin hakan bai kula ba ya hada da hannunta,ta zame
hannun nata da sauri sai wayar ta subuce zata fadi a qasa,cikin zafin nama ya
tarota da hannu daya yana ambaton
"Bismillahi" dan ja baya tayi kadan,sai taga ya juya kawai yabar wajen ba tare da
yace komai ba.
Maida qofar itama tayi ta rufe tana sauke numfashi,wanne irin taushi hannunsa
keda shi haka?,take tambayar kanta,sai tasa yatsa ta dungure kanta da kanta tana
fadin
"Shiga hankalinki".
_ZAFAFA BIYAR_🤙🏽🤙🏽🤙🏽🤙🏽🤙🏽
_(MASARAUTAR KAMSHI)_
_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma
da ingataccen had’i yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa..._
_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_
_carpet spray_
_air-fresheners_
_scented pebbles_
_body sprays_
_oil perfumes_
_Perfumes_
_kabbasa_
_burners_
_coal igniter_
_tong_
_kasko_
_kujerar tsugunno_
_english coal_
_dilke&halwa set_
_scented body mist_
_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata ba, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura
kayayyakin su ko’ina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram:
_@yerwaincense_and_more. Ko _Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta
number su: ___08095215215/09044191709! _
*M'S TREATS*
_BASU FITO BA SAI DA SUKA SHIRYA_
*KAYAN SPICES*
Curry powder
Corriander powder
Tumeric powder
Mix spices
Ginger powder
Black pepper
White pepper
*SNACKS*
Samosa
Spring rolls
Meatpie
Cupcake
Birthday cake
Doughnut
*_ZAKU IYA ZUWA KU SAMESU A bayan northwest university layin gidan ruwan dish KANO
NIGERIA_*
Tana kwance a daki tana iya jiyo motsinsa a falo,har zuwa sanda ya bude
dakinsa ya shige,saita saki ajiyar zuciya ta tashi ta dauko maganinta tasha ta
kwanta.
Shi dinma bayan yayi wanka ya saka kayan baccinsa saiya haye gado,yanajin
gajiya kadan kadan cikin jikinsa,don tunda ya fita bai zauna ba,bayan sun gama
meeting da manyansu kuma ya nemi zama da Battalia da yake jagoranta suka
tattauna,babba kuma muhimmin aiki ne yake tunkarosu kan tsaron qasarmu,wanda yakeji
a jikinsa da wahala wannan karon bai aje girma ko muqaminsa ba ya shiga cikin aikin
da kansa anyi dashi ba.
Neman bacci yayi ya rasa,saiya dinga kame kamen abinda zai debe masa
kewa,irin wannan yanayin na rashin zuwan bacci baqo ne a rayuwarsa,ya saba a duk
sanda yaji bacci,kawai daya kwanta zai daukeshi,sai gashi yau zancan yasha
banban,saiya dauki system dinsa yahau duba saqonni,har zuwa sanda yaji baccin da
gaske,ya kasheta yayi addu'o'insa ya kwanta.
Duk yadda yakai ga jin barcin sai yaji kwanciyar babu armashi,ya soma canza
position daga dama zuwa hagu,yana tambayar kansa ya akayi jiya yayi barci lafiya
lau?,yau kuma abun ya faskara?,saiya tuna abinda ya farun jiya,da sauri ya kauda
tunanin,ya dinga maimaita hasbiyallahu la'ilaha illa huwa,alaihi tawakkaltu wa huwa
rabbul arshil azim,sannu a hankali yaji yana samun dai daito,bai dade da yawa ba
baccin ya sureshi shima.
Washegari ma tayi breakfast din,ta kuma aje masa ta shige daki,saboda sam
batason haduwarsu,kallon dra lura yana mata ne bataso,nauyi yake mata da yawa,tana
tsoron tsirfarsa kada ya lauya mata wani laifin,koya kwaba mata magana,saidai a
rashin saninta ranar tunda sassafe ya fita,meeting din dai suke ci gaba dayi har
sai sun kamo bakin zaren,batasan bai nan ba sai data fito wajejen la'asar zata dora
girkin dare sannan ta ganshi,sai fita tayi dashi ta baiwa maigadi ya bayar,na dare
ma data gamanan ta jere masa,saidai shi duk da ya dawo a makare kuma a gajiye bai
fasa ci ba,saboda taste din yana masa dadi sosai.
Sai da safe xata gyara gidan ta gani,tayi tsammanin yau din ma ya fita da
wuri,don haka tea kawai ta hada,ta soya qwai guda biyu ta hada da bread taci,saita
gyara gidan,ta hada kayanta data saka zata wanke,don haka ta sanya t.shirt me
qaramin hannu ta daura plain zani,hakan datayi saiya tuna mata da makarantar
boarding,saita saki murmushi,ta tsaya gaba mudubi ta dubi kanta,ta tuna lokacin da
bata fiya son shigar ba,saboda zakaga kamar ta saka pushup bra ne kuma ba ita ta
saka ba,idan ma tayi shigar saidai tana maqale da hijabi,saboda baiwar halitta da
qirar jiki da Allah yayi mata,sai suyita tsokanarta,shi yasa take zama da hijabin.
A nutse ya fito daga dakinsa yana rufe bakinsa saboda hammae data subuce
masa,ya dubi kan dining yaga wayam babu komai,sai yasa hannu ya shafi cikinsa,don
yunwa yakeji qwarai,gajiya ce ta hanashi fita yau da wuri yadda ya saba,ya yanke
kawai ya kwanta yadan huta zuwa azahar ya fita din,ganin babu komai akan dining din
saiya juya ya shige kitchen.
Ƙarar faduwar bucket daga hannunta shi ya taimaka masa ya dawo zuwa
hayyacinsa,da sauri ya taka a hankali da baya ya koma cikin kitchen din,yana sauke
ajiyar zuciya tare da jin dadi da bata ganshi ba,cak ya tsaya tsakiyar kitchen
din,yama rasa wanne tunani yake,yasa hannunsa ya ranqwashi tsakiyar kansa,cikin
zuciyarsa yana gayawa kansa me yake damunsa?,me yake aikatawa haka?,dogon tsaki
yaja ya taka zuwa inda gas yake ya kunna ya dauki tukunya ya zuba ruwa,saidai kafin
yakai ga zuba kayan hadin tea din ya lura da flask din tea dake wajen,yakai hannu
ya daga sai yaji akwai a ciki,don haka ya dauki cup ya zuba ya jingina bayansa yana
kurba a hankali.
A hankali ya dinga ganin motsinta na daxu cikin idanunsa,ba tare daya ankara
ba zuciyarsa ta soma zayyano masa irin abubuwan da yake buqata tare da mace,kowanne
tana haska masa shi cikin idanunsa,yana kaucewa da qarfin tsiya tare da qaryata
kanshi da kanshi,ya dinga jan tsaki shi daya yana kokawa da tunanin.
Sake daga idanunsa yayi karo na biyu yana kallonta ta qasan idanu,kallon da
idan duba daya kayi masa ba zaka zaci ita yake kallo ba,saika dauka a lumshe
idanunsa suke,dab da zata giftashi tace
"Ina kwana" ya amsa qasan maqoshinsa.
Ji take kamar zata harde ta fadi,jikinta yana gaya mata akwai idanu a
kanta,kamar ta zuqo qofar ficewa daga falon ta fice gaba daya,saidai kash!,dab da
zata fita taji muryarsa a dake yana cewa
"Zo nan" haka kawai ya tsinci kansa da fadin hakan ba tare daya shirya ba,sai yaji
baiso ta fice ne kawai,kamar tace masa zata qarasa daki ta dauka hijabi,to amma
batasan me zaya fassara hakan ba,don haka ta sake juyowa ta dawo zuwa inda
yake,dukka idanunsa na kanta da salon kallon qasa qasa mai kama da me bacci
"Hadamin breakfast" ya furta yana sake kurbar tea din hannunsa,ta zaci fita zayayi
ya bata waje,sai taga ya matsa gefe kawai abinsa yana ci gaba da shan tea
dinsa,daga qarshe ma sai yaja kujera yayi zamansa cikin kitchen din,sannu sannu
kansa tsaye yaci gaba da binta da kallo duk motsin da zatayi.
Gaba daya duk sai ta rude ta daburce,sabida wani irin tasiri da idanunsa ke
mata cikin jikinta,jikinta duka rawa yake,gani take kaman ba ya zakinsu ba,tun da
can idan ya tsareka da idanunsa saika gwammace ya dakeka akan kallonsa mai
nauyi,wani irin kwarjini ne cikin idanunsa,batasan me yasa ya tsareta haka da kallo
ba,don haka duk aikin da zatayi saita dinga yinsa kwan gaba kwan baya.
Cikin tsananin jin zafi ta saki prying pan din tana sakin qara,abinda ke
ciki ya tarwatse,radadi da zugi ya soma ratsata,ta fara yarfe hannunta.
Cikin sauri ya iso wajen kamar qiftawar idanu,yasa qafarsa da sauri ya ture
frying pan din wanda saura kadan ta sanya qafarta still,hannun nata ya kama da
sauri yana dubawa,tuni qwalla ta fara cika mata idanu saboda zafi,tuni yatsun sunyi
ja,sai yajata suka isa bakin famfo ya kunna ya tara hannun a qasan ruwan dake
zuba,a hankali sanyin ruwan ya fara ratsata,radadin ya tafi,saita lumshe idanu tana
sakin ajiyar zuciya,dai dai lokacin da yake kallon fuskarta da lamsassun idanunta
ke a rufe har yanzu.
Abinda bata so yawan kusancinsu,duk sanda yayi kusa da ita sosai haka
takanji wani nauyi daga gangar jikinta har zuciyarta,sai taji kamar ya cika wajen
da kwarjininsa da haibarsa,bugun zuciyarta yakan dadu,jiki da zuciyarta yayi wani
laushi,ba zata iya fayyace me takeji game dashi ba,saidai ta sani cewa ya rage jin
haushi da tsanarsa tun ranar bikin qara musu girma,maimakon haushinsa sai bugun
zuciya da jin nauyinsa daya maye gurbi,haka kawai taji wani rauni na
mamayarta,hakan ya baiwa qwalla damar ratsowa ta gefen idanunta.
A lokacin yana tsaye yana qarewa fuskarta kallo,yaga wasu abubuwa sama
fuskarta da suke kama da nashi,wanda ko qannensa da suka fito ciki daya basuyi
tarayya wajen kamanceceniya a su ba,a baya sanda take qarama idan aka fadi akwai
kamannin,yana kallon mai fadar ne a matsayin me matsalar gani da kyau,amma a yanzu
a dai dai wannan lokacin ya yarda kai tsaye babu musu.
Bayan ya shiga daki saiya aje wayar a gefan bedside drower dinsa,ya shiga
bandaki yayi shirya kansa,sannan ya dawo ya shimfida abun sallah ya tada
sallah,yakanyi sallah raka'a biyu ko hudu duk sanda xai kwanta,musamman idan yana
jin gajiya a jikinsa wadda yake saka ran zaiyi wuya ta barshi ya iya tashi cikin
dare yayi sallah.
Sai daya sauya kayan bacci sannan ya isa gadonsa bayan ya kashe qwan
dakin,yana shirin jan duvet dinsa ya rufa idanunsa suka sauka kan wayar tata,saiya
saka hannu ya daukota ya kuma kunnata,ta daidaita sanda ya kwanta sosai saman
gadon,yasa hannu ya budeta,don babu passoword ko security pattern.
A hankali ya dinga bin hoton da kallo kafin daga bisani ya sauka ya shiga
gallery dinta kai tsaye.
Ya jima kan wani hotonta da tayi da wata farar armless shirt,da straight
skert,kayan sunyi masifar fidda qirar qirjinta da qugunta,kanta babu dankwali sai
manyan kalba guda uku da tayi ta saukar da jelarsu,daya lura da kyau a falon hajja
akayi mata,kuma da alama batasan an dauki hoton ba,haka kawai sai yaji ranshi nadan
baci bayan ya gama kalla din daya tuna cewa gidan nasu akwai samari,kuma suna iya
shiga sassan hajjan kowanne lokaci,sai yaja dogon tsaki ya dannawa hoton
delete,kana ya kashe wayar ya aje a gefansa wata kasala.na saukar masa,ya soma
saukar da ajiyar zuciya a jejjere kamar yaron goye da yaci kuka ya qoshi.
Ya jima yana juyi zuciyarsa na gaya masa abubuwa da dama,ciki kuwa harda zai
rasa damarsa ne,ya kamata ya tabbatarwa da kansa da ita din kanta cewa matar tasa
ce da gaske,tsahon lokaci a haka kafin ya samu bacci ya daukeshi.
Washegari bayan sallar isha,yana saman dining don cin abincin dare,dai dai
sanda take miqewa ita kuma ganin ya zauna din,sai yasa hannunshi ya dauko qaramar
leda mai dauke da tambarin wani babban shagon saida wayoyi ya miqa mata,duk da
batasan meye a ciki ba tasa hannu biyu cikin mamaki ta karba
"Na gode" ta fadi tana sauka daga wajen da dan saurinta,saiya dan bita da
kallo,yana ankare da ita daga safiyar yau zuwa daren nan kamar walwalarta ta
qaru,yasan kuma qila hakan baya rasa nasaba da zancan tafiyarsu gida,saiya kauda
wannan tunanin yaci gaba da cin abincinsa.
Tana shiga daki ta fada saman katifa gaba daya,sannan ta zazzage ledar tana
duba abinda ke ciki.
Tsalle ta buga ita kadai tare da dan qaramin ihu,sai kuma ta nutsu tana zare
idanu da rufe baki don kada ya jiyota,take ta sanya layuka da memory dinta daya
dawo mata dasu da safe,sannan ta jona mata chargy,ta dawo ta zauna tana jiran ta
cika.
Shirin tafiya gida kawai take hankalinta kwance cikin zaquwa,musamman data
kira taji cewar yasira ta haihu,randa kuma zasu koma gidan saura kwana biyu suna
kenan,ta gama tsarawa sai washegarin suna da kwana daya ko biyu zata koma
makarata,don tasan za'a hadu sosai da 'yan uwa da aka jima ba'a hadu ba,tunda anan
gidansu za'ayi taron.
Ana ya gobe ranar da yace zasu tafin ta cika haka ta wuni tana
zumudi,fuskarta ta cika da walwala,ko falon ma bata fito ba,tana can daki tana
charting da 'yan gida.
Hakan ya sanya ranar shi kadai yahau dining cin abinci,sai yakejin
banbarakwai yau din,ya dinga kallon hanyar dakin nata amma shuru babu ko
motsinta,baisan me ya sanya yaji baijin dadin zaman ba,ya dinga jan tsaki,ya
fahimta rawar kai da zumudin tafiyar takeyi,saiya sake jan wani tsakin kawai ya
dauki sauran abincin da bai gama ci ba ya wuce daki dashi.
*_WASHEGARI_*
Tun bayan sallar asuba take zaune saman abun sallarta bata tashi ba,agogon
dake dakin yana nuna mata qarfe shida ta miqe,ta soma gyara dakin tare da tattare
da rufe duk abinda tasan zai iya qura bayan babu kowa a dakin,daga nan ta yiwo
falo,tana yi tana duba hanyar dakinsa ko zataji motsinsa,alamun ya tashi ko kuma
wani abu,saidai har ta gama gyara falon,ta wuce kitchen ta gyarashi shima,ta
killace dukka kwanukan ta gogesu da kyau ta maidasu muhallinsu yadda ya dace,ganin
cewa tafiya zasuyi yasa bata dau wani girki mai tsaho ba,chips kawai ta soya ta
dafa tea,ta koma daki ta shiga wanka.
Ta kuwa samu kusan dukansu a online,suka shiga hira tana gaya musu suna
hanya,hirar tasu tasaka mata zaquwar su tafi din,batasan ta jima a zaune ba sai
data duba agogo,sha daya har tayi,saita fidda idanu tana aje wayar,ta miqe ta bude
qofar dakin ta fito falo,shawagi ta danyi har zuwa kitchen ko zataga alamun da zai
nuna mata ya tashi,saidai babu wata alama,hakanan ta sake komawa daki tanajin kamar
ta shiga dakin nasa taga meya riqeshi haka.
Sha biyu na rana takai maqura wajen qaguwa,kamar zata saki kuka haka ta
dinga ji,ta dinga safa da marwa tsakanin dakin zuwa qofar nashi dakin,tayi
attempting na shiga dakinsa yafi sau biyar,saidai data isa qofar dakin saita kasa
shiga ta juyo ta koma.
Qarfe daya dai dai na rana haqurinta ya qare,ta tsaya qofar dakin nasa tana
saisaita kanta,tare da baiwa kanta qwarin gwiwa,a hankali ta dora hannunta saman
handle din ta murda qofar ta bude.
Dai dai lokacin yana kwance rub da ciki cikin lallausan bargonsa yana duba
saqonni cikin wayarsa,ya lulluba har kusan kansa,wanda duk wanda ya shigo xai dauka
ma duka har kan nashi ya rufa,duk da acn dake kadawa cikin dakin amma jikinsa babu
riga,sai wani boxer dake a jikinsa.
Tsayawa yayi da replying massages din sanda yaji an turo qofar ba tare daya
waiwayo ba,zuciyarta na wani irin bugawa ta dake tayi sallama,saiya juyo
rigingine,wanda hakan ya basu damar ganin juna sosai.
Tsoro sosai ya shiga bata ganin yadda ya soma juye mata zakin sosai,ya fara
fita daga hayyaci da kamanninsa,ya koma yin komai da zafi zafi kamar mayunwaciyar
dabba,mazantakarsa da jarumtarsa kawai yake nunawa ba tare dashi kansa ya sani
ba,tsoro sosai ya cikata da fargaba,dana sanin shigowarta dakin ya fara mamayeta.
Bata gane abun da gaske bane sai daya fara neman hanya ɗoɗar,ta tabbatar
idan dabararta batayi aiki ba tana ji tana gani kome zai lalace mata,saita saki
kuka sosai,wanda dama tun daxun take yinsa,saidai baiyi qarfi ba kamar yanzu da
take neman agaji da gaske,kiran sunan hajja da umminta data fara yi shine ya
karyashi,ya kuma dawo dashi hayyacinsa,a hankali saiya fara dawowa hayyacinsa,ya
kuma soma tuna abinda yake shirin aikatawar,sai duk aka zare masa wata laka ta
jikinsa,saiya zame gefe guda,ya kuma hanata tashi sanda take yunqurin tashi cikin
kuka,sukaci gaba da kasancewa a haka har tsahon wani lokaci da kukan nata ya tafi
gaba daya,sai dan zafi zafi da take ji daga can,duk da ba wani me yawa bane.
A falo yaci burki,saiya samu daya daga cikin kujerun dining ya zauna
akai,yasa gwiwar hannunsa saman cinyarsa yana dafe kansa da dukka tafukan
hannayensa,wani iri ciwo kan nashi yaji yana masa,dukka jijiyoyin kansa sun
tashi,idanunsa da suka sauya launi har yanzu basu daidata ba,duka kansa ya cushe ya
kuma kulle,ya rasa wanne tunani zaiyi,miqewa yayi kawai ya koma dakinta,ya bude
nata toilet din ya shiga ya hada nashi ruwan wankan.
A hankali ta sauka daga gadon tana karantar kowanne canji daga jikinta,ta
soma takawa zuwa bandakin,yanayinta yadan sauya saidai ba sosai ba,hakan shi ya
tabbatar mata bai gama cimma manufarsa ba,don haka data shiga din ma ruwan dumi
kadan tayi amfani dashi tajita normal,sai tayi wanka bata jima ba ta maida kayan
jikinta ta dawo cikin dakin.
Idanu ta dinga rabawa tana cike da fargabar fita,don batasan ta inda zasu
hadu ba idan ta fitan,gaba daya ita wani irin tsoronsa takeji,sanda taji an turo
qofar dakin sai taji kamar ta zura da gudu,sai kawai ta sulale ta durqushe a wajen.
_____________________________
_IDAN KAJI GANGAMI DA LABARI....! INA MASU ZUBIN ADASHEN DA BA RANAR DAUKA NA DATA?
_
_TO KU MARMATSO KUJI, KU KUMA SHARE HAWAYEN KU, MUNZO MUKU DA SABBIN TSARE TSARE NA
DATA, WADDA KOWA ZAI IYA SAYA DAI DAI KARFIN SA. A FARASHI MAI RAHUSA_
_TSAYA KUJI, A RANO NET ZAKA IYA ZAMA RESELLER KO WHOLESALER KAI MA, EH ZAKA/KI IYA
ZAMA MA SAYAR DA DATA A FARASHIN SARI MUKE BAYARWA, KAI/KI KAFA KASUWANCIN KU KUMA.
