Trump na nazarin kai hari kan yan ta'adda a Mali
July 29, 2026
Tambayar ita ce: Shin irin wannan mataki zai rage barazanar ta'addanci a yankin Sahel, ko kuwa zai kara rura wutar rikicin da tuni yake kamari?
Tsawon shekaru kenan Mali ke fama da hare-haren masu tsattsauran ra'ayi da ke ikirarin jihadi, kuma har yanzu an kasa gano bakin zaren warware rikicin balle nasarar murkushe su. Bayan janyewar sojojin Faransa da kuma hadin gwiwar da Mali ke yi da Rasha, kungiyar Jama'at Nusrat al-Islam wal-Muslimin ko kuma JNIM ta ci gaba da kara karfi da fadada tasirinta.
An kafa kungiyar JNIM a shekarar 2017, kuma ta hada kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi da dama karkashin inuwar Al-Qaida. A yanzu ana kallonta a matsayin babbar barazanar tsaro a ilahirin yankin Sahel, inda ta mamaye wasu yankuna, tana karbar haraji, tana sasanta rikice-rikicen cikin gida, har ma a wasu wurare tana da tasiri fiye da gwamnatin Mali.
Rahotanni sun ce a shekarar 2025 kungiyar ta haddasa mutuwar fiye da mutum 1,200, lamarin da ya sa ta zama daya daga cikin kungiyoyin ta'addanci mafi hadari a duniya. Rikicin da kazalika ya bazu zuwa Burkina Faso, da Nijar da wasu kasashen gabar tekun yammacin Afirka.
A gwamnatin Amurka dai akwai sabanin ra'ayi kan matakin kai hare-haren soja. Masu goyon baya suna ganin dole ne a kawo karshen JNIM. Masana kuma sun ce dabarar tsaron Rasha a Mali ba ta kawo sakamakon da aka sa ran samu ba, domin kungiyar JNIM ta fi karfi yanzu fiye da shekarun da suka gabata.
A nata bangaren, gwamnatin Mali ta ce ba ta da tabbacin cewa Amurka za ta kai hare-hare. Ministan harkokin wajen Mali, Abdoulaye Diop, ya jaddada cewa kasar na dogaro da dakarunta da kuma kare 'yancin kai, ba wai tana jiran wasu su zo su magance mata matsalolinta ba.
Ra'ayoyin jama'a ya kasu biyu. Wasu na cewa duk wani matakin da zai kawo zaman lafiya abin maraba ne. Wasu kuma suna ganin idan har Rasha na kasar, zuwan Amurka ma ba zai zama matsala ba, muddin zai taimaka wajen yaki da ta'addanci.
Sai dai masana sun yi gargadin cewa hare-haren soja kadai ba za su magance matsalar ba. Sun ce idan fararen hula suka mutu, hakan na iya bai wa JNIM damar samun sabbin magoya baya. Haka kuma matsalolin da suka haddasa rikicin, kamar talauci, rashin ingantaccen shugabanci da rikice-rikicen kabilanci, za su ci gaba da wanzuwa.
Masana sun kuma bayyana cewa duk wani matakin soja da Amurka za ta dauka zai kasance yana da alaƙa da gasa tsakanin Amurka da Rasha wajen fadada tasiri a yankin Sahel, ba wai yaki da ta'addanci kadai ba.
A karshe, masana sun jaddada cewa ba za a iya kawo karshen rikicin Mali ta hanyar amfani da karfi kadai ba. Sun ce dole ne a hada yaki da ta'addanci da inganta shugabanci, gina cibiyoyin gwamnati da samar da ci gaban tattalin arziki.
Har yanzu dai ba a tabbatar ko Amurka za ta kai hare-haren ba. Idan Trump ya amince, Mali za ta zama kasa ta takwas da Amurka za ta kai hari cikinta tun bayan fara wa'adinsa na biyu.