FIFA: Guguwar sauyi na neman tafiya da Infantino
August 5, 2026
Talla
Tun da fari dai, tsohon manajan Arsenal, Arsène Wenger, ya nesanta kansa dangane da wannan dambarwa, inda ya ce ba shi da hannu a shirin kafa kamfanin masu neman zuba jari a hukumar. Shirin ya haɗa da sayar da kashi 20 cikin 100 na kamfanin ga masu saka hannun jari, lamarin da ya fuskanci adawa mai ƙarfi daga UEFA da sauran kungiyoyin kwallon kafa ta duniya.
Karin bayani:FIFA ta yi amai ta lashe kan shirinta na sayar da hannun jari
A halin yanzu dai, ƙasashen Afirka da Kudancin Amurka da Oceania na ci gaba da mara wa Infantino baya, yayin da ƙasashen Asiya ke nazari wajen tantance makomarsa. Wasu ƙasashe irin su Qatar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa sun nuna goyon bayansu ga Infantino.