DA KUDI KALILAN._
_MUNA KUMA SAYARWA AKAN ‘DAI DAYA, KOWANE NETWORK MUNA SAYARDA DATA PLAN DINSA AKAN
KUDI KALILAN, MASU FARASHIN SARA KUWA MA KU KUDIN BAI KAI HAKA BAMA_
_AIRTEL_
_9MOBILE/ETISALAT_
_MTN_
_GLO_
_DUK MUNA SAYARDA TSARIN DATA DINSU. KAMAR MISALI MTN MUNA SAYARDA 1GB.24MB AKAN
FARASHIN NERA 300 KUMA YANA KAIWA WATA DAYA, GWARGWADON YADDA KAKE AMFANI DA DATA,
2GB 600, 3GB 900!!_
_DUKA WADANNAN TSARIN DATA DAMA NA SAURAN LAYIKA MUNA SAYRWA AKAN FARASHI MAI
RAHUSA, WANDA KOWA ZAI IYA YIN TSARIN DAI DAI ALJIHUN SA_
_Ranonet.com.ng_
_GA SITE DINMU NAN DAKE YANAR GIZO, KAI TSAYE ZAKI/KA IYA SIYAN NAKA TA NAN. _
_KO A TUNTUBE MU TA NAMBAR TARHON MU: +234 803 081 1300/+234 808 540 5215_
_KYAU, INGANCI, RAHUSA, ADADE ANA YAWO A YANAR GIZO SAI RANO NET._
_RANO NET..!!!!_
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: 35
Cikin wata nutsuwa daya samu ta sanadin sakarma kanshi ruwan da yayi yake
takowa zuwa cikin dakin,hannunsa dauke da babban mayafinta da kuma abun sallah,sai
daya fara shimfida abun sallar sannan ya qarasa gareta
"Kinyi alwala?" Ya tambayeta,tana daga duqen tana hawaye ta gyada masa kai
"Ohk....getup,tashi muyi sallah" ya fada yana miqa mata hannusa,a hankali ta daga
kai,maimakon ta bashi hannun yadda ya buqata saita fuske masa,ta miqe tsaye a
hankali tana jin yadda cinyoyinta suke so su fara tsami,riqe dantsen hannunta
yayi,ya tsaidata sosai,sannan ya ware hijabin hannunsa ya sanya mata,saita isa da
kanta saman abun sallar ta tsaya,don ta fuskanci jam'i yakeso suyi,saboda guda biyu
ya shimfida.
Cak ya dagata ya rabata da qasa,ya isa da ita saman gadon ya kwantar da ita
yana dan nishi
"Ashe dan banzan nauyi ne dake?,ke kika jawo na kusa miki aika aika,sannan zaki
fice ki qunshe kanki a daki,salon ciwo ya rufeki ki ja mani magana wajen waccar
tsohuwar,tace naci amanarta ban kula da ita ba" rau rau idanunta sukayi suna tara
qwalla,lallai ma ya haidar din nan,ya cita wasa da yawa,amma babu komai,saita
rama,saiya saka dan yatsantsa saman labbansa yana duban qwayar idanun nata yace
"Shshshsh....keep silence please"lumshe idanunta kawai ta dinga yi a hankali har ta
rufesu,don tasan bata da wani sauran abun fada,tana gama rufe idanun nata yaja mata
bargo ya lullubeta,sannan ya miqe a hankali ya fice daga dakin.
Da kansa ya dauki mota ya fita nema musu abinci,haka ya dinga tuqi a titin a
kasalance,ya sauke dukka glass din side dinsa iskar waje tana shigo masa,wadda ke
cakude da sanyin tasowar hadari,don ko rana babu a garin sosai,sai daya gama
shawaginsa sannan ya zaba wani gidan abinci ya musu takeaway,ya kuma biya na dare
da zasu kawo mishi har gida,don bai saka ran zata iya girki ba,daga dan tabata
kadan duk ta wani langabe,saiya saki murmushi shi kadai yana shafa sumarsa zuwa
habarsa sanda abinda ya faru ya dawo masa,idanun hajja kawai yake hangowa a lokacin
ace taga abinda yaso aikatawar,tabbas da kashinsa ya bushe,tijara kuwa yasan sai
wadda bata tuna ba.
Sanda ya koma ma bata tashi ba,saiya zauna yaci nasa abincin shi kadai,ya
zauna yana duba labarai daga ingantattun jaridun dake kawo labarai online,saboda ya
sake samun information da haske kan aikin dake gabansu.
Ranar gaba daya wasan buya dashi takeyi,gudunsa take hakanan wani tsoronsa
take ji,tunda ta samu ta fice daga dakin nashi bata sake bari sun hadu ba,iyaka
idan yayi knocking xai gaya mata ga abinci nan ta fito taci,sai ta dai daici ya
gama ci sannan zata fito ta diba ta koma daki.
Ta gefe guda gaba daya hankalinta ya karkata zuwa gida,saidai bata ga alamu
ba,bata kuma sake jin ya tada maganar ba,gashi a yanzun bata jin zata iya
tunkararsa bare tayi masa zancan.
Kwana na uku da faruwan abun,da wani yammaci yana zaune a falo shi kadai,yana
dai xaune ne kawai,amma sam bayajin dadin zaman,wanda shi kansa bazaice ga dalili
ba,lokaci lokaci yakan dubi sashen qofar dakinta,tun ranar gaba daya hankalinsa da
tunaninsa yayi kanta,baisan me yasa ba,amma baya yin wani qwaqwqwaran awanni bai
tunata ba,duk data yanke daga hulda dashi,shi kuma bai tsawwala ba,saboda baison ya
fiya shiga rayuwarta da yawa ya zamana akwai takura.
Kamar ance ya daga kanshi saiya hangeta bakin qofar dakinta,da alama taji duk
yadda sukayi da hajja,kanta ta dauke yayin dashi kuma ya sassauta murmushin
fuskarsa,tun daxu take dakon jin fitarsa ta fito taci abincin rana daya ce mata
taci amma taji shuru,ganin babu alamun zai tashi,ga yunwa zata hallakata shine
kawai tayi shahada ta fito.
Da magariba yayi waya aka sama masa ticket na jirgin da zai tashi daga
abuja zuwa kano qarfe biyu na rana,bai shaidawa zahran ba ita kanta sai washegari
daya dawo daga sallar asuba,haka nan wannan karon sai taji bata wani daukin tafiyar
sosai,haka ta sake abinda yake da buqatar a shirya din,zuwa sanda ya gaya mata xasu
fita ta kammala komai,ta yafa mayafinta,ta janyo akwatinta tayo falon.
A tsaye ta sameshi tsakiyar falon yana amsa waya,ya baiwa qofar da zata fito
din baya,tun kafin ta qaraso ta gama qare masa kallo,sanye yake da wani trouser da
shirt,sai high top takalminsa daya dace da kayan jikinsa,tun bata ga fuskarsa ba
amma ta tabbatar da cewa shigar ta amsheshi,ta qara masa kwarjini.
Suna sauka a aminu kano airport driver ya daukesu sai gida,ji take kamar
tayi tsuntsuwa ta ganta a gida,tafiyar kusan minti arba'in ita ta kawosu gida,wanda
tun daga harabar gidan tasan tabbas taro ake,saboda jama'a da kuma rumfunan da aka
kafa,indai lissafinta yayi dai dai yaune sunan yasira kenan,harga Alla ta fidda rai
data ji bai sake tada zancan ba,shi yasa ta daina lissafin ma.
Zumudi fal ranta ta saka hannu xata bude murfin motar,sai taji an dafe hannun
nata,ta waiwayo da sauri idanunshi na akanta,hakanan tana iya jiyo hucin
numfashinsa sosai saman fuskarta saboda yadda yake dab da ita,da wata irin
kwantacciyar murya taji yace
"Ki nutsu da kyau,kada ki manta ke din wacece,banason yawo jiki a bude da sunan
kina cikin gida....ki kiyayemin mutuncin igiyata" gaba daya ita zancan nauyi ma
yayi mata,saita maida kanta daya side din,daga nesa tana hango su salma suna kai
kawo,da alama hidima ta dauki zafi
"Soja baya son kawo qorafi ko kawo uzuri,just be obedient to my commands" cikin
ranta take mitar ance masa a bariki ake dazai soma lissafa mata wasu qa'idoji,bata
gama wannan ba taji ya zame wayarta daga hannunta,yayi wasu danne danne ciki sannan
ya miqa mata
"This is my number,just call me idan kina da wata matsala ko buqata,bance ki
tambaya kowa komai ba,ummi ko hajja,nayi cancel duka,zaki iya tafiya" da sauri ta
buda murfin motar ta fito,wanda fitowar tata yaja idanun mutane da yawa,donma
aliyyun zamanshi yayi cikin mota,ya kuma nada umarnin a sake fita dashi daga
gidan,batasan inda xaije badai,tadai san koda can baison hayaniya kwata kwata,indai
ana wani taro a gidan bai zama,sanda bai kuma wani zama saurayi ba wuni yake cikin
dakinsu ya kebe kanshi shi kadai,mama tayita faman fadan me yasa baya son shiga
dangi ko ya fito su gaisa,tun tana mita da qorafi harta gaji ta qyale,tunda ta
fuskanci halinsa ne hakan,
Nan da nan labarin dawowar tata ya zagaye gidan,aka fara cecekuce da zancan
dawowarta,ta fara gaisawa da 'yan uwa data samu harabar gidan,suna amsawa gami da
tayata murnar qarin girman da aliyyun ya samu,ta sake fuska sosai tana amsa musu
cikin walwala da nuna jin dadi,da yawa suka dinga binta da kallo wanda batasan na
meye ba,da haka harta isa sassan abba babba,inda canne yafi cikowar yan suna da
yawa,tunda anan mahaifiyar yasiran take wato mommy.
Ihun murna 'yan uwan nata suka saka sanda sukayi arba,kowa yayo kanta,suka
cika kunnuwanta da magana,kowa da abinda zaice,salma ce daga can tace
"Allah matar ya haidar ba haka muka taho muka barki ba,anya ya haidar bai cika aiki
ba kuwa?" Ta qarashe fada qasa qasa,wani wawan dundu zahra takai mata,akayi sa'a
kuwa ta sameta,fa gantsare saboda zafi,sauran suka sheqe da dariya,dai dai sanda
mommy ta shigo
"Waiku kam bakusan kun girma ba don Allah,yanzu kalli yadda sahal yake kallonku,kin
dirke masa uwa.....daga dawowarki kin biye musu,tashi ki qarasa gaisawa da jama'a
ki qyale wadan nan shirmammun,kuna nan a waje ana nemanku kunata baqi"tana kaiwa
nan ta fice ta barsu.
Tare suka fito da ita,ta soma lalubar mama don su gaisa,a kitchen na
tsintota sunata rabon abinci da taimakon masu aikin gidan,wai yau sai ta tsinci
kanta tana kunyar maman,tana kunyar hada idanu da ita,tana shirin tsugunnawa har
qasa ta gaidata tace
"A'ah,tashi inna wuro kada ki bata kayanki,bakiga yadda kitchen din yake a kacame
ba" saita lalubi kujera ta zauna akai saboda ji take kamar zata fadi ta gaida maman
tayi mata barka
"Ki shiga wajen hajja,can ne naga da sauqin mutane" da to ta amsa mata,suka fito
tare da hafsa.
Kusan a tsaitsaye suka gaisa saboda jama'a itama dake cike a sassan nata,sai
kawai ta wuce sashen mutuniyar tata hajja.
A dakinta ta sameta ita kadai tana tsaye inna gaje na wanke mata
bandaki,da alama wani ya shigar mata ne,haka take,duk sanda wani ya shigar mata
bandaki indai baqo ne to sai an wanke mata,har mamakin tsafta irin na tsohuwar
zahra keyi,wani lokaci kuma ta tsokaneta
"Waike da kika kusa gangarawa tsaftar nan duk ta meye?" Wanda idan wani ne ya
gayawa hajjan haka sai inda qarfin zahran yake,takance
"Kaga tafiya lahira a kanka,hajjanmu ba yanzu ba".
Wani kallo hajjan tabi zahran dashi kafin ta yamutsa fuska sanda take
gaidata
"Munafukai....sai yau kuka ga damar tahowa?,aida kun sani kun dawwama a can" ta
fada da biyu,sabida ta bigi cikin zahran taji me zata ce,hade rai zahra tayi tadan
ja baya
"Zaki fara daga dawowata,ni inacan kamar nayi me saboda kewarki,amma irin marabar
da zakimin kenan?"
"Na miki da arziqi ma 'yar nan,ina daya ja'irin?" Baki ta turo ta haye gadon
hajjan,wanda tayi kewarsa sosai
"Ki kirashi ki tambayeshi mana" ta fada tana kwanciyarta
"Toooo...da saura kenan" hajjan ta fada a ranta,don tayi tsammanin zata kareshi ne
"Muje zuwa mahaukaci yahau kura" ta kuma fada a ranta
"Duk na isheku riga da wando" ta fada tana shigewa bandaki.
Wunin ranar cikin walwala tayi abinta gaba daya cikin dangi,har zuwa dare
sanda aka qare sunan,baqi suka tattafi saura 'yan gidan da yaran gidan aurarru
wadanda sukayi aure,suma a cikinsu wasu sun tafi,tawagar su zahra kuwa suna tattare
a sassan hajjan sunata kwasar hira,kamar ba za'a rabu ba,don yasiran a nan sassan
hajjan take zaune tunda tazo haihuwa.
Tana idar da sallar isha'i zahran ta koma wajen ummin nata,suka sake gaisawa
sosai sannan suka taba hira,wanda ta lura kusan fiye da rabin hirar tata kan
aurenta da aliyyu ne a fakaice,tana mata jirwaye mai kamar wanka a kansa,ta rasa
wanne irin qauna ce a tsakaninsu
"Nasan zakiyi mamaki me yasa na damu da zancan aliyyu a kanki ko inna wuro?....nafi
kowa sanin aliyyu mijine na kerewa sa'a,irin mijin da ake cewa mijin
marainiya,mijin dana jima ina miki addu'ar samu,kici gaba da gyara mu'amalarku inna
wuro,zaki fuskanci abinda nake gaya miki,mazan aure irin haidar a wannan zamanin
wahala sukeyi,cikin dari guda daya ne tak,Allah ne ya amshi addu'ar dana jima ina
muku ya kawo sanadi da kika zama matarsa" wannan shine magana kusan ta qarshe da
sukayi da maman nata,wanda da ita ta dawo zuwa sassan hajja,wanda zuwa yanzu an
sake yoyewa,inna gaje ta gyara falon fes,sai fidda qamshi yakeyi.
Tunda can dama ba wani shiri suke sosai da suwaiba ba,don haka da badi'a suka
gaisa kawai,ta diba kayan wankanta ta shige bandakin tayi wanka,sannan ta fito ta
dauki kayan da zata saka ta wuce dakin hajja donta shirya,saboda ta fuskanci kamar
suwaiba ta sanyawa duk wani motsinta ido,batason ta fusata harta buda baki ta gaya
mata magana,shi yasa tabar musu dakin da niyyar kwana dakin hajja.
Tana tafe a hanya riqe da kwandon kayan abincin kamar ta sakesu ta sanya kuka
saboda takaici,ji take gaba daya hajja ta gama takura rayuwarta tako ina,tana
wannan qunci har takai qofar dakin nashi.
Turawa tayi hadi dayin sallama qasa qasa,alamun ranta na a bace ne,a lokacin
yana zaune saman kujera,ya miqe qafafunsa lan center table dan qarami dake
gabansa,system ce saman cinyarsa yana typing da mugun sauri,da alama wani muhimmin
magana yakeyi,dakin a dan hargitse yake da kaya.
Sau daya ya daga kai ya kalleta ya amsa sallamar ya maida kansa ga system
dinsa,saita qaraso a hankali ta aje kwandon gefanshi,tsaye tayi ta rasa meye abunda
zatayi,tana tunanin ta koma idan yaso hajjan tayi kwadonta ta cinye,idan kuma ta
zauna din kamar ta zubda kanta ne,zaiga ita ta kawo kanta ma kenan,kamar tadda yayi
mata sharri a abuja.
Sake daga kai yayi ya dubeta,idanunta nacan wani sashen daban,don ta jima
bata iya hada idanu dashi,tun lokacin da wancan abun ya faru,duk yadda yakai ga
qwaqwqwafi da qwaqwar su hada idanun bata yarda
"Have a sit please.....bana son tsaiwa" ta jishin,saita samu waje tana zama
din,cikin ranta tana mitar har a gayawa soja tsaiwa zaice wani baison
tsaiwa,takaicinsa ya sake cikata,ta rasa me zata masa ta fanshe haushin da hajjan
ke cusa mata a kanshi,don haka ta tsiri zuba mishi abinci,kowanne plate saita
cikashi ta tura gabanshi,shi sam baisan ma me ake ba,harta gama zubawar,saita miqe
ta nufi dan qaramin fridge dinsa dake dakin ta bude.
Jere yake da hadaddun zobo,wanda da alama jin zuwansa yasa umminta tayi
masa,tunda dama itake masa,saboda din mutum ne da idan ba dole ba bai fiya son
lemon kwali roba kona kwalba ba,yafi gabe gagajiya,zobo ginger ko kunun aya,su yafi
sha indai yana gida.
Sai data iso dab dashi ta soma tsiyaya zobon,taf ta cika kofi,sai kawai ta
saki cup din ya sullube daga hannunta,ya kuwa fada saman cinyarsa,take ya masa
wanka a fararen kayan dake jikinsa,ya kuma fantsame har screen na system din da
yaketa faman latsawa.
Cikin ba zatar zubar abu mai sanyi daya ji a jikinsa ya daga kai yana
dubanta,tana tsaye a kansa,saidai tayi narai narai da idanu alamun rashin
gaskiya,baice mata komai ba sai qoqarin kashe system din da yake saboda karya shiga
ciki.
Idanu ta zura masa qirjinta na bugun uku uku sanda taga ya nufota,hannusa
guda daya cikin aljihun wandonsa fari daya baci face face da zobo,wani taku yake
slowly,saidai ya aza qwayar idanunsa cikin nata sosai,wanda hakan taji ya mata
nauyi matuqa,ya kuma qara mata fargaba,duk da haka ta kasa dauke qafarta ta ɗara
daga inda take tsayen harya cimmata.
Wata iriyar tsaiwa gab da juna sosai,har yatsun qafarsa na dungurin nata,har
yanzu kallon qwayar idanunta yake data kasa janyewa daga cikin tasa,hannayensa ya
daga sama gaba daya,kamar wanda yayi laifi aka kamashi yayi surrender
"Farashin da zaki biya wannan gangancin da kika yimin shine,ki cire kayan jikina ki
daurayemin jikina da kika batamin haka kawai ina zaman zamana.....na yafe miki
wankin kayan.....don yanzu dana saki ma waccar tsohuwar zata isheni da kwarorota da
terere" kamar ya dauko guduma ya kwada mata haka taji,tsoro da firgici suka
cikata,saboda daga yanayin yadda yake maganar ya tabbatar mata cewa da gaske yake
bada wasa ba,ta kalli hagu da damarta,ko ina ya tare babu wajen kubuta,amma zata
gwada,don kome zai mata ba zata iya abinda yace din ba,gwara ya mata duka da
bulalarshi yafi mata sauqi.
"Am so sorry" ta samu kanta da furtawa cikin rawar murya,sake hade rai yayi
tamau
"A soron gidanku nake kwana?" Yayi maganar yana dage mata dukka girarshi,saita kada
kai
"Kayi haquri....banfa sani ba" kanshi ya kautar yana sake hade rai
"Sanda aka raba haquri bacci nakeyi" saita ware idanunta duka,wai dama ya haidar
din ya iya magana haka,harda su baqar magana duka?
"To ka cire kayan....ka bani Allah xan wanke"
"Banaso,nima ina da hannu,and bakisan ni qazami bane....daqyar nake iya yin
wanka?,kinga shine xaifi bani wahala ba wanki ba" sake zare ido tayi,tasan dai
zaginta kawai yake,mutumin da idan heater din sassansa ta samu matsala kowa a gidan
ya banu da dafa ruwan wanka.
Ta gama fahimtar bazai haqura ba dai din,don haka ta faki idanunsa,tayi wuff
da niyyar guduwa,saidai taku uku kacal tayi taji an danqi hannunta
"Baki isa ba,ki batan jiki,ki batan kaya ki batamin guri kuma sannan ki
gudu?,selfish girl".
Qafa ta soma bubbugawa tana tara qwalla ko zai tausaya mata,yadda dai takeqa
hajja ta karya mata zuciya,saidai abinda bata sani ba,hakan da takeyi tsokano 'yan
maza takeyi,saboda ko ina na jikinta dake rawa,idanunsa ya lumshe ya dora yatsansa
saman labbansa bayan ya bude idon yace
"Shshshsh......ni banyi kuka ba saike?,zan baki another option.....koki wankemin
jiki,ko na wanke da kaina,amma fa yadda kika jiqani kema saikin jiqe" da sauri ta
gyada kanta,a tunaninta wannan shine zaifi mata sauqi,saboda tayi zato zaya dauko
zobon ne ya kwara mata shikenan an wuce wajen,saidai ina,kafin takai ga wani
tunanin sai ji tayi kawai ya dauketa gaba daya yayi bandaki da ita.
Shi kuwa baya ya juya mata,haka kawai murmushin yadda tayin ya subuce
masa,yakai geji,yana jin ya kamata ko yaya shima ya dana.
Batayi aune ba saijin mutum tayi tsulum cikin ruwan,da sauri ta daga kai don
yin qorafi,amma suna hada idanu ta maida kanta qasa,qirjinta na wani irin
bugawa,zuciyarta kamar xata fito,bata raina kanta ba sai daya dauketa gaba daya
yayi mata masauki a qirjinsa,cikin hanzari ya ware hannayensa ya soma yawo dasu ko
wane sashe na jikinsa,duk wani waje da yasan yana tsole masa idanu.
Cikin lokaci qanqani ta gigice,tana tuna abinda ya faru kwanaki uku ko hudu
baya kada ya sake maimaita kansa,shikam ko a jikinsa,sai da yaga dama a qashin
kansa sannan ya saurara.
Wankansa yayi har a sannan bata iya kallonshi ba,sai daya gama ya daura
babban towel a qugunsa,saiya bude rariyar ruwan ya fita ya tara mata wani
"Zaki iya wanka" daga haka ya taka ya fice.
Tana qananun qwalla tana wankan,a haka harta kammala,sai kuma ta rasa me
zata sanya ta fito?,idan ma ta fito din wanne kayan zata sanya tunda wanda tazo
dasu sun jiqe?,towel ta hanga don haka dole shi ta daura,Allah yasa ya cire mata
hijabin bai jiqe ba,saita saka shi ta fito daga toilet din a hankali kamar wadda ta
yiwa sarki qarya kanta a qasa.
Waje daya ta samu ta zauna sanda ta fito din,yayin da yake gaban mudubi
yana shafa mai,wani wasai yakejin ranshi da gangar jikinsa,wani shauqi da baisan
daga ina ya taso ba yana ratsashi,itadai batasan me ake ciki ba sai taji sautin
muryarsa yana cewa
"Hello hajja.....a samu yaro ya kawo mata kayan sawarta" shuru ya danyi da alama
silleshi hajjan take,don murmusawa yayi kadan sannan yace
"Gani nan....zanzo na dauka da kaina" da haka ya kife wayar,ya qarasa shiryawa a
gurguje ya fice,saita bishi da kallo tana dora hannu saman ka,shikenan ya janyo
mata,ta shiga uku wajen hajja,tasan wallahi watan yi mata tijara ne ya kama,yanzu
duk wanda yaga yaje dauka mata kaya saiya dauka wani abunne ya faru,kawai sai taji
hawaye yana sauko mata.
Ya kusa minti goma sannan ya dawo,ya zube mata kayan wajen kala uku,abun
kunyar ma data daga harda undies dinta da bra,ji tayi kaman qasa ta tsage mata ta
shige,sauqinta daya ma daya dan fita ya bata waje ta shirya,bayan ya dawo yana daga
zaune yasa tayi serving nasa,saita samu waje ta zauna bayan ta gama,lokaci lokaci
yana satar kallonta,murmushi na subuce masa,can qasan ransa ya furta
"Silly girl,zanyi maganin wannan tsiwar taki" yana kallonta tayi kwanciyarta saman
kujera,baice da ita komai ba,saida baccinta yayi nisa kawai ta tsinci kanta saman
gadonshi,ta motsa yace da ita
"Kina tashi akwai punishment,just sleep" saita maida kanta ta kwantar tana irga
qarfin hali da iya qarfa qarfa na ya haidar din,ita gaba daya kwance mata kai
yakeyi,dukka halayen da take gani yanzu tattare dashi mugun baqin halaye ne da babu
wanda ya zaceshi dasu
(Ni kuwa nace matar mutum ai ba wasa ba,duk wanda ke cika baki akan mace ba'a biyo
ta kansa bane),ta qasan ido take hango duk motsinsa,saboda bayan yaci abincin
aikinsa yaci gaba dayi,saidai wannan karon rubuce rubuce ne yaketa yi wanda batasan
na meye ba.
A hankali qamshinsa daya kama zanin gadon da abun rufarsa ke ratsa qafofin
hancinta,wani tattausan qamshi data kasa banbance na meye da meye,tun da can kusan
lambarsa kenan,dashi ake gane yana waje,har zuwa yanzu kuwa duk wanda ya sanshi ya
sanshi da qamshi,sannu sannu take shaqar iska zuwa hunhunta har wani bacci mai cike
da nutsuwa yayi awon gaba da ita.
*_WASHEGARI_*
Tun bayan sallar asuba bacci ya sake daukarta me nauyi,ita da tayi niyyar
zata gudu tunda duku duku,don ba zata iya hada idanu da jama'ar gidan ba,sai gashi
bacci ya kwafsa mata,ba ita ta farka ba sai goma saura.
A rude ta sauka daga gadon,saita hau juye juye,babu kowa cikin dakin sai
ita,don haka ta nufi qofa da hanzarinta tana addu'ar kar ya shigo har sai ta
fice,don babu abinda taqi jini irin su hadu a yanzun,idan ta tuna abinda ya faru
jiya ji take kamar qasa ta tsage mata ta shige.
Duk wanda suka gamu dashi sai taji kunya ta kamata kamar ta shige qarqashin
qasa,musamman da sukaci karo da abba babba,cikin farinciki yake dubansu sanda suke
gaidashi,harda yi musu addu'a sannan suka wuce.
"Muje ki fara gaida ummi" yace da ita yana tareta daga yin sassan hajja,saita
bishi suka wuce sassan ummin tata.
Tana cikin yin breakfast suka shiga,saita ture kwanon,fuskarta itama cikeda
jin dadin daya kasa boyuwa take amsa gaisuwarsu,haka taci gaba da binsu da kallo
har suka fito daga sassan
"Kinsan girman ladan sanya farinciki a zuciyar iyaye?,muje ki gaida mama itama" ya
fadi yana nuna mata hanya,bata ce masa uffan ba ta bishi suka isa sassan maman,ita
dinma kamar sauran,farincikinta bai boyu ba,hatta da momy da suka gaisar,sai
jikinta yayi sanyi,dukka wannan farincikin na meye?,na ganinsu ne tare da Aliyyun
kawai?,da wannan tunanin suka wuce sassan mai gayya mai aiki hajja.
Bayan sun gaisa haidar din yadan zauna a cikinsu anty aliyan,abinda yakan
jima baiyi ba kenan,ba kasafai suke samun damar zamansa cikinsu ayi hira sosai
ba,sai lokaci lokaci,hakan ya sanya zahra barin falon ta shige dakin hajja,don nata
dakin su suwaiba su shige ciki.
Tana nan kwance hajja ta shigo dakin yakai sau uku,a fakaice take mata
habaici a waqe anaso ana kaiwa kasuwa,irin salon waqoqin mutan da din nan,dadai ta
gaji da habaicin hajja saita miqe ta fice tabar mata dakin.
Har yanzu yana falon shida anty aliya da anty nusaiba,zata wuce kitchen ta
samu abinda zataci taji suna masa godiya,da alama ya musu irin alkhairin daya saba
ne.
Inna gaje ce kawai a kitchen din,sai tayi zamanta kawai a ciki,ta hada mata
abincin ta soma ci suna hira,ita dinma zancan haidar din take mata
"Ai gaskiya uwar masu gida kin dace,kinyi dace da mijin qwarai mai hannun
alkhairi,inda ace shidin wani hamshaqin attajiri ne Allah ne yasan mutum nawa me
zasuyi kudi ta sanadinsa,ko a yanzun ma ya zama inuwa ga mutane da yawa,saidai
addu'ar Allah ya qara arziqi" murmushi ta yiwa inna gajen kawai,ta can qasan ranta
sai taji zuciyarta na amsawa da amin............
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: 38
Wani mugun shewa taji sanda ta shiga dakin kwanansu,dama tun cikin aji ta
fuskanci suna gulmarta da ido,don dai da malami a ajin,babu damar suyi mata magana
ne.
Babi babi na tsiya suka bude suka dinga yi mata,ita dai ci kanku bata ce
musu ba,hakanan ta samu kanta da kasa tanka musu,sai data tafi bandaki sannan suka
saurara mata,data dawo kuma aka shiga hirar yaushe gamo,nan ma sai da suka
tsokaneta
"Daga yanzu zanje na dawo qawa kuma sai mukaji dif" tsaki taja tana nade abun
sallarta
"Wallahi hajja ce,ashe ta timer min" dariya duka suka saka,janna tace
"Allah dai ya biya hajja,wallahi ta kyauta min" harara ta jefa mata,hindatu ta
cafke
"Ta taimakeki kuwa,don bakiga kyan da kika qara ba,Allah yasa anyi me gaba daya" ta
fada suna tafawa,dadai ta fuskanci iskanci da tsiya suka tanadar mata buhu
buhu,saita miqe tabar musu dakin,saidai zancan hindatu ya tuna mata da abinda ya
faru a wancan ranar,ranar da yaso yayi mai gaba daya din,sai wani qaramin murmushi
ya sube mata,ita kadai taja hijabinta zuwa qasan hancinta tana jin kunyar kanta da
kanta.
Dawowarta ba jimawa aka soma jarrabawa,wanda daga ita din watanni kadan
suka rage musu suyi jarabawar kammala makarantar,kamar kowanne lokaci dai bata daga
qafa ba,ta bada himma wajen karatunta sosai,duk da cewa lokaci zuwa lokaci
tunaninsa yakan fado mata a rai,har yakan tsaidata na wasu mintuna kafin ta
dora,tun tana yaqin ture zuwan tunanin kwanyarta harta haqura ta bashi dama,saiya
zame mata jiki,don kusan duk sanda tazo kwanciya bacci shine abu na qarshe da
zatayi kafin baccin ya dauketa,kaf xamansu na abuja sai tayi bitarsa,ranar da
zasuyi sallama na qarshe da sauran moments nasu.
Batasan me yasa a kwanakin take yawan duba wayarta ba,koda yaushe tana kan
cheaking sms da watsapp massages fiye da yadda ta saba,batasan dalili ba,sai randa
zuciyarta tayi mata wata tambaya,wanda a take ta girgiza kai alamar a'ah
"Kina tsammanin samun kira da gareshi ne?" Wannan itace tambayar data yiwa
kanta,wanda ko sau daya bata taba yarda da hakan ba.
Jarabawar wannan karon suna samun intervals sosai,don haka duk sanda taga
akwai interval mai yawa saita tafi gida,tafiya gidan yakan sa mata nutsuwa,kuma
yakan sanya taji kamar tadan rage nisan dake tsakaninta da wani abu wanda ada yake
nesa da ita.
Kuka tayi sosai wanda ta kasa yarda da dalilin kukan nata da zuciyarta keta
bata,saidai ko ba komai ta danji nauyin dake qirjinta ya ragu,ranar sama sama tayi
karatun jarrabawar da zata zana a jibi,washegari ta hada kayanta ta koma
makaranta,wanda jarabawar kawaidai tasan saidai Allah ya tsallakar da ita,amma ita
kanta bata gama tantance abinda take rubutawar haka yake ba,ko akwai kusakurai da
gyararraki ba.
Hajja kuwa bin zahra tayi da kallo tun sanda taga tayi daki da sauri sanda
take jajjabin kwanakin da haidar din ya shafe babu shi babu labarinsa,murmushi ta
saki,duk da tana cikin fargaba,saita daga hannunta sama tana cewa
"Allah na gode maka,Allah na gode maka,ko yau na mutu ubangiji ka cikamin dukka
burina,Allah ka qara hada kan zuria'ata da iyalina,Allah ka qarawa annabi muhammad
S A W wasila da fadila" daga haka ta sauke hannun nata,zuciyarta na mata dadi,ba
shakka komai yayi dai dai yadda takeso,tasan cewa da zarar ya dawo komai zai
kammala dai daita.
Ranar da suka kammala jarrabawarsu suka samu hutu na wasu kwanaki ba masu
yawa ba,saboda zasu dawo ne suyi maza su dora sabuwar semester ta qarshe,tana
kwance a dakinsu kamar ba wadda ke shirin tahowa gida ba,tana kallon su hindatu
sunata shiri.
Hindatun ce ta qaraso ta taba zahran dake kwance rub da ciki,saita daga kai
tana duban hindatu,hijabi ne dan madaidaici a jikinta wanda ta dorashi saman
abayarta,wadda ta rufe jikinta ruf
"Tunanin me kike mrs haidar?" Murmushi ta saki,ta tashi ta zauna tana duban
hindatun,fuskarta qunshe da murmushi
"Ina mamakin me ya canza qawayena haka tashi guda" murmushin itama hindatun tayi,ta
zauna gefan zahra
"Tasirantuwa mukayi da qawar qwarai,hakan shiya canza mu,sannan kuma mukayi aiki da
hankali da tunanin da Allah ya bamu,muka ga cewa
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: 37
*KIJI TSORON ALLAH,☝🏾☝🏾☝🏾KADA KI TABA KAYAN DABA NAKI BANE,BA KUMA MALLAKINKI BANE*
☝🏾☝🏾☝🏾
Washegari kuwa qaryar ciwo ta yiwa hajja bayan ta gama hada kayan da xata koma
makaranta dasu a washegari,tayi kwanciyarta da wuri,duk da baccin bai dauketa ba
amma tasha chart dinta,har daga bisani baccin gaske yayi gaba da ita.
Tunda ilham ta kawo masa abincin yace ta ajiye a nan,tsahon wani lokaci yana
zaune,shi baici abincin ba,bai kuma ce a fita dashi ba,haka kawai duk yaji baya
cikin sukuni,abincin ma baya sha'awa ci,xuwa wani lokaci sai gashi ya miqe,ya saka
hannu ya bude dakin,ya leqa farfajiyar waje kamar me neman wani abu,daga baya kuma
ya rufe qofan ya dawo ciki yana jan tsaki.
Tsaye take dakin hajjan rataye da qaramar jakarta,tana tsayen amma sai faman
duba agogo take,tana so ta isa akan lokaci ne,akwai lecturer din dake nemansu,kuma
tasan halinsa sarai,mtuqar ta wuce lokacin tofa ba shakka ko dawa take yawo ba zai
bari ta shiga ba.
Sai data shiga ta yiwa duk mutanen gidan sallama,bata tarda mama ba ta fita
tun sassafe dubiya,umminta dubu biyu ta bata,sai taqi karba,duk da ta yiwa account
dinta tas saboda siyayyar data yiwa kanta da kanta,don kada ta tambayi haidar
din,wanda tunda take bata taba yiwa kan nata siyayya ba sai wannan karon.
Gaban motar ta shige sanda mustapha ke kunna motar,ya tasheta suka fice daga
gidan.
Tun basuyi nisa ba suka soma hirarsu yadda suka saba,cikin raha da
zolaya,gab da zasu shiga farawa wayar mustaphan tayi tsuwwa,sai zahran ta xolayeshi
"Tun daxu ake faman kiranka,hala wata mai rabon wahalarce" ta fada tana sheqe masa
da dariya
"Allah kinga makwancina da yawa.....ki zuba ido,sai nafi mijinki kudi,kibar ganin
aikinmu har yanzu baizo hannu ba,hausawa suka ce gayawa wanda ya tara ya kiyayi me
nema.....kai shine ma ke kira" ya fada yana zaro ido,sai zahran ta qyalqyale da
dariya
"Qaryar kawai,ashema cika bakin naka bai kai ba,tunda gashi daga ganin sunansa
kawai ya saka fargaba" hannunsa daya ya daga
"Na yarda wallahi....ke....kinsan soja kuwa....hmmmm" daga haka ya daga wayar,ya
sanyata a handsfree.
Yana zaune gaban motar ya kamo sashen labari na bbc hausa yana sauraron
labaransu na ranar,yayi masifar kyau cika da kwarjini cikin qananun kaya,idanunsa
saye cikin wani sunglasses mai azabar kyau qirar wannan shekarar,wanda glass din ya
qara masa kwarjini qwarai,jikinsa ba abinda yake fitarwa sai qamshi mai sanyi,wanda
yacakuda da qamshin freshner na motar da sanyin ac dai wadda baya rabo da ita.
Tana shiga motar sanyin daya cikawa motar ya sanyata yin gulmarsa a
ranta,taja murfin motar ta rufe,sannan ta waiwaya kadan tana gaisheshi,ko kallonta
baiyi ba ya tada motar,ya jata da gudu suka fice daga gidan,saita lafe jikin murfin
motar kawai,tana jin bugun zuciyarta yana sauyawa.
Shuru ne ya ratsa motar sanda yake tsala gudu dasu saman hanya,duk da suna
cikin gari basu fita wajen gari ba,ta karanci shima gwanin gudu ne sosai a mota.
"Kin rainani ko?" Ta tsinci muryarsa yana fada a taqaice,dan waiwaya tayi
ta dubeshi kafin ta dauke kai,kansa da idanunsa suka suna kallon titi ne,kasa
amsawa tayi,sai tayi shuru tana murxa yatsunta kamar yadda shima yayi shurun,kamar
bazaice komai ba kuma saiya bude bakinsa gently yace mata
"Ko auren uwaka ubaka mukayi dake auren tasha nidin mijinki ne,kinda da haqqi
wuyana kamar yadda nima nake da haqqi wuyanki,bare ma aurenmu yafi gaban nan,koda
bakiso bani so,koda babu shaquwa a tsakaninmu,tunda iyayenmu mutane mafi daraja a
rayuwarmu su suka daurashi,fita babu izinin miji haramunne kuma ba dai dai
bane....sannan komai niya kamata na zama a sahun gaba wajen sani kafin kowa.....so
please.....please kada ki sake,idan ba haka ba saina daure qafafunki a inda ake
daure qafafun marasa ji irinki" maganganunsa sunsa jikinta yayi sanyi,saita tsinci
kanta da furta
"Kayi haquri" softly,wanda hakan ya bashi mamaki,sai kuma yaji dadi har cikin
ransa,kamar yadda itama mamaki ya kamata,tayi tunanin zai balbaleta da fada ne har
yayi ma kamar zaya daketa,kamar yadda yake musu acan baya idan sukayi laifi,ko kuma
zai gaggaya mata magana,ko yace ta tafi a motar haya,a haya suke hangen
halinsa,mutum mai kushin hali fushi da fada,kafiya da taurin kai,amma sai taga duka
baiyi ko daya ba,ya gaya mata magana ce ta hankali,wanda duk me hankali ta isheshi
ya fahimta cikin ruwan sanyi,basai an qara masa da wani abun daban ba.
Bata yanke daga wannan tunanin ba taga ya tsaya qofar wani babban
kanti,wanda ya hada komai da komai,kusan komai.na buqatar yau da kullum da amfanin
rayuwa suna saidashi
"Wait" kawai yace yana cre set belt din jikinsa ya bude motar ya fita ya nufi
shagon,saita bi bayansa da kallo,yana yin yadda yake taku cike da nutsuwa qasaita
da ginshira,sai daya shige sannan ta dauke idanunta a hankali tana sauke ajiyar
zuciya,yaushe ya haidar ya sauya?,yaushe yayi laushi,to amma ita game da yadda yake
mu'amalarsa da yaran gidansu bataga sauyi ba,donko ranar suna sai daya yiwa su
salma fata fata kan sunkai dare,kuma mazansu sunzo daukarsu kowacce ta shanya
mijinta,har kusan kuka sukayi.
Babu jimawa taji an bude set din baya,shine riqe da babbar leda ya sakata a
bayan motar ya rufe,sannan ya dawo set dinsa ya shiga ya sake tada motar.
Basuyi nisa sosai saman titi ba taji ya sanya casset na karatun dr malam
umar sani fage,kamar yasan xabinta kenan cikin dukka malamai,babu malamin da take
bin karatunsa qafa da qafa kamarsa,take kuma nutsuwa da dukka fatawoyinsa kamar
shi,zallar hikima da dora bawa bisa hanya,da doron shari'a hanyar da zaka samu
lahira irin malamin,batajin a wannan qarnin akwai malami kamarsa,zaiyi wuya,duk da
ba'a rasa bayin Allah,wadanda suke lunguna da saqon qasa da garinmu,kuma Allah
baiyi ambatonsu ya bayyana ba a bakunan bayinsa,amma shi yasan da zaman kayansa.
Wannan karatun shiya jagorancesu,ya kuma rakasu har cikin makarantar.
Suna shiga ya rage gudu,ya dinga gangarawa a hankali har yakai iyakar inda
motoci ke tsaiwa daga nan babu qari,ya kashe motar sannan yana qoqarin bude murfin
motar yace mata
"Dawo set din baya" saiya fita,bude murfin tayi kamar yadda ya umarcetan.
Yana tsaye jikin set din data zauna dazun,kuma tabar jakarta a wajen tana da
buqatar dauka,murya qasa qasa sanda take tsaye a gabanshi nesa kadan dashi tana
facing dinsa tace
"Jakata" saiya dauke idonsa daya tsareta dasu,ya bude motar ya dauko jakar,kudi ya
ciro dubu ashirin daga aljihunsa ya bude jakar ya sanya mata yana cewa
"Ki riqe wannan saboda koda wata buqatar zata taso....zanyi tafiya ne,koda zasu
yanke miki kafin na dawo,karki tambayi kowa,kiyi gayawa mustapha,zaiyi handling
komai" saiya miqa mata jakar,ta sanya hannu zata ansa,sai daya tabbatar ta riqe
saiya janye jakar,ta bada amannarta gaba daya,hakanan bata zata ba,don haka ta biyo
jakar talau,sai gata taja birki a gabansa,dab dashi,don taqi kadanne tazarar dake
tsakaninsu.
Qas tayi da kanta saboda kallon da taga yana mata,ta kuma kasa
janyewa,saboda ko yaya ta motsa jikkunansu zasu hadu.
Jakar ya sake miqa mata,ta miqa hannu a sanyaye karo na biyu zata karba,sai
yasa daya hannun masa caraf ya damqe tsintsiyar hannunta,a tausashe ya jata ya
jinginata da jikin motar,a maimakon dazun da shine ke tsaye jikin motar,sannan a
tausashe ya sanya qafarsa tsakanin nata qafafun,ya kuma dafe gwiwar hannunsa saman
motar dab da kafadarta,idan daga nesa ka hangesu zakayi tunanin tana rungume cikin
jikinsa saboda kusanci,kusancin da jikinta da zuciyarta suka kasa dauka,saboda duk
wani fitar numfashinsa tana jin saukarsa saman fuskarta,hakanan qamshin turarensa
daya danne nata,uwa uba idanunsa masu kaifi da suka sake yi mata nauyi,sai tayi
hanzarin yin gefe da kanta,wanda kafin sakan daya yasa yatsun hannunsa ya kamo
habarta,ya maido da fuskartata saitin tashi.
Bai barta ba sai daya lalubo qwayar idanunta ya saka tashi a ciki,cikin
wani irin sauti dake fita da qyar,can qasa kamar wanda bacci yaci qarfi ya soma
magana
"Zanyi tafiya me nisa.....waje mai hadari,zan iya dawowa,zan iya salwanta a can,duk
da bai cikin aikina.....amma zan shiga da kaina saboda na sake sadaukarwa da qasata
ruhina,inason in samawa wadanda suke cikin qunci salama da nutsuwar ruhi.....pls
forgive me if i hurt you a tarayyarmu"wani irin rauni taji ya mamayeta irin wanda
bata taba ji ba,saita daga idanunta da cikin qaramin lokaci suka hada qwalla taf ta
dubeshi,bata wani abu mai nauyi na sauka saman zuciyarta cakude da wani yanayi da
batasan wanne iri bane,idan kuma ya mutu fa a can kamar yadda yace zai iya
salwanta?,wani sashe na zuciyarta ya raya mata,rayawar daya sanya qwallar data tara
ta subuce mata,ta gangaro saman kuncinta zuwa habarta
"Oh....no,bafa kuka nace ba,banason kuka ko kadan" yatsunsa ya sanya guda biyu ya
dinga dauke mata qwallar,sai daya gogesu tas,maimakon ya daukesu saiya zarto dasu
saman qirjinta,tun daga wuyanta zuwa qasa ya fara mata tafiyar tsutsa dasu,ya kuma
sanya idanunsa cikin nata,take jikinta ya dauki rawa
"Am gonna miss my......" Shuru yayi bai qarasa ba yana ci gaba da kallonta,cikin
qarfin hali ta sanya lallausan hannunta tayi caraf ta riqe hannun nasa tana girgiza
masa kai,murmushi ya saka yana sauke hannuwan nasa,sannan yace
"Matsoraciya......" Saiya saka tattausan labbansa a hankali,yayi kissing nata
softly da wani irin sanyi saman labban nasa da suka ratsa har kwanyarta ya sakata
lumshe ido,tana jin wani feeling na cika zuciyarta,wani yanayi na farinciki yana
cikata kamar ana yawo da ita a duniyar gajimare.
A hankali take tafiya,duk da ta bashi baya amma tana jin tsaiwarsa a wajen
cikin jikinta,saidai batasan meye ya tsaidashin ba,kafin wani lokaci kafin takai ga
bacewa a wajen taji tashin motar tasa a hankali,saita dinga jin wani abu me kama da
kewa yanason kamata,inda tayi qarfin hali ta tattara duk wani jarumtata tayi tayi
fatali da wannan batun,ta kuma qaryata kanta da kanta.
38
Wani mugun shewa taji sanda ta shiga dakin kwanansu,dama tun cikin aji ta
fuskanci suna gulmarta da ido,don dai da malami a ajin,babu damar suyi mata magana
ne.
Babi babi na tsiya suka bude suka dinga yi mata,ita dai ci kanku bata ce
musu ba,hakanan ta samu kanta da kasa tanka musu,sai data tafi bandaki sannan suka
saurara mata,data dawo kuma aka shiga hirar yaushe gamo,nan ma sai da suka
tsokaneta
"Daga yanzu zanje na dawo qawa kuma sai mukaji dif" tsaki taja tana nade abun
sallarta
"Wallahi hajja ce,ashe ta timer min" dariya duka suka saka,janna tace
"Allah dai ya biya hajja,wallahi ta kyauta min" harara ta jefa mata,hindatu ta
cafke
"Ta taimakeki kuwa,don bakiga kyan da kika qara ba,Allah yasa anyi me gaba daya" ta
fada suna tafawa,dadai ta fuskanci iskanci da tsiya suka tanadar mata buhu
buhu,saita miqe tabar musu dakin,saidai zancan hindatu ya tuna mata da abinda ya
faru a wancan ranar,ranar da yaso yayi mai gaba daya din,sai wani qaramin murmushi
ya sube mata,ita kadai taja hijabinta zuwa qasan hancinta tana jin kunyar kanta da
kanta.
Dawowarta ba jimawa aka soma jarrabawa,wanda daga ita din watanni kadan
suka rage musu suyi jarabawar kammala makarantar,kamar kowanne lokaci dai bata daga
qafa ba,ta bada himma wajen karatunta sosai,duk da cewa lokaci zuwa lokaci
tunaninsa yakan fado mata a rai,har yakan tsaidata na wasu mintuna kafin ta
dora,tun tana yaqin ture zuwan tunanin kwanyarta harta haqura ta bashi dama,saiya
zame mata jiki,don kusan duk sanda tazo kwanciya bacci shine abu na qarshe da
zatayi kafin baccin ya dauketa,kaf xamansu na abuja sai tayi bitarsa,ranar da
zasuyi sallama na qarshe da sauran moments nasu.
Batasan me yasa a kwanakin take yawan duba wayarta ba,koda yaushe tana kan
cheaking sms da watsapp massages fiye da yadda ta saba,batasan dalili ba,sai randa
zuciyarta tayi mata wata tambaya,wanda a take ta girgiza kai alamar a'ah
"Kina tsammanin samun kira da gareshi ne?" Wannan itace tambayar data yiwa
kanta,wanda ko sau daya bata taba yarda da hakan ba.
Jarabawar wannan karon suna samun intervals sosai,don haka duk sanda taga
akwai interval mai yawa saita tafi gida,tafiya gidan yakan sa mata nutsuwa,kuma
yakan sanya taji kamar tadan rage nisan dake tsakaninta da wani abu wanda ada yake
nesa da ita.
Kuka tayi sosai wanda ta kasa yarda da dalilin kukan nata da zuciyarta keta
bata,saidai ko ba komai ta danji nauyin dake qirjinta ya ragu,ranar sama sama tayi
karatun jarrabawar da zata zana a jibi,washegari ta hada kayanta ta koma
makaranta,wanda jarabawar kawaidai tasan saidai Allah ya tsallakar da ita,amma ita
kanta bata gama tantance abinda take rubutawar haka yake ba,ko akwai kusakurai da
gyararraki ba.
Hajja kuwa bin zahra tayi da kallo tun sanda taga tayi daki da sauri sanda
take jajjabin kwanakin da haidar din ya shafe babu shi babu labarinsa,murmushi ta
saki,duk da tana cikin fargaba,saita daga hannunta sama tana cewa
"Allah na gode maka,Allah na gode maka,ko yau na mutu ubangiji ka cikamin dukka
burina,Allah ka qara hada kan zuria'ata da iyalina,Allah ka qarawa annabi muhammad
S A W wasila da fadila" daga haka ta sauke hannun nata,zuciyarta na mata dadi,ba
shakka komai yayi dai dai yadda takeso,tasan cewa da zarar ya dawo komai zai
kammala dai daita.
Ranar da suka kammala jarrabawarsu suka samu hutu na wasu kwanaki ba masu
yawa ba,saboda zasu dawo ne suyi maza su dora sabuwar semester ta qarshe,tana
kwance a dakinsu kamar ba wadda ke shirin tahowa gida ba,tana kallon su hindatu
sunata shiri.
Hindatun ce ta qaraso ta taba zahran dake kwance rub da ciki,saita daga kai
tana duban hindatu,hijabi ne dan madaidaici a jikinta wanda ta dorashi saman
abayarta,wadda ta rufe jikinta ruf
"Tunanin me kike mrs haidar?" Murmushi ta saki,ta tashi ta zauna tana duban
hindatun,fuskarta qunshe da murmushi
"Ina mamakin me ya canza qawayena haka tashi guda" murmushin itama hindatun tayi,ta
zauna gefan zahra
"Tasirantuwa mukayi da qawar qwarai,hakan shiya canza mu,sannan kuma mukayi aiki da
hankali da tunanin da Allah ya bamu,muka ga cewa,babu wata rayuwa ta wayewa face
wadda addininmu ya tsara,hakanan kome zakayi kayi abinda zai kauda mummunan tunani
a kanka,mukayi karatun cewa samarin yanzu sam basu da ALQIBLA....ko kuma ince
ALKIBLARSU mafi yawansu bame kyau bace,ba miqaqqiyar ALKIBLA bace,kowanne yana
amfani da yanin shigarmu yana mana hukucin cewa mu din lalatattu ne,duk wanda zai
durfafemu zai durfafemu ne da mummunan niyya.....,suna tunanin cewa mu din mazinata
ne,mun saba kowacce harka data saba addini da al'adarmu,mukaga meye ribar rayuwar
diya mace?,ki killace kanki,ki tsare mutuncinki dana iyayenki,kikai qimarki gidan
miji,qima kuma bawai ta budurci kawai ba,harda ta kyakkyawar shaida da kyakkyawan
tarihi,abun yabo,abun alfahari da zaki barwa 'ya'yanki da jikokinkin ba,rayuwarki
kawai ta zame mana abun misali,yanayin rayuwarki bazai hana a kiraki wayayya
ba,saidai komai naki bisa tsari ne,irin tsarin daya dace"murmushi sosai zahra keyi
cikin jin dadi da Allah yasa ta zama silar gyaruwar halayyar wasu,ta kuma sake jin
dadi qwarai data sake samun tabbacin babu wadda ta saida mutuncinta a cikinsu,sai
tace
"Na godewa Allah da yamin baiwar da mutum hudu suka gyara tsarin rayuwarsu saboda
ni,Allah yaci gaba da tabbatar damu akan shiriya"
"Amin zahra" hindatu ta fada tana ci gaba da shiryawa,jifa jifa suna taba hira da
zahran da har yanzu take kwance
"Wai ba zaki koma gida bane naga babu alamun shiri tare dake?" Baki ta kwabe tana
gyara kwanciyar tata,sam sam batajin wani doki ko murnar zuwa gidan
"Zanje,so nake rana tayi sanyi ne"
"Amma zahra....sai nakega kamar akwai abinda ke damunki kwanakin nan" murmushin
qarfin hali tayi
"Me kika gani?" Sai data rufe akwatinta sannan ta dawo gefanta ta zauna
"Yanayinki ba kamar yadda na sanki ba,don ba haka mukeyi dake ba....like kamar
akwai damuwa a ranki" qaramin tsaki taja
"Ba wani damuwa,kawai yana yine"
"Yanayin kewar soja ko?" Ta fada tana qunshe dariya,cikin qarfin hali da son
qaryatawa tace
"Kamar da can na sanshi ne da yanzun zan damu kaina,karki sake wannan batun don
bashi bane,stress ne kawai na exam" tabe baki hindatu tayi tana miqewa
"Tunda wannan shine karon farko da kika fara yin exam din,maji ma gani" ta fada
tana dariya abunta,batason dogon magana sai kawai ta barta a hakan taci gaba da
kwanciyarta.
Kayan jikinta ta cire ta sauya wasu bayan ta shiga daki,saboda taji inna
gaje bata nan,tana tunanin ta karba girkin daren tunda Allah ya dawo da ita,kafin
nan umminta ta dawo,don ta fara leqa sassan nasu bata taras da ita ba,su ilham din
ma suna islamiyya,duk da sun fara zama 'yammata,gidansu sam babu wasa da karatun
addini,ita kanta da take boarding duk sanda tazo hutu akwai islamiyyar da take zuwa
har a koma hutu,don haka babu wani karatu da yake hanasu karatun addini tun suna
qananunsu har a aurar dasu,ko samarin gidan yanzu haka akwai makarantar dare ta
maza manya da suke zuwa duk dare,har kwanan gobe.
Fitowarta kenan zata wuce kitchen din taji muryar abu sufyan yana cewa
"A matsayinsa bashi zaije wajen ba....shi xai tura,amma kishin qasarsa yana ya saka
kanshi sahun masu shiga wajen,waje ne mai hatsari,wanda yawanci ko rashi aka samu
sai randa suka dawo ake qididdige wadanda suka mutun a bada sanarwar mutuwarsun a
hukumance.....amma kuma abun daure kan shine,shi din yana da 'yancin fita ai yayi
wayarsa,ko ya sauka a masaukin daya zaba.....amma shurun yayi yawa,ace har yanzu
babu wani motsi daga wajensa" kamar an buge mata gwiwoyinta haka taji,sai taji
kamar ba zata iya qarasawa kitchen din ba,zata zube ne a wajen,daqyar a daddafe dai
ta samu takai kitchen din,saita dafe kantar kitchen din ganin tana niyyar zubewa
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" abinda ta dinga maimaitawa kenan,sai taji
hawaye na sauko mata,zuciyarta ta shiga gaya mata ya mutu,ya haidar ya mutu kawai.
Kifewa tayi saman kantar ta soma kuka sosai,kuka mara sauti,mai dauke da
rashin madafa,batasan iya lokacin data shafe a haka ba,sai data tsinci muryar hajja
na fadin
"Ke,lafiyarki kuwa?" Dago kanta tayi da fuskarta ke jiqe jage jage da hawaye ta
dubi hajja,cikin muryar kuka
"Hajja....." Saita kasa.magana,ta juya da sauri ta fice a kitchen din,hajjan ta
bita da kallo kawai.
Tun daga lokacin bata kuma fitowa a dakin ba bare ta tambaya wani
abinci,har zuwa washegari data sake jin abinda ya daga mata hankali,tara su abba
yusuf da hajja tayi cikin damuwa tanason su nemo wani labari daga bangaren haidar
din,wata kusan biyu shuru?,wannan shi yasa ta qara rafkewa,saiga zazzabi mai zafi
ya rafketa.
Ba wanda ya sani saida hajja taji shurun yayi yawa sannan ta leqota,hankali
tashe hajjan ta kira mustapha ya kira mata abban tsakiya tun baikai ga fita da
motarsa su kai zahran asibiti,koda akaxo tafiya ma kasa tashi tayi,Allah yasa sadiq
yana gidan yazo hutu daga wajen aikinsa,shiya dauketa ya kaita bakin motar suka
wuce asibitin.
Taimakon gaggawa suka bata,aka daura mata ruwa bayan allurai,ba jimawa bacci
mai nauyi ya dauketa.
Zaune take saman gadon asibitin,inda ta jingina bayanta da bango,ta kuma miqe
qafafunta saman gadon,cup din tea ne a hannunta take kurba kadan kadan,tanayi tana
yamutsa fuska,saboda anty aliya ce ta sanyata a gaba akan sai tasha din,tana ta
fada gami da bambamin ta yaya zata samu lafiya taqi abinci sai magani da aketa
dirka mata,bayan ga ulcer nan itama da takeson tayar mata.
Dukkansu bakin gadon suka taho kai tsaye,anty aliya na gaida abba yusuf da
hajja,ya sadiq kuma ya gaida anty aliyan,gaidasu tayi sannan sukayi mata sannu da
jiki,abba yusuf da ya sadiq din basu jima ba su suka tafi suka bar hajjan,don dama
ita din kusan kullum yini takeyi.
Dakin saiya zamana daga ita sai hajjan sai anty aliya,sawa tayi aliya ta kawo
mata kujera gaban gadon,tana shirin zama tace
"Nidai jikin nan naki har yanzu banga irin sauqin da nakeso ba....anya zahra'u babu
wani abun kuma?" Ta tambaya tana dubanta,shuru tayi mata,don batasan amsar da zata
bata ba,duk amsar da xata bata din zata zama tamkar tonuwar asirinta ce,sirri ne da
a yanzu bata buqatar kowa yasanshi.
Bata kai ga cewa komai din ba wayar hajja ta soma ringing,tayi kiciniyar
daukowa ta kasa,saita miqawa aliya
"Ke fitomin da wayar nan,umaima ce don jaraba ta cusa min ita can ciki....ni idan
banda dole ma me ya kaini ta'ammali da wannan aba" dariya sosai aliya tayi sannan
ta karbi jakar ta ciro mata,idanuwanta ta fiddo waje
"Kai.....haidar ne" zancan da ya sanya zahra saurin dago da kanta,qirjinta yayi
wani irin bugawa,saita tsurawa wayar da hajja tayi hanzarin karba,ita dinma kamar
zata wafta ne daga hannun aliyan saboda tsabar sauri.
Batasan mintina nawa tayi a hakan ba saijin dawowarsu hajja tayi,ta bude
idanunta da sauri,tabi hajjan da kallo,ta tsammaci jin wani abu daga bakin
hajjan,amma sai taga taja kujera tayi zamanta abinta kamar yadda ta tashi dazu,hada
idanun da sukayi da zahran sai hajjan tace
"Lafiya?,ko jikinne?" Kai kawai ta girgixa mata,ta maida idanun nata ta sake
lumshesu,ita kadai tasan yadda zuciyarta ke mata,kamar ta jawo hajja ta tambayeta
me yace?,shi dinne da gaske?,saita sanya ran idan anty aliya ta shigo zata ji wani
abu daga gareta,aqalla ko relief zata samu.
Sai daya daga cup din ya qarasa shanye shayin ciki ya dire kofin sannan ya
bashi amsa
"Inaso ne a sanda xan koma soyayyata tayi mata yawan da ba zata iya boyeta ba,tayi
ɗokina fiye da kowanne mutum cikin ahalina...." Murmushi saif ya sake sannan yace
"Kana da yaqinin tana sonka kota fara sonka kenan?" Miqewa tsaye yayi ya maida
hularsa saman kansa,ya dauki bindigar da sukayi amfani da ita,ya kira daya daga
cikin sojin dake zirga zirga ya bashi yace yakai tint dinsa sannan ya maida dubansa
ga saif
"Ba'a iya rayuwa da al'ummata nake soja kawai ba,har a soyayya ni din sojan ne,ban
barta na taho nan ba,sai dana tabbatar na dana mata tarkon da bata isa ta
tsallakeshi ba,na bar mata tabon da bazai taba goguwa ba........na yarda da
kaina,na kuma yarda da qwarewata....".
Miqewa saif yayi yana murmushi yayi saluting nashi,sai shima ya saki
murmushin ya juya yana takawa a hankali zuwan wajen sojojin daya baro.
******** ********
Tun daga ranar take kasa kunne ko zataji wani yayi zancan ya zakin amma bata
ji ba,har hajja kuwa,saidai wani lokaci idan ya kira hajjan tana gane hakan,amma
harsu gana wayar ta koma gida ba zatace da ita komai ba.
Sannu sannu saita fahimta bayan hajjan ma yana kiran manyan gidan,ranar data
gane hakan kawai sai taji ranta ya baci sosai,a lokacin nurse tana zare mata ruwan
da yayi saura
"Ya kamata ku sallameni hakan,na gaji da zaman asibitinku" murmushi nurse din ta
saki
"Madam ko kina tausayin me gidane daya biya kudin asibitin?,shi yace a barki ki
huta sosai koda an gama baki dukka magungunan" shuru tayi tana mamaki,wanne me gida
kenan?,ta tambayi kanta,amma kuma tunda taji tace maigidanta lallai ba shakka ya
haidar take nufi,idan hakane shin yasan bata da lafiya?,tambayar da bata da amsarta
kenan.
Washegari ta takura akan lallai sai sun sallameta,hakanan suka rubuta mata
sallamar tunda ta takura suka tattara suka koma gida.
Tun randa suka koma gidan tayi qoqarin basar da komai,tayi qoqari ta cire
tunaninsa da damuwa dashi daga ranta,saboda ta fuskanci akwai wata a qasa tattare
da hajjan,sai taci alwashin ba zata bari kuwa bari hajjan ta gano lagonta,amma
abinda bata sani ba shine shin zata iya?.
_gobe ina da uzururruka,idan kunjini shuru kuyi afuwa,idan kuma dama ta samu zaku
ganni da yardar mai duka,na gode_
39
Da yake anguwar tasu babu laifi basa rasa nepa,tv ce a kunne take
aiki,saidai dukka hankalin zahra yana kan wayar hannunta,charting take,kuma tana
jin dadin xaman sosai.
Wayar hajja dake gefanta taji ta dauki burari,ta waiwaya ta kalli wayar da
yake tana dab da ita kan hannun kujerar da take kai,number ce babu suna,yanzun
hajja ta tashi bata jima ba ta shiga toilet,saita miqa hannunta daya ta jawo wayar
ta daga ta kara a kunnenta,yayin da daya hannun take ci gaba da danne dannenta
dashi a tata wayar
"Hajjan bata kusa,amma idan ta iso xa'a gaya mata" shuru taji anyi,duk da cewa da
alamu bawai rashin network bane,tunda ga hayaniya irin daga dan nesa da inda me
wayar yakeyin wayar nan tana shigo mata tana ji,saita dan maida hankalinta kan
kiran,ta daga wayar ta duba taga ana kan layi,ta sake maidawa kunnenta tana fadin
"Hello....ance hajjan bata kusa,idan ta fito za'a gaya mata" jin still dai an sake
yin shuru sai ta daga wayar daga kunneta hadi da jan tsaki,ta kashe kiran,ta maida
wayar gefanta ta aje taci gaba da chart dinta.
Tana shirin shiga wani grp nasu na 'yan makarantar kachako unity
girls,group ne na 'yan set dinsu da suka gama makaranta a shekarar,saiga saqo daga
saman watsapp dinta ya shigo da baquwar number,bata fasa shiga grp din ba,sai data
shiga ta gama uzurinta ta fito sannan ta duba saqon,saqone da bai wuce layi daya
ba,amma saiya tsaya mata a rai,ta dinga nanatashi ita kadai
*_KINYI NESA DA IDANUNA DA RAYUWATA,AMMA KINA KUSA DA RUHI DA ZUCIYATA_*
sake shiga profile din tayi ko zata ga suna,babu suna babu dp,ta bincike
contact dinta tsaf babu me irin number,zargin da yazo kanta yasa tayi saurin daukar
wayar hajja ta bude,ta loda numbers din ta danna dial ko zataga suna ya fito a
number amma babu,tabbacin zarginta ba haka yake ba kenan,ba haidar bane,to waye?.
Jin takun tahowar hajjan yasa ta maida mata wayar ta ajjiye,don ta lura
yanzu wani gani gani take mata akan wayarta,saidai ta ganta hajjan
"Me akemin da waya ne?,bana son fa satar lamba ahto....idan mutum naso yayimin
magana da kaina na dauka na bashi" shuru zahra ta mata,sai da taga ba zatayi shuru
ba sannan tace
"Ni ai duka wayarki hajja babu lambar da xan sata fa,babu,ni kawai ko bandakin zaki
shiga ki dinga shiga da abarki ma huta" baki ta tabe
"Oho dai,banda rashin gaskiya daga jin tahowata sai a maida waya da sauri a
aje,kinga kuwa ai babu gaskiya ne" ta qarasa maganar tana zama,sai kawai zahran
tayi kwanciyarta ba tare data sake amsa mata ba,tana ci gaba da maimaita
saqon,jikinta yana bata daga inda saqon ya fito,amma zuciyarta ta gaza gasgata
hakan,har sai data gaji da kallon saqon,kamar shi xai bata amsar tambayarta,ta
sauka daga watsapp dinma gaba daya,saita dora wayar saman qirjinta ta lumshe
idanunta tana tuna wasu abubuwa da suka zame mata farilla kullum sai tayi bitarsu a
kwanyarta,haka nan tunasu suke sanyata nishadi suke kuma debe mata kewa.
Yamma ce lis,wanda tun safiyar ranar ake fama da hadowar hadari da kuma
washewarsa,saidai zuwa yammacin hadarin ya hadu sosai a sama,yana bada iska mai
sanyi hadi da qamshin qasa,wanda hakan ke alamta cewa ruwan sama na tafe kowanne
lokaci daga sannan
Suna daga zaune suka jiyo qarar shigowar mota harabar gidan,ilham ta kalli
umaima
"Kai....yau wani cikinsu abba ya dawo gida da wuri,mun shigesu yau munyi fashin
makaranta....wallahi mu nema wajen buya" harara zahra ta aike musu tana cewa
"Ko kun buya saina gaya musu,ba yadda banyi daku ba ai kuka qi ji,haka ma
hajja,gwara ma ku xauna suxo su ganku yafi muku sauqi" tana rufe baki hancinta ya
soma shaqar mata qamshinsa,saita saki ajiyar zuciya,tana mamakin yadda ta damu da
lamarinsa haka da yawa,tasan cewa ba shi din bane,kawai kamar ta saka lamarin a
ranta ne da yawa shi yasa take jin hakan,don haka tayi shuru tana duban bakin qofar
dakin hajja tana kallon yadda iska ke daga labulen falon.
Kamar a mafarki taga tsaiwar mutum bakin qofar falon,gabanta yayi wani
faduwa data jima bataji irinta ba,ta daga kanta a hankali daga kan takalman da
idanunta ke iya gani zuwa sama fuskar mutumin dake tsaye.
Kansu gama ficewa hajja ta fito,tayi turus cikin mamaki tana dubansa
"Kai kuma yaushe ka shigo?" Fuskarta na washewa da fara'a
"Yanzun nan,ko minti daya banyi ba" sakin labulen data riqe tayi,ta soma takowa
ciki
"Lale marhabin,wannan irin tafiya haka babu sanarwa babu labari?,tun muna ta zuba
idanun ganinka har mun haqura mun janye" dan qaramin murmushi ya saki na gefan baki
yana gyara tsaiwarsa,har yanzu idanunsa yana kanta,ita ke daukar hankalinsa tunda
ya sanya qafafunsa cikin falon,wani irin kyau da haske yaga ta qara masa,sai yake
ganin kamar an canza masa ita,bai sani ba,tsabar kewar data addabi ruhinsa
zuciyarsa dama gangar jikinsa ce,ko kuma dai hakane da gasken ta sauya,yaci gaba da
dubanta ta gefan ido sanda take miqewa daga qasa zuwa kujera,saboda wani irin weak
da jikinta yayi cikin qanqanin lokaci
"Barka da dawowa" ta fada kanta na kallon yatsunta data sawa lalle jiya da
daddare,saboda ta gaji da yadda sukayi fari,har faratan hannunta.
Ko kadan ba tare da wani jin nauyi ba,kamar ma ya manta da hajja dake wajen
ya zuba mata mayun idanunsa
"Barkanki......mun sameku lafiya?" Yadda ya amsa din ya tilastata daga idanuwanta
ta kalleshi,taci sa'a kuwa sun hada ido,saiya jefa mata wani kallo data ji ya girma
kanta,tayi saurin dauke qwayar idanunta,sai kuma tayi rashin sa'a suka fada kan
hajja,ashe su take kallo,hajjan kuwa data gwanance wajen iya fuskewa dauke idanunta
tayi kamar ba'ayi hakan ba,saita miqe ma data jiyo ringing din wayarta tana cewa
"Yauwa....ina zuwa,Allah yasa nusaiba ce".
Fitarta sai falon ya zamana daga ita sai shi,gyaran murya yayi kamar wanda
ya qware,ta fuskanci so yake ta sake kallon qwayar idanunsa,wanda ta karanci
al'amura masu dama a ciki,bata jin xata iya bari cikin lokaci kadan ta fadi qasa
warwas,kota bari ya gane lagonta,ita din ba yau ta fara soyayya ba,tuntuni ta gama
karantar kanta tsaf,ta kuma karanci inda zuciyarta tasa gaba,saidai karatun ya bata
tsoro qwarai,saboda banbance babancen soyayyarshi data mata wani irin kamu ta ruwan
sanyi da sauran soyayyar data yiyyi a baya,wanda yawancinsu sun mata kamu ne ta
farat daya,bata taba zata ko kawowa cewa soyayyar da zata dinga shiga jikinka tana
dafa ka a hankali tafi illa fiye da wadda zata kamaka farat daya ba.
Bata dauki wani lokaci mai tsaho ba,kasancewar abincin dai dai cikin daya
zuwa mutum biyu tayishi,ta shirya komai bisa wani tsari me birgewa,tana gyara
kitchen din hajja ta shigo,ta kalli yadda ta tsara komai saita kyabe baki
"Ashe dai ashe dai,yanzu dukka zakin aka yiwa wannan?" Waiwayowa zahran tayi tana
duban kwanukan data shirya da hannunta,sam batasan ma tayi abunda hajjan ta gani
din ba sai data magantu,komai a tsare,duk wanda ya kalla saiya burgeshi bare ya
bude ciki,flask din hajja ne sababbi,wanda jikoki da 'ya'yanta ke siyo mata da
wanda ake bata kyautarsu dake ajiyewa bata amfani dasu suta dauko ta bare ta zuba
masa abincin a ciki
"Ya gama ci kuyi lissafin kudin kwanukana,saikun bayani,ko naje har gida na fanshe
a kitchen dinki" kunya taji ta kamata sosai,don bata kawo komai a kanta ba sai
yanzu,sai ta yiwa hajjan tabarmar kunya,tahau zumbura baki tana cewa
"Wai komai mutum yayi shi bai iya ba,inafa zaman zamana kika ce sai na masa
abinci....inda naqi tashi kuma nan ma qilu ta jawo bau,nayin kuma nan ma ban miki
gwaninta ba....to inaga kawai a fasa kai abincin"
"Iyeee.....to uwata,ni meye nawa a ciki idan baicin bama,asarata ko taku keda
shi?,ki tambaya kiji,mijina bai taba neman abinci ya rasa ba wajena har ya
mutu,girki ma daya amsa sunansa ba irin nakun nan ba taba ka lashe....wanda kula da
mijinma kamar an muku gori sai ance kuyi,yo ni meye nawa afasa kai
masa.....kai....mustapha" tahau qwala kiran gangan da ganganci,don tasan mustapha
baya falon,baya ma gidan gaba daya,tun safe abba yusuf ya aikeshi gyaran
motarshi,ai kam a sukwane ta saki kwanon hannunta cikin sink ta isa gaban kwanukan
"Saiki bari na bayar da kaina nida nasha aiki,amma kya kira ya musty mai shegen ci
da saiya kusa hadawa da flask din duka ya cinye ma?" Dariya sosai ta qwacewa hajja
ba tare data shirya ba,sai kuma tadan maze bayan ta gama dariyarta
"Ya suke da mijinki wajen shegen ci,kijimin yarinya" itadai sai raba ido take,kada
hajja tayi mata aika aika,bata sake tanka mata ba har ta gama abinda ya kawota
kitchen din ta fice abinta ko a jikinta.
Gangar jikinsa ce kawai zaune waje daya da sunan hutu,amma gaba daya
zuciyarsa da qwaqwalwarsa sun gaza samun hutun da yake buqata din,ga yunwa da
yakeji amma ya kasa katabus,minti daya biyu saiya dubi qofar shigowa sashen
nasa,haka kawai jikinsa ke bashi tana nan zuwa gareshi kowanne lokaci,saiya yunqura
zai tashi ya aiwatar da abinda zuciyarsa ke gaya masa,sai kuma miskilanci ya
maidashinya zaunar,yana sonne ya tabbatarwa kansa cewa aikinsa yayi kyau?,duk da ya
fara ganin alamomi da suka sanya ya baiwa kansa mark,tare da shanshano qamshin
nasara,mutum ne shi daya tashi kaf rayuwarsa cikin cimma nasara kan abunda yasa
gaba,matuqar nasararsa ta kasance......to wannan shine mataki na qarshe da zai kawo
qarshen komai.
Mummunar faduwar gaba hadi da bacin raine suka bijiro mata sanda taji ya
ambaci sunan mace cikin wayarsa,hakanan yana wayar cikin sakin fuska,abinda ba zata
iya tune yaushe ne lokaci na qarshe data jishi yana waya da wani koda namiji bane
cikin walwala haka,wani abu ya taso ya tokare mata maqogaro,har yasa kunnuwanta
suka toshe,ta daina ji ko gane maganar da yake,maganganun da hasashen da zuciyarta
keta kawo mata su take fahimta,don haka tana dire kwandunan hannunta tayi hanyar
fita ba tare data ko kalleshi ba.
Ganin ta nufo qofar gadan gadan saiya taka a hankali ya qarasa rufe
qofar,ya murza muqulli ya rufeta gaba daya,sannan ya jingina jikinsa da qofar,sai
ya zaman shida ita suna fuskantar juna.
Zata iya cewa bataji ya yiwa wadda suke wayar sallama ba,yadai zame wayar
daga kunnensa ya jefata gefanshi,tsintar kanta kawai tayi cikin jikinsa,ya mata
wata kyakkyawar runguma da taso zabge duk wani baci da ranta yayi kan wayar da yayi
yanzun.
Mintuna a qalla kusan biyar suna tsaye a haka,shuru ba tare da ya sake cewa
komai ba,ita dinma haka,kowa na sauraren bugun zuciya da fitar numfashin dan
uwansa,ita kanta batasan ke ya debeta taci gaba da zama cikin jikinsa ba,sai taga
ya kamata tayi koda pretendin ne,kada ta zubda kanta
"Ka sakeni" ta fada tana tura hannayensa,da sauri ya hannunsa ya birkitota ta dawo
tana fuskantarsa,a maimakon dazu data bashi baya,hannayensa duka biyun ya sanya ya
kama qugunta ya ruqe yana qarewa fuskarta kallo,cikin wata murya mai laushi da
sanyi,can qasan maqoshi wanda koda kana kusa dasu sai ka kasa kunnenka sannan zaka
iya jin abinda suke fada yace
"Zahra...." Mamaki ya kusan kasheta a tsaye a wajen,dama yasan sunanta ne?,eh dole
tace haka,saboda tsahon rayuwarsu cikin gidan bata taba jin ya ambaci sunanta ba ko
a wasa,ji tayi duk duniya kamar yafi kowa iya ambaton sunanta,kamar ya fadi sunan
nata ne da wani yaren daban ba hausa ba
"Ke kadai ce rayuwata bata da amfani cikin taki rayuwar ko?" Ji tayi tambayar ta
mata nauyi sosai,bata kuma gama fahimtar abinda ya fada din
"Yes....kowa yayi kewata amma banda ke....kowa yana nemana amma banda ke,kyautawa
kenan?" Lallai yau mamakin da haidar din yake bata ya wuce tunaninta,da zata iya
zata so ta daga kanta ta kalli idanunshi da fuskarshi,don ta samu tabbacin daga
bakinsa kalaman ke fita
"Kin kyauta....matsamin daga jiki" kamar me jira kuwa ta janye jikinta,haushi ya
cikata taf,ita din ya nemeta?,sau nawa yana kiransu hajja tana wajen ba wanda ya
taba bi ta kanta,kwanciyarta a asibiti saboda waye tayi?,ko don ba zata iya gaya
masa bane.
Caraf aka riqe hannuta,ta waiwayo da sauri don har ta soma yin
gaba,fuskarshi a hade kamar bashi ne yayi maganar da yayin dazun ba,saiya sakar
mata hannun sanda take zamewa itama daga hannunsa,ta juya zuwa inda ta ajjiye
abincin ya bita a baya,ya samu waje ya zauna.
Tana fita ruwa ya tsinke,saita tsaya cak tana kallon yadda ruwan ke sauka
daga sama da gudunsa,shahada tayi ta saka qafarta ta fara takawa cikin ruwan,wata
walqiya me azabar haske aka saki,take ta haska ko ina kai kace tsakiyar rana
ce,cikin sakanni ta dauke,kafin ta gama mutstsika idanunta da walqiyar ta kashe
tsawa mai qarfi ta biyo baya,ai batasan sanda ta juya da mugun gudu ba ta koma
ciki.
A hankali taji sanyin yana raguwa,data lura ashe kashe acn yayi,ya maye
gurbinta da room heater,saita dan samu nutsuwa kadan,ta sake saka kanta tana leqen
ruwan.
Ta saman kanta taji an yafa mata wani abu me qamshi,ta daga kanta da sauri
sai taga ya bude mata lema
"Muje" kawai ya fada,ta tsaya sosai ta fara takawa yana biye da ita riqe da
lemar,hannunta riqe da abinda ya yafa matan,wanda ya kasance qaramin bargo ne mai
laushi sosai,kuma yana da nauyin da zai kare maka sanyi.
Tayi mamakin yadda yake tafe cikin ruwan,yana riqe da lema yana kare mata
ruwan,shi kuma ruwan yana dukansa kamar bai damu bama,hakanan taji ta kasa
daurewa,kamar idan tayi shuru bata kyauta ba,cikin sanyin murya tace
"Da ka saka lemar kai a kanka....ni wannan bargon zai qarasa dani ba tare dana jiqe
ba"
"Kada ki damu,an koya mana tsaiwa cikin ruwa da rana kona awanni nawan ne ba tare
da mun gaji ba....." Kai ta jinjina tana ci gaba da tafiya yana biye da ita.
Suna zuwa bakin sassan hajjan ya zuge lemarsa ya juya abinsa,saita tsinci
kanta da cewa
"Na gode" juyowa yayi kawai ya kalleta sannan yayi gaba,sai dataga bacewarsa cikin
ruwan dake sauka farfajiyar gidan sannan ta taka ta shige sassan hajjan.
A falo ta tadda tsohuwar tana shan kunun tsamiya,ta rasa qaunarta da kunun
tsamiya,saita bita da kallo sanda take sauke bargon daga kanta,can cikin ranta taji
tausayin haidar din,daga yadda ya amsata tasan yaji zafi ne,to amma koma meye
tafison sai an aiwatar da komai daya kamata sannan,yadda hankalin kowa zaifi
kwanciya,ta tar cikin gidansa,an rakata kamar kowacce mace,ko a baya ma data barsu
tayi yaqinin ransu babu komai a ciki,babu wannan abun data gani yana yawo yanzu
cikin idanuwansu a da din (hmmm to hajja,Allah yasa dai burin naki ya cika na miqa
zahra'u dakinta).
Dakinta ta wuce ta canza kaya,ta dawo falo taci abinci,bata jima ba taji
bacci na ziyartar idanunta don haka ta wuce dakinta abinta tabar hajja da husna da
ilham,wanda suma wani lokaci nan wajenta suke kwana,abba babba ya tsara
hakan,saboda yace zahra'un idan ta tafi xa'a bar hajjan ita kadai ne a sassan,kuma
ko yanzun ma idan ta tafi makaranta wajen nata babu kowa,shi yasa suka yo qaura
suka dawo,dama kuma sunfi son nan din.
Kwanaki biyu kenan da dawowarsa,qarfe sha daya saura na safe ya shigo sassan
hajjan,a lokacin abba babba abba yusuf da abban tsakiya duka suna falon
hajjan,zahra na kitchen tana wanke kwanukan data hada musu breakfast,don tun safe
sukazo suna ta lissafi,na haqqin Allah da za'a fitar cikin kudin hajja da ake juya
mata,lokacin fiddawa yayi.
Tunda ta gama ta zuba masa nasa a fulasan da ake zuba masa kamar koda
yaushe,kwanaki biyu kenan tun randa ruwan saman ya tareta hajjan bata sake bari
taje din ba,saidai ta bayar a kai masa kamar yadda ya fada,ita kam zahra nata idanu
ne,saboda tasan halin hajjan,katafila ce sarkin aiki,takan kowa take bi idan
aikinta ya tashi.
Kowanne a parlour din son barka yake gami da sanya masa albarka,tare da
yaba wannan namijin qoqarin sa yayi
"naso ace na qara da abban tsakiya da abba yusuf,to amma kudin hannuna sun qare,ba
zasu isa ayi komai na mutum biyu ba,amma in sha Allah sune a lissafina na gaba"
nunawa sukayi babu komai,su da dan uwan nasu duka abu dayane,sannan suna da yaqinin
da yardar Allah shi mai kai kowa ne cikin dangi idan da halin yiwuwar hakan.
Sun dan jima anan suna tattaunawa cike da farinciki,kafin daga bisani suyiwa
hajja sallama kowa ya nufi wajen neman kudinsa,sai falon ya rage daga hajjan sai
haidar din,sai kuma zahra dake kitcehn tana dora abincin rana kawai don idan ta
zauna ta huta gaba daya,inna gaje ciwon qafa ya hanata zuwa aiki tun shekaran jiya.
Kira hajjan ta qwalawa zahra tace ta fito da abincin haidar,ta zata kai masa
za'ayi,batayi tunanin yana falon ba don haka ta fito gaba gadi haka abunta,wata
straight gown ce a jikinta,wadda tayi mata das a jikinta.
Bayan sun gama gaisawa tayi masa godiya da addu'ar qaruwar aziqi kan umarar
da ya biyawa iyayensu saiyayi mata maganar da ita ta sanya ya kiratan
"Kaya nakeso a hadamin,irin wanda ake hadawa amare a akwati" dariya ce taso kubce
mata amma ta danne,don kada tayi dariyar ta jama kanta jagwal,duk da cewa ita ke
gaba dashi
"Ohkey.....lefe kenan....kaman na nawa?,kuma akwati nawa?"
"Akwati bakwai is okey,nayi hidima da kudaden hannuna....amma banison kaya low
quality please,designers kumadd high quality"
"In sha Allah babu matsala"
"Please su zama ready kafin na dawo"
"To shikenan....babu damuwa" saiya yanke wayar ya aje gefa,ya maida idanunsa kan
titunan da suke wucewa.
40
Wayar ya sake jawowa,wata number ya sake laluba,wanda suke masa aikin ginin
filin da ya siya a nan,yadan jima da siyan filin,tun farkon fara aikinsa ya hada
albashinsa ya siya,hakanan da kadan da kadan ake aikin gininsa,yadda zaifi masa
sauqi bazai wahala ko ya kashe kudi masu yawa ba lokaci guda,zuwa yanzu ginin yayi
nisa qwarai,don abinda ya rage ma sauran abubuwan da ba'a rasa bane,da farko yayi
niyyar ma ya kammala gidan ya saida,amma da yayi tunani sai yaga,bashi da mazauni
kenan duk sanda yazo ganin gida saidai a cikin gidansu,auren da aka daura masa da
zahra yasa ya fasa saidashin kwata kwata,saboda koba zahra ba dama dole zaiyi
aure,idan kuma yayi auren zai dawwama zuwa gidansu ya zauna?,dole yana buqatar
muhalli.
Bai sakewa hajja zancan tafiyar zahran ba,kamar yadda bai amshi kudinta
ba,tayi tunanin waskewa yakeson yi,saita matsa da mita da qorafi,sai ranar daya
sameta zaune ya miqa mata komai da komai na tafiyar zahran da aka kammala bayan an
dage tasu tafiyar da sati daya.
Da motoci hudu duka aka dunguma aka tafi rakiyarsu filin jirgin saman don
wucewa qasa me tsarki,suna ajesu sukayi bankwana dasu aka maida motar gida,dama
daya ta abba yusuf ce,daya ta abban tsakiya,zasu wuce kuma kasuwa ne abinsu,sauran
biyunne na haidar,mustapha yaja daya,ya shamsu da suke tare da ya sadiq sukaja daya
suka koma gida da sauran yaran gidan da aka taho dasu.
Gaba daya wani irin nauyi takeji,surukutar abba babba da mama takeji tana
mamayarta,ko hira ake bata iya magana cikinsu,dama shi haidar din ba wani gwanin
magana bane,sau tari wayarsa tana hannunsa ne yana faman danne danne,wanda baya
wuce duba labarai,ko duba saqonni da suka shafi aikinsu.
Qafarshi daya dora daya kan daya ya sauke bayan ya gama karantarta,ya duba
agogon hannunsa,akwai sauran lokaci kafin a nemi passingers din,don haka ya miqa a
nutse yana daukar hularsa dake ajjiye gefe ya soma takowa inda suke.
Ita ta fara ganinsa,a sace take kallonsa,tunda suke da shi ba zata iya tuna
sau nawa ta taba ganinsa da qananun kaya ba,yau sai gashi sanye da wata dakakkiyar
shadda gezner gray colour,sabuwar dal,sai maiqo take da daukar idanu,wani irin
annurin kyau yake fitarwa na musamman,gaba daya kamanninsa sun canza kamar ba
Aliyyu haidar sojan nan ba,batasan yaganta,batasan tunda ta fara kallonshin ya
ganta ba sai da yazo dab da ita,ba tare da su abba suna gani ba yadan ranqwafa ta
gefan kunnenta kamar xai dauki wani abu
"Idan kinaso kawai kice kinaso,kada ki wani damu da jan ajin nan naki" saiya miqe
ya barta daskare cikin tsananin jin kunya da nauyi,yayin daya bar mata sauran
turarensa tana shaqa wanda ke qara sanyata cikin wani yanayi nason kasancewa dab
dashi
"Waini babu inda zan samu ruwa ne,ishirwa fa nake ji tunda muka fito daga gida"
hajja ta fada,sai haidar din yace
"Akwai.....muje a duba mata" yayi maganar yana duban zahra,a hankali ta miqe,tayi
gaba yabi bayanta.
Slow ta fara tafiya bayan sun fito daga wajen,don a jikinta takejin qare
mata kallo yake tsaiwar da yayi daga baya,rage hanzarinta da tayi yasa ya
cimmata,saiya jera da ita,suka ci gaba da takawa a hankali kuma tare,saidai kamar
wadansu masu shirin film,lokaci lokaci saisu waiga kallon juna,kowanne saiya kama
dan uwansa,sai kuma kowa ya dauke kansa,saidai shi haidar yana maida kansa gefe
daya ne ya murmusa,komai nata ya gama fallasa kanshi,wai amma dole saita ja masa
aji?,saiya samu kansa da wassafa yadda zai qure jan ajinta da kuma kunyarta,qaramar
dariya ta kubce masa.
Kafin su qarasa provision din haushi duka ya cikata,ta dinga jin ba dadi
saboda yadda ake binsu da kallo,abun haushinma yadda duk 'yammatan da zasu gifta
sai taga sun bishi da kallo,yau aiport din a dan cike take,alamun akwai yawan
matafiya kenan a ranar.
Bai fahimta meke faruwa ba sai daga baya,cikin ranshi ya dinga dariya
sosai,shikam zuwan yammatan ma kamar taimakonsa yayi,saiya tallafeta sanda take
kwance kafadar tasa yana tayata,ta dinga zare ido a boye tana tsoron kada fa ta
wuce gona da iri.
Hotel me kyau suka sauka,dab da harami,don daga window dinsu suna iya
hango masallaci,su shida harda wata 'yar qawar hajjan da suka hadu a jirgi,itama
umara ta kawota
"Daki daya mas'ud da halima su zauna daki daya,daki daya kaida zahra,nida rabi mu
zauna a daki daya" hajja ta tsara yadda zasu zauna,duk da mama najin nauyi amma
haka suka amsa,hakanan itama zahran nauyinsu takeji,ga haidar kuwa sai yaji
nutsuwa,yaji har ransa hakan yayi masa,amma saiya basar bai nuna ba saboda yasan
tsiyar hajjan,don haka kowa shida kayanshi ya wuce dakinsu.
Dakine madai daici mai kyau,wanda yake dauke da duk abinda xasu iya buqata a
kwanakinsu,itace qarshen shigowa don tuni haidar shi ya shigo,tana ajjiye qaramar
jakar hannunta taji ya riqe mata hannu,dubansa tayi,ya kafeta da idanunsa har wani
lumshewa sukeyi,saiya matsa hannun da qarfi har sai data dan saki qara
"Badon hajja tace haka ba,da bazaki ce komai ba kenan ko?,saiki bita gotai gotai ki
dinga kwana a bayanta?" Kasa amsa masa tayi,saboda wani nauyinsa kunya da qimarsa
data dadu a idanunta,da kansa ya sakar mata hannun yadan ja da baya sannan ya dauke
idanunshi,order din abinci yayi musu sannan ya wuce bandaki.
Cikin kwanaki biyu suka gama ibadar umara,sai sauran ziyarce ziyarce da suka
biyo baya,sun ziyarci gurare masu yawan gaske wadanda suke da alaqa da tarihin
musulunci,manyan gurare da suke da tarihi da kuma alfarma.
Sosai imani qaunar Allah da manzansa suka sake shigarsu,a kwanakin ibada
sukayi ba kadan ba,hakanan tsakanin haidar da zahra kowa ya tsinci kansa da yin
addu'a cikin zuciyarsa kan katari da kyakkyawa kan tarayyarsa da dan
uwansa,dukkaninsu babu wanda yasan dayansa yana addu'a dominsa.
A kwanakin da suke cikin ibadarsu duk da suna daki guda kowa yana
kwancinsa,da sun dawo daga masallaci ko xiyara kowa zaiyi wanka ya samu wajen
kwanciya,kusan duk kwanciyarsa a qasa yakeyi,yabar mata gadon,yayin data dinga jin
nauyin hakan,duk sanda ta daga idanu ta ganshi kwance saman carfet sai taji kamar
bata kyauta ba,a hankali ta tsinci kanta yana burgeta matuqa,baya ga soyayyarsa
data shigeta ba tare data ankara ba,ta yi mata shigar burtu.
A hanya suka ga wani kantin saida kayan qwalam da maqulashe,zaka iya siya
ka tafi dashi,zaka iya kuma zama kaci a nan,hajja kam cewa tayi bata shiga,zasu
tsaya a waje ita da mama,don dama shi abba babba tashi tafiyar daban,ya hadu da
abokan kasuwancinsa a can tun zuwansu,don haka shi tare dasu yake,su hajja ne
haidar din ke jagorantarsu,ganin haka yasa yace zahra ta biyoshi suje su siyo,su
suka samu abun xama nan suka zauna su kuma suka wuce ciki.
Ita ta dinga dauka musu abinda take ganin zasu iyaci,hannunta ya cika saita
rasa inda zata sanya,tana waiwaya ta ganshi gefanta riqe da kwando,suka hada idanu
saiya saki qaramin murmushi ya miqa mata kwandon,ta zuba a ciki,ga mamakinta binta
kawai yaci gaba dayi tana zaba tana zubawa,kai kace yaro ne da uban gidansa har
suka gama.
Wajen biyan kudin akwai dan layi,saiya duba daura dasu yace ta zauna anan
kada ta gaji,idan ya biya zai mata magana ta taso su tafi,murmushi ya subuce saman
fuskarta,mutum ne shi mai nuna kulawa qwarai,tana sane da yadda yakema mamanshi duk
safiya,dama ba'a maganar hajja,duk wanda ke qarqashinsa yana samun kulawarsa yadda
ya dace.
Ƙirjinta ne taji ya quntat sosai,saita miqe tana cire earpiece din kunnenta
dai dai sanda yake juyowa shida yarinyar suna kallonta,yana kallo ta miqe daga
gurin ta fice da hanzari,zuciyarta na mata zafi,tana hango yadda ya sake mata fuska
sosai kamar ba haidar data sani ba.
"Ke lafiyarki kikema mutane tsaki?" Hajja ta tambayeta sanda ta isa inda
suke,shaf ta manta data isa dab dasu,kishi kawai ke nuqurqusar zuciyarta
"Eh mun gama siya,na barshi a can zai biya kudin,wajenne akwai layi"
"Ai dama....su da basu rabo da siye siyen irin wadan nan abebaɗen".
Tunda ya fito har suka qarasa hotel a tsume take,taqi ma koda kallonsa bare
ta nuna tasan da wanzuwarsa,cikin ransa hakan ke masa dadi gami da burgeshi,ko
banza yasan ya gama kama zuciyarta TABBAS! baya ko shakka kan hakan.
Shima baice ba har zuwa sanda ya dawo daga dubasu mamansa,ya tabbatar basu
buqatar komai kafin ya kwanta.
Sam bata tsammaci dawowarsa da wuri ba,saboda tasan yanayin awa daya a
qalla idan yaje musu sallama kafin ya dawo,itama yau gajiyar da sukayi ne ya
sanyata bata kuma fita ba,saita shige wanka ganin ya fita,donta samu ta shirya a
nutse,tunda yawanci idan yana nan saidai ta shirya cikin hijabi,fitar tasa ne ya
sakata fitowa daga wanka daga ita sai towel a daure a jikinta,ta kuma tsaya gaban
mirrow tana shafa turarukan da take amfani dasu,sannan ta ware gashinta daya jiqe
da shower tana son yadan sha iska kadan kafin ta maida ta kulle,dai dai lokacin
daya turo qofar dakin kunnensa maqale da waya yana amsawa.
Kamar wanda aka jonawa wutar lantarki a jikinsa haka ya dinga ji,karon farko
kaf rayuwarsu daya taba ganinta a haka cikin irin wannan shigar,take aka zare masa
dukkan wani kuzarinsa da lakar jikinsa,saiya juya a hankali yana maida qofar tare
da katse wayar da yakeyi,duk da bai gama isar da saqon da yake isarwar ba.
41
A hankali ya isa bayanta ya tsaya dab da ita,sai a sannan tsoro yadan darsu a
ranta,amma ta dake taci gaba da tsaiwa,tsaiwarsa tasa har jikkunansu na gogar
juna,ya daga tafin hannunsa ya dora saman kafadarta yana kallon fuskarta ta cikin
madubin,saita motsa zata matsa,yayi hanzarin saka daya hannun nasa ya tsaidata tsam
a wajen,sauko da hannun nasa yayi a hankali daga kafadarta zuwa dantsanta har
yatsunta na hannu kamar me mata shafar mai,saiya hade yatsuntsu waje daya sannan ya
saki qaramin murmushi
"Me yasa ko yaushe kike son nuna baki so,kuma baki damu ba,bayan nasan qaryane,kina
so,kuma kin damu dani" idanu ta waro dukka yana kallonta ta cikin mudubi,duk da
jikinta rawa yake saboda kusancinsu da tafiyar tsutsar da yake mata a hannayenta
amma hakan bai hanata magantu ba
"Ni.....ni bana sonka,kuma ba damuwa nayi ba,koma meye kayi rayuwarka cefa"
"Kishi zalla"ya fada a sarari sannan ya birkitota ya zamana suna fuskantar
juna,dukka hannayenta ya kama ya riqe cikin nasa,yana kuma kallon qwayar idanunta
"Rayuwar mu dai mrs pretender.....am tired....na gaji da wannan jan ran ranki ya
dade,na gaji da jira,sai yaushe zaki yarda zuciyarki nason dan uwanki aliyyu kamar
yadda ALIYYU KE SONKI!,sai yaushe zaki yarda kin damu da haidar kamar yadda HAIDAR
YA DAMU DAKE?,sai yaushe zaki fuskanci ke dashi duka kun hau ALKIBLA DAYA ta
soyayyar junanku?....idan ke kinqi fada,kina jamin aji ko?....." Ya tambaya yana
sakar mata wani murmushi da babu abinda yake qara mata face saukar mata da
kasala,da kuma wani mugun sonshi
"Kin cancanci kija ajinki ZAHRATY.....amma yau kam haidar dukka wata jarumtarsa ta
qare,duk dauriyarsa ta tafi,abinda ya jima yana boyewa,abinda ya jima yana
binnewa,abinda ya jima yana tunanin ya mutu babu shi yau ya raya kansa da
kansa......." Saiya dora kansa saman kafadarta duk da cewa ya fita tsaho,yadan
rusuna ya rage tsayinsa,ta yadda hakan zai bashi damar rungumeta sosai cikin
jikinsa,laushin fatarta na ɗai ɗaita tunaninsa,yana jin kamar bakinsa bazai iya
qarasa furta abinda yakeson fada ba saboda nauyi da yayi masa,kamae me rada,kamar
wadda ake zanawa kalaman tun daga saman zuciyarta zuwa qwaqwalwarta haka ya dinga
amsar kowanne furuci me cakude da harafi dake fita daga bakinsa
"Ina sonki....soyayyar da qauna ce tafi rinjaye da qarfi a cikinta,qaunar kuma da
ba daga zuciya kawai take ba,ta ratsa jini qasusuwana da kuma tsokata.....qauna
irin wadda ke cakude da numfashina da kuma raina,wadda babu yadda za'ayi ta fita
daga jikina....saidai ta hada harda numfashina" kalaman da bata tsammaci samunsu
daga wajensa ba,shi din daya kasance cikin sahun maza da dukkaninsu ta basu sunan
MAYAUDARA kuma marasa ALKIBLA,cikin mazan kuma ya kasance mai baudadden hali,mara
uzuri mai zafin zuciya da fada,yau shine rungume da ita kamar zai karya qasusuwanta
yana gaya mata yana sonta?,shine rungume da ita kamar zai maidata cikinsa yake fasa
mata sirrin zuciyarsa?,bata gama wannan tunanin ba taji numfashinsa na sauya yanayi
"Kina sona zahra?" Ya tambayeta kai tsaye sanda ya cusa kansa tsakanin
wuyanta,saita kasa bashi amsa saboda yawo da yake da harshensa a wajen
"Uhmmmm.....ki amsa min mana" ba zata iya magana ba,saboda abinda yake aikata matan
tuni ya sanya qafafunta sun fara rawa
"Ohkey.....bari na dasa miki sabon harsashin da zaki fara sona koda baki shirya ba"
daga haka ta nemi haske a dakin ta rasa,yasa hannunsa tuni ya kashe dukkan qwan
lantarkin dake dakin wanda yake kusa da madubin da suke tsaye,sai qaramar futilar
gefan gado wadda me dim light,gaba daya ya dagata yayi mata masauki saman gadon
dake dakin shima ya daga qafafunsa da yajisu kamar basu taba sanin meye qarfi ko
kuzari ba ya haye saman gadon.
Kuka take sosai amma shi murmushi ne ke fita saman fuskarsa duk da yana jin
kukan yana sukar zuciyarsa sosai,ya sani akaran kansa cewa bai raga mata ba ko
dis,amma ya ya iya da ranshi,zai iya cewa ba laifinsa bane,tana maqale da ita kamar
wanda aka ce masa za'a qwaceta,zallar sonta sabo fil yake kwarara cikin
ranshi,kamar ya ciro zuciyar tasa gaba daya ya bata kyautarta,ba irin lallashin da
baiyi mata ba,gashi har sha biyu da rabi na dare ta hanasu barci,shi da kansa ya
gasata sosai,sannan ya barta tayi wankan,data gama shiya taimaka mata ta fito,amma
wajen shiryawa fir taqi yarda,sai baya ya juya mata yana dariya ciki ciki yabarta
ta shirya da kanta,ko a yanzunma da take kwance cikin jikinsa sai daya mata fin
qarfi tukunna,baisan me zai sanyata tayi shuru ba,duk da ya lura irin shagwabar da
takema hajja yau take sauke masa,shagwabar da abaya idan yaga tanayi yake aike mata
da saqon harara ko tsawa,sai gashi yau yasa hannu bibbiyu ya amsa
"Kona kira miki hajjan?" Ya fada qasa qasa,da sauri ta maqale kafada,saita cusa
kanta cikin qirjinsa tana sassauta kukan nata,ita kam waya aiketa da wata
hajja?,tazo ta tijarasu kota titsiyesu da tambayoyi?.
Cikin salon qwarewa da dabara hannunsa saman sumar kanta ya dinga kashe
mata jiki,har wani bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita,wanda cikin baccin ajiyar
zuciya ta dinga saki,sai daya tabbatar baccinta yayi nisa sannan ya sauketa a
hankali,ya dora mata kanta saman pillow ya rufa mata duvet,sannan ya soma gyara
mata sumar kanta yana kallon fuskarta,fuskar zahransa,murmushi ya subuce masa daya
tuna tsiwa irin ta zahran,amma yau bakinta yayi laushi sosai,duk da cewa dama ta
jima da canzawa,abubuwan da suka faru dazun suka dawo masa,rakin data dinga
yi,magiyarta da ban hanqurin data dinga masa tana cewa ba zata qara ba,shi kuma
yana tambayarta ba zata qara me ba,dukkansu shida ita ya tabbatar mahaukata suka
zama tuburan,ita ciwo ya isheta,shi kuma duniyar data jefashi ne yasa ya kasa
fahimtar komai.
Sallah ya sauka yayi yana miqa godiyarsa ga Allah,ya sani cewa ubangiji ya
gama masa komai,sai kuma neman taimakonsa kan bauta masa da tsare haqqoqinsa,sannan
ya kuma ya shiga lamarin xamantakewar aurensu,ya bashi ikon da zai riqeta bisa
doron shari'a,kan gaskiya amana tausayi da kyautatawa.
Tana bude idanunta dashi ta soma tozali,ya sanyata a gaba yana qare mata
kallo,saitayi rub da ciki da sauri tana boye fuskarta,yana murmushi shima ya haye
bayanta,ya aza mata nauyinsa yana cewa
"Good morning zahraty amarya" sosai ya bata kunya bayan wadda takeji,nauyinsa
takeji sosai,musamman idan ta tuna waye ya haidar a wajensu,amma gashi dare daya ya
sauya komai a tsakaninsu,kamar bashi ba,kamar wani aka canza musu dashi,bata taba
ganin fuskarsa a yanayin data ganta ba tsakanin jiya da yau.
Wuni sukayi sur cikin dakin ba tare da shi ko ita sun fita ba,sai yayi
amfani da wannan damar,ya dinga lura da ita tare da dasa mata sabuwar qaunarta
cikin zuciyarta,bai yarda sunyi nisa da juna ko raba mazauni ba,ya sanya nata sabo
dashi da saboda jikinsa,tun tana kakkaucewa harta sallama.
Washegari shi da ita kadai suka fita wani waje,bayan sun biya sun gaida su
hajja,yadda ta dinga sussunne kai da jin nauyinsu su duka ya alamtawa hajja me
afkuwa ta afku,duk da ba haka taso ba,taso sai bayan anyi taron biki an kaita amma
ba abun damuwa bane,tunda already matarsa ce.....da fatan alkhairi ta bisu sanda
suke ficewa,saita lura mama ma idanunta yana kansu fuskarta na nuna farincikin dake
qasan zuciyarta.
Karo kusan na hudu kenan tana hada ido dashi sanda suke zaune saman table
din daga ita saishi,waje ne me kyau,wanda kallonshi kawai ya isa ya sanya zuciya ta
debe kewar dake damunta,gabanshi shi babu komai face ruwan roba,sanda aka kawo menu
ita ya zabarwa abubuwan da za'a kawo mata,wanda kusan duk abubuwan kwadayi
ne,yatsunsa ya sarqafe kawai cikin na juna ya zuba mata idanu yana kallon duk wani
motsi nata,kyau take qara yi masa,qaunarta yakeji har babu iyaka.
Karo na qarshe da suka hada idanu tadan kwabe fuska kamar mai shirin yin
kuka,murmushi ya sakar mata yana girgiza kansa,gyara zamansa yayi still dai baibar
kallonta ba,a hankali yace
"U r my first love" cikin mamakin furucinsa ta dakata daga kai ice cream din data
debo bakinta ta zuba masa idanu alamun son qarin bayani,kai ya gyada mata
"Yes u r"Saita samu kanta da tattara dukkan hankalinta a kanshi,cike da mamaki take
dubanshi
"Tun lokacin da aka haifeki na fara sonki,a lokacin da nike tamkar ɗa a wajen
ummi,duk da na fara samun qanne a lokacin,amma sanda aka haifeki ji nayi sai a
lokacin na samu qanwa,a sannan ni kadai kike yarda dani baya ga ummi kaf fadin
gidan" yana fadin haka saita tuna sanda hajja ke bata wannan labarin,amma a lokacin
ta zata hajjan na fada ne kawai saboda taji dadi a ranta,kota rage kaifin jin
haushinsa da rashin jituwar dake tsakaninsu
"Sannu a hankali kina qara gama inajinki cikin zuciyata da gangar jikina,hakan yana
yiwa ummi dadi,amma takan kwabeni kan...nayi a hankali,kada kulawar da nake baki
tasa ki sangarce,saina fara sanya lura da nutsuwa,a sannan sai na lura da kin fara
tabara saboda gata da kike samu daga wajen hajja itama,duk gidan kece ta gaban
goshinta fiye da kowa,saboda sunanta da kikaci,sannan kuma cikin jikokinta kinfi
kowa wuni wajenta,tunda jima sashenta shine wajen zamana a yawancin lokuta.
"Bari na samo maka abun sha a wani kanti nan" ta fada ta soma takawa,da
hanzari na tsaidata
"A'ah....ni ganinki kawai nazoyi,bana buqatar ci ko shan komai" kafada ta maqale
"Ban yarda ba....saboda nima irin karamcin nan naka nakeso na koya,saboda haka
saina samu ladan baqona" daga haka ta soma takawa ta cikin ciyayin nan tayi gaba,a
cikin zuciyata inason tsaidata amma kamar wanda aka daurewa baki na kasa,inasin
ince kada tabi ta wannan ciyayin amma na kasa fada mata,inason ince mata ta tsaya
na rakata amma dukka kamar wanda aka daurewa baki duk na kasa fada,ashe ajali
ne,ajali ne ya kirata,don batayi wani nisa da idanuna ba naga gilmawar wani abu ta
bayanta,na fuskanci maciji ne,idan nayi magana kuma zata iya rudewa,don haka na
fara takawa da wani irin hanzari da zafin nama,dai dai sanda ta waiwayo tana
kallona,sai fuskarta ta nuna mamakin ganina ina tahowa inda take da mugun
gudu,bansan ya akayi ba saijin ihunta nayi ta durqushe cikin ciyayin.
Sanda na isa na sameta riqe da qafarta,ta hada gumi sharkaf tana juye
juye,dana dauke hannunta saiga inda macijin ya sareta nan,na bata taimakon daya
dace,na riqeta zuwa asibitinsu na cikin makaranta,saidai abun haushin abun takaici
basu da allurar kashe gubarsa,raina ya baci sosai,amma ban tsaya biye musu
ba,saboda kada bata lokaci ya jawo asarar ran da naketa gudu,na sanyata a mota
kawai muka wuto zuwa kano.
"Irin gudun dana dinga tsalawa ni kaina nasan Allah ne kawai yayi motar ba
itace ajalinmu ba nida ita gaba daya,tana cure waje daya set din gaba taba
murqususun ciwo da azabar dafin daya zuba matan,hankalina rabi ga titi rabi a
kanta,qarin abun haushin asibiti manya guda biyu mukaje suma basu da allurar a dai
dai lokacin ta qare,sanda muka dauki hanya zuwa asibitin mu a sannan ta
kalleni,launin idanunta yana canzawa
"Kayi haquri ya haidar....kayi haquri,kuma naga ranka ya baci,duk abinda Allah ya
shiryawa bawa bai isa ya tsallake mishi ba" saita maida kanta ta kwantar,kalamanta
suka dagan hankali,na tsaya gefan hanya sanda naga yanayin jikinta ya saki gaba
daya.
Nasan a sannan ta mutu don zuciyata tana gaya min haka.....amma idanuna a
rufe suke,saina tashi motata da mugun gudun da yafi na dazu na nufi asibitin,saidai
abinda nake tsoro dai shi aka gayamin,zahra ta rasu,dafin yaci jikinta yakai inda
ba'a so yakai......"saiya tsaya da bata labarin yana duban yadda hawaye ke zuba a
idanunta,a wancan lokacin sam batasan yadda mutuwar zahra ta kasance ba,kawai dai
tasan saran maciji ne,hakanan tana ganin haidar yaqi daukan qaddara ne kawai,amma
data kwatanta mutuwar masoyi ko aboki gaban idanun abokinsa sai taga abun ba mai
sauqi bane,dole ya shiga irin yanayin daya shiga din,kasa jurewa tayi,sai tayi qasa
da kanta kuka na kubce mata.
42
Murmushi ya saki,sannan ya taso daga inda yake zaune,yaja kujera dab da ita
ya zauna har gwiwarsa na gogar tata,hannunsa ya sanya ya dago fuskarta gaba
daya,saiya girgiza mata kai alamun
"A'ah"yatsansa guda daya ya sanya ya dinga dauke mata hawayen,murmushi kwance saman
fuskarsa,har sai daya goge duk wani hawaye da yayi saura,saiya hada goshinsa da
nata suna musayar numfashi,qamshin turarensu na gauraya da juna
"A wancan lokacin kinyi fushi....kin nuna kishi saboda ganina da wata
balarabiya.....wadda nake ganinta da muni sosai idan na hada da kyakkyawar
fusakarki,da kuma yadda zuciyata ta rayu da sonki......ta samu dukka fara'ata ne da
kulawa saboda yabonki da tazomin dashi,ta shaidamin tunda taga shigowarmu taji mun
burgeta.....tana son qawance dake,dalilin da yasa ta biyoni kenan har kika ganmu
tare....saidai kuma a yanzun gashi kina kuka saboda wata da na taba so na baki
labarin mutuwarta...me yasa bakiyi kishin xahra ba?" Ta rasa amsar da zata
bashi,amma dole duk me imani yaji a yadda zahra ta rasun ya tabashi,ta riga data
wuce zahra ba zata taba dawowa ba,kishi da ita tamkar abun nan da hausawa ke kira
da ihu bayan hari ne.
Kwan daya tak suka qara suka fara shirin dawowa,ya bata dama ta siya dukkan
abinda take da buqata,siyayya me yawa da batasan me za'ayi dasu ba.
Kamar yadda suka tafi tare haka suka dawo,sun tadda 'yan Tarbarsu danqam
suna jiransu,family ne mai cike da hadin kai da qaunar juna,babu wani bambanci da
xaka gani tsakaninsu.
Tun a airphort din ta ankare da yadda 'yan gidan nasu keta gulmarta ita da
ya zakin,saboda duk inda yayi yana maqale da abarsa,baya jin kunya ko nauyi
sam,motsi kadan nata idanunsa da hankalinsa yana kanta.
Da zasu tafin bai bar kowa ya shiga tashi motar ba,zahran ta rasa dalili
amma yayi fuska,ta sani dukkansu shakkarsa suke,saboda haka ba wadda ta iya
tunkararsa,sai hafsat data rage bata samu waje ba,tayita zagaye tanason tace ya
dauketa,amma ta kasa,sai zahran ce ta dubeshi
"Please ya haidar....maman khairat ce bata samu waje ba" ta fada cikin
marairaicewa,wani kallo ya watsawa hafsat din ta window,ba shiri ta fara qoqarin
juyawa tabar wajen,amma sai zahran ta yaficeta ganin baice komai ba.
Bai tanka musu ba har aka fara tafiya,basuyi nisa da airport din ba ya
bawa driver umarnin ya tsaya,saiya fidda kudi tana ajema hafsat din fuska a tsuke
"Sauka ki tari napep ki hau....." Kallonshi duka suyi cikin mamaki,saiya hade rai
tsam,zahra ta dubeshi a shagwabe
"Yayaaaaa"
"Shshshshhh...ba gida muka nufa ba,so take muyita yawo da ita?" Mamaki ya
kamata,toba gida suka nufa ba ina suka nufa kenan?,tana ji tana gani hafsat din ta
sauka ta tari napep su kuma sukaja motarsu suka wuce,sai tayi kicin kicin ita ala
dole fushi take dashi,bai tankata ba,data kalli fuskarsa ma sai taga walwalarsa
yake abinsa.
Tanata zuba ido tana ganin yadda suka shiga unguwar,mamakin wajen wanda
zasuje take,daga dawowarsu daga doguwar tafiya irin wannan.
Bata samu amsar tambayarta ba har sai da suka tsaya qofar gidan,mai gadin
madaidaicin gate din ya bude musu suka shige madaidaiciyar harabar gidan da zata
iya cin motoci uku zuwa hudu ba tare da sun takura ba,da kansa ya fita,ya zagaya
inda take zaune ya bude mata motar,fuskarsa dauke da murmushi yace
"Bismillah" dubansa tayi tana maqale kafada tare d zumbura baki,Ranqwafowa yayi
saman kanta yana murmushi
"Beautiful.....wannan bakin naki...." Sai ya saka yatsunsa biyu ya kama labban nata
ba tare daya qarasa fadar abinda ke bakinsa ba,janye bakin tayi da sauri saboda
yawon daya fara da yatsunsa saman labban nata
"Ranki ya dade.....ina miki barka da shigowa gidan aurenki" ya fada murya can qasa
kamar meyin rada,da sauri ta daga ido tana kallonshi
"Ya haidar....kada kayi haka,shi yasa ka hana kowa shiga motar mu....hajja fa"
yatsansa ya dora saman lips dinsa yace
"Shshsshhhhh....banason kiran sunan kowa ba,bansan kowa ba sai ke,nan din duniyarmu
ce ni dake,kema kuma zaki manta da kowa da komai soon" ba tare data shirya ko ta
ankara ba taji gaba daya ya sunkuceta,ta Maqaleshi sosai,saboda ji da take kamar
zata fadi
"Karki damu,a hannun soja kike" ya fada yana murmushi,saita maida masa martani
itama ta maida kanta qirjinsa ta kwantar,tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da
sauri da sauri,sai ta daga kanta cikin mamaki ta dubeshi,murmushi ya sake sakar
mata
"My heart beat ko?,kada ki damu,sonki ne da zumudin kasancewa tare dake" wani
farinciki taji yana ratsa zuciyarta,tanajin alfahari da kasancewarsa mijinta yana
mamaye ruhinta,qaunar hajja ta sake fadada a ranta,tabbas ita din ba qaramar
masoyiya bace,me yasa kaf cikin jikoki da 'ya'yan 'yan uwa bata zabi kowa ba sai
ita?,ita kadai ta dauka ta mallakawa mutum mai tsada da daraja irin aliyyu?,a
hankali a hankali take fuskantar komai,kamar yadda ta taba gaya mata cewa zata
gane,zata fahimci gatan datayi mata,bata da bakin gode mata,bata kuma da abinda
zatace mata face addu'ar gamawarta da duniya lafiya.
Tana daga hannunsa take qarewa gidan kallo tun daga hanya har shigarsu
falo,ba'a cika masa kayan alatu na qarya da barnar kudi ba,amma ya qayatar matuqa
ya kuma bada ma'ana,parlour,two bedrooms with toilets a qasa,dining
area,kitchen,store da wani toilet din a falo,saman benan gidan ma falo ne da
bedroom biyu,kowanne shima da toilet,gaban kowanne daki akwai qawataccen corridor
da zai baka damar ganin gaba da bayan gidan,akwai dakuna daga bayan ainihin ginin
gidan guda biyu masu falo daya da bandaki,sai wajen ajiye motoci matsakaici ha
matsakaiciyar haraba don shan iska.
Dubansa tayi sanda taga yana aje kayansu a dakin daya direta
"Ina nawa bedroom din?" Wani kallo ya mata mai kwantar da zuciyar masoyi,saidai
fuskarsa a dan hade take,saiya zare rigar shaddar jikinsa,jinsa yake gaba daya a
takure,don bazai iya tuna rabonshi da saka manyan kaya ba,banda wannan tafiyar da
hajja ta tubure kan lallai bashi ba saka fingilallu kuma damammun kayan
yahudu,bayan garin ma'aiki zashi.
Sai daya qaraso dab da ita ya dagata tsaye yana riqe da qugunta da hannu
daya,daya hannun kuma yana warware rolling din doguwar rigar dake kanta
"Banason na raba komai da matata,nafison komai namu mu dinga sharing....bawai
saboda babu wadata ko ikon siya ba,a'ah.....inason mu samu kusanci qauna da shaquwa
matabbaciya.....irin wadda a tarihin masoya kaf na duniya babu masoyan da suka samu
shaquwa da fahimtar juna irin tamu" yakai qarshen zancan sanda yake fidda mata
doguwar rigar jikinta,saiya zamana daga ita sai under wear da vest,kaman maye haka
ya bita da kallon qurilla,yadan ja baya kadan ta yadda zai samu damar kallonta da
kyau,saiya miqa hannunsa i zuwa muhallin dako yaushe yake tsone masa idanu,ya
kumayi tafiyar ruwa da nutsuwarsa,gocewa tayi tana dariya,a 'yar tarayyarsu ta
qididdigaggun kwanaki,ta gama fuskantar shi din mutum ne da yake qaunarsu,suka kuma
matuqar tafiya da hankalinsa,cikin zafin nama ya bita zai cafko yana cewa
"Oh....no,don Allah,kada muyi haka dake pleasessssssss" dai dai nan ya samu nasarar
kamotan,ya mannata da jikinsa yana sauke qatuwar ajiyar zuciya,tsayin minti guda
kafin yace
"Duk sanda nake tare dake,nakan manta wanene ni....ashe dai da gaske kedin aljannar
duniyata ce,don Allah....ki rayu dani,mu mutu tare" martani ta maida masa ta hanyar
rungumeshi tsam itama,yadda takeji cikin zuciyarta bazai misaltu ba,a hankali take
rada masa wasu kalamai cikin kunnuwansa,kalaman da suka sake rura wutar dake ruruwa
cikin zuciyarsa,suka kuma sanya ya daina gane komai,cikin qaramin lokaci suka qwace
dukka hankali da nutsuwarsa,wanda hankalin da nutsuwar basu dawo masa ba,har sai
data kaishi wata duniya ta daban,duniyar da kullum yake bege da muradin tabbata a
cikinta matuqar da zahran ne.
Kwance saman qirjinsa wanda tuni bacci yayi awon gaba da ita,yayin da shi
kuma yayi nisa cikin duniyar tunaninta,duk da tana tare dashi amma baya gajiya da
tunaninta,bai taba zaton cewa qaunarta a zuciyarsa tayi nisa har haka ba,bai taba
tunanin zuciyarsa zatayi nisa da zurfi cikin soyayya har kamar haka ba,ashe
ubangiji sonshi yake da rahama daya sanya matsaloli tsakaninta da manemanta a
baya,ashe tanadinsa ce ubangiji yayi masa,shi yasa yake rusa dukkan wata alaqarta
da wani.
Qarar da wayarsa tayi ita ta katse masa tunaninsa,sai daya miqa hannu
sosai sannan ya iya lalubota,saboda fadawa da tayi gefan gado,yana duba sunan yaga
hajja ce,saiya sauke zahran yaja mata bargo ya lullube mata jikinta,ya zura
qafafunsa qasan gadon sannan ya amsa wayar
"Wai ina kuka tsaya ne haidar?,baka duba lokacine?,kusan awa uku?,hafsa tace a
hanya kuka sauketa,kuna ina ne?" Ya bude baki zaiyi magana sai yaji muryar tasa a
dakushe take,don haka ya danyi gyaran murya
"Banason qaniya....ka bude baki kayimin magana"
"Muna gidanmu.....,gobe ko jibi zamu shigo mu sake yi muku ban gajiya"
"Gidanku?,wanne gidan naku"
"Gida na na gaida gida dubu" salati hajja ta saki tana sallallami,jin haka sai
kawai ya datse wayar,yama kasheta gaba daya,ya tashi ya lalubo wayar zahran itama
ya kasheta,ya hadasu gaba daya ya watsa cikin sif sannan ya wuce bandaki yana
murmushi qasan ransa,yasan za'asha daru da rigima,tana can qila ta tadawa kowa
hankali,shikam bazai dauki wannan gantali da aure da hajjan keta yi musu ba,ana
masa wasa da hankali kamar zahran bata gama zama mallakinsa ba.
Kamar kuwa yadda yace din,kwanansu uku cikin gidan su kadai,babu abinda
suke banda morewa amarcinsu,gami da sake dasawa juna sabo da shaquwa mai qarfi a
tsakaninsu,cikin kwanakin zahran tayi mugun sabo da soyayyarsa,wadda ya dinga koyar
da ita salo salo cikin dabara da tsabar qwarewa,sau tari takan saki baki tana
tambayar kanta
"Da gaske ya haidar ne wanann?" Duk inda ta motsa yana maqale da ita,tare suke
komai,girki gyaran gidan,wanke wanke,kai hatta ma wanka bai bari ta shiga ita
daya,idan ko ta sake tayi ita kadai to tayi aikin banza,don sai ta sake,suna aikin
yana tsokanarta,wasan guje guje sam batasan a inda ya koya ba,ya qware a sosai a
tsokana,idan mamaki ya cikata ta saki baki da ido tana kallonsa,saiya hure mata ido
da iskar bakinsa,wani lokacin kuma saiya hade bakinsu waje guda,yace bari ya rage
mata mamakin da takeyi,saiya tsotsi lips dinta iya son ranshi sannan ya saketa,ya
dubeta yace
"Kairukum kairukum li ahlihi,wa'ana kairukum li ahly. خيركم خيركم لآهله وانا خيركم
لآهلي,annabi yace mafi alkhairinku shine mafi alkhairinku ga iyalansa,sai annabi da
kansa yace nine mafi alkhairinku ga iyalina,yana taya iyalansa dukka ayyukan gida
da kika sani....ni din waye da bazanyi koyi da wanda akayi duniya da lahira saboda
shi ba?" Maganganunsa sunyi matuqar burgeta ba kadan ba,da gaske ne duk wanda ya
hukunta wani mutum bisa wai wai ko kuma kallonsa da yake daga nesa ba tare da ya
mu'amalanceshi ba,zai aikata babban kuskure,ashe kalar abinda umminta keta mata
kwadayi kenan?,lallai uwa uwa ce,a kowanne hali makomar rayuwar ahalinta na nan
cikin ranta,komai runtsi komai wuya,Aliyyu miji ne ɗaya da ɗaya,mai tarin nagartar
da kaso mafi yawa daga cikin mazan yanzu suka rasa irinta
(Idan baki samu ba,saiki roqi Allah ya gyara miki dabi'ar naki mijin,ya zama me
koyi da sunnar ma'aiki,idan kuma kin samu,saiki godewa Allah,kuma kada kiyi wasa da
damarki,koki wofantar da baiwar da Allah yayi miki,idan budurwa ce ke....kina da
sauran dama,ki fidda so ko burgewar dukkan wani qyale qyalen duniya daga ranki,ki
tsayawa sallar dare,kiyita gayawa ubangiji da roqarsa ya zaba miki miji na gari,ba
mai arziqi ko kyau ba,miji na gari ya wuce dukkan wani irin nau'in miji daya
mallaki dukiya kyau mulki ko sarauta,miji na gari shine abu mafi tsada da daraja
cikin rayuwar diya mace kaf!!!,da zarar kin dace dashi,tofa matar du wani mai mulki
kudi kyau ko sarauta saidai ta biyoki a baya,matuqar itama ba katari tayi da irin
naki mijin ba,ubangiji ya wadata qannenmu 'yan uwanmu da 'ya'yanmu da nagartattun
maza🤲🏽🤲🏽🤲🏽,dama daukacin matan musulmi gaba daya).
Cikon kwana na hudun suka shirya wajen sha biyu saura suka nufi gida,duk a
kunyace take,saboda batasan da wacce fuska zata kalli jama'ar gidan nasu
ba,musamman mama da umminta,har gwara hajja an saba gauraya.
Sai da suka shiga kowanne sashe suka gaidasu sannan suka wuce sassan
hajja,ga mamakinta ba wanda ya tsokanesu ko ya tada maganar,bare ya nuna yasan me
ya faru,suna sallama sukaci karo da akwatuna masu azabar kyau blueblack guda takwas
cas,kowacce shaqe da kaya a cikinta,wasu daga cikin 'yan uwan hajja ne suka gama
kalla,da alama tafiya zasuyi ma,don har sun miqe.
Zahra dai bata sanya hannu ba har hajjan ta gama kalla tana daga gefe a
zaune,har saida hajjan da kanta tace ta matso ta gani mana,saita girgiza kai alamun
a'ah,hakan saiya burge hajjan,duk da cewa an riga da an zama daya,amma har yau
akwai abubuwan da zahran ke kunyar yinsu,ba kamar 'yammatan yanzun ba,da wata ma
randa za'a kawo lefan tana gidansu,masu kawowa ko qofar gida basa gama kaiwa take
tsallen albarka ta fito aci gaba da gani da ita,tana gani tana comment,tana hanawa
a tattaba mata wasu abubuwan,Allah ya kyauta.
Walima gagaruma haidar din ya shirya a sabon gidan nasu,ranar walimar aka
taho mata da akwatunan lefanta,saiya zamana kamar itace a madadin yinin biki,sosai
aka ci aka sha,aka gabatar da wa'azi da nasihohi ga mata kan zamantakewar
auratayya,wadda ta ratsa zukatan mata da dama,dangi sosai suka halatta,gidan yayi
cikar kwari,saidai anyi taro lafiya an kuma watse lafiya.
Tako wanne fanni yana jin zahran ta cancanci ayi mata kowanne iri so,don
dan xamansu da 'yan satittika yasa ya gama fahimtar wacce irin macace ita,ta dauki
dukka halayen umminta wajen biyayya wa miji da iya kula dashi,wani irin salo da
yake da tabbacin wasunsu ta samosu ne daga wajen hajja,wanda sau tari akwai
lokuttan da zai samesu suna hira da ita,tana bata labarin yadda mata ada ke
biyayyawa miji ba irin matan yanzu ba.
8:30 pm
A nutse take kai kawo tsakanin kitchen da parlour tana shirya masa abinci,duk
inda ta gifta idanunshi yana kanta,shigar da tayin ta dauki hankalinsa matuqa da
gaske,duk sanda xata gifta saita bar masa qamshinta,bai taba zaton mata nada son
turare haka ba sai da zahran ta kasance matarsa.
Kamar yadda ya fada din kuwa tare suka tsara komai,kamar yadda yake kama
mata aikin gida haka yake tayata karatun jarrabawar,bata taba tunanin haidar din
gifted bane,mai matuqar ganewa tarin basira da kuma dabarun koyar da karatu,bata
taba marmarin karatu ba,bata taba jin karatun jarrabawa me dadi ba,wanda babu ginsa
ko qasawa a ciki ba sai wannan karon,yasan tarin abubuwa game da abinda ta karanta
din,idan tace ta gaji yasan yadda zai mata ta samu relief su dora daga inda suka
tsaya,su huta suyi bacci su tashi suci gaba,yace so yake ta fita da sakamako mai
kyau wanda zata bar tarihin cikin makarantar,kamar yadda shima yabar tarihi cikin
tashi makarantar daya gama.
Yana tsaye daga saman dining yana hada musu tea shi da ita a cup
biyu,yanayi yana duba agogo,a shirye yake tsaf cikin wata dakakkiyar shadda sabuwa
fil ruwan zuma,wanda saida aka sha daru shida zahran tashi kafin ya yarda ya
sanyata,shiri ne na tafiyarsu jarabawa a rana ta farko,ya sake daga kansa yana
duban hanya,sai gata ta fito dauke da plate a hannunta,sanye take da wani
lafiyayyen lace itama ruwan zuma,dinkin riga da plain zani,sabida yace bai yarda ta
saka skert ba.
Duban fuskarta yake sosai,tana tahowa inda yake din tana yatsina fuska
"Yau wani laziness kikeji hubby,kodai exam dince tun kafin a fara take
bugunki?,karki fa damu,ina da zato mai qarfi a kanki,kisa a ranki an gamata kawai"
ajjiye plate din tayi a gabansa,ta hade hannayenta waje guda 🙏🏽
"Bani da haufi tsoro ko shakka indai sojana yana kusa....mutumin dake iya kula da
qasarsa ma bare ni mutum daya?,....na yadda da kaifin basirarsa,hakanan inda malami
ne shi xaiyi wuya a sami malami kamarsa kaf qarninsa kuwa,koda bayan mutuwarsa ne
da shekara dari" wani kallo ya kafeta dashi,yana jin kamar ya hadiyeta,gwana ce
wajen iya tsara kalaman da zasu tafi da hankalin dukkan mai hankali,ya rasa amsar
da zai bata illa tukuicin lallausan murmushinsa,wanda ya jima yana shaida mata ya
tanadeshi ne kawai saboda ita,ta kuma yarda da hakan dari bisa dari,don takanyi
mamakin yadda yake komawa zakin gaske a gaban duk wata mace koma bayanta,hatta da
qannensa shakkar nan tasa tana cikin zukatansu
"Kawai dai qwan nan ne,tunda na fara soyashi zuciyata ke tashi...." Ta amsa mishi
tambayarsa ta farko sanda take daukar cup din tea din daya miqa mata,idanu ya kuma
zura mata yana karantarta sanda take kurbar tea din,har sai data lura,saita dage
masa girarta dukka biyun,alamun tambayar lafiya?
"Anya ko hubby....anya ban jefa qwallona a raga ba?" Ido ta fiddo tana aje cup din
"Bana tunanin haka.....haba watanmu nawa sojana....kawai ko a gida banson qarnin
qwai,kuma ko xanci ma saina yanka wadatacciyar albasa akai nake ci" kafadunsa ya
dage yana bude plate din chips da qwan data aje masa
"Ohkey....amma ko chips din ai kyaci ko?" Fuska ta kyabe cike da shagwaba tana
maqale kafada
"Nifa qamshinsu ya gama cikamin ciki.....saidai ka taimaka ka siyamin meatpie a
wannan gurinnnnn" dariya taso bashi,tunda ya taba siya mata meatpie din ta maqale
masa,saiya maqale kafada shima
"Naqi wayon,saidai idan kin yarda nima....." Qarshen zancan ya furta mata qasa
qasa,sarai ta gane abinda yake fada,saita sakar masa kukan shagwaba,ta dauke hand
bag dinta dake gabansa ta sauko daga dining din tana diddira qafa,dariya sosai
yakeyi shima,ya aje abincin ya biyo bayanta.
Har suka je suka dawo yana tattalinta,suna gama exam din ta zagaya inda
ya zauna zaman jiranta ta sameshi,bata yarda kowa ya biyota ba,ya gama ganeta amma
tana togewa,kishinsa take hakan ya sanya bata hada kowa dashi.
Randa sukayi paper din qarshe ta dinga jin jikinta sama sama,haka dai ta
daure akayi sallama da qawaye da abokan karatu,ko cikin mota ma cikin seat ta
lafewa haidar din,daya tambaya tace babu komai gajiya ce,bai gasgatata ba amma ya
qyaleta,saboda ya lura kaman batason magana ne,zatonsa bai tabbata ba sai da suka
bude falo zasu shiga,saita tafi luu zata fadi ya tarota,ya qarasar da ita saman
kujera yana mata sannu,gaba daya ya rude cikin qanqanin lokaci,ruwa ya bata mai
sanyi tasha,sai numfashinta ya koma normal
"Sannu"
"Lafiyata qalau" tayi qarfin halin fada,saboda zallar damuwar data hanga tattare
dashi
"No hubby....baki da lafiya" don kada tayi masa musu kota bata masa lokacima yasa
bai tsaya sauraren kalaman bakinta ba ya dauketa cak sai bandaki,ya ajjiyeta sannan
ya tara mata ruwan wanka
"Ki wanka na baki minti goma,zan shirya na kaiki kiga likita" saiya fiddo mata
towel soson wanka da sabulun wankan ya aje mata,sannan yaja mata qofar ya
rufe,saiya wuce daya bandakin shima.
Idanu ya zuba mata sanda ta gama shirin ta fito,saiya riqe hannunta sosai
"Duk yadda kika kai ga boyemin baki da lafiya hubby bazai boyu ba,kin manta ne,ni
dake ruhi daya ne yake rayuwa a gangar jiki guda biyu?" Murmushi ta sakar
masa,saiya karata da jikinsa suna takawa a hankali yana sake gaya mata wasu kalaman
da suka sanyata sakin ajiyar zuciya a jejjere.
A qalla ya kusa minti talatin zaune shida ita cikin motar riqe da
hannayenta yana jero mata kalaman nuna zallar qauna da godiya a gareta,tun lokacin
da likitan ya shaida masa tana dauke da juna biyu gaba daya yayi wani irin
rudewa,ko a yanzun ma hawaye zahran ke futarwa,saboda kalaman da yake amfani dasu a
kanta sun girmi kanta,kalamaine da take da cikakken yaqinin ba kowacce mace bace
Allah yake mata baiwa da samun mijin da zai furta mata su ba
"Gobe as early as possible zamu wuce abuja...thank god kin gama abinda ya zaunar
damu,kinji kuma yace kin da buqatar cikakken hutu,so zan buqaci hajja kawai ta bamu
baba gaje mu wuce da ita....but...banda fadar dalili,don i sure tsaf hajja zata
hanani tafiya dake" dariya sosai ya bata data tuna da hajjansu,hajiya hajja,ayi
tsiya ayi dadi,tana sonsu tana tattalinsu,amma idan tsiyarta ta tashi har su saita
dandana musu.
Kamar yadda ya tsara kuwa tun a daren ya gama hada musu abinda yasan suna
da buqata,ba wasu kaya bane masu yawa,tunda komai a kwai a can,ya kira hajja yace
baba gaje ta shirya gobe zata rakasu abuja,ta fara masa tambayoyi yace ta bari idan
yazo gobe zasuyi magana,ranar kusan kwanan zaune yayi,rabi bacci rabi idanunsa
biyu,duk sadda ya farka saiya tuna cewa wai shima ya kusa zama uba?.
Shida ita a baya suka zauna,don bazai iya juriyar awanni suna waje daya
amma ba ita a gefansa ba,baba gaje da driver suna gidan gaba,hakan ya baiwa zahra
damar kwanciya sosai bisa jikinsa,don sam bata jin qwarin jikinta,shi kuma ya
tattarota cikin jikin nasa sosai,ya gyara mata yadda zata fi jin dadin kwanciyar.
Zuwansu da baba gajen ba qaramin ma'ana yayi ba,domin itama ta hangi abinda
hajjan ta hanga,duk da basu gaya mata ba,don haka bata barin zahran tayi
komai,komai na gidan ta dauke shi,ita kanta zahran ba qaramin dadin zama da baba
gajen takeyi ba,tana debe mata kewa,hakanan duk randa ta tashi jikin babu dadi zata
gaya mata wani abu da zatayi wanda zaisa taji sauqi da qwarin jikin nata.
Ta fannin haidar kuwa ta samu dukkan wata kulawa taimako da qwarin gwiwa a
matsayinta na mace mai haihuwar fari wadda batasan yadda abun yake ba,shi kansa bai
barinta tayi wani abu da zai wahalar da ita,ta kowanne fanni ta zama 'yar lele ta
gaske.
Hajja batasan da zaman cikin ba,sai sanda ya samu hutu na sati guda,yace
su shirya suje kanon su roqi hajja tabar musu baba gaje,a lokacin cikin nata ya
shiga wata na uku,kuma ga duk mutum mai saurin tsinkaye da daukar haske zai fahimci
akwai ciki tare da zahran,tayi wani kyau,hakanan ta sake cika,fatarta ta qara
haske,sau tari haidar kan sanyata gaba da tsokana,ya hanata sakat,bini bini yana
shafa fatarta,idan tayi qorafi sai yace
"Ke dince ki qara wani kyau,fatarki kamar atafa,karfa nan gaba na soma kasa gane
hanyar fita daga gida,ko naje nayi shirme gaban manya ki jawomin hukunci" saita
tureshi tana tura baki,sabida ita gani take kamar tsokanarta yake,don rannan daya
goyata ya zagaya da ita cewa yayi ta sauka,ta fara ninka nauyinta,sai data dinga
masa kukan wasa sannan kuma ya lalace wajen lallashi da bata haquri,ire iren
yanayin rayuwarsu kenan,idan ka ganshi a cikin gida saika rantse da Allah ba ALIYYU
MAS'UD DABO bane,sojan nan daya kasance dodon 'yan ta'adda da marasa gaskiya dake
cikin qasar nan,idan ka ganshi a waje sanye da kaki ba zaka ce zaka sameshi a haka
cikin gida ba.
Tsaye suke cikin dakin hajja,taja rungume cikin jikinsa saidai ya rungumeta
ne ta bayanta saboda tsinin cikinta wanda ya dora dukka hannayensa biyu akai,yana
jin yadda yaron cikinta ke motsawa,kai kace zai fasa cikin ne ya fito,bai dauke
hannun ba har sai daya tsagaita da motsin,suka saki ajiyar zuciya shida ita a
tare,sannan ya juyo da ita suna fuskantar juna.
Tausayinya yakeji fiye da kima,koda can shi mutum ne mai tsananin tausayin
mace,macen ma ace mai juna biyu,yau saiga abuj cikin gidansa,a jikin mace mafi
soyuwa duk duniya a wajensa baya ga iyayensa
"Banda hajja ce hubby duk duniya babu wanda ya isa ya sanyani na wani kawoki wankan
gida" murmushi ta saki,ta sanya hannunta tana shafan kwantaccen gashin fuskarsa da
ko yaushe yake qara masa kyau da kwarjini
"Kasan dai hajja ta fimu damuwa da kwanunanmu....sannan tun ban dade da shiga third
trimester dina ba tace ka dawo dani gida,yanzu idan baka kawoni ba zataga cewa
kamar bata isa damu bane,bayan ina da tabbacin cewa tayi hakanne saboda amfanin
kanmu" fuskarta ya riqe tsakiyar hannunsa,ya matso da ita dab da tashi,cikin
softness yace
"Hubby....inason in zama mutum na farko da zaya dauki 'yarshi" yatsanta ta dora
saman lips dinsa tana cewa
"Shshshs.....point of correction.....soja nakeso na haifa,jarumi kamar kai....mai
kuma kama dakai" dagowa yayi yana murmushi,ya kama hannayenta duka ya riqe cikin
hannunsa
"Little zahra ni kuma nakeso.....kuma inaji a jikina itace"
"Ok....ok,ba anyi yarjejeniya ba akan a bari har sai ranan?,duk wanda yayi wining
zai zaba abinda yakeso mutum ya bashi..."
"Yes hubby" ya fada yana lakace hancinta,saita jefa masa harara
"Ka takurawa hancin nan nawa" dariya sosai ya saki yana cewa
"Ya qara kyau ne,kamar na dauke kayana na tafi dashi" tasan cewa girma ya qara fiye
dana da,amma ba zai taba fitowa ya gaya mata hakan ba,saidai kullum idan ya dameshi
da cewa hancinta yayi qato ko yayi muni sai yace mata suyi musanye da nata,ko ta
bashi kayanshi yana so shi a haka.
Rigima ta soma yi masa kan ta gane dariya yake mata saboda tayi
muni,lallashin duniya taqi shuru saboda bai daina dariyar badai,har sai da hajja
tazo ta tankada qeyarsa sannan aka samu salama.
_zan qara kwana daya ko Allah zaisa ina da rabon ganin baby na,but please kada ki
sanarwa kowa_
A falon tayi kwanciyarta suna hira da hajja,jifa jifa tana cije lebe idan
aka mintsineta,saita dinga mamaki,don bata taba ciwon mara haka mai naci ba kamar
nayau,ana mintsinarta amma da tayi daya biyu uku a rana shikenan sai washegari,amma
nayau din yaqi barinta batasan dalili ba.
Ciwon bayan da taji yana yawa saita koma daki da niyyar kwanciya ko zai
ragu,saidai tana shiga kamar an dado ciwon ne,tayi tayi ta zauna ta kasa qafarta ta
riqe gam,dole ta dinga qwalawa hajja kira,sai gata bagatatan ba shiri.
Tuni ta fahimci haihuwa ce,ta aika umaima ta kira mata mamarta matar abban
tsakiya,ta sanya ilham kuma ta shiga tsohon dakin zahran ta dauko kayan da aka ware
don tafiya asibiti.
Kafin ilham ta dauko kayan maman umaima ta qaraso ciwon ya ta'azzaran
mata,ta kasa tafiya bare akai ga batun zuwa asibiti,don haka hajja tace adan dakata
ko zai lafa mata sai a tafin,saidai ina,gaba kawai ciwon yakeyi,wanda harta kasa
jure masa tana neman taimako,baba gaje da kuma hajjan su suka riqeta lokacin da
suka fahimci haihuwar tazo gadan gadan,cikin ikon Allah da taimakon addu'a cikin
mintunan da basu wuce uku ba kukan jariri ya karade sassan hajjan gaba daya.
Kusan tare suka saki ajiyar zuciya ita da hajjan,farinciki mara misaltuwa
ya sauka a zukatansu gaba daya,hajjan ce da kanta,duk da tsufa ta dauke yaron
daketa watsal watsal cikin qazantar da suka fito tare yana canyara kuka,ta kasa
daurewa saidata rungumeshi cikin jikinta qwalla na gangarowa daga idanunta
"Alhamdulillah....alhamdulillah" shine kawai abinda yake fita daga bakinta,sannan
ta qarasa dab da zahran ta dora mata yaron saman cikinta tana shafa sumar kanta
"Sannu takwarata,sannu da qoqari,barka da arziqi" saita lumshe idanunta cikin
matuqar jin kunya,gefe guda na zuciyarta farinciki na mamayeta,idanunta kan fuskar
yaron,fuskar da ko ba'a wanketa ba ta bayyana kamar ya Aliyyunta daya dauko,sak
shi,kamar kaki yayi ya aje,take wata qauna irin wadda ubangiji S W T yake dasawa a
zukatan bayinsa tsakanin uwa da ɗa ta fara kwaranya a zuciyarta.
Kafin kace meye wannan labarin haihuwar ya zaga gidan,tuni aka soma gyaran
zahran da jaririnta,cikin qasa da awa guda tayi wankanta da ruwan dumi,an goge
yaron da kyau,an gyara mata dakin hajjan yadda zai dace da yanayin jaririn,hajjan
tasa an dora mata kunu bayan ta soma da bata tea mai uban kauri da bournvita saboda
ruwan nono.
Sau wajen biyar yana attempting bude gidan nasa ya shiga sai yaja tsaki ya
fasa,yayi imanin koda ya shiga baqiqqirin gidan zai masa,bazai ma iya zama
ba,saboda babu fitilar gidan,daga qarshe kamar wanda ake umarta,yaji kawai
zuciyarsa ta yanke masa ya koma gidan hajjan ya wuni da zahran,idan yaso idan dare
yayi ma ya bude tsohon dakinsa na gidan yayi kwanciyarsa,duk da babu komai yanzun a
dakin sai katifa,ya tabbatar sai yafi samun relief akan ya kasance tana nesa dashi.
Tunda ya doso gidan yaji gabansa yana faduwa,sanda shamsu ya bude masa qofar
gidan ya ga kamar yanason magana dashi,amma bai tsaya ba sai daya isa inda suke aje
motocinsu,yana kashe motar kuma yayi sassan hajjan.
Sanda ya shigo yayi dai dai da lokacin da jaririn ke kukan neman nono,baba
gaje na kan zahran tana gwada mata yadda ake feeding yaro,tana ta dariyar rashin
sabo irin na zahra
"Saiko kin dage,don na fuskanci me gidan nawa acici ne".
*_TAMMAT BI HAMDILLAH_*
_Kada ki sake,kada ki bari damuwar wani d'a namiji ta hanaki sukuni,kada ki bari
damuwar wani saurayi daya yaudareki tasa ki tsaida taki rayuwar cak,bayan shi yana
can yana tashi rayuwar_
_sau tari abinda kake so saiya zamana ba shine alkhairi a tattare dakai ba,abinda
kake gudu kuma shine alkhairi a tare dakai ba tare daka sani ba_
_zama mai hankali ta hanyar zurfafa tunaninka,kada ka yarda ka yankewa wani dan
adam hukunci ba tare daka mu'amalanceshi ba,kada ka yarda ya fadi halin wane bayan
baka zauna dashi zama na gaske ba_
_koda yaushe ka zama mai kyautata zatonka ga mutane,sai gobenka tayi kyau_
_MAZA kuji tsoron Allah,nasan bazan aureki ba,to bazan soma tsayawa zuwa zance
wajenki ba,kona bata lokaci kan layin waya ina qona miki kati ko ina qona nawa
katin ba,ina bata miki lokaci,ina dauke hankalinki daga kula maza 'yan gaske masu
niyyar aurenki ba,KADA KU MANTA KAI YAYA NE,WATARAN KUMA UBA NE!,ZAKA HAIFA KO A
HAIFA MAKA!,AKWAI KUMA HISABI,ALLAH BAYA QYAKE HAQQIN WANI AKAN WANI TUN NAN GIDAN
DUNIYA_
*_muna miqa saqon godiya da jinjina a gareku masoya kuma makaranta litattafan
zafafa,wadanda a kullum basa gajiya da sanya kudadensu su siya rubutunmu,ubangiji
yabar qauna_*
*_muna neman afuwan wanda muka batawa,ko wanda muka yiwa ba dai dai ba,ko labarinmu
ya batawa,ko bai masa yadda yaso ya kasance ba,dukkanmu ajizai ne,duk inda ajizi
yake kuwa saiya nuna ajizancinsa_*🙏🏽
*_kurakuran dake cikin rubutunmu muna fata Allah ya yafe mana,ya bamu ladan dake
ciki_*
*_ubangijin ya sadamu a rubutu na gaba,ya bamu aron rai da lafiya,yaci gaba da riqo
da hannyenmu,ya kuma bamu damar rubuta abinda al'ummar annabi muhammadu zasu amfana
dashi_*